Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ya haifa a cikin yayansa mata, a hanyata ya tafiya aka fara ruwa daman hadari ya gama rufe garin kaduna a wacan lokacin... A hanyata ta tafiya na hango wata mata tare da danta sun fake a wata kazantaciyar tumfa, yana daya daga cikin halina taimakon mai rauni a duk lokacin da na samu hali, and it does not matter if musulmi ne ko ahalul kibat, a nan na gagara wucewa na matsa kusa da inda matar take na faka motata na fita sai na same ta tana ihu da dukannin karfinta, ashe nakuda take a gurin tana dauke da tsohon ciki ne, ga kuma danta da ya kasance marar lafiya, "Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke?" Haka na jera mata tambaya ina leken fuskarta, sai ta kalleni amman bata iya magana ba sai dai ta kalleni a lokacin ta mika hannayenta ta riko hannuna. "Subhanallahi... Christen ce ke?" Na tambaya domin na lura da sarkar cross din dake wuyanta, sai na yi cire hannuna hannayenta, a kokarin yin haka agogon hannuna silver color ya zame ya tsaya a hannunta, sai ta jimke agogon tana cizon baki tana nishi mai karfi alamar tana jin zafin ciwo, hakan ya saka ban yi yunkurin karbarsa ba. "Am... Akwai wanda kika sani nan kusa?" Na sake tambayarta sai ta girgiza min kai alamar aa, "Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan..." Na tambaye ta, kamin na dagata na sakata a motata ina istigifari. "Allah ka yafe min wannan ba da niya na aikata ba" Na saka danta na tuka motar ina tafe ina mata sannu har muka isa asibiti, na bada damar ayi mata komai a cikin aljihun familynsu domin asibitin da na kaita kamar ta gidanmu ce, a nan na barta na tafi gurin mahaifina, bayan na dawo sai a aka samu bata dakin da aka aje ta ta gudu ita da yar da ta haifa da danta kamar yadda suka fada min, tun daga ranar ban sake ganinta ba, abun da kawai zan iya tunawa a game da ita ita wacan tana da jiki fara ce sol kamar baturiya, tana jan gashin kai da blue eyes. Fatan kin isa gida lafiya... Ta lumshe ido hawaye na cika fuskarta, jikinta kuma yana ta bari mazari, abun da ya rubuto mata a yanzu shi ne abun da ya faru a wacan lokacin da ta rike a zuciyarta saboda taimakon da yayi mata har ta rayu ta kawo labari yanzu... ALIYU POV. Ya dago daga jikin karfen dage gabansa yana slipped tea dake hannunsa. Mamaki yake yadda time yake gudu kamar jiya komai ya faru amman gashi yanzu lokaci yaja. Yayi murmushi at least ya ceci rayuwa har biyu, ta Emily da kuma Fatima, sai a yanzu yake mamakin kansa na rashin ganeta da be yi ba tun farkon ganinta, ko da yake kamaninta sun sauya yanzu, a baya tana da jiki yanzu kuma babu yanzu ta zama yar kwalliya ba kamar so acan karon da ya ganta ba. Sai dai ko a lokacin da yake ganinta a gurin aikinsa yana ji a jikinsa kamar ya santa ko ya taba ganin wata mai kama da ita, ashe ma matar abokinsa ce ya taimaka a wacan karon kuma yar abokinsa ce ta ceto... "Subhanallahi" Ya fitar tare da iskar bakinsa, amman taya Turhan ya bar har ta fada a wannan halin dauke da cikinsa? Lallai akwai alamar ta tayu da kalubale a zamansu, shiyasa ta yi ma yarta karyar cewa bata da mahaifin, kuma take gudun ya dawo rayuwarta a yanzu. Ya dago wayarsa ya fita daga sashen sakon ya shiga sashen kiran waya ya kira matarsa yana jin cewar shi kam sam ba zai taba iya wulakanta matarsa ba kamar yadda Turhan yayi. Wayar na daf da tsinkewa ta amsa cikin wata murya dake bayyana damuwarta. "Salam..." "Hello Dear, yanzu nake son na kiraka na san ranka ya bace dan Allah ka yi hakuri da abun da ya faru" Yayi jimmm domin be san da faruwar komai ba. "Me ya faru?" "Kayan da aka kawo ne Hajiya ta sa aka maida wai yayi kadan" A take fuskarsa da zuciyarsa suka rikedewa zuwa bacin rai. "Kameela ya kamata ace muna lurar da iyayenmu inda ya kamata su kyautata ko su daga kafa, Ina sonki kin sani amman duk wani abu da zai munanawa iyayena ko ya zama cin mutunci a garesu ba zan jure ba, ban san Ummi ta aika miki da kaya ba sai da kika kirani dazun kika fada min, na kira na yi mata godiya, ban san komai akan al'adar haihuwar mace idan ďa ya zo ba rai ba, duk abun da kika gani kokarin Ummi ne, ina son wannan abun ya zama na karshe" "Yadda kake son iyayenka kake gudun bacin ransu haka nake gudun nawa, ai kasan dai ba zan taba bada go ahead akan amai da kayan da har kiranka na yi ina maka godiya ba, iyayen ba yadda zamu yi da su sai hakuri, mu dai mun san muna son junanmu that's all, wacan a tsakaninsu ne, be kamata ya shafe mu ko ya shiga abun magana a tsakaninmu ba" Be sake ce mata komai ba ya kashe wayar, domin shi ba gwanin sa'in sa ba ne. Dawowa yayi cikin falon ya aje cup din hannunsa sannan ya kira Ummi ringing daya ta daga tana ta masifa. "Anya za a jure a auren nan na ku Aliyu? Har yaushe zaka je ka dauko mata a gidan kananan mutane da ba su san mutunci ba, a nemi wulakanta mu, kayan barkar da aka kai mata ne Hajiya Ramatu ta kira ni wai sun dawo da su, sun raina kenan ko? A gidan su waye za a kai kayan barka na mai jego kadai akwaiti goma ace an raina, alhalin ma ďa be zo da rai ba" Ya sauke ajiyar zuciya. "Ki yi hakuri Ummi yanzu na kirata take fada min, kin yi kokari sosai, ita da kanta ta yaba shiyasa dazun na kira na miki godiya da abun da kika yi" "Akan su aka fara faduwa zabe ne? Kujerar sanata tuwon gidansu ne da za ace dole ko wane zabe sai sun ci? Yanzu saboda sun fadi Allah yace mahaifinka ne zai ďana sai abu ya zama dan zane? Har yana neman zama cin mutunci?" "Ayi hakuri Ummi In Shaa Allahu hakan ba zai sake faruwa ba" "A'uzubillahi wannan hassada ta yi yawa, idan son suke su kashe auren su aura mata Governor su sani dai yarsu ba daraja zata yi a idonsa yanzu ba, kuma wahala kawai zata je ta sha da wannan bakin kishin nata, kuma ya ma yi aurensa me zai yi da ita yanzu" "Ummi kin hau da yawa, Allah ya huci zuciyarki amman dai idan tunaninsu kenan sun yi kuskure domin babu saki tsakanina da Kameela, ko ba ita ba daman na kudurta a raina duk abun da zai faru ba zan taba iya sakin matata ba, kuma na mata magana In Shaa Allahu irin wannan ba zai sake faruwa ba" "It better, domin na fara gajiya sai kace kansu aka fara siyasa, shekara nawa Engr yana hakurin faduwa zabe sai bana dan Allah ya ba shi sai kuma su juyar da siyasa kiyayya" "Ummi ayi hakuri" Ta masa kwatankwacin abun da yayi ma Kameela, ita ta kashe wayar a cikin fushi. Ya sauke ajiyar zuciya. "Daddy ma lalabawa yake da Ummi, balle ni da nake ďa, iyayen Kameela suna neman kunno min wuta" Ya fada cikin yanayin damuwa. Sai bayan bayan sallah magariba Kameela ta kira shi tana bashi hakuri suka jima suna waya, yawanci abun da take bincikarsa na ina yake cin abinci ne sai kuma inda yake zuwa yanzu da bata gidan. "Ina zan je? Ina gida mana" "Yaushe zaka zo" “Soon" "So soon" "Not so soon" "Okay, ka kula min da kanka, kuma dan Allah kar ganin bana nan ya saka ka rika kula mata ko kallonsu" Yayi murmushi kawai ya girgiza kai. "Toh ranki ya dade" Ta yi dariya, ya mata kiss a wayar sannan suka yi sallama. KAMEELA POV. Tana sauke wayar Farida ta shigo kiranta wai Abbansu yana son ganinsu gaba daya a bangarensa, haka suka dunguma gaba daya suka tafi bangarensa suka zauna har Mama Barakat da Kameela ke ta harara. Alhaji Tukur Nazifi Ataka ya fara kallon Hajiya Asma'u ya ce. "Waya ce a mai da kayan barkar da aka kawo?" "Alhaji ba fa wani kayan kirki bane, kamar gidan nan za a kawo kayan barka akwaiti 10, ko ya muke riko a gidan nan ai ta fi karfin haka balle kuma jininka, da gangan suka yi saboda su walakanta mu" A take Alhaji Tukur tsohon sanata ya rufe ta fada. "A wane dalili za a maida? Idan ma sun yi ne saboda abun da kike tunani miyasa za ki fiye masu? Wannan ai rashin dattako ne, kuma ba kowa ya janyo ba sai Kameela, su basa tunanin komai sai soyayya, gashi nan tun ba aje ko'ina ba sai abubuwa ake samu na rashin jindadi, toh daga yau sai yau kar a sake aiko wani abu daga gidan Bappa Mudallab a maida shi, ko ba can ko daga ina ne kar hakan ya sake faruwa" Ya kalli yaransa daga mazan har mata a fusace ya ce. "Ku kuma a cikinku kar wanda ya sake dauko ya ko dan makiyinmu yace sai zai aureshi last warning, shiyasa na tara ku a nan" Mama Barakat ta ce. "Alhaji ayi hakuri, kar a bari siyasa ta yi tasiri akan rayuwar yau da kullum, na san faduwar nan bata yi ma kowa dadi ba, amman kar a hana yara abun da suke so" Hajiya Asma'u taja tsaki. "To ke me kika sani a siyasa Barakat? Da har zaki fadi haka? Siyasa ai mu muka santa ciki da waje, domin Alhaji tun yana ba shi ba nake fadi tashi da shi akan siyasa har ya zama wani abu a yanzu" Alhaji Tukur ya kalli Hajiya Asma'u domin ya san da biyu ta fadi maganar. "Me ya kawo wannan maganar yanzu? Ku tashi na sallami kowa" Mama Barakat ta yi murmushi ta mike tsaye ta fice daga dakin, Hajiya Asma'u ta watsawa bayan Mama Barakat harara ta jin haushin yadda take karkada mazaunai kai kace da gayya take yi. (Mtssss kayan kashi) ta fada a ranta sannan ta mike tsaye suka fice ita da yaranta. ALIYU POV. A yau ya shigo aiki da wuri domin gidan yayi masa ba dadi, saboda hatsaniyar da aka samu tsakanin iyayensa da na Kameela gashi kuma Kameela bata gidan baya jin motsin kowa sai hakan ya saka shi jim gidan yayi masa girma. A nan yayi breastfeed yana gamawa ya kira Kameela suka gaisa ya ji tashinta, a nan ta saka masa kukan yaron da ta haifa ya koma, wai sai a yanzu take jin babu dadi abun yana damunta har mafarki take. Rarrashinta yayi ta yi sannan suka yi sallama, ya dauko qur'anensa dake office din yayi karatu daidai gwargwadon yadda zai iya sannan ya aje bayan yayi addu'a ya amsa kiran Turhan dake shigowa wayarsa ta WhatsApp video call. "Salam.." "Hey Aliyu ya gidan ya aiki?" "Lafiya kalau, ya Ammy?" Aliyu ya tambaya yana karantar ramar da abokinsa yayi. "Tana kaduna" Yanayin yadda ya amsa masa ne ya bashi tabbaci ya bar kasar. "Ka koma Sudan ne" "Eh jiya, abun da naje nema ban samu ba, still Ammy bata duba hakan ba, anyway na kira ne na maka barka matar ta haihu ashe?" "Eh amman yaron be zo da rai ba" "Eh Allah ya baku hakuri, kara kai ai kana haihuwar ba kamar ni ba, ban ma san ya ake ji ba idan aka rumgumi yaro" Tausayinsa kadan ya fada zuciyar Aliyu. "Kai ma wata rana zaka rumgumi yayanka In Shaa Allahu" "Ina fatan haka, agaishe da Madam" "Zata ji" Daga haka suka yi sallama, Aliyu yana jin kansa kamar wani mai laifi, meyasa Emily zata daure shi har haka? Ya kasa fadawa abokinsa a inda take tare da yarsa. Ya dago yana kallon kofar dakin da aka kwankwaso. "Yes" Nick ya shigo ya sanar masa Emily tana son ganinsa, Aliyu yayi shiruuuu yana kallon wani gurin kamin ya bash izinin shigowa da ita. Ya mike tsaye ya nufi windows din office din ya bude ya tsaya a gurin yana kallon kasan benen. Emily ta turo kofar office din ta shigo tana sanye da short gown black color gaba daya ta daure gashin kanta a baya tana rike da makulli mota da wayarta, sai kuma agogonsa a dayan hannunta. Ta dade tana kallon bayansa sannan ta matsa kusa da teburinsa ta dora agogon. "Zumudin zuwa ganin mutumen da ya taimake ni a yau, be bar ni na runtsa ba, da na zo ban san office din ba da tambaya na kawo kaina a nan. Kullum mafarki da buri na yadda zan maida alherin da aka yi min ne da alheri, na kasa manta yadda ka ceto rayuwata, a lokacin da ba ni da kowa babu mai taimako na, Vito yana yawan cewa na jefar da agogon nan ko na manta da shi, sai na fada masa indai har zan iya manta alheri to zan iya mantawa da agogon, manufar ba ta agogon ba ce kawai, ta mamallakinsa ce, ashe kuma na aje kwarya a gurbinta ne, ashe dai ka cancanci ko kasa ka taka na jimke na aje" Ta share hawayen idonta. "Ka taimake ni a lokacin da iyalinka da kai kanka kuke neman taimakon juna na karfafa guiwa, baka damu da addinina ko kazantar da take jikina ko ciwon yarona na ba ka taimake ni, hakika Aliyu kai mutumen kirki ne, kuma na yarda a ciki musulmai akwai na gari" Sai a lokacin ya juyo ya kalleta kallo daya ya dauke idonsa. "Duk abun da na yi na yi ne saboda Allah" "Fada min me zan yi na rama daya bisa ukun abun alheri da ka yi min?" Ya nuna mata kujera sannan shi ma ya zauna. "Wacece ke? Tun farkonki har zuwa yau, yadda kika hadu da Turhan har zuwa rayuwarki ta yanzu, shi kawai nake da bukata a gurinki yanzu" Ta nuna kanta tana hadiye bakin cikin daya tsaya mata. "Ni... Ńi ni ce kawai, ni ce wata yarinya data tashi a gidan marayu bata san kowa ba sai kanta da mafarkinta..." Taja numfashi ta lumshe ido, Aliyu ya kalleta a karo na biyu kwarjin farar fata a cikin bakin tufafi ya cijeshi, ya dauke idonsa da hanzari ya maida akan agogon da ta aje masa. [4/28, 6:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣8️⃣ *June 4 2014* *Lagos State Nigeria.* *Little Saints Orphanage (ABULE EGBA HOUSE) 149, Carpentar B/stop, Ekoro Road.* *MAFARI...* Tafiya na ke a hankali ina kallon sababin talkamin da suke kafata wadanda wata kungiyar taimakon kai da kai ta kawo mana tun satin daya gabata. Talkamin sun min kyau sosai a kafa kamar daman dan ni akai su. "Emily.." Ina jin muryar mai kiran na juyo fuskata ba yabo ba fallasa na kalleta. "Ibo lo lo?" Ta tambayi gurin da zanje da yaren da mafi yawan marayun da suke zaune a wannan gidan na marayu suka fi ji, wato yarbanci. "Mo n lọ si ọja lati ni awọn eso diẹ. kilo de ti o bere?" "Ohunkohun. irin ajo ailewu" "O dara emi yoo pada wa ni titọ" Na karasa amsa mata tare ta mikawa mai gadin gate din gaisuwa "E kaaro arabinrin" Sai ya amsa min da murmushi. "O dara, Ọlọrun yoo bukun fun ọ" "Amen" Da kansa ya bude min gate din duk kuwa da kasancesarsa dattijo, amman yana ganin girma da kuma mutunci. Wani dogon numfashi na ja na sauke sakamakon iska mai dadi da take kadawa, daga kaina nai sama ina kallon hadarin da ke haduwa a tsararin samaniya rana tana ta lumshi tana budewa gwanin sha'awa. Babu mutane sosai daman unguwar ekero road, kamar gra take abu ne mai wahala ka ci karo da hayaniya ko kaikawo na jama'a kamar cikin tsakiyar lagos. Mini skirt ne a jikina mai aljihu sai wata farar vest mai kama da ta kwana wuyana na sanye da sarkar cross hannuna ma yana rataye da warwaron wanda akai da farin dutse. Kitso ne jan gashin dake kaina, na yi parking dinsa da ribbon tsorayen sun sauko har bayana. Tafiya nake cikin natsuwa da aminci, zuciyata kuma nata rara min wakar da muke a coci duk da kasancewar bana jin natsuwa da da wakar amman sabo yasa ni yake jin dadinta. Sai da na fito daga unguwar gaba daya na nufi hanyar da zata sadani da wata karamar kasuwa da take layin. A bakin titi na tsaya sai da motocin suka gama wucewa sannan na tsallaka zuwa gaban teburin wani mai siyar da kayan marmari. Na tarar da mutum biyu a gurin so hakan na nufin dole nai hakuri na jira har ya sallamesu. Da yaren igbo suka yi magana dayan ya siyar masa da abaya da kankana dayan kuma mai zubin hausawa sai ya mika masa dubu biya yace ya hada masa kayan marmarin da turanci. Na saba siyayya gurinsa magidanci ne mai jin yaren igbo domin shi baya jin turanci balle kuma yarbanci, rike kudin da mutumen ya mika masa dan be san abunda zai bashi ba, shi ko kyakkyawan saurayin mai kama da mazan novel ya dage sai bayani yake masa da turanci. "Kaji matsalar rashin jin yaren mutane" Ya fada cike da jin haushi. "Kuma ba zaka nemi taimakon kowa ba?" Da mamaki ya kalleni jin na masa hausa. "What did you just said?" Murmushi nai ban bashi amsa ba, na kalli mai siyardar kayan marmarin na fada masa cewar ya hada masa na dubu daya da dari biyar kamar yadda ya fada masa da yalshen turanci da farko ni kuma na fada masa da yaren da yake ji wato yaren igbo. "Nye ya puku akwukwo nri" Sai ya amsa da okay ya shiga hada masa. Mutumen ya matsa kusa da ni. "Kina jin yarena?" "Duk mutumen daya zauna lagos dole ne yaji yare kala biyu, ko dai ya iya turanci ko kuma yarbanci, har da igbo ma idan ta kama, domin shi wannan mutumen baya jin yarbacin igbo yake ji, ya kamata ka koya" Na fada masa ba tare dana kalli inda yake tsaye ba. Murmushin kasaita ne ya bayyana a fuskarsa da alama na burgeshi jin ina hausa kamar jakin kano. "Amman ina kika koyi yare nan har hudu turanci, hausa, yarbancin, igbo wace yare ce ke?" Kallonsa nai muna hada sai yayi saurin kawar da nasa, ba mamaki blue eyes dina ne suka firgita shi. "Ban san yarena ba" "Why?" "Because ni marainiya ce" Fuskar tausayi yai ya zuba hannayensa a aljihu. "Ayyah I'm sorry" "You shouldn't, it's not your fault" "Yeah i know, mi zaki siya a nan" "Ayaba ina son ayaba" "Owk you look cute" Ya fada yana kallona. "Thanks handsome" Na fada still ban kalleshi ba. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro dubu uku ya mika min. "Gashi ki siya" "No na gode" Na fada ba tare da na kalli kudin ba. "Wow ba kasafai zaka bawa yarinya kamarki a lagos kudi ba ta ki karba" "Likewise, ba kowa zai iya kyautar kudi a take ba a Lagos sai bahaushe" "Yeah musulumci ya koyar da mu rika kyauta saboda halin Annabin mu ne, by the way sunana Hamza Ali ana kirana Khaleefa" Cike da burgewa na ke kallonsa, ban san abunda yasa na ke son naji ana maganar abunda ya shafi musulumci ba Hannu na mika masa "Ni kuma sunana Emily Emmanuel" Kin karbar hannun yai. "Mu musulmai bama gaisawa da mace musulumci ya hana mu sorry" "Never mind" Sai da mutumen ya mika masa ledar kayan marmarin sai ya karba yana kallon. "Fada masa ya rike canjin" Da yaren Igbo na fada masa cewar ya ce ya bar canjin, sai ya mikawa mutumen dubu ukun. "Ki fada masa abunda kike so ya hada miki, nice to meet you young lady" Ya fada yana kallona kasa da sama, kamin ya buga babur dinsa ya daga min hannu yana murmushi ya wuce. Murmushi nai na rashin dalili na bishi da kallo har na daina hangoshi. *** *** *** Godiya mutumen igbo yai min sannan na fada masa abunda zai bani ya hada min da sauran canjina na kamo hanya cike da farincikin da ban san dalilinsa ba, kawai dai ina jin nishadi ya cika min zuciya da ruhi. Ina tafe ina wasa da dayan hannuna mai nade da sarkar cross sai aka fara yayyafi, kowa ya fara gudu an fakewa a wani gurin domin ruwan ya sauka da karfi, ni kam tafiyata na ke da dai daya ina daga kaina sama ruwan yana saukarka min a fuska da kai. Hango bakin shagon wani mutume dake road din mu babu kowa a gurin yasa naje gurin a guje na aje ledar hannuna na fito tsakiyar titi da babu motoci na tsaya ina waka da ruwan saman ina juyawa ina rawata domin babu abunda ya dame ni. Shakaf ka jike a guri a gurin idan na hango mota tafe sai na koma gurin shagon a guje na fake dugun kar a min daukar mahaukaciya sai motar ta wuce sannan na fito na cigaba haka nai ta yi har aka gama ruwan a kaina. Sannan naje na zauna bakin teburin mutumen na saka hannuna a aljihu na ciro yar karamar wukar da babu wanda yasan ina yawo da ita na dauki lemu daya na yanka na sha. Sai da naji na koshi da kayan marmarin sannan na faki idon mutane na maida wukar ajihuna, na dauki ragowar kayan marmarin na kamo hanyar gidan marayu wanda zan iya kiransa da gidanmu ko kuma na ce gidana. Kamar dai dazun yanzu ma sai da muka gaisa da mai gadin gurin har yake min sannu da jikewar da yai sannan na wuce sashenmu wato block C. Rossy na ganina ta rugo da gudu ta tare ni, daman ta saba min haka ita ba ma ita kadai ba har da sauran an block din, domin ni mutuniyar kowa ce komai nawa na kowa ne, idan na samu bana iya ci nidai ko da basu san da shi ba. "Ku aabọ pada. arabinrin mi" Ta min sannu da zuwa da yaren yarbancin tana kokarin karbar ledar hannuna. Sakar mata ledar nai ina murmushi na ce. "Kije ku raba tare da du Elina" "Wow wato oga shakur yayi miki sallama ta kwarai kenan nan yau" Da yaren yarbancin muka yi maganar ni dai murmushi kawai nai na kama hanyar dakinmu, daman na san kowa zai dauka cewar kyautar oga Abdulshakur ce, domin ya saba min irin wannan sallamar idan rana tai hi kyau. Oga Abdulshakur wani oganane a gurin aikin gyara mota, shi yake da gurin a gurinsa nake zuwa ina koya duk kuwa da kasancewarsa musulmi, na fara aikin ne a lokacin dana kare makarantan kuma ban samu damar shiga babba ba, an rubuta takarda zuwa ga gabnatin Lagos domin daukar nauyin karatun mu zuwa mataki na gaba mu yan wannan shakarar da muka gama, amman har yanzu babu wani abu da ya fito daga can, wata kila dan aikin har yanzu be kai ba, ko kuma ta manta da sha'aninmu ne. Ni kuma bana son zaman banza ba aiki, bayan kuma shugaban gidan marayu ya bawa kowa damar mai son aiki ko sana'a yayi domin tallafawa kansa. Ko da na shiga dakinmu babu kowa sai Nine ackor ita kadai a gafenta tana bachi, dakinmu babban daki ne mai daukar mutum takwas kamar sauran dakunan, an kawata dakin da kananan gadaje na kwanan mutum daya da yar karamar waduruf ta saka tufafi. Gadona kusa da window yake hakan kuma na min dadi duk kuwa da kasancewar wani lokacin ina jin tsoro. Tufafin jikina na fara cirewa na canja zuwa wata yar karamar gown, sannan na dauki wukata na saka a cikin jakata inda na saba ajeta, gado na hau na kwanta fuskata da murmushi mutum dazun ne har yanzu na kasa daina ganinsa a idona, yana da kyau sosai kamar wani aljani gashi fari ni kuma ina son fararen mutune duk kuwa da kasancewata fara. 'Musulmi ne fa!' Zuciyata ta fada min, miyasa zan yi tunanin musulmi bayan a coci ana yawan fada mana cewar musulmi yan ta'adda ne kuma basa son kistoti irina, a take gabana ya fadi sai na ji kamar nayi wani sabo, take nai saurin praising Jesus na roki gafarsa, nai saurin tasowa na baro dakin gudun kar tunanin ya sake dawo min

Chapter 14 of 63