tsoma kanka ko bakinka a tsakanina da Aisha, balle kuma ka sako zancen yata, kuma babu kai babu Aisha babu Fatima daga yau, kallon matata ma karka sake yi, na san inda ka dosa ai, shiyasa kake zugata kake hore mata kunne kuma ka boye gaskiyar komai har sai da matarka ta gaji ta bayyana, ba kai babu Aisha daga yau, kaga dai kamar mutumen kirki mai tarbiya ashe dai kura ce lullube da fatar akuya, tirrr da kai... "
Turhan ya juya, sai Aliyu ya gyara zamansa.
"La la lala Aliyu. Bari na fada maka wani abun da baka sani ba, a lokacin da Emily zata haifi Fatima ni na dauke ta da hannuna na saka ta a mota na kaita asibiti, gurin aikinmu daya da ita, Fatima ta shaku da ni fiye da kai, na san ciki da wajen na halin Emily fiye da kai, babu abun da bata fada min ba na zamantakewarku, a Part hartcour muke zaune dukanmu, a duk lokacin da na so ganinta ziyara kawai nake kai mata. Yanzu ina son ka je ka mutu..."
Turhan ya ji zuciyarsa kamar zata fado tsabar bakin ciki da kishi numfashinsa har daukewa yayi ya dawo. Turhan ya juyo
"Kana magana kamar wanda yayi nasara, Jarumi ne kai haka kake son na kira ka? Ko kuma na taba ma? Ka taba ganin wanda yayi cin amana yayi nasara? Ko yanzu kasuwa ta watse dan kwalli ya ci riba, Fatima bata da wani Uba sai Turhan, bata da wasu family sai nawa, har abada kuma alaka ba zata yanke tsakanina da Aisha ba, kuma zaka ga sakamakonka... Ko da yake kq fara gani ai, tun a gurin matarka, yanzu kuma gaka kwance a asibiti waya san mi zai biyo baya kuma..."
Ya dauke kai ya juya ya fice yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba irin yau, ba a taba fada masa magana mai daci kamar ta yau ba.
KAMEELA POV.
"Au baki ci abincin ba?"
Hajiya ta tambaya sannan ta zauna bakin gadon da Kameela take kwance jiki ba kwari domin ta kwaracewa komai tun a ranar da Aliyu ya sake ta, bata fahimci girman laifin data aikata ba sai sakin ya shiga tsakaninsu, sai dai kuma sakin ya kara tabbatar mata Aliyu yana son Emily domin ko a lokacin da ta saka masa guba be sake ta ba sai a yanzu dan kawai ta dauki yarta ta kai gurin ubanta, hakan ya kara karantar da ita cewar Aliyu yana son ya auri Emily ne ko kuma shedan ya ci karfinsa yana son ya shirya zaman banza da ita. A duk lokacin da ta yi yunkurin daukar waya ta kira Aliyu da nufin ba shi hakuri sai zuciyar ta ta tuna mata ya fifita wata banza ne akanta fa, bayan marinta da yayi har da saki a cikin gidan iyayenta, gashi kuma ita ma nata iyayen sun dauki zafi sosai kuma sun goyi bayan abun da ta aikata, har suna farincikin mutuwar auren, sai dai ita ta san abu ne mai wahala ta iya cigaba da rayuwa babu Aliyu a tare da ita.
Ta yi ta sauraren ko zai gane kuskuren abun da ya kamata mata ya dawo ya bata hakuri kuma ya gyara aurensu, sam a rayuwarta bata taba tunanin Aliyu zai iya furta kalmar saki a gareta ba, kuma abun abun bakincikin ma saboda wata karuwar banza. Bata gane rabuwa da wanda kake kauna bata da dadi ba sai a yanzu da igiyar aure daya ta warware tsakaninta da Aliyu, a yanzu ne ta fahimci ashe duk son da take masa a baya karya ce yanzu ne take ainahin kaunarsa, washe garin ranar da ya sake ta ma sai da ta yi kamar zata yi karamar hauka, kamar wata mai aljannu haka ta zame musu a gidan, ta hanyar ihunta ne Mama Barakat ta san abubuwan da suke faruwa...
"Ke kan dai Allah ya wadaran wannan hali na ki, wai anya Aliyun nan ba magani yayi miki ba kamin ya zo neman ki ma? Akanki aka fara saki ne? Ina ce ga yar uwarki nan damuwa kika ga ta yi? Sai ke? Sai kace Aliyu ne autan maza, toh bari kiji na fada miki ko ma dawowa yayi ba zaki taba komawa ba, aure tsakaninki da shi ya kare har abada, da ma ya sani saki uku yayi miki ba daya ba, sai mu san shi dan iska ne"
Kameela ta tashi zaune ta sauka daga kan gadon tana share hawayenta ta fice daga dakin kasa ta sauka ta fice daga bangaren na su gaba daya, ta nufi bangaren Mama Barakat domin acan ta san ta saba jin sanyi idan wani abu ya faru tsakaninta da Aliyu, ko ba komai Mama Barakat tana bata shawarar yadda zata bullowa lamarin, ba kamar mahaifiyarta da yar;uwanta dake kara bata abun ba. A lokacin da ta shiga falon Mama Barakat ta samu ita ma shigowarta kenan daga cikin gari idonta ya kumbura yayi ja kamar zai fashe. Mama Barakat na ganinta ta katsi hanzarinta.
"Dan Allah indai kin san kin zo ne saboda Aliyu to ki tashi ki koma bangarenku, ni ma ina da nawa tarin matsalolin a gabana, Emily ce kin riga kin yi nasara akanta to me ya rage kuma?"
"Wallahi har yanzu ban yi, amman dai zan yi, sai na ga bayan yarinyar nan, kuma na zan sake zuwa neman shawara a gurinki ba"
"Karki sake ki sake zagin Emily"
Kameela har ta juya ta juyo tabe da baki jin abun da Mama Barakat ta fada.
"Tohmmmm ko dai ta miki maganin ne ke ma?"
"Emily ฦดata ce...!"
Kameela ta yi dariyar da bata shirya ba, ta rike kumkuru ta kara matsawa kusa da Mama Barakat.
"Eeehhhh? God Forbid Wallahi karya ne, to ta ina? A zaren ma ba kalar yadin ba ne, sai idan dai Lake lake dangin nepa, ko lake laken ne ma Wallahi babu kama, Mama Barakat ki ma daina alakanta kanki da watsan yar iskar yarinyar kafirar ba..."
Bata kai karshe ba Mama Barakat ta dauke fuskarta da mari.
"Fita daga falon nan"
Kameela ta juya da sauri ta fice daga falon babu shiri, domin da take da Mama Barakat bata taba ganin bacin ranta irin yau ba, gashi har ya kai ga ta mareta.
"Ahhh Ahhh ni fa duk ban gane wannan ba, anya shekarar nan ba so ake na haukace ba? To ta ina ma zata zama... Oh.... Hadin kai aka yi da Aliyu ko Ummi wai ni ake son durawa bakinciki"
Ta shiga bangarensu rike da fuska tana ta mamaki sai tunani take.
[7/21, 9:49โฏPM] ๐๐ต๐ฎ๐ฑ๐ฒ๐ฒ๐ท๐ฎ ๐๐ฎ๐ป๐ฑ๐: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=r_t
*๐ ABOKIN RAYUWA ๐*
*ยฉ Khadeeja Candy*
Page 5๏ธโฃ6๏ธโฃ
Tana jefar da wayar ta cigaba da tafiya, a yanzu ta yi giving up akan rayuwarta da duk wani abun da ya shafe ta, ta sha wahala iya wahala, daga karshe kuma burinta da mafarkin da take da shi ya rushe. Jin tsayawar motar bayanta be saka ta juyo ba har sai da ta ji an fisgota an juyo da ita da karfi. Wani mutum ta gani wanda bata sani ba, ya rike ta gam sai ga wasu maza biyu sun fito daga motar wacce ta kasance ta jigila ma'ana motar haya, dukansu suna sanye da kayan gida ne.
"Ke ce Emily?"
Dayan dake rike da ita ya tambaya, sai ta daga kai ko kadan babu tsoro ko faduwar gaba a tare da ita, domin a yanzu ta shirya ko da mutuwarce tana ra'ayin a mutuwar.
"Kina tare da wani a nan ne?"
Ta girgiza kai. Sai ya ciro wayarsa ya kira.
"Mun same ta"
Yana fadar hakan ya amsa da
"Okay Sir"
Sai ya kashe wayar.
"Su waye ku?"
"Jami'an farin kaya ne"
"Me aka ce na yi?"
Yayi shiru be ce mata uffan ba kuma be sake ta ba duk kuwa da irin kokarin da take na kwatar kanta. Sai da wayarsa ta sake ringing ya daga yayi magana.
"Abunda muke gani dai babu wani rauni ko matsala a tare da ita"
Ya saka Hands-free ya mika mata.
"Emily ki shiga mota za su taho da ke"
"Waye wannan?"
"Sunana Adam Bello"
"Dr A-B, suwaye dan nan me aka ce ana yi?"
"Baki yi komai ba, na kira baki daga ba, sai na sake kira na ji kina waya bayan kin fada min kina neman taimakona, shiyasa ni kuma na nemi taimakon Babana aka yi tracing dinki"
"Na nemi taimakonka a dazun saboda ina tunanin kamar ฦwaฦwalwata ta tabu, amman yanzu na samu lafiya, bana son taimakon kowa bana son kowa kusa da ni"
"Emily ko da tsiya ko da arziki za su zo da ke, dan haka ki bada hadin kai su zo da ke ta arzikin zai fi"
Ya katse wayar, mutumen dake rike da ita ya sake ta ya nuna mata motar da suka shigo, ta nufi motar ta dayan ya shiga ta shiga dayan ya shiga aka saka ta tsakiya sannan guda ya shiga front seat direba yaja motar suka yi gaba.
Headquartersu suka tafi da ita suka bata guri mai kyau da abinci, bayan sun dauki Information dinta, amman ruwa kawai ta iya sha, shi ma saboda makoshinta yana bushewa ne, daman bata ci komai ba ya tafi gidansu Turhan.
Da dare yayi suka dauke ta daga nan suka sakata wata mota mai kyau da ac aka kaita gidan wani babban mutum, suka tarbe ta da hannu biyu a nan ma suka bata masauki mai kyau aka kawo mata abinci, shi ma ta kasa cin komai, bata raina kanta ba sai da dare yayi bachi yaki zuwa mata sai tunani gashi ta gagara kuka, gaba dayan rayuwarta sai da ta tuna shi a dare, yadda Khaleefa ya latsata ya yaudareta, zaman da ta yi gidansu, fitowarta haihuwar London, haduwarta da Ammy aurenta da Turhan zaman da ta yi a masarautarsu, dawowarta wahalar da ta sha da cikin Fatima, haduwarta da Vito yar rayuwar jindadin da ya bata mai hade da duka da kangin na zaba mata abokan mu'alama, haduwarta da Aliyu, mutuwar London, yadda ta rasa Fatima har zuwa yau da Fatima ta zabi ubanta sama da ita, wanda shi ya fi komai yi mata ciwo, da karya zuciyarta.
Ba'ayi wani dare da yafi kowane tsayi a idon Emily kamar wannan daren da bachi be rabi idonta ba, tunani be barta ba, kuma hawaye ba su ziyarce ta ba, kamin safe kanta ya cika yayi mata nauyi kamar wanda aka hurawa iska ciki, idonta ma sun yi nauyi sosai kana kallonta kasan bata samu runtsawa a daren ba. Misalin karfe takwas wata yarinya wacce ta fi kama da mai aiki ta shigo gidan ta ce mata ta shirya za a zo a dauke ta karfe 8:30, Emily ta daga mata kai kawai, babu jimawa yarinyar ta dawo ta kawo mata ruwan tea da kayan hada shayi sai bread.
"Na a gama hada abun karyawa ba, amman ki ci wannan saboda za ku tafi"
Nan ma Emily ta daga kai kawai, saboda bata son yawan magana ko musu, yarinyar ta fita Emily ta kalli kayan da aka kawo ta dauke kai har lokacin bata ji tana sha'awar cin wani abu ba, gaba daya bata jin yunwa cikin ya daure jikinta ne kawai take ji babu karfi sai kuma ciwon da kanta yake. Misalin karfe takwas da rabi yarinyar ta sake shigowa tace ance ta fito.
Emily ta mike tsaye ta bi bayan yarinyar suka fita tare, yarinyar ta rakata har harabar gida, har lokacin masu gidan masu farka ba, sai yan aiki ne suke ta kai da kawo.
Mutumen da ya kawo ta jiya ne ya dawo ya dauke ta a wata motar ta dabam ba wacan ba, sai da ta shiga cikin motar ta tarar da wani a mazaunin direba, dayan ya shiga front seat suka damka mata duk abun da ya kamata sannan suka nufi airport da ita, suna yin farkin a harabar airport din ta fashe da kuka tunawa da zata tafi ta bar yarta, idan akwai abun da take kauna a duniyar nan be wuce Fatima ba, saboda ita ce kadai sanyin idaniyarta, sai dai tunawa da ita kanta Fatimar bata bukatarta ya saka ta takaita kukanta ta share hawayenta ta duba ticket din hannunta. Da kanta ta bude motar ta fita mutanen suka mata rakiya har ciki, ba su bar gurin ba sai da jirginta ya daga zuwa Abuja, a jikin Window ta zauna ta jingina tana jin kamar jirgin ya juya ta koma ta dauko yarta ko da da karfi ne.
ALIYU POV.
Duk inda ake saka ran za a samu Emily kamar tasha ko unguwanin dake kusa da su, sai da Ummi ta aika aka bincika mata ana cigiya amman ba a samu ganinta ba, a nan hankalin Mama Barakat ya kara tashi ta sha kuka sosai kamin Ummi ta iya rarrashinta har ta samu karfin guiwar tafiya gidanta, daman yaranta tun gabanin ta yi magana da Ummi ta ce su tafi gida. Ummi bata samu tafiya Asibiti da safe ba sai aikawa ta yi aka kai masa abinci da tufafin da zai canja. Da dare ta dafa masa abun da ya fi so wato sinar da miyar kaza ta tafi masa da shi hadi da watermelon juice.
Ko da ta shiga ya same shi zaune yana karatun qur'ane a wayarsa. Direban da suke tare ya aje abincin ya yayi masa ya jiki Aliyu ya amsa masa da kai, bayan ya fice Ummi ta zauna tana murmushi.
"Maa Shaa Allah, jiki dai Alhamdulillah alamar sauki yana ta bayyana"
Aliyu yayi murmushi ya yi addu'a yayin da ya kai karshen aya ya fita daga app din.
"Ummi barka da rana"
"Barka dai ya jikin?"
"Alhamdulillah"
"Haka ake so, wayar nan taka zan karbe ta gaskiya na aje har sai ka samu sauki tukuna"
"saboda me?"
"Saboda bana son ta dauke maka hankali, zan kawo Kur'ane sai ka rika karatu da shi"
Ummi ta bude abinci zata fara zuba masa.
"Saboda Emily ne?"
Ta kalleshi.
"Kamar ya? Ka yi magana da ita ne?"
"Na yi magana da ita, ta fada min Turhan ya sake ta, kuma Fatima ta zabi ubanta tace ba zata bita ba, and lastly ta fada min wai wata mata ta bayyana a matsayin mahaifiyarta, kumq ta fada min zata shiga duniya"
Ummi ta maida plate din ta aje.
"Taya ka samu magana da ita? Mun yi ta kiranta bata daga ba, daga baya kuma muka ji wayar a kashe har yanzu wayar a kashe take"
Yanayin fuskarsa ya sauya sosai.
"Kamin ta kashe layin na kirata mun yi magana, Ummi me yasa kuka bari ta fita gidan?"
"Babu wanda yasanta fita, satar kafa ta yi bayan dawowa daga gidansu Turhan ta gudu saboda ta ji muna magana da Hajiya Barakat, kai ma kasan da sanina dai ba zan bari ta gudu ba, ko dan ma gudun tashin hankalinka, amman ya zan yi tun da haka ta zaba ma kanta?"
"Haka dai rayuwa ta zaba mata, ba zata tana zama guri daya ba, sai ranar da wani ya gina gida mai cike da burinkanta da mafarkan da ta dade tana yi, tana guduwa ne saboda tun tashinta bata san wani gida da zata rike a matsayin nata ba, ta kasa aminta da kowa ne saboda duk wanda ta raba sai ya cuceta, ko da kuwa ya taimake ta da farko, shiyasa take kallon kowa haka yake a yanzu, bata da wasu yan'uwa da idan wani ya nunata da yatsa zata juya taje garesu, ita kadai take rayuwarta fadi ta shi duk ita kadai take abun ta, Emily fa ko kawa bata da a yanzu, ni da ke ba za mu gane ba, saboda mun tashi da yan'uwa da iyaye, amman a idon wanda ba shi da kowa yana kallon duniya colorless ne"
"Amman yanzu ai ta samu uwa, sai ka ga yadda Hajiya Barakat take ta kuka gwanin ban tausayi"
"Daman ta fada min wata daga dangin Kameela ce take ikirarin ta haife ta, amman da gaske ita ce mahaifiyarta?"
"A yadda ta fada min dai, ita ta haife ta, amman a zahiri kam ba hadi domin Emily bata kama da ita"
Sai a lokacin Aliyu ya cika da mamakin jin cewar Mama Barakat ce mahaifiyar Emily, dazun tunanin tafiyar Emily be bar shi ya sararara ba balle yayi wani tunanin, sai a yanzu ya tuna labarin da ta ba shi cewar matar da ta zo da ita daga Kaduna sunanta Mama Barakat kuma ta tafi da ita gidanta amman bata tsaya ba ta gudu.
"Amman da gaske bata hanyar aure aka haifeta ba? Kuma da gaske jefar da ita ta yi?"
Ummi ta daga mishin kai cikin yanayin damuwa. Aliyu ya jingina ya rufe ido yana fadin.
"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un"
"Wallahi, ni ma ta ba ni tausayi, wasu iyayen basa da tunani ne kawai, taya zaka jefar da abun da ka haifa bayan duk wahalar daukar ciki da nakuda, saboda kawai ba ta aure aka samu yaro ba sai ka jefar? Ko a ina suke aje tausayi da kaunar da uwa take da shi ga yayanta lokacin da suke aikata haka? Kuma baka san wane hali yaronka zai tashi ba, baka san ya rayuwa zata kasance masa ba, kalli dai wannan yarinyar, yanzu ai ta daukarwa kanta hakkin yarta, wannan kiwon da Allah yake cewa ya bawa iyaye na yayansu ka ga matan da suke jefar da yayansu ba su sauke wannan nauyi ba, kuma sun jefa kansu da yayan a ciki bala'i da bakinciki, Allah dai ya shirya mana zuri'a"
Aliyu ya bude ido yana kara jin tausayin Emily ya kama shi.
"Amman ta hanyar banza ta same ta ko kuma dai kuskure aka samu?"
"Shi ne ban tambaye ta ba"
"To miye amfanin bayyana akanta a yanzu? Kuma a irin wannan lokacin da take cikin matsala? Kawai sun kunno mata wuta ta rasa ma ina zata saka kanta? Ban tashi tare da ita ba, amman dan zaman da muka yi ina jin tana yawan maganar iyayenta amman ban yi tunanin haka abun zai zo ba"
"Allah dai ya saka idan ta huce ta dawo, idan kuma ta zabi tafiyar ne Allah yasa ta fada hannun kwarai"
"Ameen"
Ummi ta bude abincin zata fara zuba masa ya dakatar da ita.
"Ummi karki zuba abincin nan, ba zan iya cinsa a yanzu ba"
Ummi ta yi kamar bata ji ba ta zuba masa ba da yawa ba.
"Ka daure da kai ka ci"
Ya karba yana kallon mahaifiyarsa, sai kuma ya saki murmushi kadan yana jindadin da shi ta shi uwar ta kasance a tare da tare. Ya fara cin abincin yana tuna wasu kalamai da Emily ta fada masa lokacin da ya kawo ta gida daga gurin aikinsu.
"Yarinyar ta yi kokari, ban san irin rayuwar da mahafiyarta ta gani ko ta ji ba daya saka ta jefar da ita, amman dai ita Emily ta tsaya tsayin daka akan yayanta, daga wanda ya mutu har wannan Fatima babu wanda bata sha wahala gurin rainon ciki da haihuwarsa ba, amman bata gudu ta bar ko daya ba, har London da yake da lalura ma, wata kila saboda ta san yadda ake ji ne idan babu kowa na su a kusa da su, saboda ita sa dandana dacin haka, ita kadai sai irin mutanen da suka tashi a irin yanayinta suke iya fahimtar yarenta, amman dai abun da na sani Emily Jaruma ce, ma manta ban fada mata wannan ba"
Ya kai abincin a bakinsa ya tauna ya hade amman baya jin dandanonsa ko kadan, kawai dai yana ci ne saboda ya ranta ran Ummi.
TURHAN POV.
Ammy na tsaye balcony tana kallon Turhan da ya fito motar abokinsa Manir ya doso entrance cikin yanayin damuwa.
"Sannu Manir an gode Allah yayi albarka"
"Ameen sai da safe Ammy"
Yaja motar ya wuce Ammy ta juya ta shiga falon ta zauna kusa da danta.
"Ba wani labari ne?"
Ya dago jiki a sanyaye, murya kamar ba tasa ba.
"Babu, na yi report har gurin police, amman dai har yanzu ba ace an ganta ba, ni da manner mun zagaye rabin garin nan ba mu ganta ba, mun tafi har wata unguwa nemanta, muka kwatanta na nuna hotonta sai suka ce mana ta zo amman da dadewa kusan shekara bakwai da suka wuce, wai mahaukaciya ce sun fada mana irin rayuwar da ta yi a gurin da ciki, ina kyautata zaton bayan ta bar Sudan ne, saboda sunce tana tare da yaro"
"Wata kila da cikin Fatima ne, ta fada min ta zauna a unguwanin duk suna mata daukar mahaukaciya"
Turhan ya duba agogon falon dake nuna karfe 11pm ya sauke ajiyar zuciya.
"Ammy na cutar da yarinyar nan, na gode da baki bar ni sai da na nemo ta, sai dai yanzu ban san wane hali zata fada ba, a ina take?"
Ya soke kai kasa ya dafe cike da damuwa. Ammy ta kai hannu ta shafa kan danta.
"Alhamdulillah, ka gane gaskiya shi yafi komai kyau ai, na jidadin haka, kuma In Shaa Allahu zata dawo, uwa ai bata iya tafiya ta bar yaranta, komai zai daidaita"
"Ina fatan haka"
Ammy ta sumbance shi, tana jin kaunar danta sosai ga kuma jikarta dake dakinta tana bachi abun burgewa.
"Gobe zan bar garin nan da karfe 10am, saboda kiran da Abie yake min"
"Toh Allah ya kaika lafiya ya tsare"
"Amman ina son na tafi da Fatima Ammy"
Ammy ta janye hannunta a jikinsa.
"Aa, ba zan yarda ka sake tafiya da kowa ba, haka ka tafi da uwarta labari ya canja"
Ya kalleta.
"Wannan baya ne, Wallahi yanzu ba Emily ba ko dankwalinta na tafi da shi ba zan bari ya wulakanta ba, balle kuma Abunda ta haifa min"
"Aa ka barta anan dai, kai ma zaka fi jin karfin dawowa"
Baya son ya musa mata, dan haka ya amince ba dan ransa ya so ba ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya haura sama, dakin Ammy ya fara shiga ya zauna bakin gadonta yana kallon Fatima dake ta bachi rumgume da teddy, ya matsa kusa da ita ya kai hannu yana shafa fuskarta, matar da ya wulakanta ya kaskantar ita ce yau ta ba shi farincikin da yake nema kuma wanda ba a siyarwa.
"Wata mahaukaciya? Mai ciki? Ana tunanin cikin an mata shi ne ko kuma asiri aka mata, wacan shagon ta yi zama lokacin ba ayi gina a gurin ba"
Haka yayi ta tuna yadda mutanen suka yi ta labarta masa Emily. Ya kai bakinsa ya sumbanci Fatima hawayensa ya zuba a kan fuskarta.
[7/25, 8:28โฏPM] ๐๐ต๐ฎ๐ฑ๐ฒ๐ฒ๐ท๐ฎ ๐๐ฎ๐ป๐ฑ๐: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
*๐ ABOKIN RAYUWA ๐*
*ยฉ Khadeeja Candy*
FOLLOW ME ON ๐๐ป
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
WATTPAD
https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy
Page 5๏ธโฃ7๏ธโฃ
Jirginsu na sauka mutumen dake kusa da ita ya kalleta ya ce
"Ki biyo ni zan miki ragora, Dr A-B ne yace a kula da ke"
Ta kalle shi sai, tun da ta zauna yake a gurin amman be ce mata komai ba sai a yanzu. Yana tashi ita ma ta tashi ta bi bayansa duk inda ya shiga tana biye da shi har suka isa gurin motar da aka kawo, sai ya bude mata baya ta shiga shi kuma ya shiga gaba ya shiga ya rufe aka ja motar, Emily dai na zaune shiru har suka isa unguwar manyan mutane, ba ka ganin komai sai gine gine daga hawa biyu sai uku sai ka tona zaka ga mai hawa daya.
Gaban wani katafaren gida direban motar ya tsaya yayi horn security ya bude masa gate, gida ne babba sosai mai dauke da gini mai kyau na burgewa ga shuke shuke ta ko'ina amman ko kadan hankalin Emily be kai can ba saboda tunanin yana wani gurin dabam, direban na fakawa aka bude gefen da take data dago kai sai ta yi arba da Dr AB fuskarta dauke da murmushi ya miko mata hannu.
'Haka rayuwa take tafiya da ni? Daga wannan sai wacan?'
Ta tambayi kanta tana kallon hannunsa kamin ta mika masa nata hannun ta rika shi ta fito motar. Tsaya ta yi a gabansa yana ta kallon fuskarta zuwa cikin idonta, kallon karantar damuwarta ne yake, idonta ya nuna alamar bata samu bachi ba, fuskarta kuma na nuna alamar damuwa, sukuku kamar wanda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 63