dare, a nan yunwa ta fara tunkaro ni ga yarona be san babu ba. Kukansa ya saka mai gadin lekowa ya tambayi tafiya na fada masa yunwa yake ji sai ya shiga ya dauko ragowar abinci ya bani na bawa yaron da muka gama yace dan Allah mu kara gaba kar mai gidansa ya dawo ya same mu a nan zai masa fada.
Na yi masa godiya na tashi na kara gaba, haka na yi ta rayuwa a unguwar daga wannan kwararo sai wannan wani gurin a hantare ni wani gurin a bani abinci ko sutura wani gurin kuma a ba ni hakuri, gaba daya na koma wata kazama saboda babu gurin da zan raba na yi wanka, bahaya ma sai na shiga daji, rayuwa ta yi tsanani gareni a lokacin, ga ciki ga yaron da ba lafiyayye ba, idan ciwonsa ya tashi sai dai na yi ta kuka domin ban san wani abu da zan yi ba bayan wannan, ni da shi muka rame muka lalace, nakan shiga gida gida neman aiki ko wanki, idan na samu mai son wanki na yi ta murna na wanke a biyani na ciyar da kaina da ɗana, na samu wani tsohon shagon kwano na laba ciki nake kwana ciki nake wuni idan ina cikin unguwar.
Tun mutane ana jin tsorona a unguwar har aka fara sabo da ni wasu ma idan sun raga abinci da kansu suke kawo min saboda suna min kallon mahaukaciya, wani lokacin ba ni sadakar kudi ko abawa ɗana da haka nake ta fadi tashi har cikina ya tsufa, wani sa'in sai na yi tafiya mai nisa zuwa wata unguwa nake samun abun da zan ci, kuma ban sake bawa kowa labarina ba, idan naje gida sai dai na yi bara ko kuma na tambaya idan suna bukatar a musu wanki ko wani aiki. Wasu suka kam tambaye ni waye uban yarona ko kuma cikin da nake dauke da shi sai nace musu ban sani ba ni ma, hakan ya saka suka kara daukata mahaukaciya suna tunanin kamar fyade aka min na samu cikin ko kuma wani ya yaudare ni.
Akwai masu fadar wai ko dai kishiya ta yi min asiri saboda ina kyau ta raba ni da mijina? Su tambaya daga ina nake sai na ce Lagos, idan aka ce Lagos a ina? Sai na ce ban sani ba, to gurin wa zan ce daman? Har lokacin ina jin da kamar akwai sauran kurciya a tare da ni, wata kila kuma shiga mawuyacin hali ne yasa ban taba kula da watan cikina nawa ba, ban taba kirgawa na gane ba, ciki dai yana ta girma kuma yana motsi, idan na ji motsin cikin sai na ji zuciyata ta yi fari tas kamar ba ni da damuwa, ni dai burina na haihu lafiya na samu karin wasu iyalin...
Ana haka wata rana nakuda ta fara taso min tana kwantawa na kwashe kusan kwana biyu sai ta motsa min sai ta koma, idan ta laba min sai na cigaba da harkokina, wata rana na fita neman abun da zan ci ban karasa inda zan je ba aka sako ruwan sama na kuda ta taso min mai karfi kamar zan fita hayyacina gashi kuma na yi nisa da gida ba zan iya komawa ba, ɗana kuma ya firgice saboda tsoron ruwan da iska sai ihu yake min ni ma kuma ihun nake a gefen hanya babu wanda ya kula ni sai kai Aliyu, shi ne farkon haduwata da kai, na zan iya manta wannan alherin ba, na gode na gode Aliyu, a lokacin ne na rike hannunka har agogon ya cire ya dawo hannu sai na matse shi ina ihu na yi tunanin mutuwa zan yi ma gaba daya, ka taimake ni ka dauke ni ka kai ni Asibiti, duk wani taimako daya kamata likitocin nan sun ba ni na wahala sosai kamin na samu na haihu da kaina, ada har ina tunanin ko dai sai an fasa ni za a iya cire abun da ke cikina saboda na kasa nishi.
Da na haihu sai suka bukac a kawo kayan jaririya ba ni da su, zanen da aka hadeta a ciki ma tsohon zanen wata mata ta bada a gurin aka lulkube Fatima, suka ce ina audugar da zan saka ina kaza ina kaza, na ce duk ba ni da, sai suka tambaya wanda ya kawo ni waye shi? Nace ban san shi ba taimakona yayi, a nan wata nurse ta fita ta shigo min da pad ta pant ta kuma ba ni zane na daura sannan suka canja min daki suka kawo ni wani dakin na dabam suna tambayar ina yan'uwana ya kamata na ci abinci na ce musu ba ni da kowa, daya daga cikin wadanda suka karbi haihuwa ta ta kawo min agogonka ta ce ga wannan kin saki a kasa dazun na karba na rike ga. Daker na iya awa hudu a asibitin na kamin na saci kafa na gudu da ɗana da kuma jaririya dana haifa, zanena mai jini da uwar da ke fadowa bayan haihuwa a asibitin na bar musu na gudu. Ban nisa sosai da unguwar da asibitin take ba jiri ya debe ni na fadi ban sake sanin inda kaina yake ba.
Sai da na farko naga ana min fifita ga jaririya a kusa da ni ga kuma London yana ta kuka, mutane nata min sannu aka ba ni abinci na ci sannan aka dauke ni zuwa gidan wata mata dake kusa ana tambayar a ina nake daga ina na fito na fada musu a gidan na kwana sai washe gari bayan na karya matar ta siya min wani pad ta bani tsohon wandonta na saka bayan ta dora min ruwan zafi na yi wanka, ta bani wani tufafin na saka da hijab, makota kuma suka kawo min tsofin kayan jarirai na sakawa Fatima, ta kawo min abinci na ci na sha kunu sannan mai gidanta da wasu mutum biyu yan unguwar da kuma ita matar kanta, suka dora ni a napep muka tafi unguwar da nake rayuwa na nuna musu inda nake kwana sai suka fara tambayar wadanda suka san ni a unguwar, kowa sai yace da rana tsaka ya gan ni a gurin kuma ba ni da cikakiyar lafiya, cikin ma suna zargin yi min aka yi ta karfi, wasu kuma su nanata wai asiri aka min.
Ni dai jinsu kawai nake idan aka tambaya daga ina nake sai na ce Lagos wane guri a Lagos nace ban sani ba, sai suka yanke shawarar za a kai ni police station ayi report, ina jin haka nace ba zan je ba da suka matsa na saka musu kuka a dole suka koma can gefe suka yi maganarsu sai aka dawo aka fada min wai zan bi matar zuwa gidanta na koma can da zama a nan ma na tirje domin na san akwai abun da suka shirya, ni kuma ina tsoron a yadani Cocin da na gudu su gani ko kuma Ammy. Na dake akan nan gurin zan zauna da kowa ya watse na goya jaririyata na kama hannun dana na bi ta cikin gidanen dan kar ma wani ya gan ni na gudu na bar unguwar.
Tafiyar kuma wani sabon labari ne, domin ba san kowa a inda na tafi ba, haka na kwana a jikin wata tsohuwar gina sauro ya cije ni ya cije yarana musamman Fatima dake ta jaririya a lokacin, a daren ne na rana mata suna Fatima sunan da ba a yanka mata rago ba kamar yadda kuke yi a addinin musulunci, a lokacin akwai son addinin a raina shiyasa na zabi sunan da yake min dadi bayan Aisha, da gari ya waye na barka dankwalina na yi amfani da shi domin pad din ya lalace kuma ba ni da wani, na cigaba da tafiya kafafuwana sun gaji haka nake ta mika su ga danyen jego ga yaro karami idan ya fasa min wani ihu sai na rikice, na daukeshi idan na gaje na aje shi haka dai har na isa wata unguwar marowata domin duk gidan da na shiga na yi roko hakuri ake ba ni wasu kuma su koroni.
Yunwa ta ci ni sosai ga tafiya na gaji har na fara ganin jiri, tsakaninkanin kafafuwana ma ciwo nake ji sosai domin ban samu hutu da kulawar daya kamata ba bayan haihuwar da na yi kwana biyu da suka wuce. A haka har na isa kofar wani karamin gida irin na mazan nan da ba su da aure a bude na sallama na sallama na ji shiru sai na taka ciki kadan na jiyo kamshin girki, sai na yi sunsun na dawo baya na koma can bayan gidan dake da wata gona na samu wani guri na raba na kwance Fatima dake bachi yarinya kyakkyawa fara sol na kwantar da ita a gurin na zaunar da London dake ta kukan yunwa na fito na koma wacan gidan dake bude na kara sallama ina sallama ina shiga ciki har na kai inda nake jiyo kamshin a wani karamin Kitchen na duba waiga na ga babu mai ganina na nasa kafata a Kitchen din, sai na yi arba da mutum kwance cikin jini farar vest din dake jikinsa duk ta bace da jini, da sauri na dawo baya ina numfashi daker, na ga tashin hankali kala kala amman ban taba ganin gawa ba sai a ranar, na fito da sauri na falfala da gudu na dawo gurin yarana ina dawowa na samu London yana ihu yana yunwa, ni kaina kuma yunwar nake ji, sai hakan ya saka na manta da tunanin abun da zai biyo baya na sake komawa zuciya na zillo kamar zata fado na shiga Kitchen din na duba ko'ina har na hango karamin gas a kusa da kafar mutumen da ban san ko waye ba, da alama dai girki yake aka kashe shi, na fito na sake leka waje na dawo da sauri na nufi girkin na bude indomie ce har ta fara kamawa na tara hijabina na juye na saki tukunyar na fito a guje ga zafin indomie ga tashin hankali na dawo gurin da yarana suke na cire hijab din gaba daya na aje a gurin na bude indomie na saka hannu ina hurawa ina ci ina bawa London.
Ban an kara ba ma ga mutum tsaye a gabana dana daga kai na kalleshi sai na ga fuskarsa babu annuri ga katon Cross a wuyansa, ashe ma ba shi kadai yake ba har da wasu mutun uku.
"Miye alakanki da Risk Guy"
Ya tambaya cikin hausarsa da bata gama zauna wa a bakinsa ba.
"Ban san waye shi ba, ni abinci kawai nake nema"
Ashe yayi zaton na ga lokacin da ya aikata kisan kan ne, a take ya nuna Fatima da bindiga.
"Jaririya ce, bata san komai ba bata maka komai ba karka dauki alhakinta"
Ya maida bindigar a gurin London dake ihun ganin bakuwar fuska.
"Ba shi da lafiya, Autism ne kuma be maka komai ba"
A take ya dawo da bindigar a kaina.
"Idan ka kashe ni yarana ba su da wanda zai rike su ba su da kowa sai ni, ni ma ba ni da kowa sai su, Wallahi ban ga abun da ka aikata ba kuma bazan fadawa kowa ba, abinci kawai naje nema tun jiya rabona da abinci ni da yarona yunwa muke ji, dan Allah ka yi tafiyarka ni ban san waye kai ba, kuma daga nan tafiyata zan yi daman a hanya nake, ina neman mafaka ba ma dan yarana da sai nace maka na shirya mutuwa a yanzu"
Ina maganar cikina da muryata suna rawa ina kuka sosai a take Fatima ta farka ta fara kuka ga London yanayi. Ya kalli yaran ya sake kallona sannan ya sauke bindigar ya juya ya tafi, ni kuma na dauki yata na rumgume London a dayar cinyata ina hura abinci ina ba shi ina kuka. Kamin na daga kai sama na kwala wani irin ihu iyakar karfina sai kuma na tashi na goya Fatima da sauri na dauki London na dauki agogon ka Aliyu da nake ta yawo da shi na fita gonar domin na fara hango mutane kar ayi zaton ni na kashe shi alhalin ban ma tana ganinsa ba sai ranar.
Na yi nisa da gonar na samu wani ice na zauna a gurin na rumgume yarana ina kuka jikina nata rawa ina fargabar me kuma zai sake faruwa da ni. Ashe mutumen daya tashi kashe ni yana biye da ni saboda yana ganin kamar zan iya tona masa asiri ne, a nan kamar daga sama a sake ganinsa gabana sai ya saka hannunsa ya dago fuskata ya kalleni ni ma na kalleshi sai ya hura min abu a fuska mai kamar farar hoda amman yana da karfi sosai da zogi domin ina shakarsa hankalina ya bace...
***. ****. ****
Aliyu ya lumshe ido ya jinginar da kansa yana kallon sama, kwallar dake makkale a idonsa suka sauko masa ta gefen idon, Fatima na gani ta fara masa tambaya.
"Ba za mu isa Lafiya ba? Mutuwa za mu yi?"
Ya bude idon da sauri ya kalli Fatima yana murmushi domin be san ma kwallar ta sauko masa ba.
[6/28, 10:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 4️⃣2️⃣
Tausayinta da na mahaifiyarta ya ratsanshi ya saka ya tare hawayen yana murmushi sannan ya shafa kanta.
"Aa Lafiya za mu isa In Shaa Allahu, kawai wani abu nake saurare na ji tausayinta shi ne"
Ta yatsina baki irin na su na yara tana wani iyayi.
"Ni bana yin kuka wa mutane, mutum idan yana da matsala ai shi zai yi kukansa ko?"
"Eh amman tausayawa yana da kyau, ana son haka"
"Okay"
Ta amsa ta cigaba da kallon da take.
"Mun kusa sauka"
"Okay"
Ta amsa ba tare da damuwa ba. Aliyu ya sauke numfashi a hankali idonsa basa masa gizon komai sai fuskar Emily, and he remember yadda suka tsabanin kira har ta yi ta masa dariya a waya, sauti dariyar nata dawo masa, ya tuna haduwarsu a office da tsabanin da suka samu na shiga Elevator da lokacin da ta yi masa tambaya har ta so ma magana da yaren da bata yi zaton yana ji ba, tunani na ya jefo masa ganin da yayi mata na karshe da yadda take ta murmushi kuma murmushi yayi mata kyau a cikin bakar abayarta kamin ya ankara sai gashi yana nasa murmushin a take.
"You deserve happiness..."
Fatima ta amsa masa da sauri tana dagowa ta kalleshi.
"Yes i deserve it"
Kakkaurar dariya ce ta subuce masa irin mai gunna da kal kal.
"Yeah you deserve happiness too baby"
A rasa kuma sai ya ce.
"And now i know why Vito hate you, idan baki son mutum ya shiga uku wannan baki naki is something else"
Ya kunna dayan voice din wanda shi ne na karshe ya cigaba da saurare, wanda a cikin yake son tabbatar da wani aukuwar wani abu ko akasinsa.
***. ****. ****.
Daga lokacin da na shaki wannan hodar ban sake sanin inda hankalina yake ba, ban kuma san tsawon awanin dana dauka cikin gushewar hankalin ba, ni dai na farko da karfi ina jan numfashi, numfashi yana janyewa sai dakin da duk abin da yake ciki yana ta juya min ina jin jiri ga jikina a jike da alama ruwa suka zuba min.
"Yarana yarana yayana, su kadai gare ni yarana"
Yarana kawai nake nema domin su ne a raina, ruwan suka kara watsa min aka kama kaina aka soma a cikin wani bokiti dake cike da ruwa aka cire suka rike gashin suka jijjiga ni da karfi, a take na fara amai domin akwai yunwa a tare da ni ga kuma abin da na shaka warin da nake jinsa wani iri a hancina yana kai min har makoci, ga kuma jijjigar da suke min. Yar indomie da na ci ce na amayar na kwanta a gurin a wahale ina ta kiran sunan yarana.
"Fatima ta... Ibraheem.... Yarana..."
"Ke musulma ce?"
Ita ce tambayar dana fara ji, na dago na kalli mai tambayar daker har lokacin ina dan ganin jiri ga jikin nawa ya kara mutuwa.
"Mu kashe ta kawai boss, duk yadda aka yi budurwarsa ce ko kuma ta san wani abu kansa kawai tana wasa da hankalinmu ne"
Na ji dayan ya fada da halshen igbo, sai dayan ya ce.
"Ko ma ba matarsa bace wannan ai kazama ce daga ganinta, zamu iya kashe ta dai saboda ta san mu muka aikata kar ta kara a gaba ta fada"
"Dauko wuka"
Wanda yake babbansu ya fada a take na tashi zaune na ce.
"Wallahi ban san wanda kuka kashe ba, bani da alaka da shi, ku yarda da ni mana"
Na amsa musu da yaren Igbo sai duk suka cika da mamaki, ogan na su ya taso ta zo inda nake ya turani da kafa na koma kwance ya dake wuyana.
"Taya kika san me nake fada?"
"Ina jin yaren igbo"
Na amsa daker har bakina ya fara zubar da jini domin talkamin da ya take ni da su masu zafi da nauyi ne. Ya daga kafarsa
"Ya kike jin yaren?"
"Saboda na zauna a Lagos"
"Wacece ke?"
"Labarin yana da tsayi"
"i don't care ki fada min yanzu"
A dole na takaita labarin na fada masa abubuwa masu muhimmanci har zuwa inda ya gan ni. Kamin yace komai dayan daya dauko wuka yace karya nake na tsara komai ne.
"Me zai saka na tsara komai?" ai ba biyana za ku yi ba, ba wani abu nake nema daga gareku ba, me zai saka ba za ku bincika ba?"
"ina da mutane a ko'ina har Lagos zan saka a bincika min Idan karya kike zan kashe ki"
"Na yarda"
Na amsa a take, sai ya saka aka dauko masa takardar na bada address din guraren da komai ya faru ya rubuta sannan ya tashi ya fita ina tambayar ina yarana. Har ya fice be amsa min ba, bayan ya fita wani ya shigo min da yaran London yana ta bachi kai langabe wata kila ya dame su da kuka ne suka shaka masa irin abun da suka shaka min, Fatima kuma tana ta tsosai hannu tana sauke ajiyar zuciya irin na babyn da ta yi kuka ta gaji.
"Ba zaki fada mana gaskiya ba ko?"
Na kalleshi na rasa me zan sake cewa, shirun da na yi ya saka shi fiddo wata karamar wuka ya yanki kafata da ita sai da na fasa ihu.
"Ban san komai ba gaskiya na fada"
Na matsar da yarana na rumgumesu domin na lura Fatima yake kallo zai iya cutar da ita. Ya mike tsaye ya fice haka na zauna a dakin har dare jini na zubar min a kafa ga aman da na yi a gurin ga kunzugun da na yi ina son na canja ba ni da wanda zan saka nonona na dauke babu ruwa saboda ban ci komai ba, ga tsoron ban san me zai faru da mu ba, ga kuma ɗana be farka ba har lokacin, abubuwa suka hade min goma da shirin. Ina cikin wannan halin shugan na su ya sake shigowa ya kalleni yana toshe hanci. Ya haska ni da kyau ko'ina na jikina.
"Waya yanke ke ni a nan?"
"Wannan ne ya yake ni, kuma gaskiya na fada muku ban yi karya ba"
"Waye?"
"Wanda ya kawo min yarana"
Ya juya ya fita be jima ba ya dawo tare da mutumen ya haska min shi.
"Wannan ne?"
"Eh"
Mutumen ya bude baki zai yi magana Shugaban na su ya ciro bindiga ya harbe shi a ramen wuya a take ya fadi kasa yana karkari jini ya samu hanya kamar ruwa, ni kuma na shiga aikin ihu yana daka min tsawa bana ko ji sai ihu nake, jikina na rawa hankalina ya tashi ban tana ganin an kashe wani a gabana ba sai ranar, ban daina ihun ba sai da suka shaka min wani abun a hanci hankalina ya sake bacewa. Da na sake farkowa farkowa sai na gan ni a wani daki na dabam yarana suna kusa da ni sun sai kuka suke, ashe tun da suka shaka min ban farko ba sai safe.
Na kama su na rumgume ina jin jikina ba karfi, can anjima sai ga wani ya shigo ya tambaya me nake bukata yanzu?
Na fada masa ina son abinci. Sai ya fita ogan da kansa ya shigo min da abinci ya aje min babu ko zancen wanke hannu balle baki a take na bude shinkafar na fara ci, Ibrahim ma ya rika ci da sauri ko minti biyar ba mu yi ba muka cinye abinci har muna neman kari. Shi dai yana tsaye yana ta kallona.
"Akwai bandaki a nan ki yi wanka, za a kawo tufafi ki canja tare da yaranki, and why are you bleeding?"
"Saboda sabuwar haihuwa ce"
Ya juya ya fita. Ya kawo min tufafi dogayen riguna da pad da panties ga kayan yara na maza da na jarirai. Haka na yi rayuwa a dakin na tsawon kwana uku a yan kwanakin nan na samu kulawa da abinci mai kyau wanda rabon da na ci shi tun bayan da na bar gidan Ammy, ko a sudan tura abinci kawai nake ba dan ina iya ci ba kuma ba dan ina jindadinsa ba sai dan babu yadda na iya. A ranar da nake cika kwana hudu ya shigo ya same ni ina zaune a kasa domin a kasa muke kwanciya ni da yarana gashi tiles ne, Fatima har tari take, Ibrahim kuma yana zazzabi har kuma lokacin ban san a wane gari nake ba balle unguwa azo kuma zancen gida.
Ya zauna kasa kamar yadda nake zaune yana kallona.
"Emily na bincika labarinki a Lagos, here in Kaduna places din da kika zauna da Kaduna, a Sudan ne kawai ban bincika ba, and you're right akan abun da kika fada baki da alaka da mutumen da kika nake zargi, this is the first time da na ji tausayin wani ya kamani sosai wani da ban sani ba, and na ji dadi da ban kashe ki a take ki ba. Emily ina da kyakkyawan sako a gareki"
Shirun da yayi ne ya saka na kalleshi sai da ya karanci natsuwata sannan ya ce.
"Wannan ne karo na farko da nake son na kyautata rayuwar wani, na yi abun alheri a gareki, Emily ina son ki zauna a karkashina zan baki kulawa zan miki gata ke da yaranki, zaki zama a cikin ikona ni kawai cin amana ne bana so, wanda kika ga na kashe ma amanata ya ci, kina son haka"
Na daga masa kai.
"Tohm amman fa bisa sharadi daya, zaki bar wannan addinin ki koma addinin ki na asali, domin babu abun da na tsana kamar musulunci da musulmai, kuma kin zauna da su a yanzu kin fahimci yadda suke, idan kin yarda ki fito waje ki same ni, yau zan bar garin nan"
Ya tashi yayi tafiyarsa, a lokacin zuciya da tunani suka fara min rawa, har na kasa zaba tsakanin addimai guda biyu, an kai ruwa rana daga zuciyata zuwa tunani kamin na fahimci komawa asalin addinina na shi ne gata ne, kuma shi ne rufin asirina ko da yake ban sani ba a lokacin ko shi ma zai ci amana ta ne, amman ba ni da wani zabi domin na gaji da rayuwar dake.
A take na dauki Fatima na saba a kafada na rika hannun Ibrahim muka fita ta kofar dakin da sai a ranar ya bar min ita a bude. Dana fito sai na hango wata kofar a bude na nufi gurin haka na rika bin kofa kofa har na fito harabar gidan dake cike da ciyayi ga kuma wani bangare na gidan da ba a gama ginawa ba.
"Zaki bimu ne?"
Ya tambaya yana kallona da fuskarsa mai ban tsoro. Sai na daga mishi kai.
"Kin yarda da sharadin?"
"Nan ma na daga mishi kai"
"Miye sunan wannan yaron"
"Ibraheem"
"Yarinyar fa?"
"Fatima"
"A cikin sunan mata ina jindadin Lisa, daga yau sunanta Lisa, shi kuma London shi ne sunan da na fi so, ke kuma zaki koma sunanki na asali Emily no more Aisha, that's my number one rule My
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 63