wata yunwa da zai ji a wunin ranar.
Ya daga mata kai yana murmushi kadan, yana jin kamar ace su daure a haka, su yi zama irin na masoya ko ma'aurata, sai dai ya san samun haka a gurin Emily a yanzu ba abu ne mai sauki ba. Kallon agogon falon da ta yi ya saka ta yi hanzarin karasa cin abincin ta mike tsaye.
“Bana son na yi latti, karfe 6:30am zan tafi aiki”
“Wane irin aiki ne za'a tafi karfe 6am? Me yasa kike son takurawa kanki a yanzu Emily kina da komai a nan”
Bata ce masa komai ba, ta cire jacket dinsa ta aje a jikin dayar kujerar, ta kwashe kayan da ta bata ta kai kitchen sannan ta wuce ta haura sama. Mikewa yayi tsaye ya nufi jacket din ya dauka yana kallon stairs din kamar mai jiran fitowarta.
TURHAN POV.
“Baka amsa ni ba”
Ta maimaita da yaren da ita da shi suka fi fahimta, wato Larabci. Lemun dake gefen Laptop din ya dauka ya sha ya aje sannan ya kalleta ta cikin Systems din dake gabansa.
“Ba yanzu ba, akwai wani aiki da ya taso min, ina son sai na karasa shi tukuna?”
“ما طبيعة عملك يا حياتي؟”
“Wane irin aiki ne Hayatie?”
Ya kawar da fuska kaminnya juyo ya kalleta yana shafa kansa, bata jira amsarsa ba ta sake aika masa da wani zancen.
“لا أستطيع تحمل غيابك عني.”
“Ba zan iya jure rashinka a kusa da ni ba”
“Abu mai muhimmanci baki bukatar sani, idan na kammala zan dawo”
“Ka canja min a yanzu”
Ya shafa kansa yana jin wani sabon fushi na kokarin rufe shi.
“Saboda bana haihuwa ne, ko kuma dai ka gaji da zama da ni ne?”
“Zaki iya ba ni ďa? Zaki iya haifa min jinina Jalila?”
Ta yi shiru tana kallonsa kamar yadda shi ma yake kallonta, kamin ya kai hannu ya rufe Laptop din ya kwanta jikin kujerar yana maida numfashi, me yasa ya fada mata haka? Al'adunsu da dokokin sa ake cilasta masa bi ba daga ita ba ne daga masarautarsu ne da kuma mahaifinsa.
Ya tashi zaune yana jin fushinsa yana karuwa tunawa da yayi da yadda Ammy ta yi fushi da shi, saboda yarinyar da bata da ala komai da ita.
Gaba daya an hada masa zafi ta ko'ina, babu wani daki daya da zai laba yaji sanyi. Wayarsa ya dauka ya kira abokinsa har lokacin be sauka daga fushi da bacin rai da yake ji ba.
ALIYU POV.
Yana zaune a kan gado, matarsa na kwance kanta na cinyarsa, ita da shi sun sakarwa plasma dake dakin idonsu, gadon da suke kai kuma ya karbi amanarsu, domin kana kallonsu zaka san hankalinsu a kwance yake basu da wata damuwa ko kadan.
Wayarsa dake can kan karamin tebur ajeye ce ta yi ringing, a take ya ja tsaki domin ya ji dadin zaman baya son motsawa.
Gashi be saba zama kusa da wayarsa ko yawo da ita idan yana tare da matarsa ba.
Abu ne da ya sabawa kansa da shi aje wayarsa a nesa da matarsa a duk lokacin da yake tare da ita, doka ce ya sakawa kansa matukar yana gida tare da iyalinsa to lokacinsa na matarsa zai bata kulawa iyakar kokarinsa.
Gwanar na jin haka sai ta tashi zaune tana kallonsa.
“Na dauko maka ka ba ni dubu biyu?”
A take murmushi ya subuce masa.
“Wai ke ina zaki kai kudi da son kudin nan?”
Ta saka dariya.
“Zaka biya na dauko?”
“Aa ni ma fa na san zafin kudi Hajiya, zan dauko kayata”
Sai ta maida kanta a cinyarsa.
“Ni gaskiya na jidadin kwanciyar nan ba zaka tashi ba”
“Okay saboda ni zan dauko ko?”
“Idan ni zan dauko zaka biya, idan ba haka ba gaskiya ba zan daga a cinyar nan ba, ai kasan idan kana gida kai nawa ne ni kadai”
“Ko ma bana gida ni naki ne har abada, yanzu daga ni na dauko sai na biya 2k din, kin ga wannan tsohon cikin naki ba zan so kina wahala ba”
Ta daga masa saboda ta ji yace zai bata kudin kuma zai dauko wayar da kansa.
“Hmmm ku dai maza idan kuna tare da mu ku namu ne idan kun fita kuma na wasu dai”
Ya mike tsaye ya isa ya dauko wayar yana murmushi already kiran ya yanke.
“Ke dai kishi zai miki illa, me ya kawo wannan maganar kuma?”
“Ai na san halin maza”
“Bayan wa kika aura? Da zaki ce kin san halin maza?”
“Kai kadai na aura amman ai ana fadar halinku”
“Ni dai na banbanta da sauran, yanzu wanda yake da mace yar dumaduma irinki har wata zata burge shi?”
Ya fada bayana bin bayan kiran da aka masa.
“Hello Allah ya taimaki Yarima”
Daga dayan gefen Turhan yayi murmushin karfin hali.
“Tsokanar ta tashi kenan, ya gida?”
“Lafiya kalau”
“Sorry na kira late na san kana tare da Madan ko?”
Aliyu ya kalli uwargidansa yana murmushi
“Kamar ka sani kuwa, daker ta bar ni na amsa wayar ma”
“To a bata hakuri, wani uzurin ne ya taso min...”
Turhan ya shimfida masa kudurinsa sannan ya bijiro masa da bukatarsa.
Aliyu ya dan sosa kansa.
“Akwai wandanda zan hada ka da su ba ma daya ba, amman Turhan kana ganin nemanta abu ne mai sauki? Ni ma fa na saka anbincika maka lokacin da na yi zama a Lagos din nan amman ba a dace ba”
“Wannan karon ina son na bi gidajen marayun da yake cikin garin Lagos ne, na bincika ko zan dace”
“Eh toh kuma ka kawo shawara, amman duk da haka ina ganin zai yi wahala saboda an kwana biyu, kuma ka fada min tun tana karama aka yi rikonta a can, kuma ba lallai ne ka sami ma'aikatan gurin na da ace su ne har yanzu?”
“Yeah amman ina zaton indai sun santa sosai da sosai za su gane ta idan na bada misalinta wata kila za a dace”
“Dama dai kana da hotonta abun zai fi sauki”
“Haka din ma zan gwada wata kila a dace, ina tunanin duk wanda na fadawa sifofinta blue eyes red hair, fara mai kiba sosai zai gane ta matukar ya santa”
“Allah yasa a dace, zan yi magana da wani yarona da yake can da safe sai na hada ku”
“Okay thank you”
Ya aje wayar ya sake zaunawa kusa da matarsa, wannan karon sai ta tashi zaune tana kallonsa.
“Kyakkyawana”
“Hmmm”
Ya amsata yana wani tunanin na dabam, har idonsa suna motsawa, sai kuma ya tabe baki zuciyarsa na raya masa abun da be isa ya fada a gaban matarsa mai tsananin kishi ba.
“Kana ji na”
Ya aje wayar ya mika mata hankalinsa gaba daya.
“Ina jinki Sarauniyata”
“So nake ka yi min wani alkawari”
“Na me?”
Ta yi shiru na wani lokaci kamar mai nauyi fada sai kallonsa take tana nokewa kamar marar gaskiya.
“Na miki alkawari cewar ba zan kara aure ba bayan ke?”
Ta daga masa kai tana mamakin yadda yayi saurin lagonta.
“Eh ya aka yi ka gane me nake son fada?”
“Na sanki da kishi ne ai, zuciyarki zata raya miki idan na fita waje mata nake kulawa ko?”
“Na san ba halinka ba ne, ba zaka kula mata ba, amman su matan za su iya kawo maka hari kuma zuciya bata da kashi, kuma ni gaskiya ba zan iya sharing dinka da kowa ba”
Yayi murmushi ya shafa fuskarta.
“Saka ranki a inuwa, Aliyu na ki ne ke kadai daga ke babu kari babu wanda zata kawo hari na rufe kofa, na miki alkawari ba zan taba miki kishiya ba”
Ta bude ido tana mamakin yadda yayi hanzarin bata hadin kai da wuri haka, ko da yake ta san waye mijinta ba mutum ne mai son mata ba, kuma ya sha fada mata tun kamin ya aureta cewar shi ba shi da ra'ayin aure mace sama da daya.
______________
Anya Aliyu zai rike alkawarin nan kuwa?
Turhan zai samu ganin Aisha kuwa?
Wane irin so Vito yake yi ma Emily?
Meyasa Emily ta dage sai ta yi aiki? Bayan duk gatan da ta samu a gurin Vito?
[4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Barka da warhaka mutanen arziki😍
Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda ɗan mutum da mutum😃
Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser.
Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing ɗina.
Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp.
KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less...😊
Page 5️⃣
Bata sauko ba sai da ta tabbatar ya fice daga gidan, sannan ta sauko ta sakawa Fatima lunch dinta a lunch box ta shirya mata komai kamar yadda ta saba, Londom kuma da ake masa darasi a gida sai ta zuba masa a nasa na nasa kayan cin abincin, sannan ta haura saman ta shiryawa cikin shiga ta riga da wando ta saka turare ta maida sarkar Cross dinta a gaban rigarta yadda zata fito da kyau.
Red hair dinta ma ya faku da kyau ta yi kyau ta fito tsab, kana ganinta ka ga kyakkyawar mace mai aji, da matukar daukar hankali. Id card dinta na aikin ta fara dauka ta saka sannan ta dauki jacket ta saka saboda yanayin garin akwai sanyin sai dai ba sosai ba. File din jiya ta dauka tare da jakarta ta wayarta ta fice daga dakin, sai da ta shiga dakin Londom ta duba shi ta sunbance shi sannan ta fito ta leka dakin Fatima, sai ta same ta zaune da alama farkawarta daga bachi kenan. Da murmushi Emily ta karasa kusa da ita ta aje kayan dake hannunta ta shafa kanta.
“Good Morning Princess”
Fatima ta kalleta ba tare da tace komai ba.
“Okay jiya na san mun yi fada kamin ki kwanta kin kwanta da fushina I'm sorry”
Ta bata fuska.
“I just hate Vito Mom, ke kuma kullum kina shigar masa baki ganin laifinsa”
“Princess V be mana komai na ganin laifi ba, yana kula da ku yana kula da ni, gidan nan da duk abun da yake ciki nasa ne, be taba mana komai ba”
“I just hate him, bana son ki aure shi Momy”
Ta fada cikin kuka, Emily ta juyo ta fuskance da kyau damuwar ganin hawayen yarta na bayyana a fuskarta.
“Ba aurensa zan yi ba, ni na gama aure a rayuwata, amman baki da dalilin tsanarsa, shi yake kula da mu, shi kadai ne mutumen da ya rike ni ba tare da kyama ba, shi kadai ne ya kaunace ni a yadda nake yake kokarin kyautata min, shi ya maida ni yadda nake a yanzu”
“Ya fada min aurenki zai yi ko da bana so, yace min na fara kaunarsa tun a yanzu saboda shi zai zama step father dina”
“No no... Princess ba zan auri kowa ba, ba zan aure shi ba, ba zai zama stepfather dinki ba, but ya kamata ki girmamashi”
“No... To mu bar masa gidansa Momy”
Emily ta shafa fuskarta.
“Shi ne kudirina, amman ba zan iya haka ba sai na tsaya da kafafuwana, shiyasa na dage nake son fara aikin nan, zan rika saving kudi idan na tara zan koma wani gurin za mu bar masa gidansa da komai nasa, na miki wannan alkawari Fatima”
Fatima na jin haka sai ta rumgume ta da sauri tana murna.
“Promise Mom”
“I promise”
Ta fada yana shafa bayan yarta, Fatima ta dago daga jikinta ta rike fuskarta.
“Momy a ina kika samu aiki”
“Wani babban kamfani ne dake hakar ma'adanai da bincike akan albarkatun kasa, babba guri mai girma kuma mai hawa har biyar”
“Ke a hawa na nawa kike?”
“Na hudu, ina aikin da wata mace mai mumman hali, sunanta Amal kin san musulmai ba su da kirki ko? Ita ma bata da kirki ko kadan”
Fatima ta wara ido kamar ba ita ce ta gama fushi dazun ba.
“But I'm Muslim Mom you know”
Emily ta ja kumatunta.
"You're different because you were raised by a Christian mother"
Ta yi dariya ta sauka daga kan gadon, Emily ta bita da kallo tana jin kaunarta sosai, haka take son yaranta fiye da kanta, tana son farincikinki yaranta fiye da nata, bana son su rasa komai domin ta san yadda ake ji idan ka rasa wani abu, domin ta tashi ita kadai ba tare da yan'uwa ko iyaye ba.
Ta sani ta rasa farinciki, sai dai ta daukarwa kanta alkawarin ba zata yarda yaranta su rasa farinciki ko su shiga makamanciyar kazantacciyar rayuwar da ta shiga ba. Tana zaune gurin har Fatima ta fito daga bandaki ta shimfida karamin sallayarta ta dauki hijab, kallonta kawai take cike da burgewa tana jin dadi tana jin farinciki a duk lokacin da ta ga yarta tana ibadar da ta zabarwa kanta, bata son tauye mata hakki ko kadan hakan ya saka ta barinta ta aiwatar da addinin da ta dorata akanshi da farko kamin ta yi kokarin canja mata ra'ayi hakan kuma ya gagara saboda abun da shiga zuciyar Fatima sosai. Even though ba ko da yaushe take sallah ba, amman duk inda zata shiga ko a tambaye zata fadi cewar ita musulma ce, hakan kuma ya kan bawa duk wanda ya san mahaifiyarta mamaki, domin mutanen da suka san Emily a yanzu sun santa a Christian, kamar yadda sarkar Cross din dake wuyanta take nunawa a kullum.
“Okay Princess zan tafi aiki, na san yanzu Chidimma zata shigo ta shirya miki zaki tafi makaranta, i love you”
Ta fada sannan ta mike tsaye ta dauki kayanta ta fice daga dakin. Ta yi tafiya sosai kamin ta samu abun hawa kasancewar safiya ce ba kasafai ake samun ababen hawa a unguwar da safe irin lokacin da ta fita ba, gashi bana da ra'ayin amfani da motar da V ya siya mata tana son nesanta kanta da wasu abubuwan ne tun a yanzu.
Karfe bakwai daidai mai texi din ya shiga da ita cikin kamfanin, sai da ta sallame shi sannan ta fita tana kallon yadda a yanzu ake bude wasu bangaren ma, masu shara da mopping na yi. Tsirararun mutane ne kawai suke shigowa a kamfanin. Kai tsaye ta shiga ciki ta hau Elevator zuwa 4 floor din da take, a nan din ma ta samu masu mopping suna gyara floor din. Da Keys din hannuna ta yi amfani ta bude kofar Office dinta ta shiga sai ta shiga ga mamakinta sai ta samu an goge ko'ina. Da mamaki ta aje file da jakar hannunta ta fito ta tambaye wani namijin dake mopping a gurin.
“Dan Allah ka ga wanda ya shiga office din nan?”
“Gaskiya bayan ni babu wanda ya shiga”
“Kai ka gyara office din?”
“Eh ni na gyara ni nake gyara ko'ina ai”
“Kana da key din dakunan kenan?”
“Eh ni nake kula da ni ni aka hannatawa komai”
“Okay sannu da kokari”
Ta koma ciki, har ta zauna sai ta tuna da Office din Amal a take ta yi hanzarin tashi ta fito ta nufi office din ta bude sai ta juyo ta kalleshi.
“Me yasa baka gyara nan ba?”
“Tace ke zaki rika gyara mata”
“Okay...”
Ta furta with little bit of confused, why her? Bayan ya fada mata shi yake gyara ko'ina, ko da yake Amal din ta fada mata da kanta tun a ranar farko.
“Idan ka gama ka ara min mopper zan gyara gurin”
A madadin ya bata sai yayi mata jagoranci zuwa gurin da ake aje moppers din ta dauko daya da tsintsiya ta gyara office din tsab sannan ta mayar ta aje. Komawa ta yi office dinta ta zauna bata san me zata yi ba dan haka ta bude data ta ta shiga social media sai misalin tara ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa. Misalin 9:15am telephone dinta ta yi ringing, a gurinta abu ne sabo a kirata da telephone in her own office, sai da ta yi murmushi sannan ta amsa kiran
“Hello”
“Ki same ni a office”
“Oka...”
Kamin ta karasa wayarta furta okay din Amal ta aje telphone din. Emily ta mike tsaye ta fice daga office din zuwa office din Boss dinta. Tsayawa ta yi tana knocking domin bata manta gargadin da tayi mata ba a jiya.
“Yes”
Ta mata izinin shiga bayan ta bata lokaci tsaye a gurin.
“Good Morning Maa”
“Na fada miki sunana Amal ki daina kirana Maa kamar wata tsohuwar”
“I'm sorry”
“Waya gyara dakin nan yau?”
“Ni na gyara”
“Good, sauraka kasa ki samo min snacks zan yi breakfast da ki siyo min bubble tea”
Ta jafa mata Atm dinta, tana duba wasu takardu.
“Ina file din da na baki jiya”
Emily ta kalli Atm din dake kasa, me yasa ba zata iya bata da hannunta ba ko ta dora a tebur ta dauka? Me yasa take son wulakantata? Ko da yake ba abun mamaki ba ne ita din ai musulmace, ta duka ta dauki Atm din tana amsa mata.
“Yana office dina”
“Idan kin ga dama ki kawo nan”
Kallonta kawai Emily ta yi ta juya ta fice daga office din, nata office ta koma ta dauko file din ta sake knock ta tsaya har sai da ta yi mata izinin shiga sannan ta shiga ta aje mata ta fito. A nan kuma ta fara tunanin ina zata samo mata snacks da bubble tea a yanzu, ita ba sanin kamfanin ko unguwar ta yi sosai ba.
Haka dai ta nufi elevator ta danna botton din dake jiki ta bude mata, ta shiga sannan ta taba number 1, a take ta fara yin kasa har ta isa first floor ta fita, wata zuciyar na fada mata ta tambaye mutane wata zuciyar kuma na hana ta, ita wa ta sani ma balle ta tambaya. Haka ta mike ta fita daga roof din kamfanin ta mike doguwar hanyar har ta isa gate. Ta kalli dama ta kalli hagu kaminnta yanke shawarar nufar left side tana tafiya tana dubawa ko zata samu mai siyar da wani abu amman bata samu ba sai da ta bar unguwar gaba daya ta shiga wata karamar unguwa dake kusa da su, sannan ta fara ganin masu siyar da abubuwa wasu ma yanzu suke fitowa domin goma ta dan gota.
Abubuwan da ta fada su ta siya mota ta biya da Atm din sannan ta sake juyowa tana takowa a kafa, tun tana tafiyar tana jurewa har ta fara gajiya ranta ya fara baci, tana daf da isa kamfanin ta ji an yi mata magana da shigar da Vito ne kadai yake mata haka.
“My Beautiful Babe”
Ta kalli gefen da titi yake sai a lokacin ta lura da motar dake binta, yadda fuskarsa take hade kai kace ba shi ne yayi mata furucin mai dadin sauraro ba, dan murmushi ta yi ta tsaya har ta bude motar ya fito, tana mamakin ganinsa. Ko da yake ba abun mamaki ba ne domin ya san kamfanin take aiki kuma kamfanin ba boyayyen kamfani ba ne.
“Waya aike ki siyen abu?”
Ta kalli robobin dake hannunta da bubble tea.
“Uhmm...”
Ta yi shiru kamar mai tunanin abun da zata fada.
“Ba ki sha Bubble tea na sani, kuma na shirya miki breakfast kamin ki fito, so don't lie to me”
“My Boss”
Ya gyara tsayuwarsa yana jin ba dadi.
“Are you a maid hare? A aike ki ki siyo abinci shi ne aikin nan Babe?”
“No ita kadai ce ta aike ni, saboda a karkashinta nake aiki, kuma ta zo bata karya ba”
Ya kalli kayan dake hannunta da kyau sannan ya sake kallon fuskarta.
“Ba ki rasa komai a gida ba, ban san miyasa kika zabi wannan rayuwar ba”
A kokarinta na kawar da zancen ta ce.
“Me ya kawo ka nan?”
Ya sauke numfashi a hankali ya matsa kusa da ita sosai.
“Na zo ne na yi miki bankwana zan tafi Lagos yanzu, akwai kayana da aka rike dole sai na tafi za a sake su”
“Drugs...?”
Ta tambaya kai tsaye, be amsa mata ba sai kawai ya kai middle finger dinsa yana shafa soft kuncinta na dama up and down, idanuwanta cikin nasa ita tana jira amsar tambayarta shi kuma kaunarta kawai ke kara zafafa daga idonta zuwa nasa idon then straight to his heart. Dauke yatsansa yayi ganin tana kokarin kawar da fuskarta ya juyo ba tare da yace da ita komai ba ya bude bakar motarsa mai bakin gilashi ya shiga ya ja ya barta tsaye a gurinta yana kallon sawunsa.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta karasa cikin kamfani, a nan ma sai da ranta ya kara baci saboda tafiya ce mai tsayi daga gate din zuwa cikin kamfanin, haka dai ta daure saboda tana son aikin, daman hausawa sun ce daukarwa ya fi bauta ciwo.
ALIYU POV.
Yana daura necktie dinsa ta aje masa littafi a gaban madubin da yake shiryawa ta zauna gefen gado tana kallonsa. Kallon littafin yayi sannan ya kalleta
“List din yaudara za a fara min? So kike duk sai kin karar da abun da na tara kin maida ni talaka ko?”
Ta saka dariya tana kai apple din dake hannunta a baki.
“Aa Wallahi kasan jiya ka yi min alkawari, to ni dai ban gamsu ba so nake ka rubuta, domin a doka ya fi ka'ida”
Ya zauna kusa da ita yana murmushi mai sauti.
“Rantsuwa fa na yi miki jiya baki yarda ba?”
“Na yarda amman dai kara ayi a rubuce ko da ka manta na rika tuna maka, ni fa a rayuwata babu abun da na tsana irin kishiya, ni bana sonta ko kadan, ko wata macen ka kalla a tv bakinciki nake ji, kuma mata a yanzu sun yi yawa da kansu ma suke kawowa mazan mutane hari, idan na mutu dai sai ka yi aure amman idan ina raye ban yarda ka yi aure gaskiya”
Ya girgiza kai, ya dauki littafin yayi rubutu a kai.
“Ni Aliyu Mudallab na yi alkawari ba zan yi ma Matata Aisha kishiya ba, har abada zata zauna ita kadai a gidana sai yayanta”
Yana rubutawa yana fadar alkawarin har ya gama yayi saka hannu, ba tare da tunanin komai ba, domin har ga Allah ba shi da ra'ayin kara aure.
“Hakan yayi miki?”
Ta daga mishi kai tana murmushi sonsa na karuwa a ranta. Bakinta ya sumbanta kadan sannan ya mike tsaye
“Sarkin kishi, anya zaki bar ni a aljanna na more hurul'aini kuwa?”
“Wallahi ba zan bari ba”
Ta fada da karfinta, kyalkyalewa yayi da dariya sosai ya dauki abubuwansa ya fice tana masa addu'a tare da rakiya har kofar falo. Sai da yayi addu'ar fita daga gida sannan ya fice ya shiga motarsa yana dago mata hannu da blowing mata kiss sannan ya fice. Karatun Qur'ane ya kunna a motar kamar yadda ya saba, domin baya sauraren waka idan ma yana son rage kadaice ne sai dai ya saurari karatun ko ya karanta ko ya rera kirar da kansa.
Kamar kullum baya shigowa sai 11am ko fiye da hakan ma, idan yayi sakammako shi ne zai shigo 10am, kasancewar CEO na kamfanin, sai dai kuma baya barin kamfanin sai 3pm ko 4 sometimes har 5pm ya kan kai idan aiki yayi yawa, ko wani Meeting. Ya faka motarsa a gurin da aka tanadar masa sannan ya bude motar ya fito, iPod dinsa ya saka a kunne ya cigaba da sauraren karatun Qur'ane a kunnensa na hagu, ta ko'ina ya wuce gaishe shi ake har nufi elevator, matar dake cikin yake kallon irin kallon nan da ya kasa kyabta ido ma balle ya dauki, kallonta yake da kyau yana tantancewa, tunaninsa kuma yana tafiya wani gefen.
Yana shiga ciki sai ya taba 5, a take Emily ta taba 4 ba tare da ta kalleshi ba.
“Ni na fara zuwa”
Be ce mata komai ba bayan karkatowa da yayi ya kalleta ya kalli ID din dake kirjinsa, ita kuma sai ta yi zaton kirjin nata yake kallo, hakan ya saka ta kokarin gyara rigarta da maballi sama yake bude ya bayyana wani bangare na kirjinta sai dai be fito da dukiyar fulaninta ba. A kokarinta na yin hakan Bubble tea din dake hannunta ya fadi ya zube. Bakinciki ya saka bata san lokacin da ta fara yi masa ihu ba.
“Kallo har na bala'i har na masifa, ka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 63