Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yayan kanwa ne, wato su kansu abokan wasan junansu ne. Yayana samanin tattalin arziki ne, gwararre ne sosai a bangaren Economics shiyasa mahaifinmu ya dauke shi ya damka masa rabin ragamar kasuwanci a yanzu shi yake tafiyar da komai, Mahaifina kuma ya maida hankali gurin Siyasa, ni kuma na karanta Engineering ne wannan ya saka ake yawo da ni gari gari gurin aiki, na zauna a sokoto na yi zama a Kano na zauna a Lagos daga baya aka dawo da ni part hart-cour, tarbiyar gidanmi Alhamdulillah Ummi ta yi kokari da jajircewar Daddynmu, ta bangaren karatun addini duk gidanmu babu rago, ba dan karki ce na yi son kai ba da sai na je na fi kowa kokari ta bangaren Karatu, domin na yi karantar wa a islamiya har uku ba dan a biya ni ba, sai dan na samu ladar kawai, hasali ma ni nake musu ihisani a duk wata, da dare kuma sai na je wata islamiyar maza da ta zama majalisi na karo karatu, a islamiyar ne ma na hadu da matata wadda nake aure a yanzu, Kameela. Dalibata ce mai kokari sosai tana da kaifin basira tana yawan zuwa makaranta even though dai takan taba rashin jin magana sosai a makaranta domin ana yawan kawo min kararta, amman ni ban duba wannan ba, na duba karatunta ne domin ni ina son mace mai addini saboda yayana su samu uwa ta gari, sai dai kamin mu auri junanmu mun sha gwagwarmaya saboda iyayenta bata so na, ni ma kuma Ummi na ba wani gamsuwa ta yi da auren ba kawai dai ta mara min baya ne saboda tana son abun da yayanta suke so, banbanci jam'iya da kuma yin nasara da faduwa ya yi tasiri sosai a gurin iyayenta har ta kai suna kallonmu a matsayin makiyansu, ada abun ya fi haka tsami ma, amman dai auren mu ya saka an yafe wasu abubuwa wasu abubuwan kuma an ba shi baya, a lokacin akwai masu son Kameela ita kuma ni take so, iyayenta kuma Governor da yake Mulkin garin Kaduna a yanzu His Excellency Rilwan Mu'azu Mai Nasara shi suka so ta aura, domin abokin mahaifina ne kuma gashi yana Governor, da ta aure shi ita ce zata zama first Lady domin matarsa bata yi karatu mai surfi da zata iya tsayawa a gaban mutane ta yi turanci ba, amman kishi be bar Kameela ta amince da zabin iyayenta ba, kuma kishi be bari kudi ya rufe mata ido ba. Kameela mace ce mai kishi sosai gaskiya, daga lokacin da na fara soyayya da ita na gano haka, bata bari kowace daliba ta kalle a inda nake karantarwa, tun ina boye alakarmu ina jin kunya sai ga shi ta bayyanawa duniya, yadda take yawan fada da dalibai a makarantar a kaina sai ki dauka ni kadai ne namiji, kuma wasu da yawa ba so na suke ba kawai gaisuwar mutunci ce da girmamawa a matsayina na Malaminsu amman duk bata duba wannan ba, an kai ruwa rana tsakanina da iyayenta da kuma iyayena har ta kai na ce ni na janye daga auren saboda ba zan dauki wulakanci ko raini ba, sai dai damuwar da Kameela ta shiga a lokaci saboda tana tsananin so na ya saka na dawo na yarda zan aureta, amman duk wani hidima da ake ta biki like event ban yi ba sai ta Walima ita ta maza kawai ban da mata, ita ma ta yi nata dabam, amman wani shagalin biki da zai janyo shidai a lamarinmu ban aikata ba, kasancewar ni ba mutum ne mai son bidi'a ba, shekara daya da aurenmu Allah ya ba mu karuwa, amman abun be zo da rai ba, yanzu haka Kameela tana gida gurin wankan amman ta gama tana shirye shiryen dawowa ne, lokacin da kika kira ni naje ganinta ne wayar tana hannunta, kin san mace mai kishi bata iya rike kanta idan ta ji muryar wata macen a wayar mijinta, amman dai na ja mata kunne, wannan shi ne takaitaccen labarina, ina fatar a yanzu hankalinki zai kwanta da Aliyu" Ta yi murmushi sosai ta ji dadin yadda yake tsara mata labarinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali muryar ma kasa kasa kamar mai magana da karamar yarinya. "Ba ki tambayi ya aka yi na san Turhan ba, ko ya aka yi ni da shi muka zama abokan juna" A take murmushin dake fuskarta ya gushe, Aliyu ya saci kallonta kadan. "Kamar na taba fada miki mahaifina yayi rashin nasara har sau uku ko? Sai a na hudu ya samu nasara? Toh a rashin nasararsa ta farko gurin takarar sanata bayan ya fadi zabe sai Shugaban kasa na wacan lokacin ya nada shi ambassador Nigeria to Sudan, a lokacin ne ya tafi har da ni domin Ummi bata yarda yaranta su yi nesa da ita, kusan da mu take shawarar komai da mu take hira kuma Allah ya dora mata son yaya kamar dai yadda kike ji Fatima a yanzu, da muka koma can sai kyakkyawar alaka ta shiga tsakanin Sarkin Sudan na yanzu da kuma mahaifina" Ya mike tsaye ya nufi windows din office din ya bude. "Na manta ban fada miki ba, ni mutum ne mai son wasan tseren doki, wani da wata wasa sai ita a koda yaushe idan na samu free time haka zan hau doki na yi ta zaga gari, idan kuma akwai gurin wasan zan tafi na yi, a Khartoum muke zaune babban birnin kasar sunan a birnin akwai wani babban filin wasa na wasa da dawaki, na kam tafi yin wasa duk Weekend, duk yadda nake da son wasan dokin nan Turhan ya fi ni, kuma ya fini gwanewa domin shi dan sarauta ne ni kuma haye na yi, a duk lokacin da muke je wasa akan shirya tsare tsakanin yayan manya ko yan sarauta, wata rana sai aka hada mu na nuna gwanewa shi kuma ya nuna min ya fi kwarewa akai, da haka dai muka sabu ya zama mun san junanmu idan an shigo za a gaisa, har kai idan na shigo be shigo ba wasan baya dadi ni ma bana shi dadi haka shi ma ta bangarensa. Muka fara following juna da a social media, har ta kai muna gaisawa a waya ko chat, har mukan hadu mu yi hira ko mu tafi wani gurin shakatawa da dawaki. A lokacin Turhan ba shi da ikon shiga Nigeria ba Nigeria kadai ba mahaifinsa be yarda ya bar kasar ba, har ya kan bukaci na ba shi tarihin Nigeria da yadda kasar take, da ya ji cewar daga kaduna na fito sai yake ba ni labarin mahaifiyarsa yar kaduna ce amman baya zuwa gurinta mahaifinsa ya hana shi fita Kasar saboda kar ya tsallaka ya tafi gurinta, amman ita an mata lamuni tana zuwa ganinsa, kuma suna magana da waya, wata rana tsaman sai gashi ta shigo da kokon bararta gurin Mahaifina ta hanyar Ummi, tana son Daddy yayi mata tsaye a bawa Turhan damar ziyararta a duk lokacin da ta so, mahaifina ya sha wahala sai da ya jajirce sannan sarkin ya yarda domin ganin yake kamar Ammy zata karbe masa Turhan ne, kuma su a gurinsu bakar fata ba shi da wata kima, like kamar mahaifin Turhan be so mahaifiyar Turhan ta zama bahaushiya har Nigeria ba, mu kan mu saboda muna yayan manya ne a lokacin ya saka ake daga mana kafa a dole, mahaifina yayi nasarar karya dokar sarkin aka bawa Turhan damar ziyararta kasar a duk lokacin da ya so, saman kuma bayan ni yana da wani amini Munir dan Nigeria ne sosai shi kuma a can yayi karatu a can yayi rayuwa daga baya ya dawo gida, Ummi ta san Turhan, Ammy ma ta san ni ta dalilin abota da kuma abubuwan da suka faru, sai ya zama abotarmu ta kara kwari sosai, kusan rabin hausar da ya iya gurina da Ummi da yaran da Ummi take riko a lokacin ya koya, daman kuma na tarar da shi mahaifiyarsa ta shimfida masa kaunarta da yarenta da rabin al'adarta a zuciyarsa da kansa, amman ma kaunarta Turhan yana son Ammy sosai, daga haka abotarmu ta daure har yau" Ya sauke numfashi a hankali. "Na yi mamaki da na ji kin tsani Turhan har kina gudun ganinsa, domin ban san wani hali mummuna na Turhan ba, shiyasa na kagu na ji wane irin zama kuka yi da shi, taya rayuwarsa ta sauya har ya munana miki haka?" Emily ta kalli hannun Aliyu dake sanye da agogon data dawo masa da shi. "Baka yi tunani ba? Da ace ni yar sarki ce ko kuma balaraba kamar shi ba zai wulakanta ni ba? Farkon abun da Turhan ya fara kushewa a tattare da ni shi ne halittata, kamin ya muzanta tubana, sannan ya kaskanta asalina" Ta yi shiru idonta na cika da hawaye. Ya dauki takardar a gabanta ta ciro pen a aljihunsa ya dora a kai. "Idan ina son na canjawa Fatima suna daga Fatima Aisha Emily zuwa Fatima Aliyu Mudallab ya kike ganin zai kasance rubuta min" "Canja sunan Fatima yana nufin daukar ragamarta ne, tsaya mata a matsayin uba ne a kowa guri a kuma ko wane irin hali" "Abu ne kamar ruwan Sha a gurina ko ban yi dan tana yar abokina ba da zan yi dan ke Emily, ki barta ta dandani dadin da yake karkashin inuwar uba" "Na gode da kokarin da kake ta yi Aliyu, amman wannan karon ya zama dole na yi rejecting wannan offer din" "Idan baki ra'ayin sunana ai zaki iya so na Vito ko? Shi zaki iya rubuta min yadda sunan zai kasance saboda gudun kuskure" "Fatima bata karbi Vito a matsayin Uba ba, ba zata yi farin ciki da hakan ba" "Ban taba tambayarta da kaina ba, ban ji amsar daga bakinta ba, dan haka karki yanke hukunci, idan tana ra'ayi ba sai na saka kin rubuta ba, idan kuma bata ra'ayi kin ga shikenan mun huta" Ta rubuta masa full name din Vito da na mahaifinsa ajikin takardar, sunan da babu wanda ya sani sai ita sai mahaifiyarsa sai kuma amininsa na kud da kud sai kuma daidaikun mutanen da aka haifeshi a gaban idonsu Aliyu ya karbi takardar ya karanta. "Toh ina Vito ya samo asali?" After Aliyu yayi mata tambayar ne ta fahimci babu amfanin using wacan sunan a yanzu tun da ya zabi canjawa. "Shi ya canjawa kansa suna saboda sana'ar da yake a yanzu kowa Vito yake kiransa amman ya fada min ba asali sunansa ba ne" Aliyu ya dan yi murmushi kadan yana kara karanta sunan. "Za a iya kiranta Fatima Vito" "Mun gama da yau zaki iya tafiyarki a yanzu, gobe zaki zo aiki karfe 9am haka zaki rika zuwa kullum, Good Luck" Yana fadar hakan ya fice ba tare da ya tsaya jin ra'ayinta ba, is like kamar ya mata umarni ne, yana son ta bishi ta fada masa ba zata iya aikin ba amman ta kasa, lokuta da dama kimarsa bata bari ta musa masa wani abu. ALIYU POV. Office dinsa ya dawo the first time da ya fara yi after zamansa shi ne ya dauki wayarsa dake kan teburin ya duba miss calls din Kameela da kuma sakonta wai ya dauki wayarta ta ji sanyi. Yayi murmushi ya girgiza kai bayan ya gama karanta sakon, sannan ya kirata. Tana daga wayar ya ce. "Idan kin san zaki min maganar Emily ne ko wasu mata ko maganar kishi to ki bari na aje wayata ba sai mun sake kai ruwa rana ba" Sai kawai ta fashe masa da kuka. "Yanzu kuma mi na yi? Waya taba min mata yar jaririya ta yar amanata rabin rayuwata?" "Amman idan ni ce wani yayi min magana ai zaka ji haushi ko?" "Ke ai mace ce a karkashina kike kin san hukuncinki, ni kuma namiji ne, kuma ba lallai sai aure ko soyayya zata hada ni da mata ba, kuma karamar magana sai ki dauketa ki kai a gaban iyaye, na ja miki kunnen Kameela akan kame baki da rike sirri amman babu abun da ya canja" "Ka yi hakuri" Ta fada cikin kuka. Sai ya fadada murmushinsa. "Komai ya wuce yanzu ai, sai ki kiyaye domin ba zan daukar miki wannan ba, yanzu yaushe zaki dawo?" "Ka wuce ko?" "Eh mana, naje gurin Ummi har na dawo gida...." Daga haka ya dauko mata hirar yadda ya so su tafi gurin Ummi su kwana biyu amman ta ruguza komai, sun dade suna magana a waya har ya katse kiran ya kirata Video Call suka ga juna sannan ya fada mata Ummi zata aiko ayi bikonta. Yana gama wayar da ita ya taba chat kadan ya kira mahaifinsa shi kam sun dauki kusan awa daya suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Sai da ya tashi daga aikin gaba daya ya dawo gida sannan ya kira Ummi suna gaisawa ta yi masa maganar Kameela daman ya san zata masa shiyasa ya kira kawai ya gaisheta, daga karshe ta hanye shawarar aikawa ayi masa bikonta daga Kaduna kai tsaye a kawo masa ita har PH. KAMEELA POV. Bayan ta gama wayar da Aliyu a falon Mama Barakat ta mike tsaye zata fice ranta fess kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da zata kira shi bangaren step Mom din tasu take zuwa saboda gudun kar ya amsa su samu matsala ko kuma yayi mata wata maganar marar dadi yan'uwanta su ji, gashi kuma Mama Barakat tana yabon Aliyu yana dan mata nasiha yadda zata bullowa lamarin ko ta zauna da shi, ba kamar uwarta da yan'uwanta da suke zugata ba suna zagin Aliyu, shiyasa ko kadan bata son su san tana kiransa ma, haka idan ya tura masa sako sai ta goge saboda kar a dauki wayarta a duba ace naci take masa da magiya. "Haka ya fi, ki daina bari shedan da zuciya na shiga tsakaninki da mijinki" Cewar Mama Barakat tana kokarin zama, ba dan ta ji tattaunawarsu ba sai dan ta ga alamar komai ya wuce a fuskar Kameela da Kuma muryarta. "Ke yanzu ko kishiya za a miki ai be kamata ki tada hankalinki ba Kameela kina da kyaunki daidai gwargado, mace bata gwada miki komai" Ta tabe baki. "Mama Barakat baki ganta bane, kyakkyawa ce kuma yarinya, ina tunanin ma duk yadda aka yi baturiya ce tun a gidan marayu ta tashi wata kila jefar da ita aka yi ko tsintarka, domin gashin kanta ja ne irin na turawa idanuwanta blue ga farinta ma ba fari ne irin na mu ba fari ne irin na turawa" Mama Barakat ta natsu sai kuma ta yi jimmm kamin ta ce. "A a ina take?" "Lagos wai" "Miye sunanta?" "Aisha amman Emily ake ce mata" "Tana da yara? Kina da hotonta?" "Ni mi zan yi da hotonta? Ko kishiyata ce ai ba zan aje hotonta ba balle wata banzar alaka can gamon tsintsiya da ragga, tana da yara, baban yarinyar ma nemanta yake ruwa a jallo wannan matar criminal ce, kin san daman yan Lagos da wadanda ba hausawa ba ba su da tarbiya ita kanta nemanta yake amman kin ga ta mallakewa mijina, ai Wallahi ina komawa ko dai Aliyu ya zare hannunsa daga gareta ko kuma duk yadda za'ayi ayi, haka kawai wata katuwar banza ta lakewa mijina" Tana sane take fadar yan Lagos ba su da tarbiya da kuma yare saboda Step Mom din ta ji haushi, ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya domin ta ciki na ciki ba son Mama Barakat take ba ko da kuwa zata bata duniyar nan, ta mike tsaye ta fice rike da wayar zuciyata cike fal da kiyayyar Emily. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/25, 9:50 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣0️⃣ ONE WEEK LATER... Ba zata iya musa masa ba, dan haka ta amsa bukatarta ta dora tata bukatar akai. Tun a washe garin wacan ranar ta cigaba da zuwa aikin, sai dai a tsawon zuwan da take bata fada ma Tasmia cewar ta koma aikin ba duk kuwa da irin dukan ruwan cikinta da Tasmia take na son ta ji labarin Aliyu ta, tana yawan tambayarta ya kira ki? Kun yi waya? Emily ta ce mata aa saboda gudun kar Tasmia tace bata dauki shawararta ba, ba kuma dan bata gamsu da shawarar ba, sai dan Tasmia ta bata ba sai dan bata son musawa Aliyu ne. Kusan tun da ta koma aikin bata hadu da Aliyu ba, ko a hanyar shiga Office dinta ko nashi, hakan kuma sai ya kara mata kwarin guiwa da natsuwa, da fari ta yi tunanin ko zai takura mata ne ko dan neman jin karashen labarinta da Turhan, ko kuma ya nemi wani abu a gurinta ko da yake Tasmia ta fada mata bata gama karantarta namiji ba ne, wata kila haka ne wata kila kuma ita din wawuyace shiyasa ta kasa son mai sonta tsakani da Allah, amman kuma idan bata so Vito ba wa zata so? Ai bata isa ta bude zuciyarta ga wani ba. Ta gama saka dankunnenta ta dauki jakarta ta fito tana tafiya a hankali, tun da ta fito Chidimma ta hade rai saboda yadda Vito yake kallonta har ta iso gurin dinning din ta dora jakarta ta fara zubawa kanta abinci. "Good Morning Beautiful" Ta juya ta kalli Chidimma dake kujera biyu kamin tata. Hakan kuma ba karamin bakantawa Vito rai yayi. "Why would I called Chidimma Beautiful?" Chidimma ta ji kamar an tsomata a ruwa tsabar muzantata da yayi agaban Emily, ba kuma dan bata da kyaun ba, sai dan a gurinshi babu wata mace mai kyau sai Emily. Emily ta kalleshi. "Because she is pretty, isn't she?" Ta fada tana kai abinci a bakinta, da ido Vito yayi ma Chidimma magana sai ta tashi ta dauke abincinta ta bar dinning din. Ya dora hannayensa kan dinning din "Miyasa kike tunanin zan ga kyaun wata mace idan kina nan?" "Da bata da kyau ai ba zaka sakata a matsayina har ka ci abinci a teburi daya da ita ba, har ka nemi ta dafa maka abinci, ko ba haka ba VITO" Ta ambaci sunansa da babban baki, madadin yaji haushi sai yayi murmushi, bukatarsa ta biya daman makasudin yin hakan saboda ya gani idan zata ji kishi ne, idan har ta ji kishin hakan ya nuna tana son shi kenan. Ya jimgina da kujerar dinning din yana cigaba da kallonta, kamin ya ciro wayarwa dake vibration ya duba sannan ya amsa kiran. Yayi shiru na dakiku yanayin fuskarsa ya sauya zuwa bacin rai. "Ganin nan zuwa" Ya mike tsaye sai ta kalleshi tana kai lemu a bakinta. "An sake kama kayanka ne?" Har yayi gaba sai kuma ya juya ya kalleta. "Nope wani ne yake wasa da rayuwarsa, someone set me up" Ta aje glass cup din. "Me kake nufi?" "NDLEA aka turo su bincike gidana daga Abuja" Ta mike tsaya da sauri ta karasa inda yake tsaye. "Kuma zaka tafi" "Yes ina bukatar na tafi" "Aa karka je dan Allah bamu san manufarsu ba, gashi kana da saurin fushi ba mu san abun da zai faru ba" Ya shafa fuskarta. "Babu abun da zai faru" Ta rike hannunsa tana girgiza masa kai idonta har ya fara tara hawaye. "Ya kamata na tafi ko dan na nunawa wanda ya turo su wanene ni" "Be zama lallai turowasu aka yi ba, sana'ar da kake yi ba mai kyau bace kana jefa rayuwarka be kawai cikin hadari, daman dole wata rana za a iya bincike za a iya ganeka" Tana maganar tana kuka jikinta na rawa gaba daya ta tsorata. "Set up ne, NDLEA da suke da nan ko jami'an tsoron duk mutanenmu ne, shiyasa ba ayi amfani da su ba aka turo baki daga Abuja, amman ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru" Ta girgiza kai. "Aa karka je" "Dole sai na tafi ai, suna bukatar ganina" "Kace musu baka nan" "Ina nan" Ya amsa mata yana kai hannanyensa ya rika fuskarta. "Toh ka aje bindigarka karka je da ita" "Zata min amfani" "Idan zaka je da bindiga ba zan bari ka tafi ba" Ta rumgume shi tana kuka, sai yayi murmushi ya dago ta daga jikinsa. "Ba zan je da ita ba" Ta fara lalaben aljihunsa. "No idan kika taba zata samu shatin hannunki, idan na aikata wani laifi da ita aka yi bincike za a samu shattin hannunki kai, ba ni bukatar haka" Ya cire bindigar da kansa ya nufi Kitchen ya dauko wata madaidaiciyar cooler ya saka bindigar ciki sannan ya fito rike da wuka ya nufi gurin da Swimming pool dinta yake yayi gina a inda kasa take ya saka cooler ya rufe sannan ya janyo daya daga cikin kujerar da suke aje a gurin ya dora a sama, sannan ya kalleta ya ce. "Ko da bincike ya biyo ta nan baki da matsala babu wanda zai san da wannan you're safe" Ya rika hannunta ya jimke ya saki sannan ya fice daga gurin zuwa gurin motarsa. Biyo shi ta yi ta tsaya tana kallonsa cikin tsoro da tashin hankali, shikam damuwa data nuna masa a yanzu ta gusar masa da duk wani bacin rai da ya ji a lokacin da aka sanar da shi abun da yake faruwa a gidansa. Dawowa ta yi falon ta doshi gurin da jakarta take ta bude ta dauko wayarta, number Aliyu ta fara kira domin shi zuciyarta ta raya mata, wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, ta sake kiransa be daga ba ta sake kira be daga ba, sai da ta jera masa miss calls kusan tara sannan ta maida wayar ta dauki jakarta ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta cause she want to see him badly... ALIYU POV. Tana kallon yadda ya saka wayar da ake ta kira tun dazun a aljihu ya ki ya amsa kiran sai ma saka wayar da yayi a silent kuma ya ki ya aje a inda zata ga sunan mai kiran zuciyarta ta raya mata ba kalau ba, amman bata nuna masa ba da ya gama saka turare ta mika masa agogon da ke aje, ya karba ya fara sakawa. "Yaushe ka siya agogon nan Honey?" "Wannan agogon ina da shi, bata yayi sai yanzu na ganshi" "Da alama yana da muhimmanci a gareka kusan tun da na dawo kullum shi kake sakawa idan zaka je aiki" Ya kalleta da dan mamakinsa domin be yi zaton ta maida hankali a gurin ba. "Toh har kin saka min ido kenan, yana da tsada ne shiyasa duk wanda zai gan ni da shi zai san babban agogo ne" "Hmmm" Ta furta sannan ta mike tsaye ya kama hannunta suka fito seating room, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna ya ciro wayarsa gudun ya zaune ta domin ya sakata

Chapter 24 of 63