Aliyu yace yanzu kina murnar zuwan Fatima a bari sai dare idan kun zo kawowata kar a yi ruining din moment dinku"
"Ina wuni Aisha"
Cewar Mahaifiyar Khaleefa. Emily ta kasa amsawa hawaye na sauko mata, kewar ɗanta ya dawo mata farko.
"Wata kila la lallai ki gane mu ba, duk dai Hajiya ta miki bayani kuma ta mana bayanin komai, ashe kin gane mahaifiyarki Aisha, muna miki murna ta fada mana kin yi aure shi ma muna miki fatan alheri, mun zo nan ne saboda neman yafiyarki, abubuwan da suka faru wadanda ba su yi dadi ba, musamman tsakaninki da Hamza, ki yi hakuri ki yafe masa dan Allah, Wallahi abubuwa masara dadi sun faru kuma mun san hakkinki ne, rayuwa ta zama babu dadi, musamman ma yanzu da ya koma gida saboda mai gidansa ya koresa saboda ke, ya fada mana ya ganki amman an hana shi magana da ke, tun da ya koma kullum cikin maganarki yake, daga karshe muka yanke shawarar zuwa kai tsaye mu nemi yafiyarki"
Cikin tsoro da fargaba Mahaifiyar Khaleefa take magana. Khaleefa ya dago idonsa da suka zare tsabar yunwa da wahalar ciwo ya kalli Emily da a yanzu ko kafarta be isa ya taba ba ya ce.
"Ki yi hakuri Aisha na san ban kyauta ba, na san na zalunce ki na cutar da ke, amman ki yafe min, Wallahi na yi nadama kuma na yi ta nemanki amman ban same ki ba, ban san inda zan ganki ba"
"Kowa ya cuceka sai kawai ya zo ya ce ka yi hakuri shikenan aikinka? Ka cutar da ni, ku biyun nan baku ragawa rayuwata ba, kara Ammy ta nuna min soyayya a baya, amman kai mahaifiyarka tana kallo ka tsake ni, na bar gari na kama hanyar da ban san kowa ba, kuka wulakanta ni kuka wofintar da ni saboda kawai ba ni da kowa, kasan ina da cikin ɗanka amman baka damu da halin da zan shiga ba, idan jininku ce za ku yarda ayi mata haka? Na haihu a titi kamar na haifi shege, na dinga wahala da shi kamar ba shi da uba, har ya bar duniya be san ubansa ba, wai saboda kawai ni mushirika ce na musulunta na bar addini na bi na ku, kuka rika kirana tubabbiya kowa ya kasa tsaya min, kuka hade min kai bana jin sanyi kowa, bayan kuma kai ka rabo ni da inda nake da gata, ka yi aure baka fada min ba sai da na ji, kuma haka be maka ba, kuka bini da gori kuka koreni gidan, sanadin wahalar da ma sha na haifi ɗana ba lafiyayye ba"
Tana maganar tana kuka sosai kukan dake taba zuciya, Aliyu kallonta kawai yake yana kara jin tausayinta da kaunarta suna shiga ransa. Khaleefa ya girgiza kai yana kuka.
"Wallahi hakkinki be barmu ba, bayan kin tafi rayuwa bata mana dadi ba, gidan da kika bar ni ciki ni da matar da na aura gobara yayi komai ya kone, ni kaina daker aka fitar da ni ciki, kalli yadda jikina yayi fuskar babu rabi Aisha, matata bata fita ba, sai yara biyu kawai data haifa min aka samu ceto wa, bangaren mahaifiya aka siyar a gidan aka shiga nema min magani amman har yau ban warke ba, saboda ba ayi treatment din yadda ya dace ba, yanzu haka idan yanayi ya sauya na zafi wutar tana taso min, sun ce akwai cutar har a cikin cikina, Wallahi ba mu da komai a yanzu Aisha, kuma na san hakkinki ne dan Allah ki yi hakuri ki yafe min, aiki ma ya gagara samuwa a gareni sai daker aka dauke ni a gidansu Alhaji Aliyu, ashe shi ma rabon na ganki ne, tun bayan da ya tura ni gida kuma ban sake samu komai ba, ana ba ni da albashin amman kullum gurin magani suke karewa, abun da za'a ci ma wahala yake mana, shin duk ba hakkinki ba ne? Ki yafewa min na zo neman yafiyarki ne da tambayar cikin da na barki da shi"
"Na haifi ɗanka da wahala da bakinciki da ciwo, ya rayu da rashin sanin waye ubansa, ciwo ya wahalar da shi, amman abubuwa sun yi sauki da na hadu da Vito, ya taimaki rayuwarmu kamin na rasa shi, ya rasu cikin ruwa ya fada ba tare da mun sani ba, da taimakon mijina an yi masa sutura an masa sallah an kai shi makabartar musulmi. Zancen yafiya kuma ba zan yafe ba, wannan shari'ar sai an yi ta"
Hankalin Khaleefa ya tashi jin cewar ɗan da aka haifa ya mutu, sai dai tashin hankalin be kai na jin furucin ba zata yafe masa ba. Shi da mahaifiyarsa da kawunsa da suka zo suka shiga bada hakuri. Aliyu ya mike tsaye
"Khaleefa, ina tunanin zai fi kyau ku kuma inda aka ba ku masauki a yanzu, gobe da safe idan kun karya sai ku koma garinku, Ummi na da numberka zan karba, duk lokacin da hankalin Matata ya kwanta ta ji zata iya yafe maka zan kiraka"
Khaleefa ya kalli Aliyu...
"Ranka ya dade ka fahimce ni, idan na koma ba tare da yafiyar Aisha ba, ban san iya abun da zai faru a gaba ba, wata kila rayuwar ba zata kai lokacin da kake zato ba"
"Amman tana cikin damuwa yanzu ba lallai ta yafe maka ba"
Mama Baraka ta fada.
"Bana cikin damuwa, na samu iyali yan'uwa da uwaye, ma samu miji ina da ya, rayuwa ta sauya na gamsu da abun da aka ba ni a yanzu, na gamsu da wannan sakamakon, kawai dai ba zan iya yafewa ba ne"
Aliyu ya nunawa Khaleefa hanya yana jin kamar ya kai masa duka.
"Please..."
Khaleefa ya kalli Emily yana mamakin yau shi ke zaune a kasa tana kan kujera, yau shi yaje neman yafiyarta tana kin yafe masa, yau ita take da mijin da yake kira da maigidansa, ga duniya ta samu tana gida mai kyau gaba daya ma ta sauya kamar ba ita ba, babu wanda zai fadawa cewar ya taba aureta ya yarda. Baya son jayayya da Aliyu saboda ta bangarensa albashi ke shigo masa duk da baya tuka musu mota a yanzu.
"Tohm na barki lafiya Aisha, ina jiran ranar da zaki yafe min, mun gode Hajiya"
Ya nufi hanyar fita yana hawaye mahaifiyarsa kuma na kuka wiwiwi kawunsa kam tun da aka shigo ya ma kasa cewa komai. Bayan sun fita Mama Baraka ta kai hannu ta shafa fuskar Emily.
"Dan Allah ina sake rokin yafiyarki, ki yafe min, duk ni ce silar shigarki wannan halin"
Emily ta kwanta jikinta tana kuka, Mama Baraka ma kuka take tana kara jin tausayin Emily sosai. Aliyu ya sauke kansa kasa. Fatima ta nufi inda Aliyu yake tsaye
"Wanene wannan? Ni ban gane abun da ake ba"
"Mahaifin London ne"
"Amman fuskarsa ta kone fatar wuyansa ta hade, gobara aka yi a fuskarsa?"
Aliyu yayi murmushi ya duka ya dauki Fatima ya fice da ita yana mata hira.
"Na Wahala, a baya rayuwa bata ɗanɗana min dadi ba, na shiga tasko kala kala, an nuna min ƙyama, babu wanda yake damuwa da matsalata, na zauna a gidan Khaleefa abun da zan ci ma sai ya gagare ni, sai na yi wankakau, ina jin ciwo ya hana ni zuwa asibiti sai a biyo kamar zan haifi shege, amman da amaryarsa ta samu cika suka rika murna, ni gaba daya ban haifi yarana da farinciki ba, mazan nan biyu ba su dandana min komai ba sai azaba da rashin imani, bana kaunar ko ɗayansu har abada... "
Emily tana fada tana kuka. Mama Baraka ta kasa cewa komai saboda ta san ita ce silar komai da ace bata jefar da yarta ba da duk ba wannan labarin ake ba. Suna haka yar da Ammy ke riko ta shigo da sallama Mama Baraka ta amsa Emily na share hawaye, har ta gaisa da Mama Baraka ta tambayi Fatima idonta na kan Emily.
"Fatima kamar tana waje ko? Tare da Aliyu"
"Okay, bari na tafi daman na zo daukar ta ne, babanta yana can yana jira"
"Okay tana nan waje"
Ta mike tsaye sai Emily ta nuna mata ledodin dake aje gefen kujera.
"Ki tafi mata da wannan kayan nata ne"
"Tohm"
Ta dauka ta fice. Aliyu be dawo falon ba sai da ya tabbatar hankalin matarsa ya ɗan kwanta da ya shigo sai yake ta kallon fuskarta, baya son yayi zancen ta sake tuna damuwar kuma he need to hug her ko zata ji sanyi dan haka ya ce.
"Bari mu tafi gida dare yana yi, direban ya dauki Fatima sun yafi"
"Eh ta shigo nan ai, yarinyar da ta kawo ta, ban san ko za su sake kawota ko kuma aa"
"Yace zai barta a gurin Ammy ai, idan tana nan da sannu zata dawo hannunmu, ita da kanta zata yi hankalin yin haka ai"
"Haka ne, haka yayi miki Aisha? Idan ba miki ba ke ma kina da hakki sai a masa magana"
Mama Baraka ta tambaya.
"Yayi ko ba komai ya kula da yarsa ba kamar Khaleefa ba"
Sai da suka kara bata minti talatin sannan suka yi ma Mama Baraka sallama daf da za su fita take tambayar yan'uwanta, Mama Baraka tace mata suna daki ita ta hana su fitowa saboda abubuwan da ta san za su faru. Emily ta shiga ta gaisa da su suna ta murnar ganinta har da rumgume ta sannan suka fito gaba dayansu suka rakota har gurin mota ta shiga.
Da suka isa Aliyu ya bude mata mota ta fita ya saka hannayensa ya share mata hawayen dake mata zuba.
"Kukan nan ya isa haka Qalbina"
"Na tuna ɗana, da Vito ne taimake shi ba da Allah kadai ya san kalar wahalar da zai sake sha"
Ta fada jikin mijinta tana kuka, sai ya rumgumeta yana shafa bayanta.
"Indai zaki tuna rayuwar baya ne, zaki yi ta kuka da bakinciki ne, ki manta da komai dan Allah, bana son kukanki balle na ganki a damuwa"
Ya duka ya saka hannunsa biyu ya dauke taya nufi kofar falon, da zai saka key ya bude kofar falon sai ta raba kafafuwanta biyu ta makale masa yayi sama da ita ya saka key din ya bude sannan ya tura ya shiga da ita, a hankali ya zauna kan kujera tana lake a jikinsa kamar yadda yara suke yana shafa bayanta, hausawa suka ce macen da ake so yar gata ce a gurin mijinta. Haka Aliyu yayi ta rarrashin matarsa kayan dadin daya siya mata ma daya dauko daker ya samu ta sha ice-cream din da ya fara narkewa ya bude biscuit ya bata piece daya ta ci ta kawar da kai.
Ta kwana da tunanin abun da Khaleefa yayi mata da kuma London, hakan ya saka ta mafarkin ɗanta, Aliyu na zaune kusa da ita yana lasa waya ya ga hawaye na sauko mata, sai ya kai hannunsa ya share, a firgice ta farka sai da ya rike ta.
"Lafiya? I'm here no one can hurt you"
Ya dawo da ita jikinsa ya yi mata addu'a ya tofa mata ya shafe mata jikinta, sannan ya bude kur'ane wayarsa ya soma karantawa sautinsa na fita, har sai da bachi ya sake dauketa sannan ya aje ya lullube matarsa ta kashe wutar dakin ya rumgume sosai yadda ba zata ji tsoro ba.
Ya san ta kwana da zazzabi saboda a kirjinsa ta kwana jiya, dan haka be bari ta shiga kitchen ba shi ya shirya musu komai na karya, da ya kawo kuma ta gagara cin komai. Ya taba jikinta
"Ki daure ki ci wani abu, sai mu tafi asibiti daman ina son muje tun last week, kawai ban miki maganar ba ne"
Ya kai kunnensa bakinta.
"Daure fada min, me kike so?"
Ta kwanto jikinsa.
"Kai nake so, Abokin Rayuwata my Soul mate"
"Abu mai sauki, a soye kike so na ko gashe?"
Dariya ta subuce mata ta daga kanta sama tana jin kaunar Aliyu, sai ya dawo da ita jikinsa yana murmushi.
"Fada min mana"
"A saka mai da yaji a bani na cinye kayana"
"Na nawa kuma? Ai tuni kika cinye kurwar gangan jikince kawai ta rage, na miki na mayu"
Ta saka dariya tana shafa fuskarsa, da dabara da waya da hira da janta da nishadi ya samu ta yi breakfast din da bata yi niya ba saboda ta farka jikin nata ma babu dadi bata ra'ayin cin komai. Kamin ya dauke ta zuwa asibiti sai da ya saka ka mata booking komai ta yadda da sun tafi ba sai sun wahala ba, haka kuwa aka yi suna zuwa ta hau layi gaba ta wuce ciki likita ta dubata ta yi mata tambayoyi sannan ta rubuta mata maganin da zata fara sha ta bata test din jini ta bata PT tace taje ta gwada idan sun koma gida, saboda Aliyu ya ki yarda ta yi fitsari a asibitin wai it's public place. Jinin kawai ya yarda aka bada sannan ya sauke ta gida ya tafi gurin aikinsa.
The following day shi ya tashe ta bachi kamar yadda ya saba, ya saka ta yi fitsarin ya saka abun awon domin shi ya san yadda ake amfani da shi, ita kam bata sani ba saboda bata taba gwajin ciki ba sai dai kawai ta ganta da shi. A bathroom ya bar abun be sake shiga ba sai da suka gama sallah yayi mata karatu ta koma ta kwanta sannan ya shiga bandakin ya dauki abun gabansa na faduwa ya duba. Ya dube kansa a mirror yayi murmushi mai kyau ya jinjina kai sannan ya fice rike da abun ya isa inda take kwance yayi bedsheet din da aka siya gurin Khadeeja Candy ya kalli fuskar matarsa yana ayyana yadda yaransa za su yi kyau idan suka biyota.
"Alhamdulillah... Alhamdulillah..."
Ya furta sannan ya sumbance ta, ya shafa fuskarta yana hura mata iska a fuska.
"Qalbina... Yi hakuri ki tashi... Ba zan iya barin ki ki yi wannan bachin ba"
Ta bude ido daker ta kalleshi sai ya tada ita zaune ya rumgume ta, da ya ji hakan be masa ba ya mike tsaye da ita ya kwantar da kanta a wuyansa kafafuwanta makale a jikinsa. Ita dai ta yi lamo domin bata san wainar da ake soyawa ba. Daga dakin ya fito falo da ita ya zaunar da ita kan kujera ta ya zube gaban guiyoyinsa ya kama hannayenta yana kallonta with so much emotional.
"Qalbina, ni zan miki albishir, kuma ni zan baki goro, fada min me kike so? Ko me kike so a duniyar fada min zan miki"
Ta zama confused.
"Me ya faru?"
"Komai ma ya faru, fada min"
Ta tsaya tunani mai zurfi.
"Ina son ma tafi makka"
"An gama, sai kuma me?"
"Ina son na tafi Europe"
"Bayan shi?"
"Ina son ka so ni har abada"
Ya matsa da fuskarsa ya hade da tata.
"Sonki har abada wajibina ne, kaunarki ciwo da ba zan taba warkewa ba, na gode Ayusher da kika ba ni damar zama mijinki, kin hada duk wani abun da nake so, kuma yanzu ta hanyarki Allah yayi min wata babba kyauta da ba zan taba iya biyanta ba har abada"
"Minene?"
"Babena you had my baby in your tummy... Daman na san haka zai bayyana tun da kika zo gidan nan ina kirgawa baki yi period ba"
Ta bude baki da dan mamaki, daman ita ma ta zargi haka.
"Ciki ne kawai, kake ta wannan abun?"
Ya zauna kusa da ita ya rike fuskarta kana ganin tasa fuskar kasan yana cikin farinciki marar misaltuwa.
"No... Jinina a jikinki Ayusher i got everything i wanted... Kin maida namijin da ya fi kowane gata da farinciki a duniyar nan, to ni yanzu me zan bukata kuma? My dream Girl"
Hawaye ya sauko mata.
"Wasu mazan ba su min haka ba"
"Wasu mazan kika ce, a yanzu kina auren namiji, ina kaunarki Ayusher ina kaunar abun da abun da yake cikinki fiye da tunaninki, hasken da ke haskaka duniyata, ke ce komai nawa, we're family now... Alhamdulillah"
Ya kwantar da ita kirjinsa a hankali ya rumgumeta kamkama kamar za a kwance masa, kuka sosai take tana jin wani yanayi da bata saba ba.
[9/7, 7:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 7️⃣6️⃣
Kin dade kina sha’awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba?
Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na ’yarki? To, ga sauƙi ya iso!
ADASHE NE NA GATA!
Ki zuba kuɗi, ki ɗauki abin da kike so daga:
Sutura da zannuwan gado
Kayan kitchen
Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu)
Talkami da jaka
Zanen gado
Frames (flowers decoration ko standing ones)
Console mirror
Boxes na Lefe ko na traveling.
Warmers iri-iri
Food flask iri daban-daban
Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so!
Sauƙi ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa.
📌 Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati.
📌 Akwai sharudda da ka’idoji.
Domin ƙarin bayani, ki/ka
tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660
Ko ta hanyar WhatsApp 👉 Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1
Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t
Thank you 😍 🙏
"Kasan jiya da muka je Asibiti"
"Uhm"
"Likitan tace kowa ta fadawa mijinta idan ta koma gida"
"Mee"
"Wai akwai wani sabon Technology da ya shigoo"
Tana fada tana cin gauta. Shi kuma hankalinsa yana kan system din da yake tabawa.
"Tace wai akwai allurar da ake yi ma mace bayan kwana biyu sai ta dawo a debi jininta sai a sakawa mijinta"
"Tooo saboda me?"
"Wai saboda idan lokacin haihuwa yayi sai shi yayi nakudar ba sai ta yi ba, shi zai ji zafin"
Sai a lokacin ya kalleta yana dariya.
"Saboda ba ni da gata?"
"Aa ita ce tace kowa ya fada idan miji zai iya sai yayi"
"Yanzu dai ba dan kin raina capacity na ba ta ina za a saka min nakuda dan Allah? Shi kenan ni ban da gurin kai kara idan an taba ni?"
Ta kyalkyale da dariya.
"New Technology ne fa"
"To ba za a fara da ni ba, ina namiji ina nakuda abun ai ba zai bada kala ba, amman kuma da kin ga jarumta kamin ki motsa ido na haihu"
Ya aje system din yana dariya itama dariyar take. Ya nufo inda take zaune ya dauke ragowar gautan da ta ci ya kwashe hancin ya zuba a plate ya kakkabe mata jikinta ya dauke plate din ya sumbanceta.
"Allah ya sauke ke ki lafiya"
"Ameen"
Ya nufi kitchen ya aje plate din ya dauko mata ruwa da cup biyu ya zuba mata daya daya ya zubawa kansa.
"Qalbin kin matsawa riguna lamba"
Ya fada yana kallom t-shirt dinsa dake jikinta, domin tun da cikinta ya girma kullum kayansa take sakawa. Ta sha ruwan ta mika masa cup.
"To ya zaka yi? Laifin waye?"
"Na wa"
Ya fada yana lankwafe kai kamar wani maraya. Ya aje cup din sannan ya koma ya cigaba da aikin da yake da system dinsa yana mata hira sama sama saboda baya son ta ji kamar ya kyaleta duk kuwa da aikin dake gabansa.
Hannu ta kai ta shafa katon cikinta a hankali tana kallonsa, a yanzu kuma me zata roka? Me ye Allah be bata ba? Miye ta raba ba a maye mata gurbinsa da shi ba? Ita ce yau ake yi ma lele ake taraiyarta kamar yar Gold.
Wannan ne cikin farko da ta raineshi da soyayya ubansa da kulawa kamar dan da daga shi ba za a sake haihuwa ba a duniya.
Aliyu ya bata kulawa, ta soyayya ta kauna, ta tararaiya ta tausayi, ta kyautatawa, ya dauke mata nauyin komai, idan zata yi ma sai ya hana sai idan be gani ba, domin ta saba wahala da ciki sai ya zama aiki be mata illa bata jin nauyin aiki da ciki, amman Aliyu ya sauya kalar jikinta ta zama wata shagwababbiya kamar ba ita ba. Zama da tashi duk rikata yake idan zata yi, motsi kadan sai yace me take ji? Me take so? Bata san ta yi kwadayi da zaben abinci ba sai da ta auri Abokin Rayuwarta.
Tun cikin na wata uku Aliyu yake lelenta da abun ciki har cikin ya tsufa, ta bangaren Ummi ma duk bayan kwana biyu sai ta kira, da Emily ta gane amfanin haka sai ta rika rikata da kanta ta gaishe ta. Idan tana kwadayin wani abun na dabam Mama Baraka zata aiko mata. Duk wani motsi nata yana kam idon Aliyu, a yanzu ta san ta yi aure, a yanzu ta san me ake nufi da aka aure mai sonka fiye da wanda kai kake so, a yanzu ta san ribar hak'uri tana da yawa, ta san amfanin wanda yayi hakuri sakamakonsa mai kyau ne.
Cikinta na wata takwas aka yi auren Misra da Kameela da mahaifinsu ya hade, banbancin kawai na Event ne, domin Kameela bata yi komai ba bayan henna day, Misra kuma ta yi duk wani event daya kamata budurwa ta yi. Haka Emily ta sake jiki aka rika komai da ita a nan ta kara sanin dadin yan'uwa da kuma muhimmancisu, kusan komai za'ayi sai an nemi shawararta sai an sakata a ciki. Each and every minute sai Aliyu ya kira ya tambayi lafiyarta wanda kusan shi ne abun da ya fi kowane yi mata dadi, tana son kulawa kuma ta samu a gurin Abokin Rayuwa na har abada.
Auren Kameela da wata daya Emily ta haifo kyakkyawan yaronta, bayan kwashe awani tana nakuda, ta yi sa'a cikin be so mata da wani laulayi sosai ba, wata kila saboda ta saba da wahala ne, wata kila kuma wannan daga jinin ubansa ne. Amman gurin nakuda bata sha da sauki ba, sai dai daga karshe ta haihu lafiya aka fito da yaron fari kyakkyawa kamar ita. Sau daya Aliyu ya karbi yaron ya duba ya mikawa Mama Baraka ne sake bi ta kansa ba sai da aka fito da Emily daga dakin haihuwa sannan hankalinsa ya kwana.
Daki daya aka ware mata saboda ta samu hutu kamin a sallame su. Aliyu ne farkon mutumen da ya shigo dakin ya nufo inda take kwance ya shafa kanta cike da tausayi kamar zai zubar mata da hawaye.
"Sannu... Allah ya miki albarka, ya raya abun da ya ba mu, ya ba mu ikon masa tarbiya da daukar nauyinsa, ya baki lafiya i love you so much"
Ya sumbance ta sai shafa kanta yake kamar zai cinyeta. Idonta ya cika da hawayen farinciki, ta haihuwa lafiya kuma zagaye da yan'uwa da mijin dake ta daukin zuwan ɗansa duniya. Shi ne namiji na farko da ya nuna mata tsantsar kulawa da soyayya ya tsaya a kanta har ta haihu kuma ya rika yaronsa yayi mata godiya.
"Na gode da ka kasance a rayuwata"
Ya share mata hawayen sai sake mata kiss Mama Baraka da sisters dinta da yan'uwansa suka turo dakin sai ya daga ya janye hannunsa daga jikinsa. Mama Baraka ta mika masa yaron ya karba ya ciro wayarsa ya kira Ummi video call. Tsabar farinciki Ummi ta ji kamar ta baro Abuja a ranar ta zo Kd dama tana son yara tana son zuri'a balle kuma ta Aliyun da yake kamar abokin shawararta. Rabonta da ganinsu tun cikin Emily na wata shida lokacin da suka zo wani meeting na siyasa ita da mijinta.
The following day aka sallami Emily daga asibitin bayan sun yi mata dinki saboda ta samu kari. A gidanta aka dawo da ita, saboda Aliyu yayi yarjejeniya da Mama Baraka tun kamin ta haihuwa cewar a bar masa matarsa a gidansa ba zai yarda akaita gidan Mama Baraka ba. A dole ya amince domin mai son naka shi ma naka ne. Aka dawo da Emily gidan Aliyu, yan'uwansa da suke cikin garin Kaduna na bangaren Daddynsa da na Ummi suka yi ta zuwa barka suna kawo masa alheri daman wacan haihuwa abun be zo da rai ba, ba a yi masa kyauta ko biki ba sai a yanzu.
Yayansa kusan kullum sai ya kawo matarsa ta wuni a gidan sai dare ya dauke ta su koma, saboda tana da kyakkyawar fahimta da Emily ba kamar Kameela ba. Abinci mai kyau Emily take babu ruwanta da yaro sai idan za ta ba shi nono, wata yar danginsu Aliyu ce masu karancin rufin asiri aka bar mata tana goyon yaron, mai masa wanka dabam ta shirya shi, ta gasa mata cibiya. A yanzu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 61 Chapter of 63