An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
To my big sis, Hajiya Habiba Muhammad, words are not enough to express your worth and my love for you. I pray that Allah grants you the highest place in Paradise, fulfills your desires, and answers your prayers. I'm speechless You're even more than I imagine Wallahi.
I dedicate this book to you, Hajiya Habiba Muhammad. You mean more than words can express you are everything I could ever ask for in a big sister. You treat me like your own little sister
—I LOVE YOU deeply 🤍❤️
I couldn't introduce myself without mentioning you, Salma Ahmad Isah 🥰
I cherish you Salma, nasan ke ma kin san haka. If anyone is looking for another version of me, they’ll find it in you.
NOTE...
Labarin nan ya zo da sabon salo akwai abubuwa da yawa a ciki, sai mun taru mun yi hakuri sannan zamu iya isa gurin da nake son muje. Na san halinku abu kadan ku fara attacking mutum.
Na fara rubuta labarin tun kamin na rubuta Hurriya, wani gari, da kuma taki zaman aure, amman Allah be ba ni ikon kammalawa shi ba sai yanzu, Allah ya ba mu ikon amfana da darasin da ke ciki..
*©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠*
Page - 1️⃣
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Kai na daga sama ina kallon bakin hadarin da ya fara saukar da ruwa, iska mai karfi na kadawa kamar zata tashi gari.
“Mamy.. Mamy... Ahhhh ahhhh ahhhh”
Kasa na dawo da kaina na kalli saitin da dana yake, wanda ya kasance autism, sai ihu yake yana murza ido da nake kyautata zaton kasa ce ta shigar masa. Hawaye ne suka sauko min tare gumi, duk kuwa da kasancewar iska ne yake kadawa ko'ina, amman zafin nakudar yar da zan haifa ya tare duk wani jindadi da zai rabeni a lokacin.
A hankali na dafa kangon dake gabana na jingina sai kuma na sulale kasa na zauna, sai ruwan sama ya fara saukowa, ďana ya fara ihu na fitar hankali, nakuda ta sallamomin da gaggawa, gani ya fara min nisa, numfashina ya fara yin sama...
Babu kowa a tare da ni, babu wanda yace Emily, ki yunkura zaki iya, babu mai fada min haka ake yi ba haka ake yi ba, ba ni da gatan da wani zai damu da ni balle ya kai ni asibiti, zan iya haihuwa da kaina ko sai an sake fasa ni CS kamar wacan karon? A haihuwar ďana London haihuwata ta fari.
Jin wani azababben zafi ya ratsa marata zuwa cinyata ya sakani ihu da dukanin karfina, a gurin da babu mai cetona.
“Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke?”
Na ji wata sabuwar murya, idanuwana suka yi arba da wata bakuwar fuska dake duke a gabana yana leken tawa fuskar, saukar ruwan sama da kuma zafin nakuda, ba su ba ni damar tantance waye tsugune a gabana ba. Na mika hannayena duka biyu na riko hannayensa ina numfashi daker, azabar nakuda ta hana ni magana.
“Subhanallahi... Christen ce ke?”
A kokarinsa na zare hannunsa daga nawa agogon hannunsa ya zame ya tsaya a hannuna sai na jimke agogon da karfi ina nishi mai karfi.
“Am... Akwai wanda kika sani nan kusa?”
Na girgiza kai alamar aa, to ni a kaf duniyar ma wa na sani balle kuma a kusa da ni.
“Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan...”
Kai kawai nake iya daga masa, ni dai burina a taimake ni a raba ni da abun da nake ji a yanzu. Da alama maji karfi ne, domin cak na ji ya daga ni yana istigifari.
“Astagafullah Allah ka yafe min ba da niya na taba ta ba”
Ya saka ni a motarsa, be damu da lalacewar da jikina yayi ba, be damu da ihun da ďana yake kamar zai fasa kunne ba, be damu da banbancin addininmu ba, be duba talaucina da arzikinsa ba, haka ya ja motar da karfi yana tukin yana min sannu, yi hakuri mun kusa karasawa asibitin, kai kace ni din yar'uwarsa...
*** *** ***
Karar bude kofar dakin da take ciki ne ya dawo da ita duniyar tunaninta. A hankali take shafa tsadaden agogon dake hannunta mai ruwan zinari, hawaye masu zafi na sauko mata.
“Emily...”
Ta daga kai ta kalli mai kiran sunan nata ta cikin madubin dake gabanta. Da sauri ya karaso kusa da ita ya tsaya yana kallonta, a cikin kallonsa akwai tashin hankali, akwai kauna, akwai tsoro, akwai fargaba da suka rufe shi lokaci daya saboda ganin hawayenta.
Risinawa yayi kasa a yayinta take zaune agaban madubi mai cike da kayan kwalliya. Fari ne, mai yalwatacciyar bakar fuska mai kama da bakin hadari, kallo daya zaka masa ka fahimci annuri da far'a ba su da muhalli a fuskarsa, sai dai kuma shi din kyakkyawa ne, namiji ne mai kirar mazaje. Sarkar Cross ce a wuyansa irin wadda ke wuyanta, banbancin tashi da nata tata karama ce tashi kuma babba ce wanda ta cika kirjinsa dake dauke da zanen tattoo.
Dubansa ya kai kan agogon dake hannunta a take ya kara hade rai.
“Har zuwa yaushe zaki daina dauko agogon nan dake tuna miki rayuwar baya?”
Ta kalleshi da idanuwanta masu matukar kyau da daukar hankali, da bakin da yayi daidai da tsarin fuskarta ta furta.
“Har zuwa lokacin da zan iya manta alheri”
Ta maida dubanta a gurin agogon da take jin kamar shi din ya taimaki rayuwarta, a lokacin da mutuwa ta so ta kusantota.
“Ko waye mai wannan agogon, yana da kirki, yana da tausayi, yana da kyakkyawar zuciya, shi din ya banbanta da sauran musulmi”
Zabura yayi kamar zai dake ta cikin ihu ya rufe ta fada.
“Babu banbanci tsakaninsu, babu banbanci tsakanin ko wane musulmi, kin gwada daya kin gwada biyu kin gani, baki bukatar wani ya baki labari, miye a cikin kanki? Meyasa kika kasa manta rayuwarki ta baya? Kina da komai yanzu, baki bukatar kowa I'm here for you and I Love you”
Ya rumgumeta daga tsayen da yake sai ta fashe da kuka ta rikeshi sosai. Bayanta ya shafa yana maida numfashi a hankali tare da rarrashinta.
“Kina da duk wani abun da kike mafarkin samu a yanzu Babe, kina da Luxury Home and Cars, kina da komai Babe”
Dagowa ta yi daga jikinsa ta share hawayenta ta bude aljihun madubin ta saka sarkar ta mike tsaye ta shiga bandanki ta wanke fuskarta, ta cikin madubin dake bandakin take kallon kanta.
Ta canja, hallitarta ta sauya, halinta ya sake, kyauta ya ninku, kyaun jikinta ya bayyana.
“You can do this Emily, you have to do this, ke din a yanzu Emily ce ba wacan Emilyn ba, ke din a yanzu Emily ce, ba Aysha ba, jaruma ce baki bukatar kowa a kusa da ke”
Ta fadawa kanta domin karfafawa kanta guiwa, daman waye zai karfafa mata? Idan ba ita din kanta ba, turawa suka ce when you have no one to push you push yourself. Takawa ta yi baya tana cigaba da kallon kanta sannan ta dauke idonta ta kalli kofar bandakin, ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kofar ta bude ta fita.
Gaban madubin ta sake zaunawa ta fara shirya kanta, har ta yi kwalliyar ta gama Vito be ce mata komai ba yana zaune ya dora kafa daya saman daya, wayarsa a hannunsa sai dai duk abun da take jajayen idanuwansa suka kanta. Gurin da ta ware tufafin da zata saka ta nufa ta dauka ta nufi wani karamin daki ta canja tufafin sannan ta fito tana gyara gashinta dake hade da gashin doki attachment.
“Kin yi kyau”
Ya fada yana nufar gurin da take tsaye, ta yi kyau kam iyakar kyau, kyaun da ya wuce ayi mata kallo daya a dauke ido, yadda aka tsara hallitar fuskarta da kirar jikinta, kai kace ma ita ta yi kanta.
“Ban san miyasa kika dage sai kin yi aiki ba, ban san manufar da kike son cin ma ba, na wadata ki da kudi, ban san miya hana zuciyarki natsuwa da hakan ba, arzikin da zaki je nema a wani gurin be taka kara ya karya na arzikin da na aje miki a nan ba, amman dai ko miye, zan goya miki baya saboda ina sonki ina son farincikinki sosai”
Magana yake yana zagayeta kamar mai tantance komai na jikinta.
“Ba arziki nake nema ba, so nake kawai na yi rayuwa irin na sauran mutane, ka canja ni kuma na canju, na watsar da komai ina rayuwa ne irin na mutane, karka ji tsoro”
Ya tsaya daidai fuskarta har numfashinsa yana gauraya da nata.
“Vito be san tsoro ba, amman shi tsoro ya san Vito shiyasa idan ya gan ni yake boya, you belong to me karki manta wannan”
Ya sumbance ta.
“Wish you all the best, fatar ki fara aiki a sa'a i love you, good luck on your new Job”
Ya mata murmushi kadan ya shafa fuskarta sannan ya dauke hannunsa ya fice.
Tsaye ta yi a gurin na wasu dakiku, sannan ta busar da iskar bakinta ta nufi wayarta da jakarta ta dauka ta fice daga dakin zuwa bangaren da ďanta yake.
TURHAN POV.
“Baka tafi ba har yanzu?”
Ya mike tsaye yana kallonta idanuwa a raunace fuska dauke da damuwa.
“Ammy...”
Sai kuma ya kasa furta komai saboda yadda ta tsare shi da wani kallo irin na horo daga uwa zuwa ga danta.
“Zamanka ba shi da amfani a nan, kasan ba zan taba barinka ka kwana a gidana ba, toh ba amfanin bata wuni”
Ya bude baki sai kuma ya maida ya rufe a hankali ya taka zuwa kusa da mahaifiyarsa.
“Ammy I'm sorry, na yi nadama kin sani, na tuba ki yi hakuri ki yafe min”
Ya durkusa kasa ya rike hannayenta.
“Me zan yi ki yafe min Ammy? Me zan yi ki yarda na yi nadama?”
“Nadamar ka ba zata gyara abun da ka bata ba, ni ban kullace da komai ba, kawai alaka ce irin ta da na yanke”
“Ammy mi zan yi ki fahimci na yi nadama? Mi zan yi ki yafe min? Ina cikin damuwa ina cikin matsala”
“Na yafe maka Turhan na dade da fada maka haka”
“Ba irin wannan yafiyar nake so ba, irin wanda idan zan bar kasar nan kike kewata, idan na zo kina murna da zuwana, mu zauna mu yi hira mu yi wasa da dariya, Ammy me zan ki min irin wannan yafiyar”
Ya tambaya yana shirin fashe mata da kuka.
“Zan maka irin wacan yafiyar da kake tsammani ne, only if Aysha ta yafe maka...”
Ya girgiza kai.
“Ammy karki yi haka, idan kika alakanta yafiyarki da Aysha to ba zaki taba yafe min ba, domin ban san ina Aysha take a yanzu ba, ban san inda zan ganta ba, Ammy idan kika yi haka ba ki min adalci ba...”
A take ta daka masa tsawa.
“Kai ka yi min adalci kenan? Saboda kai yarinyar nan ta bar addinin musulunci, duk wani gata da na so na yi mata na addinin musulunci ka ture, duk wata shimfida da na yi na yaye mata damuwar da wani ya saka ta ka nade shimfidar ka jefar, na shirya zama mata uwa saboda bata san wannan gatan ba, duk wani buri da nake da shi akanta da akanka ka ruguza shi,
aikinka da yadda ka riketa yadda ka wulakantata ya goge duk wani karatu da na shimfida a cikin kanta cewar mu musulmai halinmu ba daya ba ne, a ranar da ka sauke ta garin nan da idona na ganta a gaban coci tana rokon su taimaketa, saboda tana ganin mu musulmai mun gaza.
Turhan ka saka Aysha ta ji cewar mu musulmai ba ma iya kaunar wanda ya shigo musulunci, ka saka ta ji cewar ba mu da kirki, da karfi da yaji kun cire mata son addinin musulunci, da karfi da yaji kun nuna mata tubabe ba shi da gata a addinin Musulunci, duk wani buri da nake da shi akanka da ita ka rusa shi... Ka zabi Masarautarku, ka bi mahaifinka, to ka dawo na yi maka?”
“Ammy kamar kin fi son Ay...”
Be karasa ta wanka masa mari.
“Na fi son Aysha da kai Turhan, haka ne baka yi karya ba hashenka a daidai yake, da ka rike ta a yadda na so wata kila da rikon zai iya zame min silar shiga aljanna, duk wani hali da ta shiga ko zata shiga kai ne sila...”
“Ba ni ne sila ba... Ammy ba ni ne mijinta na farko ba, kuma ban mata wulakancin da kike tunani ba, yadda kike daukar abun be kai haka ba”
Ya fada yana hawaye shi dai kokari kawai yake ya fahimtar da ita kuma ya wanke kansa. Sai ta nuna masa kofar fita falon.
“Tashi ka fice min daga falo, ai kasar nan bata cikin rikon ubanka ko? Iyakar mulkin sarautarku da ikonku ya tsaya a Sudan ne, to tashi ka koma can ka rike sarautarka da matarka da yan'uwanka da mahaifinka, ka bar ni da nawa”
Ya mike tsaye kai a kasa ya fice daga falon. Ammy ta bishi da kallo har ya fice sannan ta juya ta kalli Amal dake tsaye stairs tana kallon abun da ke faruwa.
“Ammy dai kin yi hakuri na ga...”
Ammy ta kalleta fuska babu alamar wasa.
“Idan kika furta wani abu akan matsalar nan, to zaki hada kayanki ne ki bar min gidana”
Ta rufe bakinta da sauri ta juya ta koma sama. A mota Turhan ya samu kansa ya jingina da sitiyarin gaba daya ya rasa me ke masa dadi. Wayarsa ya dauka ya amsa kiran dake shigowa yana gyaran murya domin damuwa ta gama cinye karfinsa.
“Ihm ihm Hello”
Sai aka amsa masa daga dayan bangaren.
“Hello Turhan ya gidan?”
“Lafiya Kalau”
“Ashe ka shigo kasar, dazun nake ji a gurin Uzee”
“Haka ne amman dai yau zan koma”
“Why?”
“Ba dadi, Aliyu har yanzu babu wani abu sabo, Ammy ta ki karbata, ga damuwar abubuwa da yawa suna rufe ni, na rasa me ke min dadi”
“Har yanzu babu labarin Aysha?”
“Babu, kuma yau Ammy ya tabbatar min ba zata yafe min ba, sai Aysha ta yafe min, ban san inda zan ga Aysha ba”
“Bana jin fa tana raye, domin da tana raye neman da ka yi mata da yadda aka zuba kudi da yanzu an gane ta, ni ma ta gurina ba wani labari gaskiya, ina ganin abun da zai fi, ka koma nan da kwana biyu idan na duba time da ya fi sai ka dawo muje tare mu samu Ammy mu rarrasheta wata kila zata yafe maka”
“Abu ne da kamar wuya, ta hau sosai ta yi fushi Aliyu”
“Karka karaya, za mu samu kanta In Sha Allahu, ba wai mu kadai zamu tafi ba sai mun gayyaci mutane, ka yi magana da amininka ku tattauna idan kun yi shawara da kuke ganin ya kamata mu shigo ciki sai mu shiga”
“Toh Allah yasa ta yafe min, ko da ya yafe min dole zan cigaba da neman Aysha, ina da bukatar ganinta ina son ganin...”
Yayi shiru be karasa ba.
“I will call you Back”
“Okay”
ALIYU POV.
Ya sauke wayar tare da bude bakinsa ya karbi plantain din da Sultana take kai masa baki.
“Uhmm so kike cikina ya fashe ko?”
Ta yi dariya tana jan hancinsa.
“Eh so nake cikinka yayi kato kamar nawa”
Ya saka wayar aljihu ya kai hannunsa ya shafa cikin nata.
“Ai da ba zaki zauna da ni ba, amman yanzu saboda kin ga saurayi kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa shiyasa kike zaune da ni”
Ta bude baki.
“Sai kace ba ni na saka ka yi kyaun ba, kamin na aure ka ai baka da kiba amman ina aurenka ka yi kiba ka kara kyau”
Ya zagaye cikinta da hannayensa.
“Ke ma dai kin ce na kara kyau, that's mean ina da kyau tun farko shiyasa kika rude kika ce ke sai ni”
Ta kai masa yatsina a fuska har sai da ya matsa baya yana dariya.
“See this girl”
“Zaka yi latti fa, ka tafi ko na kira Momy na fada mata”
“Sai nace mata ke kika rike ni kika hana ni tafiya aikin, kin ga idan ta min fada sai na rama akanki”
Juyar da shi ta yi ta fara turashi har sai da ya fita daga falon dan dolensa.
“Ni da gidana a rika korata”
“Ka dame ni ne, and Point of correction gidana ne ba naka ba”
Dawowa yayi kusa da ita ya sumbance ta ya shafa cikinta.
“I Love you, sai na dawo ayi min addu'a mai ciki”
A take ta kai masa rankwashi akai sai ya zuba da gudu gurin motarsa yana dariya
“Allah ya kiyaye ya tsare min kai, dan kyakkyawana”
“Amin yar kyakkyawata”
Ya dago mata hannu ta daga masa sannan ya shiga motar yayi addu'a yayi mata key yayi horn mai gadin da ya kasance inyamuri ya bude masa gate ya fice, zuciyarsa cike da so da kaunar matarsa.
____________________
Share fagen sabuwar tafiyar kenan. Da fatar zaku karbe shi da hannu biyu.
Khadeeja Candy... ✍️
+2348036126660
A hankali ta tura kofar dakin da danta yake ta shiga sautin dariyarsa ya saka ta farinciki tun kamin da karasa gurin da yake zaune.
Vito ya juyo ya kalleta ko kadan babu murmushi a fuskarsa sai ka rantse da Allah ba shi ne yake yi ma London din wasa ba yana dariya.
Kallonta yake har ta karaso kusa da shi gurin da danta yake zaune, ta rage tsaye ta kai hannu ta shafa fuskar danta, shi kuma ya kai hannu zai shafa fuskarta sai ta kauce ta yi saurin mikewa tsaye, a nan ma da kallo ya bi ta, wani irin so yake mata wanda ba zai iya dorashi a mizanin awo ba.
“Karfe nawa zaki dawo?”
Ta kalli agogon hannuna.
“Ban sani ba, sai idan na tafi”
“Karki zauna da yunwa idan babu abinci a can ki fada min zan aiko a kawo miki”
Ta kalleshi kawai ta dauke kai sannan ta sakarwa danta murmushi, ta sake rage tsayinta tana kallon danta.
“London zan fara fita aiki yau, zan wuni ba a gida ba, kai kuma zaka wuni da Chidimma your Nanny...”
Bata rufe baki ba ya girgiza mata kai ya bata fuska zai yi kuka.
“Ni bana son zama a tare da Chidimma ina son zama tare da Uncle Vito”
Ta saka hannayenta biyu ta rike fuskarsa tana masa magana a hankali, domin karami abu ne ya birkice mata a take.
“Uncle Vito zai fita yana da aiki, amman idan na dawo....”
“Zan zauna tare da shi”
Vito ya amsa mata yana kallon gefen fuskarta. Ba tare da ta kalleshi ba ta ce.
“Amman kana da gurin zuwa”
“Ba karamin abu ba ne London ya sake jiki da mutum, ya fara cewar baya son zama gurin Nannynsa so let him be with me, ko kuma ke ki fasa tafiya aikin ki kula da shi”
Ta cire hannunta daga jikin danta ta mike tsaye
“Ka zauna da shi ni zan tafi”
Ta juya ta nufi kofar dakin ta bude ta fice, da kuzari ta fito cikin gidan ta nufi gate mai gadi ya bude mata ta fice. Tafiya sosai ta yi sannan ta samu taxi ta shiga sai da ta zauna sannan ta fada masa gurin da zai kaita.
Direban ya saka sauti mai dadi yayi kasa da volume din yana tukin a hankali. Idanuwanta ta maida gefen titin tana kallon hanya da ababen hawa da kuma shagunan suka yi ma hanyar ado, sai dai gaba daya hankalinta yana wata duniyar da ta kasa mantawa da mutanen cikin da kuma rayuwar da ta yi a ciki.
“Idan baki iya larabci ba karki gwada, ba a nigeria kike ba, al'adunmu sun shan banban, saboda haka bana son ki yi magana har zuwa lokacin da zaki koma gida, zan sanarwa kowa cewar ke kurma ce”
“Saboda me?”
“Saboda bana son kowa ya san wani abu a tsakaninmu, addininmu da na ki ya shabanban, ina da daraja mai girma a nan, ni dan sarauta ne jinin sarauta, ina da iyali da rayuwa a nan”
“Ni ma musulma ce ai a yanzu”
“Kowa ya ganki ya ji muryarki ya san tuba kika yi, ba wai an haife ki a ciki ba ne, sanin cewar na auri tubabbiya zai zubar min da kima, kuma babu wanda ya san maganar auren nan daga ni sai ke sai Ammy, Ammy kuma bata nan daga ni sai ke ne a nan”
“Allah yana nan, be kamata ka yi min haka ba, be kamata ka wulakanta ni ba, wannan zalinci ne kuma Allah baya son haka”
Ya dalla min harara.
“Ke Allah kika sani? Kin san Allah kika tashi cikin kafirci? Karki kuskura ki ce zaki fadi wani abu akan hakan, domin ke baki san komai ba, sallah ki ma ba a fara karba ba, domin ba mai kyau kike yi ba”
“Amman Turhan...”
“Kul... Karki kuskura kiran sunana a nan, karki kuskura nunawa kowa cewar kin san ni, ni ba mijinki ba ne a yanzu, na aureki ne a inda aurenki ya zame min dole, a nan kuma ina da wasu iyalin...”
*** *** ***
“Madan a nan zan tsaya ko ciki za mu shiga”
Tambayar da direban Taxi din yayi mata ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, hannunta ta saka ta share siraren hawayen da suka zubo mata.
“Shiga ciki”
Ya kunna kai kamar yadda ta masa umarni har sai da ya isa gurin da aka tanada domin aje motoci, ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 63