Nan jama'a suka d'auki dariya saboda kowa yasan k'arshen zancen nata bazai wuce ace wata sabuwar k'arya zata gindaya ba,wani kallo da madakin yayi mata yasa ta dad'a tsurewa dan haka ta shiga raba idanu tana kallon jama'a
"Wollahi zan fad'a muku gaskiya...Allah yana kallo nima wollahi ba laifina bane...Ku saurareni kiji...!"
Kamar an ce Ladidi ta d'aga idonta,can daga cikin jama'a ta hango shi sanye da bak'ak'en kaya tamkar fatalwa,babu abunda take iya hangowa a fuskar mutumin sai idanu kad'ai,ganin wannan mutum take ya sake rud'ata jikinta ya shiga kyarmar data fi ta farko,nan cikin zuciyarta ta furta
"Wannan shi ne mugun gamo..Ya allah me yasa haka zata faru..?"
Tana kuka take dad'a baza idanu dan tasan muddin ta sake yin magana tofa kashinta ne zai bushe,wannan mugun gamon da tayi ya sake haddasa mata tsoro nan take tayi shiru na dole,idanunta na fidda hawayen da Allah kad'ai ma'anar abunda suke nufi sannan kuma ita,cikin zuciyarta kuwa tarin damuwa ce data cika mata zuciya nan taci gaba da maganar zuci abunta
"Wayyoo!! Allah na ni Ladidi yau mena aikata haka..? Son abun duniya da son zuciyata yana neman jefani a bala'in daya fi k'arfi na,me yasa baza ku kyaleni ba haka nan ba..!"
Tana wannan suturun a zuci taji madakin ya fara tsaula mata bulala,wani ihun azaba data saki tuni yasa al'umamar wajen b'arkewa da dariya suna mata ihu,haka aka ci gaba da lafta mata bulalan tana kurma ihu,yayin da su kuma al'ummah suke ta lissafa mata adadin bulalunta tun daga d'aya har zuwa tamanin,koda aka cikata mata bulalanta nan ta zube a gurin ta shiga halin jinya,ihun kawai take amma hawaye sam yak'i fita daga idanunta,itama ga Aisha haka ce ta faru dan ita kam tsabar azaba har suma saida tayi saboda yadda taji saukar bulalun a jikinta,nadama kuwa da tarin Allah ya isa babu wanda bata aunawa Ladidi ba,haka kewar ahalinta da danginta da bata san ta inda zasu bayyana mata ba,tayi kuka sosai har sai da taji hawaye na neman fin k'arfin ta,daga nan kuwa aka tattara su akayi prison da su dan cika wa'adin da aka d'iba musu,koda suka isa bayan an aunasu zuwa d'akin da zasu zauna,ganin d'akin da aka kaisu ma kad'ai ya sake sawa nadamar Aisha ta dad'a ninkuwa bisa abunda aka ta aikata,haka ta kwanta nan a k'asa a ruf da ciki dan zama ma ji take ya gagareta,saboda yadda bayanta duk yake a farfashe,rigarta duk ta manne a jikinta sam tak'i fita,da k'yar ta rok'i alfarmar y'an d'akin nasu suka taimaka suka rabata da rigar jikinta,bayan nan kuma suka d'an taimaka mata suka goge mata jinin jikinta da ruwa.
Isowar Captain Adama ma'aikaciyar gurin dake da alhakin kula dasu,wacce aka damk'a su a hannunta da zata dunga kula da duk al'amuransu a gidan har wa'adinsu ya cika,kuma ita zata basu duk wani aiki daya dace suyi a matsayin horon da zasu karba ta shigo ta tsaya can daga bakin k'ofa ta coge k'afa cikin muryar rashin mutunci ta furta
"Wace ce Aisha da Ladidi anan.?"
Cikin b'arin jiki da rashin kuzari Aisha tayi saurin furta
"Gani Aunty...!"
Wani kallon raini captain tabita da shi tana fad'in
"Taso kizo muje..."
Kasa motsawa tayi daga gurin jikinta duk yayi mata nauyi kamar yadda idanunta suka zama masu nauyin a gareta,cikin kalmar neman a tausayi mata ta furta
"Dan Allah Aunty kiyi hak'uri wollahi bazan iya tashiba yanzun wollahi duka jikina ciwo yakemin..."
"Keee! Dakata bana son rainin wayo,dan uwarki an fad'a miki hutawa kika zo yi..Nan gidan horo ne,idan kinsan kina buk'atar hutu uban waye yace kiyi laifin da za'a kawoki nan..? Dallah malama taso muje aiki na nan yana ji ranki.."
Sabon kuka ta sake saki tana jan jiki,da kyar ta iya mik'ewa tabi bayan Captain Adama suka fice,d'aki bayan d'aki ta dunga bi da ita tana nuna mata band'ankunan da zata wanke,a k'alla saida ta nuna mata band'akuna sama da ashirin kuma kowanne bayan ta wanke saita tabbatar da sun fita,sannan kullum zata wankesu sau uku a rana,daga nan suka nufi kitchen nan ta nuna mata uban wanke²n da zata yi sannan ta juya da niyyar tafiya ta barta,ai fa nan Aisha bata san lokacin da zube gaban captain Adama tana rok'on ta akan ta tausaya mata,ta bari har ta samu sauk'i idan bayanta ya warke saita fara aikin,wani mugun kallo ta sake jifanta da shi tana durk'usawa kusa da ita ta d'ago fuskarta
"Ke yarinya ce...amma makira...Lokacin da kika aikata abunda kika aikata shin kin tuna da yadda k'arshenki zai kasance..? Irinku abunda ya kamata ayi mukuma ya kamata yafi haka dan gaba ko saku akayi bazaku aikata ba.."
"Dan Allah aunty wollahi nayi miki alk'awari ina samun sauk'i zanyi duk abunda kika ce nayi amma kimin wannan afuwar dan k'aunarki da annabin rahama.."
Har captain Adama ta juya zata bar wajen ta juyo ta kalli Aishar,yadda ta rik'o mata k'afa yasa cikin fushi ta fizge k'afarta tayi cikin kitchen en,gishiri ta kamfato kana ta fito inda Aisha take ta kama hannunta ta shiga janta,a tunanin Aisha captain Adama ta hak'ura kamar yadda ta rok'eta,koda suka dawo cikin d'aki nan ta wurgata cikin d'akin sannan ta fizge mayafin data rufe jikinta da shi dan bata ga ta sa Riga ba a yanzun,gishirin data taho da shi daga kitchen ta dunbuzo sannan ta shiga bursunawa Aisha a jikinta,duk inda ya fashe da inda ma bai fasheba sai data mulke mata shi da gishiri,aiko azaba kam Aisha ta shashi a wannan lokacin jinta take kamar ba a duniyar data sani take rayuwa ba.
Sanda captain Adama ta juyo kan Ladidi kuwa tuni ta jima da shiga layin ban hak'uri dan yadda taga Aisha na wata irin gantsarewa da ihu sanda ake murza mata gishirin,amma ina ko kad'an captain bata saurara mata ba bare taji hak'urin da take bata nan tasa aka rik'e mata ita ta mammanna mata shi a jikin ciwukanta,kana kuma ta sake tusasu a gaba suka nufi kitchen dan aikatuwa,kamar yadda ta nunawa Aisha aikin ta hakama ta nunawa Ladidi manyan tukwanen da zata kankama a wuta sannan ta kula dasu har zuwa sanda masu girki zasu karb'a...
^^^^^
Bacci ne ya d'auke shi tun daga rufe idon da yayi a haka yadda yake a kan kujeran duk jikinsa a takure,waiwayowa YASEER yayi a hankali ya kalleshi cikin tausayi dan yadda yaga ya takure jikinsa guri guda,ya jima yana kallonsa kafin ya mik'e k'afarsa akan k'aramin table en da yake kusa da shi ya rufe idonsa shima yana y'an tunane²,k'arar shigowar text wayarsa yasa shi saurin bud'e ido yana kallon wayan,kamar kada ya duba sak'on haka zuciyarsa taketa sak'a masa dan bai san abunda zai tsinto a cikin sak'on ba,amma ina tuni wani sashi na zuciyarsa ya bashi shawaran dubawa kawai,a hankali ya d'auka waya ya bud'e sak'on ya fara karantawa
*"BRAVO* Lallai ne yaseer ka cika wawa mara tunani da har ka iya sadaukar da abunda ba lallaine ka sake samun dama akansa ba...Sai dai kuma kayi namijin k'ok'ari da har ka iya hak'ura da mulkin nan ka zab'i kub'utar da d'an uwanka,sai dai ka sani abunda ka aikata...ka tafka babban kuskure da zai kaika ga yin dana sani anan gaba,hallau kuma ka sani wannan abun daka aikata dai² yake da jefa kanka a matsalar data fi wacce ka fidda d'an uwanka aciki.....!"
Wani irin tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa,yana tunanin yadda zaiyi da hanyar da ya kamata yabi ya kare kansa wani sak'on ya sake shigowa
"Ba kana tunanin kai mai wayo bane..Abunda zamu shaida maka shi ne,idan har kayi k'ok'arin sanar da wani wannan sirrin muna so ka tabbata yin hakan dai² yake daka sake jefa rayuwarka a matsala,wannan karon baza muyi k'ok'arin sake aikata kuskuren da muka yi a baya ba na baka damar da kai kuma kak'i amfani da ita,amma ka saurari hukuncin da zai biyo baya muddin wani yasan da wannan....."
Shiru yayi yana goge gumin daya fara tsatstsafo masa zuciyarsa cike da taradaddin wanda yake aiko masa da wad'annan sak'onnin da kuma ta inda sak'on yake zuwa masa,a fili ya furta
"Waye mai wannan sak'on...?"
Tunani ne iri² ya addabe shi,nan yayi ta tunanin ya zama dole ya sanar da wani matsalar da take damunsa,dan bai kamata yayi shiru ba,dan yin shirun nasama zai iya hadsasa masa wata matsalar,tambayoyin da suke ta taso masa daga cikin zuciyarsa su suka hana masa samun nutsuwa.."Shin su waye suke masa wannan barazanar...? Dole nefa ya binciko su duk inda suke,kuma dole ne ya sanar da wani wannan matsalar dan gudun kada a k'ulla masa sharrin daya fi na YAZEED,shin waya kamata ya sanarwa..??"
Farkawar YAZEED dai² lokacin da suka had'a ido yasa shi d'an saita nutsuwar sa,kallonsa yazeed yayi cikin wani irin murya ya furta
"Wace ce JEEDDAH..??
Mamaki ne ya kama Yaseer jin tambayar data fito a bakin yazeed har ya kasa bashi amsa ya tsaya kawai yana kallonsa
"Malam tambayar ka nayifa ka tsaya kallona haka..Kaga wani abune na kallo a nan..?"
"A'a...! Kawai dai ina mamakin maganar taka ne..amma.! Wai ma mene ne dalilin wannan maganar taka ne..?"
"Ina ruwanka da dalilin yinta...Tambayar ka nayi nd ina buk'atar ka amsamin..?"
Harararsa Yaseer yayi sannan ya furta
"To ban santa ba nima,idan ka damu da saninta zaka iya zuwa ka bincika da kanka..."
Juyowa yazeed yayi ya kalleshi
"Koh....?"
"Ehhenn! Naga kana da damar yin haka,so no need ka tambaya ai.."
"Okay...! Ka kyauta.."
Ficewa yayi ya bar Yaseer nan yana binsa da kallon mamaki,dan ko kad'an baiyi tunanin yazeed en zaiyi masa irin wannan maganar ba a kuma irin wannan lokacin da yake ciki damuwa..
^^^^^
B'angaren jeeddah kuwa tun bayan da aka fito daga fada bayan yanke hukunci bata zame ko ina ba sai gida dan bazata iya tsayawa kallon wannan dukan ba saboda tausayin Aisha data fara,direct gida ta nufa ta shige d'aki ta kwanta dan yadda take jinta kamar bata da lafiya,haka ko da Inno ta shigo gidan ta isketa a haka data tambayeta cewa tayi kanta ne yake mata ciwo,sannu ta mata sannan ta mik'a mata kud'i akan taje ta samu magani tasha saita kwanta ta huta kafin ta dawo,dan itan zata koma cikin gida.
Yamma lik'is y'an aiken maimartaba suka risko k'ofar gidan su jeeddah,sallama sukayi tun daga bakin k'ofar sannan suka samu Yaro suka aika cikin gidan.
Tashinta a bacci kenan itama lokacin tun bayan da Inno ta barta a kwance ta samu bacci ya d'auke ta,tana fitowa tsakar gida Yaro ya shigo yana gaya mata sak'on da aka turo shi,hijab ta saka har k'asa sannan ta d'auki nik'ab ta d'aura a fuskarta kana ta fita,da zuwanta k'ofar gida ta iske fadawa na dakon fitowarta,ganin fadawa a k'ofar gidan ita kanta saai da abun yaso bata tsoro,amma haka nan ta danne tsoron ta ta gaishesu,sak'on maimartaba na kiranta da yake suka sanar da ita sannan ta basu uzirin zata kulle gidan yanzun ta dawo,komawa tayi cikin gida ta sake kimtsawa sannan ta fito ta kulle gidan suka d'unguma suka nufi cikin gida tana gaba suna biye da ita,duk inda suka ratsa kuwa sai kallonsu ake saboda ganin yadda fadawa ke binta a baya,a tunanin wasu daga cikin mutane ko laifi tayi aka tuso ta a gaba,a haka har suka isa b'angaren fulani,gaban jeeddah sai fad'uwa yake dan bata san abunda yake faruwa ba dan basu ce mata komai ba kawai dai sunce maimartaba ya aiko su tafi da ita yanzun,wannan yasa take cikin fargabar rashin sanin me zata je ta tarar.........
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
_Domin jin daɗin ku mutanena *QUEEN ACID,FATIMA M.D,HALEEMA YAHYA,MAMAN SUDAIZ,AMINA ABDULLAHEE,HAJIYA MARYAM (OUM FEEDY) & NAJIDA ALIYU BICCA* ina jin daɗin yadda kuke sakin comments akan wannan littafi,hakan ya tabbatar min a koda yaushe kuna tare dani,fatan alkhairi gareku da fatan kasancewar ku cikin amincin ubangiji.._
___________________
*Pg 11.*
^^^^^^^^
Koda suka ƙaraso ƙofar shiga turakar ta Fulani kasancewar maimartaba na gefenta daga nan bakin ƙof suka dakata,sannan suka aikata tare da bayi mata da suka tarar a farfajiyar gurin masu yiwa fulani hidima da suke tsimayin fitowar maimartaba,shigar su cikin turakar ta Fulani suka iske maimartaba kishingiɗe gefe guda kuma Fulani tana masa fira,yayin da shi ɗin yake cin ƴaƴan itatuwan da aka kawo masa,da shigowarsu suka zube tare da kai gaisuwa ga sarki sannan suka gabatar da jeeddah a matsayinsu na ƴan saƙon da aka aiko,izinin fita maimartaba ya basu,sai bayan fitar bayin ne sarki ya juya ga jeeddah da kanta yake a ƙasa lokacin data cire niƙab en dake fuskarta saboda girmamawa ga sarki,ta sake miƙa gaisuwa cike da ladabi tana jiran jin me zai fito daga bakin maimartaba.
"Jeeddatu mahaifiyar kowa..Shin yaya mahaifanki suke..?"
Cikin sake yin ƙasa da kai ta amsa
"Suna lafiya ranka ya daɗe.."
"Masha Allah,haka muke fata a ko wane lokaci..."
Sai da ya sake ɗaukan lokaci kafin ya sake yin magana
"Shin kin san dalilin da yasa muka aika kiranki..??"
"A'a ranka ya daɗe... Sai dai idan har ka sanar dani,sannan ne zan san dalilinku na kirana..Allah ya baka tsawon rai.."
Murmushi maimartaba yayi irin nasu na manya masu ji da mulki,kafin ya jinjina kai
"Haƙiƙa dalilin da yasa muka tura a kirawoki yana da girma a gurin mu,ba don komai muke da buƙatar ganinki ba face jin irin ƙoƙari da gudun mawar da kika bamu game da matsalar data kunno mana kai cikin wannan zuri'a tamu da kuma masarautarmu,lallai ne kin cancanci a yaba miki,sannan daga yau ke ɗin muna fatan ki kasance ɗaya daga cikin amintattun mu,kuma ɗaya daga cikin waɗanda zasu dunga yiwa yarima hidima.."
Wata irin faɗuwa gabanta yayi da tunda take bata taɓa jin irinta ba a tsawon rayuwar ta,nan take ta fara jin jikinta ya ɗauki tsuma har tana jin yahun bakinta na ƙafewa,maganar da maimartaba yayi ita ta taimaka wajen dawo da ita hayyacinta
"Muna fata zaki amince da wannan ƙuduri namu,sannan duk wani abu da zai faru baza ki taɓa ƙin duk wani umarnin muba.."
"In sha Allah ranka ya daɗe bazan taɓa ƙin yi muku biyayya ba a duk abunda zaku umarceni nayi,a ko wane lokaci cikin jiran umarninku muke,mu bayinku ne a kullum umarnin ku shi ne abun binmu.."
"Madallah..! Da waɗannan kalamai naki,wannan ya sake nuna mana ke en hadima ce mai biyayya ga duk wani umarnin mu,wannan dalilin yasa muka zaɓw ki muka baki wannan matsayi,ba don komai ba sai dan mun san zaki yi mana biyayya kuma kin cancanci matsayin...Abu na gaba da muke so daga gare ki shi ne muna so ki duba duk abunda kike so na daga dukiya ko na duk abunda kikaga kina so ki sanar damu,wannan alkƙawarinmu ne muyi miki shi abisa tukuicin kyautatawar da kika mana.."
Shiru jeeddah tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa ba tare data furta komai ba,cikin zuciyar ta kuwa taradaddin abunda zata faɗa take,dan yadda zuciyar ta ke ƙiyasta mata abunda zata faɗa
"Kawai tunda maimartaba yace ki zaɓa me zai hanaki ki zab'a..? AI tunda shi yayi alƙawari bazai ƙi yi miki duk abunda kika amtaba..."
Wata zuciyar ta bata damar yin hakan,can daga wani gefen na zuciyarta kuwa saurin kwaɓarta tayi
"To shin idan kin faɗa abunda kike so anyi miki ke kaɗai fa,iyayenki kuma fa..??? Shin mene ne amfanin ki nemi a ƴanta ki,alhalin mahaifanki na cikin ƙangin bauta..???"
Jikin tane yayi sanyi saboda yadda zuciyarta take tunatar da ita abunda take ƙoƙarin mantawa a dai lokacin da bai kamata ace ta manta ɗin ba.
"Tabbas babu amfanin a ƴantani alhalin mahaifana suna a halin bauta....zanyi ƙoƙarin jure duk halin da zan shiga indai har baza mu samu ƴanci tare da iyayena ba,to kuwa nima ya zama dole na haƙura da samun sa..Daga nan har zuwa lokacin da zan cancanci haka daga gurin iyayen gijina.."
Jin yadda tayi shiru na tsawon wasu lokaci yasa maimartaba yin murmushi sannan yaci gaba da magana
"Uwata naga alama kina jin kunya,amma mun baki lokaci kiyi tunani akan duk abunda kike buƙata daga garemu,saboda haka mun sallame ki zaki iya tafiya,mu kuma muna nan sauraron abunda zaki yanke.."
Jiki babu ƙwari tayi godiya ga maimartaba sannan tayi godiya ga Fulani tayi sallama dasu ta miƙe da niyyar fita tana tafe tana ɗaura niƙab ɗinta har ta iso bakin ƙofa zata fita...
^^^^^
Haka nan yaji babu daɗi a abunda Yaseer ya masa,shi yana tambayarsa wace ce yarinyar ne ba don komai ba sai don tunawa da sunan da yaji Matawalle ya ambata a fada a matsayin wacce ta taimaka aka fito da shi daga ƙangin wahalar daya faɗa tsawon shekaru,duk da a zuciyarsa yana jin haushi tare da jin tsanar Aisha da Ladidi a matsayin su na waɗanda suka ƙulla masa makircin da yake jin haushinsu,itan kam yana jinta musamman a cikin ransa,tunaninsa da zuciyarsa duka suna bashi duk daga inda ta fito lallai ne itan ta musamman ce,yana jin a duniyarsa ta cancanci mutuntawarsa da darajtawa a duk yadda ta kasance,haka nan yake jin zuciyarsa na son ganinta ba don komai ba sai dan ra'ayin kansa.
Fitowarsa daga gefen nasu direct gefen Fulani ya nufa cikin sauri kamar zai tashi sama,dai² ƙofar shiga turakar ta mahaifiyarsa ya ɗage curtains en zai shiga bakinsa ɗauke da sallama yaji ya bangaji abu,da sauri ya juya idanunsa zuwa gurin yana riƙo abun da yake niyyar jefarwa.
Ita kanta jeeddah lokacin da take tafiya sam bata yi tunanin yadda take tafe tana ɗaura niƙab ɗin nata za'a samu matsala ba,haka bata taɓa kawowa a ranta wani zai iya shigowa ba shi yasa take tafe kanta tsaye,yadda taji an turota da ƙarfi har yayi sanadiyyar tafiyarta baya zata faɗi,riƙota da taji anyi shi ya bata damar haɗiyar wani wahalallen yahu da ƙyar sannan ta shiga buɗe runtsatstsun idanunta data kulle a sanadiyyar saddaƙarwar da tayi saita sha ƙasa,ba tare da tayi tunanin riƙe wani abu da zai tallafa mata ba,ƙuri ta masa da ido tana haɗiyan yahun wahala,shi ɗinma kallonta yayi yadda tayi covering jikinta duka banda ƙwayar idonta babu abunda ake iya gani,tayi shigar nan nata kamar wata fatalwa kuma duka da baƙaƙen kaya yasa shi sake kallonta kafin ya miƙar da ita tsaye yana faɗin
"Sorry..!"
Mamaki ne ya kama jeeddah dan ita yafi cancanta ta bashi haƙuri dan kuwa ita hadima ce kuma ita ke ƙasa da shi,ko kafin ta gama mamakinta tuni shi kam har ya bar wajen ya nufi gurin Fulani,juyawa tayi ta raka shi da ido sannan ta juya a hankali ta bar gurin...
Shi kam a gefen yarima yazeed ko daya bar gurin yana zuwa ya tarar da maimartaba zaune,cikin sanyin jiki ya juyo zai bar wajen dan sam baiyi tunanin maimartaba yana wajen ba shi yasa har ya ƙaraso cikin turakar,kuma ko daya shigo sam hankalinsa bai kai kan maimartaba ba,sai yanzun da yayi ƙoƙarin zama sannan ya ganshi,nan take ganinsa a gurin yasa shi fasa zaman da yayi niyyan yi ya juya zai fice, cike da rashin jin daɗin abunda ya gani ya juya yana ƙoƙarin ficewa.
Rashin jin daɗin da Fulani ta hango a fuskar maimartaba ahima yasa ta saurin kiran yazeed tun kafin ya kaiga ficewa
"Yazeed dawo ka zauna za muyi magana da kai.."
Jikinsa a sanyaye ya waiwayo idanunsa har sun sauya launi saboda ganin maimartaba tuni ya taɓa masa zuciya kuma hakan ya haddasa masa tuna abunda ya faru a shekaru biyar da suka wuce,yadda yaga Fulani ta jefe shi da wani irin kallo yasa shi sauke kai ƙasa sannan ya dawo ya zauna a ƙasa idanunsa suna kallon ƙasa
"Yazeed me yasa kake aikata irin wannan abun..? Shin ina iliminka da tunani suka tafi..mufa mahaifanka ne me yasa dan mun yanke hukunci akanka zaka ɗauki abun da zafi haka..? Idan har kai da kake namu kayi mana haka,su kuma sauran al'ummah me zasu ɗauke mu ko wane irin kallo zasu mana dan mun zartar musu da hukunci..Wannan abun da kayiwa mahaifinka sam ba dai² bane kuma ina son lallai yanzun ka durƙusa ka bawa mahaifinka haƙurin ka kuma nemi afuwar abunda kayi.."
Ɗagowa yayi da sauri idanunsa taf da hawaye ya kalli Fulani kana ya buɗe baki da niyyar yin magana
"Bana son kayi min musu Yazeed,kamar yadda na faɗa nafi son ka aikata abunda nace da kai kawai ba tare da kayi jayayya da magana ta ba.."
"Dan Allah Ummah ki gafarce ni,tabbas nasan na aikata ba dai² ba amma a halin da nake jin zuciyata,da irin ƙuncin da nake ji a duk lokacin dana tuna cewa mahaifina shi ya bada goyon bayan a tafi dani a tsare ba tare daya bada damar ayi bincike ba,duk da yasan halayena a matsayinsa na mahaifina dana tabbata kaf faɗin duniya bayan ku mahaifana da ɗan uwana babu wanda yasan halaye na da duk wani abu da zan iya aikatawa dama wanda bazan iya ba,amma kash sai gashi mahaifina ya zamo mutum na farko daya bada tsammani akan zan aikata abunda ya jima da sanin ba bazan taɓa iya aikatawa ba..."
"Ya isa haka Yazeed,daga wannan bana son ka sake cewa komai kawai kayi abunda nace maka..Umarnine nake baka a matsayina na mahaifiyarka.."
"Ummah kiyi haƙuri amma bazan iya aikata abunda kike umartata nayi ba a wannan halin..!"
Bai ƙarasa ba yaji saukar mari a kumatunsa ɗaya daya sashi saurin yin shiru yana sauke kai ƙasa,cikin ɓacin rai Fulani ta kalli Yazeed tana magana
"Irin ɗabi'un daka koyo kenan a gidan yarin..? Shin wannan shi ne irin halayen waɗanda kake tare dasu..? Mene ne ya baka sha'awa har haka Yazeed da har kayi ƙoƙarin koyo waɗannan mugayen ɗabi'un...??"
"Ya isa haka Fulani.."
Maimartaba ya dakatar da ita yana lumshe idanunsa
"Amma Yallaɓai taya zan ƙyale shi yana faɗin irin waɗannan maganaganun agaban idanuna,ko da ace bakai ka haifeshi ba aurena kawai kake nazo da shi matsayin agola,taya zai kalli tsabar idonka ya faɗa maka irin wannan maganar sannan kuma kace na rabu da shi..Koda bama wannan ba kai ɗinfa matsayin shugabansa kake..."
"Tunda nace ki bari kiyi shiru haka nan.."
Maimartaba ya sake yin maganar ba tare daya kalleta ba,shiru tayi dan bin umarninsa amma ba don ta rabu da Yazeed ɗinba,a hankali ya juya ya kalli yazeed ya ajiye numfashi kana ya fara da cewa
"Tabbas Yazeed duka abunda ka faɗa banga laifin ka ba,dalili kuwa ni da kaina na haifar da wannan matsalar,da na bari anyi bincike tun farko tabbas da babu yadda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 63