mu,ke en ta daban ce kuma kinfi k'arfin a wulak'anta ki...Daga yau kam babu wani abu da zai sake faruwa da su.."
"Godiya nake captain sai kinga aiken ki.."
"Hajiya Adda nima ina matuk'ar godiya..ai tun farkoma dan ban san jininki bane da tuni na sanar dake.."
Mamaki ne ya cika Ladidi da Aisha ganin yadda captain ta saki fuska har tana iya dariya a gaban su,bayan sunyi sallama da Adda ta shaida musu sai ta sake dawowa ganinsu,tare suka fita da captain saboda sak'on su Ladidi da zata bata,su kuma captain en tasa wata abokiyar aikinta ta maida su ciki,haka suka yi ta bin Adda da idanu yayin da suke jin zuciyoyinsu kamar zasu fashe dan damuwa da k'uncin daya cika su.
Bayan komawarsu cikin d'aki da tafiyar Adda,captain ta shigo ta iske su a d'akin bakinta har kunne ta kallesu
"Muje ku karb'i kayan ku da aka kawo muku ko..??"
Amsawa suka yi sannan suka mik'e jiki babu k'wari suka bi bayanta har zuwa inda aka ajiye kayan,sanda suka isa gurin ganin irin adadin abunda Adda ta kawo musu nan take Ladidi ta fashe da kuka,Niko dai ina gefe nace ko kukan me take haka Ohoo mata...
^^^^^
Tun daga wannan rana da sak'on ya fad'o wayar jeeddah bayan ta turawa Yaseer sai ba'a sake tura mata makamancin sak'on ba,haka ba'a sake nemanta ba kamar yadda Yaseer en yayi zaton za'a ci gaba da turowar ba,haka shima tun daga sak'on na k'arshe da aka turo masa bayan fitowar yazeed ba'a sake tura masa ba,wannan yasa hankalinsa yake kwance ko dan dama can abun bai wani tada masa da hankali sosai ba,sai dai a duk lokacin daya tuna bai san mai turowar bane yakan ji rashin nutsuwa coz yasan tunda ake iya aiko masa da irin wannan sak'on mai turowar a shirye yake da ako wane lokaci ya cutar da shi.Babu wanda ya sanarwa da matsalar da yake fuskanta,haka yaja bakinsa yayi shiru har zuwa tsawon wannan lokaci.
Kamar kullum suna zaune tare da Yazeed en a parlor cikin b'angarensu akayi knocking k'ofar shigowa,batare da damuwa ba YASEER ya bada izinin shigowa,drink ne saman plate a cikin cup guda d'aya bawan ya shigo da shi,tun kafin ya k'arasa ajiyewa YASEER ya zuba masa idoko da ganin ya ajiye kusa da YAZEED tun kafin ya kaiga yin magana YAZEED en ya mik'e ya fita da waya a hannunsa yana sata a kunne,haka nan yaji bai aminta da lemon da aka kawo ba,yadda aka kawo shi guda d'aya bayan ansan su biyu ne a gurin,yasan matuk'ar YAZEED en ne ya bada order akawo bazai tab'a sawa a kawo masa shi d'aya ba alhalin suna tare,kuma koda daga cikin gida aka aiko babu yadda za'ayi a kawo guda d'aya coz ansan dole ne suna tare,saurin kallon bawan yayi dai² lokacin da yake k'ok'arin fita
"Waye ya baka order kawo drinks...??"
Shiru yayi yana daga tsaye a inda yake ya juyo had'e da sauke kansa k'asa saboda rashin sanin takamaiman abunda zai fad'a,yadda YASEER yake kula da motsin bawan nan take ya shiga hakaito wani lamari a tattare da shi,da sauri ya mik'e zaune yana masa tsawa da tambayar waya sashi ya kawo,jin yadda yake masa magana yasa shi yin magana
"Afuwaan..! Yallab'ai YAZEED ne yace a kawo masa.."
Wani kallon rainin wayo yayi masa maganrsa cike da rainin hankali ya furta
"Yaushe kenan..??"
In-ina bawan ya fara sai kame ² yake,yace d'azu yace yanzun,sam ya rasa kalmar kamawa,a fusace YASEER ya mik'e tsaye ya kalleshi yana kama waist da nufi inda yake tsaye yana cewa
"Zaka min bayanin wanda yasa ka kawo ko kuwa saina sa an d'aureka zaka fad'a..??"
Jikinsa ne ya d'auki tsuma jin an ambaci d'auri nan take murya na b'ari ya shiga bashi hak'uri
"Dan Allah Yallab'ai kayi min rai wollahi sani aka yi na kawo..."
"Uban waye ya turoka ka kawo mana nan..kuma wa akace ka kawowa..??"
"Wollahi Yallab'ai zan fad'a maka gaskiya..Wani ne ya bani shi yanzun a hanyan zuwa nan yace na kawowa yarima YAZEED kuma na tabbatar ya sha kafin na bar gurin.."
Ai jin wannan batu nan take ran YASEER ya sake b'aci,nan ya auno wata uwar ashar da baima san ya akayi yayi saving enta ba
"Kai kuma saboda gaka wawa baka yi tunanin me zai faru ba ka karb'a ka taho kawo masa ko...?? Shin baka yi tunanin waye ya aikoka ba..? Ko kuwa baka san za'a iya cutar dashi ba.? An baka abu kawai ka karb'a ka kawo..."
"Dan Allah Yallab'ai kayi min rai wollahi bani da masaniya akan komai..Ni ban san shi ba Yallab'ai, nayi zaton cikin sababbun ma'aikatan da aka kawo ne.."
Yadda ya zube guiwoyinsa a k'asa duk ya had'a zufa yana yiwa YASEER magiya abun sai ya so baku tausayi,amma ga YASEER kuwa sake had'e girar sama data k'asa yayi ya kalleshi
"Wannan ba abune da zaisa na d'aga maka k'afa na rabu da kai ba,laifi ne gagarumi ka aikata da yake dai² da a had'a baki da kai a cutar damu,shin dama aikin wasu kake yi a gidan nan ko kuwa...??"
"Wollahi Yallab'ai ban tab'a aikata makamancin irin wannan ba,yau d'inma sab'ani aka samu,kuma ni harga Allah banyi tunanin komai ba akai shi yasa daya bani banyi zaton komai ba na karb'a.."
Iya cika YASEER ya gama zuwa wuya saboda fusata,magana yake k'ok'arin yi amma kafin ya kaiga furta abunda zai fad'a k'arar shigowar sak'on ya katse shi,saurin d'auko wayan yayi dan yasan ko daga ina sak'on ya fito ya wara idanunsa akan wayan
"Ka kyale wannan bawan ya tafi,bashi da masaniya akan komai,kuma ko da kasheshi zaka sa ayi babu abunda zai iya fad'a maka..idan har kai kanka kana son kwanciyar hankali ka tabbata ka karb'a ka bawa YAZEED ya sha wannan ruwan lemon da hannuna.....!"
Shiru YASEER ya d'iba na tsawon wasu dak'ik'u ba tare daya iya cewa komai ba,har sai da shi kansa bawan yayi zaton idan YASEER ya juyo kansa zai iya sawa a kasheshi,ga mamakinsa kuwa lokacin da YASEER ya juyo gareshi gani yayi kawai yayi masa alama da hannu akan ya tafi,nan ya zube gaban YASEER kamar zai kwanta dan godiya,hakan da YASEER ya gani sai jikinsa ya sake yin sanyi,nan ya koma ya zauna yana goge gumin daya fara tsatstsafo masa dan tsabar damuwa akan wannan sabon tashin hankalin dake neman kunno musu kai,ya jima shiru shi kad'ai kafin YAZEED ya dawo,shigowarsa babu jimawa ga shi yariman kasancewar baisan abunda ya wakana ba,da zuwansa kawai sai ya nufi inda cup en yake ajiye ya d'auka lemon ba tare da tunanin komai ba yakai bakinsa....
^^^^^
Tun data fito daga wanka take ta sauri tana son shiryawa ta nufi cikin gida,musamman yadda taga lokaci yaja mata sosai yau tana gida bata tatafi da wuri ba,shigartan nan dai kamar fatalwa haka tayi duka komai bak'i,sannan ta kawo nik'ab enta ta d'aura,duka shirin komai yinsa take cikin hanzari tana yi tana kallon agogo,dai² k'arfe 3:30pm ta fice a gidan ta d'auki hanyan cikin gida,sai data fara shiga gefen Fulani ta taya inno wasu aikace²n sannan ta k'arasa gefen Ummi'n YASEER,a can ta yada zango dan tasan ita ce da hadimar gefen gaba d'aya,tunda maimartaba ya d'auke ta a matsayin mai kula da YAZEED take hidima da su duka,wannan yasa tun lokacin ragamar girkin b'angaren Ummi'n ya dawo hannunta kasancewar ta mai amana da tsafta,sai data gama shirya duk wani abu da zata mata na girki da misalin k'arfe 5pm,sannan ta shirya komai a turakar ta Ummi ta gyara mata gefen sannan tayi haramar komawa gida,gurin Ummi ta nufa cike da son yi mata sallama,a nan ne Ummi take bata sak'on ta shiryawa su YASEER abincinsu sannan ta kai gefensu yau baza suzo nan ba,amsawa kawai tayi sannan ta fita tabar Ummi'n a nan cikin d'aki,bayan fitarta kitchen ta koma ta shirya komai cikin basket sannan ta d'auka ta fita ta nufi hanyan da zai kaita side en nasu,da zuwanta ko kula da door bell bata yi ba tayi knocking k'ofan da hannunta,YASEER dake zaune yaji anyi knocked dama lokacin duka ya gama shiga cikin coma dan yadda yaga YAZEED ya d'aga cup en bilhak'k'i ya dumfari bakinsa zai sha drink en,yi yayi kamar zai yunk'ura ya mik'e YAZEED en yayi saurin yi masa alama da hannu yana nufin ya zauna,cup en hannunsa ya fasa kaiwa bakinsa,ba tare daya ajiye shiba ya nufi k'ofar yana niyyan bud'ewa.
Itama can a gefen jeeddah koda tayi knocked taji shiru ba'a yi magana ba,kawai sai zuciyarta ta bata ko basa nan,saboda haka ta yanke shawaran shiga kawai ta ajiye musu tasan duk inda suka je idan sun dawo zasu gani,bata gama tunanin ba tabi umarnin zuciyarta tasa hannunta jikin handle en ta murd'a k'ofar had'e da turawa ciki,bud'e k'ofan yayi dai² da isowar YAZEED gurin,har yakai hannunsa zai bud'e ita kuma jeeddah ta rigashi turo k'ofar,cikin sa'a tana turo k'ofar ta daki hannunsa da yake d'auke da cup en lemon,nan ya sub'uce daga hannunsa ya fad'i k'asa gaba d'aya ya tarwatse,daga cup en har lemon nan suka samu damar bajewa nan a bakin k'ofar.
Wani kallo YAZEED yayi mata daga ita har fasashen cup en,sannan ya jaa da baya ya bar wajen,ga jeeddah kuwa ba tare data iya yin magana ba ta shiga bin wajen da kallo,jikinta duk yayi sanyi musamman yadda taga ya watso mata kallon sannan kuma ya juya ya bar wajen fuskarsa a d'aure ya shige ya barsu nan a parlour, basket en hannunta tayi saurin fara ajiyewa ta durk'usa a wajen tana shirin sa hannu a cikin fasashen kwalban,YASEER dake zaune yana kallonta kuma yaga duk abunda ya faru ya saki wani mugun murmushi had'e da cewa
"Karki soma sa hannun ki a cikin wannan kwalban.."
Sam bata yi zaton yana gurin ba sai maganarsa data ji,a hankali ta d'ago kanta dake sunkuye ta shiga waige²n inda zata ganshi,yana daga gurin da yake ba tare daya bari ta ganshi ba yaci gaba da magana
"Ki wuce kitchen ki samo abu ki share da shi..ke naga ko gudun ki yanke hannu bakya yi,kike k'ok'arin sawa ciki salon kijiwa kanki ciwo..??"
Sai lokacin ta fahimci daga inda yake magana,nan ta mik'e tana yin d'an murmushi had'e da d'age nik'ab enta tayi baya da shi,har ta shiga ta d'auko abunda zata d'auko ta dawo ta gyara gurin YAZEED bai fito ba,tsaiwa taci gaba d'ayi zuciyar ta cike da son taga fitowarsa ta bashi hak'uri dan taga yadda yanayinsa ya koma lokacin data masa ta'adin
"Idan kin gama kije kawai abunki..."
YASEER yayi maganar yana kallonta,a hankali itama ta d'ago ta kalleshi dan lokacin tana tsaye ne kuma tana iya ganinsa
"Ina son bashi hak'uri ne,na masa laifi bai kamata na tafi ba..."
"Kije kawai kada ki damu zan wakilceki idan yazo.."
"Amma Babban yaya idan na tafi ai nayi rashin kunyafa..!"
"A'a..! Baki yiba je abunki ni zan masa magana idan ya zo.."
"Toh.." Tace sannan tayi masa godiya ta wuce ta fita jikinta duk a sab'ule dan yadda taji rashin dad'in bashi hak'uri da kanta da bata yi ba,tana fita babu jimawa shima ya dawo,ba tare daya kalli gurin da YASEER yake ba ya furta
"Me kace mata ne...?"
'Dagowa yayi ya kalleshi sannan ya maida kansa akan abunda yake
"Cewa nayi ta tafi.."
"No..! Bashi nake nufi ba.."
"Wani abu zata maka ne..??"
"Tambaya kake..??"
"A'a...idan ba magana nayi ba kana tsammanin mene da..??"
Banza YAZEED ya masa sannan ya nemi guri ya zauna yana hararar YASEER en,ko da YASEER yaga abunda yayi k'in tanka masa yayi,zuciyar sa shi dai cike da farin ciki mara misaltuwa,shi kad'ai idan ya tuna yadda ruwan juice en ya salwanta sai yayi murmushi, zuciyar sa cike da addu'ah yana godewa Allah daya kub'utar da YAZEED daga shiga mugun tarkon da aka d'ana masa....
^^^^^
Jeeddah kuwa bayan fitarta kasa komawa cikin gida tayi gurin Ummi'n YASEER en,haka duk take jin babu dad'i,musamman idan ta tuna da fuskarsa lokacin daya bar wajen,sai duk taji ta dad'a zargi kanta,tana tafiya tana tunane² wayanta dake mak'ale jikinta tayi vibrate,bata iya kulawa ba dan tana kan zaton ko company suka aiko mata da sak'on,dan haka har taje gida bata damu da dubawa ba dalilin zuciyarta dake nata babu dad'i,haka ta k'arashe yinin ta haka sukuku ba tare da wani cikakken kuzariba,ko Inno ma a haka ta dawo ta iske ta,sai dai bata kaiga tambayarta me yake faruwa ba ta yi mata sallama had'e da shigewa d'aki ta kwanta,sai a lokacin ne ta d'auka wayanta cike da son yin game ko zata koma dai²,tana cire key en wayan tayi arba da akwatin sak'on ganin har lokacin yana kicking yasa harta danna masa delete haka nan kuma sai tak'i bin option en da suka bata na "yes" da "no",a hankali ta bud'e duk da bata san ko sak'on na mene ne ba,tana shiga kuwa idanunta suka sauka kan wata kalma data so tada mata da hankali,cikin sauri ta zaro ido waje tana maimaita kalmar,tamkar wacce aka biyawa darasin da aka tursasata haddarsa haka ta shiga maimaitawa..............
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*Pg 14.*
^^^^^^^^
"Ki jira ganin sakamakon abunda kika aikata mana....."
Tsayawa tayi a kan kalmar ta zuba madaidaitan idanunta akai,ta maimaita kalmar ya kusa sau biyar kafin ta dawo farkon sak'on kamar yadda ta tsallake tun farko
"Kin tafka babban kuskure...kin yi mana asara mafi girma,wacce baza mu iya yafe miki itaba,kamar yadda kika aikata mana ya wuce mu kirashi da kuskure,sai dai wannan karon shi ne na k'arshe da zamu ja kunnen ki..Ki jira ganin sakamakon abunda kika aikata mana...!"
Idanunta ta ware akan wayar sosai,tabbas sai yanzun ta kula da b'oyayyiyar lambar da a baya aka tab'a turo mata sak'on tsoratarwar,sam ta manta da batun lambar haka tun lokacin bata ko kad'an bata tab'a kawowa ko a ranta wani abu zai sake had'ata da su a karo na biyu ba,shawaran da zuciyarta tabi inda tayi copying text en ta turawa YASEER,saboda tun wancan lokacin ya sanar da ita matuk'ar aka sake turo mata sak'on ko kiran waya to tayi hanzarin sanar da shi,mintuna biyar tsakanin tura masa sak'on kiransa ya shigo wayan nata,a hankali ta d'auka wayan ta karata a kunnenta bakinta cike da sallama,bayan ya amsata duka sai suka yima juna shiru,ko da yaji tayi shiru bata ce komai ba shima enma kuma rashin sanin dame zai fara saboda yadda jikinsa yake a sanyaye sai kawai ya furta
"Wannan sak'on fa..??"
Dogon numfashi ta saki kafin ta furta
"Nima ban sani ba,kawai dai na ganshi a wayan yanzun dana zo bacci..."
Shiru ya d'anyi yana tunani,zuwa wasu y'an dak'ik'u ya furta
"Kin san dalilin da yasa aka turo sak'on..??"
"Wollahi Babban Yaya ban sani ba,hasalima ni ban ko san su waye ne suke son shiga rayuwata ba...!"
"Ba rayuwarki ke kad'ai ba,har muma ba'a bari ba,yadda ake turo miki sak'on muma gare mu haka yake..."
Mamaki ne yaso kamata jin ya ambaci har suma
"Yanzun Babban Yaya kana son cewa kaima ana turo maka irin wad'annan sak'onnin.??"
"K'warai kuwa k'anwata,ni kaina ba'a barni ba,babban dalilin turo sak'on nasan ya samo asali ne tun daga kan matsalar YAZEED,dole ne wannan shine babban hujjar da masu turowar suke amfani da shi na son cutar damu,tarayyar da muka yi wajen bincike shi ne ya janyo miki fuskantar wannan matsala,sai dai ina tunanin kan wannan matsalar haka ina hakaito cewa duk mai turo sak'on yana yi ne badon komai ba sai dan niyyar *FANSA..."*
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Allahumma ajirna fii musibatiin wa'aklufna khairan minha...! Amma Babban Yaya nifa ina wani tunani akan matsalar.."
"Ehhhenn! Fad'i abunda kike son cewa..ina sauraronki.."
"Dama akan matsalar ne babban yaya,ina tunanin gaskiya anya kuwa babu sa hannun wanda yasan sirrin cikin gida kuwa...??"
Dogon numfashi ya sauke,sannan ya d'an yi murmushi mai ciwo
"Tabbas hakan zai iya kasancewa,sai dai rashin k'wak'wk'waran hujja dole zaisa baza muyi saurin zargin kowa ba a ciki..."
"Haka ne..Addu'ah a wannan bigiren shine mafitarmu,in sha Allah koma su waye ne suke da sa hannu ciki Allah zai bayyana su mu sansu.."
"In sha Allah.. Muna nan muna yi sai dai ko mu sake jajircewa.."
Sun jima suna maganganu akan matsalar har ta kai ga YASEER ya kasa b'oyewa jeeddah matsalar da shima yake fuskanta,nan ya fayyacewa jeeddan komai daya danganci inda aka samo matsalar da sak'onnin da ake aiko masa tun daga ranar farko,har zuwa kan matsalar data kusa faruwa a yau,a nan ne yake cewa
"Naji matuk'ar farin ciki da Allah yasa kika yi gaggawar zuwa a yau da ban san mene ne zai faru damu ba...Nayiwa Allah godiya kuma ina kanyi a dalilin zuwanki Allah ya kub'utar da ni daga fad'awa cikin wannan gagarumin matsala da aka so jefani..."
Yadda yake mata maganar da duk wani damuwarsa daya warware mata ya sanar da ita sai ya bata tausayi,duka sai taga ita natama nafila akan nasa,sai da suka shafe ak'alla sama da awa biyu suna tattauna ta yadda zasu b'illowa matsalar sannan suka yi sallama suka ajiye wayan,lokacin da jeeddah ta ajiye wayan ta gyara kwanciyarta zuwa rigingine tana kallon saman roof en d'akin,nan ta fad'a duniyar tunanin matsalar dake neman kunnowa YASEER dama ita kanta kai kafin ta samu yin bacci...
^^^^^
Tun da safiyar ranar maimartaba yayi aike gefen su YASEER haka zuwa gefen Ummi akan duka yana nemansu su hallara a babban parlour,jin kiran yasa su shiga tunanin dalilin kiran na maimartaba,sai dai sam sun kasa hakaito dalilinsa nayin haka,musamman duba da yadda akan d'auki lokaci mai tsaho kafin irin haka ta faru,dalili sun riga da sun san matuk'ar ba wani abu ne mai muhimmanci ya taso ba ko kad'an maimartaba baya tab'a had'a irin wannan meeting en,haka dai duka suka hallara a parlour'n tun kafin fitowar maimartaba suka zazzauna jigum² suna sauraren fitowarsa da taradaddin abunda kunnuwansu zasu ji,sai wajen misalin k'arfe goma na safe sannan maimartaba ya k'araso cikin parlour'n,d'aya bayan d'aya suka kai gaisuwa sannan parlour'n ya d'auki shiru na wani lokaci inda duk suka tattara hankulansu suka dank'a zuwa ga maimartaba,binsu da kallo maimartaba yayi ya jinjina kai kafin yayi sallama ya fara magana da cewa
"Shin ko akwai wani d'aya cikiku da zai iya bayyana min dalilin da yasa muka nemi ganinku a wannan rana...??"
Amsa d'aya ce ta fito daga bakunansu,inda suka tabbatarwa maimartaba babu wanda ya sani cikinsu,cikin nutauwa da izzar mulki maimartaba ya juya ga gefen da yaseer yake ya d'an kalleshi,sannan yaci gaba da magana
"Mun sani kamar yadda muke a matsayinmu na ahali guda,ba ko wabe lokaci muke irin wannan taro ba,sai lokaci zuwa lokaci a dalilin afkuwar wani al'amari da muke ganin zai kawo mana ci gaba a rayuwarmu baki d'aya...To alhamdulillah..! A wannan karon ma muna fatan wad'annan al'amura su kasance mana kamar yadda wad'ancan suka kasance mana masu dad'i..Muna son yin amfani da wannan damar wajen shaida muku Babban dalilin da yasa muka taru a wannan rana kamar yadda muka sani kowa cikinku bashi da burin daya wuce ya saurari abunda zamu bayyana muku,alal hak'ik'a kuma abisa faruwar wasu al'amura masu kyaui,duk da munsan za kuyi zaton wani abu da ban,alal hak'ik'a ba wani dalili bane daban kamar yadda kuka sani sai don sauraren ra'ayoyinku game da yaranmu akan karatu...!"
YASEER ne ya d'ago kansa ya kalli YAZEED suna had'a ido YASEER en ya jinjina masa kai yana murmushi dan yasan yau kam dole ne sai maimartaba ya taso da maganar da suka tab'a yi a baya lokacin YAZEED na gidan yari,bai Ankara ba yaji maimartaba ya kama sunan sa
"YASEER shin a wancan lokacin da muka yi maganar makaranta da kai kace sai kayi tunani,shin tunanin ne har yanzun baka kammala ba,ko kuwa akwai wani uzuri da kake da shi akan hakan..??"
Sunkuyar da kai YASEER yayi yana sakin d'an murmushi ba tare daya iya magana ba,jin yadda maimartaba yayi shiru baice da shi komai ba ya fahimci shi yake saurare yaji abunda zai fad'a nan ya bud'e baki da kyar ya fara magana
"Ina neman afuwar maimartaba akan wannan matsala da aka samu daga gare ni...!"
Kafin ya kai k'arshe tuni maimartaba ya katse shi da cewa
"Kai muke saurare muji hujjarka ta k'in bin umarnin mu da kayi..."
Sai daya jaa numfashi sannan ya furta
"Allah ya taimaki maimartaba...Gaskiya bani da wani dalili daya wuce na jiran d'an uwana...!"
"Jira kumaa..??"
Sauran iyayen suka ambata suna zuba idanunsu akan YASEER daya sake sunkuyar da kai k'asa
"Wane irin jira ne kake masa..??"
"Allah ya baka tsawon rai..kamar yadda ya kasance tun tasowarmu wani abu bai tab'a zuwa ya bambanta muba,wannan dalilin yasa ko daka min maganar karatu a baya yasa ban maida hankali akansa ba,nak'i maida hankali ne a saboda ganin cewa d'an uwana yana wani hali..wannan yasa naji bazan iya aiwatar da wani ci gaba a rayuwata ba matuk'ar bama tare,tun tasowarmu ranka ya dad'e wannan ya jima da zama burinmu,haka wanban alk'awarinmu ne da muka jima da yiwa juna alk'awarin wani abu bazai tab'a bambanta muba,shi yasa ko a lokacin da kayi maganar ranka ya dad'e na kasa bada amsa akan maganar sannan na nemi da a bani lokaci isashshe da zai bani damar yanke duk wani hukunci...Wannan shi ne dalilin Allah ya baka tsawon rai kuma ina sake neman afuwa abisa wannan kuskuren nawa..!"
Murmushi kawai maimartaba yayi yana jinjina kai,dan ko kad'an baiyi tunanin haka abun yake ba sai yanzun
"Amma YASEER banda shirme irin naku na yara wannan dalilin shi zai hanaka yin karatu a tun wancan lokacin..?? Matsalar yarinta kenan sam bakwa tsayawa kuyi tunanin gaba da abunda zai farj,shi kenan rashin tunani sai yasa ku kasa kawo tunanin kunyi ba dai² ba..Komai da kuka aikata kuna ganinsa dai²..."
Sunkuyar da kai ya sake yi k'asa ba tare daya iya d'aga kansa ya kalli maimartaba ba har ya gama musu nasihar daya fara musu akan muhimmancin lokaci,nan a k'arshe ba Tate daya nemi shawaran suba ya yanke hukunci akan ci gaban karatun su nan bada jimawa ba.
Y'an surutai ne suka fara tashi suna shawarwari tsakanin iyaye da y'ay'an akan inda yafi dacewa a turasu karatun,kafin daga bisani maimartaba ya sake yin gyaran murya alamun dake nuna musu yana buk'atar suyi shiru,shiru ne
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 63