fara shiga jikinta,yana maye gurbin tsantsar tashin hankali da taoron da take tare da shi tsayin kwanakin da suka gabata,sai dai tunanin da take kanyi akan lamarin shi ne yadda tayi k'ok'arin juya lamarin da son bawa yarta da kuma grandson d'inta kariya ta yaya ne zata fuskanci Yarima a wannan halin har ta iya kallon idanunsa ta sanar masa cewar ga abunda ya faru..?? Anya ma kuwa zata iya sanar masan kamar yadda ta fara burin...........??
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
_Alhamdulillah..! Am stepping towards recovery,thank u all for the prayers,nd for being my best friends,u are all a blessing in my life.._
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 33.*
^^^^^^^^
*#The game*
A kullum tun daga ranar da Inno suka yi waya da wannan criminal d'in da Yarima bai san ko waye ba,sai yake ta saka ido akan Inno'n da tsammanin zata sanar da shi gaskiyan abunda ta sani kan lamarin amma sai yaga shiru,sosai abun ya sake d'aure masa kai,gashi a gefe guda kwanaki sai dad'a tafiya suke,buh duk da hakan a mafi yawan lokuta yana samun k'arin evidence daga garesu,sai dai duk da hakan shi a gare shi hakan ba shi ne mafitar da yake da buri akai ba,kullum timing yake akan ko zasu sake yin wani attempts akai da zai kaishi ga cimma nasara buh duk babu wanda yayi wani abu still now,wannan dalilin yasa shi sake nutsuwa da zurfafa tunanin sa akan al'amuran gidan ma gaba d'aya,wanda agefe guda kuma rashin walwalarsa da sakewa tasa b'angaren ita Jeeddah abun ya fara damunta,sai dai bata fito ta nuna masa ba har wannan lokacin,haka nan shima d'in duk da ya fahimci halin da take ciki sai bai tab'a bada fuskar da zaisa ta fahimci komai akan lamarin ba,a dai² wannan lokacin ne kuma sai ya fara tunanin sake ganin Inno a karo na biyu,duk da cike yake da juyayin ko zata sanar da shi d'in ko kuma akasin hakan amma dai ya tabbatarwa ransa dole ne ya sake fuskantar ta,duk ma wanda za'ayi ayi kawai.
Around 9:45pm ya fara shirin fita,a lokacin itama Jeddah tana zaune saman resting chair da AHYAN a hannunta tana feeding d'insa,kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai ba tare data kuma bi takansa ba,coz cikin kwanakin tunda ta fahimci abunda yake wanda baya son ta sani sai ta shafawa kanta ruwa,buh deeply tana jin ciwo a cikin zuciyarta na irin halin ko in kulan daya b'illo musu da shi,saboda daga ita har AHYAN d'in ba kasafaima ya fiya tambayar lafiyar su ba,k'ark'arinsu da shi idan suka tashi ya gansu lafiya bayan gaisuwa baya wani zama dasu yasan matsalar su,wannan tasa itama ko da taga hakan sai ta d'an janye masa,duk abunda yake wajibinta shi kad'ai take yi,wanda bai hau kanta ba kuma sai dai tasa ido,kusa da shima idan har ba wai ya neme ta ba bata tab'a kai kanta kusa da shi,bayan wannan kuwa sai dai ta rungumi d'anta suyi baccin wahala coz gaba d'aya bata jin dad'in yanayin,amma ya zata yi dole ne tayi hakur'i da duk sauyin da rayuwa tazo mata da shi.
Har ya kammala shirinsa bata ko sake kallon inda yake ba saboda wani masifaffen kishin daya tunkarota bayan d'an gajeran tunanin daya ziyarce ta,idonta ta sake saukewa k'asa tana k'ok'arin mayar da thin tears dake shirin zubo mata,tana kuma kallon fuskar AHYAN da bacci ya d'auke,cikin nutsuwarta ta zare breast d'in a bakinsa ta maida ta killace cikin riga tana kuma rungume shi sosai a jikinta,duk abunda take yana watching ta jikin mirror dake gabansa,sai daya kammala abunda yake a gurin sannan ya juya ya kalleta,duk wanda ya kalleta a time d'in sosai zai gane yanayin da take ciki saboda yadda ta kasa control na damuwarta,inda take ya tako a hankali ya nemawa kansa gurin zama a kusa da ita yana d'an kallonsu duka
"Mene ne matsalar ne..??"
Ya furta har lokacin idanunsa akan AHYAN dake mak'ale jikinta,yasan da dane yayi bacci tuni zata kwantar da shi,amma yanzun da yake bai cika basu muhimmanci ba sai dai yaga ta rungume abunta a jikinta wani lokacinma tare dashi take bacci,a hankali ta girgiza masa kai sannan ta fara k'ok'arin yunk'urin tashi a gurin,hannunta ya rik'o yana kallonta,itanma waiwayawa tayi tana kallonsa da kuma yadda ya rik'o ta
"Allow me to go..!"
"Where..!?"
Shiru tayi bata yi magana ba saima sunkuyar da kai data sake yi,ganin haka yasa shi sakin hannunta kawai shima d'in ba tare daya ce komai ba,a hankali ta fara matsawa daga gurin har sanda ta nufi cradles d'insa ta shimfid'e shi,yana nan zaune yana kallonta har to 10 a lokacin tayo wanka ta fito,k'arar alert ne ya fargar da shi da sauri ya mik'e yana niyyan fita,tana tsaye gaban closet tana duba dress da zata yi amfani dasu ya nufota,daga ita sai towel daya tsaya mata saman cinya,while suman kanta tana sakaye cikin waterproof shower caps,sai bin inner wears d'in take da ido duk ta rasa wanda ya kamata ta zab'awa kanta,a zahiri duk wanda ya kalleta a gurin zaiyi zaton abunda take yi kenan,amma a bad'ininta sam ba kayan ne a gabanta ba,ta bayanta ya tsaya ya rik'o waist d'inta yana shirin d'ora kansa a jikin wuyarta tayi saurin juyowa a hargitse tana kallonsa,sake matsota yayi kamar zasu fad'a cikin closet d'in,ita kuwa gwanar nan ta fara ja gefe tana matsawa cike da fargabar abunda yake shirin aikatawa,gaba d'aya ta manta da zaman towel d'in jikinta,a tunanin ta bathrobe ne kasancewar da shi tafi amfani,yau d'in ne da salon fitinarta ya motsa yasa ta d'auro towel wanda shima d'in ba wai tayi bundling nasa bane,kawai ta d'an yi stuck nasa a k'asan arms d'inta,a tare suka ci gaba da matsawa har suka isa jikin bango,kallon k'asan ido ya sakar mata yana sake rik'o ta,jikinsa ya mannata yana kallon fuskarta zuwa jikinta dake jik'e da ruwa,siririn ajiyar numfashi yayi yana shak'ar sanyayyen k'amshin shower gel dake fita a duk jikinta,lumshe ido ya sake yi yana sake matsarta sosai,ita kam dukanta komawa tayi kamar wacce aka yi sculpturing nata a gurin,dan yadda yake goga mata tip noise d'insa a wuyanta,a hakan ya ci gaba da shiga jikinta,ganin ya fara twitching breathe da kyar ta fara k'ok'arin kwace jikinta daga gare shi,unknowingly ta fara ture shi baya dan yadda take son ya saketa ta shirya,towel d'in dake jikinta ne ya fara saukewa zaiyi k'asa saboda hannunta data d'aga,within 2 sec ta dank'o abunta ta cukuikuye a k'irji,zuciyarta banda bugawa babu abunda take,splits btween her breast da suka bayyana ya zubawa ido,a hankali ya kai hannunsa saman nata da take rik'e da towel d'inta ya fara k'ok'arin janyesu k'asa,sake k'ank'ame abunta tayi tana kallonsa da wani irin frightened a k'wayar idanunta,kallonta yake shima da idanunsa da suka fara k'ank'ancewa,a fujajan ya dumfari bakinta da take shirin magana yayi merged da nasa,yadda yake socking lips d'inta cikin salo da kwarewarsa yasa jikinta saki,nan suka fad'a duniyar sama sun jima cikin yanayin har ta kaiga itama tayiwa hannunta matsuguni saman wuyarsa saboda yadda take enjoying salonsa
"Hello..! Boss.!"
Yajiyo maganar ta cikin mini wireless bluetooth dake mak'ale a kunnensa,bai iya magana ba coz har lokacin bakinsu na had'e
"Boss...are u there..!?"
Guard d'in ya sake fad'a,Yarima kam a wannan lokacin wani mugun haushi ne ya cika shi jin maganar guard d'in a kunnensa a kuma dai² lokacin da yake niyyar kwasar gara,cikin wani yanayi mai wahalar fassarawa ya zare bakinsa a nata yana kife fuskarsa a k'irjinta yana sakin gyaran murya duk don guard d'in yasan yana jinsa,jin hakan ne yasa guard d'in fahimtar yana jinsa buh akwai abunda yake mai muhimmanci,sai daya saita kansa sannan ya d'ago narkakkun idanunsa ya zuba mata su,har lokacin nata idanun a kulle suke sai faman twitching breathe take,dai² kunnenta ya d'ora lips d'insa yana sakin numfashi har lokacin
"Am sorry babe.."
Idanunta ta bud'e masu cike da zallar sha'awa dan mamakin maganarsa coz bata san akan mene yake maganar ba,a hankali taga yaja baya yana tafiya da baya² har ya isa kusa da k'ofa,cikin wani fitinannen murya yana k'ank'ance ido ya furta
"Take care KHUSHI.. I will be back soon..!"
Yana fad'an haka ya fice da sauri yana kuma gyara zaman wireless bluetooth d'in dake kunnensa
"Hood..! Are we together..!?"
"Yes boss..!"
"Kuna tare da itane ne har yanzun..??"
Amsa masa yayi cikin girmamawa
"Ehh..! Boss.."
Bai sake magana ba daga hakan yaci gaba da nufar hanyan gidan da suke,tafiya mai d'an nisa ta kawo shi bakin gidan,kai tsaye ya shige mutum biyu a cikinsu suka take masa baya,a bakin k'ofar d'akin suma suka tsaya shi kuma ya shige ciki inda Inno take zaune a saman mat cike da fargabar yadda wad'annan halittun suke kwamusota ba tare data san hakan zai faru ba,saman kujeran ya zauna,hannayensa a hard'e guri guda sannan ya d'ora chin d'insa a bisansu yana mai bin dattijuwar da kallo,kafin ya fara k'ok'arin magana
"Inno..nasan kin san dalilin da yasa muke yawan aikata haka gareki ko.!?"
Shiru tayi ta kasa d'agowa bare ta iya had'a ido da shi ko magana
"Wannan gaskiyan da kika sani kike boy'ewa har yau akan tane muke kan bibiyar ki,da rok'on ki kan ki sanar damu..!? I know matsawar akace zamu ci gaba da tafiya a haka bana tunanin shiru da binne gaskiya zai haifar mana da d'a mai ido..buh idan hakan bai miki ba zaki iya ci gaba da boy'ewa babu komai,,,amma in sha Allah daga wannan lokacin baza mu sake shiga rayuwarki ba bare mu nemi ki sanar damu wani abu daya shafi wannan maganar,sai dai muna tunanin bayyana wata gaskiya,wanda na tabbatar duk fad'in duniyar nan babu wanda yasan da ita face ke kad'ai da kika san afkuwar shi...!"
Yana gama fad'an haka ya mik'e kamar zai fita dan yasan hakan ba komai bane face barazanar daya shirya mata,bisa ga mamakinsa har ya isa bakin k'ofa bata yi yunk'urin cewa komai ba,yana daf da ficewa yaji sautin muryanta
"Yallab'ai..!"
Ta kira shi da wani irin murya mai cike da fargaba,a fujajan ya tsaya sai dai bai iya juyawa ba saboda baya so tayi saurin gane yanayin da yake ciki dan yadda ta kira shi yasan da kamar wuya a wannan lokacin ta sake yunk'urin boy'e masa abunda yake burin ji tuni
"Zan sanar da kai komai..amma da fari ina so kayi min aikin gafaran,,,sannan ina rok'on ka da koda kaji abunda zan sanar maka a yanzun baza ka tab'a hukunta Jeeddatu ba..Saboda na tabbatar bata da laifi a duk cikin abunda ya faru.."
Sai lokacin yayi k'ok'arin saita nutsuwarsa sannan ya juyo a hankali kamar ba shi ne ya gama murmusawa yanzun ba saboda tsananin farin cikin daya ziyarce shi,cikin takun isa da izzar mulki ya fara yunk'urin dawowa muhallinsa ya zauna yana sake d'ora chin d'insa a saman hannayensa alamun yana saurarenta
"Yallab'ai.. Kayi min aikin gafara,,,ni kaina na san duk wannan boy'ewar da nake ko ba a yanzunba wata rana dole ne Ubangiji zai bayyana gaskiya,sai dai ina jin tsoron yadda al'amura zasu faru matsawar aka ce wad'annan mutanen suka san na shaidawa wani abunda ya faru tsakanina dasu..Amma babu yadda zanyi,ya zama wajibi ne a kaina a yau na bayyana maka wannan gaskiyar ko da hakan zaiyi sanadiyyar rasa tawa rayuwar..!"
Cike da kokwanton abunda zai biyo baya,haka nan fuskarta cike da alhini sannan taci gaba
"A wannan ranar Yallab'ai da AL'AMARIN ya faru ba shi ne karo na farko ba da nake attempting d'auko AHYAN ba,,,kusan wannan zan iya cewa shi ne karo na k'arshe da muka yita gwada sato shin,sai dai babu nasara a duk wad'ancan lokacin,wanda a ranar ne kuma ka ganni da idanunka.."
Tab'e baki yayi a hankali dan shi ba iya abunda yayi zaton zata fad'a masa ba kenan,cikin wani yanayin b'acin rai da y'ar maganarta ya furta
"Ke da su waye kenan kuke aikin..??"
Sai da tayi jim sannan ta furta
"Ban sani ba Yallab'ai..!"
Da mamaki yake kallonta dan baiyi tsammanin hakan daga gareta ba
"Baki sani ba..!? Kenan ke kika shirya duk wannan..?? Ke da kanki kika tsara sace jikanki da ba tare da taimakon wani ba..??"
Kai ta dad'a sunkuyar wa k'asa coz bata san ta wane fuska ne ya kamata tayi masa bayanin ya fahimta ba
"Shin Inno ke kika shirya duk wannan abun da kanki..?? Ko kuwa akwai taimakawar wasu a ciki..??"
"A'a..Yallab'ai bani kad'ai bace akwai wasu..!"
Zatonsa ya fara zama gaskiya akan lallai ne ba ita ta shirya hakan ba,sai dai abun d'aure kan shine tace masa bata san wad'ancan d'in ba,shin ta yaya kenan hakan zai faru..?? Ya yiwa kansa tambayar ba tare da tsammanin samun amsa ba
"Ba ke kad'ai bace..!? Amma kuma kika ce baki san wad'ancan d'in ba,,,shin ta yaya kenan kuka shirya duk wannan d'anyen aikin tare da mutanen da baki sani ba..?? Anya kuwa hakan zai faru..?? Ko kuwa dai aljanu me su d'in..??"
"K'warai kuwa zai yiwu..domin kuwa kamar yadda na fad'a ne tun a farko cewa,ban sansu ba..hasalima ni kiran waya ne kawai na amsa..kamar yadda na tabbatar su d'in mutane ne ba aljanu ba.."
Murmusawa yayi dan da dukkan alamun ya fara gano inda maganarta ta dosa,sake nutsuwa yayi yana sauraronta
"Kamar yadda na fad'a tun daga amsa kiran waya ne na fad'a cikin wannan matsalar,damuwa da fargaba tun daga lokacin suka zame min abokan rayuwa,a iya tsayin rayuwata na shafe tane ina hidima a cikin wannan gidan,haka nan ban tab'a fuskantar matsala da damuwa ba sai a wannan lokacin,,,Yallab'ai ban so na kasance a cikin irin wad'annan mutanenba sai dan sunyi min barazanar zasu kashe ni..sannan sunce muddin banyi yadda suka ceba,ba iya ni kad'ai ba hatta yarinyata da jikan nawa da nake son karewa bayan sun gama da ni zasu koma kansu..Na rasa yadda zanyi ne Yallab'ai shi yasa da farko na gwammace aikata abunda suka sani..!"
Sosai ya ware ido akanta yana nazarinta,tabbas a wannan lokacin ya gano gaskiya a kalamanta ko da bai kalli fuskarta ba
"Amma mene ne dalilin da yasa tun da farko kika kasa fad'a min bayan nayi ta rok'on ki akan ko sanar min..??"
"Dole ce tasa ni yin haka Yallab'ai..saboda ban san mene ne zasu aikata ba..shi yasa na amince da yin yadda suka so.."
Shiru yayi na wani lokaci yana nazarin halin da take ciki,kafin ya gyara zama yana fad'in
"Anyways..! Ina tunanin tunda haka suka zab'a muma zamu yi abunda ya dace..!"
Saurin d'agowa tayi tana kallonsa dan bata fahimci abunda zai fad'a ba
"K'warai za muyi kamar yadda suke so..Shin wayarki tana tare dake..??"
Ya tambaya yana d'aure fuskarsa,amsa masa tayi cike da fargabar abunda zai aikata
"Ina son ki kira su sannan ki shaida musu cewa zaki d'auko musu yaron a daren nan.."
"Amma Yallab'ai shin baka tunanin wani abu ya faru..??"
Kai ya kad'a mata yana murmushi
"Kada ki damu babu abunda zai faru,sannan ya kamata ki daina kirana da Yallab'ai.. Coz matsayin d'a nake a gurin ki..babu ma'ana a cikin kirana da wannan sunan.."
Kai ta d'an rausayar
"To rank'a ya dad'e.. Amma abunda zan fad'a musu kenan..??"
Da kai ya amsa yana d'an cije lips d'insa kad'an,ba tare data san me yake shiryawa ba ta d'auko y'ar wayarta dake mak'ale a jikinta tana danna kiran JIBO,cikin y'an mintuna da shigar wayar aka amsa,JIBO kuwa a can gefensa dama abunda yake kan jira kenan a kullum saboda yadda uwargijiyar tasa ta fara azalzalarsa da maganar sato jaririn
"Hello..Ya dai Baiwar masarauta..! Shin kina tunani akan lokacin da ake sake d'auka ko kuwa..??"
A hankali Yarima ya runtse idanunsa saboda jin kalaman mutumin da yake a kunnensa babu wani girmamawa,Inno kuwa a lokacin ko kafin tayi magana sai data d'an kallo shi,ido ya sake lumshewa alamun ta kwantar da hankalinta,cikin wani irin nutsuwa ta furta
"Yallab'ai.. Dama a yau naso shaida maka tun tuni zan d'auko yaron saboda na gama duk wani shirin daya kamata nayi..!"
"K'arya kike munafuka..! Wato kina son ki ruftamu ko.? Shi yasa kika nuna kamar babu ruwanki..??"
Runtse ido Yarima ya sake yi,ita kanta Inno jin yadda ya kirata da wannan mummunan sunan sai da taji wani irin b'acin rai,Yarima da idanunsa ke kanta yayi saurin saita nutsuwarsa yana sake calming nata dan baya son plan d'in su ya tashi abanza
"Ba haka bane Yallab'ai.. Duk abunda kake zato ko kad'an bai faruba,,hasalima sake shiryawa nayi saboda bana so a samu kowace irin matsala ne shi yasa nayi hakan.."
Wata mahaukaciyar dariya JIBO ya kece da ita,sai daya d'auki tsayin lokaci yana kyakyatawa wacce tasa Yarima da Inno fara zaton ko dai ya gano sune,cikin wani murya ya tsagaita da dariyar
"Shegiya tsohuwa wato dai kema kina son rayuwar ki sama data jikanki..ko..??"
Kallon kallo suka yi da Yarima a lokacin data d'ago idonta cikin kasala
"Koma dai yaya ne,zan baki nan da 1 hour kafin nan zan k'araso na jiraki,,kamar wancan lokacin zan jira a inda muka yi da ke..!"
K'it ya katse kiran yana sakin mugun murmushi mai cike da mugun nufi,ko kafin ya gama shirin tafiya kuwa a nasa gefen sai daya fara kiran uwargijiyar tasa sannan ya kama hanyar tafiya cike da tsantsar farin cikin aikinsa zai kammala a yau.
A gefen Yarima kuwa koda yaji ya katse kiran kayataccen murmushi ya saki yana jinjina kai,cikin wani nutsuwa ya mik'e yayi gaba,dai² k'ofar fita ya d'an tsagaita sannan ya furta
"Zan kawo miki yaron yanzun,saboda haka ki shirya yadda zaki basu shi.."
A matuk'ar firgice Inno ta d'ago idanunta tana kallonsa dan bata san mene ne ma'anar abunda yake shirin aikatawa ba.
"Amma rank'a ya dad'e..!"
Hannu ya d'aga mata alamun baya son doguwar magana a lokacin
"Abunda na tsara shi za'ayi,, saboda haka muje kawai.............."
*#Tofa...gwarama..ko me Yarima yake shirin yi da AHYAN..?? Sanin gaibu sai Allah.*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Ya Ubangiji ka iya mana kan abunda yafi k'arfin mu,dukkan masu naimanmu da sharri Ubangiji ka karemu da karewarka,bamu da k'arfi ko dabara,ka iya mana da iyawarka..ya Allah.*👏
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 34.*
^^^^^^^^
*#Trapped*
A b'angaren Jeeddah kuwa bayan fitar Yarima ko daya barta a nan a tsaye,kwakwaran motsi kasa yi tayi bare ta iya yunk'urin barin gurin,saboda yadda take wahale kuwa hatta da idonta kasa d'aga shi tayi a hanyar daya bi,zallar feelings daya fita ya barta da shi,shi ne ya fara addabarta a time d'in har bata san lokacin da wasu hawayen azaba suka fara bin fuskar taba,a hankali ta janye idanunta a kan hanya tabi gangar jikinta da kallon takaici coz a lokacin ko albarkacin towel d'inma bata samu ba kasancewar tuni Yarima yayi nasarar rabata da shi,ta d'auki tsayin lokaci a gurin kafin ta sulale tayi k'asa,towel d'inta dake yashe a k'asan ta sura sannan ta sake nufar bathroom da wani irin kasala,waterproof shower cap d'in tayi detach tana mai jin haushin fitar da yayi har k'asan ranta,cikin bathtub ta shige ta saki kan tap a dai² saman kanta,yadda ruwan ke sauka haka yake ratsata tun daga kai har cikin jininta dake wani irin combustion,sai data shafe ak'alla mintuna sama da ashirin a cikin ruwan kafin tayi k'ok'arin bud'e lane d'in ruwan yabi hanyarsa,yadda jininta ya d'auki sanyi haka ma cikin ilahirin jininta dake soyewa ya sanyaya,bathrobe ta sawa jikinta sannan ta fito banda ajiyar zuciya babu abunda take,a gaban closet d'in ta sake tsaiwa zuciyarta har lokacin da b'acin rai ta fisgo wani sexy robe daya kasance dangin lace mai kalar red wine,tsayin rigar duka bazai wuce iya cinyanta baa ta saka,not minded ta d'an shafawa jikinta turarukanta masu sanyi sannan ta nufi inda cradles d'in AHYAN yake,d'aukan sa tayi ta rungume abunta tana sake jin k'aunar sa mai had'e da wani irin fad'uwar gaba dake shigarta,a hankali ta fara tafiya har zuwa bakin royal bed d'in,sai data fara kwantar da shi sannan ta mik'e jinta itama a kusa da shi,panoptic d'in ta d'an ja ta rufesu half sannan ta sake rungume shi a jikinta tana mai yi musu addu'o'i sannan tayi deactivation na fluorescence d'in,coz bata san lokacin da zai dawo ba kamar yadda bata san ina ya tafiba,shi yasa take jin ba zata iya jiran dawowarsa ba.
Tafiya suke yana kan gaba Inno na biye da shi,sai guards d'insa gaba d'aya dake take musu baya ak'alla sun tasamma arba'in idan basu haura ba,a daf da apartments d'insu suka dakata cikin wani y'ar duhuwa shi kuma Yarima ya wuce cikin apartment d'in kai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 51 Chapter of 63