Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga uguwanni ta,wanda su kansu a wannan lokacin tuni sun nemi yafiyar junansu zumunci da mutuntawar dake tsakaninsu tun a can baya a yanzun ma ita suke yiwa juna,haka tsakaninsu da masarauta a yanzun sukan shiga ziyara,sannan har wannan lokacin babu gangancin daya kai SAJIDA prison,kamar yadda Abba'nta ya shard'anta mata duk da tana jin damuwa akan hakan amma tasan dolenta ne tayi biyayya akan umarnin mahaifinta d'in shi yasa a kullum take k'ok'arin sake kyautata masa take kuma girmama matar daya aura d'in,a zamantakewar aurenta kuwa da mijinta babu wata fitina,tana zaune da mijinta da yaransu uku lafiya,,,itama Aisha a yanzun haka yaranta uku biyu mata d'aya namiji kuma suna zaune lafiya da iyalinta.. A b'angaren su Jeeddah kuwa su kam a wannan lokacin ma duka tuni suka shafe tsayin shekaru basa k'asar,dan a yanzun haka sun shafe ak'alla shekaru bakwai a k'asar London ita da ABEELA da kuma yaran su duka,,inda a b'angaren su YASEER yanzun haka shi da ABEELA suke da yara biyar uku maza biyu kuma mata har BAQIR,,sai su Yarima suma da suke da yara hud'u duka,inda a bayan AHYAN ta sake haihuwa,ta samu yara uku har shi AHYAN d'in suna da hud'u duka a tsayin shekaru sha d'aya,wanda a bayan AHYAN ta haifi tagwaye duka maza,sai mace da take kan goyo mai sunan Ummah Fulani wato HAFSAT suna kiranta DINA (Love),sai tagwayen ta da suka ci sunan ALIYU (JALAL) takwaran Abba Galadima da kuma ABDULLAH (JALIL) mai sunan Abba Matawalle,,rayuwarsu a yanzun cikin farin ciki suke gudanar da ita,,inda a yanzun haka shirye²n dawowar su 9JA ya kankama dan dama wani course ne ya kaisu k'asar akan aikinsu,tunda suka samu suka kammala kuma bayan d'an hutun da suka samu sai suka fara shirin dawowa.. A can masarauta ma tuni shirye²n dawowarsu ya kankama dan duka a halin yanzun babu wanda baisan da batun dawowar tasu ba,gyara sosai aka yi a cikin gidan na ban mamaki,wanda yasa da yawa daga cikin mutane suke ganin kamar akwai wani AL'AMARIN da zai wakana,sai dai sun barwa kawunansu wannan tunani,,cikin wannan lokacin ne kuma kamar yadda ake tsammanin dawowar tasu,private jet nasu na masarauta ya sauka a airport d'auke da su duka,gagarumin taron da suka iske a gidan shi ne yasa suma duk sai suka fara zargin akwai wani abu da ake shiryawa amma ake b'oyewa ba'a so su sani,,bayan dawowarsu gidan an gama gaishe² sai duk suka nufi apartment d'insu dan su samu su huta yaran kuma duka suka barsu a apartment d'in su Ummi,,kwanci tashi asarar mai rai,yau gashu da dawowarsu har an d'ebi kwanaki uku wanda a gefe guda kuma tuni shirin gagarumin taron da family d'in suke shiryawa ya taso,,,duk wani abu da za'a buk'ata kama daga na ci ko sutura duka Maimartaba ya bada order kuma an tanadesu harma da k'ari,anyi komai cikin wadata,sai shirin dinner d'in da ake ta yi. Tun misalin k'arfe 8pm ake shirin tafiya dinner,wanda za'ayi shi ne a Meena event center,taron daya had'a al'ummah da dama kama daga jama'ar masarauta har ma dana gari,,cikin shiga ta alfarma duka suke a wannan daren hatta da iyayen,a wannan lokacin kam Maimartaba,Abba Galadima zuwa su Ummah Fulani duk idan ka kallesu sun k'ara manyanta sosai,sai dai jin dad'i daya b'oye hakan a tare da su,,a wannan daren su kansu sun san sun samu kyaututtuka na ban mamaki da girmamawa daga al'ummah mabambanta na cikin k'asar har ma da k'etare,,bayan gama jawabai na godiya da sauran jawabin taya murna sai Maimartaba ya tashi dan yin jawabinsa,a wannan lokacin da gurin yayi tsit bayan ya fara magana cikin girma da mulki,a wannan lokacin ne bayan ya kammala jawabin sai ya fara magana akan abunda mulkin jahar wanda wannan bayanin nasa ya matuk'ar tayar da hankulan jama'a,inda a cikin jawabin ne ya shaida cewa zai yi murabus daga karagar mulki,cikin wannan jawabin nefa maimartaba yasa jama'a da dama kuka,a matsayinsa na sarki daya shafe sama da shekaru arba'in yana mulki yau rana a tsaka ace zai sauka dole ne al'ummah suji babu dad'i musamman ma daya kasance ana jin dad'in mulkinsa saboda yadda yake kamanta adalci,to amma jawabin daya jero bayan nan sai yasa mutane suka fara masa addu'ah,tare da rok'a masa nisan kwana mai amfani da d'orewar lafiya,,bayan ya yiwa al'ummah nasiha sai taron yazo k'arshen,,a wannan rana anyi koke² wanda bayan nan kuma taron ya watse cike da alhini had'e da farin ciki.. Kimanin sati guda a tsakani gaba d'aya masarauta ta sake d'auka da shirin sabon nad'in da za'ayi,,,,kasancewar ranar yau ta alhamis tun da safe gaba d'aya cikin gidan ya kasance a cike babu masaka,ta ko wane fuska al'ummah ne tamkar ba'a mutuwa,tun daga haraban har cikin fada duka al'ummah sun cunkushe,,inda kuma ana cikin wannan halin ne Maimartaba sarki Abu YAZEED ya shiga jawabin godiya da nuna farin ciki da Allah ya kawomu wannan ranar,,bayan nan kuma kamar yadda ya fad'a sai a ranar ne zai sanar da wanda zai jagoranci al'ummah,ma'sna magajinsa kenan sai aka jiyo sunan Yarima YAZEED a matsayin sabon sarki a wannan masarautar,,haka ma ko da maimartaba ya kammala jawabinsa,sai ga Abba Galadima shima yace yana da magana,AL'AMARIN daya matuk'ar d'aurewa mutane kai a wannan lokacin kuwa ba komai bane face yadda shima Abba'n ya nuna yayi murabus akan tasa karagar sannan kuma ya d'ora YASEER a matsayinsa,daga nan nefa kuma mutanen aka matso dasu gaba inda sarkin nad'i yake ya shiga aikinsa,kafin wani lokaci mai tsayi saiga su sun fito a matsayin su na y'ay'an gado da suka amsa sunansu na jinin SARAUTA,,bayan wannan nad'in daya gudana a fada maimartaba da kansa ya sauka daga karaga sannan ya kama hannun Yarima wanda ya rikid'e ya koma sarki a karaga mulki,haka nan izuwa lokacin tuni har labari ya kai cikin gida inda jama'a suka fara zuwa yiwa Jeeddah murna a matsayin ta na Fulanin wannan k'arnin,,lokacin da al'amura suka sake lafawa bayan gama duk wasu shagulgula da nad'e² sai Maimartaba ya nemi ganin ahalin nasu duka,bayan taruwarsu kamar yadda suka saba,a nan ya shiga k'ok'arin tunasar da su abunda suka manta,ma'ana dai maganar su Adda kenan da suke gidan kaso,,a wanna ranar sai da tarihi ya maimaita kansa,labari ya sake dawowa sabo,daga nan ne Maimartaba yayi umarnin yana so a sake su haka nan,amma tare da jan kunnuwansu akan indai har aka sake kamasu da wani laifin daya sab'awa addini ko doka to su tabbatar hukuncin da zasu fuskanta zai wuce yadda suke tsammanin,,bisa ga umarnin tsohon sarkin tunma kafin ya gama yanke hukuncin tuni har Yarima yayi magana da S.P na gidan wanda a lokacin ma tuni har an fito da su tare da sallamar su,,,kai tsaye daga cikin Prison d'in bayan an sake su sai aka nufo cikin gidan da su,wanda izuwa wannan lokacin darussan rayuwa babu wanda basu had'u da shi ba a zaman da suka yi,dan haka duka sun sake yin hankali,,, bayan an kawo sun kuwa kamar yadda ya buk'ata duka sai aka kuma yi musu kashedin kada su kuskura wani laifi ya sake fitowa da sunasu,matuk'ar idan kuwa har aka samu labarin dasa hannunsu to su tabbata babu wani sanayya ko alak'a da nuna a ciki dan za'a koresu ne daga garinma gaba d'aya,, cikin tsananin jin kunyar abunda suka aikata ita dai Hajiya Suwaiba ta bada hak'uri sannan ta nemi yafiyan laifinta,haka nan duka suma suka yi duka sai aka sake yafewa juna daga nan kuma aka sallame su kowa ya kama hanyarsa.. *Some months leave...* Watanni sun sake zuwa sun shud'e a bayan sakin su Adda haka nan dukansu duk rayuwarsu tuni ta sake sauyawa dan akan dole kowannensu ya aro sabbin halayen kirki ya jingina wa kansa,,suma kansu a b'angaren sababbin shugabanni cikin al'amuran da suka shafi mulkin garin suna iya kar k'ok'arin su sai dai suna fuskantar wahala saboda har yanzun abun bai gama zame musu jiki ba,sai dai dama mun sani komai na rayuwa dole ne sai mun fuskanci k'alubale daban²,dan haka sai dai mu ci gaba da taya su da addu'ar samun nasara wajen tafiyar da mulkin yadda ya dace kuma bisa kamanta adalci.. Shigowarsu kenan shi da yara daga fada hadimai suna take masa baya har zuwa sabon apartment d'in da suka dawo tun bayan nad'in SARAUTAR da aka masa a matsayin sarki,kai tsaye sai ya shigo turakarsa yana murmushi dan jiyo daddad'an k'amshinta mai tafiyar da duk wani b'acin ransa,gajiya har ma da duk damuwarsa,,,a bakin mirror ya hangota zaune cikin enormous hijab mai had'e da nik'ab,tun kafin ya k'arasa kusa da ita ya zare rawanin dake kansa yana sakin murmushi mai k'ayatarwa,tana hango tahowarsa ta cikin labulen data rufe fuskarta da shi ta saki murmushi itama dan ita kad'ai tasan tsiyar data ke shirin shukawa a lokacin,ba tare daya mata magana ba ya tsaya ta bayanta yana mai janye rufin nik'ab d'in,, abunda ya gani a fuskarta shi ne yasa shi yin wani murmushin da sai da hak'oransa suka bayyana,kafad'unta ya kamo ya d'agota sannan suka isa bakin bed suka zauna har lokacin kuwa ita yake kallo sai dai itan tak'i kallonsa saboda bata so ace shirinta ya wargaje,wani sabon murmushin yayi sannan ya furta "Ranki ya dad'e..! Yau kuma wannan shigar aka tuna.??" Saurin kallonsa tayi dan taji yana murmusawa wanda sautin yake fita,k'ura masa ido tayi tana kallon yadda yake jin nishad'i,nan take itama sai ta tsinci kanta cikin nishad'in,tana cikin murmusawa kuma sai ta had'e rai dan ta tuna dalilin da yasa tayi shigar,ganin hakan da tayi cikin k'ank'anin lokaci tuni yasa shi kallonta yana rik'o hannunta,fuskarsa da y'ar damuwa ya fara tambayar ta "KHUSHI..! What's going wrong..?? Are u alright.!?" Baki ta murgud'a masa bayan ta harare shi sannan ta ce "Duk ba kaine ba kasa nayi ruining plan d'in dana shirya..!" D'an fiddo idanu yayi yace "Ni kuma..??" "Ehh mana.." Tayi saurin bashi amsa,saurin rik'ota yayi zuwa jikinsa yana mai bata hakur'i cikin sigar lallashi mai had'e da rok'on iri,,tana kumbura fuska alamun jin haushi ta ce shi kenan ya wuce,,sake kamota yayi lokacin tana shirin guduwa daga kusa da shi "KHUSHI mene ne matsalar ne wai..?? I think na ce kiyi hak'uri ko,banyi dan na b'ata miki shirin kiba,,don't tortured someone manaakan laifin da bai san ya aikata,,ta kamata ace kin fahimta.." Saurin kallonsa tayi nan ya d'age mata gira sama,sake tsuke fuska tayi shi kam cikin sauri ya d'age ta zuwa jikinsa duka,a hankali ya fara bin jikinta da wasu irin mahaukatan shafa ta ko ina,yana kuma aika mata da ruwan kisses,fuska tayi ita a dole zata shanye ba zata nuna masa tana so ba,nd ko kad'an tak'i masa respond,,a jigace ya d'ago ya kalleta da shanyayyun idanunsa da babu komai cikinsu sai zallar buk'atar tata,cikin wani muryansa dake ruguza duk wani matakan tsoronta ya furta "KHUSHI wai mene ne haka kike yi ne..?? Kin barni ni d'aya ina ta fama,,ya kike so nayi ne..?? Ke da kanki kin sani tunda nauyin al'ummah ya hau kaina duka bani da wani cikakken nutsuwa nd bani da cikakken lokacin zama da ku sosai..Shin ina so ki fad'a min da matsalolin da suka shafi mulki kike so naji ko kuwa da naki da kike son haifar min..?? Ya kamata ki fahimci halin da zan iya shiga idan baki yi wani abuba.." Yadda yake magana gwanin tausayi ne yasa ta fara tab'e baki zata dira masa shagwab'a,hakan da tayi masa kuwa ba k'aramin tasiri yayi ba akansa,sannan kuma nan take ya bashi wani gagarumin daman da yake ta sauraron samu,cikin azama ya cafki lips d'inta ya shiga aika mata wasu sabbin salon da ba duk kai ba,,a wannan karon kam itama kanta kasa jurewa tayi inda nan take ta shiga mayar masa da martani suka dulmiya cikin duniyar k'auna. Sai da suka gurji junansu irin yadda suka d'auki tsayin lokaci basu yi kamarsa ba sannan suka sarara,har lokacin suna kwance rungume da juna,tana wasa da gashin jikinsa ta furta "Ranka ya dad'e.. Ni kuwa na jima da son yi maka wani tambaya amma bansan ya zaka d'auke shi ba.." Izini ya bata idanunsa a kulle,nan take kuwa sai ta shiga watso masa tambayar ta "Yallab'ai..! Shin me yasa ne ada da yanzun duk naga ka canja ne..ina nufin ada nasan ka mutum mai yawan fad'a amma kuma daga bayan sai naga duk ba haka ba,,ko kuwa dai dama nice na kasa fahimtar hakan ne ban sani ba..na kasa fahimtar komai" Idanunsa dake kulle yayi saurin bud'ewa had'e da zuba mata su,sai daya gama kallonta sannan yayi murmushi da cewa "Soyayyar ki ce ta sani canjawa..Ita ce ta mayar dani haka.." Da mamaki take kallonsa har tsayin wasu mintuna sannan tace "Nifa kace..!?" "Kwarai kuwa ke..kin san ya akayi ya zama haka..!?" Da sauri ta girgiza masa kai dan itama mamaki take da taji ya fad'i hakan,nan take kuwa sai ya shiga bata labarin kamar yadda ya samo asalina tun daga taimakonta gareshi a lokutan da suka gabata can wanda ya sani da kuma wanda aka bashi labari,,har ya dasa aya bata bar kallonsa ba cike da mamaki,,iska ya hura mata sannan daga haka yayi sama da ita suka shige royal bathroom d'insu,, sanda suka fito a wankan tana zaune saman stool a gaban mirror take kallon kanta ta cikin mirror, nan da nan sai tunanin abubuwan da suka gabata cikin rayuwarta suka fara dawo mata musamman ma yadda tun tana yarinya ada Inno take yawan tsoratar da ita game da kallon mirror d'in,, bayan shi kuma sai yadda suka dunga kai ruwa rana akan had'in manta wanda aka kwab'e da shuni,wanda matuk'ar ace ta shafa shi a jikinta babu yadda za'ayi duk iya kallon mutum ya ganota a matsayin wata kala ta daban ajinsin fata sab'anin abunda idanunsa suka gani,,murmushi tayi tunawa da lokacin da take cewa Inno ita dai gaskiya bata son wannan fatar tafi son nata ma'ana asalin yadda take kafin ta shafa wannan man kenan da yake maida ita bak'a wuluk,yadda Inno ta ringa mata wayo da dabara a lokacin tana fad'a mata ai mutane duk sunfi yayin irinsu tana mata dad'in baki sai yasa take ganin hakan ne,,lokacin data gama tunanin ta saki murmushi sosai wanda ya bayyana asalin kyaunta duk da a yanzun ita kanta ta sake zama wata babbar mace amma kuma bawai ta tsufa bane,,tana a cikin wannan halin Yarima ya riske ta,inda ya ganta tana ta murmusawa,, ta bayanta ya tsaya yana kallonta ta cikin mirror d'in kafin ya tambayeta abunda ya bata nishad'i haka har take murmushi ita d'aya,ba tare data b'oye masa ba ta shiga sanar da shi komai,shima murmusawa yayi sannan a hankali ya rungume ta tsam a jikinsa yana fad'in "Tabbas Inno ta cancanci dukkanin wata yabawa da jinjina,,domin kuwa ta kulamin da abunda duk duniya bayan Allah da manzonsa,babu abunda nake so a bayansa kamar ta,,kalmar godiya kad'ai bazata tab'a wadatarta ba,,sai dai muyi ta musu addu'ar fatan ganawa da duniya lafiya.." Murmushi tayi masa mai k'ayatarwa tana shafo moustache d'insa daya sake cika a lokacin fiye da da can,a hankali ta furta "Na gode sosai mijina da wannan karramawar,,ina sonka sosai fiye da yadda nake son kaina..Allah ya sake tsare min kai ya kuma baka ikon sauke nauyin al'ummah dake kanka,,tare da fatan yin adalci a cikin mulkinka.." "Ameen farin cikinah,hasken gidana,abun alfaharina,uwar y'ay'ana sannan kuma WALIYIYITA.." Murmushin jin dad'in yabon da yayi mata tayi sannan ta furta "Ina alfahari da kai angona..." Shima kansa cikin shauk'i ya furta "Nima haka madam..amma dai yanzun muje kisan yadda zaki yi dani dan kin sake tayar min da tsumi..!" Ido ta zaro waje dan ganin ko cikakkiyar awa guda basu yi da fitowa a wanka ba yake fad'an haka "KHUSHI..! Me kike tunani ne haka..?" Saurin girgiza masa kai tayi alamun babu,ko kafin tayi aune tuni har ya bar wajen da ita yana cewa "Tunda babu komai ai sai a san yadda za'ayi da wannan bawan Allahn ko..??" Murmushin dai still ta sake yi sannan ta shiga biye masa kamar yadda yake so,,,,cikin wannan k'adamin rayuwa mai cike da jin dad'i ya ci gaba da wanzuwa a tsakaninsu dama ahalin su duka,ta kowane fuska,gida ko ahalin rayuwarsu tana cike da jin dad'i,they all lived happily ever after.......... *K'ARSHE..* _ALHAMDULLAH..!_ _A nan na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai sunan *WANI AL'AMARIN..* kashi na *1&2* Ina mik'a d'umbin godiyata ga Allah (S.W.T) daya bani iko,dama da kuma lafiyar dana kawo k'arshen wannan labari nawa,inda nayi kuskure ubangiji ya yafemin ni daku,inda kuma nayi dai² Ubangiji ya had'amu a ladan..._ *Jinjina ga duk wani group da nake ciki ko bana ciki matuk'ar ace ana posting novel d'ina ban ware shiba kama daga Facebook,whatsapp nd wattpad,hakama masoyana a duk inda suke ina jinjina muku dan wannan d'an shafin yayi kad'an na zayyana sunaye,,,sannan y'an uwana writers suma ban barsu a baya ba ina yi muku fatan alkhairi duka da fatan rabb ya k'ara d'aukaka..* _Sannan ina sake mik'a godiyata ga masoyana,y'an uwana,dama magoya bayana,da sukayi jimirin saurarona a koda yaushe,inda har ga shi cikin hukuncin ubangiji na samu na kawo k'arshen wannan labari,Allah yasa jama'a suyi amfani da darussan dake cikin wannan labari,ina godiya sosai tare da fatan alkhairi a gareku masoya....Sai mun sake had'uwa nan gaba idan Allah ya nufa cikin labarin da nayiwa lak'abi da *ALK'AWARIN JINI..* kada kuji na kira shi da haka kuyi tsammanin littafin yak'i nake nufi,,no it's all about harsh lurv,duk da bawai shi naso ace na fara ba,buh shi d'inma dai ina fatan zai k'ayatar,ku kasance tare dani idan mai duka ya nufa...Fasubhanakallahumma rabbana wabii-hamdika nash-hadu an-laa-ilaha illa-antaa nastagfiruka wana tubu ilaiik..._ _TAMMAT BII HAMDULLAH...!_ _FOR CORRECTION'S/COMMENT'S JUST CONTACT ME @MY WHATSAPP ACCOUNT +2348165726609._ *UR'S AND ONLY....* #Hawwa M.U #JEEDDAHMU898 #REAL SMASHER 😉 #WANI AL'AMARIN #4/Aug. #End@11:45pm. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 63 of 63