Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
basu ganta ba.Abir ce ta basu amsa da cewar tana cikin turakar Abba,shiru suka yi na d'an wani lokaci kafin ABEELA ta mik'e ta nufi hanyan kitchen d'in Ummi kasancewar su kad'ai ne sai ko su Yarima da suka shigo yanzun,kuma suma d'in da suka shigo ba wani hira suke yi ba,tana shiga kitchen d'in ta hangeta ta juya ma k'ofa baga shigowa baya sai aikinta take babu wani mai taimaka mata ko da hira ne,murmushi ta d'an yi cike da son ta d'an tsokaneta,cikin sand'a ta isa kusa da ita,a hankali ta d'an yi d'age saboda ta d'an fita tsayi ta mik'a hannunta saman kanta had'e da yaye nik'ab d'in data rufe fuskarta da shi,cikin razani jeeddah dake kan had'a farfesun jin an yaye mata nik'ab nd she knows there is no one near to her,yasa ta fasa wani k'ara mai firgitarwa tana runtse ido gami da dafe k'irjinta dake bugawa da sauri,dai² nan dariyar ABEELA tasa ta bud'e ido a hankali kamar wacce aka ce idan ta bud'e su one time zata ga wani gagarumin abu,a d'an tsorace ta sauke idonta akan Abeela'n,hararar wasa ABEELA tayi mata ta ce "Kai..! gaskiya kin cika tsoro wollahi,ni da nazo na taimaka miki dan yadda ake zafi amma na ganki da nik'ab kuma ki rasa inda zaki sa sai a kitchen,sai kawai ki wani tsorata.." Ajiyar zuciya ta sake saki mai nauyi sannan ta juya ta ajiye utensil d'in hannunta tana cewa "Haba ai dole ne naji tsoro dan ban san da zuwanki ba..nd nasan babu wani a kusa dani.." Dai² nan YASEER ya k'araso gurin yana kiran sunan ABEELA coz bai san da wani a gurin ba,duka tunaninsa ya tafi akan wani abu ya sameta ne,sai daya iso cikin kitchen d'in sannan ya ga jeeddah tsaye suna magana da Abeela'n,ajiyar zuciya shima ya saki dai² yana sake k'arasowa kusa da ita,da murmushi a fuskar jeeddah harma ita kanta Abeela'n suka kalle shi tana amsa kiran daya mata na k'arshe "Chocolatey..! Gani fa kana kira na.." Hannunta ya rik'o yana sake janta zuwa jikinsa yana kallonta cike da so kafin ya furta wani abu tuni jeeddah ta juya musu baya dan yadda taga Babban yayan nata yana neman rungume ABEELA a gabanta ba tare da jin kunyarta ba,cikin rad'a yake tambayarta "What's wrong kuke ihu haka..??" Ture shi ta fara yi tana masa nuni da jeeddah dake cikin kitchen d'in da ido,murmushi ya sake yi kafin ya sake rik'o ta yana rad'a mata,ganinta is nothing to him,k'ok'arin k'wace kanta ta ci gaba da yi tana b'ata fuska,dai² nan sai ga Yarima shima ya kawo kai,a bakin kitchen d'in ya tsaya ganin halin da suke ciki sai yasa shi yin voice amendments,still ba tare da YASEER ya saketa ba ya waiwaya baya yana kallon Yarima da yayi kicin² da fuska,harara ya zabga masa kafin ya janye idonsa akansu yana fad'in "Ai sai ku fice anan ko sarakan rashin ta ido..!" Dariya maganarsa tasa YASEER kafin ya bashi amsa "Idan munk'i fa..??" "I will try to inform Ummi..So u have to leave..now.!" Zaro ido YASEER yayi sannan ya saki ABEELA yana cewa "Me yayi zafi..?? Ko kana so ka had'ani da ita tace dama bani da...." "Ba sai ka wahalar da kanka ba dan dama ba ita gareku ba.." Dariya YASEER ya d'an yi cikin zolaya ya furta "Time would convict u..We would see ur phase.." Sake d'aure fuska yayi kafin ya wuce ta gefe ya d'auka cup ba tare da yayi magana ba ya tsiyaya ruwa a ciki,half cup d'in ya sha sannan ya ajiye dai² lokacin da idanunsa suka sauka kan jeeddah wacce iya bayanta kawai yake iya gani,saurin jutawa yayi zuwa gefen da su YASEER suke tsaye har lokacin yana tambayarsa da ido akan dama tana gurin tun d'azun..? Da kai ya amsa masa,jinjina kai kawai yayi ya ajiye cup d'in ya nufi hanyan fita zai bar wajen,har ya iso dai² inda yake tsaye a tunaninsu ya gama abunda yake a gurin ne,sai dai ko da zuwansa ba tare da tsayawa tunanin komai ba ya fizgi hannun YASEER suka yi waje,ABEELA kuwa bakinta kad'ai ta iya toshewa saboda dariyar dake neman k'wace mata na ganin yadda Yayan nata ya fizgi YASEER suka yi waje ba tare daya shiryawa hakan ba,kusa da jeeddah ta k'arasa dai² tana cewa "Lemme help u.." D'an juyo wa tayi ta kalleta da murmushi a fuskarta "A'a..kam na gode sosai,gara ki huta kema.." "Ohh! Nice bakya so na taimaka miki ko..??" Murmushi ta sake yi kafin tace "Ko kad'an ba haka bane,kawai dai naga rashin dacewar hakan ne,shi yasa na fad'a.." Babu yadda ABEELA bata yiba akan ta taimaka mata amma tak'i yarda dan haka sai kawai ta hak'ura taja gefe saman stool ta zauna tana ta mata hira,wani abun tasa ta dariya wani kuma sai dai tayi d'an murmushi kawai abunta a haka har ta kammala abunda za tayi suna tare a kitchen d'in,haka ko sanda zata fito da kayan zuwa dining area tana setting gurin nan ma duk suna tare sai anan nema Jeeddan ta hak'ura Abeela'n ta taimaka mata. Su YASEER kuwa lokacin da suka fito a kitchen d'in babu jimawa sai ga Ummi ta fito saboda lokacin Abba ya fita,nan ta iske su suna y'an hirarrakinsu YASEER d'in sai tsokanar Yarima yake,zama tayi cike da farin cikin ganin a kowane lokaci kan yaran nasu a had'e,nan suka maida hankulansu kanta suka shiga gaisheta,cike da farin ciki ta amsa musu,kana ta fara tambayarsu batun zuwa gurin mai magani coz sun fad'a mata zasu je amma bata san ainihin takamaiman lokacin da zasun ba,bayanin duk yadda suka yi da malam Adamu a lokacin suka mata,cikin nuna jin dad'i da bayanin nasa kuwa ta kalli Yarima tana cewa "Son to ko dai zamu je bikon Sajida ne..??" Saurin kallonta suka yi su duka har suna had'a baki gurin tambaya "Ummi wace Sajida kike nufi..??" D'an murmushi tayi itama na zolaya kafin tace "Kuna da wata Sajida da kuka sani ne bayan y'ar baffanku Matawalle..??" Ai kuwa take suka sake furta "Whaaat..?? Ummi wannan kike nufi..?" Kallonsu tayi dan yadda suke had'a baki a magana abun har ya bata mamaki "Wani abu ne dan nace itan..??" Duka suka girgiza mata kai "A'a Ummi babu komai,amma dai ai...!" Sai duk suka yi shiru suna kallon juna dan suma maganar tasu mamaki take basu,murmushi Ummi tayi kafin tace "To sarakan had'in kai nima da wasa nake..Taya zanso wani abu ya sake had'a mu da irin Hajiya Suwaiba imma badan shi Matawallen da yake da alak'a da gidan nanba,ai nasan My son ya wuce ajin Sajida,ko yarona...?" Baice komai ba sai murmushi kad'ai da yad'an yi,nan Ummi tasa su gaba bayan d'an wasan da ta saba jansu sannan tayi musu nasiha akan su nutsu kuma su san rayuwa,kada dan suna ganin Allah ya d'aukakasu su nemi cin zarafin wani bawa nasa,ta jima tana musu nasihanta mai ratsa jiki kafin suka koma kan maganar auren Yariman............... *Wai shin Fan's wace ce kuke ganin a wannan lokacin ta dace da Yarima tunda dai kun san halin mutumin ba kula y'an mata yake ba..??* *Amma kuyi alk'alanci tsakanin y'an matan nan biyu wacce tafi dacewa da gidan Yariman..??* *#Aisha..??* Ko kuma *#Sajida..??* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 10.* ^^^^^^^^ *#Wife searchable.* Hiran da suke akan neman matar da ya kamata a aurawa Yariman suka ci gaba da tattaunawa,shi dai bai ce da su komai ba hasalima sai komawa da yayi ya kwanta a jikin manyan tuntum dake baje a parlour'n yana clicking wayansa data d'auke masa hankali,duk maganar da suke ya kasance tsakanin Ummi ne kad'ai da YASEER,can YASEER ya d'an tab'a shi yana cewa "Broah..! Can't u say something..??" Gira d'aya ya d'age masa alamun tambaya akan abunda zai yi magana "Ohh! U don't even know what to say..??" Da ka ya masa alamar haka d'in ne ba tare daya san me yake cewa ba,ganin hankalinsa baya tare da su yasa YASEER d'in fizge wayar dake hannunsa,saurin d'agowa yayi ya kalleshi yana had'e girar sama dana k'asa "Why always kake so ka dungamin irin haka ne..??" "I don't even know.!" Ya d'age shoulder sama yana sakar masa d'an k'aramin smirk,tsaki ya saki kafin ya mik'a masa hannu alamun ya bashi abunsa "I can't do this,unless u were free ur mind.." Harara ya zabga masa cikin takaici ya ce "Bazan ce ba d'in,it's necessarily sai nayi magana..??" Duk wannan abun da Yariman yake ko d'aya baisa YASEER jin babu dad'i ba sai ma shi d'in daya maida abun kamar tsokana "Ai kuwa yau bazan bada ba har saika yi magana.." Ummi ya juya ya kalla yana marairaicewa "Please Ummi say something..!" "Waye zai shiga tsakaninku..?? Haka kawai ina zaune yanzun kusa ni jin kunya..Tsakaninku ne maza karb'i a hannunsa ai ba k'arfin ka yafi ba.." Shima d'in koda jin abunda Ummi ta fad'a sai tasa shi sakin siririn murmushi kafin ya juya ga YASEER yana fad'in "Heey Man..are u ready to confer or not..??" "Am not..!" YASEER d'in ya fad'a,mik'ewa yayi ya nufi inda yake tun kafin ya k'araso tuni YASEER ya ajiye masa ita a k'asa,k'wafa yayi kafin ya d'auka yana cewa "Coward men..! Daka bari ai na iso kaga abunda zanyi maka.." Dariya duka suka fashe har Ummi data zuba musu ido tana murmushin drama d'in nasu,sai daya koma ya zauna sannan Ummi ta kalleshi tana fad'in "YAZEED son..when zaka nemo matar ne.?? Naga kai hankalinka sam baya tare damu.." D'an kallonta yayi ta gefe ya had'iye yahu kafin ya iya bata amsa "Soon Ummi in sha Allah.." "To Allah yasa kada a tsaya shiririta kamar wancan lokacin.." Saurin cafe maganar YASEER yayi "Ai wollahi kuwa Ummi kamar kinsan abunda zai faru kenan,yo mutumin da baya tsayawa da y'an mata wace ce zata yi sha'awar ganinsa kusa da ita,wasufa y'an matan har nunawa suke suna ra'ayi amma mutum kamar Gunki shi ko damuwa da lamarin baiyi.." Kallonsa duka suka yi lokaci guda kuma suka yi murmushi tsakanin Ummi da Yariman "Hey! Man it's not a case of urs..u have to cover up ur lips.." "Bazan yiba d'in,kin jishi ko Ummi sai an fara magana yace babu ruwana a ciki,idan har babu ruwana a ciki me zai hana kayi zuciya ka duba mai sonka ko da cikin wanda suke maka tallar kansu ne..??" "Yeah! YAZEED son u have to fixed up someone da zata kula mana da kai,kada ka duba maganar d'an uwanka,but ya kamata ace ka tsaya kayi tunani kaji kaga wulak'anci babu dad'i koba haka ba..??" Shiru yayi cikin ransa yana gasgata maganar Ummi'n,a hankali kuma ya d'an d'ago kansa ya kalleta ya furta "Ok Ummi.. I will try my best.!" Murmushi tayi masa itama na jin dad'i,saboda ganin a ko wane lokaci yakan yi k'ok'arin yabi shawararta "May almighty Allah pinpoint us uprightness..!" "Ameen" suka amsa duka,kallon gefen YASEER Yarima yayi cikin zolaya ya ce "Man..! Ashe u are slower sometimes.." Hararar sa YASEER yayi kafin yace "Ka manta am from asylum.." Dariya duka suka sa,haka suka ci gaba da hira a nan apartment d'in Ummi,basu sukabaje ba sai dare sannan kowa ya nufi nasa apartment d'in. Jeeddah kuwa ko data gama aikinta bayan ta gyara ko ina ta maida komai muhallinsa sai ta sulale ta k'ofar baya,tayi ficewarta dan yadda take jin suna hira bata so ace ta biyo ta nan,bare kuma har ya zama tayi calling attention nasu zuwa gareta,ranar kam bata ko samu damar yiwa Ummi sallama ba,sai sak'on data bawa ABEELA akan ta sanar da Ummi'n ta wuce sai da safe.Kasancewar yanzun duk wani aiki na apartment d'in Ummi an d'auke mata illa iyaka girki kad'ai da take yima Ummi'n,shima dan tak'i yarda da kowa yayi mata ne,duk da adadin hadimanta amma tak'i amincewa a kawo mata wata sai jeeddan ke yi. Da zuwanta gida ta iske babu kowa dan haka kai tsaye ta wuce d'aki ta rage kayan jikinta sannan ta fito tsakar gida tana y'an aikace² da baza'a rasaba,sai a sannan ta tuna da abunda ya faru d'azun a kitchen,haka nan ta d'an saki murmushi,ta jima tana tuna abun tana murmusawa da alama abun yana matuk'ar bata nishad'i, har ta gama y'an share² babu wanda ya shigo gidan, dan haka ko data kammala itama alwalar Maghreb ta d'aura sannan ta wuce zuwa d'aki abunta. A gefen Yarima kuwa tunda Ummi tayi masa maganar ya kamata ya duba wata mai sonsa ko da cikin y'an matan da YASEER yake magana ne,tun a sannan sai hankalinsa ya kasu shima akan ya duba d'in,babban burinsa a lokacin kuwa bai wuce ace yayi abunda Ummi'n nasu ta sashi ba,a dai² wannan lokacin shima d'in da kansa bayan waccan maganar da suka yin sai ya dunga jin bashi da buk'atan daya wuce yayi auren,sai dai kuma abu d'aya ke dakatar da shi a duk lokacin da tunanin hakan yazo masa,shi ne rashin tsayayya wacce ya kamata ace ya nufa da irin wannan maganar tunda shi d'in ba ma'abocin kule² bane bare yace ga wata wacce suka fi shiri tunda ko wacce share ta yake. Yau kam tunda ya dawo daga office ya zauna a parlor yana clicking waya,kamar daga sama new number tayi masa magana,har ya wuce sai kuma zuciyar sa tasa shi dawowa baya,cikin basarwa ya shiga amsa maganar,zuwa sanda ya gama fahimtar da mace yake magana,abun mamaki a d'an wannan maganar da ya d'an tsaya suka yi haka nan sai ya fara jinsa kamar wani cikakken mutum,yana zaune sai ya d'an saki murmushi,wisely suke hira tun baya sakewa sosai yayi magana har kuma ya zama ya d'an fara bada had'in kai,wasa² tun abun bai soma shigar sa ba,sai gashi yau da gobe tasa ya fara sakewa da Yarinyar,wacce tuni ta shaida masa sunanta Zahra,da kasancewarta y'a ga ambassador Abdulmalik,jakadan nigeria a k'asar london,kasancewar through internet ne suka had'u sai had'uwar tasu tazo musu a bazata,kwanaki sunci gaba da gangarawa,wanda izuwa wannan lokaci da aka d'auka tuni shak'uwa ta fara shiga tsakanin Yarima da Zahra duka kuma ba tare da sun tab'a ganin juna ba,cikin haka ne wata rana suna hira kamar yadda abun ya zame musu sabo,a nan ne Zahra take tambayar Yarima when zai zo gidansu..?? Tambayar da fari taso bashi dariya amma sai yaga itan da gaske take,dan haka sai ya maida abun serious shima suka ci gaba da hiran har ta kaiga ya sanar mata sanda zai je gareta,amma dai ta fara tura masa address nata,da murnarta ta tura masa details d'in komai,after sai suka ci gaba da hira kamar ko wane lokaci har zuwa sanda suka yi sallama. Kwanaki biyu tsakani kasancewar itama suna zaune ne a garin Abuja'n,suna waya da Yarima yake sanar mata da zuwansa a washe gari daya kasance Friday saboda yana son wucewa Kano shi yasa ya yanke shawaran zuwa a washe garin. Hakan ce ta kasance a washe garin kamar yadda ya fad'a mata,bayan sun kammala duk abunda za suyi suka d'auki hanyan zuwa gidan su Zahra'n shi da YASEER, sanda suka isa sunji mamaki sosai dan ganin yadda suka riski line d'in da securities duk da yasan wace Zahra Abdulmalik,tun daga farko har k'arshen line d'in ta ko ina securities ne,duk wanda zai shiga ko ya fita a harabar line d'in sai ya sha tsanani gurin bincike,suna zuwa sukam basu wani b'ata lokaci ba kasancewar sun fad'i gidan da suka zo haka an san da zuwansu,dan haka ba'a b'ata musu lokaci ba aka basu hanya suka wuce kai tsaye,wannan abu daya faru ba k'aramin mamaki ya basu ba har sanda suka isa zuwa mansion d'in wanda idan har ana batun had'uwa da tsaruwa to wannan gidan ya wuce duk yadda za'a kwatanta shi kuma ba wai iya kad'ai a garin Abuja ba hatta da sauran garuruwan 9ja sai an bincika kafin a samo kwatankwacin sa,guest sitting room aka kaisu wanda ko iya shi kad'ai mutum ya kalla zaisan naira na kokawa a wannan gida,babu jimawa tsakanin zuwansu sai ga itama Zahra'n ta shigo cikin ado sai murmushi take dokawa,barka da zuwa ta musu sannan suka gaisa fuskarta a sake,basu wani jima ba sosai kasancewar dama a hanya suke,nan suka barta akan idan sun dawo zai yi mata zuwa na musamman,daga haka suka yi sallama da ita suka wuce,itama ta koma gida sai farin ciki take musamman na irin wannan tsintar dami a akala. Lokaci yaci gaba da tafiya,cikin haka shak'uwa mai tsanani ta sake shiga tsakanin Yarima da Zahra wanda har ya wuce a kwatanta,sai dai shi a gefen Yarima duk wannan shak'uwar da suka yi da ita duka yana d'aukan tane a matsayin ba komai ba,ko da YASEER ya masa maganar yana sonta ne nan yayi ta masa musu akan hakan,wai shi dai kawai friendship ne tsakaninsu,lokacin daya fad'a dariya kawai YASEER yayi ya rabu da shi dan yasan ko kwana zaiyi yana masa bayani bazai tab'a yarda da shi ba. Sai dai wani abun mamaki bayan y'an kwanaki tsakanin maganar tasu sai ga yarima yazo masa da maganar da tasa shi darwa sosai,yana zaune Yariman ya zo ya zaune kusa da shi,a hankali ya d'an kalleshi cikin wani yanayi kafin ya furta "Broah..! Ina tunanin yin aure kwana kusa..!" Saurin kallonsa YASEER yayi yana sake bud'e idanunsa,kamar wanda bai fahimci abunda ya fad'a ba yace "Kace mene..??" Ba tare daya kalleshi ba yace "Abunda kunnenka suka ji maka..!" Dariya YASEER yayi ta masa kafin ya tsagaita yana tambayarsa "Wace mai sa'ar ce haka..Allah yayi da rabonta..??" Kallonsa ya d'anyi dan yasan maganarsa akwai wani abu da take nufi,bawai iya tambayar bane kad'ai,ganin bai ce wani abu kuma sai yasa shima ya share ya kuma bashi amsa "Zahra ne.!" Jinjina kai yayi bayan yaji amsar tasa,sannan yaci gaba da magana "Eheen! Allah ya taimaka to.." Bai iya cewa komai ba dan yadda ya fahimci hankalin YASEER yayi wani gurin daban,ko da ganin YASEER d'in baice masa komai ba sai shima d'in ya kyale shi bai sake masa maganar ba,sai dai ya yankema ransa zai kira Ummi suyi maganar kawai,hakan kuwa akayi da dare after sallar isha'a ya kira Ummi ya zayyana mata komai tun daga had'uwar sa da Zahra'n har kawo yanzun bai bari ya fad'a mata wani abu da babu shiba,addu'o'i na fatan sanyawar alkhairi ta bishi da su sannan ta shaida masa in sha Allah da idan Abba ya shigo zata sanar masa dan ayi komai cikin lokaci kad'an ba sai anzo ana ta jan rai ba. A gefen Zahra ma haka abun ya kasance dan tuni ita kam Yarima yayi mata kawai dai tana ta addu'a ne da fatan ya kasance nata har abada,kuma da yake itan ta kasance y'ar boko mai masifar wayo sai bata fito fili ta nuna masa ba,kamar yadda ya sanar da ita ta fad'awa iyayenta maganar zuwan magabatansa dan neman aurenta,yasa bata yi k'asa a guiwa ba ta shaida musu,ai kuwa nan ambassador Abdulmalik ya shiga shirin tarbar bak'in nasa kamar yadda suka yi zasu iso a cikin satin. Maganar nemawa Yarima auren Zahra tuni ya kankama a cikin k'aramin lokaci,wanda kan kace kobo tuni har maganar ta gama karad'e Royal Family,masu murna nayi haka ma masu bakin ciki duka tuni suka fara bayyana kansu.Kamar yadda aka al'k'awartawa ambassador Abdulmalik cikin satin tawagar su Abba GALADIMA ta d'auki hanyar birnin tarayya,kasancewar a private jet na masarauta suka tafi,wanda a wanna tafiya bawai iya kad'ai Abba GALADIMA bane,tafiyar ta k'unshi wasu daga cikin manya na masarauta ciki kuwa har da Abba Matawalle,wanda shima cewa yayi baza'a barshi a baya ba,wanda yace tunda y'arsa tak'i wannan ba shi ne abunda zaisa shi kuma ya nuna jin haushi akan neman auren na Yariman ba,a cewar sa duk abunda ya faru ita ta jawowa kanta.Haka suka je Abuja suka kuma dawo cike da farin cikin yadda al'amarin ya kasance cike da mutunta juna,bayan dawowarsu babu b'ata lolaci Abba GALADIMA ya sanarwa Maimartaba yadda komai ya wakana,inda Abba GALADIMA'N ya shaidawa maimartaba batun tsayar da ranar auren nan da sati uku masu zuwa. A can gefen Zahra kuwa a dai² wannan lokaci da duka ahalinta ke cikin tsananin farin ciki,ita kuma a sannan ne wani abun tashin hankali ya kunno mata cikin lamuranta a wayewar garin data fara tabbatarwa ranta ita da Yarima abun daya rage musu su mallaki juna bashi da yawa. Fitowarta a wanka kenan daga ita sai towel iya cinyanta ta tsaya gaban mirror don shiryawa saboda Yarima ya shaida mata zai zo,bata kaiga zama ba k'arar shigowar sak'o ya katse mata abunda take,cike da son dubawa ta d'ago wayar tana murmushi duka a tunaninta sak'on ya fito ne daga gurin Yariman............... #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *Zuwa ga masu k'orafin bana son amsa musu idan sunyi comments,babban abunda nake son ku fahimta shi ne,a duk lokacin da kuka ga kunyi sharhi marubuci bai yi magana ba,uzuri ne farkon abunda ya kamata kuyi mana coz ba kowa ne lokaci ne muke samu mu bibiyi sak'onnin kuba,amma nasan iya k'ok'ari muna yi na ganin mun duba d'in har ma muyi sharhi idan lokaci ya samu,sai dai muna fatan zaku sake yi mana uzuri,sannan ina mai k'ara baku hak'uri ga

Chapter 33 of 63