Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fatan sake nemanki..!" K'it ya katse kiran dan ya riga ya gama fad'an abunda zai fad'a,dai² ya gama wayan ya juya yana huci ya bar Yarima da binsa da ido kamar bai tab'a ganinsa ba.. ^^^^^ Itama Zahra a lokacin da YASEER ya gama fad'ar abunda ke ransa,bayan ya kashe kuka ta sake saki,da gudu kuma ta fice tayi apartment d'in iyayenta dan sanar da mahaifiyata abunda ke k'asan zuciyarta. Cikin sa'a kuwa ta fara cin karo da Hajiya Amina,tana kukan ta nufeta ta fad'a jikinta tana sake fashewa da wani irin matsanancin kuka "Mommy ki taimake ni please..!" 'Dago kanta ta shiga k'ok'arin yi ganin irin kukan da take tsananta yi "Auta what happened..!" "Mommy bana sonsa...bazan auresa ba..!" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Auta are u insane..?? Kin san abunda bakinki ke fad'a kuwa..?? Why sai yanzun da muke tsaka da farin cikin ganin auren ki kuma ya rage mana lokaci kad'an kiyi batun fasawa...Eeaaayy! maza sanar dani idan akwai matsala." "Mom he's captive,ya tab'a rayuwa a jail..Mom i don't want any relations with him.." "What..!!! Zahra are u serious..? how kika san ya tab'a zama a jailhouse,for how long..??" "Mom da gaske nake babu k'arya a magana na..ki yarda dani,kin san bana miki k'arya,if u didn't endorsed my words,kisa a sake miki bincike.. Amma ni ina da evidence da zai gamsar daku da gaske nake..!" Rik'e baki Hajiya Amina tayi tana kallon yarinyar tata dake wani irin kuka kamar zata cire ranta,a hankali kuma ta sake jan kanta zuwa jikinta tana patting bayanta cikin sigar rarrashi "It's Ok baby..Ko cewa kad'ai kikai kin fasa auren babu mai takuraki,ballema nasan tunda wannan maganar ya fito a bakinki akwai k'anshin gaskiya,but ina son ki nutsu kinji kada kisa damuwar wannan abun a ranki,matuk'ar ina numfashi babu mai tursasaki akan sai kin auresa,zan yiwa mahaifinki bayani kinji ko..??" Kai ta gyad'a mata,sannan ta sake lafewa a jikinta tana sakin ajiyan zuciya.Hajiya Amina kuwa banda gyad'a kai babu abunda take alamun da ke nuna tana jimanta maganar da Zahra tazo mata da shi. ^^^^^ Yarima YAZEED kuwa yana nan zaune har lokacin a inda YASEER ya barshi,banda ajiyar zuciya babu abunda yake,alamun dake nuni da yana cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara,sai da ya shafe tsawon wasu awanni a gurin kafin ya yunk'ura ya mik'e yana tafe yana tangad'i kamar wani drunker,a daddafe ya iya k'arasawa bedroom d'insa yana shiga kai tsaye ya nufi toilet,ba tare daya damu da rage kayan jikinsa ba ya saki shower a kansa,yadda ruwan yake sauka a jikinsa haka yake jin tarin damuwar sa a hankali itama tana sauka,kafin wani lokaci ya rage daga shi sai ajiyan zuciyar kawai da yake saki,ya b'ata lokaci k'ark'ashin shower'n sannan a hankali yaja k'afafunsa y fito sai d'igar ruwa jikinsa yake,sai daya fito ne sannan yayi k'ok'arin raba jikinsa da jik'ak'k'un kayan,sanda ya gama direct bed ya nufa ya kwanta a rigingine yana facing ceiling zuciyarsa duka har lokacin a cunkushe yake jinta,kamar wanda aka tsikara haka ya sake mik'ewa ya nufi closet,kayansa duka dake ciki ya fara fitowa da su ya shiga had'a su a luggage's,sanda ya tabbatar ya gama had'a duk wasu muhimman kayansa ya soma jan luggages d'insa da niyyan fita,yana cikin shirin fitan kuwa suka kusa yin karo da YASEER a hanyan,kallonsa ya tsaya yi for some minutes kafin ya fizgi maganar dake mak'ale "Broah..! Ina zaka jene haka..??" Bai juyo ba yana ci gaba da tafiya abunsa,sai daya kusa rabin parlour'n sannan ya furta "Am leaving..!" "To where..??" "My homeland..!" Zaro ido YASEER yayi cikin yanayin firgici "Why so soon...??" D'an juyowa yayi kad'an yana kallon YASEER "Mene amfanin zamana anan...??" Girgiza kai YASEER ya shiga yi amma kafin yayi wani magana tuni ma shi yayi waje,da hanzari YASEER d'in ya biyo bayansa yana kiransa,a harabar gidan ya tarar da shi nan ya d'an dakata kad'an "Wai mene hakan yake nufi,aikin kumafa kana nufin mene..??" "Already am reserving.." Ido waje YASEER ya ci gaba da kallonsa cike da alamun tambaya "Kana nufin kayi resigning..??" Kai ya shiga gyad'a masa alamun haka ne,shima jinjina kai yayi kafin yayi masa alama da hannu alamar ya jirashi zai fito yanzun,cikin mintuna da ba zasu gaza goma ba sai ga shi shima jaye da luggage's d'insa har ya iso kusa da Yariman wanda tunda ya fito yake binsa da kallon tuhuma har sanda ya k'araso kusa da shi bai bar jifansa da kallon ba,yana zuwa ya bud'e booth ya shiga loda luggage's d'in nasu ba tare da yayi magana ba,sanda ya gama tsaf sannan ya amshe key d'in a hannun Yarima ya shige mazaunin driver yana yiwa masa magana da ya zo su wuce. Daga nan direct office suka wuce babu wanda suka bari ya fahimci halin da suke ciki da haka kowannensu ya wuce office d'insa,bayan shigar yarima a office d'in a gaban table d'insa ya tsaya sai daya shafe wasu y'an mintuna yana k'arawa wajen kallo kafin ya zare fara kar d'in envelope ya ajiye akai ya fito,yana fitowa bai sake jiran wani abuba yayi hanyar fita zuwa parking lot,a mota ya tarar da YASEER yana jiransa wanda already shi d'in kawai yake jira,sanda ya k'araso har ya dai²ta zamansa sannan YASEER yayiwa motan key suka kama hanyar airport......... *Kuyi hak'uri da ni,naso posting d'in yau yafi haka sai dai uzuri yasa ban samu damar k'arasa typing ba sai yanzun,mu had'u gobe idan rabb ya ara mana rai da lafiya..* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 13.* ^^^^^^^^ *#His Slave* Har jirginsu yayi arriving a Kano,babu wanda yasan da zuwansu,dan haka ko da suka sauka banyi tunanin akwai wanda zaizo tafiya da suba,amma abun mamakin sai naga wasu mutum biyu sanye da kayan fadawa wanda bayin masarautar kano ke amfani da shi,a wani k'atuwar range robber mai duhun glasses suna jiran isowarsu,fitowarsu babu jimawa bayin suka nufe su had'e da amsar luggage's d'in sannan suka bud'e musu k'ofa suka fad'a cikin motan,mintuna 30 suka kawo su royal palace,ba tare da kowa yasan da zuwansu ba suka nufi apartment d'insu,sai a sannan ne YASEER ya d'an kalli yarima cike da fargabar abunda zai biyo baya yana cewa "Broah.! Yanzun me zamu fad'awa maimartaba idan ya tambaya dalilin dawowar mu dai² lokacin da yasan muna kan aiki...??" Wani kallo Yarima yayi masa mai kama da harara kafin yace "Say's whatever ur mind personified.." "Haba broah yanzun kawai saina fad'a masa nayi resigned a aiki,me kake tunanin zai faru..??" Gaba d'aya ya juyo yana fuskantar sa,cikin magana mai kama da gatsali ya furta "Are u ready to violate at him..??" Kai YASEER ya girgiza,nan shima Yariman ya ci gaba da abunda yake yana sake cewa "If u didn't..Just ka fad'a masa abunda ya faru kawai.." Jinjina kai yayi kamar wani dole sannan ya zube cikin cuition yana sakin ajiyan zuciya,zaman kurame suka fara ko da ganin haka yasa YASEER d'aukan waya ya shiga clicking,number Ummi'nsa ya fara kira kafin ya nemi matarsa,da sallama ta amsa masa after sun gaisa take tambayarsa "Son ya aikin..??" Ajiyan zuciya yayi guiwansa cike da sanyi ya ce "Ummi muna Kano ai yanzun.." "Kano..?? Yaushe kuka zo d'in.. Nd mene ya kawo ku Kano..??" Jim yayi yana tunanin yadda zai fad'a mata abunda ya faru,yana a halin shirun yajiyo muryar ta cikin fad'a tana sake tambayarsa,sai da yayi jarumta sannan ya iya cewa "We make a decision to resigned..!" Duk da Ummi bata gurin sanda ya fad'i kalmar sai data fidda ido waje,kalmar Innalillahi wa'inna ilahiii raji'un kawai take maimaitawa,sai data maimaita yafi sau nawa sannan tace "What happened..?? Da har ya janyo za kuyi wannan d'anyen aikin ba tare da kun sanar damu halin da ake ciki ba..?? Anya kuwa yaran nan kuna cikin hankalinku..??" Shiru yayi har zuwa lokacin data kai aya sannan cikin sanyi yace "Ummi please na,bafa haka nan muka yi abu da kai ba,it becomes necessary..!" "Kai ban son shirmen nan naku,idan banda kun raina mutane me zaisa kuyi hakan..?? Shi kenan idan kunga dama tunda kun baro aikin sai ku zauna gida tunda haka kuka zab'a.." "Please Ummi zan k'araso yanzun zaki ji dalilin faruwar hakan in sha Allah,bada niyyan muka yi ba..." "Allah ya kawo ka lafiya,idan naji abunda bai min ba ai kasan rai zai b'aci.." Ajiyar zuciya yayi sannan ya furta "Ummi sai dai na shigo d'in.." Daga haka suka ajiye wayan,duk abunda yake idanunsa na kan Yarima daya kwanta idanunsa a rufe yana kallon sama.Bayan daya gama wayan mik'ewa yayi ya shiga musu packing kayansu a gefe sannan ya wuce toilet dan d'aura alwala saboda gabatowar sallar Maghreb,har ya fito YAZEED na nan a yadda yake kamar mai bacci,a kusa da shi ya d'an tsaya yana sauke hannun white long sleeve dake jikinsa yana magana "Broah.! Wake up..! Lokaci fa yayi." Bud'e ido yayi a hankali ya d'an kallesa kafin ya yunk'ura ya mik'e,a hankali shima YASEER d'in ya zauna yana jiran ya idar su wuce masjeed,har ya fito ya riske shi a inda ya barshi daga nan suka fice suka nufi masallaci,sai after isha'a sannan suka shigo cikin gidan,sai a nan yarima ya samu daman yin magana da YASEER d'in yana shaida masa zai je yaga Umma'nsa,jinjina kai YASEER yayi sannan ya ce "Muje idan mun fito sai mu k'arasa gurin Ummi,coz ina tsoron fad'an Ummi idan ta kamanin ni d'aya.." Tare suka jera amma babu wani hira a tsakaninsu,har suka shiga suka fito daga nan suka nufi apartment d'in Ummi'n,tun daga shigarsu Ummi ke binsu da kallon tuhuma,a haka suka gaidata kana suka zauna shiru,kallonsu tayi su duka biyun taga kowanne fuska a cunkushe,had'e fuska tayi itanma sannan ta kalli YASEER "Dama abunda ya kawo ku kenan kuzo kumin shiru..?? Ina bayanin da kace zaka sanarmin..??" Shiru yayi yana sauke kai k'asa hakan da ta gani yasa ta sake yin magana "Kai nake sauraro ko kuma ka tashi ka bani guri tunda ba abunda na kiraka kamin ba kenan ka sani.." Bai iya d'agowa ya kalleta ba,sai magana daya fara cikin sanyin jiki ya fara mata bayanin duk abunda ya faru a Abuja,har kawo kan resigned da suka yi.Shiru tayi cike da jimami da kuma takaicin abunda ya farun,idanunta akan Yarima tana binsa da kallon tausayawa,a hankali ta girgiza kai tana mai jin wani irin yanayi yana tsirga mata na tsantsar b'acin rai,amma duk da haka bata fasa mgna ba,nasiha sosai tayi musu mai shiga jiki wacce duka ta karkata ne akan hak'uri da K'addara mai kyau ko kishiyar hakan,sannan suka mata sallama suka fice,bayan fitarsu a apartment d'in sallama suka yi da juna dan yadda suka ga dare ya soma nisa,daga nan YASEER ya nufi apartment d'insa shima Yariman ya nufi ainihin apartment d'insu. Washe gari kam tun da safe maimartaba yasa aka kira masa su lokacin yana apartment d'in Umma Fulani coz lokacin fitarsa fada baiyi ba,ba tare da b'ata lokaci ba suka nufi apartment d'in dan amsa kiransa,suna shiga maimartaba ya nuna musu gurin zama cike da nuna musu alamun su zauna,kawunansu a k'asa suka zauna zuciyoyinsu cike da fargabar abunda zai biyo baya dan sun san kiran bana lafiya bane,nan suka fara shan ruwan tamvaya daga maimartaba,inda a karon farko ya fara jifansa YASEER da tambaya "YASEER..! Shin wane dalili ne yasa kuka ajiye aikin ku..?" Duk da yasan amsar da zai bayar a lokacin sai da yaji shakkar fad'an,Umma'n YAZEED tana zaune itama a gefe tana sauraren abunda zai faru dan tunda aka yi waya masarauta aka sanar da maimartaba abunda ya faru ya shaida mata,wannan dalilin yasa ta bashi shawaran a kirasu a tambayesu dalilin aikata hakan,b'angaren da YAZEED yake maimartaba ya kalla yana had'e fuska dan baya son ya nuna musu wani alama da zaisa su k'i fad'ar gaskiya,babu zato Yarima yaji muryar mahaifinsa yana musu fad'a akan abunda ya faru,har ya gama babu wanda yayi koda tari,sai a sannan YASEER ya d'an gyara zama ya shiga yiwa maimartaba bayanin duk abunda ya faru,duk da maganar ta tab'a musu zuciya gaba d'aya'nsu,hakan bai sa ya nuna musu ba ko a fuska,daga haka ya sake musu nasiha ya kuma nuna musu kuskuren da suka aikata game da aikinsu sannan ya sallame su suka fice. Bayan fitarsu a apartment d'in ya rage sai Umma Fulani da maimartaba kad'ai,a nan suka fara tattaunawa akan matalolin da ake yawan samu akan Yariman wanda a kullum idan aka samu irin wannan damuwar ko wata magana ta fita dangane da shi d'in take sawa yaji matuk'ar bak'in ciki da damuwa,sun jima suna tattaunawa kafin suka gangara kan maganar auren Yariman da Zahra da ake kan samun matsala a yanzun,wanda a k'arshe basu bar maganar ba har sai da suka yanke shawaran jiran ganin abunda zai faru ta b'angaren Ambassador Abdulmalik. Kwanaki sun ci gaba da tafiya,ba tare da wani sakamako ko magana daga b'angaren Ambassador Abdulmalik d'in babkamar yadda maimartaba yayi tsammani,wannan tasa kan dole maimartaba ya taushi zuciyarsa had'e da yanke shawaran tura d'an aike don samo masa gamsashen bayani game da inda matsalar ta kwana duk da ya fahimci Ambassador d'in ba babban mutum bane,wanda shi da kansa sai yanzun ne yake ganin gara ma da aka samu wannan matsalar har tayi sanadiyyar yankewar alak'ar dake tsakaninsu,ko da sak'on maimartaba ya riski Ambassador Abdulmalik ba tare da b'ata lokaci ba ya shaidawa d'an sak'on masarauta nasa sak'on na janye batun aure tsakanin yarima da Zahra,haka d'an aiken ya juyo da mummunan labarin da ambassador d'in ya shaida masa na rashin yiwuwar auren tare da soke alak'ar su da masarauta.Lokacin da sak'on ya riski ahalin masarauta ga wasu daga cikinsu sam basu ji dad'in wannan abun daya faru ba,sai dai babu yadda za suyi nan suka fawwala lamarin zuwa ga Ubangiji,tare da neman sauk'i daga gurinsa. Haka rayuwa taci gaba da gangarawa yayin da a kowanne bigire al'amura da dama suke kan faruwa,wanda mafi yawa daga ciki suka ta'allak'a akan neman aure ga Yarima YAZEED da akayi tayi amma duka babu nasara. ^^^^^ A b'angaren Adda da ladidi kuwa kusan zamu iya cewa rayuwarsu ta koma gefe guda wanda tun bayan auren Yariman da suka d'aukewa masarauta k'afa,ko da zuwansa ya kama su basa lek'awa,idan kuwa har ka gansu sun zo tofa sai dai ko munafurcinsu ya kawo su,haka a ko wane lokaci zaka iske su basu da buri ko fatan daya wuce ace sunga wani abu na rashin jin dad'i ya samu wani daga cikin ahalin,tofa a nan ne zaka ga farin cikinsu da murnar su ta bayyana. Ita kuwa Aisha a nata gefen tuni ta fara samawa kanta lafiya sai dai har kullum itama kan neman mafita take amma ta rasa inda ya kamata ace ta nufa wanda zai zame mata wani jigo da zata kama ya zame mata madogara a rayuwarta. Kamar ko wane lokaci yauma tana zaune a bedroom d'inta tana sana'ar tata na mugun tunanin daya zame mata jiki,haka nan ta fara jin fad'uwar gaba na damunta,can kuma kamar wacce aka tsikara ta mik'e ta zari veil d'inta ta fito fuskarta kamar ta macen dake takaba,babu wanda ta kula tsakanin Adda ko Ladidi duk da ta gabansu ta wuce tayi ficewarta a gidan ba tare data tsaya ko bi takan d'aukan mota ba ta kama hanyar fita a line d'in nasu,a bakin hanya ta tsaya tana duba abun hawa,tricycle ta tsare ta kwatanta masa inda zai ajiyeta daga nan suka d'auko hanya,dai² kan titi ta sauka bayan ta sallame shi taci gaba da takawa da k'afarta zuwa cikin royal palace d'in,sai dai maimakon ace ta nufi hanyan cikin gida kamar yadda ta saba,sai ta d'auke hanya bayan ta wuce k'ofa zuwa wajen line d'in gidajen bayin,sannu a hankali take tafiya zuciyarta cike da fargabar abunda zai faru har ta k'araso k'ofar gidan,a dai² k'ofar gidan ta tsaya shiru har zuwa wani lokaci,ta d'auki lokaci a tsaye a gurin tana tunanin gidan ne ko kuwa..?? Kafin ta motsa,ko data gama tabbatarwa kanta gidan ne nan ta tasamma k'ofar shiga ainihin gidan gadan² zuciyarta na daka. Bayan fitar Aisha a gidan kuwa da yayi saura daga ladidi sai Adda,nan suka sake bud'e sabon shafin hira kan al'amuran da suka shafi masarauta,sun kwashe tsawon lokaci suna maganar kafin Adda ta yunk'ura ta mik'e tana cewa "Kashh! Kinga nayi ragon azanci na manta ban tambayi yarinyar nan inda zata ba,dan ni kam cikin kwanakin nan sam na gaza yarda da zaman shiru da take yawan yi,gaba d'aya cikin y'an wad'annan kwanakin ta daina walwala,itace kulle kanta a d'aki,fita park duk da nasan d'abi'ar tane to amma ba kamar yanzun ba,haka wani lokacin kuma zata tusa mu a gaba tana kallo..shin kin kula da wannan canjin kuwa..??" Shiru Ladidin tayi tana d'an jinjina kai alamun itama d'in ta gano hakan "Anya kuwa bakya ganin an samu wata matsala ne da har hakan yake faruwa..??" Adda'n ta sake yin maganar cikin yanayin jimantawa "To Adda ni mene zance ne akan wannan maganar,na sha fad'a miki babu abunda ya farufa kawai ki kwantar da hankalinki,ni nasan ba abunda kike tunani bane..Yanzun kam ko da ma ace abunda kike zargin ne ai na fad'a miki abunda za muyi,daga zara'n mun b'atar da ita shi kenanfa babu wanda zai zargemu ko ya kawo tunanin mune muka aikata wani abu akanta.." Cikin gamsuwa Adda'n ta girgiza mata kai "Tabbas wannan shawaran naki yayi,amma bari kiga yanzun'ma ni masarauta nake son zuwa dan na jiyo wani labari ina son ko da ace bamu yi nasara a baya ba a yanzun muyi nasaran shiga tsakaninsu ta inda zamu samu burin da muka d'auki tsawon shekaru muna dako ya cika.." Thumbs up ladidi tama Adda cikin kurantawa had'e da kambamawa ta fara hura mata kai,ai kuwa take Adda ta fara jin kanta yana k'ara girma kai kace dutsen Dala ne,wanda daga haka ne ita Adda'n tayi mata bankwana ta fice a cikin gidan tana kama hanyar masarauta. ^^^^^ 'Dan k'aramin meeting maimartaba ya kira wanda duka² bayan Hajiya sai shi kansa,Umma Fulani,Abba GALADIMA sai kuma Ummi'n YASEER,kasancewar meeting d'in na sirri yasa basa so ace adadinsu ya wuce hakan,maimartaba ne ya fara magana yayin da duka suka yi shiru suna sauraren dalilin daya tara su a gurin,maganar cike da zallan mulke yake cewa "Kamar yadda kuka sani wannan taron namu bawai taro ne da yake kama da sauran zaman da muka yi a baya ba,nasan dai duka ko ban fad'a ba wasu cikinmu zasu iya fahimtar dalilin faruwar hakan...Alal hak'ik'a wannan zaman da muka yi a nan a kuma wannan lokacin ina son shaida muku ba akan komai muka yi shi ba,face akan yawan matsalolin da muke fuskata a wannan gidan..Wanda mu kanmu idan muka tsaya muka yi duba babu lallai ace munyi saurin gano dalili ko mak'asudin da yasa hakan ke yawan faruwa,sai dai bisa mizanin hankali idan muka yi duba da abubuwan dake kan faruwa a yanzun dama wad'anda suka faru a baya wannan abubuwan suna b'ullowa ne daga wasu mutane wanda mu kanmu bamu san ko su waye ba,haka suna faruwa ne ba don komai ba sai don ana so aga bayan wannan gida namu,amma koma su waye idan har sunfi k'arfin saninmu basu wuce da sanin ubangiji ba,kuma mu gareshi kuma mik'a dukkan wasu lamuranmu,haka kuma a kullum gurinsa ne kad'ai muke kai kukan mu tare da neman mafita a gareshi..mun sani wayo,dabara ko K'arfin mu duka ciki bai isa ya bamu abunda muke nema ba..da wannan ne muke fatan Ubangiji yaci gaba da karemu daga sharrin masu sharri." "Ameen" duka suka amsa dan kowa yana da damuwa musamman akan lamarin gidan da lokaci bayan lokaci sai an samu wani abu ya faru,y'an maganganu aka d'anyi na d'an wani lokaci kafin Abba GALADIMA da tun zaman bai ce komai ba yayi gyaran murya ya fara magana shima "Tabbas wannan AL'AMARI akwai rud'ani a cikinsa,haka nan akwai abun dubawa akansa,sai dai mu a gurinmu babu wani da zamu d'aga muce muna zargin da sa hannunsa a cikin matsalar,sai dai addu'ar dai ita zamu ci gaba da yi,,haka nan ina rok'on alfarmar musamman akan matsalar yarona da mu sake jajircewa muna nema masa kariya daga mak'iya..!" Duka sun fahimci akan wanda yake maganar koda baiyi specifying ba,dan haka duk suka sake nutsuwa suna sauraren jawabin "Sannan maganata ta gaba,itama dai kan matsalar yarona ne,saboda haka idan na fad'i wata magana ba dai² ba ina fatan duk zakamin uzuri,dalili kuwa shi d'an adam ajizi ne.." Na'am suka yi da jawabin nasa,ba tare daya saurara ba ya sake nausawa cikin bayanin abunda ke ransa "A dai² wannan lokacin, ina so nayi amfani da wata y'ar dama da naga Ubangiji (S.W.T) ya bani,wanda a nawa hasashen da kuma tunanin nake ganin a yanzun tunda har Allah yasa kowa yana jin bazai iya amincewa ya bamu aure a gidansa ba,kan wani dalilinsu da har yau an kasa samun wanda zai same mu ya mana bayanin kai tsaye,nake ganin mai zai hana mu baza mu taru mu rufawa kanmu asiri ba..." Hajiya da itama dukkansu babu wanda ya tofa albarkar bakinsa tun zaman,idan aka d'auke maimartaba daya fara magana sai ko yanzun da Abba GALADIMA yake kan yin nasa jawabin,take ta yunk'ura tana tambayar Abba GALADIMA'N "Wane irin rufin asiri ne kake magana Aliyu..??" Jinjina kai yayi sannan ya kalli maimartaba da cewa "Tun daga lokacin da aka fara samun matsala game da maganar auren yaron nan nayi ta hasashen anya bazamu hak'ura da neman auren Yarinyar kowa ba,tunda har Allah (S.W.T) ya azurtamu da yaran nan ko da dai ba wai masu yawa bane Alhamdulillahil.!,tunda har muna da su naga dacewar nace mai zaisa mu baza mu tsakanin yaran namu ba tunda har muna da yadda za muyi mu nemawa kanmu maganin damuwar mu,amma yaya kuke gani..?? Ni wannan itace shawara ta,na tabbata dai Abir k'anwa ce a gurinsa babu yadda za'ayi idan har wani a waje ya guje shi saboda ciwon dake jikinsa ko wani aibu itama ta gujewa hakan,na tabbata bata da yadda za tayi dole ne ta zauna dashi ko da kuwa ace zai k'are rayuwarsa a haka haka nan shima kansa,shin yaya kuke ganin shawarata..??" Yayi maganar

Chapter 35 of 63