Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Bross ka samu kayi wanka yanzun kafin a shiga fada...Dan lokacin halartar maimartaba ya kusa.." Amsawa yayi yana zaunar da Umma'nsa a saman shimfid'a sannan ya kalleta da murmushi a fuskarsa "Ummata bari na shirya sai na dawo.." "To yazeed amma ka wanke wannan fatar taka da kyau...kaji ko..? Allah ya saka maka,yabi maka hakkinka.." 'Dan yak'e ya sake yi mata sannan suka fice suka nufi gefensu,tun daga shigarsu yake bin ko'ina da kallo tamkar wani bak'o,har sai da yaja yaseer ya sake masa magana sannan ya shiga wankan,ko shigar sa toilet en sai daya b'ata lokaci a ciki kafin ya samu ya fito,lokacin kuwa tuni har an fara zuwa ana kiransu dan tuni har maimartaba ya halarci fadar,sauri yayi ya shirya cikin wata d'anyar shadda data amsheshi,duk da irin ramar da yayi,sannan suka kamo hanya da niyyar zuwa gefen mahaifiyar tasa suci abinci kamar yadda ta labarta musu,dai² lokacin da suka fito daga gefen zasu je yiwa Umma'nsa sallama akan zasu fada tukun yanzun idan yaso bayan fitowarsu a can sai su zauna cin abincin tunda har an fara turo y'an aiken,si suka sake cin karo da wasu bayin akan suzo su sake kiran su,hakan tasa dole suka hak'ura da zuwa gefen Fulani suka nufi hanyar fada dan bin umarnin maimartaba. Lokacin da suka iske k'ofar fada da k'yar suka samu hanyar wucewa suka isa cikin fadar saboda yadda jama'a suka sake yin cikar kwari,baga mata ba baga maza ba,hatta da k'ananan yara suma ba'a barsu a baya ba.Sai da suka mik'a gaisuwa ga maimartaba sannan suka koma gefe suka zauna kusa da juna suna jiran jin yadda zaman zai kasance. Maimartaba ne yayiwa Matawalle umarnin dasu fara gabatar da abunda ya tarasu a gurin ba tare da b'ata lokaci ba,ko kafin Matawalle ya kai ga yin magana sai da suka yi y'an maganganu da TALBA kasancewar shi matsayin wanda Alkalai suke k'ark'ashinsa kuma ta hannunsa suke ganin Sarki,Shi kuma MATAWALLE Shine mai kula da aikin dukkan Alkalai haka yana iya yin hukunci idan har abun ya shafi masarauta,bayan Matawalle ya mik'e yayi gaisuwa,sannan ya fara jawabin abunda ya tarasu,kamar yadda yayi jawabi a wad'ancan shekarun da suka gabata a ranar da aka kawo k'arar ta yarima yazeed,sai dai na yau ya bambanta dana wancan ranar kasancewar wannan ranar shaidu suke niyyar gabatarwa da zasu wanke yariman,bayan nan kuma yasa a shigo da Ladidi da Aisha da suma tuni aka zo da su cikin gidan. "Kamar yadda wannan fada ta shaida,kuma kamar yadda ya al'ummah ta shaida,a shekaru biyar da suka gabata,wannan Yarinya mai suna Aisha ta shigar da k'ara a wannan kotu ta fada da akan tana k'arar yarima yazeed bin abu yazeed,bisa laifin da suka yi ik'irarin da cewar yariman ya aikata na keta mata haddi kamar yadda suka ambatawa kotu a shekarun da suka gabata,sai dai bisa ga bincike da wasu a cikin wannan masarauta suka gabatar akan wannan case da idan fada ta bada dama zamu gabatar da shaidun da muka samu da suke kore tabbatatuwa akan cewa lallai ne yariman wannan masarauta bai aikata abunda aka zargeshi da aikatawa ba,hasalima a wannan ranar da abun ya faru yarima yana tare da mahaifiyarsa a wannan dare,haka kuma bayani gamsashshe ya riskemu kan cewa bayan barinsa a gefen Fulani suna tare da d'an uwansa kuma abokinsa wato YASEER kasancewar kamar yadda aka sani duk dare tare suke barci haka duk wasu al'amura nasuma k'asan tare suke gabatar dasu....." Sai da yad'an tsagaita sannan yaci gaba da magana "Sai dai abun tambaya a nan da kuma d'aure kan shi ne...A lokacin da ake maganar wannan AL'AMARI ya faru,Shin iya yarima yazeed ne ya aikata ko kuwa duka su biyu ne...? Idan kuwa har iya shi yarima ne shi kad'ai to a wannan lokacin shin shi YASEER yana ina hakan ta faru..? Ko kuwa dai ana nufin ace yariman ya fita daga gida ne ba tare da sanin YASEER ba haka ba tare da sanin wasu a cikin masu tsaron wannan masarauta ba,duk da kasancewar kowa yasani tun tasowarsu duk wanda ya sansu tare ya sansu...Ina neman afuwar wannan fada bisa wad'annan tambayoyi dana gabatar,amma idan har fada ta bada izini muna da buk'atar mu samu amsoshin wad'annan tambayoyi daga jama'a sannan daga su Kansu wad'anda suka kawo wannan k'ara..." Jinjina kai maimartaba yayi zuciyarsa cike da farin cikin wannan AL'AMARI duk da a baya sam baiyi tunani akan matsalar ba,haka kwata² baiyi tsammanin abunda ake zargin d'an nasa da aikatawar bai faru ba,sai yanzun daya fara jin yadda matawalle na bud'e bayanai,haka sai yanzun ne ya fara jin inama tun kafin wannan lokacin ya bada damar ayi binciken kamar yadda Matawalle ya nemi izinin daga gare shi,haka ko Mahaifiyar yazeed zuwa kan K'aninsa GALADIMA,WAMBAI dama Wazirinsa duk sai da suka same shi da maganar amma yak'i sauraren su,haka har zuwa kan y'an majalisarsa kusan babu wanda baiyi maganar ba,amma duka ya share su saboda a lokacin yana kan dokin zuciya na mugun Fushin da yayi da yariman. Shiru fada ta d'auka babu amsa,koda ganin haka sai Matawalle yayi d'an murmushi sannan yaci gaba "Ran maimartaba ya dad'e ubangiji ya k'ara tsawon rai yaja kwana,wannan shirun da al'ummarmu suka yi ya isa ya sake tabbatarwa da lallai nefa yarima bazai tab'a iya aikata abunda ake magana ba,idan kuwa har an samu wanda ya yarda da cewa ya aikata en to muna buk'ata daya hallara a gaban fada domin ya mana bayanin da zai gamsar damu akan faruwar hakan.." Nan ma shirun dai aka sake yi,babu wanda ya iya koda tari bare a samu wanda zaizo gaban fadar ya fad'i abunda ake buk'ata,ko da ganin haka sai yasa Maimartaba ya bashi damar ci gaba "Ina fata wannan abu daya faru a gaban fada zai zama shaida ta farko ga wannan laifi da ake ik'irarin yarima ya aikata..." Bayan shud'ewar wasu y'an min tuna,Matawalle ya sake kallon al'ummar fada cike da k'warin guiwa yana cewa "Idan har wannan fada mai alfarma ta bada izini ina son gabatar mata da shaida ta gaba,wato Aisha a matsayinta na wacce al'amarin ya faru akanta,sannan ina son yi mata tambayoyi.." Kafin ya gama magana tuni har an kawo Aishar gaban fada,duk wanda ya kalleta a wannan lokacin tsaf zai iya gano rashin gaskiyar dake tattare da ita,jikin ta duk sai tsuma yake musamman yadda taga idanun gaba d'aya al'umma akanta,kuma kowa su kad'ai yake saurare yaji me Matawalle zai ce sannan itan wace amsa zata bayar..? Irin kallon da taga Matawalle yayi mata fuskar nan babu alamun wasa aciki tuni ta dad'a firgita "Aisha muna so yanzun ki yiwa fada bayanin abunda ya faru a waccan ranar..." Shiru tayi ta kasa magana saboda tsabar firgicin dake tattare da ita,a hankali ta juya ta kalli Ladidi idanunta na tsatstsafo da ruwan hawayen da ita kad'ai tasan ma'anarsu,jin shirun nata yana neman yin yawa yasa Matawalle sake maimaita mata tambayar daya mata,duk da yayi hakan ne dan kawai ya tabbatar da ta fad'i gaskiya.Cike da in-ina ta fara magana tana yi tana tsayawa tana kuma kallon Ladidi,hakan yasa Matawalle yin magana "Aisha so muke ki bud'e baki sannan kiyi magana a nutse saboda nan a gaban fada kike kuma ita fada ki sani ba'a mata k'arya..Muna fatan zaki kiyaye harshenki da fad'in abunda yake ba daidaiba.." Hawayen daya ziraro mata ta goge sannan ta fara da fad'in "Yallab'ai ina neman afuwar fada amma ni babu abunda na sani game da abunda ake magana akansa.." Girgiza kai Matawalle yayi kafin yace "Shin kina nufin baki sani bane..? Ko kuwa kina son nunawa fada ke bama ki fahimci abunda ake magana akansa ba..?" "A'a Yallab'ai ni ina magana ne akan shaidan da ake magana.." "Toh..! Aisha ko zaki iya yiwa fada cikakken bayani akan abunda kike nufi,dan ina ganin dukanmu nan bamu fahimci abunda kike nufi ba.." "Ehh! Yallab'ai zan iya...Maganar da nake anan Yallab'ai shi ne,wannan abu daya faru dani shekarun da suka gabata babu k'arya a cikinsa,haka AL'AMARIN yake,duk wani abu da muka fad'a a wancan lokacin haka yake..." 'Dagowa yarima yazeed yayi ya kalli Yaseer, koda suka had'a ido sai Yaseer en ya masa alama da kada ya damu komai zai zama dai²,badan ya gamsu ba ya sake maida hankalinsa gaban fada don jin mai Matawalle zai fad'a shi kuma,nan ko ya tsinto Matawallen yana fad'in "Haka ne Aisha...Idan har ban manta ba kuma kema ina fatan baki manta ba,haka zalika idan al'ummar da suke sauraren mu basu manta ba,a waccan ranarma irin abunda kika fad'a kenan ko..?" "K'warai kuwa Yallab'ai haka ne..." "Shin har yanzun kina kan bakar ki akan yarima ya aikata miki hakan ko kuwa zaki chanja maganar ki kafin na bayyana wani sirri da baki san da shi ba,wanda kuma ke en dama mahaifiyarki kuka jima kuna b'oyewa..?" "A'a Yallab'ai babu abunda zan fad'a.." "Kin tabbata babu wani abu da zaki chanja ko ki k'ara,ma'ana kina nan kan abunda kika fad'a.. Ko da bayan bayyana wannan gaskiyar da nake fad'a..?" "Eehh! Yallab'ai babu.." Sai da suka yi haka da ita har sau uku tana tabbatar masa itafa tana nan kan k'udurinta kuma babu wani abu da zata chanja cikin maganar ta,nan take Matawalle ya juya ga Maimartaba da sauran al'ummah yana fad'in "Hak'ik'a wannan abu da Aisha ta fad'a ba gaskiya bane ya maimartaba.." Hannunsa ya d'ago da yake d'auke da wata y'ar k'aramara recorder yana cewa "Wannan na'ura dake d'auke a hannuna ya maimartaba d'auke take da shaidar sak'on murya na wannan Yarinya Aisha a inda sukayi wata maganar sirri da d'aya daga cikin masu binciken suka gabatar,ina neman izini da idan har maimartaba ya bada dama,kuma fada ta bada dama ina so yanzun a gabato mana da speaker dan sanyawa kotun fada shaidar da muke d'auke da ita a cikin wannan sak'on murya da muka samu,wacce muke ganin saurarenta kad'ai zai iya gamsar da fada dama ilahirin al'ummar data halarci wannan guri..." Cikin y'an mintuna tuni har an kawo k'atuwar speaker en da zata wadaci gurin,nan aka jona y'ar na'urar da Matawalle ya saka memory en daya d'ora voice recording en na Aisha,sannan akayi playing nasa,nan take muryar Aisha ta soma amsa kuwwa a cikin fadar da tayi tsit kowa na son shaida abunda zaiji daga sak'on muryoyin,cikin sheshshek'ar kuka take fad'in _"Dan Allah jeeddah ki dakata kafin ki shiga muyi magana,wollahi akwai wani muhimmin sak'o dana zo na sanar dake a yanzun..."_ Jin haka yasa jama'a sake nutsuwa suna sauraren maganar da take fitowa daga bakin ita kanta jeeddan...Duk yadda suka yi da jeeddah da kuma ita Aishar babu abunda recording en bai bayyana ba har zuwa k'arshen maganar tasu inda jeeddah ke kwantar mata da hankali bisa abunda ta fad'a mata na abunda zai iya faruwa da ita idan har aka san ta bayyana hakan,ana zuwa nan Matawalle ya tsayar da abun sannan ya juya ga ita Aishar fuskarsa d'auke da wani irin murmushi mai cike da nuna nasarar dake tattare da shaidar daya gabatar,nan ya sake kallon al'ummah da sai a lokacin ne suka samu bakin magana kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan matsalar tare da yiwa Ladidi da Aisha tofin ala tsine bisa ga wannan gagarumar k'arya da suka shirga a gaban fada,sai da sa jama'a suka yi shiru sannan yaci gaba "Aisha....! Shin kin saurari wannan sak'on..?" "Ehh! Yallab'ai na saurara.." Murya na cracking cike da rashin gaskiya ta amsa masa "Shin ko kina da wani abun fad'a game da hakan..?? Ina nufin ko zaki iya gane wannan muryar Waye...??" Nanma muryarta na kyarma ta furta "Ehh! Yallab'ai.." "To Aisha muna sauraronki muna kuma buk'atar ki fad'awa fada shin wannan muryar ta waye..? Sannan kuma da waye kika san kinyi wannan maganar.A kuma ina hakan ta faru.?" "Muryata ce Yallab'ai.. Kuma bada kowa muka yi wannan maganar ba face da jeeddah.." Girgiza kai Matawalle ya sake yi kafin ya furta "Yanzun kin tabbatar wannan en muryarki ce..? Kuma ako ina aka tambayeki zaki iya fad'ar cewar tak'i ce ba tare da tunanin komai ba..?" Shiru ne ya biyo baya dan gaba d'aya Aisha ta gama tsinkewa da lamarin,kamar yadda bata zata ba haka ko kad'an tunanin ta bai kawo mata cewa jeeddah zata iya recording maganar tasu ba,gumi ne mai tsanani yake ta keto mata saboda yadda gaba d'aya aka d'aureta da jijiyoyinta,ji take inama zata samu hanya da ko kad'an babu abunda zai hana bata take k'afafunta a gurin ba,amma ina duk inda ta wulga idanunta dakaru ne na fada haka jami'an tsaro da Matawalle ya kawo da suka sake bawa fadar kariya ta yadda duk k'ok'arin mutum bai isa ya nemi tserewa ba. Nan Matawalle yaci gaba da magana "Bisa ga wannan tak'aitattun shaidu da suka gabata a gaban fada da kuma al'ummah muke fatan wannan fada da kuma kotu zasu saurari hukunci da za'a gabatar ga wad'annan azzaluman mutane,bisa cutarwa da suka yi ga yarima na d'ora masa laifin da bai aikata ba,da kuma wannan ne kotu zata yi amfani wajen tsarkake wannan bawan Allah dan ya fita a cikin zargin da aka lik'a masa.." Komawa Matawalle yayi ya zauna a kusa da TALBA suka d'anyi magana kafin ya gabatar da hukuncin da za'a yankewa su Aisha kamar yadda shari'a da addini ya tanada,zuwa wasu y'an mintuna kowa ya d'anyi taking breath sannan Matawalle ya sake mik'ewa don zartar da hukuncin da daga shi,shi kenan zaman yazo k'arshe. Bayan tabbatarwa da aka samu daga bakin ita Aishar da fada ta saurara da kuma gabatar da shaidu wanda duka suka gudana a gaban idanun dubban al'ummah,tashin Matawalle a dai² lokacin yasa gaba d'aya surutan dake tashi a fadar ya dakata kowa yayi shiru yana jiran jin irin hukuncin da za'a yanke,dan hatta ni kaina shiru nayi na zubawa Matawalle ido ina sauraren naji mai zai ce,nan kuwa ya fara da yin sallama sannan ya d'ora da fadin "Bisa ga shaidu da muka shaida,fada ta shaida kuma al'ummah ma ta shaida gaba d'aya muke fatan al'ummah gaba d'aya zasu sake saurarawa don jin hukuncin da addini da kuma shari'a ta tanada ga wad'annan mutane..." Shiru ya d'an sake yi na wasu y'an dak'iku kafin yaci gaba "Da farko zamu fara da gabatar da hukuncin da addini ya tanada ga duk wani wanda aka samu da laifin K'AZAFI ga wani mutum....Bisa ga hukunci daya tabbata daga al'qur'ani mai girma,ya tabbatar cewa ga duk wani da aka samu da irin wannan laifin nayin k'azafi,tofa hukuncin sa ya ta'allak'a ne kamar yadda Allah mad'aukakin sarki ya fad'a a cikin suratun-nur,ayata hud'u zuwa ta biyar inda Allah mad'aukaki yake cewa:"WALLAZIIYNA YARMUNAL MUHSANATI THUMMA LAM YA'ATUU BI ARBA'ATI SHUHADA'A FAJLIDUHUM THAMANINA JALDATAN WALA TAK'BALUU LAHUM SHAHADATAN ABADA,WA'ULAA'IKA HUMUL FASIIK'UUN..ILLALLAZIIYNA TABUU MIN BA'ADI ZALIKA WA-ASLAHU FA'INNALLAHA GAFURUR-RAHIIYM..." _Ma'ana "Kuma wad'anda ke jifar mata masu kamun kai,sa'annan kuma ba su je da shaidu hud'u ba to ku yi musu bulala,bulala tamanin,kuma kada ku karb'i wata shaida tasu, har abada.Hak'ik'a wad'ancan su ne fasik'ai...Sai dai ga wad'anda suka tuba daga bayan wannan,kuma suka gyaru,to lallai ne Allah mai gafara ne,kuma mai jin k'ai..."_ "Bisa ga saukar wad'annan ayoyi hakan ya tabbatar da cewa duk wani wanda aka kama da laifin k'azafi ga wani bawa salihi,tofa lallai ne za'ayi masa bulala tamanin domin tsarkake shi da kuma kub'utar da shi daga halaka,a saboda haka ne suma wad'annan bayin Allah za'a gabatar musu da hukuncin bulala tamanin kamar yadda nassi ya tabbatar,kuma a gaban al'ummah dan su zama shaida akan cewar an zantar da hukuncin kamar yadda ubangiji yayi umarni.................. _Hhhhhh! Jama'a kada kuso kuga idon LADIDI da AISHA dan ni dai da nake gurin tsabar ganin yadda suka koma har ban san lokacin da hawayen mugunta suka fara biyo fuskata ba......😂😂😂_ #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ _Alhamdulillah..! Am stepping toward shifa'a,am always grateful for getting u as my F³ (Family,Friends,Fans) thanks all for d prayers..._ ___________________ *Pg 10.* ^^^^^^^^ Su Ladidi ido yayi tsilli² jin yadda aka ambaci bulala tamanin,kafin kuce kobo tuni ta zube a k'asa ta fara rusa kuka mai tsanani, wannan yasa gaba d'aya hankalin jama'ar fada ya koma kanta,nan wasu ciki suka shiga zaginta da jifanta da bak'ak'en maganganu na ita ta janyo faruwar hakan,kuma son zuciyarta shi yayi mata jagoranci ga aikata hakan,ga fadawa kuwa nan suka shiga mata tsawar ta shiga nutsuwarta sannan ta san a inda take wannan ihun kafin jikinta ya tsamama,shiru tayi tana damk'e bakinta idanun nan kuwa tamkar an matsa agwaluma. Shiru akayi umarnin mutane suyi a gama yanke hukunci kafin a tashi a zaman fadar,nan mutane kowa ya sake saurarawa yana jiran yaji me zai sake faruwa dasu Ladidi,Matawalle ne ya sake mik'ewa sa'annan yaci gaba da magana "Kamar yadda muka sanar da jama'ah hukuncin da addini ya tabbatar da za'a gabatar wa dasu Ladidin nan bada jimawa ba in sha Allah,bayan an zartar musu da wannan hukuncin kuma akwai k'arin hukunci da zasu karb'a wanda wannan kotu ta bada izinin ayi musu,abisa la'akari da irin lokacin da aka b'atawa yarima,haka nan b'ata masa suna da akayi bisa hakan,sannan ga tsare shi da akayi abisa laifin da bai aikata ba,wannan kotu ta zartarwa da wad'annan mutane hukunci kamar haka:Na farko zasu biya tara ta naira dubu d'ari biyar ga shi yariman,sa'annan na biyu kuma za'a tsare su a gidan yari na tsawon watanni shida tare da basu horo mai tsanani,ba tare da bada damar yin bailing nasu ba,sannan daga wannan lokaci wannan kotu ta wanke yarima akan laifin da aka zarge shi daya aikata,a bisa samun sa da akayi bashi da hannu a cikin wannan matsala,wannan kotu mai alfarma tana k'ara bashi hak'urin b'ata masa lokaci da suna da akayi,sa'annan kotun tayi watsi da wannan k'ara saboda rashin ingancinta,kuma ta gargad'in duk wata kotu da karb'ar case makamancin wannan har sai an tabbatar da mutum ya aikata kafin a yanke masa hukunci..." Sai daya d'an saurara sannan yaci gaba "Da wannan hukuncin muka kawo k'arshen wannan shari'a,muna fatan wannan hukunci zai zama izina ga y'an baya dama duk wani mai sha'awar aikata kwatankwacin wannan laifi,haka muna fatan wannan zai zama k'alubale gareku al'ummah baki d'aya....." Ihun da Ladidi taci gaba da zundumawa yasa gaba d'aya hankalin jama'a ya sake komawa kanta nan mutane suka ci gaba da zund'enta suna aibantata saboda munanan halayenta da suka bayyana a icon duniya,nan akayi addu'ah sarki ya sallami kowa,daga nan kuma aka tattara su Ladidi ita da Aisha akayi waje dasu harabar gidan inda ake hukunci dan gabatar musu da nasu hukuncin kamar yadda aka tabbatar,ga Yaseer da yazeed kuwa ana kammala yanke hukunci bayan zaman ya tashi nan suka fito daga fada da niyyan komawa gida,Aifa nan jama'a suka yi ta zuwa suna masa jajen abunda ya faru da Allah ya tsare saboda kasancewar sa tun asali mutum ne shi da bamai yawan shiga abubuwan daba nasa ba kuma ba'a sashi ba,sun jima suna karb'ar jaje daga mutane daban²,sai da k'yar suka samu hanya suka bar wajen suka nufi cikin gida gefen mahaifiyarsa,dan su kam dama tun kafin a tashi a fada suka k'udirce babu abunda zai kaisu gurin hukuncin tunda Allah ya bayyana gaskiya su wannan ma ya ishesu abun godiya ga Allah. Suna shigowa gefen na Fulani suka isketa ta idar da salatud-dhuha tana addu'ah,suna shigowa suka kalli juna suka yi mata murmushi, saurin idar da addu'o'in tayi sannan ta juyo garesu har lokacin yanayin damuwar da take ciki bai barta ba "Alhamdulillah..! Alaa kulli haliin..! Har kun dawo..??" "Ehh! Ummah mun dawo..sai gajiyar zama da muka sha.." "Alhamdulillah..! Tunda anyi nasara hakan ba wani abu bane..yanzun dai ku samu kuci abinci tunda Allah ya dawo da ku.." Maimakon su nufi abincin da tasa aka shirya musu kamar yadda take musu izini,saima taga YAZEED ya koma ya kwanta yana rufe idanu ya musu shiru,juyawa Fulani tayi ta kalleshi kafin tayi magana "Yazeed ka tashi ka samu kaci abinci saika kwanta ko..?" A hankali ya bud'e idanunsa yayi mata murmushi "Ummah ki bari na huta tuku,bama jin zan iya aiwatar da wani abu yanzun..." "Amma YAZEED ai daka samu kaci wani abu saika kwanta en,nima ba hanaka hutawan nayi ba..amma rabonka da cin abincin gida ka d'auki tsawon lokaci,saboda haka nake son ka fara cin abincin saika kwanta.." Yadda yayi shiru ya zuba mata ido kamar wanda baya cikin nutsuwar sa yasa ta yin magana,amma sai taji yayi shiru baice komai ba har sai data sake yin magana da d'an d'aga murya,hawayen da yake neman zubo masa yayi saurin mayarwa fuskarsa tana rikid'ewa zuwa yanayin damuwa,saurin tashi yayi ya nufi hanyar fita,da sauri ta kalleshi ta kuma juya ta kalli YASEER da shima ya bishi da kallo,ko kafin Fulani tayi magana tuni har ya fice da sauri,maganar ta mayar kan Yaseer cikin yanayin kid'ima "Yaseer maza kayi saurin binsa bamu san ina zai nufa ba a yadda ya fitan nan cikin damuwa,dan Allah kayi saurin binsa kada wani abu ya faru da shi..." Girgiza kai yayi sannan ya mik'e cikin hanzari yabi bayansa,b'angarensu ya nufa direct nan shima yaseer en ya iske shi har ya kwanta saman kujera idanunsa a rufe,ganin alamun yana cikin yanayin damuwa,sai yasa yaseer en k'arasowa cikin sanyin jiki,a kusa da shi ya zauna yana dafa shi,ba tare daya bud'e idoba ya furta "Dan Allah Yaseer ka kyaleni zuwa wasu lokaci,ina buk'atar na samu hutu da nutsuwar zuciya.." Cikin sanyi Yaseer ya girgiza kai da fad'in "Okay..! Amma dai kayi hak'uri kada ka sa wani abu a ranka har yazo ya haifar maka da wani ciwon..." Daga haka bai sake cewa komai ba ya mik'e yabar kusa dashi,can ya koma gefe ya zauna yana y'an tunane²nsa shima.... ^^^^^ *K'OFAR FADA* Yadda harabar gurin ya sake cika da al'ummah kai kace mutanen k'asar sin aka aro,wad'anda da dama basu samu damar halatar cikin fada ba a d'azun yanzun kam sun samu damar isowa dan ganewa idanusu abunda zai wakana,can daga sama cikin tanti sarki ne zaune sai manyan y'an majalisarsa,nan aka sake gabato dasu Aisha gaba kana mabugi ya halarto da zabgegiyar dorinarsa,ai koda Ladidi taga k'osashshiyar bulalar da aka d'auko nan take idanunta suka sake raina fata,jikinta ya sake d'aukan tsuma,in ina ta shiga yi tana magana cikin tsoro da fad'in "Yallab'ai dan Allah ayimin aikin gafara...amma wollahi zan fad'i gaskiya..."

Chapter 8 of 63