iya amfanawa rayuwarta..?? Ai ni wollahi nama ga k'ok'arin ta data iya hak'uri da juriyar watanni biyar,Allah ya sani babu yadda za'ayi rayuwa ta yiwu kuma tayi kyau tsakanin mutum mai lafiya da kuma *GUNKI........."*
*Bola'i...! Wai shin fan's dawa Hajiya Suwaiba take ne...? Waye ta kira da GUNKI..??* 😱😱😱
*Sai kunyi hak'uri dani,har yanzun muna cikin wani yanayi ne na rashin wutar NEPA,amma in sha Allah komai ya zo k'arshe dan a ko wane irin yanayi zaku ga na dawo kamar da,nd sai kunyi hak'uri da turancin nawa coz na y'an koyo ne...*🙈🙈
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.* 😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE.*
_On this birthday i wish that u have a young life by living honestly,eating slowly and learning to lie about ur age.😜Happy Birthday in advance sisters.!🎂🎁_
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 8.*
^^^^^^^^
Kalmar data fito a bakin Hajiya Suwaiba ba k'aramin bawa ilahirin mutanen parlour'n mamaki tayi ba musamman ma Umma Fulani who feels Hajiya Suwaiba's words like descent of fluid steel,yau wai ita ce har ake jifan d'an cikinta da irin wannan kakkausar maganar kuma tayi shiru ta kasa cewa komai duk da yadda taji maganar a ranta,sai dai ko kafin ta kaiga gama wannan tunanin har tayi magana tuni Ummi ta amsa maganar
"Hajiya Suwaiba waye kike kira da *GUNKI..??*
"Yo akwai wanda sunan yafi dacewa da shi ne sama da wanda aka had'a yarinyata da shi..?? Fisabilillah! Ai kunsan bashi da cikakkiyar lafiya amma kuka gagara sanar damu gaskiya saboda tsabar cuta,kuma a rasa wadda za'a had'a da shi sai yarinyata,duk iya irin wannan abun kuma bai isa ba sai azo a nemi k'arawa da makircin ta jirashi har na tsawon shekara guda..??"
Tsawa Hajiya tayi mata saboda yadda taga zuba mata idon da suka yi ya kasa sawa tayi shiru,irin kwarjinin dake tattare da ita shi yasa ta yin shirun da bata yi niyya ba,ran Hajiya a lokacin idan akace yayi dubu wajen b'aci tofa tabbas babu musu,ga Abba Matawalle kuwa a dai² wannan lokacin kunya ce tayi masa wani irin sauka duka ta lullub'e shi saboda irin maganganun da Hajiya Suwaiba ta furta ji yake kamar ya tsaga k'asa ya shige dan yadda yake jin kunya da nauyin wad'annan bayin Allah,kaf babu wanda baiji daban ba a gaba d'aya kalamanta sai dai babu wanda yayi mata magana,nan take Maimartaba dake zaune tun farko baiyi magana ba ya kalli Yarima kana ya juya ya kalli Sajida maganarsa cike da mulki ya ce
"Sajida shin kina ganin zaki iya zama da d'an uwanki duk da wannan larurar da aka tabbatar yana tare da shi..??"
Duk da bata d'ago ba bare ta kalli maimartaba sai da taji shakkar amsawa dan yadda nuryarsa kad'ai ta cika ido da zuciyar ta da kwarjini,kusan sau uku yana maimaita tambayar amma ko guda d'aya ta kasa amsawa sai kai da take sake sunkuyarwa a duk lokacin da yayi maganar,duk abunda ke wakana akan idon Abba Matawalle ne dan yana ankare da yadda Hajiya Suwaiba wacce tun d'azun take girgizawa Sajida kai tana kuma warning d'inta da ido akan kada ta kuskure ta amsa abunda ake tambayarta,wannan dalilin yasa Matawallen jin wani irin takaici da haushin abunda Hajiya Suwaibar keyi sai dai ya zuba mata ido ne yaga ko zata yi hankali ta kuma yi masa kara,b'angaren Yarima Maimartaba ya dawo da tambayarsa inda yake cewa
"YAZEED..! Shin har yanzun kana son matarka,zaka iya ci gaba da zama da ita..Ko kuwa kana da wani uzurin..??"
Shi kansa kasa magana yayi dan yadda yake jin nauyin mahaifansa da nauyin abunda yake k'unshe a k'asan zuciyar sa,saima sake sunkuyar da kai da yayi tamkar mai d'aukan darasi,tab'a shi YASEER yayi yana masa alamar ya amsa amma ina gogan yayi kirim babu amsa (kamar dai sunan da hajiya Suwaiba ta rad'a masa..face smile:-),a hankali Abba Matawalle ya sauke ajiyar zuciya sai dai ko kafin ya k'arasa sauke numfashinsa tuni muryan Hajiya Suwaiba tayi masa kutse cikin lamarinsa
"Gaskiya harga nifa ina da abun cewa,tsakani da Allah idan har ba'a bani dama an fita hak'k'ina na uwa mahaifiya ba anyi ba dai² ba..!"
Kallonta kawai yayi yana girgiza kai cike da takaici ba tare da yayi magana ba,dan yadda takaicinta ya sa shi neman abun fad'a ya rasa,maganarta babu wanda bata bawa mamaki ba sai dai kowa ya adana hakan a ransa,ga maimartaba kuwa duk da yaji rashin dad'in kalamanta hakan bai hana shi yin magana ba
"Hajiya Suwaiba shin kina da wani abun fad'a ne..??"
Tun kafinma ya k'arasa har ta karb'a masa
"K'warai kuwa ni nake da abubuwan fad'a tunda naga kowa ya rasa.."
Daman magana ya bata inda take ba tare da tsoron Allah ba ko kunyar wad'annan nayi nasa ta fara fayyace duk abunda ke k'unshe a ranta
"Yanzun Fisabilillah! Tun farko da aka san yaron nan yana da larura ai bai kamata ma taso da batun za'a had'a auren nan ba,sai a bari idan ya samu lafiya duk ma abunda za'ayi ayi kufa duba zancen nan,amma saboda Allah sai bayan komai ya cab'e sannan ayi batun zama tsakanin wacce take lafiyayya da majinyaci..?? A gaskiya idan har a son raina ne kuma ana neman mafita nikam gara a raba auren nan shi yafi komai zama masalaha a garemu,in yaso a nema masa magani ko kuwa wannan fa itace magana ta domin Allah.."
"Shin abunda za ki iya cewa kenan..??"
Abba GALADIMA ya tambaya
"K'warai kam wannan itace magana ta,kuma nasan ko ita yarinyar nan shirun da tayi ba yana nufin zata iya zama da mutumin da bazai iya morarawa rayuwarta wani abu bane..!"
Babu wanda ya iya yin sharhi akan maganarta sai Abba Matawalle da ya kalleta ya zabga maa harara cike da haushinta yace
"GALADIMA nifa ina ganin tun farko munyi kuskure.."
Kallonsa duka parlour'n suka yi jin wannan furucin da yayi wanda yasa wasu da dama a ciki har sun fara zaton ko dai shima d'in yabi bayan maganar Hajiya Suwaiba,fuskar Abba GALADIMA da mamaki ya kalleshi yana tambaya
"Kuskure wane iri kenan Matawalle..??"
Ajiyar zuciya yayi yana d'auke kansa daga kallon Hajiya Suwaiba da yakewa warning da ido akan kada ya sake jin bakinta a zancen da ake
"Yo nace munyi kuskure mana,ai duk abunda za'a sa mata aciki lallaine akwai kuskure acikinsa,shi yasa tun farko da nasan irin wannan maganar za ayi dana bada shawaran muyita a tsakaninmu idan yaso su d'in a sanar da su daga baya.."
"A'a Matawalle gara dai da akayi hakan kaga kowa an fita hak'k'insa ai yafi,ba wai ace mun yanke hukunci tsakaninmu ba.."
"A to.! Ai kai da yake kasan gaskiya kaji abunda ka fad'a,gara abawa kowa hak'k'insa shi ne batu.."
Cike da hasala Abba Matawalle ya kalli sashen da matarsa take
"Hajiya Suwaiba wollahi kada ki kuskura na sake jin bakinki akan maganar nan,shin babu wani mai baki ne anan sai ke kad'ai..?? Kowa yayi shiru yana jiran yaji me za'a zartar amma ke tun d'azun kin hana mu neman mafitan da duka ita ta had'a mu anan,wannan wace irin rayuwa ce ne haka..??"
"Nifa ba wani abu yasa nayi maganar nan ba face akan y'ancin yarinyata tsakani da Allah ni kam nafi son a raba auren nan,kuma itama kanta nasan zata fi son hakan saboda dama ce zata samu da zata sa ta auri wanda take so.."
Cikin mamakin kalamanta uasa Hajiya ta kalleta tana maimaita abunda ta fad'a
"Ta auri wanda take so..?? Shin dama Sajida tana da wani saurayin ne amma baku fad'a ba aka aurar da ita ga YAZEEDU..??"
Shiru parlour'n ya d'auka ba tare da an samu mai bawa Hajiya amsa ba,ranta a b'ace taci gaba da magana
"Shi kenan yanzun naji duk abunda kuka tattauna kuma in sha Allah ba za muyi abunda zai zo ya lalata zumuncin mu ba,zamu bada dama don a fita hak'k'in kowa kada daga baya azo ana k'ananun maganganu."
Sajida ta kalla kafin taja numfashi da cewa
"Sajida nasan kinji duk abunda ake magana akai ko..?? To ina so ki tabbatar mana shin zaki iya hak'uri ki zauna da YAZEEDU har zuwa nan da shekara d'ayan ko kuwa..??"
Sunkuyar da kai tayi ta kasa amsawa
"Ke sakarya ki d'aga kai kiyi magana kada ki cuci kanki.."
Hajiya Suwaiba tayi furucin cike da masifa
"A'a..!"
Wannan kalmar data fito a bakin Sajida ba k'aramin jefa su ta sake yi a commotions ba musamman ma Abba Matawalle,sake kallonta Hajiya tayi da kyau kafin ta ce
"Me kike nufi da A'a..Ina so kiyi magana yadda kowa zai fahimci abunda kike nufi."
"A'a Hajiya..Na hak'ura da auren..!"
"Kina nufin kema kinfi son a raba auren naku..??"
Hajiya ta tambayeta,da kai ta amsa mata alamun hakan ne,jinjina kai kawai Hajiyar tayi cike da mamaki da kuma takaici,ba ita kad'ai ba hatta da su Abba GALADIMA,Abba Matawalle mahaifinta,dama su Ummi babu wanda baiji mamaki ba,a b'angaren Yarima hamdala yayi ga Allah (S.W.T) dan dama haka yake so,haka nan zamu iya cewa yama fi Hajiya Suwaiba farin ciki da maganar ta zo a haka,kunya a gurin Abba Matawalle kuwa a lokacin data tabbatar musu tafi so a raba auren ko wata macen albarka,sun d'auki lokaci mai tsayi ana ta muhawara akan maganar raba auren kafin Hajiya tasa aka kawo abun takarda da alk'alami nan take taa umarci Yarima daya rubuta takardar kuma ta hire shi da kada yayi abunda ya sab'awa addini,saki d'aya tak ya rubuta kana ya mik'awa YASEER ya karantawa iyayen kafin aka mik'a musu,Hajiya Suwaiba ta karb'a tana mai jin farin ciki duk da dai ba haka ta so ba,haka nan a saman fuskarta ma sai data kasa b'oye haan,daga haka taron ya tashi Abba Matawalle sai hak'uri yake ta bayarwa,babu wanda yaji haushin sa duka ciki saboda ba k'aramin namijin k'ok'ari ba na ganin cewa an samu masalaha,kuma tabbas ba don Hajiya Suwaiba na nan ba wacce itace ta assasa hura wutar har ya kasance a k'arshe sai da aka rabu da babu abunda zai hana bai yiwa Sajida umarnin taci gaba da zama a gidan ba a kuma matsayin matar Yariman,daga haka kowa yayi nasa gidan sai dai duk da haka rayuka basu yi dad'i ba..
A b'angaren Abba Matawalle kuwa lokacin da ya isa gida kasancewar ba tare suka koma dasu Sajida ba,nan ya iske su a parlor Hajiya Suwaiba sai hud'uba take sake yi mata suna ta shewa abunsa,shigowarsa ce tasa su kintsuwa nan ya nemi guri ya zauna yana binsu da kallon mamaki dan dukansu ba k'aramin kunyata shi suka yiba a yau,ya d'auki lokaci yana kallonsu kafin yayi magana
"Sajida a yau nayi bak'in cikin kasancewar ki y'ar dana haifa a dalilin k'in yimin biyayya da kika yi,wannan ya gwadawa duniya cewa kinfi k'arfi na,ban kuma isa na baki umarni ki biba sai abunda uwarki tasa ki shi za kiyi,sai dai abunda nake son shaida muku yanzun shi ne tunda har ni kuka kunyata a idon y'an uwana ku sani,dama wannan gidan nawa ne ko..?? Kuma babu da wanda muka had'a kud'i wajen ginawa,to abunda nake so da ke shi ne ki bud'e kunnenki sosai ki sauraren ni,a yau kin biyewa mahaifiyarki kin kashe auren ki ba,kinga wannan gidan da kike ciki..?? Ina so maza kafin fushi na ya sauka akanku,ki gaggauta fitar da miji daga zaran kin gama idda saboda ni bazan zauna da d'an da bazai min biyayya ba.."
Kanta a k'asa saboda yadda take jin kalaman mahaifin nata wanda ko a mafarki bata tab'a tunanin hakan zai faru tsakaninsu ba,wai yau itace da mahaifinta yake fad'a mata gidansa bana zamanta bane.Lallai kam sai yanzun ne take jin tayi kuskuren da zaiyi wuya ta iya gyarawa,haka nan sai yanzun ne take ganin aibun abunda tayiwa mahaifinta mai tsananin k'aunarta,shin wannan shi ne sakayyar irin soyayyar daya nuna mata..?? Da wannan ne ya kamata ace ta biya shi ladan nauyi da d'awainiyar da yayi da ita tun daga haihuwa..??
Wannan tunanin shi ne yasa taji a duniyarta tayi asarar wani abu mai girma wanda zai yi mata wahala ace ta dawo da shi.
Abba Matawalle kuwa koda ya gama fad'an ya tashi ya bar musu gurin dan dukansu yana fushi ne da su shi yasa ma baya son a yanzun ya zauna guri d'aya da su duka saboda yadda yake jin haushinsu.
Bayan tashin sa a gurin hajiya Suwaiba ta kalli Sajida taga ta kife kai a tsakanin laps d'in ta tana sheshshek'ar kuka,sai ta dafa ta tana sake ingizata da kalamai marasa ma'ana nan ba tare da y'ar ta kulata ba ta mik'e da gudu ta bar wajen tana rusa kuka,da ido ta bita tana tab'e baki dan tasan za tayi kuma ta bari Harma ta dawo kan turbar data d'ora ta.(ni kuwa dai na ce da Sajida matuk'ar kuka ne yanzun ta fara shi,lokacin da zata zubar da hawaye bai zoba tukuna).
A b'angaren Yarima kuwa lokacin da suka tashi a meeting d'in koda ya fito babu wata damuwa a tattare da shi dan haka duk wani jaje da ban baki da su Hajiya keyi masa shi jinsu kawai yake coz abun bai b'ata masa rai ba haka nan bai d'aga masa hankali ba,hasalima da zasu bincika zuciyar sa a lokacin to da babu abunda zasu tsinto face zallar farin ciki mara misaltuwa.
Tun daga ranar da wannan al'amarin ya faru ta gefen Yarima bai sake bi ta kan wani maganar aure ko mata ba,hasalima aikinsa ya sake rik'ewa da gaskiya,wanda ko a weekend ma a magiya yawancin lokaci sai ya zama ba ko wane weekend yake dawowa gida ba,dan wani lokacin ma sai ya shafe a k'alla sati uku bai zoba sai dai ko suyi waya,haka rayuwar ta ci gaba da gangarawa cike da nasarori,wanda abubuwa da dama suka faru a cikinta wasu masu dad'i wasu kuma akasin haka..............
*ONE LEAP YEAR...*
*Aradun Allah zanyi muku tijara,dan yanzun sam babu comment's d'in da suke gamsheni,so zanja gefe na k'ame dama dagiya ce kawai nake tunda kunsan matsalar da muka samu,kunga daga yau saina koma posting duk sanda na bushi iska,tunda kuma kun koma gefen sai aikin na turo amma babu comment's,masu yin comment's duka basu wuce na lissafa da yatsun hannuna..Allah ya sani kamar yadda kuke son farin ciki kowa ma yana so,mu fa da comment's d'in ku kawai muke samun farin cikin,yanzun idan babu comment's Fisabilillah ku fad'a min yaya kuke tunanin tsarin labarin zai kasance...???*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
🎈🎉🎊
_My love for u knows no bounds,my respect for u is equally immense.U are my ultimate emotional support and my sweetest love.Every memory from the gone years,makes me glad that u are my sisters.And i wish both of u a very warm & happy Birthday.I love u my sisters.!_
🎂🍿🥂 *Happy belated birthday (NI'IMATULLAH & RAHMATULLAH).*🥂🍿🎂
🎊🎉🎈
___________________
_It's all for u alone *🌷FENERH🌷* of Golden pen writer's asso,d writer of *🌷KUSKURE NA🌷,* i have heard that friends do a lot in life.But,now i saw for myself,i can't thank u enough for the pain u took for me,i appreciate the time nd efforts.So,glad that i have a loving friend like u.Truly thank u.!_
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 9.*
^^^^^^^^
*ONE LEAP YEAR...*
Kimanin shekara guda kenan da faruwar *AL'AMARI'N* wanda izuwa wannan lokaci abubuwa da dama sun faru,wasu masu dad'i wasu kuma kishiyar hakan,a bayan rabuwar auren YARIMA YAZEED da Sajida kuwa,wanda kafin rabuwar tasu sai da aka kai ruwa rana tsakanin iyayen na Sajida,haka bayan wannan kuma sai labarin rashin lafiyar Yariman da shima tuni ya baza ko ina a cikin k'waryar birnin,naji mamaki akan ta inda labarin ya bazu haka wanda ba iya ni kad'ai ba,hatta da cikin gidan Sarautar su kansu sai da abun ya so girgiza su,dalilin da yasa duk suke mamaki da faruwar hakan kuwa sun sani ko a lokacin da cikin gidan suka san cewa Yariman yana fama da larurar su kansu a tsakaninsu ba kowa ne ya sani ba,amma yanzun ace hatta da mutanen gari sun san da matsalar,dole ne wannan yasa su shiga tsananin mamaki.
A b'angaren Yarima kuwa koda yaga zuwa lokacin shekara guda har ya zagayo da karb'ar maganin da suka yi,nan ya fara tunanin ta inda zai fara tunkarar gurin malam Adamu dan sanin ainihin inda matsayar su take,da yammacin ranar bayan ya kammala shirinsa ya fito cikin shigar gargajiya ta manyan kaya wanda suka sake fitar da cikar kamalarsa da girmansa cikin wani farin yadi haka hulan dake sanye kansa wacce akewa lak'abi da minister itama farar ce kar,atak'aice dai tun daga sama har k'asa shigar da yayi kenan na farin color,da fitowarsa apartment d'insu YASEER ya fara nufa yana zuwa yayi knocking door d'in,dai² an bud'e k'ofar ya juya yana kallon wanda ke gurin a tunanin sa ko cikin hadiman dake kula da side d'in ne,da YASEER suka yi arba nan take ya juya ba tare da yayi magana ba cike da k'asaita, girgiza kai YASEER d'in yayi sannan ya biyo bayansa cikin d'an d'aga k'afa,a mota suka had'u ba tare da wani cikinsu yayi magana ba yayi warming motan sannan suka d'auki hanyar sharad'a,dai² inda suka tsaya wancan lokacin wannan karonma a nan yayi parking duk da y'an canje² da aka samu wanda ba za'a rasa ba,kafin suka ci gaba da takawa da k'afa har suka iso k'ofar gidan wanda yake d'auke da katuwar bishiyar ced'iya da d'an madaidaicin masallaci sai d'akin da yake ganin masu larura dake nan jikin gidan nasa yana kallon k'ofar masallacin,a lokacin kasancewar yamma,bai hana mutane taruwa ba dan haka ba tare da wani ya fahimci wani abu a tare da su ba,suka nemi wani benche suka zauna suna jiran mutane su d'an ragu a gurin,suna nan zaune har zuwa lokacin da mutanen da suka tarar suka yi sauk'i sannan suka matsa dai² bakin k'ofar tasa suka yi masa sallama,cikin sakin fuska ya amsa musu kafin yayi musu izinin shigowa yana gyara musu shimfid'ar dake baje a cikin gurin yana sake musu marhaban dan izuwa wannan lokacin tuni datijjon ya shaida su,saboda lokaci zuwa lokaci sukan je su gaishe shi tare da yi masa alkhairi,bayan sun gaisa kamar ko wane lokaci da suka saba sai duk suka yi shiru na d'an lokaci kafin YASEER ya kalli malam Adamu da cewa
"Baba yau dai gamu mun sake dawowa kamar wancan lokacin na farko da muka fara zuwa gareka,cikin hukuncin Ubangiji kamar yadda kayi mana bayani a wancan karon Allah ya ara mana rai da lafiyar dawowa kamar yadda a yau muka kawo shekara guda dai².."
Jinjina kai malam Adamu yayi cike da gasgata maganar YASEER yana cewa
"Haka fa akayi,yau shekara guda cif da kuka zo,Ubangiji mai iko da hikima kamar yau ne kam gashi cikin k'udirar Ubangiji har lokacin ya kuma zagayowa..To Ubangiji ya bamu ikon cikawa da imani.."
"Ameen" suka amsa masa,cikin hikima ya d'an juya ya kallesu su duka biyun kafin yayi magana
"To samari yanzun yaya muke ciki..??"
Ya kalli Yarima da kansa ke k'asa yana sake cewa
"Ina fatan akwai matar dai ko..??"
Cikin rashin fahimtar maganarsa YASEER yace
"Baba ai tun wancan lokacin ka shaida mana ba zaiyi aure ba har sai mun shekara da karb'ar magani..!"
"K'warai haka muka yi..Kuma maganar da nake yi nima a yanzun ba wai ina nufin wani abu bane,abunda nake magana akai shine shin akwai matar da zai aura kwana kusa ne ko kuwa..?? Saboda ta haka ne kad'ai zamu iya mu fahimci inda muka nufa gaba d'aya ni da ku..ko ba haka ba..??"
Jinjina kai YASEER yayi cike da gamsuwa da maganar dattijon yana cewa
"Haka ne baba.."
"Yawwa..! To Malam YAZEEDU ina fatan kaji batuna kuma a shirye kake a ko wane irin lokaci zaka iya zuwa min da labarin auren ko..??"
Tunda suka zo bayan gaisuwa da suka yi da malam Adamu ya sauke kai k'asa sai yanzun ya d'ago kansa fuskarsa d'auke da murmushi ya jinjina kai sannan yace
"In sha Allah Baba..!"
"To Ubangiji yayi mana kyakykyawan jagoranci."
Nan ma da "ameen" suka amsa kana d'akin ya d'auki shiru na y'an wasu mintuna,y'an wasu magunguna ya sake had'a masa ya bashi sannan yayi masa bayanin yadda zai yi amfani da su,bayan sun kuma tsaida magana akan bayan auren Yariman zasu sake komawa gurinsa dan yasan yadda ci gaban al'amarin yake,godiya suka masa sannan suka masa alkhairi suka sake d'aukan hanyan komawa gida.
Mintuna goma sha biyar ya kawo su gida kasancewar sun d'an samu tsaiko a dalilin traffic da suka mak'ale har na wasu y'an mintuna,sanda suka dawo direct apartment d'in Ummi suka nufa dan dama itace abokiyar shawararsu a kaf gidan,duk da a wasu lokutan sukan je gurin Umma'nsa sai dai itan ba ko wace irin magana yake sakewa suyi da itaba,haka nan irin wannan maganar tun daga sanda al'amarin ya faru ko sau d'aya bai tab'a tsayawa sun tattauna akan matsalar ba,sai dai ko ayi da Ummi ta kuma ta sanar mata,yanzunma suna shigowa da ABEELA da Abir suka fara tozali,cikin girmamawa suka gaida su kafin suka samu guri suka zauna suna tambayar Ummi saboda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 63