waje tana maimaitawa
"Zata kashe kifa kika ce.? Me yasa zata kasheki..?"
Hawaye Aisha ta fara cikin kuka taci gaba da magana
"Saboda ta sha gayamin,ta kuma jima tana jamin kunne akan duk ranar dana bari wani yasan gaskiyar wannan Al'amarin saita kasheni ba tare da ta bar wata shaida da za'a san ita tayi hakan ba,na sani baba ba ita ta haifeni ba,amma yadda ta raineni ta kuma bani damar sake rayuwa a lokacin da aka sata ta kasheni yasa nake d'aukarta fiye da kowa dana sani nake kuma rayuwa da shi,itace uwa da ubana dana tashi na ganni tare da ita,itace komai nawa a duniyata,haka lokacin da ake k'ok'arin rabani da rayuwa ta ita tayi k'ok'arin bani kariya,wannan yasa nake jin tsoron bayyana abunda na sani gudun kada mu fad'a mugun hali daga ni har ita.Duk da ina tunanin ita kanta ba haka nan ta aikata wannan abunba,amma nasan halinta a duk lokacin da tayi niyyar aikata abu ko mene ne zata iya aikatawa,jeeddah duk yanda zan kwatanta miki mugayen halayenta wollahi ta wuce nan..."
Wani sabon tashin hankalin jeeddah ta shiga jin wannan maganar daga bakin Aishar
"To ke ina iyayenki suke..? Ko kuma sune suka bata ke sukace ta kashe ki..?"
Girgiza kai tayi tana ci gaba da kuka
"Nifa na fad'a miki bani da iyaye,hasalima ban sani ba ko ni en shegiya ce.."
"Wa'iyazhu billah...! Kaii haba dan Allah ki daina fad'ar haka in sha Allah haka bazai faru ba,kema y'ace kamar kowa,ki daina cewa baki da iyaye..amma abunda ban fahimta ba idan har Ladidi zata karb'e ki ta raineki tun kina jinjira,akan me yasa su iyayen da suka haifeki basu raine ki ba,akan mene suka bata ke ta kaahe ki..? Shin duk akan mene wannan AL'AMARIN zai faru..? Me yasa iyayenki zasu aikata irin wannan kuskuren..??"
"Wollahi ban sani ba nima jeeddah,tun dana taso ni dai na ganni a hannunta kuma ko sau d'aya bata tab'a nunamin wani tace shine dangina ba,hasalima kamar yadda na fad'a miki tace bata ni akayi akace ta kasheni,ganin baza ta iya ba yasa ta k'yale ni taci gaba da rainona,koma me yasa tayi haka ni ban san dalilin ta ba,haka suma wad'anda suka aikata min hakan ban san dalilin su ba...ban sani ba..!"
Shiru duka suka yi zuciyoyinsu cike da tsantsar mamaki da al'ajabi
"Shi kenan Aisha in sha Allah iyayenki zasu bayyana kema kinji,kada wannan ya sa kiyi tunanin aikata wani abu da zai iya janyo miki ciwo,amma ni ina da tabbacin Babarki tasan ko su waye iyayenki idan kuma har bata sani ba to wad'anda suka bata ke sun san inda iyayenki suke..."
Kuka Aisha taci gaba dayi ita kuwa jeeddah sai bata baki take akan tayi hak'uri ta maida lamuranta gurin Allah shi zai bayyana mata iyayenta duk tsayin zamanin da za'a d'auka.
"Kinga ko ki share hawayenki muje ciki mu zauna sai mu k'arasa maganar,in sha Allah na miki alk'awarin babu wanda zai san wannan labarin da kika bani,amma ina neman wani abu guda a gurinki.."
Kallonta Aisha tayi sannan ta girgiza mata kai alamun tana jinta
"Muje dai mu zauna tukuna saina sanar dake.."
"Toh..!" Tace sannan suka shiga d'aki,sai data faki icon Aishar sannan ta d'auki wayarta ta kuna recording ta dawo kusa da ita ta zauna kana ta furta
"Ina saurareni Aisha,idan har kina ganin aminta dani yasa kika yanke shawarar sanar dani abunda kike son fad'a na miki alk'awari babu wanda zaiji.."
Kai Aishar ta girgiza cikin sanyi ta furta
"Wollahi na yarda dake d'ari bisa d'ari,idan da ace ban yarda dake ba wollahi babu ta yadda za ayi yau nazo da niyyar fad'a miki wannan sirrin.."
Kai itama jeeddan ta jinjina sannan ta kalleta
"Idan har kin yarda dani da gaske kamar yadda kika fad'a to ina son ki fad'a min gaskiya da dalilin da yasa mahaukacin nan yake son ki fad'a yanzun.."
Marairaicewa tayi kamar zata yi mata kuka hawaye kuwa har sun fara sintiri a kumatunta
"Jeeddah na fad'a miki wollahi idan har na fad'a miki kasheni za tayi da gaske babu wasa..Amma na miki alk'awarin zan fad'a miki wani abu daga ciki..."
"Shi kenan ki fad'a min wannan en ina sauraronki,amma ki tabbatar gaskiya zaki fad'a min kamar yadda kikayi alk'awari kin san shi alk'awari girma ne dashi da kuma had'ari muddin kika k'i cikawa to kada ki manta ubangiji bazai kyaleki ba matuk'ar baki cika ba zaki gamu da azaba na sab'a alk'awari da kika yi.."
Share fuskarta tayi sannan ta girgiza kai
"Kamar yadda nayi miki alk'awari tabbas zan fad'a miki gaskiya...Abunda ya faru a shekaru biyar da suka gabata,da dalilin da yasa wannan mahaukacin yake binta yana tsoratar dani naje na fad'a ba wani abu bane illah yana so naje fada na fad'a cewa duk abunda na fad'a akan yarima yazeed k'arya ne,kuma wollahi nima na tabbatar cewa a waccan ranar duk abunda baba ta fad'a k'arya ne,makamancin wannan bai faru ba,duk abubuwan data fad'a wollahi ba gaskiya bane,amma ina jin tsoron na fito na ce ba haka bane saboda na santa wollahi muguwa ce duk abunda ta fad'a zata iya aikatawa matuk'a.Gaskiya ne nayi k'arya kuma nayi shaidar abunda babu shi amma wollahi ki yarda dani dole ce tasa ni yin haka ba don son raina na aikata ba,ina rok'onki don Allah kada ki bari kowa ya san wannan sirrin,kamar yadda kika yimin alk" awari ki zama mai cikawa,kinga tun farko munyi alk'awari dake,kuma yarda ce tasa na fad'a miki wannan sirrin,dan Allah kema ki kasance mai cika naki alk'awarin..."
Kai jeeddah ta jinjina kafin ta mik'e tsaye ta zare wayarta daga inda ta mak'aleta sannan ta kalli Aishar tana cewa
"Gaskiya ne Aisha nayi miki alk'awari,amma a gaskiya wannan maganar ba irinta ce wacce ni jeeddah nake yin alk'awari akanta kuma na cika ba,shin bakya tunanin rayuwar bawan Allah'n da kuka jefa a masifa..? Ko kuwa saboda son kai da zuciya irin naki sai yasa bayan nasan gaskiya naci gaba da rufa miki asiri..? Shin nayi shiru na zuba ido ina gani ana cutar da shi bayan nasan gaskiya shi ne burinki..? Dole ne na fito na bayyana gaskiya ko da hakan na nufin faruwar komai,amma alk'awari d'aya zan iya yi miki,shi ne zan rok'a miki alfarma in sha Allah sunan ki bazai tab'a bayyana a matsayin wadda ta fad'a min ba,idan kuma har al'amarin ya wuce yadda muke tunani in sha Allah zanyi k'ok'arin ganin wata matsala bata same ki ba,zamu san yadda muka yi aka d'auke ki daga hannun Ladidi saboda kada ta samu damar cutar dake.."
Tana fad'ar haka ta juya ta fice daga d'akin,duk kiran da Aishar ke mata ko d'aya bata amsa ba bare tasa ran zata juyo ta saurari abunda zata sake fad'a mata. Ita kuwa Aisha koda taga jeeddah ta fice daga d'akin nan tashin hankalinta ya sake k'aruwa saboda bata san ta wace hanya ce su jeeddah zasu bi su bayyana gaskiyar da suke fad'a ba...........
_DON'T FORGET TO VOTE ME ON WATTPAD @jeeddahmu898._
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*Pg 7.*
^^^^^^^^
B'angaren jeeddah kuwa tunda ta shiga wanka take sakin murmushin jin dad'in da rabonta da tayi irinsa har ta kusan mantawa,cikin sauri tayi wankan ta fito cikin shirinta,a nan inda tabar Aisha zaune haka ta dawo ta isketa fuskarta cike da damuwa,ta buga tagumi da duka hannayenta biyu,bata bari sun had'u da Aishar ba sai data tabbatar ta kammala shirinta,duk shirin babu wanda ta tsaya b'ata lokaci akansa sannan ta fito cikin shiganta ta yau da kullum,kusa da Aishar ta zauna ta dafa kafad'arta,da sauri itama Aishar ta d'ago ta kalleta sannan ta marairaice mata fuska
"Dan Allah jeeddah ki rufamin asiri,kamar yadda kika min alk'awari kema ki kasance mai cikawa,na miki alk'awari ni da kaina zanje fada na fad'i duk abunda kuke so,in dai zaisa a saki yarima..amma..!"
"Amma me..? Ci gaba mana ina sauraronki.."
"Amma ba yanzun ba..ina so ki bani lokaci,in sha Allah zanyi duk abunda kuka ce..Sai dai ina jin tsoron fitowa na fad'a a yanzun.."
Wata dariyar rainin wayo jeeddah ta saki tana kallon Aisha
"Aisha kenan..! Ni yanzun abunda kike so zanyi ko kuwa ni wanda nake so zanyi...? Wai ke anyama mutum ce kuwa..? Taya zan san gaskiya sannan kiyi tunanin naci gaba da b'oyewa? Shin idan na aikata haka nawa za'a biyani ko kuma nawa zan samu..?"
"A'a jeeddah wannan fa ba maganar nawa za'a biyaki bane,magana ce ta salwantar rayuwa.."
"Kinga Aisha bana son jin wannan maganar taki,akan taki rayuwar sai kuma muyi k'ok'arin salwantar data wani wanda baijiba bai gani ba...Kina jina koh abunda na fad'a miki kawai ki d'auke shi,na riga na fad'a miki sunan ki bazai bayyana a cikin maganar nan ba,amma kuma banyi miki alk'awarin zanyi shiru da wannan maganar ba,yanzun kawai ina son ki kama hanyar gida sannan kamar yadda muka fara ko da zamu had'u a hanya da duk inda kika san mutane za su iya zarginmu ina so ki nuna kamar baki sanni ba...wannan zai hana a zargeki a matsayin wacce ta sanarmin da wannan maganar..kin fahimta ai..?"
Kai ta d'an rausayar idanunta kamar zasu fara zubar da hawaye
"Shi kenan to...Amma ni dai jeeddah ina jin tsoro sosai wollahi.."
'Dan siririn tsaki jeeddan ta saki kafin ta dawo ta gabanta ta tsaya
"Kinga Aisha ko kina jin tsoro ko bakya ji wannan gaskiyar dole ne ta bayyana,abu d'aya kawai zaki dage akansa kuma nima in sha Allah zan taya ki addu'ah na san ubangiji zai kub'utar dake daga dukkan wani tsananin da zaki fad'a ya kuma bayyana miki iyayenki..amma yanzun kije gida kawai sai mun sake yin magana."
"Toh shi kenan jeeddah na gode... Kuma na fahimci abunda kike nufi,ni kaina ina bayani ki akan ki bayyana gaskiya ko da hakan zai yi sanadiyyar rasa tawa rayuwar,amma sak'o d'aya da zan baki shi ne..ko da ace bayan na rasa rayuwa ta,idan kuma har Allah ya bayyana mahaifana ina so ki sanar dasu cewa duk abunda suka min na yafe musu..Nima ina buk'atar su yafemin idan har nayi musu wani laifi da yasa su salwantar dani...."
Tana fad'ar haka ta mik'e jikinta a sanyaye idanunta suna fidda hawaye ta fice da d'an gudunta...Binta jeeddah tayi da sauri tana son tsaida ita,amma kafin ta fito daga d'aki tuni har ta fice a gidan.
Kasancewar babu kowa a gidan sai ita kad'ai hakan ya bata damar kintsawa ta fice itama bayan ta kulle gidan,sai data fito k'ofar gida ta tsaya ta k'arewa hanya kallo zuciyarta da tunanin inda ya kamata tabi,d'an tak'aitaccen tunani ta tsaya yi cikin zuciyarta take tambayar kanta
"Shin yanzun ina ya kamata na nufa..? A ina zanga yarima Yaseer..?"
Nan ta d'anyi shiru na wucin gadi sannan ta karkata akalarta zuwa hanyar da zata sada ta da cikin gida,tafiya kawai take tana tunanin anyama yanzun idan taje zata iya samun damar ganin yarima YASEER en kuwa..? Da wannan tunanin ta ci gaba da nausawa tana tafiya,har ta iso harabar gidan ta ratsa ta nufi hanyar da zata sadata da b'angaren mahaifiyarsa..
Har ta iso turakar Fulani tana tafe tana waiwaye ko Allah zaisa ta gamu da shi kafin ta iso amma ina ko mai kama da shi bata had'u da shi ba,d'an siririn tsaki ta saki sannan tayi sallama a bakin k'ofar shiga b'angaren,kamar kullum idan ta zo haka ta gaisheta cikin girmamawa,ita kuwa Fulani sai janta da hira take,amma ina ita jeeddan hankalinta duk baya kan abunda Fulani ke mata magana akansa,ta d'an jima a b'angaren nata har ta tambayeta ko akwai wani aiki da zata mata,shima har tayi ta gama amma bata ga ko kyallin yariman ba a gurin,sallama tayiwa Fulani akan zata tafi gida saboda yamma da tayi har ana neman fara kiraye²n sallar Maghreb,sallamarta tayi sannan ta fice tana tafiya duk guiwoyinta a sanyaye saboda damuwar rashin ganinsa.
Cike da b'acin rai ta kamo hanyar dawowa gida,duk ranta tana jin babu dad'i,tana niyyan shiga soron gidansu taji an rik'o hijab enta ta baya,da sauri ta juyo dan ganin waye,fuskarsa a rufe yayi shigar nan tasa tamkar ta buzaye duk dan ya b'adda kama,wani murmushin jin dad'i ta saki sannan tayi saurin kallon hanya,yadda yaga tana lek'en bayansa yasa shi saurin sakinta tayi ciki yana biye da ita a baya,a soron suka tsaya kafin tayi magana ya rigata
"Kina nemana ba..?"
Mamaki maganar tasa ta bata dan bata tab'a zaton akwai wanda zai gano hakan ba
"Babban Yaya ya akayi ka fahimci haka..?"
"Yadda fuskarki ta nuna babu wanda bazai yi saurin fahimta ba ai..bare kuma tunda naganki a b'angaren Fulani nasan akwai maganar data kawo ki.."
Fuskarta ta shiga tab'awa tana son gano abunda yake nufi,d'an murmushi yayi kafin yaci gaba
"Neman me kike min ne...?"
Sai da tayi d'an murmushi sannan ta furta
"A k'arshe dai Allah ya nufa munyi nasara..."
Kallon rashin fahimta yayi mata
"Nasara akan me kenan..."
"Case en yarima...."
Wani kallo ya mata "case en yarima..? Wannan ai dad'ad'd'en labari ne da tun tuni muka manta da shi..."
"A'a Yallab'ai bamu manta ba,mun dai hak'ura ne a dalilin rashin samun k'warin guiwa...mun hak'ura mun jingine shi a dalilin rashin shaida...Amma a yanzun zai tashi,Allah ya nufa lokacin k'ark'areshi yayi da izininsa..."
Ta k'are maganar tana sakin murmushin jin dad'i,a hankali taci gaba da fad'in
"Idan har kamin izini Yallab'ai zan bayyana maka dalilina na fad'ar haka a yanzun bada b'ata lokaci ba.."
Kai ya iya girgiza mata ba tare daya iya yin magana ba,saboda mamakin maganar data zo masa da ita a wannan lokacin,wayar daya bata tun wancan lokacin ta ciro daga jikinta sannan ta shiga gefen data adana recording en data yi na maganarsu da Aisha tayi masa playing,duk yadda suka yi da Aisha babu abunda bai jiba,tsabar mamaki da murnar da yarima Yaseer ya tsinci kansa a ciki har baisan sanda ya zube a wajen yayi sujudush-shukur ba,bakinsa sam ya gaza rufuwa saboda tsantsar mamakin daya tsinci kansa aciki,idan ya d'ago zaiyi mata magana sai ya kasa,gaba d'aya kalmomin bakinsa sun d'auke ya gaza furta komai,tura recoding en yayi a nasa phone en sannan ya mik'a mata nata,cikin annashuwa ya furta
"Ki jira kyautarki daga gareni wannan alk'awarina ne nayi miki kyauta ta musamman..."
"Ranka shi dad'e ina neman afuwa a bisa abunda zan fad'a,idan har na fad'a ba daidaiba ko maganata zata b'ata maka rai ina neman afuwarka bisa hakan..."
"Babu komai ki fad'a ina jinki,a yau kam kome za'a fad'a,kome za'ayimin ba lallai ne nasa shi a raina har ya b'ata min ba...saboda haka ki fad'i duk abunda kike son fad'a ina saurarenki..."
"Yallab'ai dama ba akan komai nake son yin magana ba..ina nufin ina son cewa ne wannan kyautar da kace ka barshi ranka shi dad'e,ba don komai nayi wannan maganar ba sai don kawai ban cancanci hakan ba..."
Wani kallo ya b'alla mata kafin ya saki murmushi
"Idan na baki ki bayar ko ki yar kice bakya so.."
"Afuwaan Yallab'ai..."
"Babu komai ai nima ra'ayina na fad'a idan har kinji bai miki ba to ki bayar..."
Kanta ta dad'a sunkuyarwa k'asa tana wasa da gefen hijab enta,ba tare data sake iya cewa komai ba.Godiya yayi mata wanda har ya janyo taji kunyar hakan,sannan ya fice ya barta nan tsaye jingine da bango tana sauke numfashi idanunta a kulle...
^^^^^
Tun daya saurari audios en zuciyarsa ke cikin matsanancin farin ciki,direct gefen su ya nufa ya shirya kana ya d'auki mota,bai zarce ko ina ba sai gidan Matawalle dan yasan shi kad'ai ne zai iya fahimtarsa a irin wannan lokacin,zuwansa gidan Matawalle ya iske shi da bak'i,dan haka sai kawai ya nemi komawa bayan sun gaisa da shi da sunan daman yazo ne ya gaisheshi,badan matawalle ya yarda da maganar ta Yaseer ba ya k'yale shi ya tafi.
Ko daya dawo gida kasa zama yayi dan babban burinshi bai wuce yaga an saki d'an uwan nasa ba,amma yaya iya dole ne yabi komai a sannu idan ba haka ba komai zai iya lalacewa kamar yadda a lokacin baya da suke kan neman shaida komai ya lallace musu,dole yasan a yanzun gaggawa ba tasa bace.
Cikin turakar mahaifiyarsa ya nufa dan yana jin ko zai iya boy'ewa kowa abunda ya sani tofa banda ita,yana shiga ya isketa da bayin dake mata hidima ciki kuwa harda Inno,juyawa yayi zai koma ta dakatar da shi,cikin nutsuwa ya dawo ya nemi guri ya zauna,yanayinsa kad'ai data Kalla tasan akwai dalilin daya kawo shi a irin wannan lokacin,dan haka kawai sai ta sallami bayin nata sannan ta fuskance shi
"Yaseer me yake faruwa ne na canja cikin irin wannan murnar haka..?"
'Dagowa yayi yana sakin murmushi sannan ya bud'e bakinsa cikin farin ciki yana fad'in
"Ummi a k'arshe dai komai zai zama tarihi.."
"Tarihi kuma...? Wane irin tarihi ne wannan da kake fad'in k'arshensa yazo...?"
"Ummi ina nufin k'arshen zaman d'an uwana a kurkuku,Allah ya nufa a yau gaskiyar da muka yita jira ta bayyana,dama nasha fad'a miki,ni nasan waye d'an uwana kuma nasan duk abunda zai aikata da wanda bazai iya ba,na tabbatar dama wasu ne suke shirya wad'annan abubuwan ba don komai ba sai don su b'atawa d'an uwana suna...amma alhamdulillah..! What is tossed upwards must falls back down...!"
Wani murmushi ne ya sub'ucewa ita kanta fulanin da bata san lokacin da tayi shi ba,cikin zak'uwa ta furta
"Yaseer me kake son cewa ne...? Kana nufin kun samu shaidar da zata iya sawa a saki YAZEED ko me kake nufi..?"
"K'warai kuwa Ummi yau Allah ya nufa mun samu gamsashshiyar shaidar da ita kad'ai zata iya sawa a sake shi..Harma a wanke shi daga mugum k'azafin da aka masa.."
Hamdala Fulani ta shiga yi tana yiwa Allah godiya bisa wannan ni'ima da Allah yayi musu a lokacin da suka riga suka gama fidda rai da samunta.
"Amma Yaseer ta wace hanya kuka samo wannan shaidar...?"
Murmushi ya saki kafin ya furta
"Ummi sanin inda muka samo shaidar ba shi ne mai muhimmanci ba,abunda yafi kawai shi ne mu maida hankali akan a sake shi..."
"Haka ne Yaseer amma sanin ainihin yadda aka samo shaidar shima yana da muhimmancii.."
"Shi kenan Ummi zan fad'a miki komai da yadda akai muka samu shaidar...!"
Yana niyyan yin magana wayansa dake ajiye a gabansa tayi k'ara,a hankali ya kalleta ganin *UNKNOWN NUMBER* yasa shi k'urawa wayar ido har kiran ya katse ba tare daya d'auka ba,juyawa yayi ya kalli Ummi da niyyan sake yin magana,k'aran shigowar sak'o ya katse shi,kamar bazai d'auka ya duba ba kuma can ya d'ago wayar ya bud'e sak'on,ga abunda sak'on ya k'unsa
_"Shin kai kana tunanin kai wani mai wayo ne...? Ko kuwa kana ganin wannan y'ar shaidar daka samu zata isa sawa a saki wanda kake tak'amar d'an uwanka ne..? Me yasa kai baka tunani ne akan future enka,kullum kai kenan kaita maganar d'an uwanka kamar shi kad'ai kake da a fad'in duniyar...? Sarauta gadon kuce ya kamata ka tsaya kayi tunani,kai kanka wannan dama ce ka samu da idan har baka bayyana yarima a matsayin mara laifi ba,wata rana zata kaika ga zama *SARKI* dole mutane baza su tab'a yarda mutum mai irin halin yarima yazeed ya mulkesu ba,amma har sai ka b'oye wannan gaskiyar da kake tunanin bayyanawa...Idan kuwa har kaji zaka iya bayyana shaidar ka,tofa ka sani daga lokacin da aka saki yarima aka kuma wanke shi a matsayin mara laifi,kasa a ranka babu kai babu zama SARKIN GOBE........! Kamar yadda jama'a suka fara maka lak'abi da yarima..."
Wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarci yarima Yaseer da bai san sanda wayan ta sub'uce daga hannunsa ta fad'o k'asa ba,saurin binta yayi ya d'auko yana sake duba sak'on data inda sak'on ya shigo wayarsa.K'ok'arin tura sak'o ya shiga yi sai dai sak'on nasa sam yak'i tafiya,idanunsa ne suka kai dai² inda yake tsammanin ganin suna da number da aka turo sak'on,sam babu lamba bare suna haka mad'aukin sak'on ya nuna masa,wannan ya nuna kenan ko zai shekara yana tura sak'o zuwa lambar bazai tab'a tafiya ba,dafe kansa yayi yana furzar da wani irin huci mai d'umi,Ummi kuwa sai binsa da kallo take kafin ta fara tambayarsa lafiya..?
"Babu komai Ummi wani sak'o na gani ne yanzun..."
Bai k'arasa ba kira ya sake shigowa da sauri ya kalla phone screen en a tunaninsa ko wancan number ne ta sake kiransa,sunan Abba Matawalle da yayi appearing a sama yasa shi sakin d'an murmushin k'arfin hali kana ya furta
"Ina zuwa Ummi..."
Wayan ya zara cikin sauri yayi hanyan fita daga d'akin,bai kai ga answering call en ba lokacin ya fito cikin parlor yaga inuwar mutum ta gifta da sauri,wayan yayi saurin mayarwa silent sannan ya tura ta a aljihunsa yabi hanyar da yaga inuwar tabi,cikin sand'a ya shiga bin hanyar amma iya bincikensa baiga kowa ba,dawowa yayi yama Ummi sallama da sunan zai je Abba Matawalle na nemansa duk dan ya k'are maganar da suka fara d'azun dan bai son ci gaba da yinta a nan,matuk'ar kuwa saiya fad'a mata to tabbas ya hak'ura ba yanzun ba dan ganin inuwar nan ya tuna masa da lokacin baya,haka kawai yanzunma yaji bai amince da ganinta ba.Da wannan tunanin ya bar b'angaren mahaifiyar tasa ya nufi nasa gefen,sai daya tabbatar duk ya sallami duka hadimansa sannan ya nemi guri ya zauna ya shiga kiran matawalle,bayan daya d'auka Yarima Yaseer ya gaisheshi cikin girmamawa da mutuntawa a matsayinsa na abokin maimartaba kuma d'an uwa ga iyayensu ta dangantaka.
Nan yaci gaba da sauraren Matawalle inda yake masa magana
"Yawwa Yaseer d'azun kazo ina tare da bak'i bisa ga alamu kuma dai akwai wani muhimmin abu daya kawoka,dan nasan ba haka kawai ake ganin kuba,sai dai kuma baka tsaya na sallami bak'in ba ka tafi..."
Sai daya sosa kai saboda jin kunyar Matawallen sannan cikin girmamawa ya furta
"Ehh! Wollahi Abba,dama akan matsalar yarima nazo..To kuma saina iske kana tare da bak'i shi yasa nace bari na tafi kawai na dawo daga baya.."
"Allah sarki ai daka min wannan bayanin da na sallami bak'in da wuri saimu tattauna batun da kace,ina ganin shi en yafi muhimmanci akan ganawata da bak'in.."
"A'a Abba ai kowa da irin uzurinsa,akan namu uzirin bai kamata mu hana sauran mutane ganinka ba.."
"Ehh! To amma dai dole kuma suma mutanen suyi mana uzuri akan namu uzurin idan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 63