maganar Ladidin,sannan na nusar da shi akan ya nemi aurenta ko Allah zaisa na sami cikar burina,bayan yanke wannan shawara sai na nemi Abu YAZEED akan yazo ina son ganinsa,ko da zuwansa nan take na bijiro masa da maganar,amma ina ji ina gani shi ma d'in ya nunamin aifa shi sam baya da muradin k'ara aure sannan ita haihuwa nufin Allah ne shi bai damu da rashin haihuwar da matarsa bata samu ba,duka ma auren nasu shekaru biyu ne kacal,dan haka shi dai ya mik'a lamuransa ga Allah yasan shi zai iya masa,wannan maganar daya fad'a ta muk'ar k'onamin rai dan ji nayi tamkar ya watsamin tafasashshen ruwa,amma haka na danne duk b'acin raina na kuma taushi zuciyata..Ba don na so ba haka na fawwalawa zuciyata yin hak'uri,duk da ba haka aka so ba..Ban sake tada wannan magana ba duk da abunda ya faru yana damuna a lokuta da dama,sai a lokacin da ALIYU mahaifi ga YASEER wato GALADIMA kenan,ya dawo daga karatu,a nan nefa kuma kwad'ayi na da tsohon buri na ya koma kansa tunda naga alamun abunda na so ba zai samu ba,kamar yadda bahaushe ke cewa 'da sanyi safiya ake kama fara' haka na bugi k'irji na sake kama hanyar gidan sarauta,tashin farko a wannan karon ma hajiyan dai na sake nufa da maganar,da fari kam kamar abun arzik'i ta amsamin cikin farin ciki,sai dai kuma daga baya sai ta kirani tana bani hak'uri akan canja shawara da tayi,inda take nunamin shima Aliyu'n da kansa ya nemawa kansa matar aure,kuma ba kowa bace face y'ar gidan wazirin mijinta Abdullah,nayi bak'in ciki na kuma ji ciwon rai,sai dai babu yadda na iya tunda an nuna ba'a son nawa ahalin...Sai dai kuma wani abu da ban sani ba a wannan lokacin,ita kanta ladidi da nake fafutukar ganin na cusa ta gidan sarauta,ashe itama wannan zuwan da aiken da nake yawan yi mata ta k'yalla idonta akan Abu YAZEED haka nan ta k'wallafa ranta akansa,sai dai bata ko fito tamin maganar ba,dan yadda taga cikin k'ank'anin lokaci maganar auren Abu YAZEED en har ta kammala.
Shekarar farko da auren Aliyu,labarin samun cikin Fulani ya baza gari,lokacin da labarin yazo min kam nayi bak'in ciki mara misaltuwa,sai dai babu yadda na iya haka na ci gaba da zuba ido,amma a kullum na bud'e ido naga Hafsatu da wannan cikin ji nake kamar na shak'eta ta mutu,haka na d'auki lokaci mai tsayi ina niyyar ramuwa ga abunda aka aikata min amma abu yaci tura,ko da ganin al'amura sun cunkushemin haka sai na tattara dani da ita Ladidin muka yi sallama da hajiya Hauwa akan zamu je saudiyya umrah amma a zuciyata ba haka abun yake ba,bayan tafiyar mu kuwa ko da muka sauka a Jidda dama nan na yanke shawaran za muyi zaman mu kawai nasan hakan zai rage mana rad'ad'in abunda akayi mana a zuri'ar mu...! Wannan shi ne kad'an daga cikin irin labarin abunda ya wakana tsakanina da hajiya Hauwa da zuri'ar ta,wanda har ya janyo na k'udurce ramuwar gayya a wannan lokaci,dan babu yadda za'ayi na kyale wannan biyani bashin ya wuce a banza...!"
Dogon ajiyar zuciya Aisha ta saki,kafin ta furta
"Lallai wannan labari Adda akwai rikici cikinsa,amma gaskiya hajiya ko kad'an bata kyauta ba,a ganina dake da ita ai duk ta tsatso d'aya kuka fito,mene ne amfanin ta nuna tafi son nata..?? Ai kamata yayi ace ta yarje miki akan k'udurin da kika je mata da shi,ko ba komai zumuncin ku zai k'ara k'arfi a matsayinku na y'an uwan juna.."
Kallonta Adda ta d'an yi jin furucin dake fitowa daga bakinta tana jinjina kai,cike da gamsuwa da maganar ta Aisha..
^^^^^
Bedroom ya wuce abunsa ya shirya cikin pyjamas,a gefen gadon ya zauna bayan ya gama yana d'an nazarin abunda ba'a rasa ba,can kamar daga sama maganar da suka yi da YASEER bayan fitarsu ta fara dawo masa,a hankali ya saki siririn tsaki mai sauti sannan ya mik'e,zuciyar sa cike da tunanin idan har yak'i bin shawaran da YASEER en ya bashi lallai ne yana jin har cikin ransa bai masa adalci ba dan yadda yayi ta rok'on sa.
Har ya mik'e zai fita kuma ya sake komawa ya zauna,sai dai wannan karon a saman resting chair ya zauna yana had'a hannayensa biyu guri guda cike da tunanin idan yaje gurinta yace me ya kawo shi..?? Iri²n wad'annan tunanukan su suka hana zuciyarsa sukuni,ya shafe tsawon lokaci a haka shi kad'ai yayi shiru ba tare daya gama yanken hukuncin abunda ya kamata ba,yana nan zaune around 11:00pm wayansa dake can gefen gado ta fara kuka,sai da yayi da gaske sannan ya iya tashi ya nufeta,ko kafin ya k'arasa tuni har kiran ya katse,tsaki ya sake ja sannan ya juya zai bar gurin,wani kiran ne ya sake shigowa nan ya kai hannu ya d'auka,ba tare daya tsaya duba wanda ya kira ba yayi picking
"Hello! Broah I hope you're not going to ignored my opinion.. ??"
Muryar YASEER ya daki dodon kunnensa
"Ehhh ..!"
Kawai ya iya fad'a yana bin hanyan k'ofar shigowa d'akin nasa da kallo kamar wanda akace masa YASEER d'in yana wajen daya bud'e k'ofar zai ganshi
"No,broah! I do not believe,na tabbata daka d'auka bazanji ka bani irin wannan amsan ba..."
"How do you want me to be..?? Who told i was worried about it da zan wani bita..Naje na mata mene ko kuma itan tamin me..??"
"Ok.! Tunda kace haka,barin barka ka huta,amma bazaka gane kuskuren abunda kake shirin yi ba sai nan gaba,amma ya kamata kayi k'ok'ari ko da baka son yarinyar nan ka danne hakan a ranka,tunda har Allah ya had'a ku babu batun ka dunga wani kauce² kawai malam ka fuskanci abunda ke gabanka yanzun..Na tabbata itanma kamar kai take babu lallai ace itama tana sonka tunda kai ba ma'abocin sakin fuska bane bare ta samu damar nuna maka abunda ya kamata,amma kayi amfani da damar da tazo hannunka kafin ta kub'uce maka..!"
Shiru yayi yana sauraren sa har ya kai aya,a hakali kuma ya furta
"To Abba na gode.."
"What do you mean da kirana Abba da kayi..??"
YASEER ya tambaya cikin sauri
"Ohoo! Maka.."
Kamar Yariman yana gabansa,jin abunda ya fad'a yasa shi jinjina kai had'e da fad'in
"Well,tunda baka yarda da shawara naba shi kenan,ni dai nasan ban isa na tursasaka kayi abu ba,amma ina da damar baka shawara idan naga kana neman kauce wa hanya,amma tunda baka aminta da abunda na fad'a ba,kuma kana ganin kamar nayi maka badai² ba shi kenan,kana da ikon yin duk abunda zuciyar ka ta sak'a maka,sai dai nasan wata rana dole ne ka tunani a matsayina na d'an uwanka kuma mutum na farko dake yawan damunka da shawarwari a duk lokacin da yaga kana neman kaucewa hanya..Fatan alkhairi,ni zan tafi gurin amaryata kasan wannan lokacin ba a irin sane mutum yake sakaci da damarsa ba.."
Ai wannan magana da YASEER ya fad'a tamkar ya tsikari Yarima,nan take ya tunzuro shi
"Sai ka fad'awa wanda baida mayar ai..d'an rainin hankali..!"
Dariya YASEER ya saki kafin ya d'an tsagaita yana cewa
"Yes..But I'm not sure you want to go where the woman is.. Ohhh! No! Broah anya kuwa lafiyar ka kalau..??"
"Ohoo! come and check!"
Ya bashi amsa yana d'aure fuska kamar wanda suke tare a guri guda
"You're not going to fool me... Let's get it,get up..."
Tun kafin ya kaiga katse kiran tuni har YAZEED ya riga shi katsewa,yana ajiye wayan ya fice zuwa parlour,ya jima anan yana ta sak'e²n yadda zai tunkari d'akin nata,can yana tsaka da tunanin wata zuciyar ta shiga bashi shawara
"Kawai kaje ai tasan ko mene ne ya kawoka.."
A fili ya furta
"If she asks me what to say.. What should i tell her..??"
Again zuciyar ta sake bashi amsa da
"Akan wane dalilin ma zata tambaya bayan tasan abunda zai kaika..Kawai ka share ka je koma mene ne zai faru ya faru.."
Nan take yayi na'am da shawaran,sannan ya juya ya kama hanyar bedroom en nata zuciyarsa cike da taradaddin abunda zai tarar,lokacin daya zo dai² bakin k'ofar sai da yayi jimm kafin yayi k'arfin hali ya tura k'ofar had'e da yin sallama k'asa² sannan ya shiga ciki,bai tarar da ita a d'akin ba,dan haka ya samu damar bin d'akin da kallo,yana daga tsaye a gurin da yake,can zuwa wani lokaci kuma ya motsa da niyyan nemawa kansa gurin zama a saman resting chair,zamansa a gurin babu jimawa itama sajidar ta fito daga bathroom,a lokacin kuwa daga ita sai towel dake d'aure iya cinyanta,sam bata yi zaton da mutum a gurin ba,dan ko kad'an bata tab'a tunanin zai zo shigo a irin wannan lokacin ba shi ya sa ko da zata shiga wankan ma bata damu da d'aukan abunda zai rufe mata jikinta ba duka,haka nan sanda zata fito ma bata yi tsammanin ya shigo ba shi yasa da zata fito d'in ma ta fito kai tsaye.
Ganin mutum zaune shi ne yad'an sata yin turus ta tsaya da mamakin abunda ya kawo shi bayan tasan tayi masa sallama tun d'azun,baya ga tarin kunya da take ji saboda yadda taga ya d'ago ya kalleta da yaji alamun ta fito,fahimtar yanayin da take ciki yasa shi d'an d'auke kai,cikin wani irin yanayi na jin kunyar kansa,da rashin sanin takamaiman abunda zai ce ya kawo shi ya d'an cije lips ensa na wasu y'an dak'ik'u yana tunani,can dabara ta fad'o masa cikin sauri kuwa ya d'an d'age kai a hankali yana cewa
"Ehmm! Koma ki d'aura alwala..!"
Saurin kallonsa tayi da mamaki akan fuskarta,sai dai nan take kuma tayi saurin b'oye hakan a tsakanin zuciyarta da fuskar ta,ta kuma bashi amsa da cewa
"Nayi sallah fa tun d'azun..!"
"Ehh! Na san kinyi...Je ki sake yin wani ina jiranki.."
"Toh" tace masa sannan ta koma cikin nutsuwa,tana juyawa yana d'agowa nan ya rakata da ido yana sakin siririn ajiyan zuciya,a nata b'angaren kuwa itama sajida lokacin data tsinci kanta a toilet,jingina bayanta tayi a jikin k'ofar ta ciki,tana sakin nannauyan ajiyan zuciya da murmushi d'auke a fuskar ta na farin cikin samun Yarima da tayi a matsayin mijin aurenta,ta d'an d'auki lokaci kafin tayi saurin gabatar da abunda ya kawota ta fita,ko data fito bata same shi acikin d'akin ba dan haka ta samu damar yin sauri ta shirya ta d'auka hijab enta ta zumbula har guiwanta,kusan mintuna biyar tsakani ya shigo hannunsa d'auke da wani white leda mai d'an girma,nan fa zuciyarta ta shiga zikiri dan tasan yau kam saita Allah dan tsakaninta da Yariman,Allah kad'ai zai kwaceta tunda yayo wannan shirin.
Tana zaune a gefen gadon tana kallonsa ya shimfid'a musu k'aton pray mat,sannan yayi mata umarnin ta taso,bayan ta tsaya a bayansa nan ya kabbara sallah,raka'a biyu yaja bayan da suka idar kuma yayi musu addu'o'i sosai na neman zaman lafiya,sannan ya juyo ya fuskanceta yana bijiro mata tambayoyi,bayan y'an tambayoyin da yayi mata a b'angaren addini,wasu dai an samu ta bashi amsa wasu kuma tayi shiru,sai dai duk da hakan babu laifi ta yi k'ok'ari,daga nan kuma suka ci suka sha,bayan wucewar wasu y'an mintuna sannan yayi mata umarnin ta shirya ta kwanta yana dawowa,amsa masa tayi da to,daga haka ya fita ita kuma ta mik'e ta nufi closet d'inta ta d'auko kayan bacci,sanda ta gama shirinta saman gadon ta haye abunta ta kwanta,nan take kuwa gajiyan zirga²n biki had'e da bacci suka fara kawo mata ziyara,can a cikin bacci taji mutum kusa da ita,ba tare data damu ba ta juya abunta sai dai tayi shiru ne kawai amma duk motsin sa a gurin tana ji,dan da tun dawowar sa tuni taji b'acin ya gudu dan fargaba.
Shigowarsa kenan ya tarar da ita harta kwanta,nan ya tako cikin nutsuwa zuwa bakin gadon ya zauna,ya shafe lokaci mai d'an tsayi a zaune sannan ya juya shima ya kwanta nan kusa da ita yana karanto addu'o'in kwanciya barci,cikin k'ank'anin lokaci da kwanciyar sa nan ya soma jin wani irin sanyi na taso masa tun daga ainihin cikin k'ashinsa zuwa saman jikin nasa,tamkar mai zazzab'i haka jikinsa ya soma neman rikicewa,matsawa yayi ya manna jikinsa da nata dan yadda yake ji a lokacin kamar ba duniyar bil'adama yake ba,wani irin rawa da jikinsa ya fara kuwa a lokacin nan yasa Sajida da dama ba baccin take ba,mik'ewa ta zauna tana binsa da kallo,cikin rikicewa ta fara kiransa
"Yah Prince..!"
Bai samu damar amsawa ba,sai ma dad'a matsawa kusa da ita da yayi yana rik'o ta zuwa jikinsa,irin rik'on tsaurin da yayi mata,yasa ta shiga shakkun anyan lafiyarsa lau kuwa..? Nan take taci gaba da kiransa tana son tambayarsa abunda ke faruwa,fizgota da yayi ta dawo ta kwanta suna fuskantar juna shi ne abu na biyu da ya sake bata tsoro,dan a lokacin kam ta kai mak'ura wajen firgita,cikin muryar razani ta shiga kiransa
"Yah Princ...!"
Bata k'arasa ba taji ya katse mata maganar da take shirin yi ta hanyar had'e bakinsu guri d'aya,cikin wani irin yanayi da salo mai wuyar fassara ya shiga aika mata wasu irin zafafan sak'onni masu wuyar fasaltuwa,mintuna sun ja suna a haka har lokacin kuma suna kan aikin abu guda,da sarrafa juna ta hanyar da take halattaciya,lokacin da suka kai makur'a a wannan gefen ne Yarima yayi nufin k'arasa aikin da ya d'aukar wa kansa dama ita kanta sajidar da take cikin wani irin mawuyacin hali,sai dai ko da yayi wannan nufin yana cikin karanto addu'ar da annabi (S.A.W) ya koyar damu yayin saduwa da iyali,tuni komai ya lalace,duk wani plan nasa daya gama tsarawa a wannan lokaci tuni ya rushe,dan yadda ya koma tamkar mace a wannan fagen,wannan shi ne mafarin *AL'AMARIN...................!*
*Alhamdulillah..! Alaa kulli haliin..!*
*Duka² masoya anan nake kawo k'arshen wannan littafin kashi na farko,abunda nayi dai² fatan rabb yasa mu had'u a lad'an,inda nayi kuskure kuma rabb ya yafe mana.*
_Kamar yadda na fad'a ne tun da jimawa,duk da yau d'in nayi posting a late,na tafiya hutu saboda gabatowar watan ramadhan,yau Allah ya kawo mu lokacin,ina fata tare da addu'a ga duka d'aukacin al'ummar musulmi dake fad'in duniyar nan,akan rabb ya bamu ikon yin ibada karb'ab'b'iya,Ubangiji yasa yadda zamu shiga wannan wata lafiya ya bamu ikon ganin k'arshen sa lafiya ameen..._
_Sai mun had'u bayan sallah da yardar Allah inda zaku jini tafe a cikin kashi na biyu,,,na kasa labarin biyu ne badon komai ba sai dan nasan ta haka ne kawai masoya zaku iya tunawa da inda muka kwana,kuma ku bambance inda ya kamata mu d'ora,fatan Allah yayi mana tsawon rai mai amfani._
*Duk wani mafita da k'arshen makirci yana nan tafe a cikin k'ashi na biyu da yardar Allah..*
_Mu tara a bayan sallah idan mai duka ya nufa.._
_Na gode...Fatan za muyi ibada lafiya kuma muyi sallah lafiya.._
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Tak'abalalla minna wa-minkum...*
_Happy Eid-el'fid'r to u and ur family may Allah accept our du'a and may he forgive our sin's,may we live to witness more with sound health and wealth...Ameen_
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 1.*
^^^^^^^^
Wani irin mugun juyi yayi wanda ya haddasa masa komawa gefe guda ya kwanta yana curewa guri d'aya tamkar kayan wankin da suke jiran mawankin da zai fiddasu daga k'angin daud'ar da suka fad'a,mararsa ya damk'e saboda tsananin ciwon da take masa a daidai lokacin,wanda cikin k'ank'anin lokaci yasa shi manta a inda yake dama duniyar da yake ciki,a hankali bakinsa ya soma motsawa cikin rauni ya shiga kiran sunan YASEER,wanda a iya hasashen da nayi nake da tabbacin tsakaninsa da shi tuni duniyoyinsu suka jima da yiwa juna bankwana,haka zalika a wannan lokaci kam na tabbata babu ta yadda za ayi ya iya sanin halin da d'an uwan nasa yake ciki.
Gareta kuwa itama sajidar ba'a barta a baya ba,dan tunda taji yarima ya mirgina gefenta ya kwanta yana sakin wani irin numfashi ta runtse idanunta cikin wani irin mawuyacin hali itama ta shiga sauke numfashin wahala,sai dai ko da jin muryar Yariman sanda yake kan kiran YASEER bata fita sosai,da kuma jin sunan wanda yake kira,tuni hakan yasa tayi hanzarin bud'e kulallun idanunta da suka mata nauyi ta juya gare shi tana zubasu a kansa,koda tayi arba da halin da yake ciki,ai take ba tare data tsaya tunani ko jinkiri kan halin da take ciki ba ta matsa inda yake tana tallafo kansa,cikin kid'imewa take jifansa da tambayoyin da bata san suna fita daga bakin nata ba
"Yah Prince what's going wrong..?? Are u alright...??"
Duk tambayoyin tana yi masa sune amma ba tare da tana cikin nutsuwarta ba,haka sai duddubawa take duk dan ta gano inda matsalar take,sai dai da yake ba b'angaren ta bane hakan yasa ta gagara ganowa.Cikin muryan majinyata yake mata alama da hannu kan ta kira masa YASEER a waya ta sanar da shi yana nemansa,saurin amsa masa tayi sannan ta ja masa blanket ta rufeshi kana ta sauka a kan bed d'in,wayansa ta d'auko ta shiga neman line YASEER amma ina ko labarin zata same shi babu dan tana kira baturiyar nan ta company ta shiga sanar da ita wayan nasa na a kashe,wani mugun tsaki ta saki mai had'e da furzar da zazzafar iska,ta gwada kiran lines d'insa yafi a k'irga amma duka babu wanda ta samu,ko da ganin haka sai ta yanke shawaran fita da kanta zuwa side d'insu YASEER d'in,dan yadda taga yana sake galabaita wannan ne kad'ai hanyar da take ganin za'a samu sassauci idan har ta samu damar yin arba da YASEER d'in,wannan tunanin shi ya bata k'warin guiwar daya sata d'auko riganta doguwa har k'asa ta saka sannan ta zari slippers da hijab d'inta ta fita,tafiya kawai take ita d'aya ta kama hanyan apartment d'in amma ko k'waro bata had'u da shi ba bare mutum duk kuwa da yadda gidan yake cike da masu tsaro,a bakin k'ofar apartment d'in ta tsaya ta shiga knocking,ta d'an d'auki lokaci kafin aka bud'e k'ofar,YASEER ne da kansa ya bud'e k'ofar,ko da ganinta a irin wannan lokacin take ya fahimci ba lafiya ba,dan haka bai yi jinkiri ba wajen jifanta da tambayar
"Sajida lafiya..?? Na ganki a irin wannan lokacin..?? Me yake faruwa..??"
Hawayen daya ziraro mata tasa bayan hannu ta goge ko kafin ta bashi amsa tuni har yayi gaba ya barta a nan a tsaye dan ya gama fahimta a kwai damuwa,sanda ta juya kuwa da niyyan yi masa magana tuni ta hango shi har yayi nisa,a baya ta biyo shi cikin sauri,dan sai lokacin nema ta fara jin tsoron fitowa da tayi a irin wannan talatainin daren,sauri ta k'ara duk dan ta tarar da shi amma duk da haka bata iya tarar da shi d'inba,sai data shiga apartment d'in nasu sannan ta ganshi tsaye a parlor ya goya hannayensa a baya yana safa da marwa
"Yana ina ne.???"
Ya tambaya dan yadda zuciyarsa ta gama bayyana masa matsala tana tattare da d'an uwan nasa,ba tare data bashi amsa ba ta wuce gaba,nan yayi saurin biyo bayanta zuwa cikin bedroom d'in,can a saman bed ya hangoshi ya cukuikuye sai numfarfashi yake kamar na mutumin da yake gargarar mutuwa,saurin nufarsa yayi yana kiran sunansa,Yarima kuwa ko da ya jiyo muryar mutumin da dama shi yake da buk'atan gani nan ya shiga k'ok'arin bud'e nauyayyun idanunsa masu cike da tsabar ciwo,sannu YASEER ya fara jera masa kafin ya kalli sajidar dake rab'e daga gefe guda yana jikanta da tambayar
"Me yake damunsa..??"
Bata iya bashi amsa ba saboda yadda takemin nauyin abunda zata ce ya faru,yadda ta sunkuyar da kai k'asa ya sashi kallon yarima sannan ya furta
"Kawomin lime da sauri.."
Ya bata umarnin ba tare daya kalleta ba,fita tayi da saurinta har tana yi kamar zata fad'i k'asa dan saurin da take yi,YASEER ne ya zauna daga gefen Yarima yana kallonsa kafin ya jefo masa tambayar
"Akwai inda yake maka ciwo ne..??"
Da hannu ya masa nuni ba tare daya iya furtawa ba,yana shirin sake tambayarsa sajida ta shigo hannunta d'auke da cup mai cike da ruwan lime juice,hannu ya mik'a ya karb'a sannan ya ajiye ya matsa kusa da Yarima ya d'an d'ago shi,sai daya tabbatar ya shanye duk iya yadda yake matsar fuska sannan ya rabu dashi,ba'a wani d'auki lokaci mai tsayi ba gumi ya fara yanko masa,ya jima a wannan halin duk da irin sanyin da d'akin yake d'auke da shi sannan ya iya zama sosai har yana jingina bayansa ajikin bed d'in yana sauke numfashin wahala,sannu suka shiga jera masa kafin daga bisani YASEER en bayan ya tabbatar da komai lafiya yayi musu sallama ya tafi,bayansa tabi da niyyar ta rufe apartment d'in sannan ta dawo lokacin kuwa tana dawowa ta tarar da d'akin wayam babu Yarima bare dalilin sa,bakin bed ta zauna zuciyarta cike da tunanin abunda ke faruwa,ta jima zaune tana tunane² sannan ta tashi ta cire hijab d'in data sa da rigan sannan ta nemi guri ta kwanta,zuciyarta da tunanin dawowar Yariman.
Lokacin da suka fita kuwa a gefen Yarima tsam yayi ya mik'e ya fice a d'akin,direct bai tsaya ko ina ba sai bedroom d'insa,yana zuwa kuwa ya nufi toilet had'e da sakarwa jikinsa ruwa mai sanyi,yadda ruwan yake ratsashi haka kasala ke dad'a rufeshi,ji yake a lokacin banda kwanciya babu abunda yake buk'atan yi,towel ya d'aura yana fitowa kuwa ya nufi closest ya cire wasu pajamas d'in masu kalar sararin samaniya,bayan daya shirya kuwa nan ya haye saman royal bed d'insa yayi kwanciyar sa,bai jima da kwanciyar ba kuwa bacci mai nauyin gaske yayi gaba da shi cike da mafarkai..
^^^^^
Lokacin da Adda tazo k'arshe a labarin da take bawa Aisha dangane da lak'arsu da ROYAL PALACE kuwa,ko da suka gama tattaunawa sai Adda'n tayi mata sallama akan zata tafi ta kwanta saboda ganin dare daya soma nisa,ga Aisha kuwa a lokacin ji tayi sam bata so ace lokacin ya zo a haka ba,dan yadda ta so ace Adda ta labarta mata har asalinta,la'alla ta san asalinta da inda iyayenta suke,duk da dai ta fara jin k'ishin² d'in inda asalintan ya fito,ma'ana dai ba iyayenta ne suka bada ita ba kamar yadda ladidi ta fara sanar mata tun a wancan lokacin daya gabata,ta dai yi mata k'arya ne da hakan ba don komai ba sai don wani k'udiri nata,hak'uri ta bawa ranta amma ba don taso hakan ba,a son ranta kam taso ace suyi ta zama da Adda har sai taji k'arshen labarin,sallamar itama tayiwa Adda sannan kowanne a cikinsu ya kama hanyar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 63