fuskarta tana sake bin jeeddan da addu'o'in neman tsarin Ubangiji.
Fitarsu a gidan direct sanda suka isa apartment din Ummi suka nufa da ita,kuma har lokacin bata bar kukan da take ba,kamar wacce za'a bar gari da ita,tun daga shigowar su Ummi ta kalleta fuskarta da wani irin farin ciki mara misaltuwa ta tare su,bayan ta amsheta ta sallame su suka fice nan aka barsu daga ita sai jeeddan haka tayita lallashinta har ta samu tayi shiru,da kanta ta kaita wani d'aki tare da y'an kayanta da Inno ta had'a mata,bayan nan ta fita ta barta bayan ta shaida mata a nan zata ci gaba da zama,amsawa tayi da girmamawa sannan Ummi'n ta fita ta barta.
Tun daga wannan ranar da aka kawo jeeddah gidan Ummi ke kula da ita,ta b'angaren Ummah Fulani kuwa specialist masu gyaran jiki tasa aka d'auko mata wanda a k'asar 9ja babu inda ba'a san da zamansu ba,nan ta basu order a soma gyara jeeddan,cikin k'ank'anin lokaci kuwa suka shiga aikinsu kamar yadda aka umarcesu a haka har aka kwashe tsawon sati biyu ba tare da tana lak'a ko da k'ofar parlor ba.Tun daga zuwanta gidan kuwa wani tsaro na musamman aka sa mata duk dan kada ta fita,duk da can a k'asan ranta tana jin kewar Inno'nta musamman a d'an wannan tsakanin da take zaune daga ita sai halinta bata ganin kowa sai masu yi mata gyaran jiki,duka kwanakin jinta take kamar tayi wasu shekaru bata ga Inno'n ba a haka taci gaba da zaman hak'uri.
Yauma a haka masu gyaran suka zo suka isketa tayi shiru sai y'an siraran hawaye da take scrubbing,har aka mata abunda aka saba bata ko ce musu ci kanku ba duk da yadda suke ta zuzuta irin kyaun da tayi,sai dai bata kula su ba har suka gama suka fice,hijab d'inta dake gefe ta harara dan yadda take jin a lokacin komaima tana jin haushin sa,ga haushin an rabata da Inno ga kuma haushin kullen da ake mata,har ta mik'e zata shiga bathroom ta kama ruwa taji apartment d'in shiru,zuciyar ta har wani tsalle take mata dan tsoro da fargabar abunda take shirin aiwatarwa,a hankali kuma kamar wata mara gaskiya ta juyo da sauri ta cafki hijab d'in cikin gaggawa ta zura shi a jikinta sannan ta d'auki nik'ab ta d'aura,sad'ad'd'afawa tayi a hankali ta bud'e k'ofar d'akin nata har ta gama fitowa parlor,bata iske kowa ba a ciki dan haka taci gaba da bin gefe tana moving forward akan toes d'inta,cikin sa'a har ta samu damar ficewa a apartment d'in ba tare da wani ya ganta ba,sanda ta tabbatar ta kamo hanyar gidansu wani irin sauri ta d'auki yi mai kama da gudu²,a haka ta shigo line d'insu ba tare da jiran komai ba tayi zaraf ta shige gidansu tana waiwayen bayanta da dubawa ko zata ga wani data sani tayi saurin b'uya kada a ganta akai labarinta.
Babu kowa a tsakar gidan sai dai tana jin alamun motsi a d'akin ta dake bud'e,da sauri ta nufi d'akin tana shiga ta maida k'ofa ta kulle har tana lek'awa ta d'an k'aramin window d'insu,Inno dake sunkuye ne tana duba wasu y'an kayayyaki taji motsin mutum a bayanta da saurinta ta waigo tana duba meke faruwa,ai tana d'agowar kuwa suka yi ido hud'u da jeeddah dake tsaye hannunta d'age da nik'ab d'inta.
Jikinta jeeddah ta zube take hawaye suka fara overflowing daga idonta har ta wani irin abu kamar zata shid'e,ita kanta Inno ganin irin kukan da take saida ta sata hawaye,sun jima a cikin wannan halin kafin da kyar ta rarrasheta tayi shiru,a hankali take sauke ajiyar zuciya,kamar ance Inno ta sake kallonta ai kuwa nan take ta hango ma kanta abunda yaso firgitata,da sauri ta d'agota tana sake k'are mata kallo,cikin had'e fuska ta kalleta tana cewa
"Jeeddatu..! Me zan gani..??''
Ita kanta jin yadda ta kirata sai data so tsorata,idanunta a fili take wulga idanun cike da pampering take kallon Inno
"To ni Inno...Me nayi ne..??"
Ta tambaya tana chanja face zuwa yanayin kuka dan dama tana kan jin zuciyar ta bata sauka daga yanayin da take ciki ba,b'ata fuska Inno tayi kafin ta kalleta
"Yaushe rabonki da shafa man dana baki..??"
Shiru tayi tana sunkuyar da kai k'asa,nan take Inno ta fahimci akwai wani abu
"Dake nake magana kin min shiru..?? Wato abunda na hanaki shi kikaje kika yi ko..?? Anya jeeddatu..! Shi kenan ai kiyi duk abunda kika ga ya fiye miki,idan kika kuskure wani abu ya faru kada kiyi kuka da ni.."
A hanakali wasu kananan tears suka sake tahowa tayi saurin sa gefen hijab d'inta ta d'auke su tana sakin ajiyan zuciya ganin yadda Inno ta b'ata rai yasa jikinta yin sanyi,a hankali ta kamo hannunta a cikin nata
"Allah kuwan ko ba laifina bane fa..bayan sune suka ce wai bazan na shafa maiba,kuma ko nayi niyyan sawa sai su hanna ni,har cewa suke min wai ina da kyau,,ni dai Inno ki dawo dani gida bana son zama a can,kullum fa idan ban ganki ba sai nayita damuwa gashi sun hanani fita ko parlor ma..Dan Allah Inno na ki je ki dawo dani gida kinji..??"
Ta fad'a kamar zata yi wani kukan tana ta rausayar da kai,tausayinta ne ya kama Inno har ita kanta bata san lokacin data d'auka tana kallon y'ar tata ba,hannunta da jeeddah ta sake rik'owa k'am cikin nata yasa ta farga ta kalleta
"A'a Jeeddatu na baza muyu wa Ummi haka ba,kinga ita tace akaiki ni yanzun bani da hurumin da zan canja musu ra'ayi,ko kuwa kina so ki ganni a halin damuwa..??"
Saurin girgiza kai tayi tana kallonta with roundish almond eyes nata
"Yanzun dukama ba wannan ba an san kin fito..??"
Sake girgiza kai tayi ai kuwa take yanayin fuskar ta ya sauya,cikin sauri ta kama hannunta tana cewa
"Maza tashi to ki koma kadama Malam ya shigo ya tarar dake,ko can su neme ki su rasa."
"Nifa Inno bazan koma ba gaskiya,na gaji da zama a can..!"
"A'a..! Jeeddatu kada na sake jin kin ambaci haka,komawa ma yanzun nan zaki koma,tun kafin a nemeki maza kiyi sauri ki koma kinji ni ko..??"
A salub'e ta gyad'a kai tana ta faman k'ok'arin mayar da nik'ab d'inta while her almond eyes were full da ruwan hawaye na jik'a.Duk abunda take Inno na kallonta,banda tasbihi da neman tsarin Allah babu abunda take nemawa jeeddan har ta kammala abunda take tana ce mata
"Na tafi to..!"
A hanakali ta gyad'a mata kai,bayan ta mata fad'an ta kula da kanta,haka ta juya ta fice jiki a salub'e ta bar Inno da binta da ido,sanda Inno ta tabbatar ta kama hanyar komawa sannan ta sauke nauyayyun ajiyan numfarfashi kana taci gaba da y'an aikace² data fara,tana yi tana jin kewar yarinyar tata da samuwa mai tsananin akan wasu abubuwa gami da fargabar wani abu da take b'oyo can daga k'asan zuciyar ta.
Can a cikin gida kuwa tuni Ummi take knocking k'ofar d'akin da jeeddan take tana son suyi magana,sai dai taji shiru har sanda tayi tunanin ko sallah take ko kuma wanka,dan haka ta koma parlor ta zauna tana jiran taji motsinta amma kusan awa guda shiru babu ko alamunta,hankalinta a tashe ta koma bakin k'ofar tana sake kiranta had'e da kwankwasawa amma shirun har ya soma yawa,sosai hankalinta ya d'an tashi,nan ta shiga kiran hadimanta sai dai duka babu wanda yasan inda take dan sun tabbatar mata basu ga wulgawarta ba,ana cikin haka sai gata ta shigo tana sunkuyar da kai dan tun shigowarta ta fahimci abunda yake faruwa,akan idon Ummi'n ta wuce sai dai bata ce da ita komai ba,haka bata mata fad'a ko tambayar inda taje ba,dan ta fahimci y'an kwanakin tana cikin damuwa.Tun daga wannan lokacin sai tsaron da ake mata ya sake nunkawa sai dai lokaci zuwa lokaci Ummi ta kan aika Inno tazo,hakan kuwa ba k'aramin dad'i yayiwa jeeddah ba tunda yanzun ta samu damar ganin Inno akai² shi yasa ma har ta d'an rage damuwa.
Kwanaki sun tafi ki da zuwan jeeddah a gidan ma yanzun kimanin sati uku kenan,wanda a kullum irin gyara da cimar da take samu duk da abayama tana samu na yanzun yafi na baya,cikin wannan d'an lokacin kuwa tuni ta sake gogewa jikinta wani lokacin ita kanta idan ta kalla har sha'awar yake bata,sai dai bata tab'a yarda ta fito ko ta had'u da wani face tana sanye da zumbula²n kayantan nan na gado.Cikin haka ne kwanakin dasu Ummi suka d'iba na hidimar bikin suka gabato.
Yau kasancewar ranar ta jumu'ah ce da ake kan tsananin zafi da rana saboda yanayin garin ana cikin summer season ne,duk da lokacin safiya ne duk wanda ka kalli fuskarsa zata iya bayyana maka irin yanayin da ake ciki,,,,,a can cikin gida kuwa taro ne na ainihin su yasu y'an gidan mata,yayin da maza ke can a harabar babban masallacin jumu'ah dake garin,misalin k'arfe 2 saura aka idar da sallah bayan dogon lokacin da aka d'auka ana khud'uba,sanda aka idar da sallah ne babban imam ya ahiga shaidawa jama'a d'aurin auren da za'a gudanar,wanda a cikin k'ank'anin lokaci ba tare da b'ata lolaci ba aka fara abunda ya tara al'ummah dominsa,dan yadda jama'a ke Allah² a idar da sallah ma su kama gabansu saboda zafi,ak'alla d'aurin aure sama da biyar ne a masallacin a wannan lokacin,,,sai dai d'aurin auren Yarima shi ne kan gaba kafin nan ragowar su biyo baya,,,maimartaba kam na a sahun gaba daga kusa da shi gefen dama Abba GALADIMA ne da Abba Matawalle,sai wasu daga cikin manyan y'an majalissar sarki da kuma manya daga cikin gwamnatin jihar,fadawa kuwa a wannan ranar sun samu abunda suke buk'ata,nan a bakin masallaci suka yi cincirindo sai fadanci suke suna kuma jiran fitowar manyan garin,bayan addu'ah daga bakin Imam,siga aka fara gudanarwa bayan bayyanar al-walin amarya da ango da kuma shaidu,bayan nan imam ya sake yin addu'ah aka mik'a sadaki zuwa ga alwalin amarya wanda ya kasance Abba Matawalle,daga nan Imam da shaidu suka tabbatar da k'ulluwar auren *YARIMA YAZEED* tare da *HAWWA JEEDDAH* akan mafi ingancin sadaki kamar yadda Addini da shari'a ta tanada,daga haka kuma aka ci gaba da gudanar da sauran d'aurin auren da sukai saura a lokacin.....................
*Afuwaan fan's yau kam bamu samu wuta ba wollah shi yasa duka typing d'in ya zama wani iri...*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Just for u my WhatsApp fan's,,masu son nayi posting da masu cewa zasu haihu idan banyi posting ba,duk kuyi hak'uri,hutu ne naso na d'anyi ko da na 2 days ne😉,buh na fasa kada ace smasher ce ta janyo haihuwa kusa😁,nd ban kama suna ba aradu kada ma ace nace..Have fun my fan's u have me,i have u..👌*
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 17.*
^^^^^^^^
*#Liberty*
Dai² an gama d'aurin aure na shiga watsa ido with affection of finding Yarima YAZEED,buh it's harder a cikin wad'annan millions of pepz d'in na iya bincika shi,a haka har aka kammala sauran d'aurin auren sannan taron jama'ar suka fara fashewa,tun daga first gate na masallacin his bondmen ke take masa baya suna watsa masa kiraki da suke nuna alamun wata rana shi ne magajin ABU YAZEED,fitowarsa kad'ai na iya detections yana cikin wani soft bazin getzner milk color tun daga sama har k'asa wankan color d'aya ne tak,ma'ana dai milk d'in sai aikin jiki da aka d'an ratsa masa coffee color,yayin da hannunsa ke d'aure cikin lanka ptp wristwatch rose gold,banda k'amshin turaren polo supreme oud dake fita a jikinsa babu abunda zaka ji idan ka kusan to shi,kallo d'aya tak ya isa sawa mutum ya gane shi d'in first class ne,irin wad'anda samun irinsa ba k'aramin wahala mutum zai sha ba kafin a binciko na biyunsa,YASEER daga gefensa na dama shima cikin shigar kingtrend bazin getzner which is brown in color,shima yayi masifar kyau a wannan lokacin har ba'a magana,nan fa mutane suka musu caa akai kowa so yake ya zama na gaba a gurin yima ango Allah ya sanya alkhairi,wasu kam duka daga ciki daka kalli fuskokinsu a cikin wannan masu trembling d'in duk zaka san y'an neman a samu labarin yad'awa a duniya ne,a k'alla taron ya tara mutane da dama kuma mabambanta kamar yadda suka fito k'abilu mabambanta.
Daga nan katafaren hotel d'innnan na BRISTOL PALACE aka dunguma coz a can ne za'ayi banquet,su YASEER kam shi ne kan gaba akan komai,dan haka ranar ba su suka samu kansu ba sai wajen Maghreb,sanda suka dawo gida kuwa a matuk'ar gajiya suka iso gidan,dan haka direct apartment d'in Yarima suka nufa suka yada zango a parlor,shima kuma basu wani jima ba dan yadda kowanne ke k'orafin ya gaji wa d'an uwansan.
A cikin gida kuwa gefen Hajiya taro ne na manyan mutane y'an zuwa mata Allah ya sanya alkhairi da y'an uwa,dai² sanda aka gama d'aurin aure bayan da aka dawo daga banquet,maimartaba,Abba GALADIMA da Abba Matawalle cikin gidan suka nufo,ko da zuwansu nan suka nemi ganawa da Hajiya,a main parlor suka had'u dukansu,sai anan nema Abba maimartaba yasa aje azo da Inno da Sarkin kasuwa,ma'ana dai iyayen Jeeddah,dai² sanda Hajiya ta shigo ta iske su Ummi suma a zaune suna jiran k'arasowarta dan a lokacin itan kad'ai ake kan jira,fuskarta d'auke da farin ciki sosai data gansu a had'e itan suke jira,haka nan alamun data hanga a fuskokinsu ya tabbatar mata da an riga an d'aura auren tuni,exchange na greetings suka yi kafin daga bisani Abba Matawalle yayi musu jawabin an d'aura auren,after kuma ya mik'a sadaki a hannun Hajiya,cas ta tusa kud'in inda ya kama naira dubu d'ari,ai take hajiya ta rangad'a gud'a saboda farin cikin da take jinta a ciki,sosai ta sasu nishad'i su kansu iyayen har basu san lokacin da suka sake ba fuskokinsu suna sake nuna hakan,sai a nan maimartaba yayi gyaran murya,hankulansu ne suka koma gare shi dan sun fahimci there's an ample enormous da yake kan son ya shaida musu,d'an murmushi maimartaba ya saki da ba kowa ne zaiyi saurin gano hakan a tattare da shi ba kasancewar akwai turban a kansa daya kewaya har bakinsa duka a rufe suke
"Jama'a Assalamu alaikum warahmatullah..!"
Duka suka d'auki amsawa,bayan nan maimartaba ya sake kallon su yana jin wani irin delighted dake ratsa jikinsa sannan yaci gaba da magana
"Alal hak'ik'a zamu d'anyi wata magana ne data zama dole a gare mu,sai dai ba wani mai yawa bane abunda zamu ce d'in,mun sani cewa wannan abu da muka aikata na aure akan d'anmu baya daga cikin abunda addini ya halartar har sai an samu d'ayan sharud'a guda biyu,na farko addini ya yardar mana mu aura daga kuyanginmu abisa tsoron fad'awa zinah,na biyu kuma addini ya amince mu auresu ne idan har mun samu rashin samun wadatar auren 'yar kamar yadda aya ta ashirin da biyar(25) a cikin suratun nisa'i ta nuna mana in da Allah (S.W.T) yake cewa "Waman lam yastad'i'i minkum d'aulan an-yankihal muhsanatil mu'uminati faminma malakat aymanukum min fatayatikumul mu'uminaat,wallahu a'alamu bi'iymanikum,ba'adhukum min ba'adh,fankihuhunna bi'izni ahlihinn,wa'aatuhunna ujuurahunna bil-ma'aruufi muhsanatin ghaira musafihatin wala muttakhizati akhdaan,fa'iza uhsinna fa'in ataina bifahishatin fa'alaihinna nisfu maa alal muhsanati minal azaab,zalika liman khashiyal anata minkum,wa'an tasbiruu khairan lakum,wallahu ghafurun rahiim."
Ma'ana "Kuma wanda bai samu wadata ba daga cikin ku bisa ga ya auri 'ya'ya muminai,to (ya aura) daga abunda hannuwanku na dama suka mallaka,na daga kuyanginku muminai.Kuma Allah ne mafi sani ga imaninku,sashenku daga sashe.Sai ku aure su da izinin mutanensu.Kuma ku ba su ijarorinsu bisa ga abunda aka sani,suna masu kamun kai ba masu zina ba,kuma ba masu rik'on abokai ba.To,idan aka aure su,sai kuma suka zo da wata alfasha,to akwai a kansu rabin abunda ko a kan,'ya'ya na daga azaba.Wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsoron wahala ne daga gare ku.Kuma ku yi hak'uri shi ne mafi alheri a gare ku.Kuma Allah mai gafara ne mai jin k'ai.."
Saboda wannan hujja ne da Ubangiji (S.W.T) ya kafa mana a cikin al'qur'ani ne muma muka ga dacewar aikata hakan ga d'an mu saboda gudun afkuwar wasu al'amura a nan gaba,dama wanda suka faru a baya,munsan kun san abunda ya faru ba sai mun maimaita ba,akan wannan dalili ne kuma muke son muyi amfani da wannan damar ta hanyar amfani da abunda muka mallaka,saboda haka muke fatan sanar daku hukuncin da muka ga ya dace a garemu,daga wannan lokacin muna sanar daku cewa kamar yadda wannan yarinya da iyayenta suka yi mana wannan abun alkhairi da muka rasa daga sauran al'ummah muke sanar daku mun y'anta wannan yarinya abisa biyayya da tayi mana tare da ita da mahaifanta...Wannan shi ne hukuncin mu,muna fatan kuma hukuncin mu zai zama karb'ab'b'e a gurinku..Shin akwai wani mai magana.."
Jinjina kai kawai suke cike da tsantsar farin cikin wannan al'amarin wanda yake mara misaltuwa,ga Inno kuwa hawaye ne ke kwaranyowa daga idanunta saboda tsantsar farin ciki mai tafe da wani irin feelings da bata san ko daga ina yake zuwa mata ba,tabbas ta sani a tsawon rayuwarta wannan rana itace mafi girma a gurinta wacce bazata iya kwatanta ta da wasu rakun ba,shi kansa sarkin kasuwa a nasa gefen ko kad'an ya kasa furta komai sai dai jinsa yake wani na daban a yau,banda murmushin farin ciki babu abunda yake ajiyewa sai dai ya kasa magana,a hankali wasu hawaye suka d'an sakko masa yasa hannu ya d'auke su,Inno cikin sheshshek'ar kuka ta d'ago idanunta har lokacin da wasu delighted tears,murya na karkarwa ta shiga fad'in
"Mun gode² ranka shi dad'e, tabbas bamu da bakin da zamu iya yi maka godiya abisa wannan abun alkhairi da karamcin ka a garemu face fatan samun tsawon rai daga gurin mahaliccinmu,mun gode Yallab'ai yasa a gama da duniya lafiya.."
Duka gurin babu wanda baiji wani irin farin ciki ba,haka nan da kyar aka samu Inno tayi shiru,Sadakin dake hannun Ummi aka mik'awa Inno amma fir tak'i amsa,k'arshe ma sai cewa tayiwa da Ummi ta ada mata ita bata san ya zata yi dasu ba idan an bata,b'angaren Babanta ma haka yayita godiya ga maimartaba da duka ahalin sun,shi kansa maimartaba sai da yaso jin kunya dan a gareshi wannan bayin Allah'n sun wuce haka,sai da suka tattauna akan abubuwa da dama ciki har da taso da zancen irin taimakon jeeddah ga yarima tun shekarun da suka gabata,wanda sai lokacin maimartaba ya tuna sun tab'a magana akan ta fad'i duk abunda take so zai mata amma sai ya manta a dalilin nauye² dake kansa,itan kuma Allah baisa ta dawo ba bare ta sanar masa,wannan ya dad'a tabbatar masa lallai ba kowa ne d'an Adam ne yasan karamci a rayuwarsa ba,daga nan kuma maimartaba ya sallami kowa nan duka suka fashe aka barshi daga shi sai Abba GALADIMA,suka ci gaba da tattaunawa akan al'amuran yau da kullum da kuma al'amuran da suka shafi mulki.
Ummi kuwa tare suka fito da Inno daga nan apartment d'inta suka nufa,kai tsaye d'akin da jeeddan take suka shiga sai dai basu tarar da ita a ciki ba tana cikin bathroom,dan haka Ummi juyawa tayi tana cewa Inno ta jirata tana dawowa,dai² Ummi tana fita Jeeddan kuma tana shigowa hakan ya tabbatar da sun tafka sab'ani kenan,kamar ance ta d'ago ta kalli saman resting chair ai kuwa nan ta hango Inno zaune ta rafka tagumi,shewar murna ta saka tana fad'awa jikin Inno
"My cweet Inno...jiya duka ban ganki ba,na shiga damuwa sosai,har da nace yau idan baki zo ba saina je na ganoki sai gaki.."
Tana daga jikin Inno take maganar ba tare data kalli conditions d'in da take ciki ba taci gaba da magana abunta
"My Inno ina Babana..?? Shima ina kewarsa sosai..Yaushe zan ganshi..??"
Surutu take ta faman zubawa har lokacin,sai dai jin shirun yayi yawa yasa ta d'agowa a hankali da mamakin abunda ya hana Inno yi mata magana kamar yadda ta saba a duk lokacin da tazo.Kyallin hawayen data gano a idanun Inno ne ya sata zabura ta mik'e zaune tana k'ure Inno'n da wani kallo with her roundish almond eyes,in startling of Inno's situation ta fara magana idanunta suna tara ruwan hawayen itama
"Dan Allah Inno kiyi hak'uri wollahi bazan kuma fad'a ba tunda har bakya so,Allah kuwan na dena cewa zan fita kinji..bazan k'ara ba..!"
Kallonta Inno tayi tana sakin ajiyar zuciya kafin ta kamota zuwa jikinta tana sakin numfashi
"Ko kad'an baki yimin laifi ba bare har yasa ki fara bani hak'uri.. Ba laifin ki bane y'ata.."
Cikin wani irin yanayi ta sake kallon Inno'n
"To amma me yasa kike kuka..??"
Girgiza kai Inno tayi mai tafe da wani irin murmushi da yayi penetrate ta tsakanin lab'b'anta,hakan da tayi ai sai ya sake jefa zuciyar Jeeddah cikin rud'ani
"Dan Allah Inno ki fad'a min abunda ya faru,ina jin damuwa na rufeni.."
Murmushin ta sake saki,kafin ta sake k'ank'ame Jeeddan tana sa mata albarkar da bata san dalili ba,sun shafe tsayin lokaci a haka kafin ta kamata ta zaunar tana kallonta da goge mata y'an slender tears dake sakko mata,sai da Inno ta bari ta komawa nutsuwar ta sannan ta shiga bata labarin abunda ya faru yanzun a gefen Hajiya kafin zuwansa,wani irin feelings ne ya soma taso mata mai tafe da hawayen tsantsar farin ciki,da wani irin speed jeeddah ta sake k'ank'ameta saboda yadda take jinta wata mai y'anci a yau,haka suka shafe lokaci mai tsayi suna shan kuka abunsu kafin suka koma sharewa juna hawaye,sun jima cikin wannan yanayin kafin aka yi knocking door d'in.
^^^^^
Babu wani shagali da ake shirin yi dan Yarima da kansa ya nuna baya son duk wannan taron coz shi ta kansa yake,nd he didn't know game da larurar dake tare da shi,ya samu sauk'ine ko kuwa bai samu ba,dan haka ya yanke wa kansa ko da za'ayima tofa shi babu sa hannunsa a ciki,Ummi kad'ai ya iya sanarwa damuwarsa wanda itama already taso tayi maganar sai dai tayi shiru ne,sai kuma shi d'in yazo mata da maganar,wannan dalilin yasa data yi magana da masu gidan aka dakatar da komai kamar yadda ya buk'ata,nan aka bar komai akan daga d'aurin aure sai tarewarta.
Misalin k'arfe 9:00pm bayan ta gama shiryawa cikin wani chiganvy atamfa mai kyan launuka da suka amshi jikinta,Ummi da Hajiya suka sata a gaba bayan Inno da babanta sun mata nasihar zama lafiya a d'akinta sannan suka mata addu'ar zama cikin salama,a wannan halin kuwa da ake ciki jeeddah kam banda kuka babu abunda take dan har lokacin babu wani da ganganci yasa ya sanar da ita ainihin wanda aka aurar da ita gareshi,sanda duk suka gama mata nasiha'n sai ga Umma Fulani da kanta ta ratso cikin parlour'n na Ummi a bayanta slaves
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 63