Yadda take kuka shab'e² da hawaye yasa jeeddah girgiza mata kai tana fad'in
"Shi kenan to kiyi shiru zan rakaki gidan yanzun,amma muje saimu fad'awa malam Nura bakya jin dad'i shi yasa zaki koma gida ko..?"
Amsawa tayi da to sannan ta goge fuskarta suka mik'e kowacce ta d'auki jakarta suka fice,sanda suka iske mal Nura shi kad'ai ne zaune saman wani dakali yana shan iska,har k'asa suka durk'usa sannan jeeddah tayi masa bayani,kamar bazai barsu su tafi ba,daga baya kuma ganin Aisha na kuka yasa shi cewa "to suje Allah ya k'ara sauk'i",haka suka kama hanya tiryan² har line gidan su Aishar,kamar wanda akace su d'aga kai can daga gabansu suka hango shi tsugune,kasancewar akwai yalwar Haske a area en yasa Aisha ta gane ko waye,da sauri ta koma bayan jeeddah tana k'ank'ameta
"Wayyooo! Allah jeeddah wollahi gashi nan a gabamu,mu koma k'ar yazo.."
Rik'e Aishar tayi k'arfin halin yi sannan ta juya ta kalli gurin da yake dan ita bata san waye take nufi ba,tasowa taga yayi ya nufo su,cikin firgici ita kanta jeeddan ta shiga kallonsa,duk da yadda zuciyarta ke skipping hakan bai hanata ci gaba da tsaiwa ba har ya kusa k'arasowa inda suke ba tare da sunyi yunk'urin guduwa ba
"Ke macuciya ce,munafuka,mak'aryaciya...Zaki fad'i gaskiya ko kuwa sai na kasheki....? Idan kika bayyana gaskiya nine nan ajalinki..."
Abunda yaita maimaitawa kenan yana zare ido har ya zo daf da su,ganin babu wacce tayi magana a cikin su yasa mahaukacin mik'a hannu da niyyar dank'osu duka,ai kafin kace kobo tuni sun take k'afafunsu sun ranta ana k'are basu tsaya ko inaba sai cikin gidansu can k'uryar d'akin su Aishar suka maida k'ofa suka kulle suna hakin wahala.
Babu kowa sai su kad'ai kawai a gidan dan Ladidi bata nan ta fita a lokacin,dukansu a tsorace suke da ganinsa ya haddasa musu,jeeddah ce tayi k'arfin hali ta kalli Aisha tana shirin tambayarta
"To wai ke menema had'in ki da wannan mahaukacin ko nace fatalwar dan ni dai ban san da wane suna zan kira shi da shi ba..haka kawai kin janyo ni ina zaman² na ni bada laifi ba,amma abu na neman firgitani..dan Allah kinga idan ma wani abu kikayi na badai² ba wollahi tun wuri bari na baki shawara ni dai dan bazan iya ba,Haka kawai a dalilinki a dunga tsoratar dani a banza ni bada laifi ba.."
Kuka Aisha ta fashe da shi cikin muryar kuka take fad'in
"Wollahi ni babu abunda nayi masa,haka kawaifa yake cewa wai na fad'i gaskiya,ni kuma bansan wace gaskiya ce yake nufi ba.."
"Wollahi k'arya kike kin sani,haka kawai za'a biyo ki ana cewa ki fad'i gaskiya ne idan baki yi wani laifi ba,amma ni koma mene bai shafe ni ba,idan kinga dama kya iya zama kiyi tunani har ki gano laifinki,idan kuma baki gani bama ke kika sani ni bani za'a tsorata ba...Ni kin gama tafiya zan dan kada ki ci gaba da gogan kashin kaji,Allah ya bamu alkhairi dan nima daga nan gida zan nufa na FASA komawa islamiyyar ma..."
Tana fad'ar haka ta sab'i jakarta tayi hanyar fita,cikin kuka Aisha ta biyota tana mata magiya
"Dan Allah jeeddah karki tafi wollahi tsoro nake ji na zauna ni kad'ai.."
A fusace jeeddan ta juyo tana fizge hannunta data rik'e
"Ni da Allah malama cikani na tafi,dan kina jin tsoro ni kuma saina zauna na tayaki zama duk randa babarki ta dawo daina tafi gida kome kike nufi..? To wollahi bari kiji kin jima ma baki ji tsoron ba,kuma wollahi tafiyata zan yanzunma,can ki yanka ni baza ki janyomin bala'i ba ina zaman zama na haka kawai ya shafi ahalina.."
Tana gama maganar tayi hanzarin ficewa ta bar gidan su Aishar tana ta zuba sauri,dai² ta shanyo kwanar line su zata shiga gida taji an rik'o hijabinta ta baya,juyawa tayi a fusace zata fara masifa taga mahaukacin su,take ta daskare a wajen dan k'arshen tsoro taji shi tunda sam ita bata ganshiba har ta zo nan,kasa motsawa tayi a wajen dan tsabar tsoron data ji,ja hankali ta shiga ja da baya tana fad'in
"Inna nakafu min rabbina yauman abuu sank'am d'ariraa...La'ilaha illa anta subhanaka inniy kuntu minaz-zalumiiyn...Ya hayyu ya k'ayyum...Allahu laa ilaha illa huwal hayyul k'ayyum..."
Duk inda ta matsa haka yake binta,tun tana iya fad'a a zuciyarta har ta fara bayyana addu'o'in nata a fili ,shi kuwa banda binta babu abunda yake,a haka har suka shiga soron gidan,sai da takai jikin bango sannan taga shima ya daka ta da binta da yake cikin kakkausar murya ya furta
"Ke k'awar wannan munafukar yarinyar ce ko..?"
Da k'yar jeeddah ta iya had'iye yahun bakinta,ba tare data amsaba sai k'ifta ido da take saboda tsoron kada taje tayi magana ya zama mahaukacin/aljanin yana duka yanzun ya luguiguita mata jiki,wata dariya da mahaukaci-aljanin ya saki ce ta k'ara firgitata har taji k'afafuwanta suna neman kasa d'aukarta,a hakanli taga ya koma baya yana tuntsira dariya har da sunkuyawa,d'agowar da zaiyi taga ya dakata da dariyar sannan ya shiga cire duk abunda ke fuskarsa,fuskar yarima yaseer ce ta bayyana,ai ko da jeeddah taga haka bata san lokacin data zube k'asa ragwaf ba dan tsabar firgitata da yayi tana sakin ajiyar zuciya masu k'arfi,yadda ta zube yasa shi kallonta da sauri yana tambayar lafiya..?
Bata iya kallonsa ba ta mik'e a hankali ta furta
"Ina zuwa.."
Gida ta shiga shima da gudu ta k'arasa shigewar,dai² inda randar ruwansu ke ajiye ta nufa ta bud'e,sai data cika kofin gurin da ruwa ta juje shi a cikinta sannan ta dawo soron cikin sauri,nan inda ta barshi haka ta dawo ta tarar da shi,ko da yarima yaga haka sai ya kalleta yana fad'in
"Dan Allah kiyi hak'uri nasan wollahi na baki tsoro,amma in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba.."
Kai kawai ta iya girgizawa dan har lokacin k'irjinta bai daina bugawa da sauri² ba,buhun da yake hannunsa mai kama dana mahaukatan gaske wanda cikinsa yake d'auke da shirgi da tsummokarai yasa hannu ya ciro wata leda,ya mik'a mata sannan ya furta
"Ki karb'i wannan waya ce a ciki,ina so daga yau duk inda zaki ya kasance tana tare dake,ina ganin zata k'ara bamu sauk'i wajen bincikenan,ya kasance a duk lokacin da zaku had'u da Yarinyar nan kina recoding en duk wani abu da zata fad'a wannan shi zai bamu damar tattara duk wasu hujjoji masu k'arfi da muke buk'ata..amma sai kin kiyaye da b'oyeta saboda da zaran an ganta to komai zai rushe..."
Kai ta jinjina,sannan ta mik'a hannu ta amshi ledar
"Sai k'arin bayani da zan miki akan maganar wayan ina so kisan dabarar da zaki yi Inno tasan da ita saboda kada ta ganki da ita wata rana al'amarin ya cukurkud'e mana,ina ganin itan idan ta sani shi kenan kuma bamu da wata fargaba amma duk wasu da kuke mu'amala dasu kada ki sake su sani.."
"In sha Allah zan kiyaye duk abunda ka fad'a min.Amma Yallab'...auu babban Yaya me yasa kayi irin wannan shigar..?"
Sai da yayi dariya sannan ya furta
"Duk cikin shirinmu ne hakan kuma saboda na tsorata tane ta fito gaban fada ta k'aryata kanta akan waccan maganar da suka yi ta baya.."
"Ohhooo! Na gane..amma kam nima na tsorata ba kad'an ba.."
Y'ar dariya yayi mata sannan yasa kai ya fice yana fad'in
"Afuwaan..! Sai wani lokacin...."
Har ta daina hangoshi bata bar lek'en hanyan daya niba data fito tana hangen ko akwai wani daya ganshi,sai data tabbatar babu wanda ya ganshi sannan hankalinta ya kwanta ta juya ta shige gida,tun data dawo cikin gidan take ta taradaddin yadda zata sanarwa da inno maganar wayan da yace ta fad'a mata amma ta kasa,dan haka kawai saita shige d'aki ta adana sannan ta dawo ta zauna kusa da inno tana d'ora kanta a kan cinyan inno tana sakin ajiyar zuciya....
Washe gari kasancewar ranar Thursday ne tun kafin ta taso daga makaranta Fulani tayo aiken idan jeeddan ta dawo tana nemanta,bayan dawowarta kuwa inno ta sanar da ita sak'on uwar d'akin nata wato mahaifiyar yarima YAZEED kenan,da saurinta ta shirya sannan ta d'auki hanyar cikin gida,a turakar fulanin ta yada zango bayan an mata izinin shiga inda take,duk da fulanin a wannan lokacin bata cika sakin fuska ba,amma ganin jeeddan sai daya sata yin d'an murmushi tana fad'in
"Lale marhabun da uwar fada.."
Itama murmushin tayi sannan ta zube gaban uwar d'akin nata ta shiga kwasar gaisuwa..."
Cikin d'an sakin fuska ta kalli jeeddan tana zama saman resting chair,sannan ta fara magana
"Uwata so nake na aikeki,amma ina so kiyi hankali duk da sawa zanyi a kaiki a kuma dawo dake.."
Kanta a k'asa ta jinjina kai tana cewa
"An gama uwar d'akina cikin hukuncin ubangiji zanje duk inda kike so naje na kuma dawo ba tare da fargaba ko nadamar aiken da kika min ba.."
Jinjina kai itama fulanin tayi tana d'an murmushi dan tana jin dad'in yadda jeeddan keyi mata biyayya a duk abunda ta sata,haka cikin ladabi da bata girma take a kullum,ga rayuwarta babu ha'inci ko cuta duk da kasancewarta k'aramar Yarinya tana da biyayya sosai,wannan yasa take sonta fiye da sauran bayin da suke b'angarenta.
"Ba wani guri nake son aiken kiba face gurin yarima yazeed.."
Sai da jeeddah tayi mamakin maganar ta Fulani dan tunda aka tafi da yarima gidan horon hakan bata tab'a faruwa ba,babu wanda yake zuwa wajensa face yarima yaseer shima dan maimartaba yasan yana zuwa kuma da amincewarsa hakan take faruwa,amma sauran y'an gidan duk ya hana kowa zuwa,kusan zata iya cewa duk tsayin wannan lokacin shi ne karo na farko da ita kanta fulanin tace za tayi aike gurinsa,b'oye mamakinta tayi kanta a k'asa ta amsa cikin girmamawa,haka Fulani tasa aka kira mata amintaccen bawanta mai suna zailani wanda duk inda zata shi ke kaita,bayan zuwansa ta bawa ta sanar masa buk'atarta na son aikensu wajen yarima da rahoton da take son su d'auko mata na rayuwar da yake dan ta fara jin k'ishin² en yadda yake rayuwa,sannan ta sallame su suka d'auki hanya...
Tun daga bakin get en gurin jeeddah take baza ido har suka shiga cikin harabar gurin,yadda yara ke shawagi a gurin kamar wata k'aramar boarding skul haka tsarin gurin yake,har office en d'in shugaban gidan aka kaisu duk da ya samu labarin zuwansu,daga nan kuma yayi musu jagoranci zuwa d'akin da yariman yake,yau kam ko fitowa bai yiba tun daya tashi da safe,abu d'aya kawai yasan yayi shi ne karatu da malaminsa yazo masa wanda sarki yake aikowo kullum yana masa,badon komai ba sai dan kada future ensa ta goce daga yadda yake buk'atar ta kasance.
Yadda suka shigo suka tarar da shi sosai abun yaso bawa jeeddah tsoro,haka taita kallonsa kamar wani sabuwar halitta,yadda ya sauya kamanninsa duk sun canja yasa jikinta mutuwa har bata san lokacin data fara kuka ba,lokacin da shugaban gidan yake musu jawabin ga yarima can shi kuma a lokacin ne ya d'ago kansa dan jin an ambaci sunansa,ita kuwa jeeddah ko da suka yi ido had'u da shi kasa tsayawa tayi a gurin saboda kukan daya ci k'arfin ta,haka ta fice a gurin ta nemi waje ta zauna a varenda tana ta kuka,sai da tayi mai isarta sannan ta yiwa wanda suka zo magana suka kamo hanyar dawowa gida zuciyarta cike da tsananin tausayin halin da taga yariman a ciki,tabbas zata iya cewa tunda take bata tab'a tunanin duk labarin da yarima Yaseer yake bayarwa abun ya kai haka ba,sai ko yau da idanunta suka nuna mata,a haka suka dawo gida ta sanar da fulanin abunda idanunta ya gani kamar yadda fulanin ta aikata ta mata binciken yanayin gurin da yadda yariman yake rayuwa,babu abunda ta b'oye mata,daga nan ita kuma Fulani ta sallameta ta tafi gida har lokacin abubuwan data gani basu bar yi mata yawo a cikin kanta ba.........
_DON'T FORGET TO VOTE ME ON WATTPAD @jeeddahmu898._
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*EDITED BY. REAL HAFSEEY.💞*
___________________
*Pg 6.*
^^^^^^^^
Shiganta gida bayan ta sanar da inno dawowarsu ta fad'a d'aki ta kwanta,take sababbin hawaye suka shiga sake tsere a fuskarta,sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e ta zauna tana gyara fuskarta zuciyarta cike da son zuwa wani waje,sake shiryawa tayi sannan ta fito tana cewa inno taje gidansu Aina'u amma ba jimawa za tayi ba yanzun zata dawo,amsa mata da to tayi nan tasa kai ta fice zuciyarta cike da taradaddin abunda zata tarar a inda zuciyarta ke k'iyasta mata taje.
Fitowarta daga gidan ta d'an tsaya a soro tana mak'ale y'ar wayar da yarima ya kawo mata,sannan ta fice ta mik'i hanyar gidan su Aisha,tana tafiya tana tunano halin da yarima yazeed yake ciki da haka ta k'arasa,da sallama ta shiga cikin gidan, babu kowa a tsakar gida dan haka sai ta k'arasa bakin k'ofar d'akin su tana sake yin sallama,Ladidi dake kishingid'e daga ita sai d'aurin k'irji ta d'ago tana amsa mata,tana binta da kallon rashin sani,sakin fuska tayi bayan ta shiga cike da ladabin da bata yi niyyan yiwa ladidin ba saboda tsabar tsanarta da take ji aranta wacce take taso mata haka kawai daga can k'asan zuciyarta,ita kuwa ladidi yadda taga jeeddah ta sunkuya cikin ladabi tana gaisheta sai taji Yarinya ta burgeta,haka ta amsa tana ta bin jeeddan da kallo.
"Aisha tana nan..?"
Jeeddah tayi tambayar,da y'ar dariya Ladidi ta girgiza mata kai
"Ayyahh! Wollahi na aiketa amma ba jimawa za tayiba zata dawo..ko zaki jirtaa..?"
"To babu komai bari na jira tunda bata yi nisa ba.."
Shiru suka yi na d'an wani lokaci ita kuwa jeeddah sai wasa take da yatsun hannunta,ga Ladidi kuwa tun da jeeddan tayi shiru lokaci zuwa lokaci sai ta d'ago ta d'an saci kallonta tayi murmushi kamar mai matsalar kai,can zuwa jimawa kamar wacce aka matsa ta ladidin ta sake kallonta tana cewa
"Y'an nan mene ne sunan ki..?"
Sai data d'ago tayi mata murmushi sannan ta bata amsa
"Suna na Hawwa'u amma da jeeddah ake kirana.."
"Allah sarki sunan manya gareki,ya mamarki take..?"
"Tana nan lafiya.."
Ta bata amsa a tak'aice tana juyar da kanta zuwa gefe,cikin zuciyarta ko fad'i take
"Kuji mata da fi'ili sai kace tasan mamar tawa har da wani tambayata ya take.."
A zahiri kuwa ko data waigo suka had'a ido sai tayi murmushin yak'e,daga haka babu wanda ya sake cewa komai,sun jima zaune shiru sannan Aisha ta dawo,tun kafin ta shigo d'akin Ladidi take ta faman rafka mata kira
"Shatu maza kiyi sauri ga jeeddah tazo tun d'azun bakya nan.."
Kallon Ladidi jeeddah ta tsaya yi jin yadda tayi caraf kamar wacce aka matsa ta fad'a,wani haushin Ladidin ne ya sake kamata har ta banka mata hararar da bata sanma tayi ba,itama Aishar kamar an cillota ta fad'o d'akin tana tambayar
"Tana ina Baba..?"
"Gata nan zaune sai jiranki take ke kuma daga aikenki kinje kinyi zamanki,kamar na aiki bawa garinsu..ni kawo min aiken nan.."
"Kiyi hak'uri Baba wollahi shi ne mai shagon bashi da hanzari tun d'azun dana je sai yanzun nefa ya sallame ni.."
"Iyyy! ai dama haka kullum na aikeki zaki dawo kice,mak'aryaciya kawai,ni dallah bani ki matsamin anan kafin na mangareki.."
Kasak'e jeeddah tayi tana kallon yadda Ladidi ke zubawa Aishar masifa,haushin daya cika tane yasa ta mik'ewa tana fad'in
"Aisha tafiya zanyi nacewa da inno bazan dad'e ba dama kuma tun d'azun nake ta jiranki.."
"Kai dan Allah ke kuwa ki d'an zauna mana..sai na raka ki."
"A'a wollahi idan taga ban komaba yanzun zata min fad'a shi yasa zan tafi.."
"To shi kenan muje na rakaki.."
Sallama ta yiwa Ladidi sannan ta fita ta zura takalminta,muryar Ladidin ta juyo tana bata sallahun ta gaida mamanta,ita kuwa tace to kawai tasa kai ta fice ita da Aisha, suna cikin tafiya dukansu sunyi shiru jeeddah ta saci kallom Aishar ta gefen ido,da sauri ta juyo ta kalleta fuskarta da d'an tsoro
"Laaa! Aisha kin san kuwa jiya dana tafi gida wollahi wannan mahaukaci/aljanin sai daya biyo ni,ai in baki labari ni wollahi abunda yayi min ma har yafi naki,kin san wani abuma daya min ya k'ara min tsoro..? Wollahi har naje line gidan mu bansan yana bina ba sai dana je zan shiga gida naji an rik'eni...Ya matsemin wuya wai saina fad'a masa abunda na sani akan k'aryar da kikayi a fada,dana ce ban sani ba,shine ya cillani jikin bango karkiji yadda na bugu,wollahi ko dan bakiga yadda yamin ba amma da kin tausayamin a jiyan nan kin fad'a min abunda yake cewa kije ki fad'a,ai zaki fad'an ko..?"
Shiru tayi tana turning fuskarta zuwa kalar tausayi,shiru Aishar tayi tana tunani fuskarta ta rikid'a zuwa wani irin yanayi,koda ganin haka ai da sauri jeeddah tasa hannu ta matsa wayar dama tana dai² b'angaren recorder
"Gaskiya ko jeeddah ni bazan iya fad'a miki ba yanzun,kinga ko ki manta da wannan maganar dan ni babuma abunda na sani akan abun kawai wannan mahaukacin yanayin haka ne amma ni ban sanshi ba,ban tab'a ganinsa ba sai jiya,to wace gaskiyace zan fad'a muku,ni babu wani abu dana sani bare na fad'a miki...Ki gaida gida sai anjima kada baba taga na jima yanzunma tamin fad'a.."
Tana fad'ar haka ta juya da sauri tabar wajen jikinta duk alamun tsoro ya bayyana a tattare da ita,binta jeeddah tayi da ido tana jinjina kai had'e da sakin wani murmushi mai ciwo,sai data daina hangenta sannan ta juya tana magana da kanta
"Zan saki fad'ar gaskiya wata rana da izinin Allah ko kina so bakya so,imma kin amince ko baki amince ba,wannan alk'awari na ne saina tursasaki kin fad'a a gaban jama'ar da kika yi k'arya a wancan lokacin..."
Hanyar gida ta kama itama tana tafiya tana tunanin hanyar daya kamata ta bi wajen tursasa Aishar ta fad'a mata duk abunda ta sani,yayin da a ko wane motsawar second take jin tayi loosing duk wani hope,karo na farko kenan da zuciyarta ta k'iyasta mata ta rasa duk wata dama...
Tun daga wannan ranar da taje gidansu Aisha'n bayan rabuwarsu sai ta fara ganin sauyi daga gurin ita Aishar,haka alak'arsu da juna ta fara jaa baya,ko gaisawa ba sosai suke yinta ba,hasalima duk sanda Aishar zata ganta saita canja hanya,abun duniya duk ya taru yayiwa jeeddah yawa gashi kullum cikin sa rai take da fatan binciko gaskiyar da zata taimaka musu wajen ganin an fito da yarima daga gidan kangararrun yaran,amma abu yaci tura duk wata hanya da zasu kama sai ta nemi sub'uce musu,dama kuma akan Aishar suke da sa rai idan har ta fad'a musu abunda ta sani shi ne zai bada damar a sake shi,bayan wannan kuwa babu wata shaida da suke da ita,wannan yasa suka tattara komai suka mik'awa ubangiji dan sun san shi ne mai ikon yin komai,hakka addu'ah kullum cikin yinta suke akan Allah ya basu dama da zasu sake yin nasara,saboda yak'inin da suka gina zuk'atansu akai matuk'ar suka gabatar da ita a matsayin shaida da suke da ita sun san nasarar da suke nema ta samu,sai dai a yanzun suna ganin komai ya zama tarihi saboda ita Aishar ma ko zama inda jeeddah take ta daina yi,wannan rashin k'arfin guiwa yasa su tattara komai suka ajiye tare da sa ran wata rana ubangiji zai sake kawo musu mafita cikin sauk'i da tafi ta baya...
*5 YEAR'S LATER...*
Fitowarta daga d'akin girkinsu kenan tana ta sauri zata shiga wanka Aisha ta shigo gidan kamar an cillota tana ta haki,juyawa jeeddah tayi ta kalleta fuskarta cike da tsantsar mamaki dan rabon data ganta har ta manta bare kuma tazo gidansu,idan ko har bazata manta ba kuma zata iya tunawa rabo da su sake had'uwa tun ranar da suka rabu da juna a wani zuwa da tayi gurinta wanda ak'alla yau kimanin shekaru biyar kenan babu y'an watanni.
Juyawa tayi ta sab'i bokitin data had'a ruwa zata shiga bayan gida ba tare data sake kallon inda take ba dan ta san tsakanin su kam a yanzun babu wani mutunci bare maganar arzik'i ta had'a su,muryar Aisha ta d'aki codon kunnenta dai² lokacin da take k'ok'arin shiga bayan gidan
"Dan Allah jeeddah ki dakata kafin ki shiga kuyi magana,wollahi akwai wani muhimmin sak'o dana zo na sanar dake a yanzun..."
Ba tare data juyo ba ta furta
"Bani da lokacin sauraren k'arairayinki a yanzun,Aisha ke kanki ki san da haka,saboda haka zan iya cewa ki gaida gida..."
"Wollahi jeeddah ba wasa ya kawoni gurin ki ba,muhimmiyar maganar dana ce miki ita ta kawoni kuma ita nazo muyi dake,amma ina so ki saurara yanzun kiji ko da kuwa hakan yana nufin baza ki sake saurarena ba har abada.."
Waigowa jeeddan tayi cikin cushi ta kalleta tana dire bokitin hannunta,cike da masifa tana d'aga harshe ta furta
"Na fad'a miki bani da lokacin da zan tsaya sauraren kalaman mutumin da yake mak'aryaci,macuci kuma maha'inci,azzalumi da babu abunda ke zuciyarsa illa zallar cutarwa...Shin Aisha kina ganin akwai wani abu daya rage ki sanar dani wanda ban riga na sani ba..? Uhmm.! Kawai kije abunki duk lokacin da kika ga dama kya iya zuwa ki bayyana gaskiya a inda kika yi k'arya a saki bawan Allah'n da bai jiba bai gani ba,tunda ku Allah baisa kuna tunawa da halin da kuka jefa bawan Allah ba.. Abun tausayi kun d'auki hakkinsa alhalin bai muku komai ba,na tabbata da ace kuna tunawa da mutuwa..Kwanciyar kabari da kuma hisabi..da ba'a kawo yanzun ba.. Sai dai na sani wannan duka ba abubuwane da zaku yi tunani akansu ba,haka ba abune da zaku yi saurin fahimtar kun aikata bisa kuskure ba,amma akwai lokaci,na tabbata lokaci zai zo da Allah zai bayyana gaskiya,abunda kuka jima kuna b'oyewa zai bayyana,amma yanzun abunda zan fad'a miki shine ina so kiyi gaggawar fita a nan gidan matuk'ar kina son kanki da lafiya,kafin na fusata na miki abunda baki tab'a tunanin zanyi ba..."
"Jeeddah dan girman Allah kiyi hak'uri ki saurareni wollahi ban zo nan ba sai da nayi alk'awarin sanar miki da komai,a yau na k'udurce zan fad'a miki komai daya faru wanda har ya janyo mahaukacin nan ya dunga bina yana tsorata ni,duk da haka banjiba a lokacin nak'i fad'a,amma dan Allah ina so kiyi min alk'awarin babu wanda zaki fad'awa,sannan bazaki bari maganar ta koma kunnen Baba ba dan ina jin tsoro idan har ta san na fad'awa wani wollahi kashe ni zata yi..!"
Zaro ido jeeddah tayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 63