An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
💠💠💠💠💠
*WANI AL'AMARIN...!💥*
_(Warwareshi sai Allah)._
*STORY,WRITTEN & EDITING BY:*
_HAWWA M.U (SMASHER)._
*COMPILATION BY:*
_HAWWA M.U (SMASHER)._
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*GODIYA.*
_Dukαnnín gσdíчα dα чαвσ sun tαввαtα gα Allah (S.W.A) ѕhí kαd'αí чαkє вα ѕhídα αвσkín tαrαччα,tѕírα dα αmíncí su cí gαвα dα tαввαtα gα fíчαччєn hαlíttα Annabi muhαmmαd (S.A.W) tαrє dα αhαlínѕα dα ѕαhαввαnѕα,dα ѕαurαn wαd'αndα ѕukα вíчσѕu dα kчαutαtαwα hαr ízuwα rαnαr ѕαkαmαkσ..._
*TSOKACI.*
_wαnnαn lαвαrín k'αgαggєn lαвαrí nє dαnα tѕαrα αвunα dα kαínα,вα tαrє dα hαd'ín guíwα da kσwα вα ina fαtαn Allαh чα вαní íkσn ruвutαѕhí lαfíчa..._
*GARGA'DI/JAN KUNNE.*
_вαn чαrdα wαní/wαtα ѕu juчαmín wαní ѕαѕhí nα lαвαrínaвα ѕαí dα чαrdαtα αíkαtα hαkαn вαввαn lαífí nє,haka zalika ban amince a saidamin da wani sashi na labari ba,wαndα чα cαnjαmín fαѕαlín lαвαrí/ya siyar zαn вαrѕhí dα αllαh ѕαвσdα nαfí ѕσn gαnín αвunα α чαddα nα ruвutα,ínα fαtαn zα'α kíчαчє.wαndα duk kumα чα ѕαídαmín ѕαѕhín lαвαrí ѕhímα nα вαrѕhí dα αllαh cσz вαnα nufín ѕαídαwαr ѕαвσdα hαkα α kíчαчє._
*JINJINA.*
_jιnjιna gα d'αukαcín mαѕσчα kumα mαвíчα lítαttαfαínα α kσdα чαuѕhє,ínα mík'α gαíѕuwα gαrєku α duk índα kukα kαѕαncє α fαd'ín duníчα,αllαh чα вαr k'αunα hαd'є dα zumuncí.._
*JINJINA TA MUSAMMAN GA..*
_HASSAN ATK,HUSSAIN ATK,IT'S B.Y EBRAHEEM,HAYAT BABA ZUBAIR,Ina k'ara godiya tare da jinjina a gareku bisa yadda kuke d'awainiya da al'umma,fatan rabb ya saka muku da mafificin alkhairinsa._
*GODIYA TA MUSAMMAN GA..*
_SMASHER & HUBBEEY NOVEL'S GROUP 1&2,ZAB'IN WA ZANBI FAN'S,NOVEL'S COMMENT ONLY,HA'DIN KAI GROUP,LEEMA NOVEL FAN'S GROUP,SAWWAMA NOVEL'S,AUFANA TRUE FAN'S,AESHAB NOVEL FAN'S,A LAUNI HAUSA NOVEL,HAMRAT FAN'S,AWESOME WRITER'S FAN'S GROUP._
_Dukkanku ahalin wad'annan gidaje,wanda na ambata dama wad'anda ban ambata ba,ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke._
___________________________
*MARUBUCIYAR..*
_1.K'addara Koh Sakaci..??_
_2.K'azafin Kisan Kai._
_3.Rayuwar Wani._
_4.Y'ar Garuwa._
_5.Bambancin Al'adu._
_6.Ina Mafita..??_
_7.Zab'in Wa Zanbi..??_
__________________________
*ASSALAM ALAIKUM WARAHMATULLAH,FATAN ALKHAIRI GARE KU MASOYA DA FATAN ZAKU KARB'I WANNAN LITTAFI KAMAR YADDA KUKA SABA,SAI DAI WANI ABU GUDA DA ZAN FA'DA SHI NE DAN ALLAH DUK WANDA YASAN BAZAI BIBIYI LITTAFIN NAN YANZUN BA SAI NAYI NISA SANNAN A FARA MIN MAGANA PC ANA NEMA DAGA FARKO,GASKIYA BISA GA YADDA WASU BASA MANA ADALCI KUMA BASA GANIN ABUNDA MUKE YI A DUK LOKACIN DA SUKA YI MAGANA SUKA GA BAKA AMSA SUBA AKAN LOKACI YASA NI YIN WANNAN MAGANAR,KWATA-KWATA AKWAI WANDA BASU SAN ME AKE NUFI DA UZURI BA A RAYUWA,SHI YASA NA YANKE SHAWARAN ZAN SANAR DA KU,KO DAI MUTUM YA BINCIKA A GROUP TUNDA INA POSTING CAN,KO KUMA A DUK LOKACIN DA NAYI POSTING YAYI STARING NASA DUK LOKACIN DAYA BUK'ACI KARANTAWA SAI YA DUBA BA SAI YAZO YANA NEMA A WAHALE BA,INA FATAN KUN FAHIMCI UZURINA DAN WANNAN KARON KAM BAZAN IYA IN DUNGA BINKU D'AYA BAYAN D'AYA INA TURA MUKU TA PC BA,SABODA HAKA MASU SO SUYI CIGIYA A GROUP.NA GODE.*
__________________
*Pg 1.*
^^^^^^^^
*KANO STATE,DALA L.G.A (GORON DUTSE AREA) @ 3:30pm.*
---Banda idanu babu abunda nake wurgawa musamman yadda aka tashi garin yau ana tsananin rana dake bada wani irin hucin zafi,haka ko iska ce ta kad'a babu abunda zaka tsinto cikinta banda tsabar tiririn zafi da take fesarwa,a dai² unguwar ta GORON DUTSE bayan mun yanko takan titin da zai sada ka da prison,muna tafe mai napep sai sauraren wak'ok'insa yake,ni kuwa ina baya sai kalle² nake a hanya,d'aga kaina ke da wuya a dai² lokacin idanuna suka sauka kan rubutun *"REMAND HOME"* shi ne abunda idanuna suka fara hangowa a jikin saman tafkeken ginin dake wajen hakama bakina abunda ya furta kenan,wanda a hausance zamu iya kiransa da *KURKUKUN YARA* ko a kira shi da *GIDAN HORAR DA KANGARARRUN YARA* masu laifin da shari'a bata aminta da shi ba,kama daga kan fyad'e/kisan kai/daba/ko fashi da makami da sauran laifuka da sukayi kama da wad'annan,sosai hankalina ya tashi da ganin sunan,nan da nan cikin hanzari na sauka daga napep en dana hau na dumfari ainihin hanyar da zata sada ni da cikin gurin dan ganin meke wakana a cikin wannan gida,nayi y'ar tafiya mai nisa kafin na fara isko ainahin get en gidan dake da masu tsaro ke baje a gurin,da k'yar na samu hanyar shiga dan ko kad'an ba'a cika barin mutane suna shiga ba sai ko idan daga makarantu ko kuma ka kaiwa wani maka ziyara,daga nan wajen get en sai dana kuma yin y'ar tafiya kafin na fara jiyo sautin maganganu k'asa²,sauri na k'ara har na isa gurin da nake jiyo alamun da mutane a wajen,shigata babu jimawa na fara cin karo da yara maza suna ta shawagi a harabar gurin wad'anda adadin shekarunsu suka gaza kaiwa sha takwas (18),a yayin da wasu ke wasa tsakaninsu da y'an uwansu a harabar gurin,wasu kuwa na can a cikin d'akunan su ko barinsu su fitoma ba ayi.
Can daga gefe idanuna suka hangomin wani yaro da bazai haura shekaru sha biyar ba a duniya,zaune shi kad'ai ya buga uban tagumi tamkar wanda aka yiwa mutuwa,duk budurin da sauran *YARA* keyi a gurin shi ko kad'an abun bai wani bashi sha'awa ba bare ya shiga cikin su,hasalima ko kallon inda suke baiyi ba,a hankali ya saki ajiyar zuciya da lokaci zuwa lokaci na kula yana yawan yi,hannunsa ya janye daga saman kumatunsa sannan cikin nutsuwa ya mik'e had'e da wucewa yana nufar wata varenda da zata sada shi d'akunan kwanansu masu kama da hostels,a baya na shiga binshi don gano wace irin damuwa ce a tattare da wannan Yaro da har ya hana shi shiga cikin y'an uwansa yara suyi wasa kamar yadda d'abi'ar yarinta take.
Tiryan² yake bin hanyar har ya kai ga isa bakin k'ofar d'akin mai d'auke da lamba ta *009* a hankali ya tura k'ofar ya shiga kana ta maida k'ofan ya rufe,katifu ne a jere reras a d'akin da ak'alla suka tasamma shida ko k'asa da haka ma'ana dai baza su gaza kaiwa biyar ba,saman katifar dake can gefe daga kusurwar gabas data kasance mallakinsa a wannan d'aki ya nufa ya kwanta had'e da takurewa guri guda tamkar mutumin dake tsananin jin sanyi,ya jima a haka kafin bacci ya sace shi.
^^^^^
Sautin kukanta kad'ai ke tashi a cikin katafariyar fadar data kasance a cikin garin na kano a cikin tsakiyar birni,cikin wani irin salo muryan nata taci gaba da tashi,wanda a cikin sautin zaka iya tabbatarwa mutumin dake kukan na cikein wani irin yanayi na k'unci da damuwa a rayuwarsa,kanta a k'asa ta kasa d'aga ido bare ta kalli dubban jama'ar dake wajen suna sauraren jin abunda zai fito daga bakinta kamar yadda aka sanar da al'umma ahari'ar da zata wakana a fadar,tana durk'ushe a k'asa sai zabga kuka take tamkar wacce aka kashewa wani nata,yadda fada tayi tsit alamun dake nuni da kowa na cikin hankalinsa,yasa maimartaba dake kan karaga da tun farkon da aka gabatar da yarinyar a gabansa a atsayin mai k'ara ya zuba mata ido yana sauraren abunda zata fad'a ko dan jin ance k'arar da take yi en tana da alak'a da masarautar yasa duka ahalin gidan sarautar suke nan zaune,cikin hikima maimartaba ganin ta kasa magana fashi ana d'aukan lokaci yasa shi sake kallonta yana d'an murmushin irin nasu na manya ya furta
"Yarinya tunda kika zo kike kuka kin kasa fad'in abunda ke tafe dake,shin me yake faruwa dake da kike irin wannan kukan...? Maza ki sanar da mu abunda ke tafe dake yanzun.."
A hankali ta d'ago jajayen idanunta da suka kumbura kan tsabar kukan da tayi ta goge fuskarta kana ta sauke ajiyan zuciya akai²,ba tare data iya had'a ido da maimartaba ba saboda kwarjinin da yake da shi a fuskarsa da ba'a tab'a taronsa gaba da gaba ayi magana da shi,MATAWALLE sarki ya kalla kasancewarsa shugaban alk'alai yayi masa alamun da su tambayeta abunda ya kawota fadar,a hankali matawalle ya jinjinawa maimarta kai sannan ya d'an sunkuya alamun girmammawa,kana ya mik'e tsaye bakinsa d'auke da sallama,sai daya mik'a gaisuwa ga maimartaba sarki kafin ya juya ga yarinyar ya shiga maimaita mata irin tambayar da maimartaba yayi mata a karon farko,yadda tayi shiru daga tsananin kukan da tun data shigo cikin fadar take yi,babu wanda yayi zaton zata ci gaba.Amma ga mammakin mutanen gurin ko da matawalle yayi maganar sai kawai suka ga ta sake fashewa da kuka,nan fa surutai suka fara tashi a cikin fada,aka fara tsegumin abunda yake janyowa hakan take faruwa a duk lokacin da aka tambayeta take sake b'arkewa da kuka,kamar daga sama can daga bakin k'ofa muryar tayo kutse cikin fadar da fad'in
"Ranka shi dad'e ayimin afuwa na magana da zanyi kan dalilin wannan kukan da Yarinya nan keyi.."
Gaba d'aya kallo ne ya koma bakin k'ofar shigowa fadar,wata y'ar dattijuwa ce tsaye sai raba idanu take tana bin jama'ar gurin da kallo,kai sarki ya jinjina kafin fadawa suka tabbatar mata da zata iya k'arasowa gaban fada don bada jawabin abunda take ik'irarin ta sani,har gaba ta ratso ta tsaya yayin da wasu fadawa ke biye da ita har gaban fada,bayan ta mik'a gaisuwa ga maimarta sarki da sauran wakilan fada dake zaune,ba tare da b'ata lokaci ba aka bata izinin magana,a nan ne ta juya ta takalli Yarinyar kana ta saki dogon numfashi kafin ta fara da fad'in
"Bayan sallama irin ta addinin musulunci ga ma'abota halartar wannan fada,nake sake neman afuwar fada bisa ga abunda zai fato daga bakina yanzun,na sani kuma na tabbatar babu k'arya cikin kalamai na ko kad'an sai dai ba lallai ne wasu su yarda da abunda zasu jiba duk da mu a gurinmu wannan shi ne gaskiyar kuma ta haka ne kawai zamu samu adalci..."
Fada ta sake yin shiru tana sauraren jin abunda zai fito daga bakin wannan mata da tun kafin ta kaiga isar da abunda take son fad'a wasu har sun fara shiga fargaba
"Da fari ni suna na Ladidi,ni marik'iya ce ga wannan Yarinya Aishatu,ranka shi dad'e zan fara da bada labarin asalin alak'armu ne kafin na fad'i muk'asudin abunda ya faru har ya kawo mu ga zuwa wannan fada mai adalci,ranka shi dad'e a k'alla zuwa yau kimanin shekaru sha biyu kenan da nake kula da Aishatu tunbayan da Allah yayiwa iyayenta rasuwa,a sakamakon had'arin mota,sai dai *WANI AL'AMARI* na ubangiji Yallab'ai tun daga lokacin da iyayenta suka yi had'arina indai aka tsiceta da wad'anda suka tsinceta sun shaida mana cewa itan sun ganta ne yashe a gefen titi kuma cikin hukuncin ubangiji ko k'warzanewa babu a tartare da ita,tun daga wannan lokaci ranka shi dad'e sai rainonta ya dawo hannuna,na sani dai ran maimartaba sarki ya dad'e Allah kuma yana kwana tun daga lokacin da nake rainonta haka har zuwa fara girmanta wani abu bai tab'a samunta ba,kasancewar kullum ina kula da ita sosai tamkar y'ar cikina,sai dai kash Yallab'ai duk wannan kulawar da nake bata da tsaron da nake mata sai gashi a jiya da dare an samu wasu mab'arnata sun kama Yarinyar nan sun wulak'anta mata rayuwa...."
Tana zuwa nan ta d'an dakata tana share hawayen daya gangaro mata,salati fada ta d'auka gaba d'aya da jin kalaman da suka fito daga bakin matar zuwa wasu y'an lokatu,ko da ganin an hau hayaniya sai matawalle yayi k'arfin halin mik'ewa ya dakatar da surutun kana ya waiwaya ya kalli matar sannan yaci gaba da magana
"Baiwar Allah Ladidi kikace sunan ki ko..?"
"Ehh ranka shi dad'e haka ne.."
"Shin ko da wannan al'amarin ya faru daga jiya da dare ko akwai wani wanda kuka sanarma matsalar da aka samu dan a d'auki matakin gano masu sa hannu a cikin wannan lamari..?"
"A'a ranka shi dad'e...nan shi ne guri na farko da muka kawo k'ara domin a karb'ar mana hakkinmu daga gurin wad'anda suka aikata mana wannan zalunci,dan munsan fada tana da wannan k'arfin ikon kuma a nan ne kad'ai zamu samu y'anci da adalci..."
Kai Matawalle ya jinjina kafin yaci gaba
"Shin ko akwai wani daya baku shawaran zuwa nan ne ko kuwa da kanku kuka kawo k'ara nan,shin kuma kuna da wata shaida ne ko akwai wani da kuke zargin da sa hannunsa a afkuwar al'amarin...?"
Shiru tayi bata bada amsa ba har saida ya sake maimaitawa,nanma dai shiru ta sake yi,ganin haka yasa matawalle yin gyaran murya ya juwa ga maimartaba yana fad'in
"Ran maimartaba sarki ya dad'e,ina fatan fada taji duka abunda wannan mata ta fad'a da kuma abunda ya wakana,abisa wannan dalilin na rashin tabbas na gane mai laifi da rashin shaidu,yasa nake neman alfarma a gurin masu fada da'a taimaka a bamu wadataccen lokaci da zai isa ayi bincike kafin a gurfanar da masu laifi,saboda muke fatan da'a jinkirta wannan k'ara da shari'a ta wad'annan bayin Allah har zuwa lokacin da fada zata gama nata binciken akan laifin.."
"Ayi min afuwa ranka shi dad'e na jinkirin magana dana samu akan tambayar da fada tayimin...Yallab'ai tabbas ba akan komai hakan ya faruba sai dan ina jin nauyin wannan fada,haka ina jin kunyar na sanar da ita ko wane mai laifin.."
Juyowa matawalle yayi ya kalleta fuskarsa cike da mamaki dan ko kad'an baiyi tunanin zata sake cewa komai ba,kana ya bata izinin da cewa
"Ke fada take saurare taji daga gareki,ba tare da b'ata lokacin fada ba ko maimaita maganar da kika yi,daga lokacin da kika zo nan da niyyan shigar da k'ara hakan ya nuna cewa kina buk'atar a karb'a muku y'ancinku ne kamar yadda kika fad'a a jawabinki na farko,saboda haka babu maganar jin nauyin fada ko makacin haka,yanzun fada a shirye take taji shin su waye masu wannan gagarumin laifin ko kuma su was ake zargi...? Domin ta gurfanar dasu a gaban mahukunta.."
Sai data yi jimm kafin ta sake duk'ar da kai k'asa ta furta
*"YARIMA NE...* ranka shi dad'e... "
Ko da jin kalaman da suka bayyana a bakinta tuni fada ta hautsine da tashin k'ananun maganganu,a yayinda wasu ke ganin wannan maganar k'agarta akayi aka fad'a nan kuma wasu ke ganin tabbas zancen zai iya zama gaske,duk da dai ba'a saurin yankewa mutim hukunci har sai an tabbatar daya aikata laifin.
B'angaren fadawa kuwa koda ta fad'i haka tuni har wasu kusan mutum biyar sun taso kanta da bulalu zatu mata saukar aradu,fad'i sauke
"K'arya kike y'ar talakawa,maza ki gaggauta tuba da gyara kalsmanki kafin fushin fada ya sauka akanki.."
Ko da ganin haka tuni matawalle ya dakatar zasu ta hanyar yi musu tsawa data sa suka fadar aka yi shiru
Shi kuwa maimartaba tunda sunan yarima ya bayyana a bakin wannan mata ai sai ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi na tashin hankali da yasa shi kasa tantance duniyar da yake,tunani yake da maimaita maganar a ransa anya kuwa kunnuwansa sunji dai² ko kuwa..? baga sarki kad'ai haka ta faru ba,hatta da y'an majalissar sarki makusantansa saida *AL'AMARIN* ya girgizasu matuk'a,hakan ya janyo gaba d'aya aka kasa magana sai jama'ar cikin fadar da suke ta y'an gulmace²nsu.
Da k'yar matawalle ya iya jan numfashi had'e da k'arfin hali sannan ya furta
"Baiwar Allah shin kin san abunda bakinki ya furta kuwa..? Taya mutumin dake cikin gidan sarauta zai samu damar fita da dare ba tare da an samu wani cikin dakarun dake tsaron fada sun ganshi ba..kuma a hakanma mutum irin yarima da kowa yasan ba ma'abocin yawo bane ko da acikin gidansu..Shin zaki sanar da fada ainihin masu laifin ne ko kuwa sai kotun fada tasa an azabtar dake azaba mai tsanani..?"
Diriricewa matar tayi jin yadda matawalle ya ambaci za'a azabtar da ita,kanta a k'asa ta kasa d'agowa ta kalli matawalle haka cikin inda² ta furta
"Yallab'ai na rantse maka da mahaliccin wannan duniya tamu da abunda ke cikinta iya abunda na sani kenan kuma shi na fad'a,idan har nayi k'arya ga Yarinyar nan fada zata iya tambayarta,da bakinta ta shaidamin wannan maganar,ba k'age nayi masa ba.."
Ran matawalle a matuk'ar b'ace dan daga alamun yadda matar take magana ya fara fahimtar da wata a k'asa,shiru yayi bai ce komai ba dan shi kam yama rasa abunda zai ce mata tunda tayi wannan rantsuwar
"Malama Ladidi shin kin tabbata abunda kika fad'a haka yake...?"
Muryar maimartaba ta daki dodon kunnenta,ba tare data iya d'agowa ba ta furta
"Allah yaja da ran maimartaba wannan magana tawa haka take,idan nayi k'arya kuma a cikin magana ta fada tana da damar tambayar Yarinyar shin haka ne abunda na fad'a ko kuwa akwai jaa.."
Jinjina kai maimartaba yayi sannan ya juya ya kalli Yarinyar,ko kafin ya kaiga yi mata magana tuni jikinta ya d'auki tsuma saboda yadda ta fara shayin fad'ar maganar
"Yarinya shin maganar da marik'iyarki ta fad'a yanzun haka take ko kuwa akwai wani abu da zaki fad'a da itan bata fad'a ba.."
Cikin saurin baki tana sake duk'ar da kai ta shiga girgiza kai
"A'a ranka shi dad'e babu abunda zan fad'a..."
K'ura mata ido matawalle yayi yana nazarin yadda tayi maganar,kafin ya kaiga yin magana sai ji yayi maimartaba na cewa
"Shin da gaske ne yarima ne ya aikata miki wannan laifin..?"
Kai ta d'aga cikin inda² tace
"Eh eh..ranka shi dad'e shi...sh..shi ne..!"
"Kin tabbatar shi en kika gani ba wani ba..?"
"K'warai ranka shi dad'e.."
'Dagowa maimartaba yayi ya kalli wasu dogarawa dake gefe,fuskarsa cike da tsananin tashin hankali da b'acin ran wannan tozarci da aka masa a gaban dubban al'ummarsa ya furta
"Maza aje azo da yarima yanzun bada b'ata lokaci ba..."
Sunkuyawa suka yi alamun girmamawa ga maganar maimartaba sannan suka fice cikin azama,direct cikin gida suka nufa basu a tsaya ko ina ba sai gefen yarima,da zuwa suka isar masa da sak'on maimartaba,murmushi kawai yayi sannan ya wuce gaba suna biye da shi a baya har suka iso cikin fada,yadda yake tafiya da al'amuransa cikin nutsuwa da ganinsa kaga innocent,a haka har ya k'araso gaban maimartaba ya mik'a gaisuwa sannan ya samu guri guda ya zauna yana jiran yaji dalilin kiran nasa.
Maimartaba ne ya kalli matawalle bayan ya numfasa sannan ya furta
"Matawalle ga yaronku nan ku tambaye shi game da laifin da ake tuhumarsa da shi.."
Saurin d'agowa yayi ya kalli maimartaba sannan ya kalli matawalle daya mik'e tsaye cikin wani yanayi dan shi kam har lokacin alamun da yake nunawa yana da tabbaci kan yarima ba zai aikata wannan laifin da ake tuhumarsa da shi ba,amma saboda babu yadda ya iya bare yace zaija da maganar maimartaba shi yasa ya shiga maimaitawa yarima laifin da ake tuhumarsa akai,wata irin razana yarima yayi cikin firgici ya mik'e tsaye yana fad'in
"Wallahi Abiiy ba ni bane,ban aikata ba...! Hasalima ni ban sansuba ban tab'a ko da ganinta ba..!"
Hannu maimartaba ya d'aga masa ba tare daya kalle shi ba ya fara magana
"Shin Yarinya wannan shi ne wanda kike k'ara..ko kuwa wani ne daban..?"
'D'agowa tayi ta kalle shi da jajayen idanunta kafin ta furta
"K'warai kuwa ranka shi dad'e shi ne.."
Cikin zallar b'acin rai maimartaba ya sake tambayarta nanma ta tabbatar masa haka suka yi tayi da ita har sau uku ta bashi tabbacin en ne,fuskar maimartaba cike da b'acin rai ya juya ga matawalle yana fad'in
"Matawalle ina fata yanzun kun gamsu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 63