kaishi dai² hancinsa yana sunsunawa kamar yadda YASEER en yayi masa izinin yi,mugun tsamin daya daki hancinsa ne yasa shi saurin cilli da cup en gefe cike da masifa ya furta
"Meye ne wannan en ka bani...?? Me yasa kasan ko mene ne zaka bani kace na duba maka...??? Me hakan yake nufi..???"
"Calm down Mr man..!"
"Ank'i ayi down en,me yasa zaka sani duba abunda bai dangance ni ba..?? Wato ka fara shaye² shi ne nima kake so na fara ko..?? Haba YASEER me yasa zaka yi haka,da can baka sha ba sai yanzun da kake cikin hankalinka,me kake so iyayen mu suce daga lokacin da suka sani..??"
Shiru YASEER en yayi masa yana binsa da kallon mamaki,koda yaga YASEER ya kasa tanka shi,shi kuma YAZEED en nan yaci gaba da magana cikin d'aga harshe sai ruwan bala'i yake zazzagawa YASEER en,cike da jin haushin gurum en daya masa ya furta
"Wannan ba dai² bane,kuma sam baka kamanci ta'ammali da kwayoyi ba,amma dan Allah rok'ona da kai d'aya shi kad'ai nake son kayi min alk'awari baza ka sake aikata makamancin wannan kuskuren ba,kasan bazan tab'a iya jura ba na ganka cikin damuwa,shin me kake tunani idan wani abu ya sameka..su waye zasu yi asarar rashin ka..?"
"Haba mana Malam taya zaka yi tunanin ni zanyi ta'ammali da k'wayoyi,kamar ni na aikata haka bayan ina cikin nutsuwata..?? How comes..?? Kai kanka kasan abune da bazai tab'a faruwa ba na aikata wannan kuskuren..."
Yadda YASEER yayi maganar cikin jin zafin abunda YAZEED en ya fad'a yasa nan da nan temperature en YAZEED sake hawa cike da masifa ya kalli YASEER en yana sake fad'in
"To idan baka fara shaye² ba taya akayi muka samu veer a nan..?? Waye ne ya kawota idan ba kana sha ba..??"
Cikin jin haushin maganar YAZEED ya sake kallon shi yana fad'in
"Nake sha ko kuma muke sha..??"
Wani kallo YAZEED ya bishi da shi kafin ya tambaya
"Ka ce mene...??"
"Abunda dai kunnanka yaji shina fad'a...Idan har zaka yi zargina akan abunda baka da iliminsa what about you..?? Ko kuwa shin kai baka san tare muka sha ba sai yanzun da nake fad'a maka..??"
Tsawa YAZEED ya bugawa YASEER cikin k'araji kamar zai dake shi ya furta
"Don't rehearses these drastic to me...Ko da wasa..! I warned u..!"
Yayi magannar yana karkad'awa YASEER yatsa cike da fushi,dariyar yake mai cike da rainin hankali YASEER yayi wacce ake cewa tafi kuka ciwo kafin ya kalli YAZEED from head to toe ya jinjina kai
"Kana d'auka da d'in da wasa nayi maka ne?? Ko kuwa tunanin ka na fara samun matsala a cikin k'wak'walwata da har wani banzan tunani zai sani ta'ammali da wine..?? Idan baka sani ba bari na fayyace maka abunda nake zargin faru duk da bani da tabbas,nd kai kanka yana da kyau ka maida tunanin ka baya kad'an,daga lokacin da muka fito da shirin fita,zuwa dawowar mu,shin zaka iya tuna wani abu da muka yi before these time around...??"
Shiru YAZEED yayi yana bin YASEER da kallon rashin fahimta,koda YASEER en ya fahimci irin kallon da yake masa sai kawai ya jinjina masa kai dan yadda yaga yayi ya tabbatar masa babu abunda zai iya tunawa
"Ba shiru za kayi ba,amsa nake buk'atan ka bani da kanka.."
"Bazan iya tunawa ba..Kawai dai kamin bayanin abunda kake nufi.."
Jinjina kai YASEER yayi sannan ya nemi guri ya zauna yana sakin ajiyar zuciya
"Idan har baka manta ba,daga kan lokacin da Ummi ta kiramu zuwa time en da muka fito cikin parlour'n nan zamu yi dinner,idan har zaka iya tuna wani abu daya faru da kai har ya janyo mana yin mugun baccin daya kusa janyo mana fushin maimartaba da har yasa bamu samu damar halartar taron da wuriba,shin kayi tunani akan wannan..?? Ko kuwa anan baka yi zargin wani abu ya faru damu a wannan lokacin ba...???"
Shiru YAZEED yayi yana kallon parlour'n zuciyarsa cike da son tuna wani abu da zai iya bada shaida akan tambayoyin da YASEER en ya jefe shi dasu,sun d'auki tsawon wasu y'an mintuna shiru,YAZEED kuwa sai k'ok'arin tunawa yake amma sam hakan ya gagara,cike da damuwa ya kalli YASEER yana girgiza masa kai
"Brohh!! Na kasa tuna komai..Ni sam ma bana tunanin wani abu ya faru makamancin haka.."
"Tabbas ya faru kuma ni na tabbatar.."
"Ta yaya kenan kake tunanin hakan..??"
Ba tare daya kalleshi ba ya shiga koro masa jawabi tun daga fitowarsu bayan amsa kiran Ummi kafin susha drinks en,har zuwa sanda suka sha lemon,da abunda ya faru da su bayan sun sha na daga mugun baccin da sukayi,nan ya ci gaba da fad'in
"Daga kan wannan bana tunanin na san kuma meya sake faruwa,da yadda akayi muka dawo hayyacinmu..amma dole ne ka yarda duk abunda na fad'a ya faru.."
"Tabbas...! Ya faru..kuma nima na tabbatar yanzun,sai dai abun mamakin anan shi ne ya akayi giya yazo mana nan..?? Nd waye ne ya kawo mana muka sha..??"
Shiru dukansu suka sake yi,zuwa wani lokaci YAZEED ya kalli YASEER ransa a mugun b'ace
"Waye ne aka sa ya shirya abinci yau.??"
A bazata tambayar ta zowa YASEER saboda shi sam hankalinsa bai kai kan tunanin wanda ya shirya abinci ba,ko da jin abunda yariman ya fad'a take yasa YASEER girgiza kai alamun dake nuni da lallai ne shima bai sani ba,nd duk wanda ya shirya musu abincin ko tantama babu shi ne abun zarginsu,shi ne kuma mutumin daya shayar dasu giya,ba tare daya samu damar bawa YAZEED amsa ba ya d'auka phone had'e da soma neman line Ummi,cikin abunda bai wuce minti biyu ba tayi picking,ba tare daya tsaya wani dogon sharhin ba ya fara tambayarta
"Ummi waye ne kika sa ya had'a mana dinner...??"
Sai da tayi murmushi kafin ta furta
"Haba YASEER kaima ai kasan duk fadin ginan,haka duk adadin masu hidiman gidan nan,da mutum d'aya kawai na aminta ta had'a muku abinci bayan ni kaina,ita ce dai wacce ka sani tun kafin tafiyarku ban sauya wata ba...."
Mamaki ne ya cika shi dan kuwa take ya fahimci kowa Ummi'n take nufi,sai dai abun tambayar anan idan har ita ta had'a abincin ya akayi haka ta faru...?? Tabbas a iya sanin daya mata ya jima da saninta haka nan abunda zata iya aikatawa da wanda ma bazata yu,ya riga da ya jima da sanin babu yadda za'ayi ta aikata haka,gefen Ummi kuwa jin yadda yayi shiru daga tambayar bai sake cewa komai ba kuma bai ajiye wayyan ba yasa Ummi'n cewa
"Akwai wani matsala daya faru ne..? Naji kayi shiru..."
Saurin danne damuwar da yake ciki yayi sannan ya k'irk'iro murmushi da cewa
"Noo!! Ummi shi kenanma kawai..."
Yana niyyan kashe wayan Ummi'n ta sake dakatar dashi da maganar da take yi
"YASEER ya akayi yau kuka k'i zuwa wajen taron nan ne...!? Shin kun kuwa san yadda kuka b'atawa iyayen ku rai...??"
"Afuwaan Ummi,mun makara ne sakamakon uzuri daya gifta mana,amma munje gurin bamu jima da dawowa bama..."
"Shi kenan to Allah kiyaye gaba,amma dai ya kamata ku gyara ko dan gaba,ko da ace ba iyayen ku ba wasu a waje suka gayya ce ku to yana da kyau ku halarta da wuri ba don komai ba sai dan cika alk'awari da kuma mutunta lokaci..."
"In sha Allah Ummi zamu kiyaye..."
Daga haka suka ajiye wayan,ga YASEER ko bayan da suka gama wayan damuwar daya b'oye ce ta dawo kan fuskarsa,nan take zuciyar sa ta shiga kaikawo akan wacce Ummi tace ta shirya musu abincin
"Shin me hakan yake nufi..??"
Yayiwa kansa tambayar ba tare da sa ran yana da amsar taba,ga YAZEED kuwa koda yaga YASEER yayi masa shiru bai ce komai ba,sai kawai ya kalleshi cike da son yin magana
"Me kacema da Ummi ne..??"
Sai lokacin YASEER ya kalleshi cike da rashin k'warin guiwa ya furta
"Na tambaya ne waye tasa ya shirya mana abinci.."
"Eheenn! Waye tace..??"
*"JEEDDAH.....! "*
Wani kallo YAZEED en ya masa,haka nan yanayin sama da yadda jikinsa ya koma tamkar wanda bai tab'a jin sunan ba sai yau,cike da mamaki ya ce da YASEER
"Ka kuwa ji abunda ka fad'a..??"
"K'warai nasan me nace,kamar yadda kaji haka nima naji,sai dai gaskiya zuciyata tana bani wani abu daban bayan wannan,na tabbata jeeddah ba zata tab'a aikata haka garemu ba..there must be something hidden da muka kasa fahimta..."
"Kana nufin baka yarda ba kome..??"
YAZEED yayi masa tambayar,cike da k'warin guiwa YASEER ya girgiza masa kai
"K'warai ban amince ba,kuma babu ta yadda za'ayi na amince da zata aikata haka,tilas ne akwai wani da yake bibiyar sahunta damu baki d'aya.."
Kallon mamaki YAZEED yayi masa kafin ya mik'e ya bar YASEER a wajen da sunan yana zuwa,bayan barinsa a gurin,tunani ne iri² YASEER en ya dunga yi,daga wannan ya koma wannan,haka nan gaba d'aya ya hana kansa sukuni,k'ofar shigowa parlour'n nasu ya tsaya kawai ya zubawa ido tamkar wanda ke neman amsan duka tambayoyinsa a jikinta,picture en inuwar daya gani a baya ne ya dawo masa,a hankali yaci gaba da takura kansa da son binciko shin da gaske ne kuwa abunda yake zargin ya faru,yana daf da tunawa YAZEED ya dawo yana tambayarsa
"Broh! Wai wace jeeddah kake nufi nema..??"
'Dagowa YASEER yayi yana sakin gwauron numfashi kafin ya bashi amsa
"Wacce dai ka sani ta asalin ita nake nufi..??"
Mamaki ne ya sake bayyana akan fuskar YAZEED kafin yayi magana
"Kana nufin wai dama tana cikin gidan nan..kuma duk tsayin wannan lokacin tana tare damu amma ban sani ba..??"
Da kai ya iya amsa masa ba tare da yayi magana ba,tsantsar mamaki ne ya sake bayyana a fuskarsa a fili ya furta
"Babu yadda za'ayi wacce tayi sadaukarwa akaina a wancan lokacin ta iya aikata wannan kuskuren..!"
'Dagowa YASEER yayi ya d'an kalleshi yana jinjina kai
"Ni kaina zargin da nake yi kenan,sai dai kuma idan har ba ita bace to waye ne mai wannan d'anyen aikin...??"
Shirun da suka sake yi shiya bawa yarima YAZEED damar yin tunanin wani abu,yadda yake squeezing face kamar wanda yaga wani abu da baya so duk kuma cikin salon son ya tuna en,da sauri ya kalli YASEER yana fad'in
"Noo!! Broh...! Tabbas kayi gaskiya akwai wani da ban daya aikata wannan kuskuren.. Shin me zaisa ta aikata haka gare mu..?? Sannan me zaisa itama wannan d'aya yarinyar ta taimaka mana lokacin da muke cikin tsaka mai wuya..? Kenan kaga bama ita kad'ai ke k'ok'arin bamu kariya ba akwai wata daban..!"
Yadda YASEER ya k'ure shi da kallo har ya gama fad'ar abunda zai fad'a yasa shi jinjina masa kai alamun tabbaci,murmushi YASEER ya saki sannan ya furta
*"ITA KAD'AI CE.....babu wani ko wata..Jeeddan dai itace a wannan karonma.............!"
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Pg 18.*
^^^^^^^^
Tsantsar mamaki YAZEED ya shiga ba don komai ba sai dan jin maganar data fito daga bakin YASEER,zuciyarsa cike da son sake gasgata abunda yaji ya furta
"Ita kad'ai fa kace...Kana nufin yanzunma ita jeeddan ce tayi wannan k'ok'arin akanmu..??"
"K'warai kuwa itance dai,babu wata a bayanta kuma babu taimakawar wani..."
Shiru yayi ba tare daya sake cewa komai ba,yanayin shirun da yayi yasa shi lulawa cikin duniyar tunani,nan take kuwa wasu daga cikin abubuwan da suka faru a d'azun kuma tsakanin su suka shiga fara gilma masa a cikin idanunsa,a hanakali picture en abunda ya faru a d'azun ya shiga dawo masa cikin idanunsa da k'wak'walwarsa,duk da a lokacin baya cikin hayyacinsa amma tsaf a dai² wannan lokacin a shirye yake daya takura kansa badon komai ba sai dan ganin ya tuna en,sai tunaninsa yayi nisa yana shirin tuna wani abu sai abu ya nemi gagararsa,sam ya kasa kai kansa inda yake da buk'atar zuwa,abunda kad'ai yake iya tunawa har yanzun shi ne sanda ya fara dawowa cikin nutsuwarsa,tabbas ya ganta fuska da fuska sai dai a hakan daya ganta akwai nik'ab a nata fuskar daya hana shi ganinta gaba d'aya,hakan tasa bazai iya tuna kamanninta ba,abunda dai kawai ya sani itan bak'ace nd bak'i kuma bana wasa ba,haka zalika yanayinta ba wata Babba bace ko a shekaruma,cikin zuciyar sa yake ta mamakinta da yiwa kansa tambayar
"Shin taya za'ayi mai k'arancin shekaru kamar nata ta iya yin tunani makamancin haka...??"
Bai wani sha wahala na neman wanda zai bashi amsa ba,d'ayar zuciyar tasa ta bashi amsa da
"Wannan ai ba wani abu bane kasan ko wane bawa da yake rayuwa ai yana da tasa kalar baiwar,ba duka halittun Allah suke dai² ba,kowa da akwai ta inda ya sab'a da d'an uwansa,koda kuwa hakan na nufin tare kuka zo duniyar,lallai ne sai an samu wani abu da kuka yi sab'ani da juna akansa...!"
Jinjina kai yayi cike da gasgata maganar da zuciyar tasa ta fad'a masa,haka nan tunawa da wannan maganar tasa shi tunowa da wani abu daya faru tsakanin sa da ita a d'azun sanda take shirin fita daya biyota yana son tambayarta,tun kafin ya kai ga yi mata magana sai kawai yaga ta zabura ta fice kamar wacce akace idan ta sake ya k'araso zai mata wani abu,yadda ta fita a cikin parlourn nasu a d'azun kafin su tafi gurin dinner da gudu shi ne abu mafi dad'i a gurinsa da tunawarsa tasa har ya ita sakin murmushi duk da a lokacin da abun ya faru ta b'ata masa rai,amma a yanzun bayan sanin wani abu daya faru sai yaji duk ya dena jin haushin duk da bawai dama jin haushin nata ya d'ora ba,cike da wani irin k'warin guiwa ya juyo ya kalli YASEER ya fara yi masa magana
"Amma broh..! Mene ne dalilin yarinyar nan na guduwa a d'azun ne...?? Naga ko kad'an bata tsaya ba kuma nasan tana jin irin kiran da nayi mata.."
"Bazata tab'a tsayawa ba.."
Da mamaki a fuskarsa ya kalleshi yana maimaita abunda ya fad'a sannan ya d'ora da fad'in
"Me yasa kace haka..?? Itan ba khadimar mahaifina bace..?? Ko kuwa bani da damar dakatar da ita idan ina buk'atar hakan..??"
"Ko kadan ba yadda kake zato bane,na tabbata tayi haka ne saboda bata son wani abu ya shiga tsakani,nd musamman duba da irin abunda ya faru,tabbas zata yi tunanin ko zamu zargeta da aikata wannan kuskuren ne,na rigaka sanin wace ce itan shi yasa na fad'a maka haka,amma bawai dan ina son kareta ba kamar yadda tayi akanka ba,ni na sani babu yadda za'ayi ta tsaya coz ban taba ganinta tsaye da wani ba ko da acikin hadiman gidan nan,sannan kuma idan kayi duba da yanayinka kai kanka lokacin daka tunkareta dole ne yasa ta kasa nutsuwa dan bata san me zai faru ba idan ka kusanceta,dan haka kawai ka d'auka hakan ya faru ne bisa kuskure..."
Shiru yarima yayi yana juya maganar a ransa,shi kuma YASEER bayan ya gama karanta masa abunda ya sani game da itan yaci gaba da sabgoginsa.Waiwayowar YASEER inda yarima YAZEED en yake jin yayi shiru,yayi dai² da k'arar shigowar text message a wayar YASEER en,murmushi yayi kafin ya shiga k'ok'arin duba inda sak'on ya fito kasancewar a time en babu damuwar komai a ransa,koda ya bud'e duk iya adadin yadda fuskarsa ta kai ga sakewa take cikin abunda baifi y'an dak'ik'u ba annurin fuskarsa ya disashe,haka nan tun bai kai ga gama karanta sak'on ba tuni har ya mik'e tsaye yana tsuke fuskar sa mai cike da rashin nutsuwa.A hankali ya shiga sake bibiyar sak'on cikin rashin nutsuwa
_"Shin kuna tunanin ku wasu masu wayo ne...Ko kuna tsammanin duk wani shirin mu akanku zaku iya dakatar da shi..?? Mun d'aga muku k'afa ne kawai ba don mun gaza ba,sai don rabuwa daku na wani lokaci..Wannan lokacin mun shirya tsaf domin k'addamar da duk wani shirinmu akanku ba tare da saurarawa ba,tabbas a yau kun tsallake troop na farko a sanadiyyar taimakon da kuka samu daga wannan yarinyar,sai dai a wannan karon shirin mu dole ne yayi tasiri akanku,ba kuma iya ku kad'ai ba,hatta da ita kanta tunda tayi k'ok'arin shiga abunda babu ruwanta sai fushinmu ya sauka akanta......!"_
'Daure masa kai sak'on yayi sam ya gaza fahimtar komai,a hankali kuma kamar mai tunanin wani abu ya juya ya kalli YAZEED dake zaune ya zuba masa ido,saurin juyawa yayi dan baya son ko kad'an ace ya fahimci halin da yake ciki,yasan gaba d'aya had'uwa za suyi cikin damuwa,shi kuma hakan ne baya so ya faru,yafi son ace shi kad'ai yake fuskantar duk wata damuwa da zata b'illo musu.Wani tunani ne ya fad'o masa nan take ya juya da sauri yayi yana tafiya,saurin kallonsa YAZEED ya sake yana girgiza kai kafin yayi masa magana
"Ina kuma zaka da kake k'ok'arin fita a wannan lokacin..??"
Ba tare daya waigo ba kasancewar yasan halin YAZEED da saurin b'aro jirgin mutum,duk yanda ka kai da b'oye damuwa matuk'ar ya kalleka yanzun zai iya fahimtar halin da kake ciki,yasa shima yak'i yarda su had'a ido,yana a yadda yake ya shiga bashi amsa still kuma yana ci gaba tafiya
"Yanzun zan dawo zanje gefen Ummi ne.."
Agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa ya d'ago ya kalla,ba tare da damuwa ba ya furta
"By this time around zaka je gefen Ummi'n..?? Kayi mene a can a irin wannan lokacin da ka riga kasan a rufe yake..??"
Saurin d'ago hannunsa shima yayi ya kalla sam baiyi tunanin lokaci ya tafi har haka ba shi yasa yaso shashantar da damuwarsa a nan idan ya fita,sai dai kuma kash lokaci ya masa tsiya,nd yana da tabbacin matuk'ar ya koma kusa da YAZEED yanzun tabbas ne saiya fahimci halin da yake ciki,d'an dakatawa yayi a inda yake yana tunanin abunda ya kamata yayi,ko kafin ya kaiga juyawa tuni YAZEED en ya cillo masa tambayar da tasa shi yunk'urin barin wajen babu shiri
"Kana cikin damuwa...Amma saboda ka koyo zurfin ciki shi yasa bazaka iya fad'awa kowa ba,mene kake tunani da zaisa ka b'oye min..!?"
Ba tare daya kalli inda yake ba shi enma ya bashi amsa
"A'a malam ni ban fad'a maka ina da damuwa ba,shi kenan mutum bashi da damar yin wahami akan abu sai yasa ka zargin ko ina b'oye maka wani abu ne.."
Murmushi YAZEED yayi mai sauti kafin ya furta
"Ka rainawa wanda bai sanka ba hankali..amma ni kam ka san ko me zaka fad'a ba yarda zanba.."
Shiru YASEER yayi dan baya so maganar tayi nisa,matuk'ar kuwa zai ci gaba da fad'a shima yana yi tofa dole ne sai YAZEED ya rafko shi,dan haka kawai sai yaja bakinsa ya tsuke ba tare daya sake tankawa ba,haka shima YAZEED ko da yaga YASEER en yayi haka k'arshe ma ya juya ya bar wajen kawai sai ya girgiza kai had'e da d'an d'aga murya,cikin sautin da yasan YASEER en zai jishi ya furta
"Shi dai duk mutumin dake zama cikin damuwa Allah yaso ya san makomar yin hakan...Ni kuma bazan gaji ba da tambaya sai dai in mutum yak'i fad'a saboda tunanin an takura masa,hakama addu'ar neman shiriya ba fasawa za muyi ba.."
Yana jinsa yasan da shi yake,ko da jin haka sai ya girgiza kai kawai had'e da sakin murmushi ya shige ciki abunsa.
^^^^^
A can b'angaren Jeeddah kuwa,tun daga sanda ta zauna tasa kukan nan,ta jima tana aikin abu d'aya cikin kuka ta shiga addu'ah,sai da tayi kirari ga ubangiji sannan taci gaba da addu'ah
"Ya Allah ka taimakeni ka fidda ni a cikin wanna damuwar...Na tabbata a yau matuk'ar aka san abunda ya faru babu wanda zai yarda da bani da laifi..Ya Allah ga baiwarka tana neman agajinka,Allah ka tallafi rayuwata ka kawomin mafita cikin sauk'i...!"
Ire²n addu'o'in da tayi ta yi kenan,haka addu'o'in da ta dinga yi har ita kanta bata san adadinsu ba,kuma ko ta fara bata kaiwa k'arshe take datsewa take kama wata,saurin mik'ewa tayi tana share hawayen fuskarta had'e da yin murmushi mai cike da godiya ga Allah,da sauri ta bar wajen ta nufi hanyan kitchen en dake cikin apartment en saboda wani tunani daya fad'o mata,dube² ta shiga yi zuciyar ta cike da fatan samun abunda take da burin gani a wajen,cikin sa'a kuwa tana bud'e freezer en idanunta suka sauka kan tarin lemon tsamin,hamdala tayi ga Allah kafin ta juya ta d'auka wani cup mai kyau ta shiga aikin yankawa da matse ruwan a ciki,sai data tara ruwan da d'an yawa,haka nan iya yadda take tunanin zai kai mata adadin da take nema kafin ta bari tana sake goge fuskarta da har lokacin gumi bai daina tsatstsafowa a jikinta ba,haka nan duka jikinta har lokacin bai bar b'arin da yake ba,a haka ta dawo cikin parlour'n tana haskawa da y'ar wayarta da kullum take mak'ale da ita,sanda ta iso gurin da suke saboda rashin tantance abun yi sai kawai ta tsaya tana raba idanu dan saboda rashin sanin ta yadda za'ayi ta aiwatar da abunda zuciyarta ke sak'a mata,ko da ganin tana dad'a b'ata lokaci a haka tuni wata zuciyar ta shiga bata shawara kan abunda yafi dacewa tayi,nan kuwa ta nemi guri ta ajiye cup en sannan ta matsa kusa da YASEER ta shiga masa magana,ta d'auki lokaci tana kiransa kafin ya iya amsawa,cikin tausasa murya ta furta
"Babban yaya ga ruwan ka sha..."
Murya na rawa tayi maganar
"Bazan sha ba..ko na ce miki ki kawo min ne..??"
Yadda yayi maganar cike da gadara,yasa ta yin Jim ba tare da tayi magana ba saboda tsabar fargaba,haka nan sam bata yi zaton hakan zai iya faruwa ba,duk a tunanin ta da tace masa gashi zaiyi obeying nata cikin sanyi ba tare data sha wahala ba amma kuma ga mamakinta saita ga sab'anin abunda tayi zato,har tayi niyyan rabuwa da su tayi tafiyar ta saboda maganar sam bata ji dad'in taba,sai dai ko data tuna cewar duk wanda yazo ya gansu a haka dole ne itace zata kasance mutum ta farko da za'a fara zargi,k'arshe kuma bata san mene ne zai faru da rayuwarta da ita kanta ba ta sanadin wannan kuskuren da take shirin yi,wannan tunani shi yayi tasiri akanta har taji dole ne akanta ta fasa tafiya,haka nan tana jin idan har ba tayi nasara ba na ceton su daga wannan mugun yanayin ba bazata iya tafiya ko nan da can ba,saurin katse tunanin ta tayi sannan ta ci gaba da lallab'a shi,a haka tun yana turjewa tana bashi hak'uri yana gayan magana son ransa,itanma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 63