Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
take mai kama da harara sai dai bata ce mata komai ba sai sake k'are mata kallo da take tana kuma karantarta "Shin hajiya zata miki k'arya ne..??" Girgiza kai tayi alamun a'a,nan Adda cikin b'acin rai ta ci gaba da magana "Wato halin nan naki ne bazaki chanja ba ko..?? Tun asali turbar da kika d'ora zuciyar ki akanta kike ko..?? Ke wace irin shaid'aniya cene da sam bakya jin bari.??" "Nifa Adda na fad'a miki ban yi wani abuba ki yarda dani mana.." "Taya kuwa zan yarda bayan nafi kowa sanin halinki,kinga idan baki bi duniyar nan a sannuba wallahi ina mai tabbatar miki wata rana abunda zaki gamu da shi sai ya wuce zaman kurkuku.." Ringima kai ta shiga yi tana k'unk'uni kamar wata yarinya,sai yan maganaganunta take a haka "Ki fito fili ki fad'a duk abunda ke bakinki ba wai ki tsaya kinamin k'unk'uni ba,ai ni dama tuni kika gama rainani tunda kinga muna kai d'aya dake..Allah ya sani ni ban baki tarbiyya irin wannan ba,amma kije ke da Allah,duk abunda kike yi yanzun kina ganin dai² ne wata rana zaki gane gaskiya idan kina da rabon ganewar.." "To waike Adda shi kenan daga mutane sun gaya miki magana sai kawai ki hau kai ni kizo kinamin fad'a bayan baki san komai ba.." "Iyeee..! Lallai ladidi ta kai miki,yanzun ni kike kallo kina fad'awa irin wad'annan maganganun ko..?? Shi kenan na gode ai ladan haihuwa kike biyana yanzun..Amma ki sani gobe ko kina so ko bakya so sai munje masarauta nabi ba'asin abunda ya faru..Nasan dole tunda hajiya take irin wannan fad'an akwai wani abu daya faru da bana nan,kuma ko rantsuwa nayi babu kaffara nasan kece shaid'aniyar.." "Ni kam gaskiya Adda babu inda zani ku dai kwaje da kuke da alak'a da su,amma ni me zai kai ni..??" "Idan kinga baki bimu ba gobe wollahi ki k'addara mutuwa kika yi,amma sahuna sahunku saina tusa ku a gaba munje nabi ba'asin fad'an hajiya,haka kawai a kanki bazan b'ata da ahalina ba,wallahi dole ne ki bini muje ko kuma ki san nayi.." Duk fad'an da Adda keyi da mita a lokacin duka tana yine badon komai ba sai don duk Ladidin ta fad'a mata abunda ya faru amma ina abu yaci tura dan ta bad'e idanunta da toka tak'i fad'a. Washe gari tun da safe Adda ta shirya,haka Aisha ma tasata ta shirya sannan suka zauna parlor suna jiran fitowar Ladidin,sun shafe mintuna a k'alla sama da arba'in suna dakon fitowarta amma shiru,Aisha Adda tasa ta duba mata ita ko ta shirya fitowar ne ya gagara,sanda ta isa bakin k'ofar d'akin nata nan ta isketa kwance ko tashima bata yiba tana ta faman bacci,komawa tayi ta sanar da Adda halin da ake ciki,ranta ne ya sake b'aci nan take ta mik'e ta nufi hanyar d'akin nata,tana shiga bata tsaya sauraren komai ba ta dai² ci cinyarta ta lafta mata duka a gurin,a firgice ta mik'e zaune tana soshe² saboda dukan ya shigeta,sai data gama wartsakewa tukun idanunta suka sauka akan Adda dake tsaye tana jifanta da mugun kallo "Wato saboda raini shi ne yasa zaki samu muyi ta jiranki mu ba yaranki ba,yo ko hadimanki kika maida mu ai bama b'ata lokaci haka akan jiranki ba.." "Nifa Adda na fad'a miki baza niba,da can banga abunda ya kaini gidan ba sai yanzun kawai ki sani zuwa,ni babu abunda zai kaini cikin wannan bak'in gidan.." "Baza kiba kika ce ko..??" Girgiza kai tayi tana kallon wani gurin daban "Wollahi kinji na rantse,matuk'ar baki bini munje ba,ki tabbata sai dai ki sauya wata uwar amma bani ba,haka nan kin san gidan nan nawa ne ko mallakina..?? Haka zaki tattara ki barmin gidana dan banga nima amfanin zama dake ba.." Saurin kalllon Adda tayi tana son tabbatarwa shin abunda kunnenta yaji haka yake kuma Adda'n ce ta fad'a..? Ga mamakinta tana d'agowa taga Adda harta juya ta kama hanyar fita a d'akin tana cewa "Minti goma na baki ki samemu a parlour,matuk'ar kika haura haka ki tabbata zaki barmin gidana ne.." Tana kallo Adda tasa kai ta fice a d'akin,nanfa tayi tsuru² a gurin zuciya cike da tunanin shin tabi Adda ko kuwa zata bi ra'ayin zuciyarta ne kawai ta tattara ta bar gidan kamar yadda ta buk'ata..? *ROYAL PALACE...* Shigowar motar Adda da Aisha ke driven ta samu guri nan a harabar k'ofar fada tayi parking,sannan suka fara takawa da k'afa zuwa cikin gidan,duk soron da zasu wuce bayine cikinsa haka nan sai gaishesu ake ta duk inda suka bi,a haka suka k'arasa wuce zaurukan suka b'illo ciki gidan,b'angaren hajiya direct suka nufa dan dama abunda ya kawo su kenan ba tare da sun biya ta sauran gefen ba bare su gaisa,tun daga sallamarsu da hajiya ta jiyo a k'ofarta ta kuma d'auki muryarsu ta d'auke kai,ba don dai hajiya ta san amsa sallama wajibi bane ina tabbar da a lokacin babu dalilin da zaisa ta amsa musu,a ciki² ta amsa ba tare data ko kalli inda suke ba bare Susa ran zata magantu,tun daga shigowarsu da yanayin sauyin da Adda ta gani a fuskar hajiya ya sake sawa ta fahimci lallai akwai damuwa,a haka dai ta tausashi ranta suka k'arasa har inda hajiyan take kana suka samu guri suka zauna,Adda ce ta fara gaida hajiyan,tun daga yanayin yadda ta amsa mata da yadda take d'auke mata kai sai duka taji bata ji dad'i ba,haka ko da ladidi da Aisha suka gaisheta k'in amsawa tayi kawai ta juyar da kanta,gyara zama Adda tayi ta fuskanci hajiya kafin ta fara magana "Hajiya Allah ya sani tun daga jiya da kika kirani a waya kina fad'a na kasa fahimtar dalilin fad'an nan naki,saboda ni dai bani da masaniya akan takamaiman abunda ya janyo hakan,wannan yasa yau na wanko k'afata takanas domin bin ba'asin faruwar haka...Dan Allah kina yiwa Allah da manzonsa,ina so ki duba girman wad'anda na had'a ki dasu ki taimaka kimin bayanin laifin dana miki da har ya janyo kin kirani kina irin wannan fad'an.." Ba tare da hajiya ta kalleta ba ta tab'e baki kana ta fara bata amsa "Yo ai Adda idan har kina son sanin abunda ya faru ne ba ta kaina ya kamata ki fara bin ba'asin maganar ba,sai ki bari ki fara bincikar wad'annan halittun na gabanki kafin kizomin da maganar baki sani ba.." "Shi kenan hajiya na gode,amma ki sani tun farko kafin nazo nan saida na tambayi ita Ladidin amma tak'i cewa dani komai,hasalima sai k'umbiya² takemin,wannan dalilin yasa na sako su a gaba muka zo,na tabbatar duk maganar da zaki fad'a babu yadda za'ayi wani cikinsu ya musa ta tunda a gaban idonsu ne.." "Shi kenan ai tunda sun kasa fad'a miki sai ki tattara su ku koma,dan nima banga amfanin yi miki bayanin ba.." Rok'onta Adda tayi ta fama tana had'a ta da girman Allah duk akan tana son ta fad'a mata,sai da kyar sannan hajiyan ta kalleta tana cewa "Shi kenan zan sanar dake abunda ya faru,tunda dai kin kafe saina fad'a miki,zan fad'a daga nan kuma sai ki yanke hukunci da kanki..." Tiryan² hajiya ta fara zayyanawa Adda abunda ya faru kamar yadda maimartaba ya shaida mata har ta kai k'arshe,ran Adda a mugun b'ace ta kalli ladidi da Aisha cike da bak'in ciki ta shiga yayyafa musu maganganu masu kaushi da suka sa nan da nan jikin Aisha ya k'arasa mutuwa,banda kuka a lokacin babu abunda take yi zuciya cike da tsantsar nadama da dana sani saboda sosai a lokacin kalaman Adda suka yi tasiri sosai a gareta,kasa d'ago kai ta kalli hajiya tayi saboda kwarjini da tayi mata,kanta a duk'e ta shiga bada hak'uri tunma kafin Adda tasa ta yin hakan tana fad'in ta gafarceta,sharrin shaid'an ne in sha Allah ko wani nema a waje bazata sake yi masa kwatankwacin haka ba,hajiya dai kam tana jinta har ta kai aya,koda ganin irin kukan da take ne a sanadiyyar k'in kulata da tayi sai yasa nan take jikin hajiyan itama ya d'an yi sanyi,har ya janyo ta d'an sauko daga mugun fushin data fara,ba tare data kallesu ba ta fara magana "Shike nan Adda komai ya wuce indai ta b'angarena ne,sai dai shawarar da har kullum bazan gaji da baki ba,haka tambayata gare ki shi ne shin duk lokacin da aka d'auka kina ina har wad'annan abubuwa suka faru..?? Me yasa zaki saki iyalinki haka sasakai ba tare da kina basu kulawar data dace ba.?? Ya kamata ace kin nutsu kin bawa ahalinki kulawa ta musamman wacce zata gina rayuwarsu ta hanyar data dace,ina fatan a yau kingano ma'anar abunda ake nufi da zumunci..??" "K'warai kuwa hajiya na gani wollahi,wannan ai babban darasi ne a rayuwa,amma wollahi duka ba daga ni bane wad'annan abubuwan suka faru,kamar yadda na shaida miki ne kin san harkokin kasuwancina ba anan k'asar nake yinsu ba,kuma ko da al'amarin ya faru wollahi bana nan,ban sani ba haka babu wanda ya sanarmin da asalin yadda abun ya wakana,sai yanzun da naji daga bakinki.." "Shi kenan ai Allah ya kyauta gaba ya sake kiyayewa..Amma yanzun sai ku k'arasa kusan ta yadda zaku fuskanci d'an Abdu ku bashi hak'urin zubar masa da k'ima da kuka yi..A matsayinku na wasu daga cikin ahalin sa ni dai ina ganin abun kunya ne ace haka ta wakana tsakanin mu,a matsayinmu na matsayin jini d'aya.." "In sha Allah hajiya zamuje kam,ko bama shi ba,yau ace wani ne haka ta faru da shi ai ya kamaci ban hak'uri ko da kuwa bazai yafe ba,ai neman gafarar wanda ka b'atawa shi ne dahir..." Juyawa tayi ga Aisha da ladidi cikin yanayin jin haushinsu duka tana fad'in "Sai ku wuce muje ai ko kun tsaya kallon mutane,kamar wasu mutanen kirki..Ai dana san abuna ya faru kenan wollahi tun a wancan lokacin nima da baku ga k'afata ba da sunan zuwa dubaku,da haka zan rabu daku duk yadda za'ayi da ku ayi.." Sum² suka wuce suna binta,godiya ta yiwa hajiya sosai sannan suka fice suka nufi gefen Fulani,a can enma dai basu wani samu fuska ba,har suka k'araci b'ab'atunsu,sai dai fulanin daga baya itama ta d'an sauka bayan ban hak'urin da Adda tayi ta mata da rok'on yafiya,a nan ne Adda take tambayarta Yarima dan tana so ita da kanta ta fara bashi hak'uri akan laifin da su ladadi suka kankama masa wanda bai jiba bai gani ba ya janyo masa mummunan hukunci,juyawa Fulani tayi zuwa gefen da y'an matan nata suke zaune suna hira abunsu kana ta furta *"ABEELA..!* maza je ki kira yayanku.." Saurin juyowa wacce aka ambata da sunan tayi tana sakin murmushi kana ta girgiza kai had'e da mik'ewa tana kama hanyar fita,Aisha ce ta d'ago idanunta shab'e² da hawaye har lokacin ta kalli Adda cikin wani irin yanayi kana ta furta "Adda dan Allah ki rok'amin Ummah Fulani ta bani dama nabi Abeela naje na fara bashi hak'uri..Kinji Adda wollahi bazan sake bin duk abunda wani zai sani ba.." Yada tayi maganar cikin muryar tausayi yasa Fulani tun kafin ta k'arasa ta tsaida Abeela kana ta yiwa Aisha'n izinin tabi ta su tafi,saurin mik'ewa tayi tana murmushi kana tayiwa Fulani godiya tabi bayan Abeela suka fice daga apartment en suna nufar apartment ensu Yariman.................... *Uhmmm..! Ko me zai faru kuma idan Yarima yayi arba da Aisha a irin wannan lokacin...???* #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@Hawwa M.U Pindiga.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻* ___________________ ヾ(✿⌒ ‿ ⌒✿)彡 🎂 _Life is very short,so enjoy every moment,dont lose your confidence,go always ahead._ *HAPPY BELATED BIRTHDAY IT'Z B.Y EBRAHEEM.* 🎂 ヾ(✿⌒ ‿ ⌒✿)彡 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 🇳🇬 *K'ASATA.* 🇳🇬 _My Nationality_ _Sis Ameerah Muhammad ina taya ki murnan kammala littafin ki na k'asata,fatan Ubangiji yasa afi haka,rabb yayi rik'o da hannayenmu baki d'aya,ya taimakemu wajen rubuta dai²,inda kuskure yake kuma Ubangiji ya yafe tare da fatan ya bamu ikon gyarawa a nan gaba,ameen._ *Pg 28.* ^^^^^^^^ Tafiya suke tana biye da Abeela banda kalle² babu abunda take yi,sakamakon hanyar data kasance mata bak'uwa,tun da takar zuwa hanya bata tab'a biyowa da ita ta nan ba sai yau,iya kacinta da gidan idan sunzo ko wani abu ya kawo su apartment en Hajiya,Fulani sai kuma apartment en Ummi'n YASEER,duk inda suka ratsa dakaru ne suke shawagi da tsaron ko wane kusurwa na gidan,a haka suka k'araso k'ofar apartment en sannan sukayi cirko²,Abeela dake kan gaba ita tayi k'ok'arin knocking,sai da suka d'an d'auki lokaci a tsaye kafin aka basu izinin shiga,cikin nutsuwa y'ar matashiyar ta tura k'ofar ta shiga da sallama a bakinta Aisha na binta a baya itama tayi sallama k'asa²,YASEER ne ya amsa kasancewar shi kad'ai ne kawai zaune a parlour'n kuma yana pacing k'ofar shigowa,tun shigowarsu idanunsa ya sauka akan Abeela nan take ya saki fuskarsa yana yi mata murmushi "Lil Sis..Yau kece a nan kuma.??" Y'ar dariya tayi itama kafin ta nemi saman hannun cuition ta zauna tana d'an juyawa kamar me neman wani abu "Yah fa yana nan kuwa...??" Sai daya jinjina mata kai kafin ya bud'e baki da niyyan yin magana,idanun sa ne suka sauka kan Aisha da sai a lokacin nema shi kansa ya ankare da cewar ba Abeela ce ita kad'ai ba,kamar wanda aka matsawa pause haka ya kafeta da ido yana kallo,zuwa wani lokaci kuma a hanakali ya shiga sake tsuke fuskarsa daga murmushin da yake yiwa Abeela'n yana nuna Aisha da hannu kuma yana magana "Abeela wannan kuma ina kika samota..??" Sai data kalleshi sannan tayi d'an murmushi kana ta fara magana "Ohh..! Yah Yaseer sis Aisha cefa,kuma Ummah tace mu taho tare,saboda tana son ganin Yah YAZEED.." Kai ya shiga girgizawa kana ya tab'e baki kamar yaga abun k'i fuska babu walwala ksannan yaci gaba da magana "Ok..! Da kyau..Duba shi cikin bedroom ina tunanin yana can.." Ya bata izini kafin ya gyara zamansa yana girgiza kai zuciyar sa cike da son ganin dramar da zata wakana idan YAZEED ya fito ya iske Aisha a gurin,mik'ewa Abeela tayi cikin sauri ta kama hanyar da zata sadata da inda bedroom en nasa yake,nan enma sai data yi knock,daga ciki YAZEED yana kwance saman resting chair ya kallo k'ofar,ba tare daya tambaya ba ya mik'e ya nufo k'ofar cikin jin haushi dan a tunanin sa YASEER ne yake neman raina masa hanakali shi yasa yak'i yin magana kawai,yana bud'ewa cike da son yiwa YASEER en masifa idanun sa suka sauka kan Abeela,tsaki kawai ya iya ja kafin ya furta "Mene ne kuma..??" Itama ba tare da wata damuwa ba ta furta "Ummah ke kiranka.." Jingina kai yayi kafin ya furta "Muje.." Juyawa tayi shi kuma yana biye da ita a baya suka fito,sam ko daya fito hankalinsa bai kai masa kan Aisha dake zaune ba sai YASEER kawai daya kalli sashin da yake yana cewa "Broh..! Naje apartment en Ummah na dawo.." "Ok..! Sai ka dawo..Amma kuma kayi bak'uwafa.." Har ya kusa da bakin k'ofa ya juyo yana shirin yin magana "Bak'uwafa..! Kuma akace maka ni take nema..??" "K'warai fa,ai dawowa ya kamata kayi baka tsaya tambaya ba.." Tsaki yaja kafin ya wuce abunsa yana fad'in "Idan ta damu da ganina sai ta jira na fara amsa kiran mahaifiyata.." "Da kyau Mr wright.. Sai ka dawo.." Ficewarsa yayi ba tare daya sake ko da waiwayowa ba bare Susa ran zai dawo yaba wacce aka ambata da bak'uwar tasa,duk da ya ganta zaune sanda ya waiwaya hakan ba wai yana nufin ya ganeta ba,hasalima ko daya kalli gefen da take bai iya hango fuskar taba bare ace ya shaidata ya kama hanyarsa yayi waje abunsa,wani k'ayataccen murmushi YASEER ya saki dan dama yasan dole za'a rina,yadda yake da kyakykyawan sani akan YAZEED ya tabbata matuk'ar yaji kiran Ummi'nsa tofa duk wani mai uzurin son ganinsa sai dai ya jira dan babu yadda za'ayi ya tsaya sauraren wani har sai bayan yaje ya dawo,Abeela ce kawai ta iya dawowa da baya har zuwa inda Aisha'n take tana cewa da ita "Sis ki taso muje kawai dan babu lallai ya dawo yanzun.." Jiki babu k'wari kamar kazar da aka jefa da gishiri ta mik'e ta bita suka fice zuwa gefen Fulanin dan kashe boss en a can kamar yadda aka fara,dai² shigowar su YAZEED ya d'ago kai saboda maganar da Umma'n nasa take masa a lokacin na batun su Ladidi da suka zo neman afuwarsa, yasa shi jin maganar wata daban,su kum suka shigo cikin turakar tata,nan take idanun sa kuwa suka sauka kan Aisha data shigo bayan k'anwar tasa,ganinta a lokacin tuni ya haddasa masa yin wata irin mik'ewa da bai shirya mata ba yana tsuke fuska had'e da jiranta da kallon tsana,cikin fusata gami da b'acin rai ya shiga nunata "Ummah dama akan wad'annan kike magana..?? Matuk'ar ace wad'annan sune wanda kike nufi na yafe musu babu abunda zai sani aikata haka,tsakanina dasu tun daga ranar da suka aikata min ta'addacin daga nan gaba ta shiga tsakaninmu ni da su babu wata alak'a a tsakaninmu face ta tsantsar k'iyayya daga nan kuwa har tashin duniya,koda ace yafiyata itace kad'ai abunda zai basu nutsuwa a rayuwa,da ace na yafe musu har abada gara suyi ta rayuwa cikin tsakani mara iyaka..Saboda haka Ummanah kiyi hak'uri kawai ki dena sa baki akan wannan maganar,ni dasu matuk'ar muna raye ina tabbatar miki bazamu tab'a zama k'ark'ashin inuwa guda ba,na tabbata matukar suna nan tofa duk inda suka yada zango zasu gurb'ata ni'imar da Allah yayi a wajen ne..Ina sake tabbatarwa babu yafiya tsakanina dasu.." Yana fad'in haka ya rusuna yana cewa "Ki huta lafiya...!" Cikin nutsuwarsa ya kama hanyar ficewa abunsa ba tare daya ko sake waiwayowa baa,haka itama Fulani tana kallo yasa kai ya fice ba tare data tsaida shiba,sai bayan fitarsa a gurin ne Fulani ta numfasa kana ta waiwayo ga Adda da fuskarta ta nuna tashin jin dad'in kalamansa "To Adda ina fatan dai kunji abunda ya fad'a,da fatan za kuyi hak'uri ku kuma ci gaba da jinkirtawa wata k'ila nan gaba idan ya sakko Allah ya bashi ikon yafe musu.." Kasak'e Adda tayi ta kasa cewa komai har sanda Fulani ta kai aya sannan ta jinjina kai tana fad'in "Gaskiya ne Fulani naga abunda ya faru,kuma naji komai daga gurin hajiya,sai dai duk da haka gaskiya banji dad'in furucin da yarima yayi ba,duba da kasancewar ladidi matsayin kamar uwa take a gareshi,haka ko ke kanki ai ya kyautu ace kin rusunar da shi ya yafe musu haka nan tunda har Allah yasa suka gane sunyi ba dai² ba kuma suka zo da niyyar neman gafarar abunda suka aikata.." Murmushi Fulani tayi mai taushi tana jinjina kai kana ta furta "Haka ne kam Adda maganar ki,tabbas ladidi tana matsayin kamar uwa ne a gurinsa,sai dai kuma tun a farko ita kanta bata d'auke shi matsayina d'a ba,na tabbata data kalleshi da wannan matsayin haka bazai tab'a faruwa ba,haka nan koda ace wani taji labarin zai aikata masa haka matuk'ar tana matsayinta na uwa dole ne zata yi k'ok'arin bashi duk kariyar daya dace,sai dai kuma kash itan da kanta tayi k'ok'arin ganin ta gurb'ata masa rayuwa..Kinga kuwa ni duk abunda yace bazan tab'a ganin laifin sa ba,matuk'ar kuma nace zan biyewa abunda kuke so har ya zama na tursashi ya yafe musu na tabbata banyi masa adalci ba a matsayina na mahaifiya..." Shiru Adda tayi banda jinjina kai babu abunda take ba tare data sake cewa komai ba,sun jima a gidan kafin sosai kafin suka yiwa Fulani sallama suka fito har lokacin jikin Adda yana a yadda yake nabayyanar da rashin jin dad'in ta. Cike da b'acin rai shima yariman ya fito a side en na mahaifiyar tasa ya nufi nasu apartment en,yana shiga kuwa ya buga k'ofar da k'arfi dan yadda zuciyarsa take masa rad'ad'i kamar ana hura masa wuta,yadda aka yi banging k'ofar yasa YASEER dake kwance d'agowa dan ganin waye,duk da yasan mutum d'aya ne zai yi hakan,koda ganin YAZEED fuska a d'aure yasa shi fahimtar akwai damuwa,tab'e baki kawai yayi kana ya maida kansa ya kwantar ba tare daya tambayi ba'asi ba,safa da marwa YAZEED ya fara a kusa da YASEER en yana jinjina kai har lokacin abunda ya faru yana sake b'ata masa rai,cikin bak'in ciki kuwa ya furta "Lallaima mutanen nan basu da hankali..!" Sake d'agowa YASEER yayi ya kalleshi da mamaki jin yadda yake magana shi d'aya, k'wafa YAZEED en yayi sannan ya nemi guri ya zauna yana sake jinjina kai,da ganinsa kasan al'amarin yana addabar ransa har lokacin. ^^^^^ Bayan barin su Adda a gidan ko cikin mota da suka d'auki hanyan komawa gida,babu wata hira a tsakaninsu,duk sunyi jigum² musamman Aisha dake driven,tunanuka ne iri² a ranta sai dai ta rasa yadda za tayi dasu,haka ko idan ta tuna abunda ya faru yanzun babu jimawa sai taji zuciyar ta kamar zata fasa k'irjinta ta fito dan bak'in cikin daya tokareta,ga ladidi kuwa babu wata damuwa a ranta dan da alamun har lokacin babu wata nadama a tattare da ita,kallonsu tayi duka ta tab'e baki kafin cikin takaici ta fara magana "Ai ni wollahi dama nasan za'a rina,shi yasa tun farko ban so biyoku ba,amma Adda kika matsamin sai dana biyo ku,yanzun Fisabilillahi..! Ina amfanin zuwan namu..? Munzo an wulak'antamu haka kawai,kema ai Adda wollahi da laifinki yanzun ki duba abunda wannan Hafsatun tayi mana wai ita nan tana ji ana ce mata Fulani sai wani d'aga kai take,har ta kalle ki wai ta fad'a miki cewa ita bazata iya tursasashi ya yafe ba..Uhmm! Nifa Adda da zaki ja bakinki kiyi shiru ki zubamin ido da wollahi sai na koyawa ahalin hajiya hankali kuma har ita ba kyaleta zanba.." Ita dai Adda tana nan zaune cikin motan tayi shiru ne kawai kamar mai tunani sai dai tana sauraren duk maganganun dake fitowa daga bakin ladidin,ajiyar numfashi tayi sannan ta kallo ladidi dake gefen Aisha daga gurin mai zaman banza,kamar wacce zata yi magana akan wani abu mai muhimmanci ta jinjina kai kafin ta d'auke kai tana kallon gefe "Ladidi kenan..! Na tabbata baki san irin tarin bak'in cikin dake raina ba,amma har na iya dannewa muka kawo yau,badon komai ba sai don rashin sanin ta inda zan b'ullowa lamarin,tsawon shekaru ina dakon wannan al'amarin ba tare dana furzar da shi ba,sai dai yanzun ni kaina na

Chapter 22 of 63