har suna son ganinmu da kuma neman biyan buk'atunsu.."
'Dan murmushi Yaseer yayi,sai da suka tab'a wasa da dariya tsakanin su bisa ga al'adar su,sannan ya nemi Yaseer en daya sanar da shi maganar daya fad'a ta kaishi.
Jawabin komai Yaseer yayiwa Matawalle daya shafi case en yarima YAZEED,har ya kai k'arshe sannan ya k'ara da cewa
"Amma Abba ina ganin wannan shaidar ita kad'ai bazata isa tasa a saki YAZEED ba..."
"Zata isa Yaseer dan kuwa gamsashshiya ce ga duk wanda zai saurareta,sai dai inda gizo yake sak'a shi ne b'arin ita wannan yarinya daka fad'a min yanzun,lallai ne a duba nata lamarin itama,idan har muka ce zamu fito fili mu bayyanata a matsayin shaidar da muke da ita tofa kamar yadda ta fad'a d'in ne komai zai iya faruwa da rayuwarta,dole ne kafin a saki YAZEED sai munyi k'ok'arin ganin mun bata kariya ta yadda babu wani da zai iya samun damar cutar da ita..."
"To amma Abba taya zamu bata kariya bayan tun farko ita ta fara jefa YAZEED a matsala..Ina ganin koma mene ne take fad'a zai faru da ita hakan zai zama BARAZANA ne da ake mata amma bawai dan hakan zai kasance ba.."
Murmushi Matawalle yayi kafin ya furta
"Yaseer kai yaro ne,wannan maganar ba irin tace wacce ake saurin yin sakaci da ita ba,dole ne kafin muyi komai sai mun bi shi a sannu,amma maganar fitowar yarima daga kurkuku ko a yanzun muna da damar da zamusa a sake shi,sai dai maimartaba yayi hani da hakan tun a wancan shekarun da suka gabata.."
Shiru Yaseer yayi yana sauraren Matawalle da bayanin da yake masa har yakai aya,dogon numfashi ya saki kana cikin sanyi ya furta
"Shi kenan Abba duk yadda kace hakan za ayi,in sha Allah kuma zan kiyaye duk abunda kace,Allah ya k'ara girma.."
Daga haka suka yu sallama da juna sannan suka ajiye wayar a lokaci guda..........
_To nima dai na ajiye birona sai mu tara zuwa gobe da yardar Allah....._
_DON'T FORGET TO VOTE ME ON WATTPAD @jeeddahmu898._
#Vote.
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
____________________
*Pg 8.*
^^^^^^^^
Suna gama waya da Matawalle ya gyara zamansa a saman kujeran da yake yana lumshe idanunsa,zuciyarsa cike da tunanin sak'on da aka turo masa,haka ganin inuwar nan daya rasa dalilin da yasa take yawan giftawa duk ya tsaya masa a rai,knocking k'ofa akayi yana a yadda yake ba tare daya d'ago ya kalli gurin komai shigowar ba ya furta
"Shigo...!"
"Ranka ya dad'e gashi..."
Bawan ya furta yana mik'o masa glass cup da ruwan lemo a ciki,a hankali ya bud'e idonsa ya kalleshi sannan ya furta
"Ajiye ka fita.."
Ajiyewa yayi sannan ya juya kamar wanda baya son tafiya,kallonsa Yaseer yayi cikin d'an d'aga harshe ya furta
"Kaje mana ba na sallameka bane kake tsaye a nan.."
"Afuwaan! Yallab'ai.."
Yadda yake tafiya cikin sanyi yana waiwayensa yasa YASEER kallonsa yana buga tsaki
"Idan baza ka tafi ba ka dawo ka nemi guri ka zauna,duk sanda kaga na sha sai ka tafi.."
Yadda yaga yanayinsa ya fara sauyawa yasa shi saurin ficewa daga part en yana sunk'e kai k'asa,bayan fitarsa Yaseer ya juyo yana kallon cup en daya ajiye,k'urawa cup en ido yayi kamar mai nazarin wani abu,ko mai son gano wani abu a cikin lemon,haka nan yaji bazai iya shan lemon ba kamar yadda zuciyarsa bata aminta da shi ba gaba d'aya,wani tunani ne ya fad'o masa da sauri ya mik'e ya fita yana neman bawan daya kawo masa lemon,duka sai daya duba bayin da suke iya shiga gefensa amma babu wanda yake nema a cikin su,haka nan yayita dubawa amma baiga wanda ya kawo masa lemon ba,hankalinsa ne ya gaza kwanciya cikin sauri ya koma side ensa ya d'auka wayansa ya shiga kiran line Ummi yaji ko ita ce ta aiko masa da lemon,sai dai kash sam itanma ba ita ta aiko masa ba,hasalima ita bata fahimci abunda yake fad'a ba,da wanda yake nufi ya kai masa lemon,cup en ya zara cikin fusata ya nufi kitchen da shi sai juya shi yake a hannunsa yana sake k'are masa kallo,cikin sink ya watsashi sannan ya bar fasashshen cup en a nan ya fito ya koma ya zauna yana sake tuna maganganun da suke cikin text en da aka turo masa.Take mugun nama ta fara masa kaikawo cikin k'irjinsa,idan ya tuna maganar cewar daga zaran an saki yarima yazeed tofa babu shi babu mulki kenan,sai kuma yaji zuciya na masa hud'ubar kawai ya binne duk wata gaskiya da yake tare da ita,idan kuwa har zaiyi k'ok'arin fitowa yayi yak'i a saki yazeed en tofa gaskiya ne babu wata dama da zai sake samu da zata masa jagoranci zuwa ga mulkin garin kamar yadda zuciyarsa ta fara kwad'aita masa tare da k'awata masa mulkin,wannan tunani shi yayi tasiri a zuciyar Yaseer da yasa shi lokaci guda ya fara jin zuciyarsa na neman canja masa akalar tunani.
Tunaninsa ne ya koma kan inuwar da take yawan gifta shi,a fili ya furta
"Shin wane ne wannan inuwar...?? Mene ne dalilin ta na rab'ata a lokuta mabambanta...??"
Shiru yayi saboda rashin amsa da wanda zai bashi amsan tambayoyin dake dank'are a cikin zuciyarsa daya rasa wanda ya kamata ya tunkara ya amsa masa,haka nan zuwan wannan bawan daya kawo masa lemo,duk da bai sha ba yana jin zuciyarsa na sanar da shi lallai ne akwai *WANI AL'AMARI* dake shirin faruwa koma yake kan faruwa,to amma taya zai fuskanci hakan...? Shin da gaskene wani ne yake shirya wad'annan abubuwan kamar yadda ya fara tunani ko kuwa dai zuciyarsa ce ke k'iyasta masa hakan zai iya faruwa..? Wannan tambaya ita tafi komai yi masa yawo acikin k'wak'walwarsa,cikin nutsuwa ya mik'e hannayensa a goye a bayansa ya shiga zarya a cikin parlor yana tunani akan abubuwa da dama.
"Dole ne nayi wani abu,idan ba haka ba komai zai iya faruwa..."
Ya furta a fili dai² lokacin da yake sake kiran line Ummi,bayan ta d'aga nan yayi mata bayanin komai daya sani daya shafi binciken da suka fara tun kafin yanzun,hatta maganar inuwar dake yawan wucewa da maganar bawan daya kawo masa lemo bada jimawa ba ya sanar da ita,ba tare daya iya b'oye mata komai ba,ita kanta Ummi'n tayi mamaki sosai dan tana da tabbacin ba kowa keda ikon shigowa cikin masarautar ba,bare kuma har ta kaishi ga yayi basaja ya shiga inda ransa ke so ba,amma to ta yaya har haka ta faru wani daban can ya shigo ya tsallake duka masu tsaron gidan ya nufi gefensa..? Lallai ne akwai wani abu dake kan faruwa da su.Katse tunanin da take yi tayi saurin yi,sannan ta shiga masa nasiha akan koda yaushe ya kasance mai jin tsoron Allah,sannan ya tsarkake zuciyarsa a koda yaushe,kada ya kuskura ya bari dai² da second d'aya shaid'an yayi nasara akansa,bare har yayi masa hud'uba ko k'awata masa sarauta,ko maganar sarautar daya fata matama sai dataa gargad'e shi daya d'auke idonsa akan mulkin masarautar,yadda ta nuna masa hatsarin dake cikin mulkin da halin da zai iya jefa kansa yasa shi jin mutuwar jiki,nan take sarautar ta fice masa akai,dama tun asali shi en bawai yana sha'awar zama mai mulkin ba,a'a lokaci guda sanadiyyar sak'on da aka turo masa aka so asa masa kwad'ayin zama sarkin.Nasiha sosai ta masa mai ratsa jiki wacce jinta kad'ai ya sake k'arfafa masa guiwa akan taimakon d'an uwan nasa daga halin daya tsinci kansa a ciki har na tsawon shekaru biyar,suna gama waya da Ummi ya shiga juya wayan a hannunsa,hamdala yayi ya kuma godewa Allah da baisa shi ya aikata abunda zai zo yana nadama ba,cikin sauri ya turawa matawalle duka recodings en daya turo sannan ya kashe wayan nasa gaba d'aya,dan yadda yake jin jikinsa tamkar zazzab'i na shirin kama shi,zuciyarsa kuwa ji yake tana neman yiwa k'irjinsa nauyi...
^^^^^
*B'ANGAREN YARIMA YAZEED...*
A gefen yarima yazeed kuwa tun bayan da aka kaishi REMAND HOME en a lokacin yana d'an shekaru sha biyar a duniya dai² da sau d'aya bai tab'a kawowa a ransa zaiyi irin wannan zaman ba,dan ko a can lokacin yana gidan kangararrun yaran bai kawo zai haura y'an watanni ba tare daya fita ba,sai dai har ya shafe shekaru uku a gidan sannan aka sake masa chanjin guri daga nan zuwa PRISON en ta nan goron dutse,ko da chanja masa gurinma yanzun da zamansa a cikin prison en shekaru biyu kenan,haka tun zuwansa tsawon wad'annan shekarun ko sau d'aya bai tab'a ganin maimartaba ba,hakama mahaifiyarsa,y'an uwansa mata da duka wasu ahalinsu,kaf maimartaba ya hanasu zuwa gurinsa haka babu wanda yake gigin zuwa,sai ko idan aka d'auke yaseer da kusan ko wane lokaci idan yayi ra'ayi zaije ya ganshi,ta b'angaren iyayensa mata sai dai ko suyi aike a gano musu lafiyarsa,iya tsayin wannan lokacin gaba d'aya kamanninsa sun sauya yayi duhu haka ya tara uwar k'asumba duka ya zama kamar wani tsohon daya shekaru saba'in a duniya,tun shigarsa kawo wannan lokaci ko kad'an yak'i yarda ayi masa aski,kullum ka ganshi shi kad'ai yayi shiru ko yana karatu,haka kullum yana killace abunsa babu sabgar wanda yake shiga,haka ko zamanin da yake can a remand home bai yarda yayi aboki ba,hakama cikin prison en tun shigowar sa bai yarda ya had'a hannu da wani ba bare ace har yayi aboki,a kullum bashi da burin daya wuce ace maimartaba ya fahimci sharrin da aka masa,shi bama ta a sake shi yake ba,a'a gurinsa da fatana har kullum maimartaba ya fahimci AL'AMARIN,tunda yaga sa ran da yake akan kwanaki kad'an zasu d'auke shi a cikin gidan,a fidda shi har sun zo sun shud'e amma shiru kake ji,wannan tasa shi ya fidda rai dan zamansa a gurin tsawon wannan lokacin yasa shi sawa ransa hak'urin dole dan tabbacin daya samu akan tun daya kawo yanzun babu shi babu barin gurin har sai ya cika wa'adin da aka d'ibar masa.
*BAYAN KWANAKI BIYU...*
Yana zaune a d'aki da alk'ur'ani a hannunsa,yayi nisa wajen karatu inda yake cikin karanta suratu alii imraan,guard ne ya zo dan sanar masa yana da bak'o,kasancewar ya bawa k'ofa baya yasa shi girgiza masa kai kawai ya masa alamu,juyawa yayi ya fita sannan yazeed en ya tak'aice karatun da fad'in
"Sadak'allahul aziiym...!"
Waiwayowa yayi sannan ya sauke tashi ka fiya nacin daya kifa akansa,yana juyawa suka yi ido had'u da matawalle tsaye yana k'arewa d'akin dama shi kansa kallo,da sauri yazeed en ya mik'e ya nufe shi idonsa d'auke da hawayen farin ciki dake sauka daga idanunsa,yana niyyan tsugunawa matawalle ya rik'o shi ya rungumeshi cike da tausayawa rayuwarsa,sun d'auki lokaci a haka sannan Matawalle yayi masa bayanin dalilin zuwansa gare shi,kukan farin ciki yazeed yasa da tun zuwansa bai tab'a hawaye masu sanyi ba sai wannan ranar data zo masa da tarihin daya dad'e yana mafarki,bayan gama koke²n yazeed da tsantsar jimami daga gurin Matawalle bisa ga abunda maimartaba ya aikatawa d'an cikin nasa wanda shi kansa Matawalle'n dama wasu daga cikin y'an majalisar sarki suke ganin anyi rashin adalci wa yazeed en na k'in bada lokaci ayi bincike da maimartaba ya hana ayi tun farko,haka ajiye shi acikin mutane da akayi maimakon a killace shi kamar yadda ake yiwa wasu y'ay'an manyan da ake kamawa,amma gashi yazeed en sai maimartaba ya hana duk ayi masa haka,kuma yasan duka yayi hakan ne ba don komai ba sai don gujewa zagin mabiyansu,wanda yin hakan da yayi kuma ba zai rage ko ya k'ara abunda mutanen suka yi niyyar fad'a ba,kamar yadda shi en yake ganin hakan zai basu kariya daga gujewa zage²n.
Sun jima a haka kafin Matawalle yayi umarnin ayiwa yazeed en aski wanda da kyar shi kansa yazeed en ya yarda aka masa,sai da yaga ya d'an fara samun nutsuwa har yana iya yin murmushi sannan yayi masa sallama akan ya jirayi dawowarsa bada jimawa ba,nan ya fice a d'akin ya barshi ransa a b'ace.
Direct office en shugaban gidan ya nufa da zuwansa bai tsaya wata² ba ya fara masa fad'an wulak'anta d'ansu da akayi,taya zasu barshi cikin ko wane irin mutane..?
Hak'uri ya bashi sannan ya fad'a masa shi kansa ba laifinsa bane,sak'on maimartaba ne hakan daya turo musu akan kada su kuskura su ware masa gurin zama shi kad'ai,yadda ya masa bayanin hakan yasa Matawalle fahimta duk da dai yaji babu dad'i,shi kam gaba d'aya ma ya rasa fahimtar halayen maimartaba akan wasu abubuwan da yake aikatawa,lokuta da dama idan yayi wani abun tamkar bashi ba,ko a fada wasu lokutan sai yayi abu amma su kasa fahimtar dalilinsa nayin hakan.
Sunyi maganganu da shugaban gidan kafin ya gabatar masa da hujjojin dake tattare da shi akan case en na yazeed,shi kansa incharge en tun lokacin baya yaso yin wani abu akan matsalar yazeed en,dan dai kada ya shiga cikin case en ne da kuma jan kunnen da maimartaba ya musu akan kada wanda yasa hannu wajen fitar da yazeed en yasa baiyi k'ok'arin yin wani abu ba,amma kam da tuni ya jima da fitar dashi,sai dai kuma yakan gaza fahimtar dalilin maimartaba akan hukuncin da aka yankewa yazeed en ba tare da an tsananta bincike ba,sam shi halinsa ba irin na sauran jama'a bane,ya jima yana aiki a gurin kamar yadda yasan manyan mutane da dama idan aka ce yau an kama nasu yayi laifi sukan tsayawa iya yinsu na ganin ba'a hukunta shi ba,amma shi maimartaba sarki Abu yazeed nasa salon sai ya bambanta dana saura.
Nan Matawalle ya nuna buk'atarsa ta son a saki yazeed en a lokacin,hak'uri incharged en ya bashi sannan ya k'ara masa da bayanin yayi hak'uri har zuwa washe gari idan aka zauna a court aka k'ark'are case en sai a sallame shi,a nasa ganin wannan hanyar ita yafi kamata dasu bi wajen tsarkake yariman daga mugun zargi sannan kuma hakan zai sa wad'anda suka masa k'ullin bazasu fahimci komaiba bare suyi yunk'urin guduwa.
Haka ba don Matawalle yaso ba ya hak'ura suka tsaya akan washe garin,ma'ana dai kamar yadda aka fara a court en masarauta a k'are a can,da wannan jawabin matawalle yama yazeed sallama sannan ya kama hanyar komawa gida...........
^^^^^
Jeeddah kuwa a nata gefen tunda Yaseer ya sanar mata da sun kammala komai na dangane da case en yarima yazeed hankalinta sai ya kwanta dan tana da tabbacin wannan hujjar ta isa zama gamsashshiya da zata sa a sake shi bada b'ata lokaci ba,sai dai hankalinta har yanzun bai gama kwanciya ba,basin komai ba sai don matsalar da Aisha ta sanar mata zata iya fuskarta matuk'ar suka yi yunk'urin bayyana gaskiya game da case en na yarima yazeed,haka tun bayan rabuwarsu da Aishar take yawan jin fad'uwar gaba mai tsanani.
Zama tayi ta buga tagumi zuciyarta cike da fargabar abunda zai iya biyowa baya,dan tunda Aisha ta shaida mata kad'an daga cikin halayen Ladidi take fargabar wani abu ya sameta,harta mik'e zata fita kuma kome ta tuna ta koma ta zauna tana d'aukan wayarta,d'an gajeran sak'on ta rubuta sannan ta turawa Yaseer en cikin sauri.
A dai² lokacin da sak'on ta ya riski Yaseer kuwa suna tare da Matawalle yana masa tambayoyi game da yadda za'ayi a kamo Ladidi da ita kanta Aishar dan gudun kada su samu labarin za'a saki yazeed su gudu,tunda har ya zama yanzun akan samu siririn cikin gidan yana fita ba tare da sanin ahalin masarautar ba,yana gama dubawa kuwa ya saki murmushi sannan ya sanar da Matawalle abunda ke kan faruwa kamar yadda jeeddan ta tura masa sak'on,suna gama maganar Matawalle ya tashi wasu mutum biyar cikin amintattun bayinsa da sarki Abu yazeed ya bashi ya musu bayanin abunda yake buk'atar su aiwatar a lokacin na zuwa a kamo masa Ladidi da y'arta Aisha,sannan su kasance cikin taka tsantsan kada a samu matsala,bayan ya sallame su suka kama hanyar gidan Ladidin da niyyan k'wamusota kamar yadda aka basu umarni.
Kamar yadda aka musu umarnin haka suka yi ba tare da sunyi wata² ba suka dak'umo Ladidi da Aisha suka nufi gidan Matawalle dasu dan dama abunda yace dasu kenan da zaran sun kamosu to su kai masa su gidan shi zai adana su har zuwa wayewar gari,koda suka cika umarnin bayan sun sanar masa hamdala yayiwa Allah sannan ya sallami Yaseer akan sai gobe idan Allah ya nuna mana lokacin zaman fada,da wannan shima YASEER en ya kama hanyar komawa gida zuciyarsa cike da taradaddin abunda zai wakana a zaman kotun..
*WASHE GARI..............…..*
_DON'T FORGET TO VOTE ME ON WATTPAD @jeeddahmu898._
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
_Wannan page tukuici ne ga duk wani masoyina kuma masoyin littafin *WANI AL'AMARIN* haka zalika musamman ga y'an *WANI AL'AMARIN FAN'S* ku en na daban ne a gurina dama zuciyata,yadda kuke sank'amo tekun comments yasa har bana son yin missing na typing,gaskiya comments enku na sani nishad'i sosai ina jin farin ciki,kuna k'ok'arin wankemin zuciyata da sharhinku akan wannan novel,fatan rabb yasa ku d'ore da haka..._
___________________
*Pg 9.*
^^^^^^^^
Yadda k'ofar fada ta d'inke ta cika mak'il da jama'a,abun sai ya so baku mamaki,duk inda ka duba jama'a ne iya ganinka,abun d'aure kan da mamakin kuwa bai wuce ganin babu wata sanarwa da akayi bisa hakan ba,amma jama'ar dake wajen tamkar idin yaumul-adhaa,tun kafin a zauna a fada maimartaba ya fito daga gida tuni har jami'an gidan yarin sun bayyana tare da Yarima YAZEED,wannan yasa sai jama'ar fadar basu kawo zargin ko wani ya sanar da jama'a abunda yake faruwa ba.
Cikin farin ciki da samun y'anci a wannan ranar yarima ya fito daga cikin motar kurkukun,da Yaseer suka fara arba ko da ganinsa take suka rungume juna suna masu farin cikin sake kasancewa tare a lokacin,daga nan cikin gida suka nufa su duka Yaseer rik'e da hannun yazeed suka nufi b'angaren mahaifiyar yazeed en.
Fulani na zaune cikin turakar ta suka yi sallama,ba tare da jiran izinin shiga ba suka kunna kai ciki suna masu sake yin sallama a karo na biyu,muryoyin da kunnenta ya kwaso mata su suka haddasa mata d'agowa daga duba littafin ADDU'A'U MIN KITABB WAS-SUNNAH da take cikin bincikenta na neman ayatur-ruk'yah,fuskarsa kad'ai ta Kalla tayi saurin mik'ewa tsaye tana binsa da kallon tsantsar mamaki,murmushin k'arfin hali yazeed yayi sannan ya nufeta da saurinsa,yana niyyan tsugunawa a gabanta tayi saurin rik'o shi tana fashewa da matsanancin kukan yadda taga d'an nata ya koma kamar wani dattijo saboda sauyawar da halittarsa tayi,cikin muryar kuka take fad'in
"Yazeed kai ne...? Ko kuwa dai mafarkin dana saba yi ne yake neman sani na zauce...?? 'Dan nan kamin magana kona tabbatar ba a mafarkin dana saba ganin ka bane.."
Kasa magana yazeed yayi sai murmushi mai cike da hawaye da yake sake mata saboda tsabar farin cikin da yake binsa a ciki,nan ya samu damar rungume mahaifiyarsa,yana sake shak'ar iskar y'anci,shi kansa Yaseer yadda yaga sun koma yau sai duk suka bashi tausayi,komawa yayi ya zauna sannan ya tankwashe k'afafunsa yana binsu da kallon da Allah kad'ai yasan ma'anarsa,ga Fulani kuwa yadda ta k'ank'ame yazeed en ji take idan har ta sake shi yanzun tofa zata iya bud'e ido taga duk abunda ya wakana a cikin bacci ta gansa,jin irin rik'on tsaurin da tayi masa yasa shi bud'e baki yana fad'in
"Ummata nine fa YAZEED enki,gani gabanki a yau cikin hukuncin ubangiji da yardarsa,kuma da izininsa komai zai zama tarihi..."
Jin muryarsa yasa Umman tasa d'agowa da sauri ta kalli fuskarsa tana k'ura masa ido had'e da tattab'ashi duk dan ta tabbatar gaske ne ba k'arya bane,sai da taji ta gamsu sannan ta furta
"Yazeed kai ne...? Kai ne ka koma haka..??"
Sai kuma ta sake fashewa da kuka,su kam dukansu nan suka tsaya kallon ikon ubangiji daga shi har Yaseer,yadda Umma'n tasa ta koma masa kamar wata wacce ta samu shafar jinnu
"Yazeed yanzun kaine ka koma haka..?? Allah na gode maka daka fito min da d'ana abun alfahari na,Allah na gode bisa ni'imar da kayi a gareni na dawomin da yarona,Allah ina rik'onka daka gaggauta bayyana duk wani maisa hannu a cikin al'amarin nan...Allah ka tona musu asiri mu gansu mu kuma gane su dan alfarmarka..."
"Nooo!!! Ummah banda cikin gaggawa..dan kuwa hadisi ya tabbata daga annabi (S.A.W) yana cewa: "Atta'anniiy minallah..wal'ajlatu minash-shaid'an.." Ma'ana jinkiri daga Allah yake..gaggawa kuma daga shaid'an take..saboda haka idan zaku rok'i ubangiji kada ku rok'i a gaggauta muku,la'allah abunda zaku rok'a ya kasance ba alkhairi bane a tare daku,amma idan aka jinkirta muku koda babu alkhairi a cikin abunda kuka rok'a sai Allah ya musanya muku shi da wanda yafi shi zama alkhairi a tare daku.."
Fuskarsa ta shafa tana rausayar da kai sannan ta furta
"Hakane yazeed amma ni a gare ni bani da burin daya wuce naga asirin duk wani mai hannu ya tonu,sam mutane zuk'atansu babu Allah,shin mene ne ka tsare musu da haka zai faru da kai tun kana yaronka...?"
Murmushin dai ya sake yi mata sannan ya juya ya kalli Yaseer daya zuba musu ido yana ta sakin murmushi abunsa,yana goge hawayen dake saman fuskarsa
"Koma mene ne Umma,kuma ko su waye suka yi wannan aikin ni bani da abunda zance dasu daya wuce nace *na barsu da Allah...* dan nasan shi zai karb'amin hakkina a hannun duk wanda ya zalunce ni,saboda haka kema ki daina sa wannan maganar a ranki coz ina tsoron wani abu ya sameki.."
Jirkita kai tayi gefe tana kallonsa cike da tausayi,Yaseer ne ya kallesu duka cikin wani yanayi ya furta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 63