Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da amsar da wannan Yarinya ta bayar kuma zaku hukunta d'anku bisa laifinsa kamar yadda doka ta tanada tunda kun samu tabbacin shi ne mai laifin.." Afirgice yarima ya juya ya kalli yarinyar zuciyarsa na k'una ya furta "Kiji tsoron Allah ki fad'a musu gaskiya,kada ki bari son zuciyarki yasa ki kallafamin laifin da ban san anyi ba,ina da tabbacin bani bane wanda kika fad'a sai dai ko had'in baki ne akan a jefani cikin musiba,ki tuna da lahira da kuma tsayuwa gaban mahalicci,duk abunda zaki aikata ki tuna ubangiji yana ji kuma yana kallo,shin mene ne ribarki cikin fad'in abunda babu shi..? Idan saki akayi kiyimin haka ina rok'onki da girman Allah ki gaggauta fad'a yanzun a gaban kowa.." Tsawa maimartaba yayiwa yarima data sashi yin shiru yana sauke kai k'asa alamun girmamawa ga umarnin mahaifinsa idanunsa na fara tsatstsafo da ruwan hawaye "Matawalle fada na sauraren hukuncin ku.." Da kyar matawalle ya iya d'agowa kana ya fara da fad'in "Ina neman afuwa a gurin maimartaba hakama a gurin fada da wakilanta,bisa neman izini nason a bamu lokaci muyi bincike dan gano gaskiyar yadda wannan AL'AMARIN ya faru.." Kafin yakai k'arshe ai har maimartaba ya tari numfashinsa "Ba buk'atar haka matawalle tunda kun tabbatar daga bakin ita Yarinyar cewar shi en ne,saboda haka hukuncinku kawai muke jira.." Babu yadda matawalle ya iya dan haka ko da yaji maimartaba ya fad'i haka sai kawai ya juya ya kalli al'ummar fada zuciyarsa cike da taraddadin hukuncin da za'a zartarwa da yarima sannan ya fara da fad'in "Bisa ga umarni da hukuncin da doka ta tana da na masu irin wannan laifin,a duk lokacin ta faru idan kuma har an tabbatar da afkuwar laifin,tofa kotu zata d'aure mai laifin tsawon shekaru ashirin da biyar a gidan yari kamar yadda doka ta tanada,haka kuma idan kamar yadda shekarunta balaga suke fadawa daga sha takwas kuma daga nan ne mutum yake fara hukunci dai² da duk wani mai hankali,a bisa rashin kaiwa da shekarun wanda aka gurfanar a gaban wannan kotu mai albarka ya zama sun gaza kaiwa shekarun balaga yasa wannan kotu zata ajiye shi a gidan horarawa na kangararrun yara daga nan zuwa sanda shekarunsa suka isa kaiwa na mutumin da hukunci ya hau kansa sai a mai da shi kunkurun horar da masu manya..." Yana niyyan ci gaba da magana maimartaba ya dakatar da shi da cewa "Ya isa haka matawalle aika riga ka fad'i hukuncin,saboda haka muna fata al'umma sun shaida da wannan hukunci,sannan kuma jan kunne d'aya da zanyi zuwa ga al'ummarmu shi ne,muna fata wannan zai zame musu izini,musamman ga y'an baya ko masu niyyan aikata iri²n wad'annan laifuka." Juyawa maimartaba yayi ya kalli jami'an dake kusa ya furta "Zaku iya tafiya da shi zuwa gidan horo...Haka kuma bana fata wani cikin ahalinmu yayi yunk'urin hanawa a hukunta shi kamar yadda za'a hukuntar da sauran al'ummah daga nan har zuwa lokacin da wa'adinsa zai cika,muna fatan al'umma zasu karb'i hakan amatsayin shaida na duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifin ko makamancinsa zai fuskanci hukunci dai² da abunda ya aikata..." Yana zuwa nan a maganarsa ya juya ya kalli yarima da kansa ke k'asa yana zubar da hawayen bak'in ciki da fad'in "Kai kuma muna fatan wannan zai zame maka darasi a nan gaba da fatan zaman da za kayi a can zai baka damar gyara kuskuranka..!" Yana gama magana yayi izinin a tafi da shi,jami'an da aka kira daga hukumar ta gidan kason yaran da tuni suka halarci gurin tuni suka sashi a gaba tare da nufan hanyar ficewa daga fada,ko da yarima yaga ana niyyan ficewa tuni ya juyo ya kalli mahaifinsa da sam yak'i d'aga kai ya kalleshi yana fad'in "Ku bawa Abiiy hak'uri dan Allah,wollahi babu ni a cikin wanda suka aikata,ban san lokacin da akayi ba..K'arya take min,kada ku bari azalunce ni kan laifin da ban aikata ba...!" Amma ina babu wanda ya saurare shi bare ya tausayawa halin da yake ciki,jama'a kuwa koda suka ga an fice da shi daga cikin fadar tuni hankulan wasu ya kasa kwanciya bisa ga alamun da suka gani a tattare da shi hakan ya sake tabbatarwa da wasu masu zaton abunda aka fad'a zai iya faruwa akan ba shi da laifi,haka kuma maimartaba yak'i bari ko sauraren y'an fada kan shawaran ayi bincike a gano gaskiya,a nasa fad'in hakan shi ne adalci a hukunta duk mai laifi da zaran an tabbatar da laifukansu. Yadda ya had'a zufa kai kace ruwa aka kwara masa,banda juya kai da surutai gami da rok'o babu abunda yake yi,bai wani jima ba ya farka a firgice cikin k'araji yana sake maimaita sunan Abiiy,idanunsa ya runtse bayan ya gama photo'n gurin da yake ya bayyana a cikin idanunsa da kuma kasancewarsa ba a inda yake tsammanin ba,a hanakali ya jingina bayansa da katangar d'akin yana sakin kuka mai tsuma zuciya kamar yadda hakan ya zame masa sabonsa,tamkar wanda ake shirin cirewa rai yake ta faman gunjin kuka,a hankali aka turo k'ofar aka shigo ba tare daya d'aga kai ya kalli mai shigowar ba,haka kuma baiyi tunanin daina kukan da yake yi ba,cikin nutsuwa wanda ya shigo en da bazai haura tsaransa ba a shekaru ba ya tako har zuwa kusa da shi ya zauna yana dafa kafad'arsa shima had'e da fashewa da kuka,saurin d'agowa yayi ya kalle shi cikin wani irin yanayi na rashin gane shin farin ciki yake ciki da ganin makusancin nasa ko kuwa ya rungume shi yana kuka bakinsa na maimaita "Ban sansu ba..! Ban aikata ba...! Ina Ummata itama tasan bazan aikata ba..! Me yasa Abiiy yak'i yarda dani...?" Bayansa yake shafawa yana nodding kansa tamkar k'adangare,cikin muryar rarrashi ya furta "I knew friend baka da laifi cikin wannan case en,sharri ne da k'age aka maka..." Saurin d'ago kansa yayi daga jikinsa,fuskarsa d'auke da hawaye yana murmushi mai cin rai "Kaima kasan ban aikata ba ko YASEER..? Me yasa to Abiiy ya yarda..? Me yasa bayan yasan bazan iya yin hakanba ya bari suka taho dani...me yasa baka fad'awa Abiiy babu ni cikin masu laifin ba tunda kaima baka yarda ba...? Ban sansu ba..wollahi ban san daga ina suke ba..Me yasa za'amin haka? me nayi musu...?" Wani kukan ya sake saki yana kwanciya had'e da sake takure jikinsa guri d'aya ya cure,sake rik'oshi yayi cikin muryar rarrashi ya dafa shi yana shirin yin magana "Kayi hak'uri ka bar komai a hannun Allah in sha Allah koma waye yake da sa hannu a ciki Allah zai tona musa asiri..." Kukansa yake ba tare d'aya iya sake d'agowa ba,shi kuwa YASEER ganin ya juya masa baya bai kuma magana ba yasan kuma ba sakewar zaiba yasa shi mik'ewa da sauri ya juya zai fice,rik'o shi da yaji anyi yasa shi juyowa yana kallonsa idanunsa taf da sabbin hawaye da a kowane lokaci zasu iya ci gaba da zuba "Ka gaidamin Ummata hakama Aunty...!" Abunda ya furta kenan ya sake shi ya juya ya sake kwanciya yana juya masa baya had'e da ci gaba da kukansa,ganin yanayin da yake ciki yasa shi fad'in *"YAZEED..!* Ka kwantar da hankali in sha Allah za munyi k'ok'arin ganin ka fita a wannan matsalar.." "Ka tafi kawai ka kuma isarmin da sak'ona ga mahaifiyata,amma nasan wannan ba abune mai yiwuwa ba tunda Abiiy ya bada dama aka kawoni nan,kawai dai ina fatan zaku ci gaba damin addu'ah.." Tunda yaji abunda ya fad'a kawai sai yayi saurin juyawa ya fice yana share hawaye,dan yasan halin YAZEED en kullum maganar da yake yawan maimaitawa kenan a lokuta da dama........... *COMMENTS ENKU ZAISA NI CI GABA DA POSTING AKAN LOKACI DA YARDAR ALLAH..* *IDAN HAR KUNJI TSARIN LABARIN YAYI MUKU MAZA KU SANK'AMA YIN COMMENT DA CEWAR YAYI MUKU KUMA KUNA SO...* #Vote,#comment,then #share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *Pg 2.* ^^^^^^^^ Duk da kasancewar a k'allah yanzun YAZEED ya d'auki hanyar watanni shida (6) a wannan gidan,amma kullum aikin abu guda yake,sam ya kasa sakin jiki da kowa a gidan haka ya kasa sabawa da zamansa a wannan guri daya kasance masa tamkar gida a halin yanzun,babu da wanda yake zama bare ya samu abokin hira ko wanda zai d'ebe masa kewar y'an uwa da gida,a duk lokacin da zaiyi arba da wani daga cikin ahalinsa kuwa tofa aikinsa d'aya ne a wannan lokaci shine jifansu da tambayoyi iri² da mafiya yawa daga cikin masu zuwan basu da amsoshinsu,wannan dalilin yasa tun wasu na sha'awar zuwa har suka cirewa rayukansu.... ^^^^^ Ko da YASEER ya fito daga gurin YAZEED hankalinsa sam yak'i kwanciya musamman yadda yaga abokin nasa kuma d'an uwansa na jini ya koma tamkar ba shiba,duk ya lalace yayi duhu kan tsananin damuwa daya tarawa kansa,irin kukan da yake a duk lokacin da zaizo gurinsa idan ya sake dawowa shi zai sake tarar wa yana yi a wani karon,tun yana iya rarrashinsa har ta kai shi ga shima ya koma taya shi idan ya samu faraga,dan haka yanzun ya zama a duk lokacin da zai kai masa ziyara shi kansa hankalinsa baya kwanciya har ya dawo gida,haka duk sanda yaje ya dawo tofa yini yake cikin damuwa,haka zai samu guri guda ya zauna yayi shiru shi kad'ai ko ya kulle kansa a d'aki yayita kuka saboda tsananin tausayin da yake yiwa d'an uwan nasa,ko yayi ta tunanin hanyar da zai bi yaga ya samo ma YAZEED en mafita nasan komai ba sai dan Sabin cewar shi an ba mai neman rigima bane bare ace ya aikata gagarumin laifi a hakanma kuma irin wannan da duk wani mai hankali da sani dokar Allah yake kyamar ya aikata. ^^^^^ Fuskarta bak'i k'irin take,wanda saboda tsabar bak'inta har wani maik'o take musamman idan rana ta haskata,tana da pointed noise,hakanan manyan eye ball enta da suka kasance masu haske da girma sune kad'ai mutum zai kalla a tsarin halittar fuskarta yasan tana da kyau duk da kasancewarta k'aramar yarinya da bazata wuce shekaru sha biyu zuwa sha uku ba a duniya ba,haka zalika a duk lokacin da zata yi magana jerarrun fararen hak'waranta idan suka bayyana wanda suke dad'a k'awata y'ar madaidaiciyar fuskarta sai duk su b'oye duhunta da muninta da wasu ke gani a sakamakom zamowarta bak'a a cewar wasu kenan,haka nan itan ma'abociyar tsayi ce duk da k'arancin shekarunta hakan a bayyane yake ga duk wanda zai kalleta,sai dai yanayin tsayin gab'b'anta zai iya sawa kayi tunanin shekarunta sun haura haka. A hankali y'ar dattijuwar ta kalleta da murmushi shimfid'e a fuskarta tana fad'in "Yawwa autar Inno maza idan kin gama kwalliyar kizo maza na aikeki *BABBAN GIDA* gurin fulani,kinga wancan gidauniyar ko da bana kusa idan kin gama kiyi maza ki d'auka,bana son ki zarce ko ina sai gurin *Fulani* sannan bance idan kin fita ki tsaya mad'e ba dan nasan halinku idan kuka ga ana wani abun sai kun tsaya kallo,kinga dai yadda al'muru ya fara kawo jiki saboda haka kiyi hanzarin dawowa kinji ko uwar masu gida.." A hankali ta d'ago kanta daga kallon da takewa d'an abun hannun ta da take wasa dashi ta saki murmushi mai birgewa,cike da ladabi ta amsa da to kana ta mik'e ta zari hijab enta ta zura,ni ko nan na tsaya ganin ikon Allah dan kayan da naga ta laftawa jikinta ba k'aramin mamaki suka bani ba danko harda su safa naga ta kirb'awa jikinta,ita ko damunta ma basa yi duk da yadda ake tsananin zafi,kwanon da Inno ta mata nuni da shi ta d'auka ta fice tana mata sallama da fad'in "sai ta dawo." Fitowarta a gidan babu jimawa tana cikin tafiya ta jiyo ana k'walla mata kira,a hankali ta juya duk da ta d'auki muryar me kiran nata,k'awarta Aina'u ta hango tafe sai faman zuba sauri take har ta iso kusa da ita suka jera dai² lokacin data kalleta tana cewa "Haba *JEEDDAH* ke kuwa wannan saurin na mene ne haka har na yage baki ina ta kiranki amma baki ko saurare niba sai da kika ga dama kika tsaya.." Murmushi kawai tayi ba tare data amsa mata ba,suka ci gaba da tafiya,hakan da tayi sai ran Aina'u ya kuma b'aci cikin masifa ta furta "Ke wollahi dad'ina dake kenan wani lokacin kin cika abun haushi,sai ayi miki magana ke kuma ki wani yiwa mutum dariya a maimakon ki bashi amsa" "Allah ya huci zuciyar k'awata,wollahi kinga mantawa nayi banyi addu'ar maraice ba tun a gida sai dana fito na tuna to shi ne lokacin da kika min magana na kasa baki amsa saboda ina kan yima a lokacin.." "Ayyoo! to koda naji,ai na zaci ko y'an wulak'ancin ne suka motsa yau,nace su rasa akan wanda zasu tashi sai ni kuma..?" "Haba dai Aina'u yanzun kema kin shiga sahun su Asabe kenan da suke cewa ina da girman kai,shi kenan na gode tunda kuka d'auke ni,amma dai koma me kuka d'auka ni baya bani haushi sai dai nakan ji damuwa a duk lokacin da aka alak'anta ni da kalmar girman kai,nasani dole akwai lokacin da gaskiya zata bayyana,kuma naga mene ma abun damuwa ne acikin wannan tunda duk matsayinmu d'aya ne walau a gidan nan ko a gurin ubangiji,sai dai kawai wanda yafimu kusanci da ubangiji shine wanda yafimu jin tsoronsa,haka zalika cikin gidan nan naga dukanmu jirgi d'aya ya kwaso mu,kasancewar kullum abu d'aya muke,kuma shi en shi ne tushenmuma da asalinmu wato *BAUTA.."* 'Dan jimm Aina'u tayi kafin ta girgiza kai tana cewa "Haka ne kam jeeddah kin fimu gaskiya,dad'ina dake kenan kina fad'in gaskiya haka bakya tab'a bawa mutum laifi koda yayi miki laifi,hasalima sai dai ki bawa mutum amsa cikin hikima da ilimi ta yadda zaki sashiya fahimci kuskuren da yayi,gaskiya ina jin dad'in zama dake saboda ina k'aruwa sosai ta dalilinki,fatan Allah yasa mu dace,amma kiyi hak'uri in sha Allah suma su Asaben zan musu magana su daina fad'in haka..." "Kai haba kema dai mene abun bada hak'uri daga y'ar wannan maganar,ai komai ya wuce nasan suma en kawai suna fad'a ne a dalilin rashin sanin ainahin halayena da rashin zama guri d'aya,shi yasa sauke cewa haka,amma nasan wata rana zasu daina suma." Duk da kasancewar su masu k'ananun shekaru sam kalamansu da maganganunsu sai susa mutum yayi tsammanin wasu manyan mata ne keyinsu,dan ko ni kaina sai da suka bani mamaki,sai dai kuma ko da nayi duba sa cewar zamanin da dana yanzun akwai bambanci shi yasa sai na share duk wata tantama dake bijiromin akan mamakin maganganunsu. Tafiya suka jera suka ci gaba da yi suna tafe suna hira abunsu,har suka yanko hanyar da zata sada su da cikin gida,dai² zasu shiga babbar k'ofar da akewa lak'abi da *K'ofar fada* wacce ke sashin K'ofar shigowa gidan sarautar ta kudancin gidan wato *K'OFAR KUDU* suka ja tunga tare da saurin komawa gefe suka rakub'e suna saurin zubewa a k'asa,kawunansu duk'e suka fara mik'a gaisuwa had'e da fara koro kirari ga maimartaba "Takawarka lafiya babban bijimi,lafiya farar giwa mai farar aniya,lafiya toron giwa,lafiya Mai da Garin Wani Kango,lafiya Barden Mahadi,lafiya Sarkin Yak'in Sarkin Musulmi,lafiya Sukukun Bakaka,lafiya Darzaza Amalen Sarakuna,lafiya Ba Hau da Wani Ba Sauken Wani,lafiya Hana Kangara,lafiya Bango Madafar Bayi,lafiya Sakaka Babba Bak'o,lafiya Hadarin k'asa Maganin Mai Kabido,lafiya Jinjirin Wata Sha Kallo,lafiya Kwankwason Jimina Mai Wuyar Shafawa,lafiya Gark'ami Wandon Ƙk'arfe,lafiya Jijjigen Addini,lafiya Toya Matsafa,lafiya Waliyyin Allah,lafiya Baya Goya Marayu,lafiya Toron Giwa,lafiya Tufaniyar Gabas,lafiya Jinjirin Wata Sha Kallo..." "An gaisheku yara manyan gobe,gaishe ku y'ay'an bayi,ku bayi iyayenku bayi,sarki ya amsa muku..!" Suna nan zube a kasa duk'e da kawuna,har sarki ya wuce zuwa cikin gida da niyyarsa ta tafiya zuwa masallaci,dan ga al'adar maimartaba yakan fito daga gida ne a duk lokacin da sallah ta gabato yafi sha'awar ya tafi da wuri ya zauna cikin masallaci yana zikiri,bashi zai koma gida ba kuma har sai bayan sallar isha'a,daga nan kuma sai Allah ya kaimu asubah,ko kad'an basu yi yunk'urin barin gurin ba har sai da suka tabbatar sarki ya wuce yayi nisa da su sannan suka mik'e cikin azama,jeeddah ce a gaba sai k'awarta aina'u dake biye da ita a haka suka shiga ratsa many an sorayen gidan suna wucewa har ta kaisu ga sun k'araso zuwa cikin harabar babban gidan sarautar,sai a nan ne hanyarsu ta rabu inda suka yiwa juna sallama kasancewar ita aina'u can k'ofar *K'WARU* ta nufa ma'ana can gaba kenan daf da k'ofar fita a gidan ta can baya,kasancewar gidan da aka aiketa yana ta can hanyar,itama Jeeddah ta mik'i hanyar da zata sadata da ainihin gefen fulanin da aka aikota gurinta. Dai² tana niyyan shiga gefen suka kusan yin karo da mutum a dai² k'ofar shiga gefen Fulanin,da saurinta ta koma baya tana durk'ushewa cikin rawar murya data jiki take fad'in "Tuba nake ranka shi dad'e wollahi ban san kana tafe ba,ayimin afuwa,kaina bisa wuya na..." K'arasa fitowa yayi cikin takun k'asaita,a hankali ya kalleta cikin yanayin rashin jin dad'i ya furta "Bance kada na sake ganin kin yimin wannan durk'uson ba..?" "Tuba nake ranka shi dad'e,ayimin afuwa wollahi zan kiyaye nan gaba.." Tsaki yaja mai sauti sannan yayi gaba abunsa ya barta nan da kanta a duk'e bisa k'asa.. Lokacin data d'ago kanta duka tuni har ya b'ace a gurin saboda jin haushi,ajiyar zuciya ta sauke kana ta mik'e tana rangad'a sallama tun daga inda take. Daga ciki aka amsa mata aka bata izinin ta shiga,kanta a k'asa ta shiga tana sake yin sallama "Maraba da uwar fada...." Fulani dake zaune ana matsa mata k'afa ta fad'a tana d'an murmushi da mik'awa jeeddah hannu alamun taje gurinta,a hankali kamar mai tsoron wani abu,ko tunanin wani abu zai kamata ta matsa kusa da ita,janta tayi zuwa gefen jikinta ta d'ora hannunta akanta,kana ta kalleta da fad'in "Allah ya miki albarka...Inno ce ta aikoki ba..? Ai dama ana ganinki ba sai an tambaya,ita kam kullum bata gajiya da hidima..Yanzun duk wannan yammar data gani bai hanata aiko ki ba ko..?" Ita dai Jeeddah bata iya magana ba,sai gaisheta data shiga yi cikin girmamawa da ladabi,cikin nishad'i fulanin ta amsa mata da tambayarta yaya Inno en take,bata iya amsawa ba,sai aiken Inno data gabatar mata,bayan nan kuma a hankali sai ta fara jan jikinta tana shirin matsawa a jikin Fulani dan Inno tace mata kada ta jima tunda yamma tayi sosai,murmushi Fulani tayi kana ta shiga kallonta cike da sha'awa ta furta "To autar Inno nasan dai dama guduwa za kiyi,baza ki tayani hira ba ko..?" Murmushi Jeeddah tayi tana sunkuyar da kai,cikin ladabi tace "Ranking ya dad'e Inno tace kada na bari Maghreba tayi min a wane ne,shi yasa zan tafi yanzun,amma idan da wani abu da za'ayi miki kafin na tafi sai na jira.." Murmushi Fulani tayi kana cikin maganar ta a nutse da hikima ta fara magana "A'a bana jin akwai wani abu daya rage ba'ayi ba,zaki iya tafiya dan nima kaima ban fita son Inno tana aikoki da irin wannan lokacin ba..Na sha fad'a mata idan taga yamma yayi kamar haka ta hak'ura da aiken sai gobe amma tak'i dole dai a lokacin da tayi niyya a lokacin zata aikoki.." Koda Fulani ta gama maganar nan ta sallama jeeddah,ita kuma tayi mata sallama kana ta juya tana shirin tafiya,barta isa bakin k'ofa tana shirin fita tana da d'an sauri duk dan kada ta b'ata lokaci gurin komawa gida,fulani ta dakatar da ita tana fad'in "Zo nan uwata ki kaiwa Fulani babba wannan,nasan zata so hakan itama.." Cikin sanyinta ta juyo ta dawo tana shirin amsar sak'on da sauraren abunda Fulani ke fad'a YASEER ya shigo cikin parlour'n ba tare da yayi sallama ba,saurin kallonsa Fulani tayi bata kai k'arshen aiken da take yiwa jeeddah ba ta fara masa fad'an k'in yin sallama da yayi,d'agowa yayi ya kalleta fuskarsa da damuwa yana d'an rausayar da kai "Afuwaan Ummi.." Yana fad'an haka yayi musu sallama,sannan ya nufi hanyan d'akinsa cikin sanyin jiki dana gab'b'ai,yana yin yadda yake tafiya yasa Ummi fahimtar yana cikin damuwa,da sauri ta dakatar da shi da cewa "Yaseer dawo nan ka zauna.." Babu musu ya dawo ya nemi guri ya zauna yana sauke kansa k'asa,sai data d'an nazarci yanayinsa kafin ta furta "Me yake damunka ne kake cikin irin wannan yanayin...? Wani abu na damunka ba,da bazaka iya fad'a ba ko.?" Da kyar ya iya girgiza mata kai,d'agowa yayi da niyyan yi mata bayani amma ina tuni hawaye ya fara sauka daga idanunsa,wani irin kallo ta shiga binsa da shi,cikin hikima tace "Yauma kaje gurin YAZEED ba..?" Kai ya kad'a mata yana share fuskarsa "Me yasa YASEER ..? Bayan kasan irin halin damuwar da kuke shiga daga kai har shi zaka je duk da haka..? Me yasa kake son ko wane lokacin kuyita shiga irin wannan yanayin..? Shin har tsawon wane lokaci ne zaku d'auka kuna abu d'aya...?" Kansa ya d'ago ya kalleta fuskarsa cike da damuwa ya fara magana "Ummi ban San me yasa ba,na kasa daina zuwa gurinsa bazan iya ba,nariga dana saba dashi duk da irin halin da nake shiga a duk lokacin da zamu had'u,bazan tab'a iya jera sati ba tare dana ganshi ba,amma Ummi kin San wani abu kuwa...?" Kai ta girgiza masa alamun bata sani ba "Wollahi Ummi ina tunani akan case en nan nasu YAZEED,ina da tabbaci Ummi Sam YAZEED bai aikata abunda aka lak'aba masa ba,kuma nasan koke Ummi idan kika ganshi yanzun zaki tabbatar da babu sa hannunsa a ciki,musamman yadda yake cikin damuwa,har kawo wannan lokacinfa ya kasa mantawa da duk wani abu daya faru,kuma yak'i sabawa da mutanen gidan,shin Ummi kema kina ganin YAZEED zai iya aikata wannan laifin..?" Ko kafin ta bashi amsa tuni ya furta "Ni dai ina da yak'ini akan d'an uwana bazai tab'a aikata haka ba,nasan halinsa nasan waye shi,haka nasan abunda zai iya aikatawa da wanda bazai iyaba,amma na tabbatar wannan *K'AZAFI NE* kawai aka masa.." A hankali ta kalleshi kafin tace "Amma YASEER shin kai akwai wani da kake zargin ko dasa hanunsa a cikin case en..? Ni kaina tun daga lokacin da labarin ya zomin nayi tunanin wannan case en wani ne daban a waje yake shirya shi.." "K'warai kuwa Ummi haka nake tunani nima,amma koma mene ne,kuma ko waye zamu yi bincike sai mun nemo su duk indai suka shiga da izinin Allah,da sannu zasu biya duka zunubansu.." Yadda yayi furucin yasa ta kallonsa,tana shirin ci gaba da magana ya

Chapter 2 of 63