yayi dan yadda yaga tana magana kai sai kayi zaton jikar bill gate ce dan yadda take nuna masa kud'i ba matsalar su bane,shima d'in nuna mata yayi babu matsala idan har suna a shirye ne to babu damuwa yanzunma za'a iya shiga dasu theatre,sake nunawa tayi babu komai ayi d'in kawai koma nawa ne zata biya,VIP ya turasu coz asibiti ba nasa bane kawai taimakawa ne nasa dan haka take duka suka yi na'am sannan suka fita dan aiwatar da abunda yace,ak'alla adadin kud'in da ko wannensu zai musu paying akan plastic surgery d'in face n neck lift da za ayima kowacce a cikinsu idan a dollar ne ya kai $3550 wanda a kud'i idan zamu yi converting d'insa da Naira wanda duk $1 yake representing #362.50,idan da kuma zamu lissafa $3550 d'in kud'in aikin nasu a kud'in mu na nan ya kai ak'alla #1.3m,,ko daga yanayin shigarsu ma kad'ai ya isa ya nunwa mutum lallai duka babu wanda ba zai iya biyan kud'in aikin ba,,itama Hajiyar sanda suka isa VIP take ta cake musu kud'in aikin sannan ta koma office d'in da shaidanta,haka nan itama d'ayan patient d'in nasa da abun nata ita ya tab'a mata wuya kad'ai wanda ya kawo ta hospital d'in ya biya wad'annan mak'udan kud'in,in less than one hour tuni har an kammala shirya komai da ake buk'ata shi kad'ansa kawai ake jira,,,office kuwa suna zaune time d'in Jeeddah dake zaune tayi zugum tunanin abun duniya duk ya cikata ya d'an kalla yana sakin d'an murmushi kafin ya fara magana
"KHUSHI.. Let's go..!"
Idanunta ta d'ago masu cike da alhini gami da fargaba sannan ta ce
"Where...!?"
Hannunta ya kamo ya mik'ar da ita tsaye had'e da cewa
"Muje mana..ko yanzun bazaki raka ni ba..??"
Narai² tayi da ido kamar zata fasa masa kuka
"Ni dai gaskiya A'a kaje ka dawo..!"
"Ohh! Baby yanzun baza mu tafi tare ba..?? Nima gaskiya A'a idan baza kije ba to a fasa aikin."
Girgiza masa kai take tana kallon fuskarsa
"A'a'a..! Yallab'aina baza ayi haka ba,kaga fa ni bana son ganin irin wannan abun ne shi yasa,amma kai kaga aikin kane,,kaje zanyi jiraka har ka fito kaji.."
Shima b'ata fuskan yayi yana mak'ale mata kafad'a
"Ni dai idan baza kiba to sai dai a nemo wani Dr yayi aikin.."
Saurin rufe masa baki tayi da hannunta tana sake kad'a masa kai
"Haba mana YAYANAH abunda ya kawomufa dama kenan,me yasa zaka ce haka,,kai dai kawai kaje ka fito zan tayi maka addu'ah da fatan dacewa,,in sha Allah babu abunda zai faru..ina nan ina jiranka.."
Kamar bazai tafi ba haka tayi ta lallab'a shi sai kace yaron goye,da kyar da yaya sannan ta samu ya barta a nan d'in duk dama zolayarta kawai yake akan saiya tafi da itan,ko kafin ya fita sai daya mata maganar idan an kawo sak'on daya bada kada ta jira shi dan yana tunanin zai jima kafin ya fito,amsawa tayi sannan ta bishi da addu'ar fatan samun nasara shi kuma ya fice yana amsa mata,,duk wani shirin da za'ayi tuni an rigada anyi dan haka yana shiga taimakon gaggawa ya fara bawa wacce fuskarta take a lalace coz akanta sai ya b'ata awanni,saboda yadda fuskar duk ta tattare nd wajen idanunta idan ba'ayi da gaske ba tofa zata iya rasa su,after 2 hours da y'an mintuna daya b'ata akanta ya gama komai,sannan aka fita da ita zuwa ward,tunda aka fito da ita akan idanun mahaifiyarta,yadda taga fuskarta duk a nad'e sai da ta zubdama y'ar tata hawaye, lokacin da aka fita da ita nan ya koma kan d'ayar dake zaune sai kuka take har lokacin,,ita kam bai wani sha wahala ba akanta,dan kai tsaye yayi abunda ya kamata sannan ya fita bayan nan itama aka fito da ita da d'aurarren wuya,,ko kafin ya wuce sai daya ga wannan Hajiyar data kawo y'artan,bayan sun d'anyi maganganun akan ciwon y'ar tata wanda ya matuk'ar d'aga mata hankali,a nan yake shaida mata yanayin yadda aikin y'ar tata ya kasance buh dole ana buk'atar photon ta na kafin abun ya faru,,amsa masa tayi sannan tace zata turo masa yanzun,ko da suka gama maganar office ya wuce a matuk'ar gajiye dan awanni uku da mintinoni ba baya bane,saman armchair ya hangota ta mik'e tana ta latsa wayarta wanda jin sallamar sane ma ya sata d'agowa tana amsawa,direct inda take ya nufa da zuwansa ya zauna a kusa da ita,a hankali itama sai ta fara k'ok'arin tashi ta zauna amma sai yayi saurin mayar da ita,kallonsa tayi ta masa murmushi ba tare data sake yunk'urin tashinba ta masa sannu da aiki,amsata yayi yana dafe forehead d'insa da hannu,after like 2 minutes ya sake kallonta yana d'aga riganta zuwa sama,da mamaki ta kalle shi kafin ta jefo masa tambayan lafiya..? Fuskarsa yayi squeeze yana k'are mata kallo,cikin muryan dake nuna babu wasa yace
"Anya kin ci abinci kuwa..??"
D'auke kanta tayi kamar bata ji me yake tambayar taba,tana k'ok'arin barin gurin shima yayi saurin fizgota ta fad'a jikinsa,fuskarsa babu alamun wasa hakama muryansa dan yadda yake magana kamar yana cikin fushi
"Ina tambayar ki kina k'ok'arin tashi ki barni,,saboda ga sa'anki ko..?? shi yasa ina magana kika kasa bani amsa.??"
"Kayi hak'uri to...ai naga bana jin yunwa ne shi yasa.."
Ido ya d'an bud'e yana kallonta irin "what.?" D'innan kafin yayi magana
"K'ina nufin dagaske har yanzun babu komai a cikinki..?? Kina zaman mene har yanzun baki sawa cikinki komai ba..??"
"Nifa ba yunwa nake ji bane shi yasa.."
Rufe mata baki yayi da nasa dan baya son ta dunga maimaita masa zancen,sai daya tabbatar ya tsotse lips d'inta dake kyallin lip gloss kafin ya saketa yana fad'in
"Oyaa! To yanzun zan baki,nasan zaki ci ba..??"
Kai ta girgiza masa a sab'ule sannan suka yima juna murmushi,after kuma ya zaunar da ita a kusa da shi jikinsu na hogan juna,lesser d'in dake ajiye ya janyo musu mai d'auke da wasu irin packages ya shiga bud'e su,tun bai kammala ba k'aran shigowar sak'o ya sashi kallon inda ya zube wayoyinsa,duk da ba niyyansa ya d'auka ba amma sai itan ta mik'o masa da kanta coz ta fishi kusa da inda wayoyin suke,murmushi yayi mata sannan yasa hannu ya amsa,yana gama karb'a kuwa bai duba ba ya sake ajiyeta,kallonsa tayi kamar za tayi magana sai kuma ta fasa,yana kula da ita shima yaga alamun son tayi magana amma ko da yaga bata ce komai ba sai shima d'in yayi shiru ya bagarar da maganar,har suka kammala ciyar da juna babu mai magana a cikinsu sai dai musayan murmushi da suke yi a duk lokacinbda suka had'a ido,,lokacin bayan sun kammala kimtsawa kuwa da niyyan barin hospital d'in nan ya d'auki wayoyin,har sun kusa da fita a office d'in sai ya tuna da sak'on da aka turo masa,wayan da sak'on ke kai ya fara clicking,ko daya shiga akwatin sak'onsa ta duniyar whatsapp nan take sai idanunsa suka fad'a kan fuskar da a tarihi baya jin zai iya mantawa da ita ba a iya tsayin rayuwarsa,,shiru yayi yana nazarin anya itace ko kuwa kama ce,amma sai idanunsa suka shiga tabbatar masa da amsa d'aya idanunsa ke bashi,haka yayi ta maimaita kallon hoton zuciyarsa d'auke da wani irin yanayi dan a lokacin kowa bace yake kallon a jikin picture da aka masa send ba face *ZAHRA MALEEK* tsohuwar budurwarsa daya so aura sai k'addara ta fad'a cikin maganar neman auren nasa,itanma kuma da yake bata tsaya ta saurare shiba a lokacin sai ta yanke hukunci cikin fushi coz a tunanin ta yaudararta kawai zaiyi,ya shafe ak'alla sama da mintuna biyar idanunsa akan phone d'in kafin ya sauke tagwayen numfashi,kallonsa tayi tana nazarin yanayinsa kafin ta d'an lek'a hannunsa dan taga mene ne yake kallo haka daya sa mood d'insa canjawa,fuskar budurwar da tayi arba da shi yasa taji lokaci guda wani irin abu ya fara taso mata kafin wasu mintuna su gifta tuni taji har ta fara kasa ko had'iye yahun bakinta,cikin saib'i da rashin kuzari ta wuce ta fara tafiya dan yadda take jin bazata iya ci gaba da tsaiwa tana kallon yanayinsa ba,tunda ta fara tafiya yake kallonta dan haka shima cikin rashin wadataccen walwala ya biyota da saurin,sai a lokacin da suka isa bakin mota aka biyo su da AHYAN dake hannun ma'aikatan dake kula da hospital d'in,shi ya karb'e shi sannan ya zagaya gurin zamansa bayan ya bud'e suka shiga a tare,bai mik'a mata shiba dan ya kula da yanayimta sai kawai ya rik'e shi a jikinsa while kuma yana tuk'in a haka har suka kai gida,still lokacin da suka shiga gidanma bata iya kula shiba tayi wuvewarta apartment d'insu har lokacin tana jin zuciyarta babu dad'i,shi kam ko da suka dawo d'in sai daya biya ta apartment d'in Ummi ya ajiye musu AHYAN sannan ya bi bayanta,lokacin ko daya shiga apartment d'in sai bai tarar da ita a parlor ba,hakan yasa kai tsaye ya nufi master bedroom d'insa,abunda ya gani sosai ya bashi mamaki dan haka Baima kaiga shiga ba dan bata ciki ya juya,a nata bedroom d'in ya isketa tayi kwance saman resting chair,,mamaki yayi kan abunda tayi shi sai yafi kwana nawa bai ganta a nan ba ammayau da yake tana neman rigima shi ne tayi hakan,duk abunda take ko da zai fita sau nawa a rana idan ya dawo a nasa bedroom d'in yake isketa,amma yanzun tana neman tada masa hankali,shiga yayi da sallama a bakinsa,a hankali ta d'aga kai ta kalleshi cikin had'e rai ta amsa masa ta sake kautar da fuskarta akansa,kusa da ita ya zauna ta wajen flat tummy d'inta da babu wata alama da zata sa ayi saurin gano ta tab'a haihuwa,sai daya gama kallonta ya kuma karanci yanayinta sannan ya fara mata magana
"KHUSHI.. Me yake damunki ne..??"
Tsabar haushin da tambayar ta bata,bata san lokacin data harare shiba,kamar zaiyi dariya lokacin da suka had'a ido da ita,masifaffen kishin dake cin ranta har lokacin shi ne abunda yayi arba da shi a cikin eyeballs d'inta,shoulders d'inta ya kamo ya tada ita zaune yana jinginata a jikinsa,cikin muryan rarrashi kuma ya shiga bata labarin ko wace ce ZAHRA MALEEK a gurinsa da alak'ar picture d'inta da shi,lokacin daya gama bata labarin,sai kawai ta tab'e baki kafin cikin sanyi kuma ta furta
"Ta yiwa kanta ai..!"
Kamar zai tuntsire da dariya amma nan take mulki ya hana masa yin hakan,sai dai d'an murmushi daya saki,daga haka kuwa bata sake tada masa da maganar ba,ta maida kanta ta kwantar ajikinsa,shima d'in biye mata yayi sannan ya shiga rage mata kayan jikinta dan lokacin data shigo ko hijab d'inma bata samu damar cire wa ba..
*BARI MU WAIWAYA BAYA...*
_CIKIN LABARIN *ZAHRA MALEEK*_
Kamar yadda muka san labarin ZAHRA MALEEK data kasance y'a ga jakadan k'asa AMBASSADOR ABDULMALIK,,,wacce tun a bayan rabuwarsu da Yarima bamu sake jin d'uriyarta ba sai a wannan lokacin,,,ZAHRA MALEEK shahararriyar mace ce wacce duk muka riga muka san labarin alak'ar ta da Yarima YAZEED a bayan,har ma da dalilin rabuwarsu wanda shi ne musabbabin da yasa ta shiga damuwa bayan fasa auren nasu duk da ita tace ta fasa d'in bisa d'an tak'aitaccen binciken da tasa aka yi mata akansa,,sai dai ko da aka sake d'iban kwanaki game da AL'AMARIN bayan ta gama zaman jimamin tuni sai tayi watsi da duk wani damuwar dake ranta game da Yariman sannan ta ci gaba da sabgogin gabanta,kasancewar iyayenta sun jik'ata da naira haka nan duk inda take son sanya k'afarta a garin ABUJA dama wajenta a kuma duk lokacin da tayi ra'ayi babu mai hanata sai yasa tun bayan rabuwarta da Yariman sai idanunta suka sake bud'ewa ta shiga yawon clubs,duk wani night club dake cikin garin abuja sai ga ZAHRA a d'an k'ank'anin lokacin ta san da zamansa,,a irin wannan bin daren nata na zuwa party clubs kamar yadda ya zame mata d'abia kwatsam wata rana sai ta had'u da wani tantiri,sam ZAHRA bata san waye shiba a garin dan haka lokacin daya shigo cikin club d'in akan idanunta ne,lokacin da suka yi kallon kallo sai ya shiga tun k'arar ta,sanda ya tarar da ita a kusa da bar sai yayi kamar zai wuce ne,amma sai kawai idanunsa suka sauka kanta,a time d'in itan ta tsaya ne kawai amma babu abunda take,dai² kusa da ita yazo wucewar kamar wanda magnet ya finciki hannunsa nan take ya dank'o boobs d'inta had'e da pressurized nasu da k'arfi,a fusacenta ta d'ago coz tunda ta fara yawon bin clubs a d'an lokacin bata tab'a had'uwa da wanda ya mata irin wannan cin kashin ba,ai kuwa tana d'agowan bata tsaya jinkiri ba ta sauke masa lafiyayyun mari har guda uku a each side na chicks d'insa,k'aran marin ne ya taimaka wajen jan hankalin sauran jama'ar dake gurin,kasancewar akwai wanda suke y'ar tsama da shi a gurin coz shi d'in mutum ne mai yawan son taba duk macen da idanunsa ya sauka akanta kuma yaji zuciyarsa ta raya masa yin hakan,a mugun mamakance mutane suke kallonta nan take gurin duk ya d'auki shiru,dan hatta cool music dake tashi a gurin DJ ya tsayar,aifa kada kuso ganin fuskokin masu adawa da saurin,bayan kamar minti biyu kawai nan take wasu suka hau ihu da sowa suna fad'in tayi musu dai²,,wannan ihun shiya tunzura kyakykyawan matashin ba tare da tunanin komai ba kawai ya sab'a wani wine bottle dake ajiye da nufin rotsa mata akai dan duk itace taja masa wannan ihun,daga can gefensa wani sanyayyan murya ya furta
"Kada ka soma..!"
Duka sai suka sake juyawa suna kallon gurin da aka yi maganar hatta ita ZAHRA d'in dake tsaye tana huci,murmushi ta saki kafin cikin saurinta ta nufi matashin dake tsaye yana k'arewa d'ayan da suke kan rikici da ita kallo,tunma bata k'arasa ba ta furta
"AARIZ Dear..!"
Da d'an gudunta ta mak'ale shi tana murmushi mai sauti kafin ta fara tambayarsa yaushe ne ya zo k'asar,murmushi ya mata sannan ya shiga bata amsa,a hakan suke d'an hira wanda duka alamu suka gama gwada tuni ma ta manta da sabgar wancan guy d'in data shararawa mari,,shima d'in koda ganin haka a fusace sai kawai yayi jifa da kwalbar dake hannunsan cikin masifaffen b'acin rai kuma ya juya da sassarafa ya bar gurin,friend d'insa dake tsaye kuma akayi komai akan idonsa shi ne yayi saurin dafa masa baya yana fad'in
"BURAYD stop..!"
Amma ina ko saurarensa baiyi ba dan tuni har ya fice,tab'e baki ZAHRA tayi sannan ne kuma suka saki juna ita da guy d'in data kira da AARIZ, hira sosai suka yi da juna irin ta yaushe gamo,saboda kasancewar AARIZ friend d'inta da suka had'u tun a London nd tare ne suka yi school,to itan tun da suka kammala degree sai ta ajiye karatun,sab'anin shi daya ci gaba inda yanzun ya kai matakin DR a b'angaren karatun,,nd ya kasance d'an wani babban minister ne a nan abuja d'in,,hira sosai mai dad'i suka dasa dan sun jima basu had'u ba,dan haka ranar ZAHRA bata koma gida da wuri ba.
Shima BURAYD bayan fitansa a club d'in kai tsaye wani arnen toyota venza ya fad'a zuciyarsa sai tafasa take,tunda yake a duniyarsa iya tsayin rayuwarsa wata mace bata tab'a fidda hannu ta mare shiba sai yau,yau d'inma mafi muni aka yi masa dan a cikin jama'a hakan ya faru,nd abunda yafi masa ciwo ma duk ba marin tane yafi bak'anta masa ba kamar ihun da aka masa wannan abun idan ya tuna yana masifar sashi jin duk duniyarma tayi masa wani daban,ko kafin ya tada motan tuni friend d'in san ya riske shi,da sauri shima ya fad'a motan,ko gama daidaita zamansa baiyi ba BURAYD ya fizgi motan ya harbata a kwalta,banda azababben gudu babu abunda yake zab'awa har suka kawo wani mansion dake nan a gwarinfa,shikam abokin nasa nan yaga tashin hankali dan suna shiga a guje yaga BURAYD yayi cikin gidan ba tare daya bi takan guards d'in gidanba ya shige abunsa,still ya biyo shi a baya,yadda BURAYD ke had'e staircase d'in yana tsallake su kai da gani zaka san ransa ya kai mak'ura wajen b'aci,,a bedroom d'insa ya iske shi sai zirya yake hannayensa duka a dunk'ule cikin matsanancin damuwa ya kalle shi yana furta
"Kamar ni wata mace zata fidda hannu ta mara..??"
Kusa da shi friend d'in san ya tsaya yana son rarrashinsa
"No Man! Kada kasa damuwar yarinyar a ranka mana,kaifa babba ne.nd i promise u zanyi handling case d'in..."
"Haba mana FADL,,ta yayane bazan damu ba,,mace fa,tasa hannu ta mare ni..kasan kuwa bazan tab'a yafe mata ba,,coz ko Umminah na manta when last ta d'ora hannu akaina,,sai wannan y'ar shilar.??"
Sosai FADL ya shiga bashi hak'uri dan yasan halin BURAYD tsaf ,tun yarintar su tare suke dan su d'in sun kasance y'ay'an aminai,sai dai shi BURAYD Abba'nsa ya kasance d'aya daga cikin Senate president shi yasa duk wani rashin ji ya haddace a kwanyarsa nd ko uban mutum waye bai k'i ya gindaya maka d'iban albarka ba,beside kuma idan har fad'a ya had'a shi da wani sai ta Allah,, shi yasa yanzunma FADL yake ta bashi baki akan yayi hak'uri,,bai kula shiba dan shi kad'ai yasan mene ne ya k'udurcewa ransa akanta.
After 2 days da faruwar AL'AMARIN wanda har ranar BURAYD bai sake fita ba bare ya lek'a club saboda b'acin rai,sai yau da yaji zaman ya isheshi haka nan,,11pm har ya gota ya fito cikin wani had'ad'd'en long sleeve V neck waistcoat mai double breasted belt kalarsu gray,tun daga sama har k'asa muddin aka kalle shi dole ne a sake dan yadda yayi masifar kyau sai dai ko kusa da tarar da Yarima bai ba bare ya kamo shi,car keys d'insa ya Zara sannan ya fice,kai tsaye sai ya nufi club d'in da abun ya faru,a zuciyarsa kuma yana raya irin rashin mutuncin da zai shuka mata,yadda yake jin abun har yanzun ji yake komai ma ta kama zai yi mata buh a tsarinsa ya k'udurce ba zai tab'a rama marinasa ba,kawai dai zai bar mata darasin da zata k'are rayuwarta bata manta da shi ba.
Cikin rashin nasara BURAYD yaje club d'in a wannan ranar coz lokacin ita kuma tuni har ta tafi gida,dan haka wani haushin ya sake kama shi,daga nan bai ma tsaya b'ata lokaci ba ya bar club d'in duka,ak'alla sai da suka shafe about 1 month da faruwar AL'AMARIN amma kullum abun na nan a ransa,kuma kullum d'in idan zaune sai ace masa tazo amma har ta tafi,,kwatsam wata ranan daya shiga club d'in a time d'in daga shi sai wani shegen arm lace da 3quarter shigan black n white,kamar wanda aka ce kalli can,yana d'aga idonsa ya hangota zaune tana ta faman dariya nd a time d'in suna tare da wannan guy d'in da bazaima iya tuna sunan saba,jinjina kai yayi daga tsayen da yake,sannan ya matsa zuwa bar ya haye saman wani stool,waya ya zare daga aljihunsa ya daddana sannan ya sata a kunne,seconds biyar zuwa goma ya fara magana
"Yeah..! Ka same ni inda muka saba had'uwa.."
Daga haka bai k'ara komai ba ya katse,kusan mintuna goma da gama maganar sai ga wani matashi wanda ko a shekaru babu tabbas ya kai tsaran BURAYD d'in,da zuwansa sai suka yi hannu da juna sannan ya d'auko masa wani bottle ya mik'a masa,amsa BURAYD yayi ba tare daya jira cewar guy d'in ba ya b'alle murfin kuma ya nufi inda take,tun daga nesa ta hango tahowarsa sai dai bata kawo komai a ranta ba suka ci gaba da firansu cikin nishad'i,shi kuwa BURAYD a time d'in koda ya tsaya gabanta bai kula ma da irin kallon da take masa ba ya fito da bottle d'insa tare da juye mata acid d'in dake ciki duka,razanannen ihu mai tattare da azaba ZAHRA ta fasa wanda yaja duka hankalin kowa dake wajen,kafin ta shiga kururuwa tana ihun azaba,shi kam AARIZ ko daya ga abunda BURAYD yayi nan yayi tsalle kansa ya shak'o wuyansa dukansa yake yana tambayarsa meya watsa mata,cikin zafin zuciya irin na BURAYD ya fara k'ok'arin hankad'a AARIZ amma sai ya kasa,hakan sai yasa nan da nan fad'a ya kacame tsakaninsu suka shiga dukan juna,,da kyar dai aka samu aka rab'a su sai haki suke kamar wasu zakaru,,kai tsaye daga nan itama wani hospital aka wuce da ZAHRAN dan bata taimakon daya dace,kafin kuma aka kira mamanta aka shaida mata abunda ya faru,nan hankali a tashe suka d'iba jiki da guards d'insu suma suka wuce hospital d'in coz a time d'in daddyn ta baya k'asar,,,, sai da ZAHRA ta shafe ak'alla kusan watanni uku a asibiti tana jinyar fuskarta kafin ciwukan ya fara k'ok'arin warkewa,sai dai duk da irin k'ok'arin da hospital d'in suka gwada akanta sai da abun ya so fin k'arfin su,daga nan nefa kuma sai aka musu kwatancen asibitin da su Yarima suka tab'a aiki saboda kwarewarsu wajen surgery,shima d'in dai koda suka je a hospital d'in sunyi abunda suke ganin zasu iya amma babu nasara dan haka ne sai suka tura su reshen asibin da yake taimakawa a can Kano tare da tabbacin idan har sun samu damar ganin d'aya cikin su biyu to za'a dace,wannan dalilin yasa kuwa basu yi k'asa a guiwa ba suka taho d'in duk dama daddyn nata yaso ace sun fita da itan bayan nan kuma sai suka kamo hanyar kamin cike da sa rai,, sai gashi kuma da zuwan nasu sunyi nasara sun samu damar ganinsa d'in..Wannan shi ne tak'aitaccen abunda ya faru da rayuwar ZAHRA MALEEK a bayan rabuwarsu da Yarima..
*INA LABARIN AISHA..??*
Aisha kam tun bayan da taron tonon asirin nan ya watse bayan maimartaba ya sallami duka ahalin,sai zuciyarta take cikin matsanancin damuwa da fargabar abunda zata tsinta cikin rayuwarta ta gaba,,dan tun daga lokacin da taji cewa itan asalinta daga gidan bayi yake sai taci gaba da rusa kukan nadama mai ciwo,a lokacin kuwa ba komai take sake tunawa ba face Jeeddah a lokacin da su d'in suke d'aukan kansu wasu tsiya a rayuwa,ta jima tana kukan da bata san ma'anar saba kafin Inno ta bata umarnin tashi su tafi,ai kuwa babu musu ta shiga bin mahaifiyarta a baya tun daga cikin gida har zuwa gidan su,lokacin ko da suka kad'aita a gidan nan Inno ta sata a gaba tayi mata nasiha mai shiga jiki sannan ta rungume abarta tana jin k'aunarta na sake bin jikinta a karo na farko kenan tun bayan saceta da akayi,,tun daga wannan lokacin da Aisha ta dawo gidan a kullum bata kasa zubar da wayen musamman na tausayin kanta dama yadda rayuwa ta juya mata a lokaci guda,,haka nan dai take zaune a gidan kullum shiru da tunani a haka har ta deb'i wasu kwanaki,,wanda a cikin haka ne kuma wata rana sai ta shirya bayan ta sanarwa da Inno zata je ta deb'o kayanta a can gidan,ita kuwa Inno bata hana ta ba ta bita da addu'ar fatan dawowa lafiya,nan Aisha ta kama hanyan gidansun,,tun daga bakin get d'in gidan take ta kuka dan yadda al'amuran da suka gabata suke dawo mata a sabo kamar ma yanzun ne suke kan faruwa,tana wannan kukan har ta shiga ciki bayan sun gaisa da baba mai gadin su,sai data tattare duk wasu muhimman abubuwan ta sannan ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 61 Chapter of 63