ya ratsa parlour'n cikin k'ank'anin lokaci sannan maimartaba ya sake kallonsu yana murmushi
"Albishir na gaba da muke fatan sanar daku shi ne,a jiya munyi magana da HAJIYA ta kuma sanar damu in sha Allah idan har Allah ya ara mana lokaci cikin satin nan tana kan hanyar dawowa,saboda haka sai ku fara shirin dawowarta....Na sanar daku wannan nauyin ne tun yanzun saboda kada wani abu ya gifta na kasa sanar da ku abunda ya kamata ku sani...Muna fatan zaku kiyaye hakan..."
Murna sosai ahalin suka fara da jin wad'annan labari daga bakin maimartaba,kafin yasa akayi addu'ah ya sallame su gaba d'aya.
Haka taron ya tashi kowa na farin ciki musamman ga YAZEED dan tunda aka fara maganar da yaji abunda YASEER ya fad'a yake jin wani yanayi a tattare da shi sai dai ko bayan nan bai yi masa maganar ba saboda yasan halin YASEER en yanzun sai ya raina masa hankali har maganar ta salwanta ba zai taba tsayawa su fuskanci juna akan maganar ba,sai dai kawai ya zuba masa ido lokuta da dama dan tun a bayan fitowarsa daga gidan yarin YASEER yake ta masa abubuwan al'ajabi,dalilin da yasa k'imarsa da k'aunarsa ta sake k'aruwa a gurinsa kenan,har ma idan wani abu ya had'a su da YASEER en ya masa badaidaiba bayan al'amarin ya lafa sai yaji rashin dad'in abunda yayi masa...
Kwanaki uku tsakanin maganar maimartaba da ahalin nasu sak'on isowar HAJIYA ya riskesu daga k'asa mai tsarki,yadda gidan ya kacame da shirye²n dawowarta sai mutum yayi zaton wani gagarumin biki za'ayi,ko ina na gidan an chanja masa tsari da fasali sai shek'i da d'aukan ido yake,girke² kuwa tamkar ana wani mashahurin taron da dubunan mutane zasu halarta,cikin haka Allah ya sauk'i HAJIYA a k'asar ta nigeria lafiya cike da jin dad'i da farin cikin kasancewar ta a cikin ahalinta,gefe guda aka gyara mata tare da bayin da zasu ci gaba da mata hidima,wanda a washe garin ranar dawowarta kuma maimartaba ya shirya gagarumar liyafar murna duka ta dawowarta.
Kasancewarta Babbar mace dattijuwa da kowa ya kalleta zai san tana da nasaba da gidan sarautar,yasa manya da dama ak'asar suka samu damar halartar taron,cikin shiga ta alfarma kuwa ahalin suka shiga shige da fice a cikin al'ummah,ko ita kanta hajiya duk inda ta gifta banda k'arar k'arafa babu abunda mutum zai dunga ji saboda yadda sautinsu ko kad'an baya b'uya,duk da girmanta da kasancewarta mai manyan shekaru hakan sam baisa ta maida kanta tsohuwa ba kamar yadda al'ummarmu hausawa kanyi da zaran shekaru sun fara ja musu,sam hajiya bata had'a hanya da irin wadannan jama'ar ba,y'ar gayu ce itan da ko wata budurwar ba lallai ne ta nuna mata sanin me duniyar ke ciki ba.
Bayan dawowar Hajiya daga k'asa mai tsarki da y'an kwanaki al'amarin tafiyar su YAZEED karatu ya taso kamar yadda maimartaba ya tsara kuma ya sanar dasu su kasance cikin shiri dan a ko wane lokaci za'a iya kiransu,haka har sanda lokaci ya gabato ko yaushe cikin shiri ake,shiri sosai maimartaba yasa aka musu,cikin hukuncin Allah kuwa a satin jirginsu ya d'aga daga 9ja zuwa k'asar ta India,inda basu sauka ko ina ba sai a birnin na BANGALORE da makarantar da zasu yi karatu take can,haka garin ya kasance daga b'angaren kudu maso yammacin k'asar ta india,a cikin wani gari da ake kira da KARNATAKA.
Gida guda maimartaba yasa aka sama musu da zasu zauna dan gudanar da al'amuran da suka shafi karatun nasu ba tare da fuskantar matsala ba,a wani estate dake cikin arean HUBLI wanda aka fi sani da HUBBALI,haka maimartaba yasa aka had'a su da bayi masu yi musu hidima zuwa masu kula da al'amuransu daga nan har zuwa lokacin da zasu kammala karatun.
Duk da a b'angarensu Yaseer en basu so tafiyarsu da bayin ba sai don kasancewar hakan umarni daga maimartaba yasa dole suka ja bakunansu ba tare da sun ko iya nunawa a fili ba bare su furta aji,coz sun san matuk'ar maganar ta koma ga maimartaba abunda zai biyo baya bazai musu kyau ba.
Ko da saukarsu sai da suka shade ak'alla sati guda da saukarsu ba tare da sun fita ko ina ba,a cikin sati na biyu ne da zuwansu sannan suka d'auki hanyar INDIAN INSTITUTE OF SCIENCE BANGALORE,tun daga zuwansu garin cikin y'an kwanakin da suka yi yasa tuni suka fahimci yadda al'amuransu zasu kaya a k'asar dama cikin makarantar.
Haka tun bayan tafiyarsu babu wani matsala ko wani abu daya sake giftawa da wasa bare ya shafi rayuwarsu ko rayuwarsu imma a cikin k'asar ko a k'asarsu ta haihuwa,cakin sha'awa da burgewa haka harkar karatunsu ta soma tafiya cike da nasarori cikin hukuncin ubangiji suka maida hankali sosai akan duk wani abu da zai kawo muau ci gaba ba tare da samun wata damuwa da zata gifta musu ba bare ta hanasu karatun ko ta tab'a rayuwarsu...
^^^^^
*A GURGUJE....*
Rayuwar su Aisha a gidan yari kam ba'a iya cewa komai,izuwa wannan lokaci tuni ta d'an sauya zani,duk da bawai captain ta sawwak'e musu wahalar da suke fuskarta ba,amma zuwan Adda gurinsu ya kawo musu ci gaba,kasancewar a wannan lokaci sun d'an samu sassauci daya rage musu wani kaso cikin irin bautuwar da suke da bin duk wani doka da aka shimfid'a musu a gidan,har ta kai yanzun captain kan sakar musu fuska batun hantara zagi ko cin fuska duk babu shi,tun suna aiki cikin rashin sabo da gogewa har abun ya dawo ya zame musu jiki,ta ko wane gefe kam sun gama k'warewa da duk wani aikin wahala na gidan da za'a sasu yinsa.
Kimanin watanninsu shida a gidan wanda yayi dai² da watanni biyar da y'an kwanaki da tafiyar su YASEER k'asar ta India aka sallamesu bayan Adda ta shiga lamarin nasu ta biya duk wani tarar da aka gindaya musu,nan ta kwashesu suka nufi hanyar katafaren gidan da ya kasance mallakinta a unguwar ta Lamid'o crescent,lokacin da Ladidi da Aisha suka yi arba da gidan tuni ta'adin gurin ya haddasa musu susucewa dan ko cikin mafarki basu tab'a tsammani ko hakaito rayuwarsu da kasancewar su a irin wannan gida ba bare kuma har ta kaiga sun ga hakan a zahiri.Tun a bayan Fitowarsu kuwa daga gidan kason nan Adda ta zage ta shiga basu kulawa ta musamman ba don komai ba sai dan tana buk'atar su koma cikin hayyacinsu cikin k'ank'anin lokaci............
*BAYAN SHEKARU BIYAR DA TAFIYAR SU YASEER ZUWA K'ASAR INDIA.........*
_Afuwaan fan's yauma dai sai hak'uri typing en nawa wollah..._
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏*
___________________
_*My Fatima Zois* Wannan page en tukuici ne zuwa gare ki,domin jin dad'in ki ke da masoyanki masu k'aunarki fisabilillah! Comments enki akan littafin *WANI AL'AMARIN* bazai fad'u ba,ki huta tawan Allah ya ara miki wannan lokaci.._
→→→→→→→→
*Pg 15.*
^^^^^^^^
A gefen jeeddah kuwa tun bayan dasu YASEER suka bar k'asar take cikin yanayin kwanciyar hankali,tsakanin ta da iyayen gijinta babu wani abu na badai²ba,kullum cikin bawa kowa girma da mutuntawa take,hatta kuwa da tsakanin su bayi bata yarda ta raina wani ba,duk wanda ke sama da ita a shekaru tana k'ok'arin bashi girmansa yadda ya dace,a b'angaren aikintama haka abun yake babu wani sab'ani da suka tab'a samu da kowa,kullum cikin hidimtawa iyayen gijin nata take cike da sabo da mutuntawa,kamar yadda take jin dad'in aiki dasu haka suma kowa yake jin dad'in kasancewa da ita.
Al'amarin dawowar su YASEER kuwa tun da labarin ya riski kunnuwan duka bayin gidan kowa yake nan²,a kullum rana tunda watan dawowar su ya kama cikin hidima ake a gidan,babu wani mai samun cikakken lokacin zama,haka ko wane lokaci basu suke samun lokacin komawa gida ba sai dare,yauma hakan take domin kuwa tun asubar fari bayan sun idar da sallar Asubah suka fito daga gida ita da Inno suka nufi cikin gidan,saboda k'arasa shirye²n da ba'a k'arasa ba...
^^^^^
Fitowar Adda cikin ado daga bedroom enta tana sauri yasa ni sakin baki na bita da kallo,shiga ta alfarma tun daga sama har k'asa haka ta zubata,zallar jan k'arfe kuwa kad'ai data baza a jikinta kamar idan ka kira shi zai tako da k'afarsa ya kawo kansa,a cikin katafaren parlour'n ta tsaya turus tana waige² kamar tana neman wani abu,zuwa can kuma a hankali ta saki tsaki sannan ta juya zuwa hanyan staircase, jikin reeler en ta kama tana d'an d'aga kanta sama cikin muryar k'osawa ta shiga fad'in
"Aisha..! Wai kam bazaki sauko bane haka nan,kin sanfa ke nake jira ko..??"
Daga can sama cikin sanyayyar muryarta ta amsa
"Please..! Adda gani nan saukowa ina k'arasa shirin ne.."
Siririn tsaki Adda ta kuma sannan ta juya zuwa saman cuition tana mita
"Ni matsalata daku kenan ke da uwarki,duk sanda mutum ke sauri sai kun nemi b'ata masa rai da lokaci,fisabilillahi yanzun k'arfe nawa nema kuma tun yaushe na sanar dake tafiyar nan..?"
Tayi maganar tana d'ago tsintsiyar hannunta dake d'aure da wani agogon sark'a k'irar Gucci
"Wollahi idan baki sauko yanzun ba zaki fito ki tarar da bana nan,wannan ai iskanci ne,tun yaushe nace ki shirya amma saboda tsabar nuk'u² da yayi miki yawa kin hau sama kinyi shiru keba tsuntsuwa ba bare nace dama gadonku ne zaman sama.."
K'arar takalminta yasa Adda d'agowa daga mitar da take zubawa tabi hanyar da kallo,a hankali cikin nutsuwa y'ar matashiyar budurwar da adadin shekarunta baza su wuce ashirin da uku ba take takawa tamkar bata son tafiyar,nan kuwa tsabar mamakin abunda idanunsa suka gani yasa nabita da kallo cike da son gane inda nasan mai wannan kammanin,cike da tantamar inda nasan mai wannan kamannin na bita da kallo har zuwa sanda ta tsaya a kusa da Adda,sosai na k'ureta da ido fuska cike da tsantsar mamakin gano ko wace ce itan,a fili na furta *"AISHA..!"*
Waiwayowar Adda da Aisha a lokaci guda yasa ni saurin b'uya k'asan staircase gudun kada su hango ni su antaya ni waje na shiga lek'en su ta k'asa,juyawa naga sunyi a hanakali suka kama hanyar ficewa yayin da Adda ta bud'e murya da d'an k'arfi tana fad'in
"Ladidi mun tafi sai mun dawo...!"
Cikin sauri ta fito daga d'aki tana amsawa da fad'in
"To Adda a dawo lafiya,Allah ya tsare hanya.."
Daga haka suka fice a gidan cikin motar da Aisha ke driven,ni dai gaba d'aya al'amuransu sun d'auremin kai musamman yadda naga Aisha da Ladidi sun koma wasu y'an gayu na ban mamaki,nasan ko ku kuka gansu a wannan lokacin dole ne kuyi mamakin yadda cikin y'an tak'aitattun shekaru suka koma,a hankali Aisha dake driven motan,cikin nutsuwa ta d'an waiwaya ta kalli Adda tana fad'in
"Adda ina muka nufa...??"
Ba tare da Adda ta kalleta ba saboda wayan da take pressing a hannunta ta furta
*"ROYAL PALACE....!"*
Wani uban brake Aisha ta taka a sakamakon jin maganar da Adda tayi,hakan kuwa ya haddasawa Adda yin gaba da baya,cikin takaici da b'acin rai bayan ta dai²ta zamanta ta kalleta
"Anya Aisha kina cikin hayyacinki kuwa yau..?? Duba yada kika kusa sawa muyi hatsari daga tambaya na baki amsa.."
"Sorry..! Adda."
Tsaki Adda ta saki kafin ta juya tana maida wayan cikin jaka tana mita,ga Aisha kuwa tunda taji an ambaci *ROYAL PALACE* tuni ta gama sukurkucewa,nutsuwar ta tayi tsallen albarka daga jikinta ta fice ta window,suna tafe tana tunanin abunda zai kaisu masarauta bayan tunda suke da Adda bata tab'a mata maganar masarautar ba,zuciyar ta ce ta kasa nutsuwa da yawan tunane²n da take,a hankali ta sake waiwayowa ta kalli gefen Adda,muryar ta cuke da sanyi ta furta
"Adda me zamu yi ne a can en..??"
Ba tare da Adda ta kalleta ba ta furta
"Me nace miki da zai kaimu...??"
Shiru Aisha tayi ba tare data iya bawa Adda amsa ba,tunawa da abunda Adda'n tace mata za'ayi masarautar a safiyar ranar,driven take amma har lokacin ta rasa da yadda zata fassara AL'AMARIN,a haka har suka yanko takan titin da zai sada mutum da ainihin cikin gidan sarautar.
Koda suka samu waje nan cikin harabar gidan suka yi parking motansu,nan suka ci gaba da takowa da k'afarsu inda suka shiga wuce manyan sorayen gidan sarautar,jikin Aisha har lokacin bai daina zikirin da yake yiba,a haka har suka k'arasa wucewa,b'angaren Hajiya suka nufa direct,tun kafin su k'arasa shiga cikin parlour'n da HAJIYA ta hango Adda ta fara bud'e baki da fara'a tana fad'in
"Lale marhabun da y'ar uwa rabin jiki Adda...!"
Ba Aisha kad'ai ba hatta da ni kaina da nake a bayan su sai da maganar hajiya ta daskarar dani lokaci guda naji ina neman gagara tsayawa da k'afafuna.Ga Aisha kuwa jin wannan magana ta HAJIYA nan itama ta k'ame ta kasa gaba bare baya,tsabar mamaki da zallar fargabar yadda akayi wannan dattijuwa tasan Adda shi ya hana mata samun nutsuwa,nan take wani irin zafi da gumi suka had'un mata a lokaci guda.
Har Adda ta nemi guri ta zauna Aisha bata shiga cikin parlour'n ba,sai da k'yar bayan tayi yak'i da zuciyar ta da hangar jikinta sannan ta iya shiga cikin parlour'n ta nemi guri nan k'asa saman shimfid'a ta zauna,cikin ladabin da ban san lokacin data koyo shi ba ta duk'ar da kai k'asa tana fad'in
"HAJIYA Barka da yamma..!"
Cike da nutsuwa dattijuwar ta juyo fuskarta ta zuwa gefen da Aisha take kallo ta amsata da fad'in
"Barka ka dai..Masha Allah..! Adda ina kika samo budurwa ban sani ba...??"
Tayi furucin tana bin Aisha da kallo,y'ar dariya Adda tayi kafin ta kalli Aisha tana bawa HAJIYA amsa
"Haba HAJIYA Aisha cefa y'ar wajen Ladidi tawa.."
"Ya salaam..! Yanzun Aishar ce ta zama haka
.?? Ai kam dole na kasa ganeta,dubifa yadda tayi girma..Masha Allah! Girman d'an mutum babu wuya.."
Ita dai Aisha har lokacin kanta na k'asa bata d'ago ba,haka maganganunsu sai sake d'aure mata kai suke,sam ta gaza fahimtar matsayin su a wannan gidan,haka nan ta gaza fuskantar yadda akayi wannan dattijuwa ta santa...
^^^^^
*4:00pm @Malam Aminu Kano airport.*
Da misalin k'arfe 4:00pm na yammacin ranar ta asabar jingin masarauta dake d'auke dasu yarima YAZEED da YASEER had'e da bayin su daya taso daga can k'asar ta India yayi dirar mikiya a k'asar tamu ta 9ja,a katafaren filin nan na tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano,tun kafin isowarsu k'asar kuwa tuni manyan motoci daga masarautar suke tsaye suna jiransu,har wasu daga cikin y'an uwama sun samu damar halartar wurin yayin da wasu ke can gida suna jiran isowarsu.Fara bayyana da bayin masarautar sukayi shi ya tabbatarmin kuma ya tabbatarwa da y'an uwa cewa suna daf da bayyana,cikin shiga ta alfarma duk da kasancewar su wad'anda suka fito daga gidan mutunci kuma mai cike da al'ada,sai dai a wannan rana kam kusan sai nace sun ajiye al'adar gefe,dan kuwa a maimakon naga sun bayyana cikin shigar al'ada kuma ta masarautar kamar sauran y'an uwa,sam sai hakan ya gagara dan kuwa a wannan rana sanye na hangosu cikin suit wacce ta amsa sunanta y'ar asali,cikin nutsuwa suka fara tako matakalar jirgin cike da nishad'i gami da shauk'i mai tattare da nutsuwar rai data hangar jiki mai cike da samun nasarori suke tafe,har suka k'arasa sakkowa murmushin dake kan fuskokinsu bai b'ace ba,yadda gurin yake shak'e da al'ummar masarauta sai yaso basu mamaki,da haka dai samu suka shige motocin dake Parke suna jiran isowarsu bayan gaggaisawa da wasu daga cikin y'an uwa,daga nan akayo musu convoy aka d'ungumo zuwa gidan sarautar.
Tun daga ainihin k'ofar farko ta gidan sarautar mutum zai tabbatar da lallaifa wad'annan samari maimartaba na matuk'ar ji dasu a wannan fada,yadda aka sake k'awata fada abun har ba'a magana,su da kansu yadda suka fara ganin sauye² a gidan har sai da abun yaso basu mamaki,amma tunawa da ko waye maimartaba da yadda matsayin su yake a wajensa nan yasa mamakinsu kaucewa.Tun kafin motocin su fara tsaiwa tuni har y'an uwa da suka zo taya su murnar dawowa sun fara hallara,tsayawarsu babu jimawa aka bud'e murfin motan suka fito,nan fa y'an uwa kowa ya fara nufio su ana san barka da taya su murnan samun wannan gagarumar nasara.
Da k'yar suka samu hanya suka nufi b'angaren Fulani,nan suka tarar da ita a cikin y'an uwa turakar tata babu masaka tsinke,wannan tasa koda suka gaisa basu samu damar zama mai tsayi da ita ba,suka fice suka kama hanyar b'angaren Ummi'n YASEER,can enma dai bata sauya zani ba dan yadda suka tarar da turakar Fulani haka itama nata gefen yake,koda ganin haka sai yasa su ficewa suka nufi gefen Hajiya,a can ne kad'ai suka d'an samu rangwamen al'ummah,sai kuma y'an k'annensu mata da suka samu damar kammala karatun secondry su uku,da maza mutum biyu,nan suka d'an tab'a hira kafin daga bisani suka fice zuwa sashinsu dan su samu su huta gajiya..
Da misalin k'arfe bakwai na daren ranar kuwa,gagarumin dinner da aka shirya na murna dawowar su da tarba dake cike da zallar nuna k'auna daga maimartaba har zuwa kan sauran ilahirin ahalin nasu dole ne ya sa mutum tunani saboda yadda wannan tarba ta sha bamban da sauran irin tarbar da ni kaina na saba jin labari a gari ya faru.
Katafaren d'akin taron dake cikin gidan na gwamnati,cike yake mak'il da y'an uwa da abokan arziki,kama daga masu mulki har zuwa kan masu sarauta,y'an boko gami da masu ji da kud'i duk babu wanda wannan k'ayatacciyar dinner bata tara ba,haka kowannesu yana cikin shiga ta alfarma,yadda gurin yake a tsare haka ma al'ummar gurin suke,abunku da taron masu da shi,babu wani da yake a tsaye kowa ya samu guri ya zauna abun gwanin sha'awa,ciki da wajen gurin kuwa duka tsare yake da dakarun sojoji da bayi wad'anda suka yo rakiya.
Tunda aka fara gabatar da taron ake ta neman su YASEER a wajen amma abun mamakin sam babu su a gurin,haka aka ci gaba da gudanar da taron walimar amma har kimanin k'arfe takwas basu samu damar isowa ba,wannan tasa aka fara neman line su amma abun takaicin shiru duka wayoyinsu a kashe,dole tasa aka hak'ura aka zubawa sarautar Allah ido aga kuma ta inda zasu b'illo.
^^^^^
Can a masarauta kuwa abunda ya faru tun bayan isowarsu k'asar bayan da suka shige gefensu,Ummi ta bawa jeeddah izinin shirya musu abinci mai rai da lafiya ta kai musu can,dan nan en tasan bazai zaunu ba a gurinsu daga lokacin har zuwa dare lokacin daya kamata ace an tafi gurin walimar,haka jeeddah ta amsa sak'on uwar gijiyar tata sannan ta nufi hanyar kitchen en dake nan cikin b'angaren,sanda ta kammala shirya komai kamar yadda aka bata umarni ta zuzzuba cikin manyan cooler's sannan ta d'auka ta nufi hanyar kaiwa sashen nasu,cikin sa'a kuwa harta kammala shirya komai ta fito a gefen bata had'u da kowa ba,a haka ta fice ta kulle musu gurin sannan ta koma ta sanarwa da Ummi ta shirya komai kamar yadda ta umarta,sannu ta mata sannan ta bata izinin tafiya gida ta shirya itama coz tana son ta halarci gurin taron kamar kowa na ahalinsu,amsawa tayi bayan tama Ummi'n sallama ta kama hanyar gida abunta.
^^^^^
Tsabar nemansu da neman wayoyinsu da ake ba'a samu yasa ran maimartaba da mahaifin YASEER b'aci,maimartaba cikin takaicin rashin halartar taron da wuri dasu YASEER basu yiba ya kalli d'an uwan nasa yana masa magana k'asa²
"Shin mene ne labari game da rashin halartar yarannan wannan taron da basu yiba..??"
Cikin girmamawa Abban na YASEER ya bawa sarki amsa
"Allah ya baka tsawon rai..ko kad'an bani da masaniyar dalilin daya hanasu isowa har yanzun.."
Jinjina kai maimartaba yayi kafin ya furta
"A kirasu a waya a tambayesu hujjar da tasa zasu ajiye mu anan muna jiransu,shin mune iyayen ko kuwa su ne..??"
"Ayi musu afuwa ranka ya dad'e bada nufi suka yiba...In sha Allah kuma hakan bazai sake faruwa ba.."
Ba tare da maimartaba ya sake yin magana ba ya jinjina kai,ga Abban YASEER wato GALADIMA kenan,ba tare daya sake yin magana ba shima,ya shiga k'ok'arin bin line YASEER,jin line a rufe yasa shi ya gwada kiran na YAZEED amma abun k'arin haushin shine shi enma nasa line a rufen yake,har yayi niyyan sanar da maimartaba halin da ake ciki sai kawai ya fasa ya shiga neman line Ummi kasancewar ita da Fulani suna gida ransa a mugun b'ace,tana d'auka kuwa taji muryansa cikin b'acin rai yana tambayar ta su YASEER,rashin sanin takamaiman amsar da zata bayar yasa tayi shiru,ai kuwa nan GALADIMA yayi ta fad'a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba tamkar ita tayi laifin haka yayita mata fad'a,hak'uri tayita bashi tunda taji fad'an yayi yawa,da k'yar ya hak'ura yayi shiru sannan ya kashe wayan shima sai da tace masa zata sa a duba side ensu a gano ko lafiya sannan ya kashe wayan,lokacin daya kashe tana ajiye wayan ta saki wani ajiyar zuciya,nan tasa aka kira mata wani cikin bayin dake gefen ta,lokacin daya iso ta juyo da niyyar aiken su je su duba mata ko su YASEER en suna can,sai ga jeeddah ta shigo fuskar nan sakaye cikin nik'ab tayi sallama,fasawa Ummi'n tayi ta sallame su sannan ta juya ga jeeddan ta kirata ta bata umarnin taje ta dubo mata sashen nasu YAZEED ko lafiya aketa kiransu wayoyinsu a kashe kuma ba'a san a wane hali suke ba.Amsawa tayi cike da ladabi sannan ta fice ta kama hanyar gefen nasu cikin sauri ganin yadda gidan yake babu mutane sosai sai dakaru masu tsaron gidan ta kowane lungu da sak'o.
Har ta k'araso bakin sashen nasu bata ji alamun motsin mutum a cikiba,har ta juya zata koma ta hangi haske a cikin parlour'n ta tsakanin curtains da sauri ta koma ta shiga knocking k'ofar tana jiran a bud'e ta isar da sak'on Ummi,ta d'auki kimanin mintuna goma tsaye a gurin ba tare da an bud'e mata k'ofar ba,hakan yasa ta fara tunanin ko lafiya hakan ya faru..?? Sake juyawa tayi zata koma nan take wata zuciyar ta bata shawarar shiga ta duba halin da ake ciki,da saurinta ta dawo zuciyar ta na skipping ta kama handle en k'ofar ta tura ciki,koda k'ofar ta bud'e nan tabi sahun k'ofar zuwa ciki bakinta d'auke da sallama kafin ta shiga kiransu
"Babban Yaya...! Yallab'ai..!!"
Shirun data ji yasa ta tunanin anya kuwa suna nan..!? Zuciyarta ce ta bata amsa "Shin idan basa nan me zaisa wutan side en ya kasance a kunne..??" Shiru tayi tana daga tsaye a bakin k'ofar kafin taci gaba da takowa cikin parlour'n tana fad'in
"Akwai wani anan da yake jina..??"
Nanma shiru
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 63