ba..Dani suke zancen ne.."
Iri²n hirar da suka yi tayi kenan a haka har suka isa gida zuk'atansu cike fa farin ciki mara misaltuwa na.
^^^^^
Yadda suka yiwa juna shiru na tsayin lokaci,yasa YAZEED kallon inda YASEER yake kwance yana latse² a waya yana ta zuba murmushi abunsa,sai daya tab'e baki sannan ya fara magana
"Wai kai baka da aiki ne saina danna waya kana murmushi kamar kayi gamo..??"
Bai d'ago ba bare ya kalleshi ya bashi amsa
"Dama mana ai gamo nayi..Amma da sanyin idaniyata ba.."
'Dauke kai yayi dan ya fahimci magana YASEER yake shirin gaya masa,wayana ya d'auka kawai ba tare daya kula shiba ya shiga kiran line Ummi dan a lokacin kam wata irin mahaukaciyar yunwa yake ji,duk yadda yaso kuma ya d'aure yaji bazai iya ba,dai² lokacin Ummi ta amsa masa cikin sallama,sai daya gaidata sannan ya fara magana
"Ummi zamu samu abincinkuwa yau..Munga shiru har yanzun Allah yasa ba mantawa kika yi da y'ay'an naki ba.."
Daga b'angarenta itama Ummi'n dariya ta d'an yi kafin ta amsa masa
"Taya zan manta da rabin raina..Kasan aikinta hidima irin wannan ba kamar na kowa ne lokaci bane ai,amma kada ka damu yanzun zaka ga aike,in sha Allah zan turo a kawo muku yanzun.."
Murmushi yayi sannan ya furta
"Godiya muke Ummi'n mu..Allah yaja da nisan kwana.."
"Ameen" ta amsa masa sannan suka ajiye wayan a tare,kusan tsayin mintuna talatin sannan akayi nocking k'ofar apartment en,izinin shigowar ya biyar yana daga yadda yake ba tare daya samu da duba wa ba dan yasan ba zai wuce aiken Ummi ba a lokacin,a hankali aka turo k'ofar bakinta d'auke da sallama ta shigo,cikin nutsuwa take tafiya jikintan nan kamar ko wane lokaci acikin shigar data zame mata tamkar gado,a haka ta isa bakin dining en ta fara shirya gurin,har ta kammala bai ko d'ago ba bare ya kalli gurin,har ta gama ta juya zata bar wajen sai kuma taga rashin dacewar hakan,daga gefen seat en da yake ta baya ta d'an kakata sannan cikin sanyin muryar ta furta
"Yallab'ai na kammala..Shin zan iya tafiya ko akwai wani abu da kuke buk'ata..??"
Da kai ya amsa mata ba tare da yayi magana ba,gar ta juya zata fita YASEER ya waiwayo
"K'anwata wucewa za kiyi ko gaisawa bamu yiba..Ko kuma dai kin sake wani Yayan ne ban sani ba..??"
'Dagowa tayi ta kallo inda yake tana sakin murmushi duk da a time en akwai nik'ab a fuskan nata,cike da jin kunyar abunda ya fad'a ta fara matse yatsunta
"A'a Babban Yaya.. Ko kad'an ban canjaka ba,kawai dai yanzun ne da ba zama kuke ba a garin shi yasa zaka ga kamar ko na manta da kai ne..Amma sam ba haka abun yake ba.."
"A'a fa k'anwata idan har baki manta dani ba,ai zaki iya nemana ko a waya ne kiji halin da nake ciki ko..??"
Shiru tayi jin abunda ya fad'a ba tare data iya cewa komai ba,cikin nutsuwa YAZEED ya d'ago ya kalli YASEER sannan ya had'e rai yana sakin tsaki mai sauti da yaja hankalinsu duka kansa.................
*Mun samu matsalar wutan NEPA yau sai hak'uri typing en nawa,nd ban samu damar yin editing ba,kuyi manage da wannan kafin muba abunda Allah zaiyi.......*
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Pg 32.*
^^^^^^^^
Sosai fuskokinsu suka bayyanar da mamaki dan basu san dalilin da yasa shi yin tsakin ba,Yaseer kuwa ko da yaga bazai iya yin shiru ba sai ya kalli YAZEED en da ya mik'e yana kama hanyar dining
"Broah lafiya kuwa kake irin wannan tsakin..??"
Ci gaba yayi da tafiya abunsa ba tare da ya tanka masa ba ya haye dining abunsa ya fara saving kansa da abunda yasan ransa naso cikin kalolin abincin dake gurin,ko da ganin haka shima YASEER sai ya mik'e yana girgiza kai cike da takaicin wasu cikin halayen Yariman da sam a wasu lokutan basa kamata,har yayi gaba ya waiwayo ya kalli Jeeddah da take tsaye kanta a k'asa tana wasa da hannunta
"Zaki iya tafiya k'anwata ina tunanin ai kin kawo duk abunda ya kamata..Idan kuma da abunda muke buk'ata zamu iya sanar da Ummi.."
Godiya tayi masa sannan ta juya ta fice abunta cikin nutsuwa,lokacin da ta fita duk jikinta yayi sanyi,zuciyarta kuwa tunani ne a ciki iri² saboda tsakin da Yarima yayi ita dai duk jikinta ya gama bata tayi wani abu ba dai² ba shi yasa har haka ta faru.Lokacin da YAZEED ya tabbatar ta fita nan shima ya juyo kan YASEER fuska a d'aure yana cewa
"Wai kai mene ne matsalar ka ne da ko wane lokaci kake son yiwa yarinyar nan magana..??"
Ba tare daya d'ago ya kalleshi ba ya furta
"Kana da matsala da hakan da nake yi ne..??"
"Tambayar ka nayi...Ya kamata ka fara bani amsa kafin ka sake tambaya na."
"Baka buk'atar na amsa maka.."
"Ok..good..!"
The place dries up,sai k'aran spoons da plates kad'ai dake tashi a gurin,zuwa can YASEER yaci gaba da magana
"Ban san me yasa lokuta da dama kake nuna irin wannan halin ba,bayan sam ba haka ya dace a matsayinka kana bi da hadiman kaba.."
"What do you want me to start with na dunga goyasu ko..??"
YAZEED yayi maganar ba tare daya kalleshi ba,d'agowa shima YASEER en yayi yana kallonsa cike da mamakin furucin nasa
"Ni bance ka goya su ba,amma dai ya kamata ka duba maganar nan,kai kenan kullum fuska babu walwala,anyone who sees you for fear of doing something,kayi tunani mana.."
Tsayawa yayi da cin abincin da yake ya zubawa YASEER ido
"To baba ya kake so nayi musu..?? Kafi so na sakar musu fuska anytime anyone who designs his evil intention sai ya warware shi a kaina ko..?? Wannan sam ba haline daya kamata ace na d'auke shi ba..Ka fahimta.."
Magana YASEER yake shirin yi da sauri YAZEED ya d'aga masa hannu
"Dan Allah broah let us enveloped this chat.."
Jinjina kai kawai yayi ba don yaso hakan ba sai dan yadda YAZEED ya nuna baya son maganar gaba d'aya, amma kam yau da sai ya warware masa shakkunsa da duk wani zatonsa akan duka al'ummah bakinsu d'aya ne,haka suka ci gaba da zaman kurame abunsa har zuwa sanda suka kammala cin abincin dukansu,YASEER ne ya fara barin gurin,duk da ya fahimci YAZEED en ya jima da gama abunda yake yi,sai dai kuma yak'i barin gurin ba don komai bazai don ra'ayin kansa,direct parlor ya koma yayi powering TV yana kama Bollywood channel,remote en ya maida ya ajiye sannan yaja wayansa ya fara latsawa abunsa,lokaci guda yana kallon TV kuma yana hira da abar k'aunar sa,cikin k'ank'anin lokaci tuni ya shashantar da duk wani damuwa da YAZEED yaso d'ora masa.
Washe gari kasancewar ba wani shirye² su YASEER suka tsaya aka tsara da su ba,yasa aka bar ranar a matsayin ranan kilisar angwanci garesu da y'an uwa saboda su en ba wasu ma'abota shiga jama'a bane bare ace suna da tarin abokai,da yamma after sallar asr aka shirya yin kilisan a nan babban harabar gidan sarautar.Sosai yadda aka tsara abun yayi matuk'ar kyau da burgewa ga jama'ar da suka jakarta taron,Washe gari jumu'ah kuma shi ne ranar da aka sanya ta kasance ranar daurin aure,da misalin k'arfe 2:30pm dubban al'ummah da suka halarci sallar jumu'ah a central masjeed en suka shaidar daurin auren na manyan y'ay'a a masarautar ta maimartaba ABU YAZEED wato DR.MUHAMMAD BIN ABDULLAH ABU YAZEED, daurin auren YAZEED aka fara da amaryarsa Aysha (sajida),sannan na YASEER da Fatima (ABEELA), d'aurin auren kam alhamdulillah! Ya tara al'ummah sosai wad'anda mutum bazai tab'a zaton zai gansu bama da wanda sai mutum ya shafe tsayin lokaci yana jin labarin su amma ganinsu sai yayi masa wahala duka wannan d'aurin auren ya samu halartar su,bayan gama d'aurin aure daga masallaci BRISTOL PALACE suka wuce dan yin reception,katafaren hotel ne dake kan iyaka na kasuwar saida wayoyin hannu ta palm center,wanda ba ko wane jigari²n mutum keda ikon shigar sa ba har sai karan mutum ya kai tsaiko,ko kuma kai en wani hamshak'i ne kammala daga kan shugaban k'asa,governors, y'an majalisu zuwa many an attajirai maa gida Nigeria zuwa k'etare.
After 8:00pm kuma nan aka fara shirin tafiya dinner wanda daga can kowacce baza'a maidata gida ba za'a wuce da ita d'akinta,shiru na sosai aka yiwa kowacce amarya tsakanin sajida da ABEELA wannan tana wace wannan gurin kyau,sanda suka isa gurin dinner cike suka tarar da wajen duk da dinner ne ba kowa ake gayyata ba,amma su kam nasu sai nace duka family'n nasu ne a gurin,komai nasu a tsare duk wani dake gurin yana zaune,su kansu zaune suke kan stage daya sha decoration, a wannan lokaci kam babu yadda za'ayi ka iya tantance fuskar waye tafi bayyana farin ciki a cikin su.
Y'an uwa da k'awaye kuwa nan rawar kai ta k'aru dan yadda samari suka cika gurin kai kace su kad'ai aka gayyata ko kuma dama sune cikon family'n,banda karad'in wake² dake tashi babu abunda ke tashi a wannan fagen.
Tunda ta shigo gurin idanun sa suka sauka akanta,babu abunda yafi jan hankalinsa gareta sama da yadda take tafiya cikin takun isa,ga wanda ya fara ganinta ko kuma ya kalleta a lokacin zai iya tunanin iyayi ne yasa take irin wannan tafiyar,sai dai ga wanda ya santa nan take zai fahimci hakan ba komai bane face zallar aji da take jin tana da shi da kuma kasancewar karanta da yakai tsaiko,har ta zauna saman seat en bai iya janye idanun sa akanta ba,dai² ta d'ago kanta tana kalle² idanunta suka sauka kansa ya tsareta da kallo,a hankali ta saki ajiyar zuciya sannan ta janye idanunta a gurin cikin rashin kuzari tana kallon can wani gefen.
Ba tare daya iya janye idanunsa a kanta ba ya tab'o YASEER a hanakali kuma ya d'an risina zuwa jikinsa,murya a can k'arshen mak'oshi ya furta
"Broah! Can you remember this girl ...?"
D'an waiwayowa YASEER yayi zuwa ga YAZEED fuska d'auke da mamaki yana fad'in
"Wace yarinya kenan fa..??"
"Gorgeous with royal blue dress .."
Ba tare da YASEER ya kalla inda take ba,ya kalli YAZEED yana sakin murmushi
"Haba Mr man..! You have a buddy beside you and wanted to find you a different one. ?? Just delete it,,komai zaiyi dai².."
"Kaga malam nifa ba wannan nayi maka magana ba,dan akwai amarya a nan sai me..?? Ko kuma an fad'a maka itan zab'ina ce,bani da ikon gano wata daban ne..?? Ko nace ina so..??"
"A'a kana da shi..Fiye da hakama idan ka so za kayi,ai masu gidan sarauta suke da mata,har k'wark'wara idan kaga dama za kayi duka a lokaci guda.."
Tsaki YAZEED yayi saboda takaicin maganar YASEER
"Kai ai matsala ce da kai,banda shirme mene ya kawo maganar wani k'arin mata har haka..? Daga cewa ka kalla har ka fara yanke hukunci.Sai ka jira to kaji nace maka sonta nake ai.."
"Haba malam..! Most intelligent people suna jin wannan magannar taka ai will understand where you intend..."
"To naji sonta nake,kuma aureta zanyi shi kenan kaji abunda kake zato.??"
Dariyar rainin wayo YASEER yayi ba tare daya kalle shiba ya furta
"Allah bada sa'a,ya sanya alkhairi..."
In the bitter anger YAZEED confesses
"Ameen...!"
Daga haka bai sake ce masa komai ba,ya juyar da kansa yana ci gaba da kallon yadda take gudanar da al'amuranta,wani abu da tayi yasa k'wak'walwarsa tafiya tunanin wani guri daya santa,ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya sake kallon inda take,tabbas wannan karon kam ya kusa tuno inda ya tab'a ganinta koma ya santa,sai dai sam k'wak'walwarsa ta gaza kaiwa inda yake da buk'ata,haka tunani duk yak'i barinsa ya huta,zuwa wani lokaci ya sake kallonta nan take ya furta
"Tabbas ita ce..........!"
*ITA WA KENAN FAN'S....???*
*AFUWAAN FAN'S..MUN SAMU MATSALA TRANSFORMER ENMU YA SAMU MATSALA TUN RANAR THURSDAY..KU TAYAMU ADDU'AH MU SAMU A GYARA MANA KAFIN AZUMI PLEASE...🙌🏻*
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Pg 33.*
^^^^^^^^
Matuk'ar ace bai manta ba kuwa wannan fuskar ya tab'a cin karo da ita a ranar dinner ensu na dawowa k'asar a lokacin da suka kammala karatu,kuma ko tantama baya yi itance ba wata daban ba.Wata zuciyar ce ta tambaye shi
"Da kake wannan maganar,have you been sure you've seen it?"
Nan take ba tare daya tsaya tunanin komai ba ya bawa zuciyar data tambaye shi amsa da
"Yeahh! I'm sure i know ita ce,nd if not,I can not understand it since my first look."
"Well..! then if aka ce kama cefa kawai suka yi da juna..??"
"It's not just a matter of fact, because it is so,babu wani chanji a tare da ita,bare ace ko rud'ewa nayi,...ko kuma saboda da dare na kalleta ace bazan gane ba,to idan dan ace dare ne wancan lokacin ai yanzunma dare ne,so there is no difference at that time just like .. "
"Good ..! Your answer has confirmed whether or not you can see it."
Murmushi ya saki irin na gefen bakin nan,kafin ya maida hankalinsa duka kanta,duk inda tayi idanunsa na akanta,sai dai a gareta kam tun karon farko da suka had'a ido bata kuma yarda ta kalli inda yake ba,sai dai duk motsin da tayi tana jin kamar duka idanun mutanen gurin suna akanta,hakan kuma ya tabbatar mata da dole akwai wani,ko wasu da suka zuba mata idanun.
Sai misalin k'arfe tara ta yunk'ura ta mik'e a gurin tana duba lokaci,ganin yadda time ya tafi yasa tayi hanzarin tattara y'an kayanta kama daga wayarta zuwa jakarta ta nufi hanyar ficewa a gurin cikin sauri,sam yarima YAZEED bai ankara da mik'ewarta a gurin ba,sai hangota yayi har ta kai bakin k'ofa zata fita,cikin wani irin murya ya furta
"Kash ... Where did that happen..???"
Saurin mik'ewa yayi zai bar gurin ba tare daya d'auki excuse ba,har ya juya yaji an rik'o babbar riganshi ta baya,da sauri ya waiwayo rai a b'ace dan ganin wane mai d'anyen aikin ne sai kawai yaga YASEER yana washe masa baki cike da murmushi
"Sake ni mana broah..ina da abu mai muhimmanci da nake son gabatarwa kuma ka sani.."
Y'ar dariya YASEER ya sake yi cikin rainin wayo ya furta
"What are you going to do?" Ko nace "Where do you plan to go?"
"Please ..! Mana na rok'eka ka sake ni kada ka b'ata min lokaci..!"
Yayi maganar cikin sauri yana sake duba hanyan data bi ta fita,k'in sakinsa YASEER yayi har sai da ya janyo YAZEED en ya b'ata rai,cikin fushi kuwa ya fara masa magana,da kyar YASEER ya sake shi,yana yin hakan kuwa yayi hanzarin sakkowa daga saman stage en ya kama hanyar fita shima,lokacin daya fito a gurin duk da yake gurin akwai yalwar jama'a amma dai ba wani sosai bane,haka yayi ta fakar idon mutane yana dubawa ko zai ganta,amma tamkar gilmawar tauraruwa mai wutsiya babu ita bare dalilinta a gurin,cike da jin haushin YASEER ya koma dan yasan shi ne musababbin da yasa bai ganta ba har ta tafi,haka yaci gaba da hak'urin zama a gurin har zuwa sanda aka tashi gaba d'aya a dinner.
Dai² lokacin da suka fito ne suna shirin shiga mota kawai sai ya hango ta can tsaye ta juya baya,mamaki ne ya lullub'eshi ko dan ganin a d'azun ya fito ya duba kuma duk fad'in gurin sai daya duba amma ko kyallinta bai gani ba bare ita,wata zuciyar ce ta bashi umarnin kawai ya nufi inda take,nan take kuwa ya juya da nufin tunkarar inda taken.
Su Abir da suka tsaya a kusa da ita su ne suka hana shi zuwa wajen,nan ya tsaya yana mamakin yadda akayi suka santa,sai dai ganin yadda suke ta hira suna zuba dariya yasan dole ne da sanayya tsakaninsu,Imma dai ace sun had'a alak'a da ita ta dangantaka ko kuma ta kasance k'awa a gurin ABEELA k'anwarsa,ci gaba yayi da tsaiwa abunsa a nan inda yake yana kuma ci gaba da kallonsu,har zuwa lokacin da YASEER ya lek'o ya masa magana akan ya shiga su wuce gida.
Haka dan babu yadda zaiyi ya bud'e motan ya shiga suka wuce zuciyar sa cike da tunanin ta yadda zai tambayi ABEELA ko Abir matsayinta a gurinsu,da wannan tunanin fal a zuciyarsa suka iso gida.
^^^^^
A b'angaren jeeddah kuwa tun da ta kama hanya ta bar apartment d'in nasu ko waiwaye bata kuma yiba zuwa gurin,duk jikinta yayi sanyi saboda yadda Yarima ya nuna rashin jin dad'i, tunanin da yafi addabar zuciyarta shi ne 'Wane laifi tayi masa da har ya janyo mata fuskantar wannan k'alubalen daga gare shi..??' Har ta iso wajejen apartment d'in Ummi bata bar tunanin da take yi ba,jikinta kuma har lokacin bai sauya daga yanayin da take ciki ba,da k'yar ta k'arasa ciki da niyyar yiwa Ummi'n sallama,a nan ne Ummi ta tsayar da ita tana tambayarta babu wani abu da suka ce mata suna buk'ata..?? Nan ta bawa Ummi'n amsa kamar yadda YASEER ya gaya mata
"Ehhh! Ummi Babban Yaya yace idan akwai abunda suke buk'atan zasu sanar dake..!"
Saboda Ummi ta hanata kiranta da wani ranki ya dad'e sai Ummi kamar yadda su Abir suke fad'a sab'anin sauran hadimanta,ta fad'a tana sunkuyar da kai k'asa.
"To babu damuwa..Zaki iya tafiya gida kema ki samu ki huta.."
Godiya tayiwa Ummi sannan ta mik'e tana shirin tafiya,har ta kusa kaiwa bakin k'ofa Ummi ta kira sunan ta,har cikin ranta sai da taji kiran dan yadda Ummi ta kirata sai da taji gabanta yayi mummunan fad'uwa,sai data daure sannan ta juyo tana saita kanta dan bata so kowa ya fahimci halin da take ciki
"Na'am Ummi.. Akwai wani abu da kike buk'ata nayi miki..??"
"A'a babu..Ina dai son ki dawo ne muyi magana yanzun.."
Cikin rashin kuzari ta juya har zuwa inda Ummi'n take ta nemi guri ta zauna nan a k'asa kan shimfid'a tana wasa da yatsun hannunta
"Uwar fada shin wani abu yana damunki ne..??"
Kanta a k'asa tayi shiru sannan ta bawa Ummi amsa da
"A'a Ummi babu komai.."
"A'a fa uwar fada,ki fad'a min gaskiya..Ko kuma dai su YASEER sunyi miki wani abu da kika je ba,dan nasan ba'a haka kika fita a nan ba.."
Saurin amsawa Ummi'n tayi tana cewa
"A'a'a..! Wollahi Ummi babu wani abu daya faru.."
Babu yadda Ummi bata yi da ita ba akan ta sanar mata amma ta dage itama kan babu komai,kan dole Ummi'n ta hak'ura ta sallameta tana binta da fatan Allah yasa abunda ta fad'a mata hakan yake,nan ta fita bayan ta sake yiwa Ummi sallama ta kama hanyarta ta komawa gida.
^^^^^
Suna yin parking direct YAZEED bai zarce ko ina ba sai tsohon apartment ensu,a baya YASEER ya biyo shi har zuwa side en nasu,nan a parlor ya iske shi ya kwanta saman doguwar kujera idanunsa a rufe alamun tunani,kusa da shi ya nemi guri ya zauna yana tab'a shi,banza YAZEED yayi masa duk da yaji abunda yayi,haka bai ko d'ago ba bare ya kalleshi,cikin nutsuwa YASEER ya shiga k'are masa kallo kafin yayi magana
"Broah.! Tashi let's talk!"
Ba tare da ya ko bud'e idonsa ba ya bashi amsa
"Just say i'm listening to you."
Sake kallonsa yayi kafin ya girgiza kai
"A'a ka dai tashin ina ganin zaifi..Dan maganar da za muyi bata buk'atan wasa.."
Da k'yar YAZEED ya iya mik'ewa ya zauna ba tare daya kalleshi ba
"Oh! I'm listening..!"
Sai daya sake d'an kallonsa sannan ya fara masa magana
"Broah...What is the reason why you have told me the story of this girl..??"
Saurin juyowa yayi ya kalleshi cikin rashin fahimtar inda maganar sa ta dosa
"Which girl are you talking about?"
A tak'aice YASEER ya bada amsa
"Ta gurin dinner nake nufi..!"
Sai daya ja numfashi kafin ya d'aga kafad'a sama yana fad'in
"Ban sani ba nima broah..! Amma dai abunda na sani shi ne,haka kawai ina jin ZUCIYATA tana ingizani naje gareta..bansan me yasa nake jin hakan ba,bayan banji hakan tun a karon farko ba sai yanzun.."
Kallonsa YASEER ya d'an yi cike da nutsuwa ya furta
"Do you love her...??"
Da sauri Yarima ya kalleshi yana tambayarsa
"What do you mean ??? Ni wai nake sonta..??"
Girgiza masa kai yayi yana lumshe idanunsa
"Eheenn! Kai d'in fa,if there's no room to eat a glass of tea..??? Matuk'ar ace ba sonta kake yi ba,ina ganin babu dalilin da zaisa kaji wannan yanayin a tare da kai.."
Shiru yayi yana sauraren YASEER dake zayyana masa jawabi,zuwa wani lokaci kuma ya d'an dafe gefen kansa yana ci gaba da magana
"Broah..! Shin haka So yake ne dama..??"
"K'warai kuwa.! your talking almost goes beyond all of your thoughts.but first you should pray and then start up and decide if you really love her,because i do not want u to do anything that would bring u to an endless life.back.."
Jinjina kai yayi kafin cikin sanyin murya ya furta
"Thank you, broah! With ur advice,in sha Allah kamar yadda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 63