Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya dad'a saceta wanda a k'arshe nan ta b'ingire ba tare data shiryawa yin hakan ba. Ko da asuba bayan tayi sallah da Inno ta tasheta bayan data idar da sallah,kasa komawa bacci tayi,haka ta zauna a gurin tana addu'o'i har rana ta hudo,nan ta mik'e ta gabatar da sallar nafila raka'a biyu sannan ta sake zama tana addu'ah game da al'amuran da suke faruwa a cikin gidan sarautar. (Tabbas wannan sallah tana da matuk'ar amfani saboda annabi (s.a.w) ya fad'a a hadith cewa:"duk wanda ya sallaci sallah raka'a biyu bayan b'illowar rana,ma'ana tun daga lokacin da yayi sallar asubah sai bai koma ya kwanta ba ya zauna yana ambaton ubangiji a gurin daya idar da sallar,da rana ta hudo kuma yayi sallah raka'a biyu,sai annabi (s.a.w) yace "duk wanda ya aikata kamar haka to kamar yayi aikin hajji da umrah ne tare da shi.." Bukhari da Muslim). Misalin k'arfe 7:30am ta fito daga d'aki cikin shirinta na tafiya makaranta jikinta duk a sanyaye,kula da hakan da Inno tayi yasa ta tsaidata tana fad'in "Y'ar nan ince dai lafiya koh? Naga duk jikinki a sake kamar baki da lafiya,shin akwai wani abu da yake faruwa da ba zaki iya sanar min ba a matsayina na mahaifiyarki..?" Kai jeeddah ta girgiza mata tana cewa "Babu komai inno haka nan dai nake jin jikina.." Karantar damuwar da inno tayi akan fuskarta yasa ta fad'in "Nasan haka bai tab'a faruwa ba jeeddatu amma me yasa yau kike k'ok'arin b'illo da wannan sabuwar hanyar...Me yasa za kiyi haka..? Kin sani sa damuwa a rai yana haifar da ciwo,shin bakya tsoron wani abu ya sameki..? Me kike tunani ni kuma zai same ni idan wani abu ya faru dake..?" Yadda Inno take mata maganar da damuwa a fuskarta ya dad'a sawa jikinta yayi sanyi,har ta ji ba zata iya b'oye mata abunda ke k'asan zuciyarta ba,bud'e baki tayi da niyyar zata fad'awa Inno duk abunda ke cikin ranta sai kuma tayi shiru tana sunkuyar da kai k'asa "Shi kenan Jeeddah tashi ki tafi makarantarki fatan Allah ya yaye miki duk wata damuwa dake ranki,Allah ya kiyaye min ke ya kareki daga sharrin dukkan abun halitta.." A hankali ta d'ago ta kalleta jikinta a sanyaye sannan ta bud'e baki tana shirin yin magana dan a wannan lokacin zuciyarta ta gama yanke sanarwa da inno,maganar yarima Yaseer ce ta dawo mata inda yake cewa _"Na aminta dake shi yasa har na tsaya muka fara maganar,sai dai jan kunnen da zan miki shi ne ina so wannan maganar ya zama sirri tsakanina da ke,ban amince ko da mahaifiyarki ne kuyi maganar ba,sai dai ko abunda ya shafi bincike wajen gano masu hannu a cikin wannan matsalar kin fahimta..?"_ "Aaaa! Uhmm! Inno dama fa jiya ne da dare ina bacci nayi mummunan mafarki shi yasa yau duk nake jin jikina kamar an yi min duka,sam bana jin dad'in jikina..." "Ayyyahhh! Sannu kinji,ni dai nasan ba haka kike ba,shi yasa nayi mamaki ko da naga baki cemin komai ba,amma duk da haka na gwammace na tambaya dan ban sani ba ko bakya son sanar dani ne ko kuma wani abu daban ke damunki." "Haba mana Innota dan Allah ki daina fad'ar haka,har cikin raina nake jin rashin dad'i idan naji kina fad'in irin wannan maganar,ko kad'an babu wani abu da zaisa ni canjawa daga yadda nake,ke mahaifiyata ce na sani babu wani abu da zai sa na b'oye miki duk wani abu dake damuna,bazan tab'a iya yin hakan ba Inno nayi miki alk'awarin sanar dake duk wata damuwa ta a duk lokacin da buk'atar hakan ya taso.." Rik'o hannunta Inno tayi tana mata murmushi kafin ta furta "Na gamsu da maganarki jeeddatuna na san ki na kuma san halinki,duk wani abu da zaki iya da wanda baza ki iya ba na sanshi,na aminta da duk wata magana tak'i,saboda nasan ke en mai cika alk'awarin data d'auka ce komai tsanin da zata fuskanta akan alk'awarin data yi,Allah yayi miki albarka,na tabbatar ke en 'yace ta gari da iyaye da dama zasu yi fatan samun kamarki.." Murmushi ta saki tana sake k'ank'ame hannun Inno kafin ta furta "Yawwa Inno mene ne ma'anar mutum yayi mafarki da wani mutumin ne...? Misali ka ganshi a cikin wani hali kamar na neman taimako haka ko ka ganshi a cikin rami..? Shin hakan me yake nufi..?" Shiru Inno tayi tana kallonta kafin ta d'anyi ajiyar zuciya tana fad'in "Gaskiya jeeddatu idan nace miki ga ma'anar hakan nayi miki k'arya dan kuwa ni bani da sani akan wannan,sai dai abunda nake hasashe wata k'ila hakan ya zama sharrin mafarki ne kawai ko kuma akwai abunda mutum yasa a ransa da zai sashi yin wannan mafarkin,amma koma mene ne hakan yake nufi,shin kinyi wani mafarki ne makamancin wannan..?" Girgiza mata kai jeeddah tayi,idon Inno akanta ta sake cewa "Shin yadda kikamin wannan maganar irin haka ne ya faru a mafarkin naki..?" Nanma kai ta d'aga,sannan ta shiga zayyanawa inno labarin mafarkin nata,sai dai ta b'oye sunan wanda ta gani a cikin mafarkin,jimm Inno tayi tana tunani zuwa d'an wani lokaci ta d'ago kanta ta kalli jeeddah "Kada ki damu kinji jeeddatuna in sha Allah anjima kad'an zan tambaya miki malam liman la'allah shi ya san ma'anar mafarkin naki,naga shi en Allah ya bashi wannan baiwar ta sanin fassarar mafarki..amma yanzun kiyi maza ki tafi makaranta idan kin dawo ko bamu je tare ba ni sai naje na ji me zai ce ko..?" "To Inno bari na tafi naga lokaci har yana neman k'uremin a gida.." Daga haka ta mik'e ta yiwa Inno sallama,tana shirin fita sai ga Aina'u nan kamar an cillota tana rangad'a sallama,kallonta duka suka tsaya yi kafin suka amsa mata,inno ta gaisar sannan ta kalli jeeddah cikin saurin baki tana cewa "Ke tun d'azu sai jiranki nake amma shiru kink'i fitowa,gashi har mun kusa makara.." "To kuyi maza dai ku wuce kuna cewa kun kusa makara kuma kuna nan zaku tsaya mad'e.." Sallama sukamata daga haka suka yi saurin ficewa suna dariya suka nufi makarantar,banda watsa k'afa babu abunda suke yi cikin sauri,a haka har suka shigo harabar primary,koda suka ga yadda d'alibai y'an uwansu suke sauri wasu har da gudu yasa su k'ara sauri suka ratsa y'ar hanyar da zata sada su da ainihin cikin inda secondary en take,tun daga nesa suka fara hango dandazon d'aliban da aka tare a makara,kallon juna suka yi kafin ko wacce cikin su ta d'auke kanta,jan k'afa suka koma yi kamar wasu marasa lafiya dan gaba d'ayansu basa k'aunar duka,a haka har suka isa cikin get en. Bayan an gama musu horon daya dace aka sallame su,daga nan duka suka nufi ajujuwansu,lokacin da suka shiga aji tuni har malamin Business studies ya shiga kuma har ya fara karatu,a haka dai suka zauna a daddafe suka maida hankalinsu a kan bayanin da malamin yake,tun basa ganewa har kuma suka fara fahimtar abunda yake darasin nasa akai,yinin ranar haka ya shud'e musu a cikin makaranta,misalin karfe 1:30pm aka tashe su lokacin kuwa duk jikinsu ya gama saki dan zuwa makaranta sai da juriya ba kowa ke iya hak'urin zama sama da awa biyar ba a guri guda,a line gidan su suka yi sallama ko wacce ta shige gida da fad'in "sai anjima" saboda sun san zasu had'u da juna a islamiyya. Tun bayan data dawo ta shiga d'aki ta cire kayan makarantarta ta fito da niyyan d'aura alwala,sai data yi sallah kafin ta fito ta zaga bayan gida ta watsawa jikin ta ruwa,sannan ta koma d'aki ta kwanta tana y'an tunane²nta,tun bayan data bar gida sai yanzun ne tunanin mafarkinta ya dawo mata,shiru tayi tana nazari,lokacin ne kuma Inno ta shigo gidan tana rangad'a sallama,saurin dirowa jeeddah tayi daga saman gadon da take ta fito cikin y'ar rumfar da suke zama shan iska tana yiwa Inno sannu da zuwa,dan dama tun data dawo bata tarar da inno a gida ba "Yawwa y'an nan ashe kin dawo tuni..?" Inno ta amsa mata tana zama saman y'ar tabarmar da jeeddah ta shimfid'a mata "A'a ban jima sosai ba da dawowa ba,na dai yi sallah yanzun na d'an kwanta ko zan iya yin bacci,sai kuma naji kin shigo.." "Ayyah to kije ki samu ko baccin ne kiyi zuwa anjima idan kin tashi sai na miki bayanin abunda malam liman yace min game da labarin mafarkin ki.." Har ta yunk'ura zata tashi taji baza ta iya hak'urin jira har zuwa anjima ba,komawa tayi saurin yi ta zauna tana sunkuyar da kai,a hankali inno ta kalleta tayi murmushi dan ta fahimci abunda ya hanata tafiyar baya rasa nasaba da maganar da tayi yanzun,kamar bazata sanar mata ba sai kuma ta gyara zama tana fad'in "Kamar yadda na shaida miki d'azun da safe idan Allah ya kaimu zanje gurin malam liman na miki tambaya game da mafarkinki,to Allah yasa naje gurinsa kamar yadda na alk'awarta miki,yanzun hakama daga can nake kuma yanin bayani gamsashshe akan hakan." Shirun da taji inno ta d'an yi yasa ta d'agowa a hankali ta kalleta zuciyarta fal da son jin me zata fad'a mata daya shafi mafarkin nata,jin shirun yana neman yin yawa yasa zuciyarta ta fara bata shawaran ta tambayi inno kawai dan ta damu taji me zata fad'a mata,har ta bud'e baki zata yi magana,kalaman dake fitowa daga bakin inno suka sata tayi shiru tana kasa kunne "Bisa ga yadda muka yi da malam yace dani,mafarki wani lokacin irin wannan yakan zama gaskiya,a mafi yawan lokaci kuma wani yakan zama ba gaskiya bane sharrin mafarki ne kawai,sai dai wani lokacin yin mafarki da wani wanda ka sani ka ganshi cikin wahala har yana neman taimako kamar dai irin wannan mafarkin da kika yi,yakan rikid'a ya zama gaske ne wannan abun da ka gani a cikin baccinkia,kuma hakan na faruwa a sakamakon wata k'ulalliya da aka yiwa mutum har abunda ba'a so ya same shi,haka nan kamar yadda yace min yin mafarki da mutum a cikin rami wannan mafarkin yana nufin makirci ne aka shiryawa shi wannan mutumin,wanda idan har an jajirce da addu'ah Allah zai warware wannan makircin da yake neman afkawa cikinsa ko kuma ya riga ya afka.." Dogon numfashi suka ajiye a tare kafin inno ta kalli jeeddah da jikinta ya sake yin laushi tana tambayarta "Jeeddatuna shin mafarkin nan naki ko zaki iya gayamin waye kika gani cikinsa yana neman taimakonki..? Tunda kika sanarmin wannan al'amarin da kuma bayanin da malam yamin hankalina ya gaza kwanciya..kiyimin bayani ko hankalinsa zai kwanta.." Shiru tayi tana tunanin ta sanar da inno ko kuwa a'a? Har ta d'ago zata yi magana alk'awarin data yiwa yarima Yaseer ya dawo mata,da sauri ta girgiza kai fuskarta da d'an damuwa duk da tana son b'oyewa inno bayyanar hakan,kawai sai ta tsinci kanta da cewa "Ni kaina inno ban san waye shi ba,tun dana farka nake ta son gano fuskarsa amma na kasa,na kasa bambance fuskar ko waye na gani a baccina.." "Ayyahh!² Dama ai wani lokaci akan samu irin wannan matsalar kayi mafarki bayan ka tashi ka manta ko waye ka gani.." Ita dai jeeddah shiru tayi bata sake cewa komai ba,daga hakama sai ta mik'e ta bar wajen,d'aki ta koma ta kwanta tana fad'in "Kiyi min afuwa ya mahaifiyata,nasan duk lokacin da kika san wannan maganar,baza kiji dad'i ba saboda b'oye miki gaskiya da nayi,amma kiyi min afuwa babu yadda zanyi ne shi yasa,ya zama dole saina yi hakan ne,amma soon zan sanar dake in sha Allah.." Daga haka ta yada hak'ark'arinta ta kanta da niyyan bacci sai dai ina sam baccin ya gagareta,tunanin ta ne ya fad'a kan bak'uwarsu ta islamiyya,saurin mik'ewa tayi ta zauna tana saka yatsanta a baki,ta jima a haka tana tunanin yadda zata yi ta shiga jikin Aisha don samun wasu bayanai daga gareta,da wannan tunanin ta kwanta tana sakin murmushi dan ta gama tabbatarwa ranta sai ta cika wannan burin,sai dai yadda zata fara shiga jikin nata ta rasa yadda ya kamata tayi,tunanin tane ya bata shin ta fara sanarwa yarima ne ko kuwa ta bari sai ta samo hanyar da zata yi hakan? ko da tayi wannan tunanin shi enma tsayawa tayi tana yin shiru dan bata san ta wace hanya ya kamata tabi ba wajen ganin nasa tunda shi yace da ita duk lokacin da buk'atar su had'u ta taso zai neme ta,shin ita to ta wace hanyar zata bi dan ta ganshi suyi maganar..? Wannan tunanin shi ya dakushe mata duk wani zumud'i na son ta fad'a masa abunda take ganin ya kamata su fara yi da hanyan da take ganin zai kaisu ga samun nasara,yinin ranar haka ta yishi tana tunani da neman hanyar da zata b'ille musu. Fitowarta daga gida bayan sallar Maghreb ta lek'a gidan su Aina'u ta biya mata zuwa makaranta,sannan suka kama hanyar islamiyyan nasu,su suka fara zuwa dan haka ko da suka ga ajin babu kowa sai suka tafi dan tafiya d'auko tabarman ajin suka yi shimfid'a sannan suka zauna suna d'an hira kafin sauran su iso su fara bita,kimanin mintuna arba'in da zuwansu Aisha ta shigo da sallama,bayan sun gaisa sai ta samu guri kusa dasu ta zauna tana musu murmushi,mik'awa jeeddah hannu tayi tana fad'in "Suna na Aisha kuma ni bak'uwa ce,shin zamu iya zama k'awaye..?" Wani kallo jeeddah tayi mata har bata san lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba,a hankali ta saita kanta sannan ta mik'a mata hannu itama tana cewa "Babu matsala,suna na jeeddah..!" Murmushi Aisha ta sake yi mata sannan ta juya ga Aina'u suka yi hannu,haka suka yi ta y'an hirarrakinsu duk da jeeddah ba sosai take magana ba,yawancin tunani duk yafi d'auke mata hankali,juyawa Aisha tayi ta kalli Aina'u tana d'an murmushi "Wai ita jeeddah bata magana ne sosai naga duk tayi shiru,ko dai bata hira da bak'i ne..?" "Laaa! Ba haka bane ai kuwa tana hira sosai dan dai kawai ko baku saba bane yanzun amma ki bata nan da kwana biyu zaki ga ta canja..nima yau duk tunanin da nake kenan na rasa gane me yake damunta.." Dai² lokacin su Asabe da y'an tawagarta suka shigo,ko da suka hango Aisha a kusa da su nan aka fara jifanau da maganganu marasa dad'i,amma sam sunk'i tankawa,ita kuwa jeeddah kanta ma ta d'auke ana sakin murmushin mugunta ga su Asabe ba tare data tanka musu ba,kallonta ta mayar kan Aina'u tana mata inkiya da su fara bita,haka ranar har aka tashi su Asabe suna yar musu magana saboda ganin Aisha a tare da su,ko da suka kamo hanyar dawowa gida babu mai magana,har suka yi sallama Aina'u ta shiga gida itama jeeddah ta shige nasu,a zauren gidan wani Yaro ya biyo bayanta yana k'wala mata kira,saurin dakatawa tayi a dai² k'ofar shigewa tana kallonsa,haki yake ta yi sai daya saita nutsuwarsa sannan ya fara magana "Wani ne yace na tsaida ke gashi can a waje.." Ido ta zare waje tana dafe k'irji "Kuma ni yace maka ka tsayar..?" Kai ya girgiza mata "Kai bani bace tafi kace baka ganni ba.." Kafin ta k'ara yin wata magana tuni har ya shigo cikin zauren fuskarsa a rufe kamar wani buzu...duk ya nad'e ta babu abunda ake gani illa k'wayar idanunsa,alama yayiwa yaron da hannu akan ya fita,da gudu kuwa yaron ya fice ya barsu nan,ita kuwa jeeddah banda kallonsa babu abunda take dan duk a tsorace take da ganin wannan mutumin da yak'i bayyana fuskarsa gare ta. Cikin inda² ta fara tambaya "Dan Allah waye kai...? Ni ban sanka ba kuma tsai dani...ina gudun kada a ganni a gida..zaka jayomin duka,ni dai kawai kayi hak'uri ka tafi dan Allah.." Kallonta yaci gaba dayi yak'i cewa komai,a hankali kuma ya d'age mayafin daya rufe fuskarsa da shi,jeeddah ko data gama gajiya da magiya kawai saita d'ago a fusace ta kalleshi kawai ta saki k'wafar jin haushi,har ta d'aga k'afa tana shirin barin gurin dan haushin shirun daya mata,taji ya furta "Daka ta kada kiyi gaggawa..." Yana fadin haka ya d'age mayafin daya rufe fuskarsa,ko da taga fuskar wanda bata tab'a tunani ba ta bayyana tuni ta sank'ame a tsaye tsoro duk ya cika mata zuciya....... _DON'T FORGET TO VOTE ME ON WATTPAD @jeeddahmu898._ #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *Pg 5.* ^^^^^^^^ Wani murmushi ya sakar mata dan yadda yaga ta firgita da ganinsa,ita kuwa gareta ko data ganshi tuni ta nemi zubewa a k'asa,saurin dakatar da ita yayi yana kallon hanyar shigowa cikin zauren gidan nasu "Kada ki kuskura ki b'ata mana shiri.." Ya fad'a cikin d'aga harshe,da sauri ta saita nutsuwarta,saurin mayar da mayafin yayi ya rufe fuskarsa kana ya fara da fad'in "Nasan za kiyi mamakin zuwa na,amma hakan ba abunda za'ayi mamaki akansa bane,a yau na samu labarin wannan yarinyar da suka kai k'arar yazeed suna nan a cikin gidan nan,sai dai ban san ainihin wane guri suke zaune ba.." Sassanyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta bud'e baki tana cewa "Ni kaina Yallab'ai nasan da wannan,dan ni har yarinyar ma na gani.." "Kin ganta..? A ina kenan?" Sai data sake sakin murmushi sannan a hankali ta furta "Yallab'ai a islamiyyar mu na ganta kuma ajinmu d'aya da ita yanzun haka." Mamaki ne ya kama Yaseer dan baiyi zaton hakan zata faru ba "Shin kin tabbatar itan kika gani da gaske ko kuwa dai wata ce daban mai kama da ita..?" "Ranka shi dad'e itace na tabbatar babu haufi a cikin abunda na gani kuma na tabbatar.." Kallonta ya sake yi yana kallon hanya cikin yanayin jin haushi ya furta "Kinga daga yau ina so ki cirewa bakinki fad'ar Yallab'ai ko ranka shi dad'e ennan,idan har kuma ba so kike a gano shirin da muke yiba,dole ne wasu abubuwa sai sun canja a tsakanin mu kin fahimta ko..?" Kai ta girgiza kana ta furta "ayi min afuwa yallab'...." "Keeeeee! Haba me yasa baza ki kiyaye bane,ana fad'a miki abu amma sai dad'a k'ok'arin maimaitawa kike..? Ki sani kuma ki kiyaye kuskure d'aya idan har muka yi sakaci zai iya rusa duk wata dama da zamu samu,dole ne ko zaki iya ko baza ki iya ba dole ne sai kin cirewa rankin fad'ar wannan maganar,sannan abu na gaba tunda kince kinga yarinyar a ajinku,abunda ya kamata kiyi yanzun shi ne kisan ta hanyar da za kibi ki gano mana gaskiyar mene alak'arsu da yarima da har ya janyo sun masa k'azafi,duk da nasan ko wane lokaci tare muke da shi amma hakan bazai sa nayi shaidarsa a nan ba,halayensa masu kyau ne haka tsarin rayuwarsa duka bashi da matsala ko kad'an amma ina son gano dalilin da yasa suka shafa masa wannan bak'in paint en..." "An gama babban Yaya in sha Allah duk abunda kace zanyi k'ok'ari akansa,zanyi k'ok'arin ganowa harma da wanda baka ceba,to amma babban Yaya idan na samu labarin daya dace na sanar da kai ban san ya zanyi na fad'a maka ba akan lokaci.." Wani murmushi ya saki jin sunan data rad'a masa,kafin ya juya zai bar wajen,har yaje bakin k'ofa yana niyyan fita ya juyo ya kalleta "Zan sanar dake hanyar daya kamata kibi wajen sanar dani,ki bar wannan a hannuna idan na shirya zan sanar dake komai dangane da shirina..." Yana fad'ar haka yasa kai ya fice a zauren gidan nasu,ta d'an jima tsaye a wajen kafin ta juya ta shige zuwa ciki da sallamarta,bata tarar da inno a rumfaba dan haka kawai sai ta nufi cikin d'aki, tana jiyo sanda Inno ta mata gyaran murya daga bayan gida,shigarta babu jimawa ta ajiye jakar litattafanta sannan ta kabbara sallar isha'a,lokacin data idar nan ta mik'e ta sake gabatar da raka'a biyu ta jima tana rok'on Allah akan ya basu nasara kan abunda suka sa a gaba,kamar bazata k'are ba har zuwa tsayin lokaci sannan ta mik'e ta nad'e abun sallar ta fita gurin Inno a tsakar gida zuciyarta har lokacin tana mamakin yadda akai yarima yaseer ya iya shigar b'adda kama haka... Kwanaki biyu tsakanin zuwan yarima Yaseer gurinta,tana zaune a islamiyya ita kad'ai a ajinsu,Aisha ta shigo cikin ajin kamar an cillota,ranar kuwa Aina'u bata zoba sai ita kad'ai,yadda ta ganta a firgice yasa ta kalleta tana fad'in "Aisha lafiya kike duk a firgice...? Me yake damunki..?" A jikinta Aishar ta zauna,yadda ta k'ank'ameta kamar zata tsagata ta shiga tsakiya,yasa ta rik'o hannunta tana kallonta,cikin lafazin kwantarwa da mutum hankali ta fara magana "Ki kwantar da hanakalinki Aisha babu abunda zai sameki fa,duk kin shigo a haka nima har kinsa ni jin fad'uwar gaba,dan Allah ki fad'a min me yake faruwa na ganki a haka.." K'ofa kawai Aishar ke nunawa jeeddah bakinta sai motsi yake amma ta kasa fad'ar komai,sakinta jeeddah tayi ta mik'e ta fita,duba harabar wajen ta shiga yi amma sam bata ga komai ba,har kusan fita tayi daga line amma bata ga kowa ba,dawowa tayi ta tarar da Aisha a irin halin data barta,sai data girgiza kai saboda takaici sannan ta shiga cikin gidan da suke karatu a soron,ruwa ta rok'i a sammata zata sha,ko da aka bata nan ta fito soron ta kawowa Aishar sanda ta sha nutsuwa ta dawo mata sannan jeeddah ta kalleta "Wai ni dan Allah mene kika gani ya firgitaki ne haka..?" Uwar ajiyar zuciya ta saki kafin ta nisa tana sake kallon k'ofar shigowa kamar ance mata zata ga wani a wajen "Wollahi jeeddah wani mahaukaci ne yake ta bina tunda na taho,sai tsorata ni yake wai naje fada na fad'i gaskiya,wancan ranar k'arya nake duk abunda na fad'a, kuma yace idan ba haka ba shi ne ajalina...!" Ta k'arasa tana fashewa da kuka,zaro ido Jeeddah tayi waje tana kallonta had'e da dafe baki "Mahaukaci...! kuma a cikin gidan nan yake..?" "Ehh! Wollahi kuma ni da idona ma naganshi,ina jin tsoron sa sosai dan Allah ki rakani ni dai na koma gida.." "Kai haba mukam nan bamu da wani mahaukaci sai dai ko fatalwa kika yi gamo da ita,amma ni ban tab'a gani ko jin labarin akwai mahaukaci a gidan nan ba,ina ga gaskiya sai dai ko fatalwowin da ake cewa ana gani na can wajen K'OFAR FATALWA sune suka kawo miki ziyara,Allah yasa kina da rabon ganinsu shi yasa kuka had'u.." Sake tsurewa Aisha tayi jin labarin fatalwa daga bakin jeeddah,tuni hawaye ya k'ara gudu yana bin kumatunta "Dan Allah jeeddah ki rakani na koma gida,wollahi ina jin tsoronta,bazan iya zama ba yau,dan Allah kinji.."

Chapter 4 of 63