tana fadin
"Afuwaaan..! Ranka ya dade nasa ku jira...!"
Juyawa suka yi a tare duka suka bi gurin da take tsaye da kallo,wata mahauciyar fad'uwa gaban YAZEED yayi sanda ya kalleta da har ya janyo ya runtse idonsa,sake tsuke fuska yayi ba tare daya sake ko da kallonta gefen da take ba yayi k'wafa,sai daya d'auki a k'alla mintuna biyar kafin yayi yunk'urin fitowa yana kallon gurin da YASEER yake da murmushi a fuskarsa,juyawa yayi gareta yana jinjina kai da sakin murmushin k'arfin hali kafin ya shiga kallonta from head to toe yana squeezing face.........................
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Tabbas..! K'auna a cikin jini take,haka nan mutum vai isa yasan adadin masoyamsa ba,sanin wannan sai Allah shi kad'ai,k'aunar da kuke nuna min na tabbata bazai tab'a bani damar aikata abunda nayi niyya ba koda kuwa hakan na nufin abubuwa da dama,tun daga jiya dana sanar zan tafi hutu sai zuwa bayan sallah zan ci gaba da rubutu,sak'onnin ku suka hanani sakat,ta ko ina abu d'aya nake cin karo da shi bakwa so na tafi,na tabbata matuk'ar na dage akan saina tafi babu adalci a cikin yin hakan,tunda ba wani uzuri ne zaisa na tafinba sai don ra'ayin kaina,wannan yasa naga dacewar hak'ura da tafiyar da nayi niyya a yanzun,sai dai ku sani ina jaddada muku kwanakin da suka rage manna kafin azumi basu da yawa a kullum suna sake gabatowa ne,ko da ace ban tafi yanzun ba kamar yadda na fad'a lokaci zai zo da dole haka zan hak'ura na ajiye rubutun sai zuwa bayan sallah in sha Allah,wannan alk'awari ne nayi muku ni da ku duka zamu ci gaba da tafiya kamar yadda muka faro da yardar Allah, hutu ne na soke shi in sha Allah saboda haka kuji dad'in ku masoya...Hawwa tana jinjina muku da irin yadda kuke nuna k'auna gareta.#tag masoya na.*
*Pg 25.*
^^^^^^^^
Wani uban kallo yake binta dashi,yayin da zuciyarsa ta lula duniyar tunani cike da son gano inda ya tab'a sanin mai wannan kamannin,sosai ya shiga takura k'wak'walwarsa duk akan son sai ta tunatar da shi abunda yake so,duk iya yadda zuciyarsa da tunaninsa suka tafi akan tunanin iya adadin yadda yake sake takura da matsawa ransa kenan da son lallai saiya tuna ainihin inda suka tab'a gamuwa da itan,ya d'auki lokaci mai tsayi yana aikin abu d'aya,duk wata mu'amalar daya tab'a yi rayuwarsa ta baya da yasan ya tab'a shiga harkar wata nace sai daya kawota aransa,idan ya tuna wannan yaga ba shi bane sai ya girgiza kai yana sake runtse ido kamar wanda akace idan ya rufe en zauga komai a hakka,ya d'auki lokaci mai tsayi kafin cikin wani irin firgitaccen yanayi ya d'ago idanunsa da suka soma rikid'ewa zuwa zallar b'acin rai mai tattare da tsantsar k'iyayya yana k'are mata kallo cikin wani irin kakkausar murya da ko a labari baza kayi tunanin yana da ita ba ko zai iya magana da ita a wani lokacin ya furta
"Keeeeeeeeeeeeee...???"
Kallonsa take da mamaki jin yadda yayi maganar cikin tsawa²,fuska ta shiga yatsinawa tana ci gaba da kallonsa ba tare data nuna tsoro ba,ba Aisha kad'ai ba hatta da YASEER sai da abun ya bashi mamaki musamman kuma da yayi saurin zagayowa inda YAZEED en yake ya kalli fuskarsa wacce tuni ta gama rinewa zuwa jaa mai cike da tabbatarwa lallai ransa a matuk'ar b'ace yake,hannunsa YASEER ya rik'o yana kallonsa da tambayarsa
"Broahh! Are u okay..??"
"Take me out of here.."
Abunda kad'ai ya iya fitowa daga bakinsa kenan yana sake binta da kallon tsana
"Haba mana broahh why so soon kace mu tafi bayan baka yi abunda ya kawo ka ba..Me kenan zaka ce da maimartaba idan ya tambaya.?"
"Are u deaf..?? I said take me home...!"
Cikin tsawa yayiwa YASEER maganar wanda shi kansa daya sake kallon yanayin da YAZEED en yake ciki sai daya firgita
"Ok..Ok.we can trek..!"
A fusace YAZEED ya bud'e motan ya shiga ba tare daya jira YASEER ba had'e da banging k'ofan sounded,Allah yaso a lokacin ba shi zai yi driven enba dan na tabbata kam matuk'ar shi zai maidasu gida zasu iya watsewa a kwalta,suna tafiya banda huci da tsabar b'acin rai babu abunda YAZEED yake furzarwa a time en,cap en dake kansa ya ture baya yana dafe forehead nasa da hannu d'aya,ganin hakan bai masa ba ya cireta duka yayi cilli da ita zuwa back seat,kallonsa YASEER yayi yana jinjina kai
"Wai kai me yake damunka nema lokaci guda ka birkice kamar ba kai ba,what's going wrong..??"
Jajayen idanunsa ya d'ago da suka koma kinda furnace yana kallonsa,cikin hasala da tunzura ya fara magana
"Kana nufin kace baka gane wannan yarinyar ba..??"
"No..I can't think so na kalleta ma ni duka bare na shaida ta.."
Uban tsaki ya jaa mai sauti yana girgiza kai,jikinsa banda prom babu abunda yake kamar ana kad'a masa mazari
"U should considered whichever come across as easy as u can..Damuwa da duk wani b'acin rai duk ba naka bane yanzun domin kuwa idan ma kace hakan za kayi b'acin rai ne za kayi ta ganuwa da shi ba adadi.."
"I can't afford this any more man..it's all aversions...! Me yasa sai ni kad'ai..?? Nayiwa wani laifi ne da abubuwa suke faruwa kamar haka a kaina..??"
"It's Ok man..Amma kai a ina ka san yarinyar..kamin bayani mana..?"
"Kayi tunanin abunda ya faru (10) years back maybe ka tuna.."
Cikin sauri YASEER ya dakatar da motan cike da firgici ya waiwayo ga YAZEED idanunsa a waje
"Me kake son cewa..?? Kana nufin wai dama itane yarinyar da maimartaba yake son ka aura en..??"
Da ka ya iya amsa masa yana runtse idanunsa da yake jinsu kamar an sa masa chilly,YASEER kuwa banda gyad'a kai da binsa da kallo babu abunda yake cike da tsantsar mamakin yadda akayi maimartaba zai ce YAZEED en ya aureta,zuciyar sa da gangar jikinsa cike da tausayi ya sake kallon YAZEED kamar zai masa kuka saboda halin daya ganshi a ciki,lokaci guda duk ya sauya kamanni kamar ba shiba,zuciyar sa da tunanuka iri daban² hakka dai ya daure ya yiwa motan key suka d'auki hanyan da zata maidasu zuwa ROYAL PALACE kowannensu zuciya da gangar jiki babu dad'i.
^^^^^
Sanda Aisha ta tabbar sun tafi ta juya da nufin komawa gida tana tafe tana yatsina fuska cike da jin takaicin abunda ya faru tsakaninta da YAZEED,da Ladidi ta fara had'uwa tun kafin ta kaiga isa cikin gidan kasancewar ranar Adda bata gida yasa sai su biyun kawai,da shigowarta ladidi ta nufota tana washe baki da son yin tambaya
"Kai y'ar amana wai har ya tafi...??? Ince dai ko babu wani abu daya faru..?? Ba dai shirmen naki kika buga ba ya gano shirin mu ko..??"
Kallonta Aisha tayi tana sakin baki da K'ik'k'ifta ido irin na rashin gaskiya kafin ta bata amsa tana cuna baki gaba
"Nifa baba babu abunda nayi..Kawai dai sun tafi.."
Cikin masifa Ladidi ta zaro ido tana fad'in
"Wollahi k'arya kike,shegiya barbad'ad'd'iya, dan uwarki shi ne zaki janyo mana abunda zamu rasa damar dana jima ina tanadi,ai wollahi dama nasan ba har zuciyarka kika amsa niba tun farko,shegiya muguwa bak'ar munafuka,ai kuwa yau zaki gane kurenki,sai kin san ni kika yaudara wollahi..."
'Dan kwalinta had'e da gashin kanta ta dank'a cike da b'acin rai tana huci
"Shegiya bak'ar munafuka dama ai hausawa na fad'a 'kaji tsoron sharrin wanda ka kyautatawa' banda ma ni en dama waye zai iya dake..?? Ai ko iyayen da suka haifeki da ace ba'a satoki daga gurinsu ba na tabbata ko su kansu zuwa yanzun sun jima da yar dake,algunguma..!"
Duk da yadda take jin zafin rik'on gashinta da ladidi tayi mata hakan bai hanata d'aga idonta dake cike taf da hawaye tana kallonta da mamaki ba
"Baba kika ce aka sace ni..??? Kenan dama ba iyayena suka yar dani ba..?? Dan Allah kimin bayanin abunda ya faru..su waye iyayena.??"
Harara ta zabga mata kafin ta tuntsire da mahaukaciyar dariya tana nuna Aisha'n
"K'warai kuwa..! Ke da kina tunanin abunda na fad'a a baya haka yake..?? Ai ni nan da kika gani ko aljani bare gayamin canja magana ba,duk abunda na fad'a a baya ko kad'an ba haka yake ba,duka wannan nina shirya shi,kawai na fad'a miki ne saboda duk abunda zan saki kada ki yimin musu amma tunda ke tsintacciyar mage ce sai kika nunamin bakinku na y'ay'an haram.."
Kuka sosai mai cin rai Aisha ta fara,ta d'auki tsawon lokaci tana rera kukan kafin ta d'ago kanta da idanunta suka koma kamar an tsomasu a mai tana kallon ladidi zuciyar cike da duhu saboda jin wannan labarin tana kallon Ladidi
"Shi kenan tunda har kin fad'a min ainihin labarin yau,amma ina rik'on ki da girman Allah daki tausayawa rayuwata ki sanar dani inda zan samu iyayena.."
Dariya Ladidi ta sake fashewa da ita kafin ta tsagaita tana kallon Aishar tana munata da hannu
"Kina son sanin inda iyayenki suke..??"
Cikin sauri ta shiga d'aga kai idanunta na tsiyayar da hawaye
"Zan sanar dake..! Amma da sharad'i..!"
"Na yarda wollahi da duk sharad'in da zaki fad'a,na amince zanyi komai matuk'ar zaki sanar dani inda suke.."
"Hhhh! Da kyau y'an mata,,,sai dai ba zan tab'a fad'a miki yanzun ba matuk'ar baki amsawa duk abunda nace kiyi ba..!"
"Na amince ni dai kome zaki sani zanyi indai hakan zaisa ki kaini naga mahaifana.."
"Bravo alaik..Na tabbata a yanzun duk abunda nace kiyi baza ki tab'a min shirme ba,tunda kina buk'atan sanin inda mahaifanki suke..daga yanzun duk abunda nace shi za kiyi,babu ke babu yin kuskure,idan kuma har kika sake kika sab'a a cikin wani abu ki tabbata har abada bazaki tab'a sanin inda suke ba.."
Kai take ta gyad'awa alamun ta amince hawaye na sakkowa a fuskarta,jinjina kai Ladidi tayi kafin ta kalleta tana mata alamar ta goge fuskarta,da sauri ta shiga goge hawayen ta tana sakin ajiyan zuciya akai²
"Maza ki kiramin hajiya a waya yanzun ki bani muyi magana da ita..!"
Tun kafin ta k'arasa tuni har Aisha'n ta kirata tana mik'a mata wayan,fuska a d'aure ta karb'a sannan ta sata a kunnenta tana yin gyaran murya,cikin yanayin jimami ta bud'e baki murya na rawa ta fara magana harda hawayen munafurci
"Hello..! Hajiya,ehh yazo amma ko gaisuwa bai jira sunyi ba ya tafi,gaskiya hajiya ni ina ganin akwai matsala,gara tun farko kawai mu hak'ura da wannan al'amarin,na tabbata tunda abun ya fara da haka bamu san inda abun zai jeba,tun kafin zumunci yazo ya wargaje gara kawai mu hak'ura kada gaba tazo ana jin kunyar juna.."
Daga can gefen hajiya ta fara magana
"Wani abu ya sake faruwa ne..?? Ki min bayani mana ladidi yadda zan fuskanta..ai tsayawa b'oyewa ba naki bane ki sanar dani komai kada ki wani b'oye min.."
Ko da jin haka da ladidi tayi an bata dama nan ta zage ta fara gindayawa hajiya k'arairayinta ta zayyana mata duk abunda ranta ya kawo mat,ba tare da bincike ko tuntub'ar shi kansa YAZEED enba hajiya ta hau kai ta zauna,tunda suka gama wayan take ta faman numfarfashi kamar wacce tayi gasar gudu,ladidi kuwa koda taji yadda hajiyan ta tsaya sauraren ta tsabar iya sharri nata har da sheshshek'ar kuka ita a dole tana cikin jimanin abunda ya faru,hak'uri hajiyan tayita bata kafin ta bata tabbacin abunda ta shirya sai ya tabbata,aure ne babu fashi ko YAZEED naso ko baya so sai anyi,murna fal ran Ladidi sannan ta yiwa hajiyar godiya ta kashe wayan zuciyar ta fal farin ciki.
Ko bayan da suka gama wayan da Ladidi kasa zama hajiya tayi,nan a parlour'n ta ta fara safa da marwa tana goye da hannayenta biyu a baya zuciyar ta kamar ta fito dan b'acin ran da take ji game da YAZEED,ta jima tana aikin abu guda,ganin hakan bai mata ba yasa ta ficewa daga gefen nata ta nufi hanyar b'angaren Fulani sai huci take,tun kafin ta k'arasa shiga ta fara rafka mata kira
"Hafsatu..! Hafsatu..!! Maza ki fito kafin na iso..!"
Fulani na zaune lokacin da littafin HISNUL-MUSLIM a hannunta tana karantawa ta fara jiyo muryan hajiya,gabanta ne ya shiga fad'uwa dan yadda take jin kiran tasan bana lafiya bane,saurin sallamar bayin dake gefenta tayi tun kafin hajiya tazo ta mata tijara gaban hadimanta,fitarsu a gefen lokacin yayi dai² da isowar hajiya,cikin fushi hajiya ta kalleta tun daga sama har k'asa sannan ta jinjina kai
"Wato ke hafsatu saboda bak'in hali irin naki yasa kika nunawa dank'i kada yabi umarnina ko..?? Shin ke ba'a aure na bari aka auroki..? To wollahi ahir d'inki a cikin maganar nan,kada ki kuskure na ksake jin bakinki ko kuma ganin kin sake shiga wannan maganar,bana son shishshigi ban sa da kowa ba face y'ay'ana da kuma jikana saboda haka naki kawai kallo ne a matsayinki y'ar karere,idan ba haka ba kuma ke kanki zaki janyowa kanki abunda zai sa ki fita a gidan nan.."
Ita kam Fulani tunda hajiya ta shigo ta fara fad'an nan ta rasa gano laifin ta,sai dai yadda hajiyar ta ambaci kalmar aure yasa ta fara hasashen inda matsalar take,cikin sanyin jiki ta d'ago kanta data sunkuyar saboda yadda fad'an hajiya yasa ta fara jin ta muzanta tana cewa hajiyar
"Dan Allah hajiya kiyi hak'uri ki yafemin,harga Allah ban san akan me kike magana ba,ban san wane laifi na aikata ba,idan har nayi miki wani abune cikin rashin sani dan girman Allah kiyi hak'uri ki yafemin in sha Allah baza ki sake samuna da aikata makamancin saba da izinin ubangiji.."
Harara hajiya ta zabga mata cikin fusata taci gaba da magana
"Dama mana kin gama k'ulla makircinki yanzun ai dole ki nemi rainamin hankali ki nuna baki san komai ba bayan kece munafukar data k'ulla komai..!"
Runtse ido Fulani tayi hawaye na ziraro mata saboda yadda kalmar da hajiya ta jefeta da ita ta daki zuciyar ta,a hankali ta koma ta zauna kan tum² en dab'as tana sauke kanta k'asa zuciyarta na mata k'aik'aiyi
"Ni dai na fad'a miki matuk'ar maganar auren nan na YAZEEDU ya lalace wollahi ki kuka da kanki babu abunda zai hana ban hukunta ki ba matuk'ar ina raye..!!"
"Data aikata wane laifin kenan...???"
Muryar YAZEED ta yiwa hajiya kutse a cikin maganar da take,juyawa tayi saurin yi tana binsa da kallo,fuskarsa a d'aure kamar bai tab'a sanin ya ake dariya ba ya tako har zuwa inda suke,a gaban hajiya ya tsaya yana zuba hannayensa a aljihu kana kuma yana bin hajiyar da wani mahaukacin kallo
"Matsa ka bani guri ni d'an nema da uwaka nake magana ba kai ba fitsararre..."
"Ko..?? Shin hajiya kina tunanin zan bari kici zarafinta ne a gabana bayan nasan fad'an rashin gaskiya kike yi..?? Me yasa zaki zo kina mata fad'a bayan ba ita ta cancanci hakan ba..??"
"Ni dai na ce ka bani guri idan ba so kake kuma na kira uban naka ba yazo yaga kakar taka balagar.."
"Babu inda zani hajiya matuk'ar kina tsaye anan.."
Fulani dai tana zaune har lokacin gaba d'aya duniyar jinta take ta mata zafi,yadda hajiya ta yayyafa mata magana yau jinta take tamkar ba rayayyi yaba,masifar da hajiya take yiwa YAZEED akan ya tafi ne a dai² lokacin yana bata amsa yasa ta dawo hayyacinta,ko da jin muryarsa a gurin tuni ta mik'e saboda yadda yake zubawa hajiyar fitsara son ransa shima,daf da shi ta tsaya kafin ta birkito shi tana kallonsa tare da girgiza masa kai alamun ya bari,kallonta yayi zuciyar sa cike da bak'in ciki yana fad'in
"Haba Ummah me yasa ne zata zo tana miki fad'a bayan baki san komai daya faru ba,akan wane dalili bake kika yi laifi ba zata d'ora miki laifi..??"
Tsawa ta buga masa data sashi yin shiru sai huci yake furzarwa
"Fita ka bar nan yanzun..Ta yaya zaka zo kana fad'a tana fad'a shin sa'arka ce itan..ko kuwa ka manta da cewa itan mahaifiyar mahaifinka ce..wannan rashin d'a'ar aina ka samo shi..??"
Kansa ya sauke k'asa yana k'ok'arin bata hak'uri tayi saurin runtse idonta tana d'aga masa hannu da nuna masa hanya ba tare da ta sake cewa komai ba,juyawa yayi kawai ya kama hanyar fita a parlour'n yana tafe yana waiwayen mahaifiyar tasa da halin da take ciki,dai² yaje bakin k'ofar fita yana niyyan k'arasa ficewa ya jiyota tana fad'in
"Dan Allah hajiya kiyi hak'uri da duk abunda ya faru in sha Allah babu abunda zai sake faruwa a duk abunda kika fad'a,in Allah ya yarda ni da kaina zan gyara komai..na miki alk'awari.."
Wata uwar zabura YAZEED yayi yana juyowa da niyyar dawowa,tun kafin ya kaiga aikata abunda yake shirin yi tuni ta sake nuna masa hanya tana fad'in
"Fita nace..Kada kuma ka kuskura ka dawo har saina neme ka..!"
Haka nan kan babu yadda zaiyi ya juya ya fice zuciyarsa cike da jin haushin hajiya da abubuwan da take yi a cikin kwanakin,wanda duk wani mai hankali idan ya nutsu ya kalla zai iya fahimtar dalilin da yasa hakan ke faruwa.Bayan fitar YAZEED a gurin hajiya bata kyale fulani ba sai data k'arewa mata tanadi sannan ta fice ta barta da k'unar rai,sanda ta koma side enta nan ta kuma sawa a kira mata maimartaba saboda abunda tayiwa Fulani yanzun sam bai gamsheta ba,har saita sake zayyanawa Maimartaba da kanta tun kafin YAZEED ya yanke wani sabon hukuncin,dalilin kuwa ta san tunda aka fara da haka gaba kuma bata san mene ne zai faru ba,gara tun wuri tayiwa tufkar hanci kafin al'amura su gama chakud'ewa,ko da Maimartaba yaji sak'on na hajiya cikin hanzari ya nufo b'angarenta da zuwansa kuwa nan ta zaunar da shi ta shiga bayyana masa duk abubuwan da suka faru,hatta kuwa da abunda ya wakana tsakaninta da YAZEED sai data sanar masa tana yi tana hawaye,ran Maimartaba ne ya b'aci da jin batun nan take bada b'ata lokaci ba yasa gaba d'aya a kira masa su hatta da GALADIMA,Ummi zuwa YASEER duka baibarsu ba,cikin k'ank'anin lokaci duka suka hallara a parlour'n hajiyar nan da nan aka tashi d'an k'aramin meeting..................
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@Hawwa M.U Pindiga.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Thank yuh SURAYYAHMS for d page,i really appreciate.*
*A few special friends can magically brighten up your heart and life...I am truly thankful to Almighty God for blessing me with such wonderful F.R.I.E.N.D.S. like you! #JAMILA MUSA (MEELAT TAMU),#MAIMOUNATH OUSMAN GAGARA (OG),#HABIBA IDREES (HUBBEEY) & #HALIMATUS-SADIYA MUHAMMAD (LEEMA).*
*Pg 26.*
^^^^^^^^
Kallonsu Maimartaba ya fara d'aya bayan d'aya kafin ya tsaida idanunsa akan yarima YAZEED cikin wani irin yanayi ma fushi ya ambaci sunan sa duk da bai tab'a yin hakan a baya ba
"YAZEED..! Waya baka ikon yiwa hajiya rashin kunya..?"
Kansa ya sunkuyar k'asa ba tare daya iya d'agowa ba bare su had'a ido da maimartaba saboda kwarjini,gaba d'aya parlour'n sunyi shiru kowa kunnensa yana ga maimartaba,Babban burinsu kusa duka bai wuce sanin dalilin da yasa ya tara su kamar haka ba,cikin gaggawa yayi musu irin wannan kiran a kuma irin wannan lokaci,cikin jimami da takaici maimartaba ya waiwaya ga Fulani saboda rashin samun amsa daga YAZEED en da baiba
"Hafsatu..! Shin kin san irin abunda dank'i ya aikatawa mahaifiyata ko kuwa...?"
Sunkuyar da kanta itama tayi k'asa ba tare data kalleshi ba cikin murya mai cike da rauni ta fara magana
"Ranka ya dad'e ina nema masa afuwarka,a yafe masa laifin daya aikata...In sha Allah haka bazai sake faruwa ba..!"
"Ya isa haka nan Hafsatu,bawai mun tara ku anan dan mu sake maimaita abunda ya riga ya faru bane,munyi haka ne domin mu nunawa yaranmu kuskuren su,dan gaba kada a sake samun wani cikinsu ya maimaita kwankwacin hakan..."
A hankalin ya sake kallon YAZEED fuska babu annuri kafin ya furta
"Duk abunda za kayi ina gargad'inka daka san a inda ya dace kayi,matsayin hajiya a garemu da matsayinka a gurinmu yana da bambanci,duk da yadda muke mahaifa a gurinka wanda matuk'ar za'a ci zarafinmu a gabanka mun tabbata bazaka jura ba,sai dai kamar haka ne muma a garemu,matuk'ar za'a tab'a namu mahaifan babu yadda za'ayi mu jure,a yau ka aikata laifi mafi girma a garemu,bisa wannan yasa muke umartarka daka yi gaggawar bada hak'uri ga ita hajiya daka b'atawa rai.."
Yadda fuskarsa take tun shigowar sa gidan har yanzun tana a yadda take ba tare da sauyin komai ba,saima k'ara fusata da yake a duk lokacin da aka yi wani abu makamancin wanda zai bashi haushi,inda hajiyan take ya d'an kalla ya d'auke kai sannan ya shiga bata hak'uri,tunda ya fara magana idon hajiya ke kansa tana kallo sai tab'e baki take,har ya gama sannan maimartaba ya kalleta yana cewa
"Hajiya a matsayina na d'a a gurinki ba wai matsayin sarki ko mahaifi ga YAZEED ba,nake sake baki hak'uri bisa abunda ya faru..Dan Allah kiyi masa afuwa.."
Jingina kai tayi sannan ta furta
"Babu komai d'an Abdu,ai ya riga ya wuce tunda dai ka nuna masa kuskurensa kuma har ya bani hak'uri babu komai,fatan Allah ya kiyaye gaba.."
Da ameen suka amsata duka parlour'n
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 63