Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kula da wajen apartment d'insu suna firan wani wanzami daga cikin irin masu maganin gargajiya d'in nan,haka nan yaji yana son sauraren hiran nasu,ai kuwa suma d'in kamar sun san yana gurin duk da basu ganshi ba suka ci gaba da maganar inda d'aya ciki yake labartawa abokin hirar nasa irin kyaun maganin sa da yadda yake aiki ciki sauri,nan wanda ake bawa labarin yake tambayar adireshin inda zai samu mai maganin "Ai bama iya adireshi kawai zan baka ba bari na had'a maka da lambar wayarsa yadda zaka fi samunsa akan lokaci kuma ya fad'a maka sanda yake babu jama'a sosai a gurinsa.." Bawan da yake bada labarin ya fad'awa d'an uwan hirar nasa,daga haka ya shiga karantawa wancan d'in lambar mai maganin,duka yarima najin su dan lokain hutawa kawai yake kasancewar ranar bai fita ba bare su had'u da YASEER,har suka gama hirar suka shiga cikin wani sashin daban babu wanda ya kula da shi duk da suna closer da juna har ya bar wajen. Bayan kwanaki biyu suna tare a Abuja lokacinn sun dawo daga aiki suna tsaka da hira Yarima ya tuna da batun wannan mai maganin da yaji hiransa tun kafin dawowar su Abuja,sai da yayi murmushi kafin ya kalli YASEER yana cewa "Broah..! Ni kuwa akwai wani magana da naji kwanaki amma kaga na manta ban sanar da kai ba.." Like seriously YASEER yake kallonsa kafin ya tambaya "Wane magana nefa.?" Sai da yayi jimm kafin yayi magana "Akan wani mai magani ne da naji ana maganarsa.." Wani uban zabura YASEER yayi yana daga kwance sai daya mik'e ya zauna yana sake tambayarsa abunda yace,nan ya maimaita masa ba tare da damuwar komai ba,kallonsa kawai YASEER yake ya kasa magana sai daya d'auki lokaci kafin ya ce "Kuma kai d'in yanzun zuwa za kayi..??" Kai ya fara gyad'a masa kafin yace "Haka nake tunani..!" "Toh! Allah ya taimaka.." "Ameen" yace sannan ya kalleshi yana murmushi "Baza ka raka ni ba..??" "Waye zai raka kan..??" "Kai mana..ko baza kaba ne..??" "K'warai kuwa..Sai dai ka nemi wani yana rakiya amma ni kam nadawo daga rakiyar irin wannan masu maganin.." Murmushi yarima ya sake yi sannan cikin nutsuwarsa ya fara yiwa YASEER bayanin duk abunda yaji game da bayin nan sanda suke tattaunawa a ranar da yaji maganar,sai daya tabbatar ya fahimtar da YASEER sannan suka bar maganar akan idan sun koma Kano zasu nemi ganin mai maganin.. Cikin hukuncin Ubangiji kamar yau suka yi maganar zuwa Kano sai gashi har lokaci ya zagayo musu,a ranar jumu'ah bayan an sakko a masallaci kasancewar duk Friday suke barin Abuja,da yamma kuwa suka fice suka d'auki hanyar zuwa gurin mai maganin,tiryan² suke tracing kwatancen har suka isa unguwar ta sharad'a masallaci,a dai² wajejen gidan Malam Aminu Kano dake nan unguwar suka yi parking sannan suka fita suka ci gaba da takawa da k'afa har sanda suka riski gidan Malam Adamu Cindo.Yarima da kansa bayan sun gaisa ya shiga yi masa bayanin duk abunda ke damunsa,shi kuma malam Adamu yana sauraren sa har ya d'iga aya,banda jinjina kai babu abunda mutumin keyi,zuwa wani lokaci ya d'ago ya kalli Yarima fuskarsa da wani irin expression mai wuyar rarrabewa "Samari tabbas naji batunka kuma na fahimci matsalarka,sai dai irin wannan matsalar taka zan iya cewa a wasu lokutan tana kasuwa izuwa kashi biyu (2) ne,na farko mutum yakan iya samunta haka kawai,ko nace tuni dama yana da ita a jikinsa sai dai SAKACI yasa ya kasa rarrabewa,ko kuma k'ashi na biyu ya kasance sammu ne aka yiwa wannan bawan Allah'n..To kaji iya abunda na sani game da mai fama da irin wannan lalura,sai dai kuma kai d'in yanzun bazan iya cewa ga ainihin wanda ke tare da kai ba,amma idan ka amince zan iya baka magani kaje ka jarraba sai dai da sharad'i......" Jimm suka yi su duka har shi malam Adamu d'in dake musu jawabin yana son yaji mene ra'ayin su game da abunda ya fad'a d'in,YASEER ne yayi saurin amsar maganar da cewa "In sha Allah Baba wannan duka ba matsala bane,muna sauraren sharad'in da kace.." Malam Adamu ne ya kallesu duka sannan yace "Ehh! To samari duka wannan ba matsala bane,amma kuma ba lallai ne ku d'in ku amshi irin wannan sharad'in ba ko kuyi juriyar amfani da maganin da za'a baku.." Wannan karon Yarima ne yayi magana da cewa "In sha Allah babu abunda zai faru Baba.." Jinjina kai malam Adamu yayi kafin yace "Ehh to yanzun zan iya baka magani amma da sharad'in za ka yi aure nan da shekara d'aya dan a lokacin ne duk wani larura da muke tunanin yana tare da kai zai kau,wannan shi ne sharad'in maganin da zan baku,amma yaya kuke gani.............??" *Tofa fan's ya kuke gani..?? Shin Yarima ya karb'a maganin ko kuwa..??* *Alhamdulillahil..! Ina godiya sosai masoya da irin addu'o'in da kuke turomin,fatan rabb ya bar zumunci+k'auna.* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *Masoyana a duk inda kuke ina yi muku fatan alkhairi na fili dana b'oye,a kullum abu d'aya na sani kuma shi nake maimaitawa #Ina matuk'ar k'aunar ku har cikin raina..* *Oum Feedy (Hajiya Maryam),Queen Acid,Bushrah,Fatima M.D,Fateema (red rose) ina gaisuwa,taku dabance da saura na gaisheku kyauta.* ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 7.* ^^^^^^^^ Kallon kallo aka fara tsakanin Yarima da YASEER dan sam basu yi tunanin jin haka ba,amma kuma to ya suka iya..? Sun sani cewa matuk'ar suna son suga sauk'i cikin lamarin dole ne sai sun karb'i maganin,a hankali Yarima ya d'aga ido yayiwa YASEER alama daya tambayi Malam Adamu,jinjina kai yayi sannan ya juyar da kallonsa ga malam Adamu yana cewa "Baba to amma idan ya kasance wanda yake da irin wannan larurar yana da aure kuma fa..?" Murmushi malam Adamu yayi sannan ya ce "Ai shi ya sama tun da farko na sanar da ku k'a'idar maganin dan haka baya tab'a faruwa,sai dai ko mutum yayi hak'uri da batun aure zuwa sanda wa'adin da aka d'iban masa zai cika..Saboda doka ce irin ta maganin kuma in dan mutum yana son samun lafiya ne tofa sai ya jure.." Godiya suka yiwa malam Adamu sannan suka karb'i maganin bayan sun cika shi da alkhairi suka kamo hanyar gida,tafe suke amma kowa da abunda yake tunani game da maganin,YASEER ne ya fara yin magana "Broah..! It's necessarily for us mu sanar da wani cikin iyayen mu game da wannan case d'in naka,kaga bazai yiwu ace kana tare da irin wannan problem din kuma ace kana tare da yarinyar mutane ba,tabbas ba kowa ne zai iya hak'uri da zaman jira har na tsawon shekara ba,due to this problem da kuma lokacin da za'a d'auka kafin a samu haske ina ganin kawai mu sanar dasu duk decision d'in da zasu yanke ma to sai mu jira muji daga gare su.." Shi kam Yarima shiru yayi ya kasa magana,buh a zuciyar sa tunanin ta yadda zai iya fuskantar wani cikin iyayensa ya sanar dasu wannan al'amarin yake,babban damuwar kuma shi ne rashin tabbas d'in decision d'in da za'a d'auka akan matsalan ba,shin idan ya fad'a za'a raba auren nasa da sajida ne ko kuwa za'a ce yaci gaba da zama da ita har zuwa lokacin da zai samu lafiya..?? Anya kuwa ma zasu amince su yarda yana tare da wata matsalar ko kuwa zasu k'aryata..?? Shi kam da za'a bi ta son ransa ko a bashi zab'i tabbas da zai rok'i alfarmar a raba auren nan dan shi har yanzun baya jin wani alamu na shak'uwa ko so a tattare da shi game da yarinyar..To amma ya zai yine tunda itan itace ZAB'IN IYAYENSA..? Irin tunanukan da yayi ta yi kenan har sanda suka shigo harabar Royal palace ba tare daya sani ba,dan tun da suka d'auko hanya abun yake ta ci masa rai yana wannan mugun tunanin har bai san sun k'araso gida ba sai jin tsayuwar motan yayi,yana d'agowa da niyyan duba dalilin tsayuwarsu ya gan har sun iso cikin gidan,ajiyar zuciya ya saki lokacin da yake k'ok'arin fita daga motan YASEER ya dakatar da shi ta hanyar rik'o hannunsa,a hankali ya waiwayo yana kallonsa da damuwa a fuskarsa "Wait mana,nayi magana tun d'azun da kai amma naji baka ce dani komai ba,anya kana ganin yin shiru akan matsalar nan mafita ne a gurin mu..?? Ya kamata fa duk abunda za ayi ace iyaye sun sani,gudun kada wani abu ya faru nan gaba,amma ban san kai ya kake gani ba.." Ya fad'a yana kallonsa "Ni kaina ban san ya za'ayi ba,buh ka bani lokaci nayi tunanin abunda ya dace.." "Shi kenan kamar yadda ka fad'a d'in amma fa ka sani wannan ba abune da za'a ce mun b'ata lokaci akansa ba,ya kamata muyi tunanin mafita da wuri kada kuma sai abun ya kwab'e mu rasa mafitan.." "In sha Allah babu abunda zai faru makamancin haka.." Sun d'an d'auki lokaci a cikin motan suna magana kafin su fito su kama hanyan cikin gida,suna tafe bayin dake kewaye da gidan suna mik'o gaisuwa ta ko wane fuska,a garesu kam hannu kawai suke iya yi musu alama da shi amma ko wanne jin bakinsa yake ya masa nauyin da bazai iya magana ba da haka har suka shige. Wasa² sai da aka d'auki a k'alla sati kusan uku ba tare da yarima ya iya nemo mafitan da yake tunanin yana da ita ba,wanda a iya tsayin wannan lokacin ma iya cewa da aurensu kad'ai an kwashi a k'alla wajen watanni biyar,yau kam abun ya ishi YASEER dan yana ganin zubawa yarima ido sam ba mafita bane a gurinsa tunda yin shirun nasa ma sam yak'i yin amfani,dan haka a yau kam ya k'udurce samunsa suyi duk ma wacce za suyi,a parlour'n Ummi'nsa ya iske shi suna hira dan haka yana shigowa koda suka had'a ido nan take ya aika masa da sak'on tuhuma,ga yarima YAZEED kuwa nunawa yayi kamar bai gane me yayi ba nan ya share shi,girgiza kai YASEER yayi kafin ya samu guri ya zauna yana gaida Ummi'n nasa,cikin kulawa ta amsa masa har tana tambayarsa iyali,sauke kansa k'asa yayi alamun jin nauyinta,zuwa wani lokaci kuma ya d'ago ya d'an kalleta,cikin wani rough sounding ya furta "Ummi gurinki na zo nd i want to talk to u.." D'an kallonsa tayi itama tana mamakin maganarsa,in a serious tone ta furta "Wane irin magana ne wannan YASEER kake son fad'a haka..?? Shin maganar tana buk'atan sirri ne..??" "Ehh Ummi.." Ya bata amsa yana sake yin k'asa da kansa "To ina saurarenka.. Allah yasa muji alkhairi.." Ga Yarima kuwa koda yaji YASEER ya furta yana son yin magana da Ummi,nd da dukkan alamu maganar sirri ne tsakaninku,dan yana jin tambayar da tayi kuma YASEER d'in ya tabbatar mata sirri ne,baiyi k'asa a gwuiwa ba sai yayi haramar tashi with intention of forsaken them alone.." Cikin wani yanayi na rashin son magana ya mik'e yana cewa da Ummi'n "Ummi am leaving,maybe i will be back.." Kallonsa tayi lokacin har ya juya baya,ko kafin tayi magana tuni YASEER ya rigata ta hanyar cewa "Wait Man,,,u have to stay..!" Wani burki yaci a inda yake ba tare daya juyo ba take zuciyar sa ta fara tunasar da shi wani abu daga cikin zancen YASEER d'in,in seconds yayi turning back to where he arose,duka jijiyon jikinsa a lokacin banda amsawa babu abunda suke yi dan yadda yake afirgicen nan yasan ba wani abu YASEER d'in zai fad'a ba face game da case d'insa da tuni ya kamata ace sun samu matsaya amma ya tsaya shiririta,dai² ya d'ago idanunsa suka had'a ido da YASEER d'in yana jifansa da wani irin kallo,yadda ya ganshi ya tamke fuska yasa shi sake shan jinin jikinsa "Have u decide to inform someone..Or else..??" Wani wawan kallo ya jefe shi da shi mai cike da warning na kar ya sake ya furta abunda ke bakinsa,kallon baka isaba yayi masa shima,sannan ya maida kallonsa ga Ummi data zuba musu ido tana kallonsu "Kunga ba zaku sani gaba kuna muhawara ba,if baku shirya sanar dani maganar ba maza ku b'ace min da gani.." "No Ummi,, ba muhawara muke yiba,I was confused ne buh now i will tell u.." "Akan mene kake confusion..?? Maganar ba shida muhimmanci ne kake fad'a min haka..??" "No Ummi zanfa sanar miki,nd maganar da zan fad'a na tabbatar tafi duk yadda zan fasalta miki.." Shiru tayi tana saurarensa,nan kuwa ba tare daya bi takan Yarima YAZEED ba duk yadda yake jifanta da mugun kallon yana masa alamun kar ya fad'a ya shareshi ya shiga zayyana mata komai,sai daya zayyanewa Ummi duk abunda ya sani hatta da had'uwar da suka yi da 'Dan DAMFARAR nan da kuma halin da ake ciki yanzun har zuwa kan maganin da Malam Adamu ya basu da duk sharad'in daya gindaya musu,shiru tayi ita kanta Ummi'n dan yadda maganar tasa ta shiga commotion,totally she's speechless sai kallonsu duka da take yi,ta d'auki tsawon mintuna a haka kafin tayi yak'i da bakinta gurin samun y'an wasu words da suma bana jin zasu wuce a lissafa "Why da kuka san da wannan problem d'in za kuyi shiru..?? Me yasa tun farko kuka kasa fad'a a nemi magani..? Sai yanzun ne kuke tunanin samun mafita bayan lokaci ya k'ure..??" Fuskokinsu duka da wani irin expressions suka duk'ar da kai k'asa,ita kuwa Ummi nan tayita musu fad'an k'in fad'a da sukayi da wuri "Yanzun ya kuke so ayi tunda kun koma iyayen mu mun zama y'ay'an ku..??" Saurin kallonta sukayi fuskokinsu na komawa na tausayi "Ummi bafa haka bane..!" "Kamar yaya ba haka bane..?? Idan har ba kun maida mu wad'anda basu da amfani ba,taya bazan ce kun koma iyayen mu ba..??" Hak'uri sukaita bata bama kamar shi YAZEED da laifin sa yafi na kowa dan shi ne babban mai laifin,amma ita kuma laifin YASEER take hanga "Shi kenan zan hak'ura amma kafin nan sai kun tabbatar kunyi magana da iyayen ku maza dan asan abun yi,duk abunda suka yanke shi kenan.." "Ummi me yasa sai sun sani..??" Kallon baku da wayo tayi musu kafin tayi magana "Ni yanzun dan kunzo kun sanarmin shi kenan kuna tunanin zanyi shiru ne..?? Ko kuwa kuna son ku d'aure ni,shi kenan duk ranar da maganar ta fita sai ace Ummi ta sani ko..?? Ni kam ban zama sakarai irinku ba dan haka maza tun muna shaidar juna ku samu kuyi magana da iyayen ku idan ba haka ba,don't even involve me in ur case.." Tana maganar tana had'e fuskarta alamun babu wasa,rasa yadda za suyi da Ummi akan tayi hak'uri suka yi dan a k'arshe ma cewa tayi su fice mata daga gurin,jiki babu k'wari duka suka mik'e suka fita. Bayan fitarsu a apartment d'in Ummi rasa yadda za suyi suka yi dan sam basu tab'a tunanin haka daga Ummi'n ba,kallon Yarima YASEER yayi yana had'e fuska,shi kam gareshi babu laifin wanda yake gani face Yarima dam duk wani abu mai muhimmanci shi bashi yake d'auka mai muhimmancin ba,yanzun abunda yake damun kama ace baza ka iya maida kai akansa ba,,,shi kuwa ga yarima kallon YASEER kawai ya d'an tsaya dan yasan laifi kam nasa ne duk abunda zai faru yasan shine ya janyo hakan,tun farko daya d'auki shawaran da YASEER d'in ya bashi ya tabbata da hakan bai faru ba,to yanzun ga abunda ya faru nan gayya zai gyara wannan kuskuren..?? A hankali ya d'ago ya kalli YASEER kafin yayi magana "Broah..! What should i do..?? "Ai bai kamata ka tambayeni ba,tun farko me nace maka..?? Nd what do u do..?? Ai sai dana fad'a maka abun nan baya buk'atan b'ata lokaci,amma da yake ka maida ni wani sauna a duk lokacin da nake nuna maka muhimmancin abu sai ka dunga gocewa,yanzun ai ga irinta naan,kaga yanzun kuma sai ka san yadda za kayi ka tunkari su Abba da wannan jawabin naka.." Saurin kallonsa Yariman yayi yana cewa "Haba Man! Me kake cewa ne..?? Ni ne zan tunkara su Abba da wannan maganar..??" "To idan baka fad'a ba da waye zai fad'a..?? Ni kake so na je na fad'a..?? Saboda gani sarkin marasa kunya ko..??" Duk yadda yarima yake tunanin abun sai daya so wuce kansa,dan yadda shima YASEER a lokacin ya birkice masa sai masifa yake zazzaga masa,tun yana lallashinsa har abun ya soma fusata shi shima d'in dan yaga abun nasa bana k'are bane,nan kuwa ya juye shima ya shiga zazzaga masa fad'a dama lallab'awar kawai yana dannewa ne bawai dan ya nutsuba (kunsan ance mai hali...!!),shiru YASEER yayi masa daga k'arshe dan yadda yaga mutumin nasa ya birkice masa,ai kuwa nan ya furta "Allah ya kyauta" kana ya wuce ya rabu da shi,wasa² sai da suka d'auki kwanaki ba tare da wata maganar arziki ta kuma had'a suba,dan yadda kowa yayi fushi da kowa,idan har ba gaisuwa ba tofa babu abunda yake had'a su,shima da sun gaisa d'in kowanne zaiyi k'ok'arin barin wajen,wannan sabuwar al'ada da suka b'ullowa junansu da ita ba k'aramin wahalar da juna suke ba,dan kowa ba son wannan wasan shirun yake ba,kawai dai sun d'auki hakan ne a matsayin makamin da zaisa kowa ya fahimci muhimmancin d'aya a gurin d'ayan,amma a bad'ini kawai suna azabtar da kawunansu ne (Shak'uwa kenan). Tashin sa kenan daga bacci a dalilin ring d'in da wayansa keyi,sai da yayi juyi zuwa gefensa na dama sannan ya mik'a hannu ya janyo wayan,ba tare daya duba mai kiran nasa ba yayi answering kiran yana sata a hands free,muryar YASEER ne ya daki kunnensa cikin wani husky voice ya furta "Zaka iya zuwa parlour'n Hajiya su Abba na son ganinka yanzun..!" Sanda yaji sak'on sai da yaji bugun zuciyarsa ya tsananta dan sam baisan mene zaije ya tarar ba a can d'in,amma dai all he knows bazai wuce kan matsalar sa ba.Amsa masa yayi da yana tafe,inda nan take ya dire daga saman royal bed d'insan ya shiga shiri,a gaggauce ya gama shiryawa sannan ya fice yana nufar apartment d'in Hajiya,lokacin daya shigo parlour'n tan sai da numfashin sa ya tafi lesser strike dan yadda ya tarar da ahalin gidan gaba d'aya a zaune kamar masu juran wani muhimmin abu,aifa nan bugun zuciyarsa ya sake ninkuwa sama da sanda aka sanar da shi sak'on kiran da ake masa,duka su Abba suna zaune a parlour'n,a hankali ya juya idanunsa zuwa kan Maimartaba yaga ya had'e fuska kamar bai tab'a dariya ba,sannu a hankali yaci gaba da bin mutanen parlour'n da kallo har zuwa sanda idanunsa suka sauka kan Sajida dake kusa da k'afar Hajiya Suwaiba mahaifiyarta,wani irin gumi ne ya fara keto masa duk da irin sanyin dake cikin parlour'n kuma da kasancewar lokacin rana bata riga da tayi ba,Abba GALADIMA ne ya kalleshi kafin yayi magana "YAZEED ka samu guri mana ka zauna..!" A hankali ya fara d'aga k'afar sa duk da yadda a lokacin yake jin duka vein d'in jikinsa suna gaf da tsayawa a aiki,har dai ya samu damar zaman a kusa da YASEER,cikin hikima da dabara Abba GALADIMA yayi gyaran murya sannan ya fara da tambayar YASEER matsalar da ake ciki,nan YASEER ya shiga zayyana komai ba tare da shakka ko ya b'oye wani abuba,kan Yarima Abba ya juya da kallonsa harma da tambayoyinsa inda nan take kuwa ya tabbatar masa da abunda YASEER ya fad'a,kaf a cikin iyayen babu wanda bai shiga commotions ba musamman ma Umma Fulani dan ita sam bata san da wannan matsalan ba sai yanzun kuma sam ko da wasa bai tab'a sanar da ita ba,ita kuwa Ummi da dama ta riga ta san maganar babu wani abu data ji,shiru duka parlour'n ya d'auka na wucin gadi,kafin aka koma batun yadda za'a b'ullowa lamarin batun malam Adamu mai magani,a nan nefa kowa yayi tsit ana jiran aji hukuncin da za'a yanke,tashin farko Abba GALADIMA bai tsaya shawara da matan ba dan yasan zasu iya kawo masa cikas a zancen ya juya ga Abba Matawalle "Matawalle..Shin yaya kake gani zamu zartar da wannan hukuncin..??" Murmushi yayi masa cikin hikima ya ce "Ai GALADIMA ina ganin zaka fini sanin hukuncin daya dace a zartar dalili kuwa duka yaran nan naka ne..Saboda haka wannan hukuncine da ko ina nan ko bana nan zaka iya zartarwa kuma ya zauna ba sai lallai ina nan ba tunda kai ne gaba dani.." Sosai maimartaba da Abba GALADIMA suka ji dad'in furucin sa Harma da sauran iyayen mata,sai dai ko dajin haka a b'angaren Hajiya Suwaiba kuwa da duk jawabin da ake jinsa kad'ai take tana jiran taji hukuncin da za'a zartar,sai kuma taji mijin nata ya fad'i hakan,ai kuwa nan ta sake jin abun wani iri sai dai kawai tayi shiru bata ce komai ba yaci gaba da sauraro tana jiran taji abunda bai mata ba,Abba GALADIMA ne ya sake kallonsu kafin yaci gaba da magana "Alhamdulillahil.! Da Allah yasa haka ta faru kuma a gaban kowa,duk da kasancewar mu mun fito ne ta tsatso d'aya,sai dai wannan ba shi ne dalilin da zaisa mu yanke hukunci kai tsaye ba tare da munyi shawaran da junan muba,alal hak'ik'a duk da ni an d'ora mun wannan nauyi wanda ya zama wajibi akaina na sauke,ba shi ne hujjar da zata sa nayi abu kai tsaye ba,sai dai duk da haka bazan ce komai ba yanzun har sai mun tuntub'i yaran nan kunji ta bakinsu gudun kada mu tauye su mu shiga hak'ik'insu,a bisa haka nake ganin dacewar mu tambayesu idan har suna ganin zasu iya yiwa junansu adalci kuma zasu iya jinkirin shekara guda zuwa muga yadda hukuncin Ubangiji da abunda ya k'addara zai kasance..Ko kuwa me kuke gani..??" Yayi tambayar yana kallon duka mutanen wajen kama daga kan Hajiya,Maimartaba,Umma Fulani,Abba Matawalle,Hajiya Suwaiba,Ummi'n YASEER,har zuwa kan sauran yaran dake zaune a gurin su da abun kW faruwa akansu,tun kafinma ya kaiga tambayar su Yarima ai tuni Hajiya Suwaiba tayi tsallen albarka da cewa "Ai GALADIMA ina ganin ba sai anyi haka ba,abunda kawai yafi cancanta kuma yafi kamata ayi shi ne a raba wannan auren ni dai a nawa ra'ayin hakan nake ganin zaifi..!" Bata k'arasa ba Abba Matawalle ya datseta "Haba Suwaiba shin abunda ya kamata ya fito daga bakinki kenan..Idan kuma ace yaran nan sun k'udurce basa son a rabasu kiyi yaya kenan..??" Hura hanci ta shiga yi kafin ta bashi amsa "Haba Abban Sajida shi kenan kai dan Allah komai ba zaka iya tsayawa kayi ba sai dai ka bada wakilci,nifa gaskiya bana son irin wannan rayuwar,yanzun dan Allah banda kai ta ina zaka sowa yarinyar nan zama da mutumin da babu abunda zai

Chapter 31 of 63