Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suna bibiyata,bama nan ba hatta cikin family ke kanki shaida ce akan yadda mutane da dama ke son suyi min magana ba don komai ba sai don kawai suna so na saurare su amma nak'i,shin toma taya zaki had'a ni da wani kiyi tunanin class enmu zai kai dai²..??" "Wahh..! Sisto gaskiya nasan haka wannan batun naki yake,sai dai ko ina son ki ture batun class enki gefe,domin kuwa shi wannan en na musamman ne,duk inda kika kai ga aji da dukma wani abu ina fad'a miki a samanki yake,dan yayi miki nisa mai girma indai ta wannan fannin ne,ke bama iya nan ba hatta da ko ina ta miki sharrr...!" Had'e fuska Aisha tayi saboda yadda maganar ta Sajida ta d'an sosa mata rai,a fusace ta mik'e zata bar wajen,saurin rik'o hannunta Sajidar tayi tana mata d'an murmushi kafin ta furta "Haba y'ar uwa fushifa ba naki bane a yanzun, kuma dai ai ko ba komai kafin kiyi zuciya dan na fad'a haka ya kamata ki tsaya kiji ko akan waye nake magana..." Kallonta Aisha tayi kawai tana sakin numfashi cikin siririyar muryarta ta furta "Dan Allah Sajee ki kyaleni da wannan maganar dan baki san yadda nake ji bane saboda kin gama cimin fuska akan wani can da ko matsayinsa ban sani ba bare nasan waye...Ina mai tabbatar miki tunda har a yanzun nan kika gayamin wannan maganar da tunda nake babu wanda ya tab'a fad'a min makamanciyarta yasa naji duk duniyata bani da wanda nake gaba dashi sama da wannan da kike magana akansa,sai dai abu na k'arshe da zan iya fad'a miki shi ne,ina so ki banu nan da kwanaki,ni kuma kafin cikarsu ina son tabbatar miki da dole ne saina zo miki da labarin na sashi ya fad'a tarkon soyayyata,dole duk girman kai da tak'amar da yake ji da shi na maisheshi ya zama tamkar bawana,matuk'ar na amsa suna na kuma na haifu cikin mahaifiyata alk'awari ne wannan nayi tsakanina dake,kuma saina tabbatar daya cika...!" Tana gama fad'an abunda yazo bakinta tayi hanyar ficewa a parlour'n,tana daf da fita ne Sajidar ta furta "Kinyi alk'awari..! Sannan kinci alwashi akan sai kin sa shi ya soki,har kika ce ko wane ne shi en ko...?? Amma abunda ban tambayeki ba shi ne,shin da kika fad'i haka kina nufin ko da ace ni en ina nufin *YARIMA YAZEED* ne....................??? #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.* 😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻* ___________________ *Pg 20.* ^^^^^^^^ Saurin juyowa tayi tana kallon Sajida fuskarta d'auke da matsanancin mamaki,ta d'ebi y'an mintuna a haka ba tare data iya aikata komai ba tamkar wacce aka dannama pause sannan a hankali ta matsa kusa da Sajidar tana cewa "Me kika ce ne Sajee...??" Kallonta sajida ta tsaya yi kawai tana murmushi,koda Aisha taga haka take fuskarta ta rikid'e zuwa wani irin mugun yanayi mai wuyar fassara kafin ta sake tambayar sajidar "Dan Allah ina son ki maimaita abunda kika fad'a yanzun.." Fari sajida tayi mata,cikin kwarkwasa tamkar wacce ke gaban saurayi ta furta "Dallah ni kada ki rainamin hankali,nasan kinji abunda na fad'a,dalilin baki san shi zan ambata bane yasa kika gama cika min baki ba...?? Haba y'an mata ai na fad'a miki tun farko kada kice zaki ja da lamarinsa domin kuwa shi en ne ba tsaranki ba,bawai kece ba tsaransa ba,amma da yake kina son mai dani wata bahaguwa shi ne zaki zauna ki shirya min shirmenki tamkar shirin jigida..Huh.! Yanzunma dai duk ba wannan ba ni abunda nake so dake kawai shi ne ki tsaya kiyi tunani akansa,idan har kika ce abunda kika saba yiwa sauran samari zaki masa wata k'ila a maimakon shi ya fad'a tarkonki ke kya kai kanki cikin komarsa...Amma fa shawara ce na baki,kina iya canjawa idan kin so,sai dai kafin kice zaki yi gaggawa ki sani,matuk'ar kika yi wasa da damar samun yarima,tofa ki tabbata babu ke babu wata dama ta alkhairi da zata sake samunki,dan wannan shine mafi k'ololuwar alkhairinki a rayuwa....!" Yadda Aisha ta kafeta da idanu gami da kunnuwa saiku rantse wani darasi sajida ke biya mata,nutsuwa ce ta dole ta shiga jikinta da ni kaina sai da nayi mamakin inda ta samota,kallonta Sajida tayi tana girgiza mata kai kafin tayi magana "Mene ne kike min irin wannan kallon haka..?? Ko na fad'i wani abu ba dai² ba.??" Cikin sanyin jiki Aisha ta girgiza mata kai "A'a babu komai..amma dai naga alamun a na damunki,da har kika iya yin wannan tunanin,shawarata gare ki shi ne ko dan gaba kafin kiyi tunanin faruwar abu ko zartar da hukuncin k'i akansa,ina so ki fara bincike ki tabbatar shin idan kinyi abun babu matsala ko kuwa,haka nan idan wasa kike ne to ina ganin gaskiya ki san irin wanda ya dace kiyi,dan ina ganin garin irin wannan wasan naki wata rana sai wani ya rasa ransa,idan kuma ba haka ba to lallai ne da irin wad'annan zantukan shirmen naki wani saiya kifa miki mari dan takaici..." "Kamar yaya kenan kike nufi..? Shin kina tunanin wannan maganar da wasa nake yinta nima..?? Bari kiji Aisha idan har ke kin d'auka da wasa to ki canja tunani,kamar yadda na fad'a miki sirrin zuciyata,nima sam bada wasa nayi ba,abun duk dana fad'a shi nake nufi.." Kallon kin cika Mara hankali Aisha tayi mata kafin tayi shigewarta zuwa waje ta bar sajida zaune a nan ba tare data sake tanka mata ba,bayan fitarta a parlour'n da sajida ta raka ta da kallo ta tab'e baki,cikin takaicin rashin bata had'in kai da Aisha tayi ta fara mita "Gaskiya a duniya ban tab'a ganin bagidajiya irinki ba Aisha,taya alkhairi zai kiraki amma ki dunga gudun sa..? Wollahi matuk'ar yarima ya kub'uce miki kinyi asara a rayuwarki ta duniya gaba d'aya,na tabbata bazaki tab'a samun mijin daya kaishi ba,kai in bandama rashin rabo irin naki taya zaki d'auki wannan maganar a wasa,ni da ace ni ce a matakin nan ai wollahi duk wanda yazo min da wannan batun har kyauta zan masa dan k'arshe ya gama burgeni saboda zaton alkhairi da yamin...Mtttsssss..!" Taja uban tsaki saboda tsabar takaicin da Aisha ta k'unsa mata,kafin daga bisani itama ta mik'e tayi waje,tana bin bayan Aishar.. Can a k'uryar d'akin hajiya kuwa itace da Adda suke nasu k'us² en game da wasu al'amura nasu na family da kuma wasu abubuwa da suke faruwa a kwanakin a gari,a cikin hiran ne sunyi nisa sosai suka fara jiyo shewar su Aisha sanda suke shigowa,wannan yasa su dakatawa dan basa son kowa yasan suna nan bare kuma a san mene ne suke magana akansa,hiran dasu Aisha dake gudana tsakanin sajidar da Aisha suka kasa kunne suna sauraro,duk abunda suke tattaunawa babu wanda basu saurara ba,a b'angaren Adda koda taji sanda sajida ke yiwa Aisha maganar yarima YAZEED take hankalinta ya karkata zuwa tunanin akan hakan,ta shiga fasalta duk yadda al'amura zasu zama idan hakan ta kasance,ai kuwa nan ta fara sakin murmushin jin dad'i,kafin ta juya ga hajiya za tayi magana,ko kafin ta kaiga yin magana tuni hajiyar ta mata alama da tayi shiru tukun,nan take kuwa tabi umarnin data bata,saboda lokacin maganar tasu aisha ya koma kamar fad'a,har tak'addamar da suka yi akan maganar duk a kunnuwansu har zuwa lokacin da suka fice,sai a nan ne hajiya ta juyo ta kalli Adda tana sakin murmushi "Gaskiya yarinyar nan ba dai tunani ba .Duba fa yadda take wannan magana kamar Babba,ni da har inayi mata kallon sha³ ashema tafi Aishar hankali,dubafa yadda take nusar da ita alkhairi amma tana guduwa,irinsu Aisha ne alkhairi ke binsu a baya suna guje masa,banda haka har kamar Sajida tayi wannan tunanin amma itan ta tsaya karanta fankon wasik'a..." Cikin jin haushi Adda ta gyad'a kai tana cewa "Ki bari kawai HAJIYA,ai wollahi dan dai kin ce kada nayi magana ne lokacin,amma da so nayi na kirasu nan su maimaita abunda suka fad'a,a inda suka fad'a ni kuma zan d'ora nawa sharhin,irin wannan dama haka data samu amma take k'ok'arin b'arar da ita,kai Allah ya mana maganin irin wannan asarar,wannan ai asara ce kana ji kana kana gani kasa hannun hagu ka tankwab'ar da damarka..Amma zan sameta ne dan ubanta,dama ai irin mijin da nake fatan ta samu kenan tuni ta tsaya shirme ita saita zab'a,garin ruwan ido kuwa taje ta samo wanda tafi k'arfi..." "A'a fa Adda wannan abun bana gaggawa bane,ya kamata ki lallab'ata har ta amince,amma idan kika ce zaki tursasata kan dole tofa zata iya k'in yin biyayya,amma ya kike ganin shawara ta..??" "Haka ne HAJIYA amma dai gaskiya wannan ba abune da zanyi sanya da shiba,irin su yarima dake wahalar samu ita ta same shi a sama ta ka zata ce bata so,ai wollahi bata isaba,haka kawai zata mana bak'in ciki.!" 'Dan murmushi hajiya tayi kafin ta furta "Allah yasa mu dace to,amma kam yau na farko dana ga wautar Aisha,banda haka yariman nan ai jininta ne,mene ne a ciki dan wannan alkhairi ya k'ullu,ina ganin ai zumunci ne zai dad'a k'arfi ko..??" "Wollahi kuwa Adda,kuma banda abunta yanzun ko cikin y'an matan nan data gani a family,bata ganin yadda ko wacce budurwa ke rububin taga ta samu damar tsayawa da shi,dana dai shi en yana d'auke musu kai,ai da tuni wata ta samu guri.." K'wafa Adda tayi tana jinjina kai cikin b'acin rai ta ci gaba da magana "Ki kyaleni da ita hajiya,ai a yau zata had'u da fushi na wollahi,yo ko uwarta idan taji wannan danyen aikin da take niyyar yi mana na asarar yarima ai bazata kyaleta ba...Ke dai kawai ki bari hajiya babu wani d'aukan lokaci da zan wajen yi mata magana,da gaske zan mata idanma auren ne bata so ni zanci mata uwa.." Dariya hajiya tayi kana taci gaba da magana "A'a ayi dai hak'uri Adda kada acinye mata Ladidin,ya kamata ki bita ta yadda komai kika ce tayi zata amsa,amma kiyi mata yadda zata koma cikin nutsuwarta tasan me duniyar ke ciki.." "Ai HAJIYA babu batun saurarawa,gara na bud'e mata wuta shi ne zata yi hankali,idan ba haka ba kuwa wannan ai sake shiga dawa za tayi..To tun yanzunma kina ganin k'aulin da take zuwa da shi bare anyi mata da sauk'i..??" Sun jima suna maganar inda duk bayan mintuna idan abun ya addabi Adda a cikin zuciyarta saita hau mita,yinin ranar abunda ta wuni yi kenan,gashi Aisha kuma sam tak'i ganuwa,dan tunda suka fice tare da sajida basu sake shigowa ba.. ^^^^^ Ko da YAZEED yayiwa YASEER magana akan su bar gurin maimakon su kama hanyar cikin gida b'angarensu,ina sai kawai suka d'auka mota suka fice a gidanma gaba d'aya dalili kuwa sun san yau gidan nasu ba wani dad'in zama zaiyi ba a gurinsu,suka kama hanyar gidan sarki na Nassarawa G.R.A,har sun kusa da gidan suka tuna da batun abinci kasancewar sun san baza su dawo a lokacin ba,tsayawa suka yi a dai² get en AUDU BAK'O SECRETARIAT da tunanin abun yi,yadda YASEER ya tsaya yana tunani yasa YAZEED kallonsa,ko kafin yakai ga yin magana tuni YASEER en ya riga shi da cewa "Malam ya dai ka juya kan mota mu koma mana,ko kuwa zamu rayuwa anan ne ba tare da abinci ba..??" Kallonsa ya juyo yayi kafin ya harareshi "Kasan Allah in dai ni zanyi driven ennan to babu inda zan koma,matuk'ar kuwa ya zama dole sai mun koma to sai dai kai ka maida mu,amma ni yadda na fito babu yadda za'ayi na koma yanzun.." "Haba malam shi kuma abincin fa..?? Zamu rayuwa ne a haka.??" "Oho! Wannan kuma kai ka sani,Amma ni na riga na fad'a maka matuk'ar zan koma to babu dalilin da zaisa ni dawowa nanma gaba d'aya..!" "Kada Allah sa ka koma en,amma ni dai kasan bazaka sani yinin yunwa ba,dan kai ka saba zaman haka nima sai aka ce maka zan zaunane..?" "Sannu acici...! Wai da kake wannan dagewan akan sai mun koma shin dole aka maka sai lallai abincin gida..?? Ina cewa ga restaurant nan a gari kaje mana kaci idan ka damu..??" Hararar sa shima yayi yana d'age kai "Kasan Allah nima babu dalilin da zaisa ni cin abincin restaurant,kawai idan zaka maidani gida na d'auko to idan kuma bazaka ba ni ka bani motan na koma fak'at.." "Ko..?? Ni kuma na zauna a ina kenan..?? Anan kan street kake so na tsaya jiranka..??" "Ina na sani nima..Kawai ka bani guri ni na juya.." Kallonsa YAZEED yayi ya zabga masa harara kafin yaja motan yaci gaba da tafiya,a tunanin YASEER koda yaji bai sake magana ba sai yayi zaton ya hak'ura ne akan zasu koma en,sai dai koda yaje dai² junction zai juya su koma gidan kamar yadda ya fad'a sai gani yayi ya wuce abunsa,saurin kallonsa yayi zaiyi magana yaga ya had'e girar sama data k'asa,cikin jin haushi ya girgiza kai had'e da yin k'wafa yana cewa "Kasan Allah bashi kaci...Tunda kayi min haka babu abunda zaisa ban rama ba.." Bai bari ya kai k'arshe ba YAZEED ya tari numfashin sa da cewa "Ka dad'e baka rama ba,banda rainin wayo kasan kana son abu ka kasa magana har saida muka kusa zuwa sannan ka wani ce sai mun koma.." "To tunda baka koma ba en ai saika min shiru ko..!" "Kanka ake ji...Ina ganin za ka iya yin waya ai ka fad'awa Ummi ta aiko maka da abinci nan,amma taya banda rigima kace mu koma cikin wannan jama'ar..??" "Dillah malam ni ka rabu dani,ina ruwanka dani da zaka bani wani shawara..Ka rik'e kayanka zai maka amfani a gaba.." Kallonsa YAZEED yayi dai² sanda suka iso bakin get en shiga gidan ya saki murmushi mai sauti,k'wafa YASEER ya sake yi yana juya kansa gefe ba tare daya sake tankawa abunda YAZEED en yake cewa ba. Bayan shigar su harabar gidan ko da YAZEED yayi parking tuni ya fice ya barshi man cikin motan,tsabar mugunta kuma irinta YAZEED koda ya fita sai ya zare key en yayi tafiyarsa da shi yana wasa da shi,haushi ne ya sake kama YASEER,nan ya fito a motan yana girgiza kai cike da son yi masa muguntar da zata wanke masa haushin daya k'unsa masa yaci gaba da bin bayansa.Lokacin da YASEER ya iske shi a cikin k'aton parlour'n zaune ya iskesa ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya da waya a kunnensa yana magana,duk da baisan dawa yake wayarba hakan bai hanashi kallonsa ba dan yadda yaga yana wayan sai yasa mutum rantsuwa akan babu wata waya da yake,kawai dai yasa tane a kunne,saboda babu abunda ake iya ji,cikin lokaci kad'an ya gama abunda yake ya ajiye wayan, ba tare daya kalleshi ba,ya furta "Ka nemo wani ka aika shi ya karb'o abincin munyi magana da Ummi yanzun.." K'in kula shi yayi kana shima ya nemi guri ya zauna yana muzurai... ^^^^^ A b'angaren jeeddah kuwa tunda safe data shigo cikin gidan bata samu damar zama ba saboda aikace²n dake kansu ranar musamman kuma daya kasance a ranar akwai wannan taron,tun safe data shiga b'angaren Ummi ko kad'an bata fito ba sai aiki take,sai wajen gabanin sallar azhur ta fito a kitchen en da niyyan zuwa tayi sallah,dai² ta fito tana shirin wucewa ta sanarma Ummi ta gama aikin da take yi,saiga Aisha ta shigo gefen cikin b'acin rai,d'agowa jeeddah tayi jin yadda aka bangajeta aka wuce da niyyar ganin ko waye,nan take idonta ya sauka akan Aisha da ita ko kulama ta buge mutum bata yiba,maganar da tayi niyyan yi ta fasa,kawai saita koma kitchen en da baya dan bata son wani abu ya sake had'a ta da ita yanzun,komawarta babu jimawa Ummi ta fito tana nemanta,a kitchen en ta tarar da ita tsaye ta jinjina bayanta jikin cabinet tana tunani,har shigowarta duk bata sani ba sai lokacin da Ummi'n ta fara mata magana "Yawwa uwata ke nake nema kuwa yanzun.." Saurin juyowa tayi tana sakin ajiyar zuciya,kana ta d'an rusuna tana yin d'an murmushi "Idan kin kammala aikin da kike yi,ina so yanzun kiyi k'ok'ari ki had'awa su YASEER abinci,YAZEED ya sanar min zasu turo wanda zai kai musu chan gidan sarki na nassarawa.." Amsawa tayi cike da girmamawa,nan itama Ummi'n ta juya da nufin komawa,itama jeeddah ta koma bakin aikin nata,bayan fitar Ummi baifi da mintuna ba,sai ga sajida ta shigo kitchen en,tun daga bakin k'ofan shigowa ta tsaya kawai tana kallon yadda jeeddan ke aikinta cikin nutsuwa da hanzari,a hankali ta tab'e baki sannan ta shigo ta bud'e freezer tana duba ruwa mai sanyi,can gefe ta koma ta tsaya taci gaba da kallonta tana jinjina kai,kafin ta gama shan ruwan ta fice ta barta tana ci gaba da aikinta. Kimanin awa guda da y'an nintua jeddah ta shafe kafin ta kammala shirya musu abincin ta d'auka kimai ta jera komai cikin basket,nan a kitchen ta barsu sannan ta fita don zuwa ta sanar ma da Ummi ta gama,bayan fitarta da y'an mintuna ta ta sake dawowa da niyyar d'auka ta fita dasu gurin driver'n da zai kai musu kamar yadda Ummi'n ta sanar mata ya zo tuni ita yake jira,shigowarta babu jimawa kawai saita tarar da su Aisha tsaye akan basket en sun bud'e flask's en suna niyyan d'iba,da saurinta ta k'arasa inda suke,ba tare data yi musu magana ba ta janye basket en sannan ta kinkima zata fita da shi,cikin jin haushin abunda tayi musu sajida ta taso kanta gadan² kamar zata daketa tana mata magana cike da gadara "Keee..! Dak'ik'iyar ina ce da kina ganin zamu d'iba ki wani zo ki d'auke..?? Dallah can dawo ki ajiye mana kucaka kawai.." Kalmar data ambata ita tasa jeeddah tsayawa a inda take ba tare data juyo ba,bare susa ran zata dawo en kamar yadda suka fad'a,sai dai ranta yayi matuk'ar b'aci da kalmar da aka kirata da ita,a hankali Aisha ta juya ta kalli sajida kafin itama ta samu damar yin magana "Ke wai ba dake ake bane,kina jin mutane amma kin mana shiru..ke wawuyar ina ce..???" Koda jin muryar Aisha take yasa ta juyowa tana sakin murmushin mugunta ta kalleta ido cikin ido,cikin wani salo ta sake sakar mata murmushi tana karkata kanta kafin ta fara mata magana "Hi..! Aisha ya kike..?? Ya bayan rabuwa...??" Wani mummunar fad'awa gaban Aisha yayi lokaci guda duka annurin fuskarta ya dusashe saboda tsabar fargaba,cikin rashin sanin makamar abunda ya dace tayi ta shiga had'iyar yahu,ganin jeeddah a wannan lokaci tuni yasa ta kasa sake yin magana,kallonta sajida tayi da mamakin jin yadda jeeddan ta kirata tana fad'in "Yane sis kin san wannan ne..??" Bata iya bata amsa da baki ba sai d'aga mata kai kawai da tayi,koda ganin yadda Aisha ta koma a sanadiyyar ganinta kad'ai yasa jeeddan ta juya abunta ta fice hannunta d'auke da basket en,tana fita itama Aisha bata iya ci gaba da tsaiwa a side enba tabi bayanta,sai dai bata ko yarda sun sake had'a hanya ba,direct bayan fitowarta gefen hajiya ta nufa nan ta nemi tadawa Adda hankali akan lallai saita tashi sun tafi a dalilin lak'anawa kanta rashin jin dad'i. Ita kuwa jeeddah lokacin data fito bayan ta nemi driver'n da zata bawa sak'on bata ganshi ba,duk inda take zaton ya tsaya da kuma wanda ya dace ta tambaya duk tayi,sai dai duk wanda ta tambaya sai yace mata ai bai jima da barin gurina,hakan yasa ta d'an dakata tana jira taga ko zai dawo amma har kusan mintuna a k'alla talatin babu shu bare labarinsa,hankalinta ne yak'i kwanciya da jin shirun,nan take tunanin abunda ya dace tayi ya fad'o mata,har tayi niyyan neman wani driver'n ta bashi ya kai musu kuma sai ta fasa saboda tunanin kada taje garin neman gira ta janyo a rasa ido,wannan tunanin yasa ta kama hanyar fita kawai da niyyan kaiwa da kanta duk da bata tab'a zuwa gidan ba amma tasan duk mai napep en data tsayar bazai kasa sani ba,har ta fita bakin titi ta tare napep bata ko sake ganin kyallin driver'n ba,dan haka kawai sai ta hau kanta tsaye suka d'auki hanyan state road,a dai² k'ofar gidan ya ajiye ta,bayan ta fito ta sallame shi ta d'auki kayan tana kama hanyar k'ofar shiga gidan gadan² k'irjinta sai tsananta bugu yake,ko da zuwanta nan fadawa suka tareta da tambayar inda zata da abunda ya kawota,bayani ta musu na gurin wad'anda tazo da kuma sak'on data kawo musu,ai tun kafin ta gama fad'a suka dakatar da ita akan ta koma,duk iya bayani ta musu ta kuma basu hujjanta na zuwa amma fir suka hanata shiga,kuma abun takaicin gareta shi ne,ta samu ma su karb'i kayan su kai shima sunk'i wai lallai sai dai ta koma da shi dan basu san wane irin abune a k'ulle a ciki ba,rasa abun yi tayi dan haka kawai sai ta koma gefe ta tsaya zuciyarta cike da tunanin mafita daya dace tayi amfani da shi a wannan gurin,tana nan tsaye ta b'ata kusan awa guda ba tare da sun barta ta shiga ba ko su karb'i sak'on ba motarsu ta fito,a lokacin kuwa tuni jeeddah ta gama gajiya saboda tsananin shan ranar da tayi hatta da idanun nan nata tuni har sun fara sauya color,daga dukkan kana kallonta zaka gane ta wahala,har sun gota ta YASEER ya hangota kawai sai ya tsaya da motan kasancewar a lokacin shi ke driven,ta side mirror ya d'an sake kallo inda take sannan yayi baya kad'an,a center en inda take tsaye ya parker,mamaki ne ya kama shi lokacin daya tabbatar itan ce dan da fari baiyi zaton hakan ba,kawai dai ta masa yanayi ne da itan shi yasa ya kasa wucewa har sai da yaji yana son dubawa,a hankali ya fito a motan fuskarsa na bayyanar da mamaki ya furta "K'anwata..! Kece a nan,me kuma kika zo yi nan..........??" #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram*

Chapter 16 of 63