Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kalli Aisha da tayi kicin² tana cewa "Kun san gurin wanda aiko ku ne dama.??" "Ehh! Gurin gimbiya Sajida ta aiko mu.." Murmushi tayi sannan taci gaba da magana "Kuma kun samu gimbiyar da aka aikoku gurinta kun isar da sak'on Fulanin..??" Da maamaki baiwar ta d'ago ta d'an kalli Sajida dake magana tana murmushi "K'warai kuwa mun isar da sak'o.." "Shin wace amsa kuka samu wacce zaku iya komawa Fulani da ita..??" Shiru baiwar tayi cike da taraddadin abunda zata fad'awa Sajida dake jifanta da tambayoyi kamar wata journalist,bata iya bata amsa ba sai sunkuyar da kai k'asa da suka yi su duka ukun,cikin murmushi mai k'ona ran mak'iyi Sajida ta furta "Daga yau ina son ku bambance tsakanin Gimbiya Sajida da sauran mutane gama gari,Wannan da kuke maganar an aikoku gurinta ba kowa bace anan da zaran lokacin zamanta ya k'are anan zata tafi,ni d'in da kuka kasa fahimtar gurina aka aikoku ni ce Sajida..Saboda haka ku wuce ku fara aikinku.." Cikin rawar baki data jiki suka juya akalarsu gareta suna gaidata da bata hak'uri,tana murmushi ta amsa musu sannan ta basu umarnin zuwa ga ayyukkan da zasu yi a lokacin. Lokacin da suka bar wajen ko wacce ta nufi aikinta,sannan ne Aisha ta d'ago rinannun idanunta tana kallon Sajida,ba tare data iya tanka mata ba ta mik'e a fusace had'e da tattara y'an kayayyakinta tayi hanyar ficewa a apartment d'in,har ta kusa da bak'in k'ofar fita Sajida ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya tana tafa hannu da cewa "A gaida na gaba.." Bata ko juyo ba bare Sajida tasa ran zata kulata ta fice cikin fushi,duk da Hajiya tasan da zuwanta a dai² wannan lokacin kam sam bata san da abunda ya faru ba,dan haka Aisha tana fitowa babu ta kan wanda ta sake bi a gidan ta kama hanyar barin ROYAL PALACE d'in,sanda ta isa gurin da tayi parking tana cikin matsanancin b'aci rai dan haka ko da tayi reverse a 360 ta bar gidan ta kama hanyar gida,gudu kawai take shek'awa a kan kwalta,tana zuwa gida bata iya tsayawa an bud'e get ba,tayi parking nan a waje ta k'arasa da k'afa zuwa cikin hararar gidan tana shiga ta cillawa malam isuhu mai gadinsu key tayi cikin gida. Shigowarta duk da bata cikin nutsuwarta nan ta iske k'arshen zancen na Ladidi kasancewar cikin d'an d'aga murya take magana "Haba Adda..! Yanzun ta yaya ne kam za'ayi ace Aisha ta gano ko su waye iyayenta..?? Ko dama ace ta sani babufa abunda zata yi akai ki kwantar da hankalinki..Ko da zata gane ma lokaci ya k'ure mata dan a dai² lokacin data gano hakan za muyi k'ok'arin b'atar da ita a duniyar,shi kenan bata had'u dasu ba bare ta sansu.." "Ba haka bane Ladidi..Sanin kanki ne daga lokacin da akace Yarinyar nan ta gane cewa daga Royal palace take kuma can ne asalinta zamu shiga uku,duk da dai bawai hakan na nufin zata yi saurin gano iyayen nata cikin sauk'i ba ki fahimci abunda nake nufi.." "Shi kenan Adda amma ni dai gaskiya kima dena taso da wannan maganar dan bana son wata rana maganar nan ta fasu har ta kai ga Aisha ta jimu muna yinta,dan bana fatan ta koma hannun iyayenta.." Saurin ja da baya tayi ta b'uya abayan k'aton flower base tana rufe bakinta da duka tafukan hannayenta dan yadda maganar ya girgizata,cike da tashin hankali ta sake kasa kunne tana sauraren taji me zasu kuma cewa,dai² nan malam isuhu yaja get da rufe shi wanda hakan yayi sanadiyyar yi mata shamaki da maganar da su Adda keyi,suma kuwa suna jin haka suka tabbatar da Aisha'n na daf da shigowa ciki,sai kawai suka rufe hiran,koda Aisha taji haka ai da sauri ta koma da baya danma kada su Ladidin su zargi ko taji wani abu daga hiran nasu shi yasa ta gwammace ta koma ta amshi keys d'in daga hannun Malam isuhu. ^^^^^ Kamar wanda aka tilastawa fitowa haka koda ya gama shirin kwanciya ya fito,dai² zai wuce zuwa kitchen ya hangi table a shirye da kayan alatu a samansa,kallon gurin yayi ya d'auke kai da nufin yayi abunda ya fito da shi kawai,har yaci gaba da tafiya kuma sai ya sake kai idonsa a gurin,nazarin gurin yake da dukkan alamun yadda aka tsara gurin ba'a tab'a komai ba har yanzun "kenan hakan yana nufin itama bata ci abincin ba har zuwa yanzun ko me hakan yake nufi..?" Ya tambayi kansa,bai samu amsa ba dan haka kawai sai ya fasa wucewa kamar yadda yayi niyya ya juyo da baya,hanyar bedroom d'inta yabi da niyyan tambayar ta dalili aikata hakan da tayi,nan ya tsinci kansa da sake tambayar kansa "Yanzun idan naje nace mata mene ya kawo ni..? Idan tayi zagin wani abu ya kawo ni fa..? Girmana ya gama zubewa kenan..??" Shiru yayi yana tunani,a hankali ya yamutsa fuska yana tura hannu a cikin curly hair d'insa,a fili ya sake yin magana "No YAZEED ba girmanka bane,idan kace zaka fara kula al'amuranta zata yi tunanin ko ka fara sonta ne..Kawai ka share dan bata ci abinci ba mene zaka damu kanka,cikinta ne idan taga dama taci.." A fiki ya saki tsaki sannan ya wuce zuwa bedroom d'insa ba tare da yayi abunda ya fito da shi ba. ^^^^^ A b'angaren YASEER kuwa tunda Yarima YAZEED ya sanar da shi ya dawo yake ta son su had'u dan akwai abubuwa a dama da yake so su tattauna wanda kuma duka ya ta'allak'a ne akan matsalarsa,sai dai har wajen 10:00pm basu had'u ba,wannan yasa ya bari zuwa gobe idan sun had'u. Washe gari da safe kuwa kamar yadda yayi timing sanda suka had'u da shi a fada,bayan an tashi a zaman Yarima ya fara fitowa sai YASEER,nan ya tadda shi a waje yana jiran fitowarsa,hannu suka bawa juna suna exchange na murmushi da greetings,sannan YASEER ya d'an kalli hanya,ganin babu mutane sosai sai ya kalli Yarima yana cewa "Broah.! When zamu zauna muyi maganar ne..??" Kallon rashin fahimta yayi masa kafin ya tambayeshi "Wane magana kake nufi ne..??" Had'e fuska YASEER yayi cikin jin haushin abunda Yariman ya fad'a ya ce "I don't know.." Yadda yayi maganar yasa Yarima sakin fuska yana murmushi,cikin sigar maganar da babu lallai mutum ya fahimci da wane yanayi yayi ya ce "Kai matsalar ka kenan,sai ka d'auko magana idan an nuna ba'a gane ba,ba zaka yiwa mutane bayani ba,idan na sani zan nuna maka ban sani bane..??" Kallonsa YASEER yayi ya jinjina kai sannan yace "Shall u says u have forget about ur conditions..??" Tak'aitaccen murmushi kawai yayi ba yare da yayi maganna ba,ganin hakka yasa YASEER jin haushi har ta kaiga yayi magana da cewa "Yayi maka kyau..!" Daga haka bai sake cewa komai ba ya rabu da shi,haka suka ci gaba da tafiya har sanda suka zo inda zasu rabu kowa zaiyi apartment d'insa,anan ne Yarima yake cewa da YASEER "Broah! Baka ji ba.." Waiwayowa yayi ya kalleshi yana d'age gira d'aya sama ba tare da yayi magana ba,kallonsa kawai Yarima yayi sannan ya furta "Maganar da muka yi da kai jiya nake nufi.." "Eheen..! Ina sauraronka sai aka yi yaya..??" Wani kallo Yarima ya jefe shi da shi kafin yace "A nan kake so muyi maganar..Da zaka cemin kana jina..??" Dariyar rainin wayo YASEER yayi sannan ya ce masa "Oohh! Ashe babu dad'i..?? Ni d'azun da nayi maka magana ina nunawa kayima kamar ba da kai nake ba,shi ne daga yin d'an wannan maganar kai saboda kafi kowa har kayi fushi.." Jin abunda YASEER ya fad'a ne yasa Yarima sakin fuska kana ya wuce ba tare da yayi magana ba zuwa ainihin apartment d'insu,girgiza kai kawai YASEER yayi sannan ya biyo shi a baya,ko da shigarsa a zaune ya iske Yarima da alama kuma shi d'in yake jiran ya k'araso,sanda ya shigo shima neman guri yayi ya zauna sannan duka suka yi shiru na wucin gadi kafin YASEER d'in ya kalli YAZEED yana sakin bayyananniyar ajiyar zuciya yana cewa "Broah.! Ta ina kake ganin zamu b'ullowa wannan matsalan..?" Shiru Yarima YAZEED yayi kafin ya girgiza masa kai alamun bai sani ba fuskarsa kuma d'auke da damuwa "Kana matsayin Doctor kace baka san ya zaka b'ullowa wannan case d'in ba..?? Haba Man kada ka sani jin kunya mana,kai da kake da maganin matsalar wasu ai bai kamata kace baka da naka maganin naka matsalan ba.." "Yeahhh! I know,,buh kada ka manta ni ba Urologist bane ko Nephrology coz ba side d'ina bane.." Jinjina kai YASEER yayi sannan ya d'an yi murmushi "To kaga yanzun ai ka fito da abunda nake son yi maka magana akai,first of it kamata yayi mu fara tuntub'ar urologist sai mu san abunda ya kamata muyi..Ina ganin wannan hanyan kad'ai ya kamata mu fara bi.." Jinjina kai Yarima yayi cike da gamsuwa akan abunda ya kamata yayin kamar yadda ya samu shawara daga bakin YASEER,sun jima suna tattaunawa akan matsaloli da dama sannan suka fice daga apartment d'in. Bayan kwana biyu da yin maganar tasu,Yarima ya dage gurin contacting likitoci da dama akan matsalan nasa,alhamdulillah hakkan da yayi sosai ya taimaka masa wajen samun mafita ta hanyar shawarwarin da yake yawan samu daga garesu akan matsalan nasa,bayan wasu y'an kwanaki kuma ko da suka koma bakin aiki,sannan ne yayi k'ok'arin had'uwa da urologist a garin abuja,amma abunda ya matuk'ar basu mamakin shi ne yadda duk wani bincike da aka gudanar a kansa yake nuna komai lafiya,wannan dalilin yasa ya sake tuntub'ar YASEER akan hanyan kuma daya kamata su sake bi....... #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *Thanks 4 d luv n care Cweet mom Maryam (Meerahgee) am really appreciate..* *MAMAN NOORUL HUDA ban manta dake ba,gaisuwarki ta mussaman had'e da jinjina ban girma,fatan rabb ya k'aro basira,d'aukaka+hak'uri da jama'a..* ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 4.* ^^^^^^^^ Shigowar Aisha cikin parlour'n yasa su Adda yin shiru kamar ruwa ya cinyesu sai raba idanu da suke cike da tsarguwa,duk da suna da tabbaci kan Aisha bata ji komai ba,fuskarta d'auke da yanayi biyu ta shigo wannan dalilin yasa su kasa tantance ainihin damuwar ta,ladidi kam tunda Aisha ta shigo take binta da kallo tana nazarin ta,a hankali itama ta d'an kallesu fuska babu wadatacciyar walwala "Adda barkanku da hutawa.." Abunda kawai ta iya fad'a kenan cikin wata irin murya ta wuce zuwa wajen da center table yake ta ajiye keys d'in hannunta kana ta wuce zuwa hanyan bedroom d'inta "Aishatu daga ina kike ne..??" Adda tayi tambayar tana binta da kallo,a hankali ta waiwayo tana kallon Adda da rinannun idanunta "Adda naje shopping nefa,kuma na bar sak'o a fad'a miki idan kin fito.." Jinjina kai Adda tayi kafin ta sake k'are mata kallo "Me yake damunki Aisha..??" Kai ta girgiza alamun babu komai,nan kuwa Adda ta fara shan jinin jikinta "Zo nan ki fad'a min abunda ke damunki,dan wad'annan idanun naki sun gama bayyanamin kina da damuwa.." Zama tayi a jikin Adda kana ta zame ta kwanta idanunta na ciccikowa da hawaye "Ni Adda fa kaina ne kemin ciwo kawai.." "A'a Aisha ban yarda da wannan ba,dole ne akwai wani abu daya b'ata miki rai,ciwon kai kawai ba zaisa idanun ki dama ke kanki ku koma haka ba..Gayamin damuwar ki kinji y'ar lelena.." Tayi furucin tana d'an murmushin da ita kad'ai tasan ma'anar sa "Ni...ni..nifa na ce miki babu komai kawai ciwon kan ne nake jin na yau kamar ban tab'a irin saba,kuma ma ko a shopping mall dana je ne kawai wani guy ya b'ata min rai,shi nefa na dawo ban sayo komai ba.." "Kayya dai ni nasan ruwa baya tab'a tsami haka nan banza,ga inda maganar take nan,da nace an miki wani abu kina cemin a'a yanzun kuwa ai naji gaskiyar zance,to amma tunda kika fita wajen 12:00pm ina kika tsaya ba ki dawo gida ba har wannan lokacin.." Tun kafin Adda ta kai aya ai tuni dabara ta fad'o mata "Adda nifa park na wuce ko zan samu damuwana ya ragu,amma aikin banza yadda naje haka na dawo duk ya haddasa min yini da b'acin rai.." Kallon Ladidi Adda tayi tana kashe mata ido had'e da yin murmushi "To yanzun maza je kiyi wanka sai ki kwanta ki huta idan kin samu bacci ciwon kan zai sauka,na tabbata lokacin da kika tashi zaki tashi normal.." Tura baki tayi gaba sannan ta mik'e tana jan d'an siririn Vail d'in data yasar nan a k'asa tayi hanyan staircase tana tafiya kamar bata so,da ido su Adda suka rakata su duka biyun,tana kaiwa ga b'acewa ganinsu kuwa nan Ladidi ta juyo ga Adda tana sauke nauyayyun ajiyan zuciya "Haba Adda ni dai nasan dama babu yadda za'ayi ace taji abunda muka ce,tunda tun kafin ta shigo muka bar maganar.." "Ke bazaki gane ba,kamar yadda hausawa ke cewa 'magana zarar bunu' wannan karin maganar tasu haka yake,muka sani ko iska ya d'iba ya kawai mata,abunda duk baka tab'a tsammanin wanda kayi dominsa zai jiba shi yafi sauk'i a gurinsa ya sani,amma tunda Allah yaso bata jiba shi kenan,dama shi yasa nayi ta tambayarta ai ko ta jin,sai kuma muka yi sa'a bata ma san munyi ba,dan ni dai yanayin fuskarta shi ya bani tsoro sanda ta shigo.." Wata dariya Ladidi tayiwa Adda dan yadda duk ta shiga reserve kamar ance mata a gaban Aisha'n suka yi zancen.Ita kuwa Aisha dai² lokacin data shiga bedroom d'inta kulle k'ofar tayi da key,a hankali hawayen dake mak'ale a idanunta suka samu damar fara sauka saman fuskarta,saurin toshe bakinta tayi da hannunta d'aya tayi hanyar toilet da gudu,sanda ta tabbatar ta shiga ta kulle k'ofar had'e da kunna tap ta k'uresa yana sauka k'asa ta saki wani marayan kuka mai cike da ban tausayi,ta d'auki tsawon lokaci tana rera kuka a nan cikin toilet kafin ta fito sai ajiyan zuciyar da take ta saki babu k'ak'k'autawa,saman bed ta haye kasancewar tana fashin sallah lokacin,duk da sallar ma ba damunsu tayi su yita akan lokaci ba,dan wani lokacin ma idan ta wuce tofa baza ayi ta ranar ba,daga nan kuwa bacci mai cike da wahala ya d'auke ta.. ^^^^^ Sam cikin wad'annan kwanakin Yarima baya wani samun lokacin zama bare Sajida tasa ran ganinsa ko samun wata kulawa daga gareshi,idan yana garinma a wasu lokutan zaka samu sun fice ne tare da YASEER,kuma duk wannan zirga² da suke yi ba kan komai suke ba sai na neman magani da neman mafitan matsalan data ke tattare da Yarima,a mafi yawan lokuta kuwa idan sun fita baya samun dawowa gida da wuri sai dare,wani lokacin kuma yana cikin gidan suna tare da YASEER a apartment d'insu na da,dan wani lokacin ma a nan YASEER yake tafiya ya barshi,ba shi zai fita ba sai ya tabbatar sahun k'afafu ya d'auke sannan ne zai fito ya wuce nasa apartment d'in. Wannan weekend d'inma koda suka dawo garin basu zauna ba,tafe suke a mota yayin da Yarima YAZEED yake driving,shiru motan ya d'auka babu mai magana a cikinsu,har YASEER ya juyo zaiyi masa magana kunnensa ya kwaso masa tallan irin masu maganin gargajiya d'in nan,ai take yayi shiru ya fasa maganar,kana ya juya yana kallon side d'in da mai maganin yake,tsaf tallan ya d'ebi hankalinsu duka musamman ma YASEER dan kisan zan iya cewa yafi damuwa da ciwon Yariman akan shi da ciwon ke tattare da shi har abun yaso rud'ar YASEER,cike da mamaki YASEER ya kalli Yariman yana shirin yin magana Yariman ya riga shi "Broah..! Anya kuwa gaskiya ne wannan duka abun daya lissafo.??" "I don't know.. Buh ina tunanin magani ai sai mutum yayi trying kafin ya gane gaskiyar ingancinsa.." "No broah i don't mean ur words..Na tambaya ne nima,ba wai zan yi anfani da shiba,amma kai yanzun kana nufin tunda har yanzun ba'a san mene actual matsalan ba sai nayi trying irin wannan traditional remedy's d'in..??" "K'waraifa..! Nima ina tunanin haka yanzun kam." Cikin k'araji Yarima ya buga masa wata tsawa "Haba..! Man nine zanyi taking irin wannan traditional things d'in..?? Ni wai kake nufi..??" Kallonsa kawai YASEER yake yana matse dariyar dake son taho masa saboda yadda yaga Yarima ya fututtuke fuska,kai yake girgizawa yana kallonsa had'e da fad'in "Never...!" Kallonsa YASEER yayi yana had'e fuska "Shi kenan to tunda baka so,ai sai kayi ta zama with ur syndromes,a hakan nan kuwa da kake wollahi babu yarinyar da zata juri zama da kai duk kusancinku ko dangantakar ku,gara ma tun kafin su Hajiya su fahimci wani abu kayi k'ok'arin amfani da different medications,if not kuma nayi alk'awari ni da kaina zan je na sanar da Hajiya har ma da su Ummah Fulani,dan wollahi kaji na rantse ko dai kayi abunda ya kamata ko kuma zan sa a tara maka family aka.." Wani uban juyowa yayi ya kalli YASEER "Are u insane...??" Harara YASEER ya jefe shi da ita "Aaa! Ka manta am from asylum.." Tsaki Yarima yaja sannan ya d'auke kai had'e da yin shiru daga magana da YASEER dan ya fahimci idan yaci gaba da magana da shi yau kam ba zai barshi ya sha ruwa cikin nutsuwa ba,yadda yayi shiru ya d'auke wuta yasa YASEER kallon side d'in da yake yana murmushi a ciki. Wasa² lamarin na Yarima yayi gaba dan yadda ya d'auki AL'AMARI'N da zafi yasa ko YASEER d'inma ya d'auke masa wuta akan maganar zuwa wani neman magani da tuni yayi watsi da komai,haka Rayuwar ta ci gaba da tafiya,a dai² wannan lokacin ne kuma ko da YASEER ya fuskanci furucin da yayi da gaske yake ba wai da wasa ba yasa shi yanke shawaran samunsa suyi magana ta fahimta kuma wacce yake ganin idan har sunbi tsarin zasu cimma nasara,a wani yammaci yana kwance shi kad'ai a parlor YASEER ya iske shi,ko da ya shigo Yarima bai d'ago ba bare ya kalle shi kawai dai ya amsa masa sallamar da yayi,guri ya samu ya zauna sannan ya had'e girar sama data k'asa danma kada Yariman yayi tunanin kawo masa wargi a cikin maganar da yake son suyi,cikin isa kammar wani wanda yake gaba da shi ya fara masa magana "Broah..! Wake up,let us discuss.." "So why now.??" Ba tare daya tashin ba yake tambayarsa,sake d'aure fuska yayi yace "Kaga malam nifa am not kidding,kawai ka mik'e muyi abunda ya kamata,idan kamin musu kuma kasan Allah ina fita a nan fadan maimartaba zan wuce dan Wollahi saina sanar masa da duk halin da ake ciki." Harara ya samu daga Yarima kafin ya mik'e ya zauna yana sake ware ido akansa "Ehhenn! Continue am all ear's..!" Gyara zama YASEER yayi sannan ya sake fuskantar Yariman yana d'an sakin smile saboda ya fahimci barazanar tasa tana samun shiga ta b'angaren mutumin nasa "Yawwa..! Kwanakin da suka gabata nayi maka maganar ya kamata muyi k'ok'arin gwada traditional medication ka nemi yi min musu ba..? To ina so ka fahimci wani abu a matsayinka na likita duk fa ka sani ta jikin traditional medications d'in nan da wasunmu ke rainawa ake fitar da wannan magungunan da muke amfani da shi yau da kullum,wanda duka idan ka duba ba ta hanyar komai muke kyamar traditional medications d'in ba illa kawai saboda an kawo mana wannan wanda aka sarrafa had'e da sanya su cikin k'yale² da sarrafa su ta hanyar amfani da wasu sinadarai,why not mu baza muyi trying mu gani ba tunda ni banga aibun yin hakan ba,nd idan muna tunanin wani abu me yasa iyaye da kakannin mu da suka sha wani abu bai same su ba,bai kamata muyi saurin yanke hukunci akan abuba har sai bayan mun gwada ne,nd ina da tabbacin muma za muyi nasara in sha Allah.." Shirun da ya d'an yi yasa Yarima cewa "If nak'i amincewa da wannan shawaran fa..??" "I will try to reveal everyone whose overlooks u as respectable person daya daina dan kaima baka san darajar kanka ba.." Wani kallon ya sake binsa da shi cikin fushi ya mik'e zai bar wajen,sai dai maganar YASEER tasa shi kasa matsawa a gurin,dan yadda ya rantse da Allah akan zai tona yasa jikinsa yin week,to him kam yasan no way out tunda abokin rufin asirin nasa ya murd'a kambun kuma daga yadda ya gano alamunsa tabass iya gaskiyar sa yake fad'a,wannan dalilin yasa shi samun guri ya zauna yana kallon YASEER kawai kafin daga bisani ya kwantar da kai ya fara lallab'a shi,cikin siga ta kwanciyar hankali ya fara masa magana ba kamar da ba da yake kan yi masa masifa "Broah.! For now mene ne abunda ya kamata muyi kenan..??" Shoulder YASEER ya d'age sama kafin yace "Aahh! Ai ni na gama magana dan na riga na sanar maka abunda ya kamata muyi,ba dan kak'i bada goyon baya ba ai da tuni mun jima da barin wannan bigiren.." Jinjina kai yayi kafin ya ce "I know..! it's all my fault..yanzun abunda zanyi nake so naji daga bakinka.." "Abunda za kayi yanzun kam ai jajircewa ne ya rage wajen neman magani tuk'uru nd no more any complaints akan duk abunda zaka gani,duk da nasan addu'ah shi ne first thing daya kamata muyi.." Jinjina kai kawai Yarima yake dan yadda yake son yin obeying duk wani shawaran YASEER a wannan lokacin baya so ko kad'an a samu matsala coz ya sani kaucewar tamkar tonuwar asirinsa ne,wanda baya son ko kad'an ace wani yasan da wannan matsalan. Wasa² neman magani ya kankama dan tun daga ranar a tsakanin Yarima ko YASEER babu wanda yayi sakaci,tako wane gefe dukansu sun jajirce kuma sun tsaya tsayin daka akan ganin sunyi nasara,sai dai duka wannan fad'i tashin da suke yi sam abun ya gagara dan tamkar shukar dusa a gona haka lamarin nasu ya kasance. Cikin wannan kwanakin ne a kan hanyansu na neman maganin da za'a dace suka had'u da wani d'an magori,yadda suka yi bayanin abunda yake faruwa da Yariman,sai kawai suka ga yayi dariya cikin kurari ya shiga kuranta kansa harma da magungunansa dan yadda ya nuna ya yarda da kansa 100%,bisa ga alamun yadda yake musu jawabi suma sai yasa dukansu kowanne ya bada amanna akan maganin,k'ulli²n garin magani daban² ya bawa yarima kafin yayi masa bayanin yadda zaiyi amfani da shi,haka suka amsa suka tafi bayan sun cika shi da kyauta ta alfarma cike da yak'inin yin nasara suka bar wajen suna sake masa godiya...... #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl

Chapter 29 of 63