Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
d'an waiwayo,sai a nan idanunsa suka sauka akan jeeddah dake zaune k'asa kusa da k'afafun Ummi kanta a k'asa,yayin da kunnuwanta ko ke kan sauraren tattaunawar dake wakana tsakanin Ummi'n da YASEER,haka duk abunda ya faru a fada a ranar da case en ya faru duk da Ummi ta sani sai daya sake maimaita mata shi a cikin Hiram nasu. "Heeyy! Girl what brings u here..?" Ba tare data d'ago ba tayi shiru duk da taji abunda ya fad'a,kasancewar ci gaban da aka samu a gidan sarautar tun bayan da aka dank'a mulki a hannun *ABU YAZEED* gaba d'aya bayin gidan suka samu damar mik'a yaransu makaranta,kasancewar akwai makaranta dama nan a cikin gida a K'OFAR KUDU,da take had'e primary n secondary. "Nina bata daman tsaiwa,ko kana da wata matsala da hakan ne..?" Saurin girgiza kai yayi da cewa "No Ummi,kawai dai banyi tunanin akwai wani a kusa da mu bane.." Juyawa Ummi tayi gefen Jeeddah ta kalleta tana d'an murmushi kafin tace "Yawwa mamanmu maza ga sak'on je ki kai mata ki kuma ce ina gaisheta,sannan idan kin koma gida kicewa da Inno na gode sosai Allah saka mata da mafificin alkhairi.." Itanma d'an murmushi tayi sannan tasa hannu biyu tayi holding abunda Ummi ta mik'a mata,bayan nan kuma ta sake yi mata sallama ta fice tana nufan gefen Fulani Babba ma'ana mahaifiyar yarima Yazeed,tana tafe tana ta tunani abunta da tuna irin maganar da Yaseer ya gama yi yanzun,a haka har ta k'arasa gefen,d'an tsayawa tayi tana nazari kafin ta saita kanta ta shiga gurin Fulanin dan Isar da sak'on da aka aikata dashi,ko data mik'a gaisuwa ga Fulani yanayin amsawarta kad'ai ya sake jefa jeeddah cikin tunanin da take ganin hakan ya samo asali ne a dalilin laifin da akace yarima yayi wanda har ta kaiga an yanke masa shekaru ashirin da biyar a gidan kaso,wanda a dalilin k'arancin shekarunta da basu kai sha takwas ba yasa aka fara mik'a shi REMAND HOME,inda daga can kuma shekarunsa suna kaiwa sha takwas za'a maida shi jail en manya ma'ana prison........ #Vote,#comment,then #share. On wattpad@jeeddahmu898. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ _Wish you a very happy birthday,may life lead you 2 great happiness,success and hope dat all your wishes comes true! Enjoy your day._ *HAPPY BELATED BIRTHDAY YAYA HAYAT.* ___________________ *Pg 3.* ^^^^^^^^ Har ta fito daga turakar Fulani Babba maganar na mata yawo a cikin kai,haka yanayin fulanin shima duk cikin wad'annan y'an watannin ya sauya,sam duk wani abun more rayuwa bai cika damunta ba,haka sam bata cikin mood en da zata damu da wani abun duniya ba,ko taga wani abu da har zai iya burgeta a gurin wasu daban. "Shin mene ne matsalar ne...??" Jeeddah tayiwa kanta tambayar da bata da yak'inin samun amsarta,shiru tayi tana yamutsa fuska kafin ta sake cewa "Tabbas koma mene ne ya faru dole ya samo asali ne daga gurin wad'annan mutanen,shin su waye ne wad'annan mutanen..? Mene ne kuma alak'arsu da gidan sauratar nan..?" Hannunta tasa k'asan hab'arta tana tunani kafin ta juya taci gaba da tafiya tana fad'in "Koma dai su waye su,kuma ko yaya matsayinsu yake anan tabbas akwai wani abu a tsakanin su da gidan sarautar nan,na tabbatar haka kawai babu wanda zai zo yayi abunda suka yi,dole ne akwai wani abu daya had'a,shin mene ne wannan abun....?" Ganin tana neman takura kanta da tunani yasa tayi saurin goge fuskarta tana sake fad'in "Koma mene ne Allah ya fimu sani kuma da sannu in sha Allah asirinsu zai tonu,azzalumai kawai da basa tsoron Allah bare su gujewa had'uwa da azabarsa.." "K'warai Allah yana sane da duk wani mai hannu akan wulak'anta rayuwar d'an uwana,haka ko su waye baza mu tab'a barin suba bare su sake samun dama a nan gaba na cutar da shi,sai mun binciko su mun hukuntar da su akan laifin su..Buh in sha Allah we will find another way da zamu bayyana gaskiya kowa ya ganta.." Juyawa tayi saurin yi jin yadda ake maganar cikin yanayi na kamar b'acin rai,Yarima Yaseer ta gani tsaye a bayanta,ba saita tsaya tunani akan wanda yayi maganar ba dan tasan shi en ne kad'ai a gurin,wannan yasa tayi saurin fahimtar shi ne yayi maganar,kanta ta sauke k'asa tana fad'in "Barka da fitowa..!" Kafin taci gaba da bambad'anci gare shi tuni ya d'aga mata hannu,sannan ya furta "Shin zan iya tambayar ki wani abu..? Amma sai idan ba zaki damu ba.." "Babu ranka shi dad'e,kuma a koda wane lokaci a shirye nake idan har na san amsar tambayar ka na amsa ta cikin gaggawa ba tare da jinkiri ba." "Shin zan iya sanin dalilinki nayin wannan maganar..?" Shiru ta d'anyi kafin ta nisa cikin sanyin jiki tana cewa "Ranka shi dad'e ina neman afuwa idan har nayi wani abu da ba daidaiba,kuma ni dai alal hak'ik'a bani da wani k'wak'wk'waran dalili bisa ga wannan matsalar da har ya janyo nayi magana sai dai kawai ina hasashen wani abu ne game da k'azafin da aka lak'abawa yarima.." Saurin kallonta yayi "Shin mene ne kike tunani akai..? Ko zaki iya sanar da ni" "Gaskiya ranka shi dad'e ni dai tunda naji wannan *AL'AMARIN* naji ban yarda da cewa yarima zai aikata ba.." "Me yasa kike ganin haka bazai yiwu ba..??" "Yallab'ai saboda ina da fahimta akansa,tabbas mutane irin su yarima ko kad'an duk mai hankali bazai kawo a aransa zasu yi haka ba,idan kuwa har haka ta faru tofa lallai ne sai dai idan ya kasance *K'AZAFI* akayi musu ko wani ibtila'in ya samesu..beside ma Yallab'ai ni tun a ranar da komai ya faru naji ban aminta da maganganunsu ba bare na yarda ya aikata en.." Shiru Yaseer yayi yana wani d'an nazari,sake kallonta yayi yana shirin yin magana yaga kamar inuwar mutum ta gifta,saurin juyawa yayi yana dubawa har inda yaga inuwar tayi amma bai ga kowa ba,da sauri ya dawo ya kalleta duk cikin rashin yadda da ingancin tsayawarsu a gurin kana cikin muryar rad'a² yace "Ina ganin wannan maganar mu barta haka nan dan naga kamar akwai wani da yake sauraron abunda muke fad'a,amma kafin nan ina so ki ajiye wannan maganar a ranki zamu ci gaba a duk lokacin dana buk'aci hakan..coz bamu kai k'arshe ba bare mu san yadda zamu b'illowa al'amarin..Kin fahimta ko?? Daga nan zuwa wani lokaci ina so ki kasance cikin shiri zan iya neman ki amma ba zamu sake yin wannan kuskurenba na tsaiwa a hanya muyi maganar kin fuskanta ko..? Na aminta dake shi yasa har na tsaya muka fara maganar,sai dai jan kunnen da zan miki shi ne ina so wannan maganar ya zama sirri tsakanina da ke ban amince ko da mahaifiyarki ne kuyi maganar ba,sai dai ko abunda ya shafi bincike wajen gano masu hannu a cikin matsalar kin fahimta..?" Kai ta d'aga tana fad'in "ehh ranka shi dad'e in sha Allah kamar yadda ka fad'a hakan za ayi,nayi maka alk'awari zan zama mai b'oye wannan sirri daga nan har zuwa lokacin da zaka umarce ni na bayyana shi..." "Shi kenan yanzun zaki iya tafiya sai kinji kirana.." "To ranka shi dad'e,na gode sosai da wannan karramawa taka..fatan Allah yaja da nisan kwana.." "Ameen amma dai na sha fad'a miki bana son wannan bambad'ancin,saboda haka a daina min shi..." Y'ar dariya tayi kafin ta furta "Gado sai d'an gado ranka shi dad'e,ni wace ce da zan iya dainawa Yallab'ai..? Wannan shi ne asalina da tushena,yin haka a gurina shi ne zai bani nutsuwa,dainawar kuwa zai zama kamar rashin kunya ne gare ka,kuma na tabbata muddin aka ji na daina fad'a dare d'aya na tabbata ta dalilin haka zan iya fuskantar hukunci,amma ina neman afuwa a gurin yarima idan har na fad'i wani abu daya b'ata ran yarima,haka idan kamin izinin tafiya yanzun ina barin gurin ba tare da yunk'urin sake b'ata ran yarima ba,afuwa nake sake nema bisa laifina.." Yadda ta sunkuyar da kai k'asa kamar mai jiran ace kyat ta zube k'asa kan knees enta,ya sashi zuba mata idanunsa yana kallo dan haka ko da yaji maganaganunta sai kawai ya girgiza kai da fad'in "Na jima da sallamarki saboda haka zaki iya tafiya sai kin ji kirana..." "To ranka shi dad'e godiya nake,a huta gajiya.." Juyawarta ke da wuya da niyyan barin wajen taga inuwar mutum ta gifta da sauri,tsayawa ta d'anyi kafin ta juyo ta kalli Yarima Yaseer dake tsaye har lokacin bai motsa ba,da sauri ta bud'e baki tana shirin magana ya d'aga mata hannu "Kiyi maza ki tafi yanzun naga abunda kike son cewa amma kada ki damu zan bincika naga no ko waye..?" Kai ta girgiza sannan tayi saurin barin gurin,tana tafiya tana d'an waiwayawa bayanta ko Allah zaisa ta gane waye wanda ya gifta sun,har ta kusa fita a cikin gidan bata ga kowa ba,dan haka kawai sai ta mik'i hanya ta bar wajen cikin sauri da haka har ta koma gida,shigowanta babu jimawa ta tarar da Inno tsugune bakin rariya tana d'aura al'wala saboda lokaci daya k'arato,da sallamarta ta isketa gurin,nan kusa da ita ta tsuguna kana tace "Inno na dawo.." Gyaran murya Inno tayi mata kamar wacce take sallah,sai data idar da alwalan sannan ta juyo da d'an murmushi tana fad'in "Yauwa autata sannu da dawowa,fatan kin baro su lafiya?? "Lafiya k'alau na barsu,sun ce a gaisheku kuma suna godiya..." "Masha Allah haka kullum muke fata..." 'Dan murmushi tayi kafin ta furta "Yawwa Inno wai me yasa kullum idan na tarar dake kina alwala bakya amsamin idan nayi magana sai dai kimin gyaran murya..?" "Uhmm! Y'an nan ai bazaki gane bane,nan fa wollahi wata naji tana cewa wai idan mutum yana alwala akan kujerar zinare ta gidan al'jannah ake d'ora shi har ya idar,amma da zaran yayi magana sai a janye ta daga gurin shi." Wata dariya jeeddah ta saki data kaita ga b'ingirewa a gurin saboda tsabar mugunta,Inno kuwa tsayawa tayi tana kallonta,ko da taga jeeddah'n ba tada niyyan dainawa sai ta kai mata bugu,da sauri ta goce sannan ta mik'e ta bar kusa da Inno,sai data tsinci kanta a k'ofar shiga d'aki sannan ta tsaya tana dakatawa da dariyar da take "Kai Inno yaseen da abun dariya kike wollahi,taya za'a zo ace miki wani wai idan mutum yana al'awala akan kujerar zinare yake..? Kuma a hakanma ta al'jannah banda tsabar rainin wayo sannan kuma kema kika yarda.." "To y'an nan taya bazan yarda ba,abu nefa da baka sani ba kaji an fad'a taya zaka k'aryata samuwarsa..?" "Hhhh! Inno tawa to yaseen duk wanda ya fad'a k'arya yake miki babu wani kujerar da ake d'ora mutum akan ta,kawai dai ba'a son mutum yayi maganar ne amma bawai dan waccan maganar da aka yi ta zama ingantacciya ba.." "To! Allah yasa mu dace,idan mun dace kuma mu dafe,kinga yanzun ai na k'aru tunda kinmin wannan bayanin,inba ku da kuka sani ba,mu ai kinga ba ganewa za muyi ba tunda ba karatu muka yiba bare mu sani,kuma in sha Allah suma masu fad'ar tunda naji gaskiya yanzun a gurinki zan sanar dasu dan su daina d'ora mutane akan zaton abunda babu shi.." Murmushi tayi kafin ta shiga cikin d'akin tana fad'in "Ameen my Cweet mommah... The one & only Inno ta.." "Ke ban son shegantaka idan za kiyi Hausa kiyi haka kawai kina fad'an wani abu kamar CUTA kika cenema ko me,kuma naji kin ambaci suna na a gaba,Allah sa ba fatar inji ciwo kike ba..." Wata dariya jeeddah ta sake kwashewa da ita ganin yadda Inno ta hak'ik'ance akan maganar,yadda ta rik'e k'ofa tana tuntsira dariya yasa Inno jin takaicin dariyar gashi ita kuma jeeddah ta kasa gane irin kallon da take mata bare ta daina,da sauri Inno tayo kanta da bulugarin data sab'a cikin kwandon kayan wanke² ko kafin kace kobo tuni har jeeddah ta shige cikin d'akin ta kulle k'ofa "Ja'ira da ki tsaya mana na taddaki aradu yau da kinci gidanku,ko an gaya muku bama jin abunda kuke cewa ne..? Ku nan baku yarda ba y'an boko,bokon k'arshen zamani,bokon kuma da ake cewa bokoko a wuta..." Jeeddah kam data shige d'aki ta bar Inno nan rik'e da bulugarin miya ai saita haye saman gadon k'arfensu tana d'an jijjiga gadon tamkar ta samu lilo,tana nan kwance ta jiyo maganar Inno tana mitar sun san komai ai suma,wata sabuwar dariya ta saki tana runtse idonta saboda muguntar data ji.Ta d'auki lokaci a haka kafin ta tsagaita,lokacin ne kuma maganganun da suka yi da yarima Yaseer suka fara dawo mata,a hankali tayi juyi ta koma rigingine tana kallon rufin d'akin da yake na azara,duk da kasancewar gidan ginin gargajiya ne hakan bawai yana nufin gidan nasu bashi da tsari ba,hasalima duk wani mutum da yake jin kansa zai iya rayuwa a wannan guri sai dai kawai burin wani da yafi na wani,wannan shi zaisa kawai mutum ya raina wannan gida nasu a matsayinsu na masu k'aramin m'arfi. Ta jima tana tunane² kafin ta mik'e ta sauka daga saman gadon,fita tayi ta d'aura al'wala sannan ta dawo ta shimfid'a abun sallah,sai da tayi nafila sannan ta kabbara sallar Maghreb,ko data idar jakarta ta islamiyya ta d'auka ta fita tana yiwa Inno sallama da saita dawo,fatan alkhairi Inno tayi mata ita kuma daga haka tasa k'afa ta fice a gidan ta nufi makarantar islamiyyansu dake nan duka a cikin gidan,tana tafiya tana tunani har ta isa ajinsu,shigarta babu jimawa ta samu guri ta zauna kusa da Aina'u bayan ta yiwa y'an ajin nasu sallama sun gaisa da wad'anda suka samu Samar amsawa,littafinta na AKHDHARI ta d'auko sannan ta fara nazari cikin FASALUN FI'D-'DAHARAH,tayi zurfi a cikin nazarinta malam Nura ya shigo cikin ajin,gaba d'ayasuka gaisheshi,a hankali ya juya ya kalli k'ofar shigowa yana bata izinin shigowa,wata Yarinya ce ta shigo nan ya juya ya sake kallonta sannan ya furta "Yawwa! kinga nan.? daga yau nan ne ajinku idan kin zo nan zaki dunga zuwa..kin ji ko..?" "To malam na gode.." Y'an ajin ya kalla sannan ya furta "Y'an aji ga bak'uwa nan kunyi saboda haka a bata gurin zama,daga yau itama ta zama d'aya daga cikinku,kun gane ko..?" Cikin had'in baki suka amsa masa da to,nan ya musu nasiha na su zauna lafiya kamar yadda suka saba banda fad'a kuma banda hayaniya,amsawa suka sake yi sannan ya juya ya fita yana musu umarni da su fara bita kafin malamin nasu ya k'araso,ko bayan fitar malam Nura,hayaniya duka y'an ajin suka fara da surutai iri² wanda suka kamata da wanda nasu dace ba,su Asabe kuwa nan suka fara shishshigewa bak'uwa suna kiranta ta zauna a cikin su,ko da haka ta faru bayan bak'uwa ta koma cikin su ta zauna nan suka ci gaba da surutu suka maida ajin ya koma tamkar gidan biki ko kasuwa,Aina'u kuwa da jeeddah dake can gefe guda suna bud'e littafinsu da shirin fara bita kamar yadda malam yayi musu umarni ko da suka ji ajin ya koma haka sai suka kalli juna,Aina'u ce tayi k'arfin halin mik'ewa tsaye ta kallesu tana fad'in "Assalam alaikum...!" Duka suka juyo suka kalleta kafin wasu ciki suka amsa mata wasu kuwa nan suka samu damar fara jifanta da bak'ar magana,uwar iyayi da tsari ta tashi,duk da taji abunda suka fad'a hakan bai hanata yin magana ba nan ta juya tana ci gaba da magana "A gaskiya dai wannan abun da muke yi bai kamata ba,ace a matsayinmu na wad'anda akace muyi bita mu tsaya hiran da bazai amfanemu ba,ya kamata ace tunda har malam yayi mana magana muyi masa biyayya a matsayinsa na uba a gurin mu,idan kuma har muna so karatun ya amfanemu nan gaba.." "Gaskiya ne wannan Aina'u maganarki haka take,mun gode sosai da tunatar damu abunda ya dace muyi da muka yi k'ok'arin mantawa.." Wata k'awar Asabe tayi maganar lokacin da itama tayi k'ok'arin bud'e littafinta tana tashi daga tsakiyar da'irar da suka had'a ta koma gefe da fad'in "Ya kamata mu fara bita kada wani malamin ya zo ya tarar damu bamu fara ba." Zama Aina'u tayi tana yiwa jeeddah murmushi,itanma murmushin tayi mata kafin suka soma bita tun daga muk'addima har suka kusa kaiwa inda suka tsaya sannan malamin nasu ya iso,sai daf da kiran sallar isha'a sannan aka tashesu,haka suka kama hanyarsu ta komawa gida suna tafe suna hirarsu ita da Aina'u,cikin hirar ne Aina'u ta kalli jeeddah da fad'in "K'awata wai kuwa kin gane wannan bak'uwar da malam Nura ya kawo ajinmu yau..?" Saurin kallonta jeeddah tayi tana girgiza kai alamun bata santa ba "Humm! Ai kuwa sai dai kice kin manta amma ba wai kice baki santa ba.." Cikin mamaki jeeddah ta sake kallon Aina'u "To ni taya zan santa..? Bayan ma ko ganinta bana tunanin na tab'a yi..?" "Aikuwa wollahi kin santa sai dai ko kice min baki gane taba,amma barin tuna miki inda kika santa,shin zaki iya tuna watannin baya da suka wuce..? Ina wata da suka kawo k'ara fada akan yarima yazeed..?" Yamutsa fuska jeeddah take tana tunani,ko da jin abunda Aina'u ta fad'a game da case en yarima yazeed ai tuni ta d'ago fuskarta tana girgiza mata kai alamun ta gane yanzun,cikin mamaki ta furta "Kina nufin ita ce wannan bak'uwar da aka kawo ajinmu yau..?" "K'warai kuwa ita ce dan ni dai na shaida ta kuma ko tantama bana yi itance dan itama a cikin gidan nan gidansu yake,idanma baki yarda ba zaki iya tambayar wad'anda suka ganeta ko a cikin ajinmu ne zaki ji gaskiyar zancen.." 'Dan murmushin yak'e jeeddah ta saki ba tare data sake cewa komai ba ta shiga sak'a da warwara a ziciyarta akan Aisha,dan ita sam bata ganeta ba,a haka har suka isa layinsu nan suka yi sallama kowacce ta nufi gidansu,ko da shigar jeeddah gida bayan tayi sallah taci abinci nan ta shige d'aki ta kwanta duk da ba bacci take jiba amma haka kawai taji tana son kasancewar ta ita kad'ai ba don komai ba sai don tana son bawa zuciyarta dama kan tunanin hanyar data fi dacewa su fara bi wajen binciko asalin *AL'AMARIN..........* _Rashin Comments da Voting a wattpad,WhatsApp n Facebook zaisa ni rage yawan typing..._ _DON'T FORGET TO VOTE ME ON WATTPAD @jeeddahmu898._ #Vote. #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *Pg 4.* ^^^^^^^^ Dare ya raba sosai inda duk wani mai rai ya yada hak'ark'arinsa domin hutawa,ga jeeddah kuwa har lokacin idanunta a k'ek'ashe suke,banda zallar tunani da neman hanyar da zata b'ille musu babu abunda take,sai misalin k'arfe 1:00am na dare sannan ta nisa bayan sauke nannauyan ajiyar zuciya ta mik'e ta fita daga d'akin,bayan gida ta zaga ta fito sannan ta sake d'aura al'wala ta koma ta kwanta lokacin da niyyan bacci,addu'ah tayi sannan ta juya ta kwanta,bata jima da kwanciya ba bacci mai nauyi ya d'auke. Bata yi nisa sosai da kwanciya ba ta fara mummunan mafarki da Yarima yazeed,cikin baccin ta ganshi cikin rami,duk da ramin ba shi da wani zurfi amma sam yariman ya kasa fitowa daga ciki sai mik'o hannu da yake waje bakinsa yana motsawa alamun yanason yin magana da neman taimako,sai dai abun mamakin shi ne sam sauti baya fita a cikin abunda yake fad'a sai dai zallar motsa bakin da yake,cikin sauri ta fara tafiya tana nufar inda yake da niyyan taimaka masa ya fito daga cikin ramin,sai dai ko data kusa zuwa inda yake sai taga kamar an mai da ita baya,haka ta ci gaba da dawowa amma duk sanda ya rage baifi taku kad'an ta iso gurin shi ba sai ta hangoshi a can gaba sun yiwa juna nisa,zubewa tayi a k'asa saboda tsabar gajiyan da tayi na maimaita tafiyar da bata san adadin sau nawa tayi hakan ba tana fashewa da kuka,a hankali taji an dafata ta baya,da sauri ta juya da niyyan ganin waye,yarima Yaseer ta gani tsaye yana binta da murmushi, bata iya mayar masa ba sai fuskarta data fara gogewa tana share hawayenta,ko data sake d'agowa da niyyan yiwa yarima yaseer bayanin abunda yake faruwa da yarima yazeed sai ta nemi yarima yazeed en ta rasa,hakama ramin data hangoshi a ciki babu shi ya b'ace tamkar gurin bai tab'a tsagewa ba bare ace da wani abu mai kama da rami a gurin,ko da ganin haka sai hankalinta ya dad'a tashi a guje ta mik'e tana nufan inda ta hango ramin data hangi yarima a ciki,sai dai tini labarin nata ya canja salo dan kwata² babu abunda ta gani a d'azun,zagaye wajen taita yi ko zata gano inda damin yake amma sam babu shi bare dalilinsa,farkawa tayi a matuk'ar firgice jikinta duk ya jik'e da gumi,dogon numfashi ta shiga ajiyewa tana share fuskarta had'e da mutsitsika idanunta da suka mata nauyi,ta d'an jima a haka kafin bacci yaci gaba da fizgarta,tana daga zaunen da take ba tare data yi tunani abunda ya dace tayi ba bacci

Chapter 3 of 63