jikarki ba.."
Baki Adda ta bud'e tana zaro ido waje
"Ohh! Ni y'ar nan yau naga abunda yafi k'arfi na,yanzun Aisha kece mai wannan maganar a gabana..??"
Rufe ido Aisha tayi tana dariya cike da nuna alamun jin kunya ta furta
"A'a Adda sub'utar baki nefa.."
"Kaji ja'ira wane sub'utar baki kina sane,dama dai kina so ne ki nunamin kin girma shi yasa kika iya kallon tsabar idona kika bani amsa.."
Tashi tayi a guje tabar gurin tana dariya,ita kuma Adda sai fad'in ta dawo take amma ina tak'i dawowar.
Kwanaki sun dad'a tafiya da maganar had'a auren,tun daga lokacin da akayi maganar a kullum hajiya cikin neman YAZEED take,haka shima a b'angarensa kullum cikin gujewa abunda zai had'a shi da hajiyan yake,duk ko sanda zata yo aiken yaje tun bayan lokacin da yayi k'aryar ciwo da an sanar masa sai ya fice ya bar gidan ba tare daya yarda ko sau d'aya sun had'a hanya ba,yau kam tura ta kai bango,al'amarin duk ya damu hajiya dan yadda Adda ke damunta da maganar yaushe YAZEED en zai je yaga Aishar su gana,amma abun har yasa tana neman rasa da wane baki zata mata bayani,tun tana fad'ar abunda yake faruwa har yanzun ta kaiga ta fara yiwa Adda'n k'arya,yauma tana zaune cikin parlour kiran Adda ya shigo wayarta,kallon wayar tayi ta d'auke kai gefe dan yadda ta fara jin haushin kiran da Adda'n ke mata a yanzun wanda babu dare babu rana kullum cikin damunta take da kiraye².K'in d'aukan kiran tayi zuciyarta a lokacin kamar zata fito dan takaici,ko kafin kiran ya katse tuni ta mik'e saboda yadda take jin a yau ko dai a ita ko kuma YAZEED amma dole ne sai ta ganshi sunyi magana,dan haka a lokacin ko data fito bata nufi ko ina ba sai gefensu,cikin sa'a kuwa sanda tayi knocking k'ofar shi kad'ai ne zaune a parlour'n ya tusa laptop a gaba,izinin shigowa ya bayar ba tare da damuwa da duba wanda ya zo ba,turo k'ofar hajiya tayi ta shigo da sallama a bakinta tana kalle²n inda zata gano shi,jin muryar hajiya tuni ya sashi d'agowa ya juya yana kallon hanyar shigowa,koda juyowarsa nan idanunsa suka sauka kan hajiya tsaye ta kama waist tana jifansa da kallon sannu hamshak'i,waskewa yayi duk da ganinta ya sashi jin rashin dad'i,k'arasowa tayi har inda yake ta tsaya kallonsa,cikin takaici ta jinjina kai tana fad'in
"Sannu YAZEEDU kaji..Allah saka maka da alkhairi..!"
'D'auke kai yayi gefe yana had'e girar sama data k'asa kafin ya durk'usa ya gaisheta,k'in amsawa tayi daga gaisuwa da yake mata ta fara balbaleshi da masifa
"Wato kai saboda ba'a isa da kai ba shi yasa kake neman ka nunamin iyakata ko..?? Shi kenan dan na nuna inason ganinka sai abu ya gagara,anya YAZEEDU..?? Shi kenan tunda ni dama baku d'auke ni a matsayin mutum ba,tunda kun girma kuma ku nunawa duniya k'unfi k'arfin ayi muku magana.."
Tana fad'in haka ta fashe da kukan kissa,cikin kukan ta ci gaba da magana
"Shi kenan na gode tunda ka nunamin iyakata,zan nemi uban naka na fad'a masa ni ban isa da kaiba,amma tunda shi ya isa ya saka kayi sai ya maka magana kaje kaga Yarinyar..Yau kam na godewa Allah da yasa nima ina da y'ay'an nan da ace bani da su yau da tuni kun sa ciwon zuciya ya kamani.."
Tab'e baki YAZEED yayi dan yadda hajiya ke wannan koke²n da maganganu shi haushi take k'ara masa da sake jin tsanar auren,danne zuciyar sa yayi nan ya shiga bata hak'uri,sai da k'yar ya samu tayi shiru kana ya lallab'ata tare da yi mata alk'awarin in sha Allah zai je yaga Yarinyar,koda jin haka take sai ga hajiya ta ware har da yi masa addu'ar Allah yayi masa albarka ya nuna mata ranar auren,nan ta sashi a gaba taci gaba da tsara masa lokacin da take son yaje gurin Aishar,to kawai yake ce mata duk abunda ta fad'a har tayi ta gama sannan ta tashi ta nufi hanyar fita,har taje bakin k'ofar fita ta dakata tana waigowa
"Yawwa d'an albarka zansa a turo maka lambar ta da adireshin gidan ko..??"
Nan ma to en dai ya sake ce mata sannan ta juya ta fita,tana fita ya koma ya zauna yana furzar da iska mai zafi,mintuna biyar da fitarta sak'o ya fad'o cikin akwatin wayar tasa,sai daya ja mugun tsaki sannan ya fizgo wayar daga gefensa yana bud'ewa,full address ne da phone number a cikin sak'on,nan take ganin sak'on ya sake tunzura shi yayi wurgi da wayar kana ya mik'e ya bar wajen.
Tun da aka turo sak'on bayan ya tashi wayar take ta ring,sai da aka kira yafi sau goma kafin ya dawo ya d'ago wayar cike da jin haushin mai kiran nasa,ba tare daya kalli screen enba ya d'auka yana jinginata a kunnensa
"Yawwa d'an albarka an turo maka number ko..??"
Muryar hajiya ta katse masa masifar da yake shirin yi
"Ehh! Na gani yanzun.."
"To².! Sai kayi saving ko kada ka manta.."
Danne zuciyarsa yayi ya amsa,da "to" sannan ya d'ago wayar yana shirin katse kiran,hajiyar ce ta sake yin magana
"Kafa tabbata ka shirya kaje yau en,kana jina ko..??"
"Uhumm..!"
Kawai yace ya katse kiran,yana cire wayan a kunnensa ya waigo yana sakin tsaki mai sauki suka had'a ido da YASEER,kallonsa kawai yayi cike da b'acin rai ya furta
"Ka shirya anjima zamu je unguwa.."
"Unguwa kuma ina kenan..??"
Tsaki YAZEED ya sake saki sannan ya furta
"Kawai malam ka shirya ni ba saika wani tambayeni inda zamu ba.."
Harara YASEER ya jefe shi da ita sannan ya juya ya bar wajen yana fad'in
"Idan nace kuma bazan jeba fa..??"
Ba tare daya kalleshi ba bare ya tanka masa shima yasa kai ya bar wajen.
Yamma lik'is hajiya tana ta zuba ido taga YAZEED ya zo yi mata sallama,amma shiru bata ganshi ba,mik'ewa tayi ta kama hanya dan yadda take ji yau kam ko daka shi nema ita kam da kanta sai tayi har gidan Adda'n,tun tun daga bakin k'ofar shigowa parlour'n ta fara rafkawa YAZEED kira kafin ta shigo tana neman inda yake,daga cikin bedroom ya fito yana tsuke fuska ba tare daya amsa kiran ba,jin alamun tukun tafiya a bayanta yasa ta waiwayawa tabi hanyar data jiyo motsin da kallo,cikin shiri ta ganshi ya fito zai kyalli da k'amshi yake bazawa,nan take annurin fuskarta ya bayyana,da ganin haka kuwa kawai saita furta
"Yawwa d'an albarka,ince dai ko can en zaka nufa yanzun..??"
amsawa yayi fuska a tamke,gudun kadama ta tsayar da shi da surutunta yasa shi yi mata sallama da sunan ya tafi,addu'ah ta bishi da ita cike da fatan dawowa lafiya,nan yasa kai ya fice,ita kuma ya barta nan a tsaye sai faman sakin murmushi take...................
*Din...din...din...dinn............! Hhh! Mutane na akwai gwarama fa a gaba,duk mabiya bayan Aisha ku fara murnar ganin YAZEED a gidansu Aishar,haka nan masu goyon bayan auren yarima da Aisha kuma ku fara shiri,dan lokaci ya gabato.....Lol.*
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
_Ina daf da tafiya hutu masoya..Watak'ila daga next page bazaku sake ganin posting ena ba sai bayan sallah,duk dai yadda Allah ya nufa haka ne zai kasance..._
*Pg 24.*
^^^^^^^^
Yana fitowa suka had'u da YASEER ya fito shima daga gefen Ummi,ba tare daya kalleshi ba YASEER en yana ci gaba da tafiya yace da YAZEED
"Allah ya kiyaye hanya,a gaisheta.."
Kana ya d'auke kai kamar ba shi yayi maganar ba,d'agowa YAZEED yayi daga k'arasa d'aura agogon da yake ya tab'e baki kafin ya tsaya a inda yake ba tare daya juya ba yana masa magana
"Wai mene ne nufinka ne malam..?? I thought na sanar da kai tun kafin wannan lokacin zamu fita ba..??"
Tsayawa YASEER yayi da tafiyar da yake ya juyo gaba d'ayansa
"To dan ka fad'a min shi ne me..!? Sai akace dole sai munje tare..?? Kaga malam kawai kaje kai kad'ai zaifi,wannan fa maganar na zuwa ganin matar da zaka aura ne ba wai wani gurin da ban zamu je ba,ka fahimta mana..!"
"Kawai malam kaga idan bazaka rakani ba ka fad'a min,sai na cire raina akan hakan zancen yazo k'arshe.."
Jinjina kai YASEER yayi da cewa
"Shi kenan ka d'auka hakan ne,yanzun nak'i rakaka amma ai akwai gaba.."
"Ok.! Thanks.."
Yana fad'ar haka yaci gaba da tafiya bai sake ko juyowa ba bare YASEER yayi tunanin zai saurari abunda zai sake fad'a,yadda ya nuna alamun rashin jin dad'in abunda ya masa yasa YASEER saurin binsa yana masa magana,bai tsaya ba haka bai juyo ba har saida YASEER ya tarar da shi
"Baka ji dad'in abunda ya faru ba ko..??"
"Kayi ne dama dan naji dad'in ba..??"
Murmushi yayi sannan a hankali ya kalleshi yana cewa
"Tunda na fad'a naga alamun haka a tattare da kai..Duk da na so ne ace ka fara zuwa kun gana da ita kafin ka nemi rakiyata,sai dai yadda kayi fushin nan ba zai barni na iya kyaleka ka tafi kai kad'ai ba.."
"God for u..! Da har ka iya ganewa kamin abunda banji dad'in saba.."
"Uhmm! Kai kam lamuranka sai kai,ni ina ganin wannan babu mai iya maka sai mahaliccinka,dan ko matar da zaka aura sai ta matuk'ar kai zuciyar ta nesa,idan ba haka ba kuwa matuk'ar tace zata dunga damuwa da al'amuran ka to ko tasa ran gamuwa da ciwon zuciya..!"
Juyowa yayi ya kalleshi kafin ya furta
"Kai ka san wannan ni ban sanshi ba.."
Haka suka yita y'an maganganunsu har suka k'arasa parking space en,mota suka d'auka k'irar Wagon AWD mai duhun color da glasses enta suka kasance masu haske suka d'auki hanyan lamid'o crescent,yadda address en yake haka suka yi ta bibiyarsa har suka k'araso dai² get en gidan,bayan yayi parking nan suka suka ci gaba da zama cikin motan kowanne da abunda yake sak'awa a ransa,sun d'an d'auki lokaci a haka kuma ba wata hira suke yiba koda zaman ya fara isar YASEER nan yayi magana
"Malam ya kamata ka sanar mata mun k'araso fa..Bai kamata ace munata zama a nan ba ba tare da munsan abun yi ba..."
A hankali ya d'ago kansa ya kalleshi yana squeezing face nasa
"Ohh! Ni zanma sanar mata nazo..??"
Cike da mamaki YASEER ya juyo gaba d'aya yana kallonsa,cikin rashin fahimta ya furta
"Ban gane me kake son cewa ba..to da idan ba kaiba waye zai kirata,ko an ce maka ni ina da number ne da zan kira..? Wannan ma ai rainin wayo ne na rakoka kuma ka wani fad'a min haka,billahillaziiy zaka sa nayi tafiya ta yanzun.."
"To ka tafin mana so what..?? Ko an fad'a maka bazan iya zuwa ni kad'ai bane sai da kai dole..??"
"Ok..! Good,ka kyauta kam daka fad'i haka kaga gobe ma ai zaka ce na rakaka.."
"Yanzunma ai ba dole nayi maka ba,ganin damanka ne yasa ka biyo ni,ko na tursasaka lallai saika rakoni..??"
Still YASEER yayi yana kallonsa har sanda ya kai k'arshe,tsabar mamakin YAZEED da kalmomin da ke fitowa a bakinsa su suka sashi yin shiru kawai ya rabu dashi da maganar,sai da suka sake d'iban lokaci a haka ba tare da wani cikinsu ya sake magana da d'an uwansa ba,zuwa can dai da zaman ya fara isar YASEER cikin takaici ya d'auka waya yana sata a kunnensa,cikin sallama gami da girmamawa ya fara magana
"Ummah dan Allah ki yiwa mutumin nan magana,tun d'azun yasa na rakoshi guri amma ya zaunar damu a mota shi baije yayi abunda ya kawo shi ba kuma mu bamu kama hanyar komawa gida ba,tun tuni na masa magana amma ya tsaya rainamin hankali..!"
Shiru yad'an yi na wani lokaci kafin yace
"Ehh muna tare da shi har yanzun..Ok toh..!"
Yana fad'an haka ya mik'awa YAZEED wayan ba tare daya ce komai ba,wata uwar harara YAZEED ya zabga masa kafin yasa hannu ya amsa wayan yana sata a hands free,maganar Umma'nsa da yaji duk da da fari yayi zaton wasa YASEER yake masa yasa shi saurin gyara zama yana sake tsare YASEER da ido
"Haba YAZEED me zai sa kace d'an uwanka ya rakaka kuma ka nemi wulak'anta shi..?? Kasa ya bar abunda yake ya rakaka amma kuma sai magana yake maka kana masa hanya²,idan har dama ba abunda ya kaika me zaisa tun farko kuje ne..??"
"Ummah k'arya fa yake,yanzun duba number da aka bani nake zan kira.."
"Ya dai fi maka,amma abunda kake yi sam baka kyautawa lokuta da dama.."
Hak'uri ya fara bata jin temper enta ya fara sauyawa tana daf da fara masa fad'a sannan ya bata tabbacin zai kira yanzun,bata iya cewa komai ba kawai ta kashe wayan dan takaicin wasu abubuwan game da halayen na YAZEED.Suna gama waya da Umma'n nasa ba tare daya kalli YASEER ba ya cilla masa wayan sannan ya fice a motan,nan a jikinta ya d'an tsaya yana k'arewa unguwan kallo,sam gurin babu alamun za'a samu mutane masu wucewa,bare yace zai samu wani ya aika ya kirata,sai daya sake d'iban lokaci tsaye nan kafin ya hak'ura ya tura hannunsa ya d'auko phone ensa daya bari cikin mota,duk abunda yake YASEER dake ciki yana kallonsa cike da mamakin abunda yake shirin yi,haka kan babu yadda zaiyi ya shiga laluben number a wayan ba tare da tunanin zai gane number ba dan shi kam yama manta sunansa yasa mata,ya d'auki lokaci yana ta nemanta kafin ya dakata a dai² kan number da sunan da akayi saving da shi ya kasance *ZERO* sai daya sake d'aukan lokaci yana tunani kafin yayi dialing zuciyarsa cike da tunanin mema zai ce idan aka d'auka,har aka d'auka bai sani ba sai da tayi magana sannan ya dawo hayyacinsa
"Hello..!"
Ta fad'a sanda ta d'auka,tsaf yana jinta tana magana amma ya gagara amsawa,sai data maimaita ya kusa sau biyar bai amsata ba,jin haka kuwa yasa ta kashe wayan ta ajiye tana sakin tsaki,kallonta Ladidi tayi dake gefen ta zaune tana tambayar
"Keda waye ne kike tsaki haka y'ar lele..??"
Wani sabon tsakin ta sake kafin ta furta
"Wannan d'an sarkin jin kan mana.."
"Wa kenan kuma haka kika samu..??"
"YAZEED fa nake nufi.."
"Ohhh! Wai kina nufin shine ya kiraki yanzun..??"
"Ehh! Shi ne amma yana ji ina magana yamin banza bai ce komai ba,shi yasa ni kuma na kashe wayan nasan shima zaiji babu dad'i ai.."
Saurin mik'ewa Ladidi tayi tsaye tana jinjina kai gami da sakin dariyar mugunta,kusa da Aishar sosai ta dawo ta zauna kafin ta kalleta tana shirin yin magana
"Wannan ba shi ne hanyar daya kamata ace munbi ba,yanzun kamata yayi mu lallab'a mu kira hajiya mu fad'a mata abunda ya faru kawai,mu kuma sake shirya mata zancen ta yadda ko maganar tayi masa bazai iya wanke kansa ba a gurinta..Ina tabbatar da ta haka ne kawai zamu samu damar da muke nema,sanya ba namu bane yanzun ta wannan hanyar ne kuma kawai zamu sanya gaba a tsakanin su ta yadda aikinmu zai zama cikin sauk'i... Kin fahimta ko..?? maza kira ta ki bani wayan.."
Murmushi Aisha ta saki na jin dad'i kafin ta shiga k'ok'arin kiran line hajiya,sanda ta tabbatar ta d'auka sannan ta mik'awa Ladidi wayan,tun kafin ta amsa wayan ta gyara muryanta zuwa ta tausayi da jimami ta yadda idan hajiyar taji abunda zata fada babu yadda za'ayi ta gane k'arya suke mata,hajiya kuwa koda taji muryar ladidi cikin yanauin tashin hankali tuni ta diririce tana tambayar lafiya..? Bud'ar Ladidi ko sai cewa tayi
"To hajiya abune naga yana neman fin k'arfina,tun d'azun Aisha sai jiran yarima take amma shiru har yanzun babu wani labari,ta kirashi ya d'auka wayan yayi shiru bai ce komai ba ya kashe..Tun kafin abun yayi nisa shi yasa nace barin sanar dake gudun afkuwar wata matsalar,wollahi kin ganta nan sai kuka take saboda abunda ya faru,saboda tausayinta nima kin ganni kamar zan tayata.."
Ran hajiya ne ya b'aci da jin labarin,nan ta shiga bawa Ladidin hak'uri sannan tace zata kira shi taji meye dalilinsa na k'in zuwan,aifa Ladidi koda jin haka sai ta samu damar zayyanawa hajiya k'arya da gaskiya,sake k'ulewa hajiya tayi nan ta sake basu hak'uri kafin ta katse kiran ta shiga kiran line YAZEED.Har lokacin yana tsaye jikin mota sai juya wayan hannunsa yake,ransa idan ya kai dubu to duka sun b'aci saboda yadda ta kashe wayan ba k'aramin bak'anta masa rai tayi ba,yana cikin tunanin kawai zai cewa da YASEER su tafi kiran hajiya ya shigo wayar,sai daya ja lokaci sannan ya d'auka yana d'osanata a gefen kunnensa,cikin b'acin rai hajiya ta fara masa masifa
"Kai YAZEEDU dama kai mutumin banza ne ko,wato baza'a ce maka abu kayi shi kai tsaye ba sai ka b'atawa mutane rai.."
Shiru yayi yana sake tsuke fuska kamar yana gaban hajiyar,cikin rashin fahimta ya furta
"Hajiya laifin me kuma nayi kike min fad'a..??"
"Kaji min mutumin kawai,wato ma baka san abunda kayi ba ko..??"
"To ni hajiya idan na sani taya za'ayi na ce miki ban sani ba.."
"To dan ubanka abunda kayi ne ya dawo kunnena,kuma matuk'ar ba so kake na kira uban naka na fad'a masa abunda kayi ba yanzun maza duk inda kake ka kama hanya kaje inda nace maka..Yau naga mutumin banza kai,d'azun shi ne har dana tambayeka kace dani can zaka ashe yawon barbad'arka ka tafi.."
Ransa ne ya sake b'aci cikin takaici ya furta
"Nifa hajiya duk wannan fad'an naki na kasa gane masa,naga dai cewa kikai naje kuma yanzunma ina nan tsaye a k'ofar gidan,na kirata ta d'auka wayan bata ce komai ba,me zan tsaya yi ne haka..? Matuk'ar bazata iya fitowa ba ni kum banga amfanin zamana a nan ba zan dawone gida kawai.."
"Ka kirata ko dai ta gaji da jiranka itan ta kiraka..??"
"Ta kira ni kuma..?? Ni en tace miki ta kira..??"
"K'warai kuwa yanzun nan Ladidi ta sanar min da abunda kayiwa Yarinyar dan ita sam ta kasama yarda tayi min maganar,tunda ka wulak'anta ta ai dole taji zafin abun har ta kasa magana.."
Mamaki ne ya kamashi jin wannan shahararriyar k'arya da aka zazzagawa hajiyar,ita kuma ba tare da bincike ba har ta hau kai ta zauna
"Shi kenan hajiya amma ni kam babu wani daya kirani yanzun,beside ma hajiya ya akayi ta kirani nida ba number na ne da ita ba,ko kuma dai da kika tashi kin tura musu ne kamar yadda kika sa aka turomin nata..??"
Shiru hajiyan tayi tana wani tunani,can kuma da taga alamun duk abunda aka fad'a mata k'arya ne,ta kuma gano duk abunda ya faru sai kawai tace masa
"To kai banda abunka ai su mata lallab'a su ake,dan ka kira an d'auka ba'ayi magana ba ko ta kira kak'i d'auka ai duka hak'uri za kuyi da juna har ku fuskanci junanku,banda ma kai en ba ji ka cika yi ba daka kira sau d'ayan ai sai ka sake kira kaji ko wata matsalar aka samu ko..??"
"Gaskiya hajiya ni ba abunda zan sake,kawai ki sanar musu idan ta damu da ganina zata iya fitowa,amma in har saina kira tane ta waya ban sake yin hakan,idan ta b'atan lokaci zan iya tafiya ta ina da abun yi..."
Yana fad'ar haka kawai sai ya datse kiran zuciyarsa cike da jin haushin abunda ya faru yanzun,hajiya kuwa daga can jin abunda ya fad'a yasa ta tausasa kalamanta tana magana cikin sigar rarrashi dan ta fahimci fad'an nata babu inda zai je matuk'ar akan sane,shirun data ji yayi yawa yasa ta fahimtar an jima da kashe wayar dan haka sai ta saki tsaki mai sauti kafin cikin masifa ta hau sababi ita kad'ai tana kuma sake neman line Aishar,wannan karon Aishar ce ta d'auka hajiya cikin jin haushi ta furta
"Aishatu Kije waje ya zo tun d'azun yana ji ranki.."
Wani takaici ne ya binneta jin wai sai hajiyar cema zata sanar mata da zuwansa,wato shi bazai iya kiranta ya fad'a mata ba kenan da kansa,lallai wannan ya cika d'an rainin hankali,can k'asan ranta ta furta
"Babu komai..! Duk yadda kake so haka zan bika amma a yanzun,na tabbata nima lokacina zai zo da zan rama fiye da abunda ka yi min.."
Maganar hajiya ta sata dawowa cikin hayyacinta,cikin muryar kuka² tace
"Yanzun hajiya dama ya zo tun d'azun nake ta kiransa shiru..??"
Katseta hajiyar tayi tana fad'in
"Sai kiyi hak'uri ki je ni yanzun ban san me zance muku ba dukkan ku,dan ni dai ba yarinyar ku bace bare ku sani a tsakiya kuna gara ni kamar k'wallo,yanzun kiyu maza kije yana jiranki a waje.."
Tana gama maganar ta ta kashe wayarta sai mita take saboda yadda daga Aisha'n har shi YAZEED en suka nemi raina mata hankali,itama Aisha ko da hajiya ta kashe wayan tana d'agowa ta kalli ladidi dake zaune ta zuba mata ido tana jiran ta idar ta bata labarin abunda ya faru,kallonta itama tayi tana tab'e baki game da yin k'wafa sannan ta furta
"Duk kuyi ku gama lokaci na baku,matuk'ar na shigo gidan nan sai kun gagara samun nutsuwa,ba dai dani kuke jayayya ba,duk zaku shigo hannuna,tamkar gari haka zan nik'e ku na maida ku abun kwatance.."
Jinjina Ladidi dake gefe tayi mata tana sakin dariyar da ita kad'ai tasan ma'anar ta da fad'in
"Da kyau y'ar amana...! Amma yanzun kiyi maza ki hanzarta fita gurin wannan d'an jin kan kada a samu wata matsalar.."
"Ama samu mana,wa garin zai yiwa zafi tsakanin ni da shi..??"
"A'a dai gara kada a samu,ai yanzun mu zamu bishi duk ta yadda yake so,ki bari tukun ko zaki yi wani abu ba yanzun ba sai mun tabbatar daya zo hannun mu sannan ne ya kamata mu wulak'anta rayuwarsa..."
Dariya ta saki tana girgiza kai sannan taja gyalenta tayi hanyar ficewa ba tare data ko yiwa Ladidin sallama ba.
Can a k'ofar gidan kuwa saboda tsabar b'acin rai YAZEED ji yake kamar ya tashi sama ya ganshi a gida,ko da gama wayarsu da hajiya ya d'auki a k'alla mintuna ashirin a wajen yana jiran fitowarta amma shiru bata fito ba,ko da ganin haka take ya yiwa YASEER alamun kawai su tafi,amsa masa yayi shima dan shi kansa da zaman motan ya isheshi fitowa yayi ya rufe motan,har sun juya zasu shige dan shi yazeed ma har ya zauna a seat en suka jiyo maganarta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 63