Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
idan aka d'auke YAZEED da YASEER,nan hajiyar taci gaba da magana wacce tasa su duka suka yi shiru "Ni dama damuwata a wannan lokacin duka ba'a kan abunda YAZEEDU yayi min bane,abunda kawai nake son sani shi ne kawai ina so nasan inda maganar auren nan ya dosa,shin akwaita ko kuwa babu ya wargajeta,tunda dai munyi waya da uwar yarinyar,ta kuma sanar dani irin rashin mutunci da d'iban albarkar da yayi musu..Fisabilillahi idan auren ne baya so ko kuma yarinyar ai saiya sanar damu tun fari ba wai yaje ya wulak'anta taba har gida.." Shiru maimartaba da duka sauran jama'ar gurin suka yi suna masu binta da kallo har ta dasa aya kafin suka jua ga YAZEED suna jiran suji mai zai ce shi kuma,shiru yayi bai iya cewa komai ba,saima kansa daya sake sunkuyarwa zuciyarsa dan tsabar yadda take masa zafi kamar ana rura masa wuta a ciki,maimartaba ne ya sake kallonsa cikin jin haushi ya furta "Shin wannan laifin kuma fa,akwai wani hujja da kake da shi da yasa kake aikata haka..?? Wane dalili ne da kai da zaisa tunda muka yi maka magana baka nuna k'in amincewarka ba sai bayan da muka gama yarda sannan ne zaka nemi tozartamu a idon duniya..?? Wane ne ya baka shawaran aikata hakan..??" Cike da rashin kuzari ba kuma tare da fargaba ba ya furta "Babu kowa ranka ya dad'e.." Cikin fushi maimartaba ya kalle shi "Kace babu kowa...kenan hakan yana nufin mune bamu isa mu saka abu kayi ba..??" "A'a Allah ya baka tsawon rai,sam ba haka al'amarin yake ba.." "Zancen banza kenan,duk abunda kayi kenan kana sane kuma bisa ra'ayin kanka ba tare da wani ya baka shawara ba kake ta neman b'ata mana rai..Wannan abune da bazai tab'a yuwuwa ba ace d'an mu ya gagaremu,matuk'ar babu wani dalili ko hujja da tasa kake gudun wannan auren,muma bamu ga dalilin da zaisa mu fasa aura maka wacce ranmu yake muradi ba,ko da kuwa hakan na nufin afkuwar komai.." Saurin kallonsa YASEER yayi yana tab'a shi da yi masa inkiyan ya sanar da maimartaba abunda yake faruwa,maimakon ace yabi abunda YASEER en yake nuna masa sai kawai ya zabga masa harara mai d'auke da kallon baka da hankali,shima ramawa yayi yana jifansa da kallon ko kuma kai en baka da hankalin ba,muryar maimartaba ce taci gaba da amsawa a gurin inda y'anci gaba da jawabinsa "Wannan magana da muka fad'a itace tabbatacciya,matukar baka bamu gamsashshiyar hujjaba,maganar aurenka da yarinyar nan babu fashi,idan kuma har muka sake samun wani sab'ani akanta muna masu tabbatar maka da zamu d'auki tsatstsauran matakin da bamu tab'a yiwa wani ba akanka..." Nan ya sake juyawa ga YAZEED "Muna fatan kaji abunda muka fad'a kuma zaka yi k'ok'arin kiyayewa..??" Gurum yayi a gurin ba tare daya amsa ba,hajiya ce tayi caraf ta amshe zancen "YAZEEDU dakai fa ake...Kayi shiru baka amsa ba,shin baka ji abunda aka fad'a bane..??" Jajayen idanunsa ya d'ago ya kalleta kafin ya furta "Na ji hajiya..!" "Zance banza kenan..Kana ji da kayi shiru kamar ba kai ake yiwa magana ba,ko kuwa duk salon rashin mutunci ne yasa ka aikata hakan..??" Kai ya fara girgizawa,YASEER kuwa dake gefensa zuwa wannan lokacin ya gama cika fam dan haushin da YAZEED ya bashi ko motsin kirki ya gagara yi bare asa ran zai iya yin magana "Ko kad'an ba haka bane hajiya.." "To idan ba rashin mutunci ba taya mahaifinka zai yi maka magana amma ka kasa bud'e baki ka bada amsa..?? Shin abunda kake kana ganin kyautuwarsa ne..??" Nanma kai ya girgiza kafin yayi ajiyar zuciya mai nauyi yana kallon mahaifiyarsa data kafe shi da ido tana kallonsa kawai "Nifa hajiya nima damuwata ba akan auren da aka ce nayi bane.." "To muna saurarenka ai sai kayi mana bayanin ko akan mene..??" "Gaskiya hajiya ni yarinyar ce bana so kwata²,idan da ace wata ce daban kuka zab'a min babu abunda zai hana ni bin umarninku,amma dai wannan...Bata minba sam.." Bud'e baki hajiya tayi tana salati gami da tafa hannaye,cikin jimami da takaici ta kallo maimartaba "Ince dai ko yanzun kaji abunda yake fad'a..?? Jikar tawa ce bazai iya aura ba..?? Amma duk sauran y'an mata zai iya..?? Shi kenan naji wannan daga bakinka,sai dai ina so kasa a ranka kamar yadda na isa da ubanka,kuma na isa nasa shi yayi ko ya bari,na san shima ya isa ya saka kayi ko..?? Ina so ka sani na rantse da Allah duk duniyar nan kamar yadda ka nuna baka sonta ni kuma banga abunda zaisa a fasa wannan...!" "A'a hajiya kada kiyi saurin rantsuwa akan abunda baki da iko akan zartar dashi ko hanawa,dan nima kaina nan tun farko na riga nayi rantsuwa da mahaliccina akan ko duka duniya zasu taru akaina na lallai saina aureta tofa bazan tab'a yin hakan ba,in tak'aice miki ma k'arshen zancen shi ne,ko da ace daga ni sai ita ne zamu rage a fad'in duniyar wallahi thumma tallahi thumma billahi banga dalilin da zai sa na zauna da ita k'ark'ashin inuwa guda b...!" Saukar mari da k'ararsa su suka karasa katse maganar da bata riga ta fito ba,ko daya d'ago dan ganin wanda ya aikata hakan nan take idanun sa suka sauka kan fuskar mahaifiyarsa dake tsaye akansa,idanunta cike da matsanancin fushi take binsa da kallo "Tur da irin wannan munanan d'abi'un naka YAZEED,shin wane zunubi na aikata haka da rayuwarka take k'ok'arin rikid'ewa daga ainihin tarbiyyar dana baka..Shin baka jin kunya ne ace agaban idanun mahaifinka ka dunga mayarwa da mahaifiyarsa magana..?? Wannan shi ne abunda ka koyo a cikin halin mutanen daka zauna tare dasu..??" Numfashi taja tana kallonsa had'e da girgiza kai cikin takaici kafin taci gaba da magana "Matuk'ar kana so na yafe maka abunda ka aikata,matuk'ar kana neman albarkata,idan har kuma nima ka d'auke ni da muhimmanci kana ganin duk abunda nace zaka yi ba tare da musu ba,ina so kabi umarnin mahaifinka akan yarinyar da yake so ka aura..wannan shi ne kad'ai abunda zan iya baka umarni akansa...!" Ba tare daya d'ago ba daga kallon k'asan daya ke ya furta "Idan har wannan shi ne umarnin ku a gare ni akan lallai saina auri wacce nasan bazan tab'a k'auna ba har duniya ta tashi..Ina mai baku hak'uri akan tabbatar muku da cewa har yanzun ina nan akan bakana,bazan tab'a janyewa daga kan k'udurina ba,idan har umarninku yana kan wannan maganar ne,na tabbata bazan tab'a iya aikata abunda kuke soba matuk'ar akan wannan ne.." Mamaki gaba d'aya ahalin gidan suke na yadda akayi wannan al'amari yake faruwa haka,duka babu wanda baisan waye YAZEED ba,amma dalilin da yasa shi aikatan hakan kad'ai suke son ji daga gare shi.Juyin duniya anyi da shi akan ya fad'i hujjar da tasa shi bayyana k'in amincewa da Aisha da yayi,sai dai abun y'anci tura,duk iya yadda aka yi da shi akan maganar sam yak'i fad'a,bak'in ciki ne ya cika zuciyar maimartaba da gaba d'aya sauran al'ummar gurin,dan hatta da YASEER zuwa yanzun abunda YAZEED en yake yi yana k'ona masa rai,cikin b'acin rai GALADIMA ya kallo maimartaba yana cewa "Yaya ina ganin abunda ya dace ayi kawai yanzun,tunda har Allah yasa ya nuna mu bamu isa mu bashi umarni yabi ba,abunda ya kamata shi ne mu rabu da shi ya kawo mana wacce yake so,idan yaso ita Aisha'n tunda har ya furta baya k'aunarta ni ina ganin kawai me zai hana a had'a aurensu da YASEER gudun kada muji kunya a idon ita Adda'n da sauran al'ummah.." Wata irin zabura YASEER yayi tun kafin GALADIMA ya kai aya yana fad'in "Abba dan girman Allah kayi min rai..!" Duka parlour'n ne suka maida hankalinsu kansa saboda abunda yayi shima ya matuk'ar basu mamakinsu dan ko basu yi tsammanin ganin hakkaan a tare da shu ba shima,ga YAZEED kuwa wani murmushi yayi mai ciwo cikin ransa yake fad'in "Wannan shi ake kira da ank'i cin biri anci dila.." Kallonsa GALADIMA yayi yana zabga masa harara kafin cikin fushi ya fara masa fad'a "Wato bakinku d'aya kenan..?? Kaima en zaka aikata abunda yayi ne yanzun..?? Tabbas hausawa sunyi gaskiya da suke cewa "zama da mad'aukin kanwa shi ke kawo farin kai." Lallai kuslwa wannan magana tasu akwai hikima a cikinta,dan kuwa muma ga shinan munga zahiri kuma mun tabbatar,sai dai abunda baku sani ba shi ne,matuk'ar wannan abun da kuke babu wata hujja da zata bayyana mana dalilin da yasa kuke wannan shirmen,babu abunda zaisa mu tsallake abunda mukayi niyya,dole ne idan d'aya a cikinku yak'i d'aya saiya karb'a...! " "A'a Aliyu ko kusa wannan magana taka,ba abune da zai yiwu ba,tun farko maganar YAZEEDU akayi ta yaya lokacin d'aya dan ya nuna baya ra'ayi zamu maida maganar kan YASEER,ai wannan ma dole ya karb'a ko yana so ko baya so,idan kuwa ba haka ba to babu ni babu zuri'ar ku zan zuba musu iso duk abunda suke so suyi..Amma dole ne kai d'an Abdu ka tursasa shi ya karb'a ko da idan an d'aura masa ita zai dinga yankar naman jikinta ne d'anye,amma dole ne ya zauna da ita.." Juyowa YASEER yayi ya kalleshi cikin takaici na abunda yake faruwa da muguwar jayayyar da aketa fama sama da awa guda duka a dalilinsa amma an kasa shawo kan matsalar,haurinsa YASEER yayi cikin b'acin rai yana yi masa magana k'asa² yadda shi kad'ai zaiji me yace "Dallah malam wai kai ganin wannan abun kake a matsayina mafita..? Tun d'azun ka fad'a musu abunda ke faruwa ka tsaya sai musu ake da kai,nifa idan bazaka magantu ba wallahi zan tona dan bazaka janyo min bala'i ban shiryar ba,garama kawai kowa ya san halin da ake ciki,dan ni banga amfanin tsayawa ayi shiru ba,kak'i fad'a kuma kak'i barina nima na fad'a,me kenan hakan yake nufi...??" Harara ya banka masa cikin jin haushi ya furta "To ba saika fad'a ba en,idan banda kai sakarai ne taya zan fito na fad'a musu ga asalin abunda ya hanani amincewa..?? Su da suke iyayena da suka ga ina ja da maganar ai ya kamata ace sun fahimci akwai matsala,amma tunda basu gano hakan ba,nima banga amfanin sanar musu ba,gara kawai na nuna bazan amince enba amma bazan tab'a iya kallon idanunsu na fad'a musu wannan maganar ba.." "Haka kace ko..? To wai kai inbanda ma kai ni wallahi ban tab'a ganin bahago irinka ba,mutum banda tsabar taurin kai babu abunda ya iya,ana nuna maka mafita amma kai ka dage gani kake abunda kake shi ne mafita,Allah yasa su tilastaka saika zauna da ita maga ta tsiya.." Take masa k'afa YAZEED yayi yana zare ido waje alamun warning akan maganar da yake masa,y'ar k'ara YASEER yayi yana ture k'afar YAZEED en wanda hakan yaja hankaalinsu GALADIMA kansa,nan aka fara tambayarsa meya faru..? 'Dan murmushi yayi na yak'e kafin ya bada amsa "Babu komai.." Wani uban kallo GALADIMA ya jefe shi da shi "Babu komai kake mana ihu..?? Yau naga shashancin banza,indai ba wani abu ya faru ba haka nan ka samu a gaba kana mana ihu,ka shiga hankalinka kafin na sab'a maka,mutumin kawai.." Kansa ya sunkuyar k'asa yana girgiza kai wa YAZEED alamun zai rama,juyowa hajiya tayi ta kallesu cikin jin haushinsu duka tana fad'in "To zaman me kuke kuma a nan..?? Tunda kun nuna kunfi k'arfinmu ai saiku tashi ku bamu guri,ma nemi wanda zamu iya basu umarni subi.." "A'a hajiya babu inda zasu,ai matuk'ar kika ga sun bar nan to wallahi sai dai ya kasance d'aya cikin su ya amince,idan kuwa ba haka ba sai dai su nemi wasu iyayen amma bamu ba tunda sun d'auki abun wasa..!" Ummi tayi maganar tana jifansu duka da mugun kallo musamman YASEER da take ganin laifin sa a lokacin ma musawa maganar mahaifinsa da yayi,cike da rashin samun nutsuwa YASEER ya kalli YAZEED da shi har lokacin duk maganganun da ake ko d'aya babu wacce tasa shi yin gezau,bugu YASEER yakai masa da hannu cikin d'aga murya yana fad'in "Dallah malam ka fad'a musu ko wace yarinya ce suke sai lallai sun had'a d'ayanmu da ita,taya muna gani za'a aikata mana haka kai kuma ka kafe kamar ginannen dutse kai bazaka fad'a ba kuma kak'i bari na fad'a ni...!" Kallon² aka fara tsakanin iyayen da su,YAZEED kuwa jin abunda YASEER ya fad'a,nan take yasa shi runtse ido yana jan wani irin numfashi,cikin takaici ya kalli YASEER en yana zuba masa harara "Kai me yasa baza'a tab'a yin sirri da kai dole saika fad'a..? Me yasa tunda nace mu bar maganar a tsakanin mu bazamu barta ba..??" "Saboda barin nata bazai tab'a amfanarmu da komai ba sai b'acin rai,shin baka ga yadda kasa kowa fushi bane akan maganar da matuk'ar suka san gaskiya suma babu dalilin da zaisa su dage sai wani cikinmu ya aureta..!" Tsawa GALADIMA yayi musu cikin fushi ya kallesu yana tambaya "Wace gaskiya ce kuke b'oyewa kuka k'i fad'a tun tuni..?? Shin zaku sanar damu ko kuwa sai ranku ya b'aci duka..??" "Abba babu komai fa,tsakanin mune dama muka samu wata y'ar matsala ta rashin fahimta.." YAZEED yayi maganar yana kallon YASEER "K'arya yake Abba babu wani rashin fahimta,kawai yana sone nayi shiru kada na fad'a muku dalilin sa na k'in amincewa da auren.." Kallonsa GALADIMA yayi da mamaki kafin yayi magana "Kai en ka sani tun farko amma kaja bakinka kayi shiru kana kallo tun dazun sai tak'addama ake akan ya fad'a yak'i..?" "Ina neman afuwarku Abba..Amma banyi haka da son raina ba sai don kawai na bari ne naga ko shi en zai fad'a da kansa.." "Kai muke sauraro ka fad'a mana abunda ka sani.." Maimartaba yayi magana cikin rashin walwala "In sha Allah yanzun kuwa Abiiy...Alal hak'ik'a Abba tun farko nayi shiru ne da maganar alhalin na san gaskiya,ba don komai ba sai don shi daya sani b'oyewa akan dalilin baya son ku kalli kawunanku a matsayin masu laifi a karo na biyu cikin abunda ya shafi rayuwarsa..Tabbas a maganar aure nan ko da kuka zo masa da ita ni shaida ne akan ya amince zai auri wacce kuka zab'a masa ko da baya sonta,sai dai ita wannan da kuka so aura masa a wannan karon duk da kasancewarta zab'in ku ya bijire ne ba don komai ba sai don kasancewarta mutum ta farko data fara yi masa bak'in tambari,bugu da k'ari itace wacce tun farkon rayuwarsa ta rusa duka wani walwalarsa gami da farin cikinsa,itace wacce a tarihinsa ta janyo masa fushin mahaifinsa,tasa aka hukunta shi ba bisa k'a'ida ba,ta kuma sa al'ummah gaba d'aya suka dunga jifansa da wani irin kallo na mutumin banza...Shin Abba idan har yayi wancan maganar bisa kuskure kamar yadda kuke gani har ta janyo kunji ba dad'i,ina kuma ga shi wanda al'amarin yake neman faruwa da shi..? Duk tarin bak'in cikin data haifar masa a baya shin bai isaba sai an kaiga k'arasa rusa masa rayuwa..?? Shin irin wannan matar ce ta kamaci mutum kamarsa..??" Shiru gaba d'aya parlour'n ya d'auka banda muryar YASEER dake tashi "Idan har munyi kuskure bisa bijire muku da muka yi tun farko,muna masu neman afuwarku a yanzun a bisa sanin gaskiya da kuka yi wacce muka b'oye tun farko.." Hannu maimartaba ya d'aga masa alamun yayi shiru kafin ya juya ga YAZEED cikin wani irin yanayi na sanyin jiki da kalamai yana fad'in "Shin YAZEED abunda d'an uwanka ya fad'a gaskiya ne..??" Sai da yaja numfashi kafin ya d'ago yana kallon YASEER shima jikinsa a sanyaye da cewa "Haka ne Abiiy... Amma.........................!" #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@Hawwa M.U Pindiga.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻* ___________________ *Just when I'm about to part with my friends is when I realize that I had the best group of friends ever...#Asma'u Sanee (asmalurv),Fa'iza Anfa,Mmn Fareesah,Kadija Usman (real khadee4life),Ameerah Muhammad,Fatima Umar Muhammad (Maman Weedad),Khadija S.Ibrahim (Mmn Amatullah),Maimuna Aliyu,Momn Sultan,Hanifah Y'ar Amana,Firdausi Muhammad Mainasara (Feeby),Asma'u Aliyu Ahmad,Safeena Muhammad & Lashminzy.* *Pg 27.* ^^^^^^^^ Hannu maimartaba ya d'aga masa yana dakatar da shi gami da girgiza masa kai,cikin murya mai rauni ya dakatar da shi "Ya isa haka ba sai ka k'arasa ba..!" Shima ko kafin yaci gaba da magana tuni hajiya ta kalli maimartaba cikin rashin fahimtar inda maganganun suka nufa ta fara magana "Wai d'an Abdu mene ne yake faruwa ne haka da ban sani ba..Shin da bana nan wani abu ya faru amma kuka kasa sanar dani..??" Shiru duka suka yi ba tare da sunyi magana ba "Ku sanar dani mana kuka yi shiru kuna sunkuyar da kai k'asa.." K'wak'wk'waran motsi an kasa samun maiyi a tsakaninsu,sai kallon kallo kawai da suke a tsakaninsu,juyawa hajiya tayi kan jikokin nata ta kallesu kafin ta tsaida idonta akan YASEER "Kai d'an albarka zo ka fad'a min nan tunda iyayen naku su basa so na sani.." 'Dagowa YASEER yayi ya kalleta yana nuna kansa,girgiza masa kai tayi tana tabbatar masa da shi en take,nanfa shima ya waiwaya ya kalli Ummi'nsa kana ya juya ga YAZEED,idon yariman akansa ya kafe shi da ido yana jiran yaya mai zai yi,d'auke kansa yayi ya juya ga hajiya cikin wani irin yanayi ya furta "Hajiya kiyi hak'uri dan Allah,amma bani ya kamata na sanar miki ba,idan kuma har nace zan fad'a yanzun nasan kawai zanyi rashin kunya ne tunda suma su Abba basu sanar dake ba.." Rik'e baki hajiya tayi tana kallonsa da jinjina abunda ya fad'a,ko da ganin an rasa mai sanar mta,kawai sai hajiyan ta shammacesu ta rushe musu da kuka,cikin kuka ta fara magana "Shi kenan kuma ni tawa ta k'are,duka saboda bakwa sona shi yasa kuke min haka,yanzun ace gaba d'ayan ku wani abu ya faru dan bana nan sai a kasa sanarmin,shi kenan ai duk dan bani da muhimmanci ne shi yasa..Allah ya kawo sanadin da zan tafi na barku ku huta tunda haka kuke fata.." Jigum² suka yi suna kallon hajiya,cikin kwana kin kam gaba d'aya banda rikici babu abunda take musu,YAZEED da YASEER ne suka yi k'arfin halin nufarta suna bata hak'uri,da kyar suka samu kanta tayi shiru tana goge fuskarta "Dan Allah hajiya kiyi hak'uri,wannanfa duka wani al'amari ne daya faru a shekarun da suka gabata,wanda na tabbata tun a lokacin da wani ya sanar miki cewa zaki yi a dawo dake gida,wanda mu kuma munsan matuk'ar kika dawo lamarin zaisa ki tada hankalinki,shi yasa kawai muka yi shawaran ki zauna can zuwa wani lokaci.." "To ni d'an Abdu idan bazaka fito ka sanar dani wannan maganar da kake ta k'umbiya² akanta ba ai gara ma baka fara bani labarin ba.." Girgiza kai maimartaba yayi yana d'an murmushi kafin ya soma warware mata duk abunda ya faru a lokacin data tafi umrah,wanda ta silar faruwar al'amarin ne maimartaba yasa aka barta can k'asa mai tsarki har na tasawon shekaru da sunan ta samu hutu a can kafin wani lokaci,lokacin daya gama bata labarin tuni har ta gama zuwa wuya,tsabar fushin da take ciki a lokacin kamar zata fashe,wayar ta kawai suka ga ta d'auka cikin abunda bai wuce shud'ewar sa'o'i ba ta kara wayar a kunnenta,y'an mintuna tsakani ta fara magana cikin fad'a² "Wato Adda dama kin san abunda kuka shuka shi yasa kuke so yanzun mu had'a yaran nan aure...? Wato wannan karon saboda kunsan illar da kukamin shi ne kuka juyo ta wannan hanyar ko,duk dan ku sake rusa rayuwar yaron da kuka zalunta shi yasa kika biyo ta hannuna dan nasa a tursashi ko da baya so sai ya aureta...To wollahi bazai yiwu ba,maganar aure ce nima da kaina na fasata daku ko da kuwa ita ce autar mata banga me YAZEEDU zai yi da ita ba,cikin manemanta da take ik'irarin tana da sai ku duba mata wani ku aura mata,amma jikana kam wollahi yafi k'arfinta.." Tana zuwa nan ta katse kiran Tana huci kamar wadda tayi dambe,sai data d'auki lokaci a haka kafin ta tsayar da kallonta kan YAZEED da shi ko kula da abunda hajiyan keyi bai yiba,cikin sanyin jiki ta kira sunansa tana dafa kansa da yasa shi saurin kallonta "Kayi hak'uri kaji YAZEEDU ka yafemin,tun farko bansan haka abu ya faru ba,kuma cikin iyayenka babu wanda ya fad'a min ko da wasa,da ban tursasaka ba tun farko...Kayi hak'uri kaji d'an nan,Allah yabi maka hak'k'inka yayi maka canja mafi alkhairi Ubangiji ya k'ara tsareminku baki d'aya..." Murmushi kawai ya iya yi mata had'e da lumshe idonsa,sannan ya d'auke kansa daga kallonta da yake,maimartaba kuwa tunda YASEER ya bud'e aiki ya kuma tabbatar haka maganar take sai yayi shiru ya kasa cewa komai,saboda yadda yayi fushi da fari akan maganar da irin abunda YAZEED en ya dunga yi yanzun duk sai yake jin bai yiwa d'an nasa adalci ba a karo na biyu,ga Fulani ma haka ce ta faru,itama tun data ji maganar ta koma wata shiru sai binsa da kallon tausayi kawai take ta kasa fad'in komai,da kyar maimartaba yayi gyaran murya kafin ya fara magana "Da farko dai zamu fara da ban hak'uri ga hajiya bisa b'oye miki wasu al'amura da suka faru a baya,da har hukunci ya biyo baya duka ba tare da mun sanar miki ba,sai dai hakan ya faru ne a sakamakon bamaso ki d'aga hankalinki kasancewar lokacin ba cikakkiyar lafiya ne gare ki ba,saboda haka muna k'ara neman afuwarki,tabbas munsan munyi laifi amma ayi mana afuwa.." "Ai babu komai tunda yanzun na sani,kuma alhamdulillah! Da Allah yasa dukanmu bamuyi gaggawa ba wajen hukunta yaron nan,tabbas da ko Ubangiji na tabbata bazai yafe mana ba,saboda mun zalunce shi matuk'ar da ace mun tursasashi sai ya auri tambad'ad'd'iyar yarinyar,amma mu godewa Allah da bamu had'a iri da ita ba.." Sun d'auki lokaci mai tsayi suna sake gutsira maganar kafin hajiyan ta fara sallamar su YASEER,fitowarsu a cikin b'angaren nata basu zarce ko ina ba sai nasu apartment en ba tare da wata magana ta shiga tsakaninsu ba har suka isa sai dai kowannensu daka kalleshi zaka gano yanayin farin cikin dake shimfid'e saman fuskokin nasu. ^^^^^ Can a gidan Adda kuwa lokacin da hajiya ta kirata dawowarta kenan daga hajj camp,sanda ta ajiye wayar cikin b'acin rai ta waiwaya inda ladidi take tana kallonta kafin ta magantu "Ladidi shin me kuka yi da kuke b'oyewa bakwa so na sani..?" Ta jefeta da tambayar,kame² ta fara nan Adda ta kafeta da ido tana kallo "Shin zakimin bayani ne ko kuwa saina b'ata miki rai..??" "Adda nifa banyi komai ba..Wani ya kiraki yace nayi wani abu ne..??' Kallonta

Chapter 21 of 63