ka fad'a zan bi komai a sannu har na gama fahimtar yadda al'amura suke.."
Kafad'arsa YASEER ya dafa yana jinjina masa kai cike da fara'a sannan ya fara magana cikin tsokana
"Ohh! Broah! It's time to walk up for a ride!"
Saurin kallonsa yayi yana yamutsa fuska
"To where are u talking about..??"
"Gurin amaryarka mana..! Ko har zaka cemin ka manta da ita ne..??"
Wani uban tsakin daya ja yasa YASEER saurin katse dariyar da yake yi a lokacin sannan ya nemi guri ya zauna yana shirin yi masa magana
"Kada ma kace min komai dan ni babu inda zani daka ganni a nan,idan zaka kama hanyar tafiya ne kai kad'ai kaje amma ni babu inda zani.."
Cikin rashin fahimta YASEER ya zaro ido jin yadda YAZEED yayi saurin katse shi daga maganar da yake shirin yi
"Me kake son cewa kenan broah..??"
"As soon as your ears are heard,shi nake fad'a kuma shi nake nufi.."
"A'a..! A'a..! Broah sam baza ayi haka ba..Shin idan kace haka me kake so su Abiiy zasu yi tunanin..?? Ko kuwa kana ganin hajiya da Ummah Fulani idan maganar ta koma kunnensu zai yi farin ciki da cewar d'an da suke tak'amar yana bin umarninsu ne ya aikata abunda doke suji kunyarsa matuk'ar aka ce ya koma kunnen iyayen yarinyar nan..?? Beside ma tun farko fa kai ka bada zab'i kace a zab'a maka ko wace ce matuk'ar ba wannan yarinyar ba,me yasa yanzun kuma zaka biyo ta wannan hanyar..?? Shin har ka manta ne da AL-K'AWARIN da kayi a gurin d'aurin aure..?? Na kiyaye dukkan hak'k'ok'inta akanka..? Ko kuwa tun daga yanzun ne zaka fara shirin rusasu..??"
Shiru yayi yana sauraren YASEER
"Sam broah..! Wannan ba halinka bane sab'a umarnin mahaifa ko karya alk'awari,dan Allah ka tashi ka shirya muje kaji please...!"
Shirun da yayi yasa YASEER shima yin shirun yana binsa da kallo,ya d'an d'auki wasu y'an sakanni kafin ya mik'e yana yi masa murmushi.
^^^^^
A b'angaren su Aisha kuwa lokacin da suka koma gida daga gurin dinner dan hatta da itanma ba'a barsu a baya ba,suna tafe suna sake tattauna yadda al'amura zasu wakana daga zaran sun samu abubuwan duk da suka tsarawa sun tafi musu a yadda suke buk'atan su.
Yadda Adda take nunawa a fili,dangane da b'acin ran dake taso mata lokaci zuwa lokaci,yasa Aisha jin ba zata iya hak'uri ba har sai ta kaiga tambayar Adda'n 'SHIN WANE IRIN LAIFI NE GIDAN SARAUTA SUKA MATA HAR HAKA..??' Ni kuwa dai nan take nayi hamdala ga ubangiji dan a lokacin ji nayi kamar Aisha ta shiga raina dama sauran al'ummah mabiya littafin *WANI AL'AMARIN* dan yadda muke ta son jin yadda aka yi aka haihu a ragaya.Lokacin data yiwa Adda tambayar,shiru Adda tayi tana kallonta na wani tsayin lokaci kafin ta d'ago tana kallonta,cikin wani irin yanayi ta jinjina kai sannan ta fara magana
"Tabbas..! Aisha duk da kasancewar ki yarinya kuma mai k'arancin shekaru zan so na sanar dake duk abunda ya had'a ni da MASARAUTA domin kuwa kema d'aya ce daga cikinmu,ko dama ace bamu had'u ta wannan fagen ba,dole ne jini ya had'a mu dake..!"
Wata mummunar fad'uwa gaban Aisha yayi dan yadda Adda ta ambaci 'jini ya had'a su',nan take zuciyarta ta bijiro mata da tambayar
"shin me Adda ke son sanar da ni..?? Asalina take shirin fad'a min ko kuwa..??"
Kamar zata tambayi Adda'n sai kuma wata zuciyar ta bata shawaran taja bakinta tayi shiru wata k'ila hakan na nufin Adda zata iya sanar da ita har daga gidan data fito,matuk'ar tayi hak'uri taci gaba da bibiyar labarin tabbas ko bata fad'a mata ba itan zata iya fahimta da kanta,shiru tayi tana kallon Adda data d'an yi shiru na wucin gadi,sai data shak'i numfashi sannan ta d'ora da fad'in
*"ASALIN ALAK'ATA DA MASARAUTA ITACE..........."*
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
_Our thoughts are with you and your family (LEEMA) at this most difficult time of loss._
*Pg 34.*
^^^^^^^^
Hanyar bedroom ya fara nufa,sai da yaje dai² k'ofan da zata sada shi da corridor ya furta
"Wait for me to come out ...!"
Yana fad'an haka ya shige abunsa,murmushi YASEER ya saki mai k'ayatarwa sannan yayi tsalle ya d'ane saman kujera yana kwanciya,ya shafe a k'alla mintuna sama da talatin kafin Yarima YAZEED ya fito ya same shi,cikin wani d'anyen shadda shampo milk color da aka yi mata aiki da coffee en zare,sai daya kalleshi tsaf sannan ya sake sakin murmushi,cike da zolaya yake kallonsa yana fad'in
"Angon SAJIDA nd someone i do not know...!"
Saurin d'agowa YAZEED yayi daga gyara link's en da yake yi yana matsawa kusa da shi fuskarsa cike da alamun tambaya
"What do u say broah..??"
Dariya yayi mai cike da rainin wayo sannan ya wuce abunsa yana shirin shigewa bedroom,cikin sauri Yarima ya biyo shi a baya,a haka suka shiga bedroom en,dai² lokacin da YASEER yake k'ok'arin shiga bathroom Yarima yayi hanzarin rik'o shi ta baya yana dawo dashi
"Ai baka isa ba sai ka maimaita abunda ka fara fad'a..!"
"Ha'a.! Broah kana so mu makara ne..ka bari na fito zan fad'a maka koma mene nace..."
"Baka isa ba,sai dai ka fara fad'a sannan na kyaleka ka wuce..amma idan ba haka ba babu inda zaka je.."
"Please! Mana ai na ce zan fad'a ko..??"
"Kai ka sani kuma kawai dai ka maimaita.."
Dariya YASEER yayi sannan cikin jin baki fa furta
"Cewa nayi angon sajida Allah ya bada zaman lafiya.."
"K'arya ne..! Kasan dai ina ji ko,cikin kunnuwana biyu babu mai matsala ba..??"
"K'warai fa nima na san da haka,shi yasa ma na fad'a maka iya kar abunda na fad'a.."
Kallon kama rainamin hankali Yarima yake masa,cike da son tabbatar masa da abunda ya fad'a ya furta
"Kasan me kace.??"
Girgiza kai YASEER yayi yana b'oye dariyar dake neman kwace masa
"Cewa kayi..Angon Sajida ko wama take..? Da wacce baka sani ba.."
Dariyar da yake b'oyewa ya saki cike rashin sanin me YAZEED yake shirin yi masa akan b'oye masa gaskiyar abunda ya fad'a yake ta dariya abunsa,k'eyarsa yaji ya make da hannu,cikin motsawar second YASEER ya d'ago yana sakin k'ara da fad'in
"Arrgh! Mr man mene ne wannan ka bugeni da shi haka..??"
"Ohoo! Maka kawai malam ka wuce kayi abunda za kayi kada ka sani jiranka.."
"Ok sir..! An gama.."
Girgiza kai kawai yayi ya fice a bedroom en,dan yasan matuk'ar ya biyewa YASEER to zasu jima a haka ba tare daya shirya ba bare su wuce en kamar yadda ya sashi a gaba da fari na lallai sai ya wuce sun tafi ya rakashi gurin amaryar tasa.Fitowarsa da kamar kimanin mintuna talatin shima YASEER ya fito cikin shiganda irin ta Yariman babu ko bambanci,tun kafin ya iso inda yake tuni har ya mik'e ya kama hanyan fita a parlour'n,kallonsa YASEER yayi yana d'an sakin murmushi kafin ya biyo shi,a varender suka had'u yana tsaye yana jiran fitowarsa,da fitowar sa basu tsaya ba suka wuce zuwa sabon apartment en da maimartaba yasa aka gina musu nan a cikin gidan,sai dai na YAZEED shi ne daga ciki sai na YASEER kuma da saika wuce shi sannan zaka isa inda na YAZEED yake,kasancewar baya so ko kad'an ace sunyi nisa da shi shi yasa ya yanke wannan shawaran tare da taimakawar Abba GALADIMA,apartment en daya kasance mallakin YAZEED suka fara nufa,yanayin yadda gurin yake shiru babu hayaniya ya isa ya tabbatarwa da mutum babu mutane a gurin,dan kam tun kafin wannan lokacin dama maimartaba yaja kunnen jama'a akan ana raka amaren a fita a basu guri,baya so a damesu da hayaniya,shi yasama ko da aka kawo su sai aka barsu daga su sai halinsu.
Shigowar su cikin parlour'n da yake shima shiru babu kowa a cikinsa,suka nemi guri suka zauna,sun d'an d'ebi lokaci kad'an a haka ba tare da wata hira da junansu ba,kallon agogo YASEER yayi kafin ya juya ya kalli YAZEED yana tambayarsa
"Broah..! Wai tunda muka shigo ka nemi guri ka zauna,idan bazaka iya shiga kayi mata magana ba mene ne amfanin zamanmu a nan ne kam...??"
Ba tare daya d'ago ba bare ya kalleshi ya shiga bashi amsa
"Ohh! Saima na mata magana zata san da zaman mu.?"
Kallon rashin fahimta ya bishi da shi kafin yayi magana
"Me kake son cewa kenan..?? Yanzun Fisabilillah! Idan har baka yi mata magana ba taya za'ayi ta san da zamanmu..??"
""Ohoo! When she gets tired she comes out."
"A'a! Broah baza ayi haka ba..Yanzun abunda ya kamata kaga babu lallai ace taji motsin shigowar mu,beside ma kaima da kanka kasan ba kasafai muke iya bambance d'ayan mu ya shigo ba ko da can,to kaga yanzun ma,ya kamata ace kayi mata uzuri itama,ka tashi ka dubata saika sanar mata da zuwanmu ko ba haka ba..??"
Shiru yayi kamar mai mazari,zuwa can kuma ya mik'e yana jan tsaki,sannan ya kama hanyan da zata sada mutum da d'akunan baccin nasu,k'ofar bedroom d'in daya gani a bud'e,ita ya fara nufa gadan-gadan ba tare da tunanin komai ba,ko kawo wani abu a ransa,ita kanta sajida a lokacin sam bata yi tunanin cewar sun shigo ba,dan haka ko a sanda aka kawota da aka fice aka barta cikin k'aton apartment en da babu kowa daga ita sai halinta,haka nan a lokacin tana lullub'e cikin alkyabba sai duk ta fara jin zafi na damunta,da kam kamar ta hak'ura ta zauna a haka ta jira har zuwa sanda zasu shigo,sai dai kuma ko da taga lokaci na sake tafiya,cikin haka da taji shirun yayi yawa sai kawai ta mik'e abunta ta hau cire kayanta da niyyan shiga ta sakarwa jikinta ruwa,sai data gama cire kayan har ta d'auko towel da zata d'aura ta ajiye shi nan bakin gadon tana k'arasa cire kayan,shi kuma ya kawo kai a dai² lokacin da tana tsaye daga ita sai pant da bra,sanda ya iso har ya d'aga hannusa da niyyan zaiyi nocking ya hangota tsaye tana facing k'ofa,tamkar irin y'an good evening d'in nan haka ta koma masa,nan take kuwa ya tsareta da mayun idanunsa yana bin ko wane sura na jikinta da kallo,jin yadda temperature d'in sa ke neman sauyawa cikin k'ank'anin lokaci da kallonta kad'ai da yayi yasa shi saurin juyawa zai bar gurin,d'agowa tayi itama jin kamar alamun motsi nan kuwa ta hangoshi yana komawa ba tare da yayi magana ba,saurin d'aukan towel d'in tayi ta d'aura a jikinta kafin ta d'an bud'e muryanta yadda tasan zai jiyo tana kiransa
"Yah Prince..!"
Kiran da tayi masa shi yasa shi dakatawa a inda yake ba tare daya juyoba bare ya kalleta ya furta
"Ki sameni a parlour ina jiranki..Nd ki suturta jikin ki..Ba ni kad'ai bane..!"
Wani murmushi ta saki mai k'ayatarwa jin abunda ya fad'a,nan take ta amsa masa cikin sauri da "toh",yana barin gurin nan take sajida tayi tsalle ta fad'a kan royal bed enta tana sakin murmushi had'e da rufe ido alamun jin kunya,tabbas tasan ko ba'a fad'a mata ba daga jin furucin da Yariman yayi tasan ya riga da ya gama ganin ta babu kaya,wata zuciyar ce tayi hanzarin tunatar da ita sak'on daya fad'a mata tun kafin tayi nisa a tunani,nan tayi saurin mik'ewa ta shiga maida kayan jikinta sannan ta maida lullub'inta ta fita,cikin zuciyarta kuwa sai godiya take yiwa Allah daya bata miji mai kishinta,tabbas tasan da ace wani ne ba shiba to fa babu ko tantama ba lallai ne ya tunatar da ita abunda ya kamata tayi ba kafin ta fito,dan idan ta wani ne ma ta fito tsirara ba abune da zai dame shi ba,musamman ga irinsu da auren su ya zama kamar na had'i.
A parlour ta tarar da su zaune shi da YASEER,kanta a k'asa har ta k'araso ta nemi guri ta zauna,sannan ta gaida su duka,YASEER dai ya amsa mata,amma gogan tunda ya dawo ya d'ora k'afa d'aya a kan d'aya naga alamun sarauta ta motsa,idonsa ya kai kanta a inda take zaune ta wani sunkuyar da kai kamar ba ita ya gani yanzun tsirara ba(amma fa acewar sa),haka nan kawai tun daga kallon da yayi mata sai ya fara jin wani irin bak'on al'amari na ratsashi a tare da ita daya kasa fahimtar ko na mene ne,tun daga kallon farko da yayi mata ya kafeta da ido ko da wasa bai iya janyewa ba,har zuwa sanda YASEER ya tab'a shi da fad'in
"Broah.! Zan wuce..Ina yi muku fatan alkhairi Allah ya bada zaman lafiya..!"
Wani wawan ajiyar zuciya Yariman yayi dan tun data fito,baya tunanin zai iya kawo kalma d'aya da YASEER en ya fad'a a bayan maganar da suka yi da shi kafin zuwanta,wato dai wannan shi yake nuna duk b'ab'atun da YASEER d'in yayi baima san yayi shi ba kenan.Mik'ewa yayi shima ya dafa masa baya suka fita tare ita kuma suka barta a nan tana dakon jiran dawowar sa,sun d'auki lokaci mai tsayi da fitarsu kafin Yariman ya sake shigowa shi kad'ai,sanda ya shigo sam baiyi tunanin har lokacin zai dawo ya isketa a zaune a gurin ba,amma ga mamakinsa sai ya dawo ya sameta har lokacin tana zaman jiransa.
Yana shigowa yayi addu'o'i sannan ya maida k'ofar ya rufe,ya dawo cikin parlour'n yana kallonta da mamakin abunda ya zaunar da ita har lokacin
"Barka da dawowa Yah Prince..! Ka dawo lafiya..??"
Yamutsa fuska yayi yana shirin bata amsa,sai kuma yaji ba zai iya fad'an wani magana da bai dace ba a gareta,dan da amsan da yayi niyyan bata matuk'ar taji ba zata ji dad'i ba,can a k'asan mak'oshi ya amsa da
"Lafiya..!"
Sannan ya wuce ta a gurin,cikin siririyar maganarta ta sake furta
"Ina yi maka fatan tashi cikin amincin Allah,tare da fatan Ubangiji ya sadamu da alkhairinsa..!"
Kamar wanda aka dannama pause haka ya k'ame a gurin,cikin wani salo ya d'an waiwayo ya kallo inda take,kanta har lokacin yana k'asa tana wasa da yatsun hannun ta,tamkar ba ita tayi maganar ba haka ya gani,sai dai sanin muryanta yasa shi gane hakan,d'an murmushi ya saki sannan ya furta
"Ameen..! Na gode k'warai.."
Daga haka bai ko k'ara wasalin 'a' ba ya bar gurin.
^^^^^
"Asalin labarin alak'a ta da MASARAUTA,zan iya ce miki alak'a ce irin ta jini da kuma haihuwa,kamar yadda kika ga muna yawan zuwa gidan sarauta matuk'ar ace babu wata dangantaka a tsakaninmu babu yadda za'ayi a barmu mu shiga duk inda naso a gidan,kamar yadda kika san sunan sarki na yanzun MUHAMMAD BIN ABDULLAH BIN MUHAMMAD (ABU YAZEED),mun had'a alak'a da Abu YAZEED ne ta b'angaren kakansa wato SARKI MUHAMMADU,wanda shi Abu YAZEED yaci sunan yayan mahaifinmu,ni da ABDULLAH mahaifin sarki na yanzun wato Abu YAZEED da kuma hajiya hauwa,mun kasance y'an uwan juna da muka had'u ta tsatso d'aya,daga b'angaren mahaifinsa wato sarki muhammadu kaka ga sarki Abu YAZEED,kasancewar da mahaifinmu da kakan shi sarki da suka kasance yaya da k'ani wanda suka fito ciki d'aya,Amma bari na miki yadda zaki gane,shi sarki muhammadu da kika ji ina fad'a ya kasance ya auri mata uku,Hajiya Hafsatu itace uwar gida ga sarki sannan kuma ita ce Fulani babba,sai dai kasancewar bata tab'a haihuwa ba yasa ba'a samu magajin sarki ta b'angarenta ba,sai a b'angaren matarsa ta biyu wato hajiya Maryam y'a ga sakin hadejia SARKI ABDUL-KARIM,wacce ta kasance ta haifawa sarki y'ay'a biyar,duk da Abdullah ba shi ne Babba a gurinta ba,amma zamu iya cewa shi d'in ne babban saboda gaba d'aya a gidan shi ne d'a namiji na farko da aka fara samu,bayansa kuma sai y'an uwansa mata hud'u da suka fito ciki d'aya,matar sarki ta uku wacce ta kasance amarya a gurinsa ita ce mai yara hud'u mata biyua da kuma maza biyu,mu kuma a gidanmu wato gidan k'anin sarki Muhammadu,a gurin mahaifinmu mata biyu ne mahaifiyarmu itace babba,sai kuma mahaifiyar su hajiya Hauwa wato mahaifiya ga sarki ABU YAZEED,duka a gurin mahaifinmu y'ay'a kawai mu kimanin sha Uku ne,mahaifiyarmu nada y'ay'a takwas mata mu Uku saimaza biyar,hakka ma a gurin amaryar mahaifinmu wato mahaifiyar su hajiya kenan,ita kuma tana da yara biyar har da hajiya hauwa a ciki,sai dai su a d'akin su ita kad'ai ce mace kuma ita ce Babba,ina fatan kin fahimci yadda alak'ar mu ta fara samo asali,kafin mu gangara kan labarin yadda al'amarin mu ya faro..??"
Cike da son Adda taci gaba da bata labarin ta gyad'a mata kai kawai,itama Adda'n jinjina kai tayi sannan ta saki numfashi kana ta d'ora daga inda ta tsaya
"Duk da bawai labarin alak'ar mu da juna yasa muke zaune a nan ba,na baki wannan gajeran tarihi ne ba don komai ba sai don ina son ki fahimci inda labarinmu ya nufa,kamar yadda kika ji alak'ar mu,yanzun bada b'ata lokaci ba zan sanar dake ainihin gagarumin laifin da aka yi min a wancan lokacin da har ya janyo raina ya b'aci na yanke wa zuciyata manufar d'aukan FANSA da nayita d'akinta har tsayin wad'annan shekaru.."
*SHEKARU TALATIN (30) DA SUKA GABATA.*
A zamanin mulkin sarki Abdullah,a kuma lokacin samartakar Sarki Abu YAZEED (the current emperor) a shekaru talatin da suka gabata,lokacin da nayi aure Allah ya azurtani da samun k'aruwa ta y'a mace a haihuwata ta fari wacce kuma daga ita ne ban sake samun haihuwa ba,har kawo wannan lokaci,wannan y'a tawa da naake baki labari kuwa ba kowa bace face ASMA'U (LADIDI),tun a lokacin dana haifi ladidi na kasance tun a bayan tasowarta sai Allah ya sanyawa zuciyata sha'awar na aurar da ita a gidan sarauta ko ga wani mai mulki,sai dai kash kamar yadda al'amarin ya faru akanki itama kwatankwacin haka ce ta faru da ita,sai dai akwai bambanci mai nisa a tsakanin naki rushewar auren a wannan karon da kuma nata...............!"
*RASHIN MAIDA HANKALI AKAN COMMENTS YASA NI KAINA NA FARA JIN K'IWAR TYPING WOLLAH..! ND KUN SAN LOKACI NA DAD'A GABATOWA,DA ZAN TAFI HUTU...IN SHA ALLAH.*
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Pg 35.*
*LAST PAGE*
*BOOK 1.*
^^^^^^^^
Dogon numfashi ta sauke tana kallon Aisha data k'ure ta da ido,kafin taci gaba
"A lokacin da ladidi ta samu damar kammala karatun secondary,duk da ban fito fili na nuna kwad'ayin abunda ke raina ba,na tabbata a lokacin ba za'a rasa wanda zai fahimci nufina na yawan aikata masarauta da nake yi ba,dan kusan kullum ne sai na san yadda nayi na k'irk'iri aiken da zaisa taje masarauta,a wannan lokacin duk tunanina da tsari na ina yinsa ne badon komai ba sai don ina so ace Abu YAZEED ya ganta,har yaji ya aminta da zab'arta a matsayin matar aurensa,sai dai kash ina nawa tsarin ne kawai amma a gurin hajiya Hauwa mahaifiyarsa tuni har tayi masa mata,inda ta zab'a masa y'ar aminiyarta,wannan kuwa ba kowa bace face Fulani mahaifiya ga Yarima YAZEED,lokacin da labarin auren ya zo kunnena,nayi duk wani yunk'uri da ya dace a matsayina na uwa mai burin ganin ci gaban nata ahalin,a haka ma ci gaba da cusa ladidi a gurin sa,sai dai shi kansa Abu YAZEED en kai tsaye ya fito ya nuna min sam ban isa ba dan direct ya fito ya nuna min rashin amincewarsa da magana ta,sannan ya d'ora da bani labarin abunda ban sani ba,ma'ana maganar auren sa da Hafsatu (Fulani) dan ni dai nasan maganar neman matar amma bansan da maganar auren ba a kusa,duk k'ok'arin daya dace nayi a wannan lokacin sai da nayi dan zama bai same ni ba,amma sai rashin nasara yayi ta bibiyata,duk hanyar da zan bi dana b'ullo zan tarar da rashin nasara,wannan tasa na fara bin shawarar k'awaye inda nima nan take na fantsama ga bokaye domin neman sa'a daga garesu(iyazan billahi iyaza,ya Allah ka tsare mu daga sharrin zuciya da bin turba irin ta shaid'an,hak'ik'a bin bokaye ba k'aramar tab'ewa bace da yin asara a nan duniya dama lahira baki d'aya, Allah ya kiyashe mu daga aikin dana sani,amin),da fari kam zan iya cewa na ga biyan buk'ata sai dai cikin abunda bai wuce y'an kwanaki ba komai ya fara rushe min,haka ina ji ina gani komai ya koma farko kamar da can asali,to bayan wannan lokacin ne kuma akayi auren Abu YAZEED da Fulani,kimanin shekaru biyu bayan bikin nasu da naga har lokacin Fulani bata ko yi b'atan wata ba sai na sake yanke shawaran na sake tuntub'ar hajiya Hauwa da maganar sa Abu YAZEED ya k'ara aure,daga lokacin dana fahimci yayi na'am sai na sake zuwa mata da maganar ladidi,amma abun bak'in cikin shi ne,koda na tunkareta da maganar sai ta tunamin itafa a wannan karon baza ta kuma iya sashi yayi aure ba,tunda har Allah yasa yayi mata biyayya ya auri wacce ta zab'a masa to wannan karon kam matuk'ar naga yayi aure sai dai idan har shi ya kawo matar da kansa kuma ya nuna sha'awar yin hakan,amma ita kam bazata sashi k'ara auren da baya muradi ba,wannan magana ta hajiya Hauwa tayi min ciwo matuk'a sai dai babu yadda zanyi na danne amma a raina inajin babu dad'i a duk lokacin dana bud'e ido na kalli hajiyan,bayan dawowata gida a wannan lokacin sai wata shawaran ta sake zuwa min,akan me zai hana bazan nemi shi Abu YAZEED enba nayi masa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 63