Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
za'ayi haka ya faru tsakanina da yarona,wannan duk laifi nane kuma na amaa,sam a matsayina na shugaba kuma mahaifi wannan ba shi ne adalcin da nake tsammanin nayi ba,ni kaina sai bayan da al'amuran suka faru nayi nadamar abunda na aikata,amma a dalilin rashin hujjar da zata sa a sakeka shi yasa naci gaba da danne damuwata na abunda nasa aka aikata maka,sam ba don son raina na aikata hakan ba...Ka gaface ni yarona,nasan ban kyauta maka ba ko kaɗan amma kamin afuwa abisa kuskuren dana aikata.." Shiru duka suka yi suna sauraren maimartaba har ya kai aya,ko da Yazeed ya ɗago kansa ya kalleshi sai yaga yana goge hawayen da suka sauko masa,saurin jan jiki yayi ya koma kusa da maimartaba yana riƙe hannunsa dan baiyi tsammanin haka daga gareshi ba "Dan Allah Abiiy kayi haƙuri.. Wollahi na fahimci uzurinka,amma dan Allah kada ka zubarmin da hawaye a dalilin hukuncin daka sa aka aikatamin,nasan kai mahaifina ne duk hukuncin da zaka zartar akaina dai² ne,sai dai wasu lokutan nakanji zafin abunda ya faru a wannan lokacin da za'a tafi dani,daya janyo har ka kasa ɗaga ido ka kalleni,amma yanzun na fahimci komai..Dan Allah Abiiy kada ka sake zubarmin da hawaye,matuƙar kuwa zaka ci gaba to na tabbata babu ni babu rahama..." Saurin rufe masa baki maimartaba yayi yana girgiza masa kai alamun yayi shiru,amma ina Yazeed kam ya kasa yin shiru "Tabbas zubar hawayen iyaye akan yayansu hakan baya ƙarar su da komai face azaba da gamuwa da bala'ai.." Jinjina masa kai maimartaba yayi sannan yayi murmushi yana goge fuskarsa "Shi kenan yarona in sha Allah bazan sake kamantawa ba bare na aikata..Hawayena kuwa idan akanka ne baza su taɓa zubaba da yardar Allah.." Murmushi Yarima Yazeed yayi sannan suka rungume juna,dukansu suna masu jin farin cikin fahimtar juna da sukayi,a hankali Yazeed ya ɗago kansa daga jikin maimartaba yana shirin yin magana sai dai ya rasa ta yadda zaiyi wa maimartaba bayanin abunda ke ransa,nan ya tsinkayo muryar Umma'nsa tana masa magana "Ehmm! Yazeed ai kuwa da akwai wani albishir dana so yi maka,sai dai abunda kayi yanzun yasa na fasa sanar da kai.." Fuskarsa ya juyar zuwa gareta sannan ya ɗan marairaice mata fuska kamar ƙaramin Yaro "Haba mana Ummanah,idan baki faɗa minba waye ne zai sanar dani..?" "Rabu da ita ni zan sanar da kai komai tunda bazata faɗa maka ba.." "Ohoo! Wai haɗemin kai za kuyi...To ai shi kenan nima dai saukin ƙawayena suna hanyan dawowa cikin satin nan.." "Amma dai Ummah kafin su dawo ai mune dake,kuma ko sun dawoma zasu koma ne,tunda ba zama suka dawo dayi a gida ba.." "Koma dai me zaku ce ai zasu dawo ne kuma zasu ɗebemin kewa kafin su koma,makarantar da duka saura kaɗan su kammala.." Sun jima suna hira tsakanin su irin hira ta tsakanin ɗa da iyaye,irin wacc suka jima rabonsu da irinta,sannan Yazeed ya musu sallama ya fita dan komawa gurin Yaseer cox lokacin kam yana jinsa cikin sauƙi da nutsuwar da ya ɗauki tsawon lokaci baiyi irinta ba. Can a ɓangarensu ya iske YASEER sai safa da marwa yake ya kasa zama,kallonsa kawai yayi sannan ya wuce zai shige bedroom,da sauri Yaseer ya tare shi yana ɓata fuska "Wai kai wannan wane irin hali ne ka koyo daga tambaya ban baka amsa ba saika fice ka barni nan inata gadi.." Yamutsa fuska Yazeed yayi kafin ya janyeshi gefe zai wuce,da sauri Yaseer ya riƙo hannunsa "Me yasa ne kam kake min haka..? Ka faɗa min abunda na maka kafin ka wuce.." "Dillah sake ni..Banda ka rainawa kanka hankali na maka magana kawai ka tsaya kana nunamin wani abu daban ba dole na maka haka ba.." Dafe kai Yaseer yayi sannan yaja hannun yazeed suka zauna "Shi kenan bro kayi haƙuri.. Naji laifina ne amma kayi haƙuri.." "Nifa malam kaga ba haƙurin ka na damu dashi ba kawai ka faɗa min abunda na tambayeka tun farko shi ne haƙurin da zan iyayi.." "Okey..! Ok! Naji zan faɗa maka..amma before ina son ka faɗa min dalilin da yasa kake son saninta..?" Dan murmushi yayi sannan ya furta "Haka nan nake jin son sanin wace ce itan..??" "Ƙarya ne wollahi ba haka nan bane..Kaga malam kada ma ka soma tunanin ɓoyemin,kasan ko zaka ɓoyewa kowa babu ni a cikin irin waɗannan mutanen ko..?" Tsayawa YAZEED yayi kawai yana kallonsa yadda ya haƙiƙance akan maganar sai kace wani babba "Sannu Babanah..." "Malam babu wani baba da zaka cemin kawai dai ka sanar dani dalilin.." "To idan bance maka baba ba me kake so nace..?" Yar dariya YASEER en yayi kafin ya kalleshi up to down "Kai wollahi ka cika matsaloli wai zamanka acan ne yasa ka koma wani matsalalle ne haka..?" "Ban sani ba..idan zaka faɗa min ne to kawai ka faɗa idan kuma baza ka faɗa ba to kaja bakinta kayi min shiru.." "To bazan faɗa ba ɗin shugaban masu matsala..." Har ya juya zai tafi yayi saurin juyowa "Faɗi ka ƙara matsala ba a cikin ta na rayuwa har tsawon shekaru biyar..." Daskarewa Yaseer yayi jin maganar data fito a bakin Yazeed,haka nan sai duk yaji baiji daɗin kalmar ba,kuma ga yadda yazeed en fuskarsa ta koma dalilin ambaton maganar da yayi ne yasa "Dan Allah bro kayi haƙuri kada ka sake faɗan irin wannan maganar." "Kaifa ka fara shin kaga laifina dan na ƙarasa..??" "Pardon me bro..dan Allah kayi haƙuri.." Wucewa yazeed yayi ya barshi nan jikinsa da zuciyarsa duk babu daɗi,rasa abunda zaiyi ya dakatar da yazeed ɗin yayi kawai saiya buɗe murya da ɗan ƙarfi ya furta "Ba kowa bace face ƴar gidan SARKIN KASUWA................" #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *Pg 12.* ^^^^^^^^ Saurin waiwayowa Yazeed yayi,a hankali kuma ya dawo ya tsaya gaban Yaseer yana kallonsa kawai,rasa abun yi Yaseer yayi saboda yadda yaga fuskar yazeed har lokacin tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa,ko da ganin haka kawai sai shima ya zubawa yazeed en ido kamar yadda ya masa,a hankali yazeed ya saki fuskarsa zuwa yanayin murmushi,mamakin murmushin Yaseer ya fara,sai daya bashi wasu mintuna sannan ya bud'e baki ya fara magana "Heeyy! Mr man..what this smile intends...??" Bai kula shi ba saima sake sakin wani murmushin da yayi sannan ya juya ya bar wajen,cikin d'aga murya Yaseer ya furta "Ya Allah..! Ya shirya min kai..ya fidda kai daga halin daka shiga.." Wata dariya ce ta sub'ucewa Yazeed lokacin da yake k'ok'arin shigewa bedroom en nasu,har bai san sanda ya waigo ba "Kai me kake nufi ne wai..?" "Ohoo! Abunda kake nufi nima shi nake nufi.." Yana daga inda yake ya girgiza kai had'e da cewa "Uhmm! Da kasan abunda nake da baka fad'i haka ba.." "Kai dai ka sani kuma,ni kaga nayi waje zani naga Ummi.." "Heeyy! Mr man ka jira na fito mu tafi tare mana nima ai ban shiga gurinta ba.." Komawa Yaseer yayi ya zauna yana jingina bayansa a jikin seat en daya zauna ba tare da yayi magana ba,shi kuma yazeed nan ya shige ya bar Yaseer yana jiran fitowarsa. A tare suka fito suka jera,duk da ba hira suke ba a tafiyar tasu haka nan suke cikin farin ciki dukansu,a haka suka nufi gefen Ummi'n Yaseer,nan suka yada zango Ummi sai jimamin yadda taga yazeed en ya koma take,haka nan duk inda ya motsa idanunta na kansa.Sun jima sosai a gefen ta,dan sai da suka ji kiran sallah sannan suka fito suka nufi masallaci. ^^^^^ Bayan fitar jeeddah daga gefen Fulani direct gida ta koma dan yin wasu aikace²n da Inno ta bari kafin ta fita,har ta koma gida zuciyar ta bata bar sak'a mata abunda ya wakana ba zuwanta kiran da maimartaba yake mata,ko data dawo gidanma tunanin dai taci gaba da yi kamar wacce ta rasa abun yi,a haka taita y'an aikace²nta har zuwa ta kammala. Tana zaune cikin kitchen ensu ta d'ora musu girkin dare,wayan dake mak'ale a jikinta ya shiga vibrating,jin haka yasa tayi saurin ciro shi daga jikinta tana dubawa,ko da taga ansa UNKNOWN NUMBER sai kawai ta tsaya ta zubawa screen en wayan ido kamar mai son nazartar wani abu a jikin fuskar wayan,sai da kiran ya katse sannan ta dawo cikin nutsuwarta tana k'ok'arin amsa kiran,ganin da tayi kiran ya katse yasa ta mayar da wayan inda ta ciro sannan ta ci gaba da abunda take,mintuna biyu tsakani mayar da wayan ta sake jin ta sake yin vibrate da sauri ta ciro tana dubawa sai dai wannan karon alamar shigowar sak'o ne,haka nan ta bud'e akwatin sak'on nata da niyyar duba abunda sak'on ke d'auke da shi "Lallai ke yarinya ce mara tunani...Taya za kiyi k'ok'arin taimakon ahalinsu mutanen da kullum basu da burin daya wuce su bautar daku..?? Ki nutsu kisan inda kanki yake,sannan muna gargad'inki da cewa wannan ya zama karo na k'arshe da zaki jefa kanki cikin matsalar da bata shafe kiba,haka duk wani abu da zaki ga ya faru kada ki sake yunk'urin shiga,idan kuwa kika kuskura kika tsoma kanki cikin abunda bai shafe ki ba,ko kika sake tunanin shiga hurumin mu,lallaifa ki tabbata kin jefa kanki a cikin masifar da baza ki tab'a iya fita ba....!" Shiru tayi tana sake bin harufan da sak'on yake d'auke da su,tafi minti biyar tana sake maimaita karantawa duk da ko kad'an bata fahimci ma'anar da sak'on ke d'auke da ita ba,haka taita faman juya kalmomin a cikin ranta,tana fad'ar su amma sam ta kasa fuskantar komai,ko da kuwa tambayarta za ayi a lokacin adadin yanda ta karanta ba lallaine ita da kanta ta iya fad'a ba,nan zuciyarta ta shiga tunanin inda sak'on ya fito da wanda ya turo mata,ta jima tana sak'a da warwara,ganin tunani na neman yi mata yawa yasa ta hak'ura ta maida wayan ta ajiye saman window sannan ta ci gaba da sabgogin gabanta ba tare data samu nutsuwa a cikin ranta ba... ^^^^^ Fitowarsu daga masallaci bayan an idar da sallah suka d'an zaga cikin gidan,ba don komai ba sai duk dan hakan ya d'ebema yarima yazeed kewa da y'ar damuwar dake cikin ransa,basu wani yi tafiya mai nisa ba sosai ya waiwayo ya kalli Yaseer "Ehenn! Mr man kace y'ar gidan waye ma Yarinyar nan..??" Sai daya waiwayo shima ya kalli yazeed en kafin ya d'auke kai yana sakin murmushi "Cewa nayi y'ar gidan Sarkin kasuwa ce...akwai wani abu dana fad'a bayan wannan ne..??" "No..! Kawai dai na manta ne shi yasa na tambayeka." "Uhmm! Kana buk'atar wani abu bayan sunan nata da sanin ko y'ar gidan waye itan..??" Kallon rashin fahimta ya bishi da shi yana squeezing face ensa "Nace maka haka ne..???" "Noo!! Na sani ko kana buk'atar saninta fiye da haka..??" "Me sanin nata zai amfaneni da shi..?" "Na sani..??" "Ohh! God.! Baka sani ba kake d'ora kanka akan zato..?? Kai wollahi ka cika sa ido,nifa duka ba wani abu yasa na tambaya ba,kawai naji an ambaci sunan ne a fada a matsayin ta na wacce ta bada gudunmawa aka sake ni,ya cancanta ace na neme ta nasan wace ce itan da dalilin ta nayin hakan,amma bayan haka fa..?" "Sorry bro...let us this chapter insulate..okay..?" Kai ya kad'a masa alamun shi kenan,daga haka kuwa babu wanda ya sake magana suka ci gaba da tafiya kowa da abunda yake sak'awa a ransa,suna daf da zasu wuce ta wani hanya da suka ratso kunnen yazeed ya kwaso masa sunan jeeddah da aka kira,saurin waiwayawa yayi da niyyar ganin wacce zata amsa,idanunsa ne suka sauka akan wata y'ar k'aramar yarinya da duka bazata wuce shekaru biyar ba,a hankali ya girgiza kai ya juya dan dai yasan wannan yarinyar babu yadda za'ayima ta kasance waccan jeeddan da yake tunani. Tsaf suka gama zagayen da zasu iya sannan suka kama hanyar komawa gida dan a lokacin tuni Yazeed ya fara yiwa Yaseer k'orafin ya gaji,shigarsu cikin parlor babu jimawa,wayan Yaseer tayi k'ara alamun shigowar sak'o,sai da yayi d'an jimm dan yasan duka a kwanakin nan sak'o d'aya ne yake iya shigo masa,haka ko wane lokaci yasan shi d'in ne zai iya shigowa wayarsa a duk lokacin da mai turowar yaso,kuma sak'on baya rasa samun nasaba da wannan b'oyayyiyar lambar,a hankali ya d'auki wayan ya shiga dubawa duk da jikinta da ya d'anyi sanyi "Little sister" ya gani,da sauri ya bud'e ya shiga duba sak'on dan yasan daga inda sak'on yake,sak'on da aka turo mata ne na d'azun ta b'oyayyiyar lambar tayi masa forward nasa,cikin tsananin mamaki ya gama duba sak'on kafin ya murza fuskarsa ya shiga neman line nata,sai dai har wayan ya katse bata d'auka ba,sake kira yayi can wayan yana daf da katsewa ta d'auka da sallama tana fad'in "Allah ya taimaki Babban yaya..?" Saurin katseta yayi da fad'in "Yaushe aka turo miki wannan sak'on..??" "Yanzun ne babu jimawa..amma naga alamun number babu suna,kuma nayi k'ok'arin tambayan waye sai dai text ena yak'i tafiya." "Na sani bazai tafi ba,yanzun abunda nake so dake shi ne..Ko da za'a kira ki da number ko aci gaba da turo miki sak'o kada ki kuskura ki d'auka,nd duk text en da za'a turo miki kada ya baki tsoro kin gane ko..??" "Ehh! Na fahimta.." "Ok..! Shi kenan sai munyi magana.." Cikin sanyi ta amsa da to sannan suka yi hanging kiran,juyowan da Yaseer zai yi idanunsa karaf suka sauka akan yazeed daya kafe shi da ido,iska ya shak'a sannan ya juya zai bar wajen,saurin rik'o shi yazeed yayi yana kallonsa "Mene kake magana akansa a waya..??" "Nothing bro..!" "Wollahi k'arya ne akwai wani abu.." "Noo! Bro Bafa wani abu ne mai muhimmanci ba,ka dena damuwa mana.." "Ohh!! Koh..? Ba shi da muhimmanci kake cewa kada a damu.?? Look Yaseer ya kamata ka sanar dani abunda ke faruwa.?? Ka san bazan iya juran naga ka shiga matsala ba ko.??" "Haba mana..! Ka yarda dani babu komai na fad'a maka.." "Shi kenan na yarda babu,amma ita wannan yarinyar wace ce..? Kuma mene ne alak'arka da ita da take kiranka,shima zaka cemin babu ne.." "Dan Allah bro ka bar maganar nan,na fad'a maka babu³ me yasa bazaka yarda ba..??" Shiru yazeed en yayi kawai yana kallon yadda Yaseer yake magana,a hankali ya jinjina kai sannan ya furta "It's ok ..na yarda babu,shi kenan...???" Komawa Yaseer yayi kan one seater ya zauna yana yin baya ya kwantar da bayansa a jikin seat en had'e da rufe idanu,fuskarsa da zuciyarsa duka d'auke da damuwa... ^^^^^ *PRISON...* Yadda captain ta gama mulke musu jiki da gishiri haka ta tusasu a gaba suka duk'ufa kan aiki babu ji bare gani,tun suna kukan gajiya da azaba,har suka zage suka dumfari aiki babu ji bare gani,da ganin yadda suke aikin kasan ba don suna yin aikin da k'warewa bane,a'a sai dan kawai ya zama dole ne akansu kuma su d'in ne za suyi shi,suna aiki Aisha naci gaba da sharar kwalla saboda rashin sabo da irin wannan aiki amma a haka sukayi ta fama dan gudun janyowa kansu jarfar captain.... Kwanakin su Aisha sun fara gangarawa a cikin gidan,haka kullum rana da zata fito ta fad'i suke cikin wahala da aikatawa tamkar bayi,kimanin watansu guda da zuwa gidan amma ko kad'an basu tab'a ganin wani ba bare suyi tunanin cewa yau ga wani ya tuna da su ya kawo musu ziyara,kullum iya abincin gidan shi ne abunda suke iya samu,zuwa wannan lokaci rayuwa gaba d'aya ta juya musu baya,zamansu a gidan ya dad'a sawa jikin su da duk wani lamari da suka bari a baya ya zama tarihi a garesu. Captain ce ta shigo cikin d'akin da ganinta kasan ba zuwan mutunci tayi ba,nan take ganinta yasa jikin Aisha ya fara kyarma tamkar taga wani sabon muridi,tsaye ta mik'e tana goya hannunta a baya,dan ta riga ta san ganin captain a gurinta ba alkhairi bane a iya tsohon wannan lokacin,harara captain ta watsa mata kafin ta kalli Ladidi tana fad'in "Kunyi bak'uwa..." Cike da mamaki ita kanta Ladidin ta kalleta tana tambayar captain "Captain mu kuma ake nema..?" "To dafa...?? Idan baku nake nufi ba uban waye nake nufi..??" "Kiyi hak'uri Aunty..." Waigawa tayi ga Aisha data k'ame kamar gunki "Ke wollahi ki shiga hankalinki,shegiya mai zubin makirai..." Kan Aisha a k'asa tana k'ifta idanu dan yadda take tsoron captain a rayuwarta sam bata tab'a jin tsoron wata halitta fiye da haka ba "Ni dallah ku wuce muje kuna b'atan lokaci.." Sum² suka mik'e suka bita,har zuwa inda ake ganawa da masu kawo ziyaran,sai da suka zauna sannan captain ta fita ta barsu su biyu a cikin gurin kowannensu zuciya cike da rauni da damuwa,suna nan zaune sunyi jugum² suna jiran ganin wanda zai shigo,aka turo k'ofar aka shigo,k'aran takalmin da yake tashi yasa su d'agowa suka juya dan ganin waye mai shigowar,ai a firgice Ladidi ta mik'e tsaye zumbur tana fad'in "Ke ce................???" _Afuwaan..! Fan's yau wollahi abubuwa sunmin yawa ban samu nayi typing da yawa kamar yadda na saba ba,kuyi hak'uri da wannan,sai mun had'e a next page......_ #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *Pg 13.* ^^^^^^^^ *"ADDA* Kece...??" Abunda ya fito daga bakin Ladidi kenan tana sake kallon matar data kira da Addan,kafin ta fashe da kuka,a yanayi na mai sunan da ladidi ta ambata daka kalleta zaka tabbatar ba k'aramar mace bace,ilahirin jiki da fuskarta d'auke yake da ado,ko ina a jikinta zallar jan k'arfe ne (gold) sai shek'i yake da d'aukan ido,sam matar a yanayinta da zubinta bata yi kama da talaka ba,yadda suka zuba mata ido suna kallonta cike da sha'awa haka itama ta kafesu da ido tana kallon ikon Allah da mamakin yadda taga sun koma,hakan sai yasa ta tsayawa kawai tana sake binsu da kallo mai kama dana tausayi,a hankali ta kama Ladidi dake neman zubewa k'asa ta zaunar sannan ta rik'o Aisha tana kallonta kamar zata mata kuka itama ta zaunar,sannan ne itama ta iya d'osana nata mazaunan akan stool en,ta jima tana kallonsu kafin ta iya jan dogon numfashi "Yanzun Ladidi meya kaiki aikata wannan al'amarin..? Shin biyan ku za'ayi ko akayi..??" Sunkuyar da kai Ladidi tayi k'asa ta kasa magana,ko da ganin haka sai yasa adda girgiza kai,cike da takaici taci gaba da magana cikin wata irin murya "Gaskiya banji dad'in faruwar wannan lamarin ba gaba d'aya,shin yanzun waye gari ya waya..? Fisabilillahi banda kawai kin rasa mafad'i shi yasa kika biyewa son zuciyar ki,da shegen son kud'in ki na masifa yasa kika jefa rayuwar yarinya k'arama cikin masifa..duka Aisha shekarunta nawa ne da har zata aikata laifi makamancin wannan har ya janyo mata d'auri.." Kan Ladidi a k'asa idanun nan nata sun dad'a fitowa ta san yau kam saita Allah tunda Adda taji maganar nan,babu abunda zai hana bata mata wankin babban bargo ba,Aisha kuwa tunda Adda ta zaunar da ita banda kuka babu abunda take dan yadda Adda ke yiwa Ladidi fad'an jefata a uku da tayi "Dan Allah adda kiyi hak'uri, wollahi duka al'amarin nan ya faru ne ta yadda idan har ba bayani nayi miki ba baza ki tab'a fahimta ta ba,mu kanmu wollahi wannan al'amarin ba muyu zaton zai zo mana a haka ba,sam ba yadda kike zato bane,ki yarda dani Adda wollahi babu laifinmu.." "Haba Ladidi taya za'ayi na yarda dake bayan nafi kowa sanin halinki,nifa nan nina raineki,shin akwai wani abu da zaki b'oye min..?? Yadda nasanki bana tunanin akwai wani da zai iya bayyana fiye da abunda na sani a kanki..yanzun ma duk ba wannan ba,tunda al'amarin ya faru wa kika sanarwa..??" Shiru tayi tana sauraron me Ladidi zata fad'a amma itanma sai tayi mata shiru "Tambayar kifa nake kin sani a gaba kinmin shiru.." "Ban fad'awa kowa ba Adda..!" "Kin gani ba..irin wannan halin naki na nunk'ufurci,abu na damunki amma baza ki tab'a iya fad'awa kowa ba...yanzun da ban samu labari ba yaya kenan..?? Haka zaku yita zama a wannan gidan cikin azaba,kalli yadda kuka koma cikin wata guda duk wahala na neman maida ku iyayena,ni da na fiku jimawa a duniyar banyi tsofan da kuke neman yi ba..." "Kiyi hak'uri Adda in sha Allah haka ba zai kuma faruwa ba da yardar Allah.." "Ai zancen kicema bazai kuma faruwa ba bai taso ba,tunda dai wannan ya faru idan har kina da hankali zaki kiyaye faruwar haka nan gaba...Tun ba yanzun ba nasha gargad'inki da shiga abunda babu ruwanki amma kika k'i ji,yanzun da bana duniyar ma ban san me zai faru daku ba kuma...Allah ya kiyaye gaba ni kam shi ne zan iya fad'a.." Shigowar captain a dai² lokacin yasa Adda mik'ewa ta d'auki jakarta ta sab'a sannan ta kalli captain tana mata murmushi "Captain zamuyi magana ta waya in sha Allah, amma ina so a dunga kula min da su,wannan y'ata ce,ita kuma wannan y'arta ce..bana son wani abu ya samesu.." Dariya captain tayi mata tana fad'in "Hajiya Adda in sha Allah kamar yadda kika fad'a za ayi miki hakan,ai ke ce,kin fi k'arfin hakka a gurin

Chapter 10 of 63