Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana kallonsu duka,tabbas maganarsa tana kan hanya,amma taya zasu fara amincewa har ayi wannan AL'AMARI'N bayan sun san cewa Abir k'aramar yarinya ce da duka har yanzun ko sanin kanta bata gama yi ba,idan har suka ce zasu yi haka tofa sun tabbata zasu cutar da rayuwarta ne,idan kuma har sun ce baza su yi hakan ba to yaya za suyi kenan..?? Wannan shine tambayar da kowa yake yiwa kansa a gurin idan aka d'auke Fulani da tayi nisa cikin dogon zangon tunani,nan kowa ya shiga kawo nasa ra'ayin akan maganar,Hajiya kam tunda suka fara maganar tayi shiru tak'i cewa komai,zuwa wani lokaci ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya sannan ta kallesu dai² lokacin da ta fara magana "Gaskiya ne duka shawaran ku abun a duba ne,sai dai wani hanzari ba gudu ba,kamar yadda kuka sani Abir yarinya ce k'arama,mutumin da bai gama mallakar hankalinsa ba,ina ganin bai kamaci ace an zartar da irin wannan hukuncin akansa ba duk da kunsan hakan ba haramun bane a addini,bayan haka shi akankansa YAZEEDU idan har baku manta ba game da matsalar dake tare da shi a wancan lokacin kun san irin sharad'in da yake kai na daga magani,shin mai zai hana muyi wani abu kafin muyi tunanin damk'a Abir a hannunsa.??" Kallon sune ya koma kan Hajiya harma da hankulansu dan maganarta sosai ta ratsa su duka,nan ita kuwa Hajiya'n taci gaba da magana "Ni anawa ra'ayin ina ganin ya kamata mu d'an jinkirta da maganar Abir daga nan zuwa ta d'an k'ara wayo,kafin lokacin sai muyi amfani da wannan damar muyi k'ok'arin dubawa koda a cikin bayinmu ne mu nema masa wata k'wark'wara,wanda ta hakama kad'ai ina ganin zamu iya fahimtar samuwar lafiyarsa..Shin me kuke tunani akan wannan maganar..??" Nan shawara ta koma kan maganar Hajiya'n dan suna ganin maganar tata abar ace sun duba ce,amma cikin bayin su kansu duk da a k'asansu suke,umarninsu suke bi shin waye zai yarda ya d'auki y'arsa ya badata har hakan ta faru akanta..?? Anya akwai adalci a cikin wannan maganar..?? "Tabbas..! Wannan shawara ne da yayi ma'ana,amma kafin nan wace baiwa ce kuke ganin ta cancanta a zab'a game da wannan AL'AMARI'N.??" Fulani ta tambaya,murmushi hajiya tayi sannan ta furta "Mutum d'aya ce nake tunani a wannan bigire,wacce nasan ko me muka ce za muyi akanta iyayenta ba zasu tab'a k'in amincewa da duk wani hukuncinmu akansu ba.." Jinjina kai maimartaba yayi cikin gamsuwa da maganar Hajiya'n nasu,a hankali Ummi ta kalli Umma Fulani bakinta d'auke da tambaya "Su waye su wad'annan d'in ni kam na gaza fahimta..??" *"GIDAN SARKIN KASUWA.......!"* A hankali tayi squeezing fuskarta tana son tunano ainihin gidan da ake magana akai,ido ta fitar waje cike da fargaba tana fad'in "Shin wannan hukuncin akan *JEEDDAH* ake magana zai tsaya..?? kuyi min bayani na kasa ganewa,kamar yadda na sani gidan tsarkin kasuwa bashi da wata yarinya bayan ta,itan ce ake nufi ko kuwa wata daban aka samo,shin sarautar tsarkin kasuwa tana nan a gidan dana jima da sani ne ko an canja..??" "Babu wani chanji da aka samu,gidan da Sarautar take har yanzun tana nan a gidan kamar yadda kika riga kika fad'a,wannan maganar duka akan yarinyarsa muke yinta.." Hawaye ne suka fara zirarowa daga idanun Ummi'n YASEER a lokacin da taji tabbacin Sarautar tana nan a gidan data sani,kuma duk maganar kamar yadda taji ba kowa ake nufin za'a bawa Yariman a matsayin sad'aka ba face *JEEDDAH,* gaba d'aya idanunsu ne ya koma kan Ummi cike da mamakin kukan da take a lokacin,wanda nima ganin hakan da nayi ya sanya ni shiga matuk'ar rud'ani game da wannan AL'AMARI'N da yake kan faruwa......... *Shin wai fan's mene ne hawayen Ummi ke nufi..? Nikam na gaza fahimtar abunda yake shirin faruwa fa..* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ _It was very thoughtful of u to send me this lovely gift.U have no idea how happy I am after receiving it.Thank u so much dear *SALMA SA'EED ADAM*_ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 14.* ^^^^^^^^ *#Apprehension* Gaba d'aya parlour'n hankulansu ya karkata ga Ummi data dage sai zubar da ruwan hawaye take gwanin tausayi,su kuwa kamar wasu dolaye duka suka zuba mata ido an rasa mai iya bud'e baki ya tambayeta dalilin zubar hawayen nata,kamar daga sama muryar Adda tayi musu kutse a lamarinsu,inda take tsaye duka suka juya suna kalo da wani irin yanayi atattare dasu,itama kallonsu take fuskarta d'auke da alamun firgicin ganinsa a haka,hajiya ce ta kalleta sannan tayi magana "Jab'b'ama Adda..! Ki k'araso mana.." A hankali ta shiga d'aga k'afafunta tana kuma binsu da ido,tun kafin ta kaiga k'arasawa tuni har k'wak'walwarta ta gama kawo mata tunanin yin wani abu saboda a yadda ta gansun nan ta tabbatar akwai wani abu daya faru shi yasa har ta riske su,zuciyarta ce ta fara mata hud'uba kan ta aikata da gaggawa dan hakan zai bata damar jin mak'asudin zamansu a tare a guri guda,akusa da Hajiya ta zauna tana mai sake binsu da kallon da ita kad'ai tasan ma'anarsa kafin ta kece da kukan makirci,dukansu hankulansu a tashe ganin tana hawaye musamman da tun shigowarta dama suka ga yanayin da take sai ya nuna musu kamar akwai wani abu,wannan tasa duka suka shiga rud'ani da taradaddin dalilin kukan nata,caa suka yi mata duka akai kowa burinsa bai wuce ya san damuwarta ba,saboda dukansu babu wanda ya kawo wani abu daban,cikin kukan ta shiga fad'in "Yanzun Fisabilillah..! Ace tun ina raye ake k'ok'arin nunamin bambanci,ni dama na sani babu wanda ya damu dani a cikinku bare har ya damu da damuwata,na jima da sanin ni d'in bare ce a tsakaninku,amma babu komai haka duniya ta gada,wanda ka damu da shi ba dakai yake damuwa ba,na tabbata badon Allah ya dubeni ba ta hanyar azurtani da ladidi da shikenan ya zama bani da kowa a duniya ta,babu kuma wanda zan kalla naji sanyi a zuciyata.." Jikinsu ne yayi sanyi ganin yadda ta tak'ark'are tana rusa kuka,sai dai a b'angaren Ummi'n YASEER da Umma Fulani su kam suna jin kalaman bakinta suka kalli juna sannan suka sake maida hankalinsu kanta,Abba GALADIMA kuwa da Hajiya nan suka shiga bata baki amma sam tak'i yin shiru sai kuka take risga abunta,Ummi kam ko da taga haka tab'e baki tayi k'asa² ta yadda babu mai jinta ta ce "Allah ya kyauta..!" Nan ta juya ga Hajiya cike da shirin kawar da zancen Adda'n tana cewa "Hajiya zamu iya tafiya..?!" Kai hajiyan ta girgiza mata alamun a'a, sake juyawa tayi nan suka had'a ido da Abba GALADIMA ai kuwa nan shima ya mata alama da ido akan tayi shiru karta sake cewa komai,kanta ta janye zuwa gefe,can daga k'asan zuciyar ta tana jin sam kukan Adda bai kwanta mata,tabbas tana jin akwai wani dalili da yasa ta aikata hakan,a b'angaren Hajiya kuwa hak'uri tayita bawa Adda'n kafin ta sanar mata da abunda ke faruwa da dalilin zamansu a gurin,sake kyab'e baki Adda tayi cikin son gwaninta tana cewa "Yo dama ai ni tun farko dan dai kawai ba'a d'auke ni da muhimmanci bane,amma tun da fari saida nayi maganar a had'a Yarima da Aisha amma sai aka kawo wani maganar case daya dad'e da had'asu,Fisabilillahi! Ai ya kamata ace anyi mata uzuri ko dan lokacin ba wani hankali gare ta ba,kuma bayan wannan ma ai zai iya zama wani ya mata barazana akan sai ta fad'i hakan..Amma dai koma yaya ne duka naga y'an uwa ne kuma idan aka had'a sun junansu zasu rufawa asiri ko ba haka ba..?? Duk da wancan lokacin ya wuce yanzun kam nasan idan har akace za'a had'a itan mai iya zama da shi ne har k'arshen rayuwa ko da kuwa ace kowace mace ta k'i shi,hakan zaisa su sake yafewa juna tare da sake fahimtar junan su!" Kaf cikinsu babu wanda maganar Adda bata bawa matuk'ar mamaki ba,musamman da duka babu wani bare a gurin kuma babu wanda baisan abunda ya faru ba,amma sai kowa ya b'oye abun a zuciyar sa yak'i bayyanawa,haka tayita zantukanta sai dai marasa ma'ana amma an rasa mai tankawa,sai da tayi ta gaji dan kanta tayi shiru sannan ne Fulani ta kalleta tana fad'in "Kuma fa Adda duka maganar ki gaskiya ne..!" Ko kafin ta ci gaba tuni duka suka zuba mata ido suna binta da kallon tsantsar mamakin furucinta,ga Ummi kuwa a lokacin wani irin kallo ne take bin fulanin da shi mai d'auke da sak'onni da dama a cikinsa,cikin zuciyarta k'issimawa take da itace a matsayin Fulani aka taso da wannan tsohon zancen bata ga abunda zai hana bata gayawa Adda'n magana ba a cikin zance kamar yadda ta fad'a yanzun,ko kafin ta gama wannan tunanin nan ta jiyo muryar Fulani na cewa "Adda sai dai ina ganin kamar kin manta da abunda hausawa ke cewa wato 'ba'a tab'a b'ari a kwashe duka' tabbas wannan magana akwai hikima a cikinta kamar yadda maganar nan take muma haka muka d'auki AL'AMARI'N,sai dai abunda Aisha tayiwa yaron nan da ciwo,wanda a duk lokacin da zan tuna ni kaina ina jin matuk'ar b'acin rai,sai dai abunda na k'udurce a raina shi ne ko da ace shi zai manta ni da nake matsayin uwa hakan bazai tab'a gogewa a idona ba duk tsayin shekarun da za'a d'auka,buh tuni muka bar komai a hannun Allah wanda dama can shi muka mik'awa lamarin,kuma cikin hukuncin sane da amincewarsa yasa Yarima ya fito a dalilin yarinya k'arama wacce baza mu tab'a mantawa da alkhairinta garemu ba..Amma Adda abunda nake so na sanar dake shi ne,yadda alak'ar zumunci ya had'a mu,mu tsaya akansa,maganar aure kuma da ake yawan tada ita tsakanin Yarima da Aisha tun farko ban amince da ita ba akan wane dalili yanzun zan amince..??? Matuk'ar dai ace yaron nan nina haifeshi banga mahalukin da zai nunamin iko akan saba,kamar yadda a wancan karon ya fito ya furta baya so nima na tsaya a bayansa,matuk'ar ba dai Ubangiji ya rubuta a littafin K'ADDARARSA ba tofa babu abunda zaisa shi zama da irin wannan matar har Abadan..!" Sakin baki Adda tayi tana kallon Fulani data had'e girar sama data k'asa tana koro jawabin akan iyakar gaskiyar dake ranta,su kansu jama'ar dake gurin ba k'aramin mamakinta suka yi ba,musamman da suka san itan ba mai yawan magana bace akan al'amura da dama,haka nan ko akan yaranta bata cika d'aga kai ta kalli abuba bare har ta kaiga ta bud'e baki tayi magana,matuk'ar kuwa aka ga ta furta wani abu akan wani lamari dole ne sai an kalli abun coz ba k'aramin abu ke sata magana ba. "To ai shikenan tunda haka kika ce,Allah ya zab'a ta gari kuma ya sab'a hali..!" Tabbas tasan maganar Adda da biyu ne tayi ta,haka yanayin dake shimfid'e a fuskarta ko shi mutum ya kalla zai gano har cikin zuciyar ta bata ji dad'in maganar fulanin ba,ai kuwa Fulani sake had'e fuska tayi tana cewa "Ai Ubangiji ya kawo masa ma,kuma da izininsa nothing will happen..!" Iya shak'a Adda ta shak'i bak'in ciki a maganar Fulani wanda nan take yasa ta mik'e tsaye tana gyara zaman veil d'inta ta kalli Hajiya data zuba musu ido tak'i yin magana tana cewa "To Hauwa ni zan wuce dan na fahimci idan naci gaba da zama za'a iya zagina ma akan d'a..Saboda haka nayi gaba Aure ne Allah ya bada sa'a..!" Ummi kam tunda taji furucin Fulani ai sai zuciyar ta tayi mata haske har hakan ya bayyana a saman fuskarta,tana doka murmushin farin ciki suka had'a ido da Adda dake k'ok'arin fita,sarai taga irin kallon wulak'ancin da take jifansu da shi,dan haka ta shiga neman hirji da ita da duk wani k'uduri dake manne a k'asan zuciyar ta,coz ita kam ta jima tana yiwa Adda'n wani irin kallo wanda da za'a tambayeta dalili babu tabbacin ta iya fad'an k'wak'wkwaran dalilin da yasa take hakan,a kan idonsu Adda'n tasa kai ta fice,bayan fitar tane hankulamsu suka karkata zuwa ga Hajiya dan yadda ta tsume tak'i cewa komai sai da suka sha jinin jikinsa,nd basu san wane irin hukunci ne zai biyo baya daga gareta ba,sai dai ga mamakinsu duk wannan kallontan da suke har akayi aka gama ko tari tak'i yi bare ta tanka musu,wannan dalilin yasa duka kuma sai suka saki jiki daga nan kowa ya shiga nasa hurumin.. ^^^^^ A gefen Aisha kuwa dai² lokacin data kama hanyar shiga gidan ko ina na ilahirin jikinta banda rawa babu abunda yake,coz bata san mene ne zata je ta tarar ba,haka nan bata san da wane irin fuska ne zata fuskanci wacce take k'ok'arin sanarwa damuwarta ba,duk da shawaran da wani gefe na zuciyarta ke bata haka nan sai take jin baza ta iya komawa da baya taci gaba da zama da damuwa ba,ci gaba take da tafiya amma har yanzun ta gagara k'arasawa cikin gidan saboda yadda take jan k'afa kamar a tsaye take a guri guda,ta kusan shafe tsawon mintuna goma tana aikin abu guda kafin ta iso cikin gidan,cike da sanyi da tsananin damuwa tayi sallama a tsakar gidan sai dai taji shiru,kusan sau uku tana yin sallama kafin a amsa ta,Inno ce ta amsa da take kan fitowa daga toilet tana ajiye butar hannunta tayi mata maraba da zuwa,a ciki ta amsa tana sauke kai k'asa da wani mugun fargaba,a awning ta mata shimfid'a then tayi authorised nata data zauna,zama Aisha tayi cike da jin wani irin yanayi har zuciyarta,nam dai ta shiga gaida Inno with some emphases,amswa Inno tayi fuskarta cike da fara'a tana yabawa da irin tarbiyyan data gani a tare da Aisha'n,after kuma shiru ya biyo baya,ganin bata yi magana ba saima shirun da tayi kamar mai tunani yasa Inno sake kallonta sannan ta fara magana "Baiwar Allah sai dai ban shaida kiba..ko kina neman wani ne,naga baki yimin bayanin gurin wanda kika zo ba,muna ta zaune shiru..!" Shifting head tayi aside kafin tace "Mama dama gurin jeeddah nazo ne,ina fatan tana kusa..!" Tayi maganar with expectations na zata samu jeeddan "Ayyahh! Ai kam jeeddatu bata kusa,amma ba kuyi waya da itaba..??" Shiru ta d'anyi tana jin babu dad'i har k'asan ranta na rashin samun jeeddan da bata yi a gida ba,nd ita gashi ba number ta gareta ba bare tace zata mata magana,hasalima ita bata san jeeddan nada waya ba ai sako number ta nema a wani gurin,da kyar ta yakice tunanin jin Inno nasake maimaita mata tambayar "Ehh! Mama bamu yi waya ba gaskiya,nayi tsammanin samunta a gida ne shi yasa na taho kai tsaye..!" Yanayin ta da Inno ta kalla yasa itama cew "Ayyahh tohh! Bari na gani idan na samu yaro sai nasa a kiramin ita..Bata kusa kam..!" Daga haka taja gyalenta dake sak'ale tayi waje cike da son samo yaron da zai je cikin gidan yayi kiran jeeddan. Sai dai ko data fita har mak'ota ta lek'a duka bata samu yaron da zata aika ba,wannan dalilin yasa ta dawo cike da jimamin abunda ya faru ta shaidawa Aisha'n a zatonta ko zata iya jira har ta dawo,sai dai ko da Aisha taji abunda ya faru nan ta mik'e da son komawa inda ta fito bayan ta shaidawa Inno zata dawo wata rana,babu yadda Inno bata yi da itaba akan ta jira a samu wanda zai kirata amma tak'i saima cewa da tayi zata dawo d'in kamar yadda ta shaida mata wani lokacin,da haka ta tafi ba tare da sun had'u ba kamar yadda taso.. ^^^^^ Can a apartment d'in Ummi kuwa jeeddah ce cikin kitchen tana ta aikinta cike da k'warewa,yau kam tun da tazo gidan bata samu Ummi ba,dan haka kai tsaye bata tsaya jiraba ta shiga aikinta kamar yadda ta saba a kullum,sai data ci k'arfin aikin natane sannan taji alamun dawowar Ummi'n,dan haka ta kakata ta fita a kitchen d'in tana nufan parlor,sanda ta fito lokacin Ummi jhar ta kaiga zama dan haka koda tazo a gaban Ummi'n ta tsuguna kanta na kallon k'asa,gaisheta ta shiga yi da girmamawa,ta amsa mata while her face were full with some delighted da bai misaltuwa,har ta mik'e zata koma bakin aikinta taji Ummi'n ta kira sunanta cikin yanayin da bata tab'a ji ya fito daga bakinta ba,jikinta a mace ta juyo tana amsawa sannan ta koma ta zauna from were she arose,sai da Ummi tayi wani ajiyan numfashi sannan ta shiga mata wani irin nasiha mai motsa dukkan gab'b'ai wanda a gefen jeeddah yadda taji Ummi'n nayi mata nasihan sai daya haddasa mata jin wani mummunan fad'uwar gaban data rasa dalilinsa,haka nan sai ta tsinci kanta da zubar da hawaye da bata san manufar saukarsu ba,sanda Ummi'n ta gama mata nasihar sannan ta sallameta tana sake sa mata albarka,cike da mutuwar jiki ta mik'e bayan tayiwa Ummi godiya sannan ta koma bakin aikinta,sai dai aikin kawai tana yinsa ne amma bawai dan tana jin dad'in yanayin data tsinci kanta a ciki ba.. ^^^^^ A gefen Yarima ma kusan haka ne ya kasance dan a lokacin shima yana apartment d'in Umma'nsa,yana zaune gabanta tana masa nasiha kan al'amuran yau da kullum,haka nan dangane da irin rayuwar da yake kan fuskata,yayi shiru ba tare daya furta komai ba har ta kai aya a maganarta,a hankali ya d'aga kansa da tunda ta fara maganar yake k'asa,yana sakin d'an murmushi mai had'e da nuna jin dad'in abunda ta masa. Godiya ya mata had'e da addu'ar fatan samun tsawon rai,suna cikin maganar kuwa suka fara tsinkayo maganar fadawa suna kirari ga sarki alamun daya tabbatar musu yana kusa da shigowa cikin gidan kenan,daga k'ofa suka dakata shi kad'an sa ya k'araso bakinsa d'auke da sallama suka amsa kamar yadda addini ya tanada,lokacin daya kaiga zama ne YAZEED ya sake sunkuyar da kai k'asa ya gaishe shi,da sarauta a maganarsa ya amsa kafin ya juya ga Fulani da take masa barka da shigowa,bayan ya amsa mata ya shiga tambayarta akan ta sanar da Yarima maganar da suka yi kuwa..? "A'a.!" Ta amsa masa nan take yanayin fuskarsa ya d'an sauya kad'an dan baiyi zaton baza ta sanar masan ba,ko data ga haka hak'uri ta shiga bashi sannan ta sanar masa shigowar Yariman kenan yanzun suka gaisa ya shigo,jinjina kai maimartaba yayi sannan ya maida kallonsa akan d'an nasa yana kiran sunansa,a jikinsa yaji something was intend to happens,amma bai iya amsawa ba saboda girman da mahaifin nasa yake masa,ganin haka yasa maimartaba farawa da nasiha mai ratsa zuciya a matsayinsa na mahaifi ba wai a matsayin sarki ba,cikin nasihar tasa sai ya shigar da maganar da suka yi a d'azun game da maganar aurensa da hukuncin da suka yanke ya sanar da shi,bai iya ko da tari ba har maimartaba ya gama jawabin sannan ya bashi damar yin magana idan yana da buk'atan hakan,duk da kasancewar ya samu damar da zai iya yin magana kasa cewa komai yayi dan yadda yake gani matuk'ar ya nuna wani alama na rashin son abunda suka zo masa da shi a lokacin ya tabbata mara adalci a gare su a matsayin suna masu fad'i tashi duk akansa na ganin yana cikin farin ciki kamar sauran al'ummah,muddin yayi haka bai kyauta ba,wannan dalilin yasa yak'i yarda yace wani abu akan maganar.Fatan alkhairi yayiwa mahaifan nasa bayan nan yayi na'am da maganarsu,su kansu sunji matuk'ar farin ciki dan basu tsammanci hakan daga gareshi ba,after kuma suka sallame shi suma suna masu sanya masa albarka,daga haka ya fita a apartment d'in zuciyarsa cike da tunani akan abubuwan da dama. Kwanaki biyu tsakanin meeting d'in su akan maganar auren Yariman,wanda izuwa wannan lokacin tuni har maimartaba yayi magana da sarkin kasuwa kan k'uduri'nsa akan jeeddah da Yarima,duk da sarkin kasuwa yasan da irin matsalar dake damun Yariman saboda yadda maganar rashin lafiyar sa ta zaga gari sam shi duk bai dame shiba,hasalima murna ya shiga yi da lamarin ko babu komai acewarsa darajarsa zata yi sama,haka nan duk inda ya shiga ya fita a yanzun zai zama ana nuna shi ne amatsayin surukin masarauta,kuma shi wannan ma kad'ai ya isheshi farin ciki ko da kuwa ace bai samu damar da zai kasance an y'anta shiba. Da wannan farin cikin ya isa gida dan labartawa Inno yadda suka yi da maimartaba,sai dai koda ya shigo bayan ta masa shimfid'a saboda yadda taga ya shigo ta fahimci akwai magana a bakinsa,hakan tasa ta nemi guri ta zauna tana jiran taji bayanin dake bakinsa,tunda ya fara maganar Inno take binsa da kallo har ya dasa aya akan maganar had'a auren Yariman da jeeddah, nan take kuwa ta tari numfashin sa "Malam kenan,shi yasa mana naga kana murna,yanzun fisabilillahi..! Kuma da maimartaba yayi maka maganar me kace masa..??" Tayi tambayar tana jiran taji amsan da zai bata,da fara'arsa ya amsa mata "Yo Inno banda abunki me zanyi daya wuce na amsa kuwa..?? Irin wannan abun alkhairi daya nufo mu ai bama k'i ba mukam..Maganar da nake mikima yanzun nan haka tuni na shaidawa maimartaba mun amince da duk hukuncin daya yanke,saboda hakama ku shi da kansa ya shaida min mu fara shiri biki nan bada jimawa ba.." Wani irin tsoro ne ya bayyana akan fuskar Inno,da har ya janyo ta shiga maimaita maganar da malam d'in ya gama sanar mata a lokacin,da rashin fahimta ya d'aga kai yana kallon yanayin ta dan yasan tabbas akwai wani abu daya sa take maimaitawar,sai dai ga Inno kuwa kallo d'aya zaka mata kayi saurin tabbatar da cewa wannan AL'AMARI ba k'aramin jefa zuciyar ta yayi a rud'ani ba,wanda hakan har ya janyo ta kasa motsawa daga inda take saboda tsananin tsoron da take ciki........... *Tofa...! Ko mene dalilin tsoratar da Inno tayi itama a wannan karon ohoo...!* 🤔 #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898*

Chapter 36 of 63