a nata gefen tun tana jin haushin maganganun har ta dawo kuma abun ya daina b'ata mata,da k'yar ta samu ya karb'a ya kafa kai zai sha,ko da ruwan ya shiga bakinsa nan yayi yunk'urin dawo da shi,ai koda ganin haka da jeeddah tayi bata san sanda ta rik'e hannunsa ba tana bashi hak'uri akan ya sha,wata uwar harara ya galla mata cikin maye mai d'auke da b'acin rai ya kalleta
"Ke...! wannan ne ruwa.??"
"Ehh! Babban Yaya ruwan lemon ba,ai kai kace na kawo maka kana son sa a haka.."
K'wafa yayi jin abunda tace,sannan ya maida kansa yaci gaba da sha badon komai ba sai don kawai tace shi ne yace ta kawo masa,yana zuwa geji ya ajiye mata cup en ba tare daya mata magana ba ya koma ya sake kwanciya,hamdala ta yiwa Allah fuskar ta cike da fara'a mai cike da fara samun sukuni ta masa godiya shima sannan ta mik'e ta bar wajen,wani ruwan lemon ta koma ta sake tarawa saboda kaf na ciki YASEER ya shanye,sannan ta dawo kan YAZEED en shima,rikicin da suka yi da shi har sai da yaso ya wuce na wanda suka yi da YASEER,sun jima suna tak'addama da juna saboda tsabar k'afewa da yayi kafin da k'yar ta samu ta sha kansa ya yarda ya karb'a ya sha,yana gama sha ta mik'e a gurin ta bar su,zuciyarta cike da murna ta shiga tattare duk wani abu kama daga cikin parlour'n har zuwa kitchen da tayi amfani da shi dama wanda suka yi ta tsaftacesu a nan,duk bayan mintuna tna aikin sai ta dawo ta duba su,ba don komai ba sai duk dan kada a samu matsala,sun d'an jima a cikin yanayin kafin mayen ya fara sakin su,sanda ta dawo da niyyar sake dubawa a karo na k'arshe,tana kawo jiki zata fito daga ciki ta hangi wutan parlour'n a kunne,a d'ari da tamanin ta fito ta shiga dubawa zuciyar ta da fargabar Allah yasa ba wani ya shigo gurin ba,sanda ta gama fitowa ne ta iske YASEER zaune saman cuition ya b'alle duka botiran rigarsa saboda yadda ya had'a zufa,haka nan idanunsa a runtse ya jingina bayansa da seat en,koda taga haka a zatonta wani abune ya sake faruwa dan yadda ta tarar da shi,a hankali ta lallab'a ta fito har sanda ta kusa zuwa daf da shi sannan ta dakata tana kiran sunansa cikin k'asa da murya,a hankali ya shiga k'ok'arin bud'e idanunsa da suka masa nauyi har sanda ya gama ware jajaye lumsassun idanun a kanta ya kafeta da su,ganin irin kallon da yake mata yasa ta yin baya kad'an had'e da tambayarsa
"Babban Yaya akwai abunda kake buk'ata a kawo maka ne..??"
Ci gaba yayi da kallonta har saida ta sake maimaitawa sannan ne ya iya d'aga mata kai da fad'in
"Bani ruwa na sha...!"
Amsawa tayi cike da k'warin guiwan samun nasara,sannan ta tafi don kawo masa ruwan kamar yadda ya buk'ata,wannan karon ma kam koda ta d'ebo ruwan bata yarda ta kawo masa shi a haka ba,saboda tuna cewar zak'i na tafiyar da maye,shi yasa tayi k'ok'arin duba zuma ganin bata samu ba yasa tayi amfani da abunda ta samu kawai ma'ana tasa masa sugar a ciki sannan ta dawo tana mik'a masa ruwan cikin girmamawa,ko daya shanye nan ya neman k'ari itan kuwa nan ta shiga aikin k'ara masa ruwan mai d'auke da sinadarin sugar,gare shi kuwa YASEER tun a karon farko da yasha ruwan d'an test en zak'in da yaji a cikin ruwan shi ne ya jashi har yayita sawa tana k'ara masa,suna nan a wannan halin YAZEED en shima ya soma dawowa dai²,kwatankwacin yadda suka yi da YASEER haka ce tayita faruwa tsakaninta da YAZEED en har Allah ya taimaketa suka d'an sauka daga halin mayem da suka tsunduma,ko data tabbatar a lokacin sun gama saituwa nan tayi musu sallama tana bin hanyar ficewa da niyyan tafiya inda zai fishsheta tunda dai burinta ta cika a lokacin,dai² tana daf da fita YAZEED ya mata magana,tsayawa tayi a dai² inda take kana ta juyo tana kallonsa sai k'ifta idanu take,cikin rashin wadataccen kuzari ya taso ya shiga nufo ta,yadda taga yana yi ne da irin mugun kallon k'urillar da yake mata ya kasa bata nutsuwa,take ta hau ja da baya saboda rashin takamaiman abunda zaije ya dawo,biyota yaci gaba dayi har sai da suka kusa danganawa da k'ofa koda taga idan sun kai nan babu kuma sauran gurin da zata nufa ai take ta faki idonsa cikin sauri ta bud'e k'ofar ta fice a guje.
Koda ganin fitarta haka nan kawai sai yayi murmushin da bai san dalili ba,seconni a tsakani kuma ya tsuke fuska yana tambayar kansa
"Shin me nake yiwa dariya ne..??"
Rashin amsa yasa shi d'age shoulders sannan ya koma ya zauna yana sakin jikin nan nasa mai kamar an nad'a masa na jaki,cike da jin haushin abunda ta aikata masa.
Ita kuwa jeeddah lokacin data samu ta gudu bayan fitarta a cikin apartment en nasu bata iya biyawa ta gefen uwar gijiyar tata ba dan a lokacin koda ace taje tofa bata da takamaiman amsan da zata iya bata idan har ta tambayeta game da labarin abunda ya faru tayi irin wannan jimawar daga aike,haka nan idan ace tak'i zuwa shima kuma bata san me zai faru ba idan suka had'u goben,wani tunanin ne ya sake dawo mata a ranta nan take ta shiga taradaddin wanda ya kamata ta d'auka cikin biyu,shin taje gurin Ummi'n ta sanar da ita gaskiyar abunda ya wakana ko kuwa ta wuce ta tafi ba tare data je ba idan yaso duk sanda suka had'u ta shirya mata k'arya..............???
_Sorry fan's wollah naje unguwa yau bam kuma samu na dawo da wuriba,typing enma sai bayan dawowata nayi k'ok'arin yi muku shi badan komai ba sai don bana son kuyi ta jirana har tsayin lokaci ba tare dana sama muku abunda zaku nishad'antu ba....Mu had'u a next page da yardar Allah._
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
🎂🥂
🍿
Let the God decorate each golden ray of the sun reaching u with wishes of success,happiness and prosperity 4 u,wish you a super duper happy birthday .
HAPPY BELATED BIRTHDAY CWEET DAUGHTER *KHADIJAT ABUBAKAR SA'AD (KHAIRAT).*
🥂🎂
🍟
*Pg 19.*
^^^^^^^^
Shawaran tafiya gida kawai ta yanke dan tana jin kaf fad'in duniyar babu da wanda zata iya yin wannan maganar,hatta kuwa da Ummi'n Yaseer en,haka nan take ji aranta ba iya Ummi kad'ai ba koda ma ace Inno'n ta ce bazata tab'a fad'a mata ba,duk iya adadin yadda za'a takurata babu yadda za'ayi ta iya fidda wannan sirrin,haka nan koda ace gobe matuk'ar taje kawai zata san abunda duk ta hanyar daya dace ta sanar sanar da Ummi abunda ya kamata,da wannan tunanin ta kama hanyarta ta komawa gida taci gaba da tafiya abunta,tana daf da isa gida ta tuna maganar Ummi akan zuwa taron da tace mata tana son ta halarta,duk da bawai itan har ranta take jin sha'awar zuwan ba,haka nan taji har ranta bazata iya k'in zuwan ba,dan tasan matuk'ar tak'i zuwa kuwa tofa kamar bata yiwa uwar gijiyar tata adalci ba,yadda taji har ranta hakanma ya zama kamar dole ne akanta ta halarta ko ba dan komai sai dan amsa gayyata kamar yadda ta amsata,har ta juya zata koma ko me ta tuna kuma ta dawo a hankali ta shiga gida ta sake gyara jikinta sannan ta fice a gidan,ita kad'ai tayi tafiyar dan ko da acema sai lallai da wani zasu je wajen to ita kam bata san da waye ya dace ta tafi ba,har ta isa d'akin taron ta gama duk kalle²n mutane ko Allah zaisa taga wani data sani amma shiru babu fuskar wani mutum d'aya data gani data mata kama dawanda ta sani,tana nan zaune shiru ita d'aya ta hangi Aisha tana shirin giftawa ta kusa da ita,tun kafin ta k'araso da idon jeeddah ya sauka a kanta ta gama ganeta sai dai itan da hankalinta sam bai kai kan jeeddan ba,haka itama kuma koda ta ganta bata mata magana ba,sai dai wani abu guda d'aya daya d'aurewa jeeddah kai,wanda ba komai bane face ganin Aisha a wannan taron,mamakinta da tarin tambayoyin da suka addabi zuciyarta a lokacin baya wuce son sanin alak'ar Aisha da taron,ta jima tana tunani da son gano wace irin alak'a ce ke tsakani amma sam tunaninta ya gaza kai mata kan amsar data dace dan haka kawai saita hak'urewa ranta taci gaba da baza ido,duka da zuwanta baifi minti goma ba suma su YASEER suka k'araso,ko da ta samu tabbacin akan halartar su taron ba tare data b'ata lokaci ba ta bar gurin ta kama hanyarta ta komawa gida zuciyarta wasai cike da farin ciki marar misaltuwa babban gurinta kenan dama taga sun isa gurin kuma gurinta ya cika,tun tana hanya take jin yadda wayanta ke vibrate amma ko kad'an tak'i kulawa har sanda ta isa bakin gidan sarautar ta sauka,ko bayan ta sallami mai napep ci gaba da tafiya tayi da k'afarta a haka ta isa cikin gidan tana tafe zuciya cike da nishad'i.
Koda ta shiga gida ta gama duk wasu uzurorinta da duk lokacin data b'ata,har lokaci. Inno bata dawo daga cikin gida ba,d'an k'aramin agogon dake mak'ale a cikin d'akin ta kalla nan take idanunta suka hasko mata nine minutes to ten,shiru tayi tana tunani dan tunda suke aiki gidan,daya kasance ba can suke kwana ba yasa basa kaiwa irin wannan lokacin basu dawo ba,amma yau ganin irin wannan shirun yasa hankalinta sam ya gaza kwanciya duk da k'ok'arin da take yi na ganin hakan ya faru,harta cire kayanta zata kwanta taji hakan bai mata ba,a hankali ta tashi ta maida kayan sannan ta fice ta kama hanyan cikin gida,hanyan shiru babu mutane sosai tana tafe tana tunanin mene ne yasa Inno yau tayi Lattin dawowa haka..Gashi dare sai dad'a jaa yake..? Dai² tana daf da fitowa daga wani line dake gaban nasu,kawai taga mutum ya tsaya a gabanta,mamaki ne ya kamata ko da taga haka sai dai bata kuka shi ba tayi niyyar canja hanya,a hankali tayi k'ok'arin matsawa zata bi ta gefe,amma nan enma sai taga ya biyo ta yayi blocking hanyan,kallonsa tayi tun daga sama har k'asa ta d'an saki dariya,kafin ta sake chanja hanya zata wuce,ga mamakinta nan enma sao gani tayi ya sake biyota,still tayi kawai a gurin tana nad'e hannayenta a k'irji gami da zubawa mutumin dake tsaye idanu,ta d'an b'ata a k'alla mintuna biyu tana nazarin sa kafin ta girgiza kai tana sakin murmushi,cikin muryar ta mai sanyi ta furta
"Yi hak'uri malam ka bani hanya na wuce,ina da abunda yafi min wannan tsayuwar muhimmanci.."
A maimakon taga ya matsa ya bata hanya kamar yadda tayi magana,sai taga ya ci gaba da tsaiwa yana kallonta,sake kallonsa tayi tun daga sama har k'asa,yadda ya rawane fuskarsa kamar wani buzu ko irin mutanen agadaz ennan yasa ta fara tunani akansa a hankali ta sauke numfashi tana d'an runtse danunta saboda bata yi zaton ganinsa ba tana fad'in
"Babba Yaya..! Kai ne a irin wannan lokacin..??"
K'in amsa mata da taji yayi,ta fara zaton ko yayi mata haka ne don yayi surprise nata,amma har lokacin sai taga yak'i yayi magana,jikinta ne ya fara bata a kwai matsala,sake zuba masa ido tayi cikin hikima da nazari ta fara fahimtar wani abu a tattare da mutumin,koda ta gama hakaitowa a ranta game da YASEER ta kuma tsaya tsaki ta kalli wannan sai yasa ta gano BAMBANCIN dake tsakanin su,koda ta gama fahimtar abunda take tunani akai,kawai sai ta juya da baya zata koma tana tafiya cikin sauri ta mik'i hanyar komawa gida,har tayi nisa zuciyarta ta sak'a mata wani abu,take kuwa ta waiwayo a tunaninta zuwa lokacin ta jima da baroshi a can nesa,ko data juyo en dan ganewa idanunta nan ta hange shi biye da ita,tsorata ta fara yi da lamarin mutumin,dan haka ba tare da jiran komai ba take ta k'arawa k'afafunta sauri,koda taga ta kusa da gida kuma tana juyawa taga ya kusa tarar da ita nan take ta take k'afafunta a d'ari da tamanin,ba ita ta tsaya ba sau data dangana da gida,tana shiga soron gidan nasu kuwa ta maida k'ofar ta kulle kana tayi ciki da sauri sai haki take saboda gudun daya sa tayi mai cike da mugun tsoro.Bata iya tsayawa nan a tsakar gida ba sai data danganta da d'aki sannan ta zauna tana maida numfashi,zuciyarta cike da zallar mamakin abunda ya faru yanzun,a fili ta shiga tambayar kanta abunda ya had'a ta da wannan mutum cikin damuwa "Shin waye ne wannan en daya tsorata ta haka kawai..??" Rashin samun wanda zai bata amsa yasa ta hak'ura,ta d'an d'auki lokaci tana maida numfashi sannan daga bisani ta mik'e ta cire kayan jikinta zuciyarta cike da tunanuka iri² ta kwanta,tana nan cikin wannan hali Baba ya dawo kasancewar bai cika zama sosai ba kuma koda yana gari mafi yawan cin lokaci baya dawowa gidan da wuri,da safe kuma kafin ma ace sun tashi tuni za'a iske shi har ya fita,ya jima yana bugun gidan kafin jeeddah ta jiyo ta fito tana nufan hanyar soron,koda ta zo soron kafin ta bud'e saida ta saurar tukun ta tsaya daga baya² saboda bata san da waye zata yi gami ba idan har ta bud'e,k'asa² ta fara tsinkayo muryar Baba yana mitar rufe gidan da akayi tun a wannan lokacin,koda jin haka sai yasa tayi saurin bud'ewa tana masa barka da dawowa kana ta amshi kayan hannunsa tayi ciki,a cikin y'ar rumfa tayi masa shimfid'a ta kawo masa ruwa da abinci sannan ta gaisheshi tana sake masa barka da dawowa,yadda yaji gidan shiru yasa bai ko tambaya ba dan daga dukkan alamu yasan Inno bata nan,ita kuwa jeeddah koda haka ta faru nan ta mik'e tayiwa baba sallama ta shige d'aki ta k'ule can k'uryar d'akin tana ci gaba da sakin ajiyar zuciya na samun nutsuwa,saboda dawowar baba a lokacin ba k'aramin taimako ya bata ba dan ko motsinsa da b'ab'atun radio ensa daya kunna yana sauraron taskar mako kad'ai ma hakan yayi mata dad'i,tana nan kwance tana y'an tunanikanta itama Inno ta dawo,tashi tayi tana niyyar fita daga d'akin,har taje bakin k'ofa ta hango wayarta dake saman y'ar locker enta ta kaya tayi Haske,da kamar zata duba kuma ta fasa,sharewa tayi abunta ta fice kanta tsaye ba tare data kula ba,bayan taje gurin Inno ta mata sannu da dawowa ta sake komawa d'akin,inda ta ajiye wayar ta fara nufa bayan ta d'auka kuma ta koma saman d'an gadon nata ta kwanta tana bud'e wayar,da miss call's ta fara cin karo a fuskar wayar,cikin tsananin mamaki ta shiga dubawa dan tasan babu mai kiranta a wannan wayan,bata gama tunanin da take ba da mamakinta k'arar shigowar sak'o ya ratsa kunnenta,a hankali ta bud'e ta shiga karantawa cikin kwanciyar hankali dan bata san ko na ina baane,irin sak'on da aka turawa YASEER itama shi en aka turo mata,koda ta gama karantawa bata tsaya b'atawa kanta lokaci akansa ba ta maida wayar ta ajiye had'e da mirginawa ta kwanta tana karanta addu'o'in kwanciya bacci zuciyarta babu damuwar komai...
^^^^^
A nasa gefen shima YASEER tunda ya samu ya bar YAZEED zaune a parlour'n,koda ya shiga bedroom soma raba jikinsa da kayan daya sa yaje dinner yayi,daga nan kuma ya fad'a bathroom yayi taking shower,sanda ya fito kayan da yasan zasu bawa gangar jikinsa damar samun wadatacciyar iska ya sanya sannan ya kwanta yana karanta addu'o'in bacci coz a lokacin sam baya son duk wani abu da zai takura shi ko sawa ransa damuwa da zata iya janyo masa kwana da ciwon kai,dai² yana juyawa YAZEED ya shigdad'iima,alamun shigowar sa da yaji yasa shi saurin rufe ido dan a lokacin sam bai shirya yin ko wace irin magana da shiba,ta gefe shima YAZEED en ya kalleshi had'e da tab'e baki dalilin kuwa yasan ko kad'an yasan YASEER ba baccin yake ba a lokacin,haka nan kallo d'aya zaka masa ka fahimci akwai abunda yake b'oyewa,shima har ya gama abunda zaiyi ya kwanta YASEER en yana a yadda yake ba tare da bacci ya d'auke shi ba haka nan kuma idanunsa har lokacin a kulle suke ta yadda babu yadda za'ayi ayi saurin gane hakan...
^^^^^
A b'angaren maimartaba kuwa tun daga lokacin da yasa akayi kiransu amma shiru har zuwa tsawon wucewar wasu sa'o'i basu halarci gurin ba yasa suka fara shirin barin gurin,suna daf da niyyan nasu ne Allah ya kawo su YASEER gurin,wannan yasa koda ganin haka sai suka fasa tafiya har sai da suka jira har zuwa lokacin da aka gabatar dasu a lokacin da suke yin tsokaci game sa irin nasarorin da suka samu a harar karatun su dama rayuwarsu,iya kar abunda suka iya saurarawa kenan saboda wucewa lokaci yasa maimartaba bada umarnin su kama hanyar komawa gida saboda dare ya fara tafiya.
Lokacin da suka dawo gida kuwa tun kafin suyi sallama maimartaba ya dakatar sa d'an uwan nasa inda yayi masa tuni game da meeting en k'arshen shekara da zasu gudanar a family'n nasu cikin sati mai kamawa,daga nan suka yi sallama kana fadawa suka rakashi har b'angaren Fulani,shima GALADIMA yayi nasa gefen saboda huta gajiya.
Tun daga shigowar GALADIMA da yadda ya d'an had'e fuska Ummi ta fara shan jinin jikinta,dalili kuwa tasan yau kam tsakaninta da mai gidan nata sai ta Allah akan abunda su YASEER suka aikata,tsaf yanayin sa ya gama bayyana mata itan mai laifi ce,sai dai koda ganin haka sai yasa ta k'udurce a ranta da duk iya fad'an da zai mata a wannan lokacin bazata tab'a tankawa ba,zata tank'washi kanta ta bashi hak'uri ne duk da ba ita takar zomon ba,tana wannan tunanin kawai sai yayi abunda ya matuk'ar bata mamaki duk da sanda ya shigo fuskarsa babu wata wadatacciyar walwala,har tayi masa barka da dawowa ya amsa,haka har sanda suka yiwa juna sallama suka kwanta bai tada mata maganar ba,sai bayan data kwanta ne wayarta tayi k'ara,sunan YASEER data gani ya bayyana shi ne yasa tayi hanzarin d'auka kana ta bar kusa da Abba GALADIMA,dan yadda yakeennan bata san me zai faru ba,tsaf suka gama maganar duk da zasu yi ta dawo,amma duka har lokacin bai ce mata komai ba,ko da ganin haka sai itama ta tattara komai ta ajiye shi gefe sannan ta kwantar da hak'ark'arinta...
*One week later...*
Kimanin kwanaki bakwai da dawowarsu k'asar,taron na family taso gadan²,a b'angaren YASEER kuwa tun daga dawowarsu k'asar har kawo yau ko kad'an tsakanin shi da jeeddah ba'a barsu sun huta ba,kullum rana da zata fito ta gabas ta fad'i a Yamma da kalar sak'on da za'a turo musu,haka ko wane sak'o akwai irin razanin da yake d'auke da shi,sai dai garesu duk da sun tabbata mai turowar a shirye yake da aiwatar da duk abunda ya fad'a hakan ko kad'an baisa sun nuna a fili ba,dalili kuwa shine sun jima da sanin matuk'ar za'a dunga turo musu irin wad'annan sak'onni tofa dole ne mai aikata hakan yana kallonsa a ko wane lokaci haka zalika a duk wani motsinsu,wannan tasa su b'oyewa dan dole saboda basa son ko kad'an su nunawa b'oyayyan mak'iyin nasu gazawarsu.
Kasancewar yau en ta kama ranar taron family'n gidan sarautar,yasa tun daga kan iyaye kama har zuwa y'ay'a da jikoki na wannan ahalin duk sun halarci taron,family ne Babba da ko cikin garin na kano babu wanda zai ce bai sansu ba,sai dai kasancewar wasun su ba mazauna k'asar ba da aiki ya rarrabasu garuruwa zuwa k'ashashe yasa ba'a cika ganin yawan nasu ba,sai ko a irin wannan lokacin da suke gudanar da bikin k'arshen shekara ko wata hidima itan ta taso,shi ne kad'ai yake iya bayyanar da asalin yawan su.Harabar gurin a cike yake taf da jama'ar family'n kwansu da k'wark'wata duk suna gurin zaune cikin manyan rumfuna da aka sa masu d'auke da shimfid'u na alfarma,gurin yayi shiru saboda jawabin da Matawalle yake gabatarwa na game da nasaba ta wannan family,a cikin batunsa na k'addamar da littafin zuri'ar mai d'auke da sunan kakan maimartaba Alh Abdullah Muhammad jibirillah wanda shi ne asalin zuri'ar tasu,ma'ana dai ta kansa ne chain en zuri'ar ya faro,har zuwa kan iyayen su zuwa kansu da y'ay'a,sai jawabi na gaba da zai gabatar da k'addamar da wad'anda basu tab'a samun damar halartar taron ba ko sau d'aya (marasa zumunci kenan),a k'arshe kuma Matawalle ya rufe da sanarwa ta sa ranar auren wasu y'ay'a nan a cikin family'n,kana aka yi addu'ar rufe taron baki d'aya.
Sanda YAZEED ya tabbatar an tashi a taron,ya mik'e saboda gajiyar zama gurin da yayi,yana yiwa YASEER magana akan su bar gurin saboda yadda ya fahimci idanun y'an matan family'n nasu na kansu,basu jima da barin gurin ba kuwa,suma Adda da HAJIYA suka keb'e a b'angaren hajiyar na nan cikin gidan,hira suka dasa sosai irin wacce suka kwana biyu basu yiba a matsayinsu na y'an uwan juna,sai ga Aisha sun shigo tare da y'ar gidan Matawalle mai suna Sajida,ko kad'an basu yi tsammanin kakannin nasu suna zaune a b'angaren ba,tun kafin su kai ga shigowa Sajida ta kalli Aisha cike da zumud'i ta shiga labarta mata irin yadda ta jima tana dakon son YASEER,yadda tayi maganar yasa Aisha tayi mata dariya kafin ta furta
"Kai y'ar uwa gaskiya ina miki murna sosai,yadda kike son nan nasa ina miki fatan ya soki fiye da haka,sannan na tabbata matuk'ar kika same shi a matsayin mijin aure kinyi dace wollahi sosai.."
"Thank yuh y'ar uwa da wannan yabi naki..Gaskiya naji dadi sosai,kuma na gode miki da kika min wannan hasashen..Ammafa kema ko gaskiya na miki sha'awar wani handsome a gurin nan..Ba don komai ba sai dan yadda idan kuka zama makusantan juna abun zai bada colors tamkar rainbow..."
Murmushi Aisha tayi ba tare data bata amsa ba,can Sajidar ta sake kallonta itama tana mata murmushi,kafin cikin zumud'i ta furta
"Kinyi dariya bayan baki tambayeni ko waye na gano miki ba,bare ki bani tukuici...Kumafa ko Allah nasan ko ke kika ji abunda zan fad'a na tabbatar sai kin susuce dan nasan shu en ba irin k'ananun yaran nan bane,mutum ne shi mai aji..!"
"Kaii! Sajee kin cika damuwa wollahi,banda abunki taya kike tsammanin ni zan kai kaina gare shi..?? Bakya tunanin ni en na fishi aji ne da had'uwa..?? Karfa ki manta da adadin samarin dana baki labari
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 63