tare da biyan tarar naira dubu d'ari biyar²,,,da wannan ne wannan kotu take jan kunnen duk wani mai yunk'urin aikata laifi makamancin wannan,bayan wannan kuma take sake kira ga sauran al'ummah akan su guji aikata munanan ayyuka irin wad'annan,,bayan nan kotu ta bada umarni da atsare wad'annan masu laifi daga yanzun har zuwa lokacin da wa'adin su zai cika.."
Ai koda Abba matawalle ya gama jan jawabai akan irin hukuncin da suka cancanci su Adda da muk'arrabansu tunma bai k'arasa ba take Hajiya Suwaiba ta waiwayo idanunta taf da hawaye tana kallon Adda
"Kin cuce ni Adda.. Wollahi bazan tab'a yafe miki ba,,yau a irin hud'ubobinki gashi kin dulmiyar dani..Allah ya isa tsakanina da ke,,da irin zaluntata da kika yi,,Allah ya tsinewa zuciya irin nak'i..Kin cuce ni,kin cuci rayuwata da rayuwar aurena,,yau gashi kin janyo min zubar k'ima a idon duniya,,In sha Allah sai kin wulak'anta sama da haka tsinanniya matsiyaciya Allah ya tagayyara rayuwarki data zuri'ar ki kwatankwacin yadda kika sani shiga cikin bak'in ciki.."
A fusace Ladidi ta taso kan Hajiya Suwaiba cikin kumfar baki kamar zata daketa
"Keee! Suwaiba ya isheki haka nan,, idan kina hauka ne to ki san iya inda haukarki zai tsaya,kada kiyi KUSKUREN sake zagar min mahaifiya,,idan ba haka ba kuma zan koya miki hankali,,dan zan ajiye miki darasin da baki tab'a ganin irinsa ba a rayuwa..!"
"Keee! Kece!! Ladidi sauraramin idan shika²n rashin mutunci kike ji da su nima fa babu wanda ban iya ba,,sannan kada ki manta duka ayyukan ku da duk wani sirri da kuke ji da shi a tafin hannuna yake,,,ko kisan irin maganar da bakin ki zai fad'a ko kuma zan tona muku duk wani abu da kuke ji da shi,,idan kina musu kuma to bismillah d'an halak ka fasa tsakanknmu,,try me nd see.."
"Bazan yiba,,kiyi duk abunda kike ganin za kiyi,ke har kin isa kisan sirrinmu..?? Ke awa..??"
Adda dai jikinta banda tsuma babu abunda yake a wannan lokacin,so take ta takawa Ladidi burki da sakin zancen da take k'ok'arin yi dan tana daf da sawa allura ta tono garma amma kuma ta kasa dan yadda idanu duka yake kansu tana tsoron sake yin wani KUSKUREN
"Ki ci gaba to kinji bazan kuma hana kiba,,amma kika yi KUSKUREN zagina wollahi sai kin gwammace baki yimin duk abunda kike yiba yanzun,,ke in tak'aita miki wollahi sai kin gwammace baki zo duniyar ba a a yau da abunda zan fad'a.."
Su kuwa a b'angaren jama'ar parlor'n gaba d'aya sun zuba musu idanune suna sauraren yadda suke musayar zance a gaban kowa ba tare da tunanin komai ba,,su ma su Yarima a nasu gefen kallon juna suka yi suka saki murmushi zuciyar Yarima fal farin ciki yake fatan a samu sab'anin da zai janyo ayi tone² tsakanin su Hajiya Suwaiba da Adda'n,tunawa da basu kad'ai ne a cikin parlor'n ba yasa shi juyawa gefen A.S.P Hood ya sallamesu akan su jira su a waje akwai y'an maganganun da za suyi da su Adda'n,godiya Hood d'in yayi masa sannan suka tusa k'eyar su JIBO zuwa motar PRISON da aka kira,,while a parlor'n Hajiya kuma tuni tura ta kai bango inda Ladidi tak'i jin kashedin Hajiya Suwaiba,,ta zage sai ruwan bala'i take ta zazzaga mata kamar wata sa'arta,,Hajiya Suwaiba kuwa tunda taga Ladidi na neman wuce gona da iri girgiza kai tayi sannan ta kalli Adda tana cizar lips
"AISHA..na ce ki jawa y'arki kunne amma kin k'i,sannan na mata kashedi tak'i ji ko..?? To tunda haka kuka zab'a ni kuma na lashi takobin falassawa kowa abunda ya gabata da aketa rufewa,yau d'innan saina ga abunda ya turewa buzu nad'i,zan tona duk wani mugun aikin ku a cikin gidan nan idan yaso kowama yasan suwaye ku d'in,ina tunanin daga yau babu wanda zai sake muku kallon arzik'i,kamar yadda kuma sai kunji kunyar sake rayuwa a cikin garin nan.."
Cikin tsawa Adda ta kalli Ladidi bakinta har sark'ewa yake wajen yi mata magana
"Da Allah kiyiwa mutane shiru anan,,kada ki kuskura na sake jin bakin ki,ko baki jiba..??"
"To ni Adda taya zan jure ace a gaban idona ana k'ok'arin tozartar ki..?? Wollahi duk wanda yayi yunk'urin tab'a ki sai inda k'arfina ya k'are,, ba zan tab'a sa musu ido ba,dole ne nayi yak'i da koma waye indai akan k'imarki ne.."
"Na ce miki ki rufemin baki a nan ko..? Ko kuwa ban isa nace ki bari kiyi shirun bane..??"
Ba don Ladidi ta so ba haka ta shiga jinjina kai tana sakin k'wafa had'e da jifan Hajiya Suwaiba da mugayen kallo,cikin maganar habaici tana k'unk'uni k'asa² ta sake fad'in
"Wollahi Allah ya taimaki mutum amma ba don haka ba da sai dai mu kwashi y'an kallo dan uban mutum naga mai shallakewa a cikinmu."
Dariyar takaici Hajiya Suwaiba ta saki kafin tace
"Yaro..yaro ne.! Amma tabbas kinyi da y'ar halak nd from now na san baza kiyi k'ok'arin sake tun karata da ko kallon banza bane bare bak'ar magana irin wannan,,,for now kowa zai san suwaye ku.."
Tana fad'an haka ta juya tana kallon kowa dake cikin parlor'n kamar yadda suma suke kallonta da tsantsar mamakin musayar yahun da suke yi da Ladidi,bata damu da irin kallon da suke mata ba nan ta juya ta sake kallon Adda da tayi tsuru² a gurin duk tayi wani irin tsuru² kamar wacce aka jefa a ruwa,murmusawa tayi irin murmushin nan da ake cewa yafi kuka ciwo sannan ta d'aga kai kamar mai son tuna wani abu,,Aisha dake gefe itama jikinta duk yayi sanyi tun bayan da aka yankewa Adda hukunci take kuka kamar wacce za'a tafi da uwarta,kan Adda ta sake juyawa tana mata wani irin murmushi sannan tace
"AISHA..coz a yanzun banga amfanin girmamawa ga mutumin da bai san girman ba,,da fari na so ace na kyaleki da iya abunda kika min,,,buh yarinyar ki ta janyo muku duka itace mutum ta farko data min abunda nake jin bazan iya yafe muku ba,,saboda haka ba zan tab'a iya hak'uri naci gaba da zuba muku ido ba,,da ace tun farko kin bi maganata kin dakatar da ita na tabbatar babu wani abu da zai faru,,amma tunda bata ji ba shi kenan,nima dama ba ji nake ba a duk lokacin da aka b'ata min rai."
Gefen Hajiya ta sake waiwaya sannan ta sake kallon Ummi'n YASEER dake zaune tayi shiru sai kallonsu take
"Hajiya dan Allah ina neman gafaran ki akan duk abunda na aikata,,,wollahi nayi nadamar biyewa son zuciya da rud'in wannan matar.."
Tayi maganar tana nuna sashin da Adda take ba tare data kalleta ba
"Hak'ik'a wannan da kuke gani sam bata dace da zuri'ah irin wannan ba,ko kad'an bata cancanci a nuna mata soyayya kwatankwacin wacce kuke yi ba,,,wannan da kuke gani a matsayin mutuniyar arzik'i ba kowa bace ita face shaid'aniya data dulmiyar da rayuwarta kuma take k'ok'arin dulmiyar da rayuwar wasu,,,na tabbatar da ace tun kafin yanzun kun san wace ce ita da tuni kowa ya jima da sallama lamuranta,,sai dai hak'ik'a a yau nayi niyyar sanar da ku wasu b'oyayyun sirri,wanda na tabbatar dukan ku sai kunyi matuk'ar mamakin yadda akayi hakan ya kasance,kamar yadda ya faru a shekaru ashirin da shida da suka gabata,wanda na tabbatar mafi yawancinmu sunsan wani AL'AMARIN daya tab'a faruwa a gidan nan,ko dama ace bamu sani dukan muba,to ina da yak'inin rabinmu sun san da faruwarsa,duk da AL'AMARI ne daya kasance ya faru a keb'e,,,amma na tabbata idan kowa ya kasa fahimtar abunda nake nufi Ummi baza ki manta ba,dan kuwa kece mutum ta farko da kika san da faruwar AL'AMARIN sannan kika fi kowa jin ciwo da faruwarsa kasancewar daga kanki ne komai ya samo asali..!"
Kallonta Ummi'n YASEER take tana squeezing face kamar mai son gano ma'anar maganar ta Hajiya Suwaiba,haka ma sauran al'umman parlor'n duka kallonta suke da son gane abunda take son fad'a d'in
"Tabbas abunda na fad'a haka yake,,kuma kuma yanzun za ku tabbatar da gaskiyan abunda nake fad'a,,,kamar yadda kuka ji na fara bayani,a shekarun dana ambata idan har zaku iya tunawa,,a wannan lokacin Ummi ta haihu,sannan bada jimawa ba aka samu gilmawar wani AL'AMARI a cikin kwanakin,buh na manta actual na adadin kwanakin dake tsakanin,sai dai ina tunanin tsakanin kwana biyu da uku ne na manta,buh tabbas atsakanin wad'annan kwanakin dana ambata ne,tazo take shaida muku kan cewar Allah ya karb'i rayuwar yarinyar data haifa,,,shin za ku iya tunawa da wannan AL'AMARIN..??"
Duka fuskokinsu cike da alamun son tunawa da AL'AMARIN daya farun wanda ita Hajiya Suwaiba take ta k'ok'arin son tunatar da su
"To ina so ku saurara ku kuma fahimci maganata,,,tabbas a wannan lokacin yarinyar da akace ta mutu,ba mutuwa tayi ba kamar yadda kuke zato,,dalilin da yasa nace haka kuwa ni shahid ce akan wannan maganar daya kasance BOYAYYE a idon kowa,sannan WANI AL'AMARI ne daya kasance ya faru a wannan daren,,buh idan har kuna ganin wannan magannar da nake fad'a k'arya nake gata nan a zaune ku tambaye ta ko anyi hakan..??"
Ummi kam lokacin tuni ta shiga wasu irin commotions masu wuyar rarrabewa,,wanda daga yanayin yadda take nuna alamun damuwa a saman fuskarta ya janyo duka kowa ya fara binta kallo son tabbatar da inda maganganun Hajiya Suwaib ke nufa,haka kowa zuciyarsa da irin zargin da take kawo masa dangane da maganar hajiya Suwaiba
"Shin kuna kokwanto ne akan magana ta..?? Gata nan ai ku tambayeta abunda take boy'ewa,,na tabbatar tasan da wannan batun,,idan kuma har ba gaskiya nake fad'a ba to ta k'arya ta ni..!"
Shiru Ummi ta sake yi tana sunkuyar da kai k'asa fuskarta d'auke da matsanancin damuwa,ita kuwa Hajiya Suwaiba wani kwantaccen murmushin takaici ta sake saki kafin ta ce
"Ummi..! Shin me yasa za kiyi shiru ne bayan kin san gaskiya nake fad'a..?? Me zaisa ki kasa amsa min magana ta.?? Na tabbatar kin san gaskiya nake fad'a,,shin yanzun baza ki iya yiwa mijinki da surukanki bayanin inda yarinyar ki take ba..?? Me yasa zaki b'oye wannan gaskiyar..?? Ki fad'a mana da bakin ki..!"
"Hajiya Suwaiba..! Ya isa haka..! Dan Allah na rok'e ki da kiyi shiru hakan nan,,shin mene ma'anar tada wannan maganar daya riga ya wuce..?? Mene ne amfanin tada zancen daya gama zama matacce..?? Me yasa kike son busawa wannan labarin mai cike da tashin hankali rai..?? Why zaki yi hakan..??"
"Ina so ne a yau na fito da wata gaskiyar data jima a b'oye,,ya kamata ace kin fahimci ni Fatima..Nima duk ba'a son raina bane,,dole ce tasa ni yin hakan saboda bana son barin zaluncin da suka jima suna aikatawa yaci gaba da wanzuwa a doron duniya,,,shin bakya tunanin rayuwar wansu tsirarin mutane a ciki,,wad'anda a koda yaushe ta kasance tana gurb'ata da tashin hankali..? Shin kin san su waye wad'annan mutanen da nake nufi..!??"
Shigowar Inno a dai² lokacin d'auke da wata y'ar jaka a hannunta ta saki murmushin takaici sannan ta furta
"Ni zanyi miki duk bayanin da kike buk'atar ji Hajiya Suwaiba,,dan na tabbatar ia sahun mutanen da suka kasance suna binne wani b'angare na daga wannan ajiyayyen sirrin.!"
Gaba d'aya kallonsu ya koma bakin k'ofa saboda jin magana a dai² gurin,zabura Ummi tayi ta mik'e tsaye tana kallon Inno da take ci gaba da takowa cikin parlor'n idanunta d'auke da wasu irin hawaye na tsantsar tsoro tana kad'awa Inno kai tana kuma nufar inda take
"A'a Inno kada kiyi min haka..?? Ki tuna irin alk'awarurrukan da kika d'auka min tun a wancan lokacin,,yanzunma ina mai sake rok'on ki da kiyiwa Allah ki ci gaba da keeping promise d'ina a zuciyarki,, ko da bayan raina ban amince ki bayyana shi ga kowa ba,,,ki tuna da wannan,ki yimin alk'awarin zaki min wannan alfarmar..."
Kai itama Inno take kad'a mata idanunta suna bayyanar da kyallin hawaye
"Ki gafarce ni ranki ya dad'e,,wannan fa *WANI AL'AMARI* ne da bai kamata ace munci gaba da b'oye shi ba,,ya kamata ne ace a yanzun tunda har an taso da maganar ayita a idon kowa kuma kowa yasan *ASALIN GASKIYA.."*
Ci gaba Ummi take da girgiza mata kai tana fad'in
"A'a..! A'a..!!"
Amma ina Inno kam bata saurareta ba,dan lokacin gaba d'aya ma ta juya tana kallon ahalin masarautar tana fad'in
"Ku gafarce ni,,nayi muku kutse cikin lamarin ku,,sai dai banyi haka ba sai dan na tabbatar da bayyana wata gaskiya da ba kowa ya san da kasancewarta ba sai ni da Ummi.."
Tana kallonsu duka duk da zuciyarta na tsananta bugawa,izinin magana Abba Galadima ya bata a hakanma wai shi ne mai dama,tunda har ya iya b'oye nasa damuwar yayi magana,bayan tayi godiya sai ta nemi guri ta zauna,,Hajiya Suwaiba kuwa koda taga haka take itama ta k'araso kusa da ita sannan ta cewa
"Ina neman alfarma a gurin ku duka,,amma ina son a bani aron mintuna goma kacal kafin Inno tace wani abu,,dan ina da buk'atar na furta duk abunda ke raina,saboda tun kafin zuwata nayi alwashin fad'ar duk wani k'ullin da suka aikata,saboda haka bana son ace an katse ni daga niyyar dana d'aura."
Babu wanda yace komai dan haka sai kawai taci gaba da magana abunta
"Kamar yadda kuka ji na fara sanar da ku,,tabbas duk wasu al'amura da suke faruwa a wannan gidan ba da sa hannun kowa suke kasancewa ba face HAJIYA AISHA (Adda) da y'arta,,kamar yadda suka sha fad'a ne da bakunansu cewa basa barin BASHIN GABA,,haka nan basa yafiya akan 'DAUKAR FANSA,dan haka ya zamana a duk lokacin da suka so suke k'ulla duk wani tuggun daya kasance ya faru.."
Hajiya cikin b'acin rai ta d'aga kai ta kallo Adda da tayi tsuru² sai kame² take dan tun gabanin a gama fad'an ayyukanta har ta fara tsintar kanta a cikin wata irin kunyar da bata tab'a jin kwatankwacin irnita ba
"Dan Allah Suwaiba ki bud'e baki kiyi mana bayanin abunda kika sani,,mene ne amfanin cakud'a zance ne haka matuk'ar kina son fad'a.?? Kiyi mana bayani kai tsaye duka muna sauraronki.."
Jinjina kai tayi sannan taci gaba
"Kamar yadda ya kasance ya faruwa a wasu lokutan da suka shud'e,na san dukan ku babu wanda zai ce bai san yadda muke Adda a cikin family'n nan ba,na tabbatar bisa yak'ini na kowa yasan mene ne a tsakanin mu,,dan irin amintaka,yarda da juna da muka mallakawa junanmu ya zamanto har wasu a cikin family suke yawan yar mana da magana a wasu lokutan,saboda yadda muka kasance masu sharing damuwar junanmu,haka ma abun farin ciki bama tab'a boy'ewa juna,akan wannan d'abi'ar muka gina rayuwarmu tun kafin yanzun,wanda har ya janyo amintarmu ta zartar duk yadda ake tunani,,duka fa wankan bayanin da nake ba don komai nake yinsu ba sai don ina son ku sake fuskantar abunda nake son fad'a muku,,sirri ko wane iri ne mun kasance bama tab'a boy'ewa juna shi ba,akan haka nema wata rana a irin ranakun da nake zuwa gurinta,bayan mun keb'e kamar yadda muka saba sai take sanar da ni wad'annan maganganun da nake son fad'a duk da ta rok'i na ajiye su a zuciyata kamar yadda na saba,sai dai a yau naji bazan iya sake ci gaba da ajiyar ba..Duk da a yau Allah ya fara tona mata asiri,ni kuma nayi alk'awarin k'arasa sauran ta hanyar sanar muku dalilan da suka haifar da zuwan YARIMA YAZEED kurkuku,,sannan da dalilin da yasa UMMI tace yarinyar data haifa ta mutu,,sannan na k'ara muku da dalilin da yasa aka zo domin sace jaririn da baijiba bai gani ba,saboda haka ku biyo ni.."
Ai dukansu jin yadda ta amvbaci zuwan Yarima kurkuku da maganar yar Ummi data mutu nan take jikinsu duk ya d'auki tsuma,kowa burinsa bai wuce yaji yadda aka yi aka haihu a ragaya ba,,to nima dai haka na zauna na baza kunnuwana dan jin wannan zazzafar tak'addamar data b'arke a cikin wannan family
"Kafin na fara muku bayanin wannan dalilin zan so na d'an yi muku highlighting wasu abubuwan da suka fara faruwa tun a shekaru sama da talatin baya,wanda a lokacin na tabbatar sune asallin faruwar komai,,a zamanin can baya a lokacin da Ladidi ke kan ganiyar k'uruciya,,Hajiya dake da maimartaba idan har ba wai kun manta ba Adda ta tab'a samun ku da maganar son had'a aure tsakanin Ladidi da Abu YAZEED,shin anyi haka..??"
Idanun Hajiya dai na kanta amma ta kasa amsawa saima numfashi data saki wanda jin yadda taja shi ya isa ya bada tabbacin anyi hakan,,wanda su kuma a gefen sauran mutanen dake zaune a gurin suke ganin abun kamar almara dan yadda suke kallonsa ko a labarin hikayoyi basa zaton za'a iya cin karo da irin wannan da suke gani
"To wannan shi ne asalin gabar dake tsakanin ku da Adda....."
Durus duka suka tsaya kowa fuskarsa d'auke da alamun tambayar ya akai hakan ya kasance bayan su yadda suka santa ya sab'a da yanayin yadda itan take k'ok'arin yi musu bayani...??
"Dole ne nasan dama sai kunyi mamaki..?? Amma ba abun mamaki a cikin duk maganar dana fad'a,, saboda nasan kun san yadda muke da ita,,saboda haka babu ta yadda za'ayi nayi mata k'arya kan duk abunda nake fad'a,, idan kuma har kuna ganin sharri nake yi mata to ku jira idan na gama magana sai ku bata izinin k'aryatawa.. Hajiya tun daga lokacin da Adda'n tazo miki da wannan batun na son ku had'a auratayya tsakanin Ladidi da Abu YAZEED wanda kika nuna mata ke bakya ra'ayi,haka shima maimartaba tun a lokacin data bibiye shi dan ya amince da maganar koda bakya so amma sai ya nuna mata kan cewar kin riga kin masa mata kuma yayi na'am,dan haka tayi hak'uri kawai,shin ta sake tada maganar..?? To a wannan lokacin bayan ta gama zagayen a tsakaninku ta tabbatar babu nasara sai bata nuna komai ba,amma kuma a lokacin da taji labarin Aliyu ya dawo k'asar dan haka sai ta sake d'ana tarkonta akansa,wanda shima d'in dai sai ya zama kamar lokacin farko dan kuwa babu nasara,to daga wannan lokacin ne sai tayi alk'awarin duk yadda za tayi taga bayan wannan zuri'ar sai tayi,,dan haka ni yanzun ina d'an sake yi muku fashin bak'i ne ta yadda zaku fahimci maganata,,saboda haka.................
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
_May this year bring u a good luck,fortune,success,love nd friendship.Most importantly,may it bring u more closer to what Almighty Allah wants from u..Happy Belated Birthday Lil Sis💝._
*@Hafsat M.U (real hafsy)🌹*
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 40.*
^^^^^^^^
*#A hidden truth 2*
"Suwaiba..!! Ki dakata nan kada ki wuce gona da iri..!"
Ladidi data mik'e tsaye cikin firgicin yadda Hajiya Suwaiba take k'ok'arin fara bankad'a musu zani ta fad'a cikin k'arajin masifa,juyowa Hajiya Suwaiba tayi ta kalleta da wani irin yakusasshen kallon kinyi kad'an kiyi min irin wannan maganar mai cike da rashin tarbiyya na sauraren ki,sannan ta ci gaba da magana abunta in a calmness way
"Me kike tunani ne Ladidi,me kuma kike tunanin yi min..?? Shin kina tsoron tonuwar asirinku ne ko kuwa kina shirya wani tuggune da kike tsoron asirinki ya tonu..?? Tun da farko mena fad'a miki da kina zak'ewa.?? Da ace kinji warning d'ina kin ja bakinki kinyi shiru na tabbata nima da na iya kwab'ar bakina,,amma kashhh! sai kika kasance mara jin magana mai taurin kan tsiya,dan haka nima ba jinku zanyi ba.. Saboda haka muje zuwa.."
Bata sake ko bi takansu ba ta waiwaya ga d'aukacin mutanen parlor'n da duk suma suke kallonta
"Na rantse da Allah matuk'ar kika sake cewa wani abun a nan gurin,zan tabbatar yau na nuna miki ainihin ko wace ce ni..!"
Bata damu da maganar taba dan tasan hakan ba komai bane face irin barazanar da suka saba yiwa jama'ar da suke mulka ko mu'amala da su kuma wad'anda suka kasance suna matuk'ar jin tsoron su,itan kuwa data tabbatar zuciyarta a dake take,babu sofanen tsoron su a ranta sai ta saki wasu irin frights smile da suka matuk'ar sa y'an hanjinsu kad'awa,,ran Yarima kuwa a b'ace jin yadda Ladidi ke kawo musu datsiya a AL'AMARIN,d'agowa yayi yabi Ladidi da wani mahaukacin kallon da babu komai cikinsa face zallar k'iyayya,yadda take pretend d'in alamunta duk sun gama bayyana ta a matsayin mara gaskiya,haka nan duk wannan surutun babu abunda yake sake nunawa face rashin son a fayyace gaskiya,ci gaba Hajiya Suwaiba tayi da maganarta
"Tun daga lokacin da kika tabbatar mata aure bazai yiwu tsakanin Abu YAZEED da Ladidi ba,sannan tun gabanin auren Maimartaba da Fulani,Adda ta fara k'ok'arin ganin auren bai tabbata ba kamar yadda kowa a cikin family yake murna,tayi abubuwa da dama akan auren amma AL'AMARIN Ubangiji duk abunda tayi sai suka dunga tashi a banza,sannan saboda Ubangiji ya tabbatar mata bata isa ba ya k'ulla auren da take son ganin bayansa tun ba'ayi nisa ba a kuma dai² lokacin da bata yi zato ba,,ko da ganin bata yi nasara a nan ba hakan bai sa ta hak'ura ba,nan taci gaba da tono mutane da take son su dinga mata aiki a cikin wannaan gidan,suna bata labarin duk halin da ake ciki,,a dai² wannan lokacin kam ta samu nasara bayan d'umbin wahalan data sha kafin ta samu wanda ya amince ya shigo cikin gidan nan,wanda wannan mutumin ba kowa bane face JIBO da aka kama cikin masu k'ok'arin sace d'an Yariman,,shi ne mutum na farko da take bawa orders akan duk wani motsin al'umman gidan nan ya aiwatar mata da aikin data sa shi akan lokaci,sannan shi ne wanda na tabbatar a mafi yawan lokutan da take sawa a aiwatar da aikin yana shigowa cikin gidan kai tsaye ya gudanar da ayyukansa ba tare da an fahimci wani abu ba,,tun daga auren Maimartaba har zuwa haihuwan YAZEED anyi ta samun sab'ani daban² haka nan abubuwa sun faru na rashin dad'i buh babu wanda yasan daga ina ne hakan ke faruwa nd babu wanda yayi zargin wani,a gefe guda kuma dangane da ayyukanta sai tafiya suke sai dai ba wani sosai bane,,,al'amura basu dad'a cab'ewa ba sai a lokacin da Ummi take daf da haihuwa na biyu,duk da kafin nasara a wasu lokacin sai an samu cin karo da rashinta,nd a time d'in ganin sun buga basu samu irin nasarar da suke son samu akan wannan ahalin ba sai suka sake shawaran yadda zasu juya akalar aikinsu zuwa ga Ummi da ahalinta a cewansu itama d'aya ce daga wannan ahalin masarauta duk abunda ya sameta ko jininta dole ne kowa dake cikin gidan zaiji bak'in ciki,da haka duk sai suka sake karkata akanta nd duk wani shige da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 56 Chapter of 63