Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fito da manyan luggage's d'inta,,haka gidanma bata barshi ba sai data tabbatar ta kulle ko ina sannan ta sallami baba bayan ta shaida masa bazasu sake dawowa gidan ba,amma sai ta b'oye labarin abunda ya faru,kawai dai ta shaida masa sun koma can masarauta ne,dattijon kuwa shima bai kawo komai a ransa ba yayi musu addu'ar fatan alkhairi sannan ya tattare y'an kayansa,daga nan kuwa sai ya kama hanyan kauyensu,itama Aisha ko da taga ya tafi bata iya barin gurinba sai data ci kuka mai isarta sannan tasa kayanta a bayan booth d'in motar Adda da key d'in ke hannunta ta kama hanyar komawa asalin gidan iyayenta.. _Wannan kenan.._ Kwanaki sun ci gaba da gangarawa a b'angaren ZAHRA MALEEK,dan ak'alla yanzun da yi mata aikin ma an doshi kwanaki kusan goma wanda kuma cikin hukuncin Ubangiji tun daga ranar da aka yi aikin a kullum ake saka ran ganin haske dangane da aikin nata,,to sai mu ce Allah ya k'aro sauk'i,nd Ubangiji yasa a bud'e aikin a sa'a.. *BACK TO PRISON......* *Bari muji ko wace wainar ake toyawa a can kuma............* *Kaiii! kumin afuwa aradu na rubutu ba zan iya kawo muku abunda ke wakana a can ba,,buh mu tarawa cikin next page in sha Allah,wanda cikin hukuncin Ubangiji zaku jini tafe da k'arshen labarin WANI AL'AMARIN....* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 45.* *LAST PAGE.* ^^^^^^^^^^^ *#Outcomes2* *#Resignation* *#Royalty* *#Captivity* *#Truth has been reveals* *#End* *CENTRAL PRISON* A can central prison kuwa dake nan a unguwar dogarai ta cikin k'waryar Kano,ma'ana prison na cikin gari kenan dake nan kusa da royal palace,su Adda suna nan idanunsu sun gama raina fata,,dan kuwa tun a bayan lokacin da su A.S.P Hood suka fito da su ita,Hajiya Suwaiba da Ladidi abun sai ya zama ba'a cewa komai,saboda da fari iya Hajiya Suwaiba da Adda ne kawai a cikin case d'in sai kuma su JIBO,,sai dai kuma daga bayan fitowar jawabai da suka bayyana daga bakunan su Inno da ita kanta Hajiya Suwaiba d'in wad'anda sune suka sake fallasa asirinsu Adda da duk wani ayyukan rashin gaskiya da suka dunga aiwatarwa a b'oye wanda duka suka shafi cikin gidan sai hakan yasa Yarima ya bawa su Hood d'in daman had'awa har da itama Ladidi'n,,nan take kuwa ba tare da sunyi jinkiri ba suka kwamusota sannan suka izza k'eyarsu duka su da magoya bayan su d'in zuwa Jail,,tun daga k'ofar shiga gidan hankalin Hajiya Suwaiba ya tashi dan kuwa tunda take biyewa zugar Adda itama ta fara aikata tsiyarta sam tunanin ta bai tab'a kawo mata cewa akwai ranar da zata zo mata a haka ba,kwakwalwarta da duk lissafinta a wancan lokacin da take aikata abunda taso gani take a kullum zata kasance mai nasara akan duk abunda tasa agaba,sai dai sam ta manta da cewar duk wanda yake zaluntar wani Ubangiji yakan bashi dama ne a cikin lokaci kad'an,nd haka nan ta manta cewa rana dubu ta b'arawo d'aya kuma ta mai kaya,dan haka sai duk bata tanadi zuwan wannan ranar ba,shi yasa a yanzun da taga sun iso duk sai jikinta ya mutu ta shiga kogin nadama,,har ciki motan dake d'auke da su ta shigar dasu,bayan A.S.P Hood sunyi magana da S.P na prison d'in suka kuma dank'a su Adda a hannunsa sannan suka masa sallama suka wuce,,inda su kuma su Adda bada b'ata lokaci ba yasa aka zo aka wuce da su b'angaren mata,su JIBO kuma aka nufi hanyar b'angaren maza da su,,tun daga shigar su Adda d'akin da aka ajiye su,hankalin Hajiya Suwaiba sai ya sake tashi fiye da lokacin da suka shigo gidan,sai ya zamana duk motsin da zata yi ko ta kalli wani abu sab'anin wanda ta sani ko ta saba gani a gidan ta sai ta furta kalmar tsinuwa mai tattare da manyan masifu da alkaba'ai iri daban² akan su Adda dan kuwa duk ita ce tasa ta fuskantar wannan k'ask'ancin,,nadama,dana sani,Allah wadai da mugayen d'abi'ar da ta koya daga gurin Adda kuwa duk sunfi damun zuciyarta,,kafin cikakken awa guda da zuwansu gurin tuni har idanunta sunyi jajir suna tsiyayar da hawayen nadama,,su kansu gogaggun tantiran duk taurin zuciyansu da son d'aukan FANSA dake cikin zuciyoyinsu a yanzun duk sun fara laushi,dan duk abunda suke kullawa tuni ya fara canja akalar zuciyoyinsu,dan haka bayan ganin d'akin da zasu zauna iya tsayin lokacin da basu sani ba zasu kai ko ba zasu kai ba duk sai yasa suka ji zuciyoyinsu suna rawa,,A cikin wannan yanayin ne kuma sai ga captain Adama akansu dan basu ga ta zama ba tunda har da horo mai tsanani akansu kamar yadda A.S.P Hood ya labartawa S.P na gidan,,duk dama kawai an shaida musu su ajiye sune zuwa lokacin da za'a buk'aci sake yanke musu hukuncin,nan fa ta tusa su a gaba suka kama hanya,inda ba ita ta tsaya da su ba sai a kitchen d'in gidan...Tun daga wannan ranar ne rayuwarsu ta fara headed zuwa ga bautuwa a cikin gidan,sannan ta kowane fuska babu sassaucin da suke gani,a kullum yini suke aiki,nd basa tab'a samun lokacin hutawa sai dare ya rab'a,sannan da safe ana yin kiran farko haka za'a taso su,su yini aiki basu zasu sake samun daman hutawa ba sai wani daren,dama² ma lokacin sallah idan yayi akan d'aga musu k'afa suyi wanda shima d'in suna idarwa ne zasu sake komawa bakin aiki,,ada kam Adda da Ladidi sam ibada bai dame suba amma a yanzun koda suka fad'a k'adamin masifa tuni suka rungumi bautar Ubangiji har ya zama wannan lokacin da zaran anyi kira zasu shiga tsere da rigegeniya wajen yin alwala,hakama sallar dare duk ba'a barsu a baya ba,a haka ne kuma rayuwarsu ta ci gaba da tafiya cikin tsananin bauta... _To sai muce Allah ya kyauta,mu kuma Ubangiji ya k'ara tsare mana imaninmu,sannan ya tsare mu sharrin mak'iya na zahiri da bad'ini,ubangiji kuma yayi mana tsari da hassada da masu yinta..ameen_ *INA LABARIN SAJIDA..??* A can gefe guda kuwa cikin rayuwar SAJIDA a dai² wannan lokacin da al'amura suka had'e mata tana fama da kanta dan yadda duk wasu al'amuranta suka tsaya,sai kuma ga labarin kama mahaifiyarta ya bayyanar mata,labarin daya zame mata mafi muni a tarihin rayuwarta,,tayi kuka ta kuma yi Allah wadai da sabbin halayen da mahaifiyar tata ta dunga bayyana wa a d'an lokacin da suka gabata,sai dai duk da taji labarin abunda ya faru da ahalin maharauta hakan bai hanata ganin laifin Hajiyar tata ba,amma kuma duk da haka son kai baisa taji haushin hukuncin da akayi ma Hajiyar ba,sai dai taji tausayin irin halin k'uncin da ita kanta zata shiga idan akace Hajiyar tata bata tare da ita,dan sanin kanta ne duk wannan badak'alar akanta ne Hajiyar ta jefa kanta a masifa,dan tuni ta fahimci al'amuran da suke gudana daga gurin mahaifiyar tata,sai dai bata iya ta yi mata magana ba dan ta san abunda zai biyo baya,sai gashi yanzun kuma shirun ta ya haifar mata da babbar damuwa a cikin rayuwa,,tayi kuka sosai da idanunta,sannan bayan nan kuma taji son taje masarauta ta bawa Yarima da sauran ahalin gidan hak'uri on behalf of her mother da abunda tayi musu,,haka kwanaki suka shiga zuwa suna wucewa wanda a kullum cikin kwanakin tunda aka kama su Hajiya Suwaiba d'in bata rabuwa da zubar da hawaye dan tsananin tausayin da take ma halin da zata tsinci kanta nd haka kullum kuma bata fasa yi mata addu'ah akan Allah yasa hakan ya zame mata izinah ko dan gaba. A b'angaren Abba'nta ma tun da aka kama su Hajiyar aka tafi da su yake ta Allah wadai da munanan halayen data kwaso d'in wanda tun a can baya ya rasa inda ta kwaso su,amma a wannan lokacin da aka yi komai akan idonsa sai ya gama fahimtar inda ta samo sun,,tunda kuwa aka wuce da su nan yayiwa kansa ALK'AWARIN duk iya zaman da zata yi bazai tab'a barin SAJIDA taje gurinka ba da sunan ziyara,saboda yana son hakan ya zame mata izinah da gyaran hali. Tun daga lokacin kuwa a kullum sai ya kasance cikin sawa SAJIDA idanu,duk da ya fahimci damuwarta a kwanakin kuma yana tausayawa rayuwarta amma sai ya nuna kamar baisan abunda yake damunta ba,dalilin kuwa ya riga yayi alwashin itanma bazai bari taje gurin Hajiyar ba,adalilinsa na son horar da ita,,tun daga lokacinma sai ya sake gindayawa SAJIDA d'in sharad'in baya so ko da wasa ta taka k'afarta a cikin prison d'in da sunan taje wajen mahaifiyarta ziyara,idan kuwa tayi KUSKUREN zuwa nd ya samu labarin taje d'in to ta k'addara daga ranar zata bar masa gidansa dan zai yanke alak'a da ita ta har abada,,wannan furucin na Abba Matawalle shi ne ya matuk'ar sake d'aga hankalin SAJIDAR wanda shi ne musabbabin daya janyo mata kwanciya rashin lafiya saboda damuwa daya had'u ya mata yawa.. _Wannan kenan._ *HOSPITAL…* A can asibiti kuwa b'angaren ZAHRA MALEEK,ak'alla zuwa yanzu ta d'iba tsayin kwanaki goma sha hud'u da yi mata plastic surgery,wanda kuma a yau d'in nema aketa saka ran za'a bud'e fuskar nata da yardar Allah,,dan haka duka asibitin nasu sai ya zama a cike yake da guards zuwa y'an uwansu,kowa burinsa yaga yadda aikin ya kasance,,ita kanta ZAHRAN duk da tana cikin fargaba ne tun daga lokacin da AL'AMARIN ya faru amma a yau tana jin duk wani damuwan da take tattare da shi tun daga lokacin da AL'AMARIN ya faru yana tafiya a hankali,banda addu'ah a time d'in babu abunda take yi,hakama mom d'inta dake tare da ita da kuma daddyn ta daya zuwansa kenan k'asar,,nan kuma aka shiga jiran k'arasowan mai gayya mai aiki wato *DR. YAZEED MUHAMMAD ABDULLAH*,wanda kowa yafi sani da *PRINCE YAZEED BIN ABU YAZEED*,the first surgeon of his phase wanda k'asa gaba d'aya take alfahari da samun kamarsa musamman a Kano State,duk dama aikin nasa bawai ya tsaya kad'ai a tsakanin Kano to Abuja bane,dan kuwa a wannan lokacin hatta da sauran States sukan zo aronsa a lokuta mabambanta duk a sanadiyyar k'wazonsa da kuma jajircewasa a aiki,haka shima YASEER a wannan lokacin ba'a barshi a baya ba dan kuwa da zaran an ambaci Yarima indai a b'angaren surgery ne to shi ne zai zama na biyu a fannin,duk da a yanzun bawai suna aiki k'ark'ashin reshen asibiti guda bane,adalili tun bayan lokacin da suka ajiye aiki tare a garin abuja sai maimartaba ya hana su aiki tare sai dai idan d'aya yana gabas to d'ayan zai zama yana yamma gudun kada wani abu ya sake sawa su kamanta shirmen da suka yi a wancan lokacin,,,duka gurin yayi shiru kowa idan aka tona zuciyarsa farin ciki ne mai had'e da wani irin fargaba dan kuwa babu wanda yasan yadda AL'AMARIN zai kasance,duk dama sun jima suna samun k'warin guiwa daga gurin mutane da dama da suka san aikin YARIMA a wannan fannin,buh duk da hakan suna jin fargaba. Kasancewar zuwa lokacin da al'ummah (ahalin ZAHRA MALEEK) da dama daga cikinsu sun hallaran akwai sauran time kafin a bud'e fuskar nata,,amma kuma wani abun mammaki sai ya zama har zuwa lokacin shi kuma Yarima ko alamun zai zo babu,haka nan babu wanda yasan dalilin k'in zuwan bare a yanke hukunci,,dan haka sai duk ilahirin ma'aikatan asibitin suka shiga mamakin dalilin rashin k'arasowarsan da wuri,adalilin sanin duk da suka masa a matsayin mutumin da yake da k'a'idarsa akan komai na rayuwa,da kasancewarsa mutum mai son mutunta lokaci,shine ma dalilin da yasa matuk'ar akayi appointment da shi idan har an yanke lokacin had'uwa to shi d'in zai riga kowa zuwa,sai dai kai d'in ka iske shi yana jiranka,,amma a yau kuma sai suka ga sab'anin haka d'in,,wanda duk sai ya jefa zuciyoyinsu cikin rud'ani da fargabar dalilin rashin zuwan nasa. Shi kuwa Yarima a dai² wannan lokacin da duk ake fargabar rashin zuwansa hospital,yana can a gida abunsa suna ta rikici da madam akan yace su tafi tare,ita kuma tace sam bata ga dalilin da zaisa taje ganin abunda zai hana mata nutsuwa ba,,wannan dalilin yasa shima Yariman sai ya nemi guri ya zauna abunsa nd yace tunda baza taje ba shima baiga amfanin yaje ba d'in,tunda dai dama bud'e aiki ne ba yin aikin ba,a samu wani ya bud'e,,lokacin daya fad'i haka dariya kawai tayi dan tana d'aukan maganar tasa a wasa ne dan haka sai ta zuba masa ido tagani ko zai mata sallama ya tafi idan tak'i bashi goyon bayan su tafi tare d'in,,sai dai kuma ga mamakinta tun tana d'aukan abun wasa,sai taga har kusan mintuna talatin yana kwance bai motsa ba,sake zuba masa ido tayi tana kuma kallon agogo,still sai taga wasu mintunan sun sake zuwa sun wuce suma kuma a banza,,saurin tashi tayi ta nufi inda yake kwance saman Royal bed d'insa ta zauna tana d'an cije lips d'inta,coz bata sanma ta ina ya kamata ta fara ba,ta gefe ya kalleta sai bai kuma ba ya d'auke idonsa yana kuma had'e rai,saurin rik'o hannunsa tayi ta k'ank'ame a nata,kamar wacce zata yi kuka ta kalleshi tana marairaice masa fuska,sake had'e rai yayi yana k'ok'arin zare hannunsa a nata,sake rik'owa tayi itama had'e da shagwab'e fuska,saurin kallonta yayi yana cewa "Mene ne aka yi miki...??" Ya watso mata tambayan dan yasan yanzun zata iya sa masa kuka,,kai ta girgiza masa sannan tace "To ba kai ne ba..dan kawai na ce bazan jeba kace kaima bazaka jeba..Kuma bayan duk kasan abunda nake gudun gani..!" Tab'e baki yayi sannan ya ce "Sake min hannu to.." "Ni bazan iya ba.." Kallonta yayi yana d'age gira sama "Baza ki iya meba..??" "To ai cewa kayi na sake maka hannu.." "Ohh! Shi ne d'in baza kiyi ba..??" Tayi saurin girgiza masa kai "Sake ni nace,,tunda bakya jin magana ai shi kenan sai kiyi duk abunda kika so ko..??" "Allah kuwan ni dai ba haka nake ba..kuma ai naga kaima ka sani.." "Babu abunda na sani..Tunda yanzun kin gwada min bakya jin,taya zance wani abu akai sab'anin wanda idanuna suka ganemin..!?" Kuka take shirin yi amma ya kafeta da ido,cikin zuciyansa kuwa fad'i yake "Gaskiya KHUSHI ba dai arhan hawaye ba,,duba daga wannan d'an maganar har ta fara k'ok'arin tarasu a idanunta.." Amma a fili da yake shi ne saima ya sake d'aure fuska kamar ba shiba "KHUSHI.. Let me be mana..kin ce baza kiba nd mene ne dalilin da yasa kuma zaki zo kusa dani..?? Ki tashi kije abunki,aikin ne nima nace ban zuwa su samu wani ya duba ta.." "A'a YAYANAH.. To ai naga kai ne ya kamata ace ka dubatan baawai wani ba,tunda kai kayi aikin.." "Sai mene to..?? Idan bana nan ai baza'a rasa wanda zai kula da aikin ba.." Ko gama rufe bakinsa bai yiba da maganar d'aya daga cikin wayoyinsa tayi k'ara,,sai data kalleshi sannan ta mik'e da sauri ta d'auko masa,a lokacin daya karb'a kuwa yana dubawa yaga daga can hospital d'in ne aka kira shi,dan haka ya juya baya yana b'ata rai,kafin ya d'auka,sam a tunanin ta idan ya d'auka d'in zata ji yace gashi nan tafe amma sai taji yana cewa bazai zoba saboda wani uzurin kai da kai daya same shi,,zuciyarta ce ta fara shaida mata ya kamata tayi wani abu,coz matuk'ar ace ta zuba masa ido tofa hakan daya fad'a yana mai iya aikatawa,magana yake niyyan sake yi da sauri ta mik'e itama ta nufe shi,da zuwanta ta bayansan sai ta fad'a jikinsa had'e da bashi kyakykyawan hug da yasa shi katse kiran wayan babu shiri,sannan ta shiga bashi hak'uri,da kyar ta samu ya hakur'an shima bayan ta tabbatar masa ne akan zata je d'in,duk da yana farin ciki da hakan amma sai ya k'i nuna mata coz shi kad'ai yasan dalilinsa na son zuwa da itan a wannan lokacin,ba don komai bane kuwa yake son yin hakan face akan ZAHRA MALEEK ta sani dan ta k'i shi to ta gani da idanunta Ubangiji ya canja masa da wacce ta fita zamowa alkhairi a rayuwarsa,wannan abun shine ya k'udurcewa ransa shi yasa duk yake ta mata pretend,,tare suka sake shiryawa sannan suka kama hanyan hospital d'in kamar ko wane lokacin da zasu fita yana d'auke da AHYAN,har suka shiga cikin haraban hospital d'in,a lokacin kam da isowar su,wanda tuni duk aka samu labarin bazai zoba amma kuma sai suka ganshi in time ya k'araso,,kai tsaye ward d'in da take suka nufa coz yana jin bazai iya cikakken zama a hospital d'in ba shi yasa ya nufi abunda ya kawo shi kai tsayen. Tun daga shigowarsu banda gaishe shi babu abunda ake cikon girmamawa a duk inda ya ratsa har ya isa room d'in,su kansu iyayen ZAHRAN lokacin da suka ji ance musu ai gashi nan ya iso yanzun tunma kafin ya shigo sai suka ji dad'i sab'anin lokacin da labarin rashin zuwansa ya riske su,yana zuwa kuwa ya tarar da har nurse tuni ta shiga da kayan aiki tana jiransa hannunta d'auke da tasa wanda scissors ne kad'ai a kai sai mirror dake,,da sallama suka shigo bayan sun gaisa da iyayen ZAHRAN sannan yayi nufin abunda ya kawo shi,scissors d'in ya d'auka yana ambaton sunan Ubangiji da neman nasara a gare shi,sannan ya yanka bandage d'in da aka nad'e ta da shi,a hankali yake warware shi yana mai sake yin kirari ga Ubangiji har ya gama tsaf,inda nan take kuma fuskarta ta bayyanar musu tamkar wani abu bai tab'a samun taba,kabbara duka d'akin ya d'auka dan yadda suka ga nasara a cikin aikin nasa,wanda ita kuma ZAHRA abunda ya janyo hankalinta kenan ta shiga k'ok'arin bud'e idanunta dake rufe hawaye suna sauka a fuskarta,da fari duka d'akin ya mata haske ya zamana babu abunda take iya gani,amma ko data ci gaba da kallon gurin tana motsasu nan take sai hasken ya fara rikid'ewa yana fitar mata da shadow d'in mutane daban² dake cikin gurin a hankali kuma sai ta fara ganin mutane dishi² daga haka har suka gama dawo mata asalin yadda suke,inda iyayenta suke zaune ta fara kallo tana sake fashewa da kuka dan ita kam bata san kabbaran da suke yiba,su kansu dan tsabar murnan ganin ta dawo normal ma bai basu daman rarrashin taba sai rungume ta da suka yi,tana cikin kukan ne kuma take sai muryan Yarima tayi mata kutse zuwa cikin kunnuwanta inda yake shaidawa iyayenta wasu cikin ka'idojin aikin,da sauri ta d'aga idanunta ta kalle shi duka a tunanin ta ba shi bane,amma sai ta ganshi tsaye a gabanta,fuskar nan tasa a had'e kamar ba shi ne wannan Yariman data sani ba a da can,sunkuyar da kanta tayi k'asa tana jin zuciyarta tana tsananta harbawa,coz a lokacin tuni ta jima da samun labarin rayuwarsa da duk al'amuran da suka faru da shi,shi yasa a yanzun take tsananin jin kunyar sa musamman ma yanzun data ganshi tsaye a gabanta,shi kuwa Yarima a gurin ko daya gama fad'a musu abunda zai fad'a d'in kawai saiya rik'o waist d'in Jeeddah bayan ya amshi AHYAN dake hannun d'aya nurse d'in dake biye dasu tun zuwansu,cikin muryansa mai dad'in sauraro da kashe jiki ya furta "KHUSHI... Let's go home,,tunda mun gama abunda ya kawo mu ko..??" Ya k'arasa zancen da tambayarta,ita kam kunya yaso bata dan yadda iyayen ZAHRA suke kallonsu sai dai ta kasa kwacewa a haka taci gaba da binsa,bayan sunyi musu fatan alkhairi sannan suka wuce,,bayan fitar su kuwa ZAHRA ta sake fashewa da kuka wanda ita kad'ai ta barwa kanta sanin dalilin yin hakan,futarsa babu jiwa kuma sai yasa akayi dismissed nasu daga hospital d'in duka,daga nan dukansu sai suka d'auki shirin barin garin cike da tsananin murna kan irin nasarar da suka samu... *A month leave...* Rayuwa ta ci gaba da tafiya yayin da a ko wane gefe,cikin rayuwar kowane ahalin suke ganin ci gaba,musamman ma ZAHRA MALEEK wacce tun bayan da suka koma gida,sai magannar neman aurenta da AARIZ ya tashi gadan²,duk da ZAHRAN ba wai ta amincewa ranta tana sonsa bane amma ta tabbarwa kanta matuk'ar ta sake kwatanta KUSKUREN data yi a baya tofa zata ga ba dai² ba,dalilin dama tun suna school shi d'in ya nuna yana sonta itane dai da bata bashi goyon baya ba,,sannan a yanzun kuwa tuni ta tabbatarwa kanta Yarima kam ya shallake duk wani tunaninta,tunda har taga matarsa da d'ansa,wanda shi da kansa ya nuna mata matarsa da d'an da Allah ya azurta su da shi d'in shi yasa sai duk taji ta zama wata iri a yanzun,,wannan dalilin yasa sai ta sawa ranta hak'uri da shi d'in ta kuma rungumi k'addararta,suka ci gaba da shirye²n biki... A ta b'angaren su Yarima suma kansu sun samu ci gaba sosai cikin wannan lokacin,musamman ma ita Jeeddah data kasance tamkar tauraruwa a tsakanin family'n ta,wanda a kullum idan taga yadda ake nuna mata kulawa da soyayya abun har mamaki yake bata,a duk lokacin da tayi arba da wani abu kuwa daya sosa ranta nan zaka tarar kowa burinsa yaji damuwarta,idan har hankula sun kwanta a gidan to k'addara ta saki ranta ne,,cikin wannan rayuwar ne lokaci yaci gaba da tafiya ba tare da mun fargaba.. *AFTER 10 YEAR...* Izuwa yanzun cikin wad'annan shekarun da suka gabata,al'amura da dama sun faru wasuma suna kan faruwa,,inda ya kasance a dai² wannan lokacin tuni a b'angaren SAJIDA da Aisha suka nemi yafiyar laifukansu a gurin Yarima dama masarauta gaba d'aya,kuma Alhamdullah! Komai ya riga ya wuce,an yafewa juna an kuma maida komai ya zama ba komai ba,sai dai har zuwa wannan lokacin su kuma a b'angaren su Adda tun bayan da aka tafi da su gidan kaso ba'a kuma waiwayar halin da suke ciki ba a masarautar,haka nan labarin duk abunda suka yi tuni ya gama zagaya gari kowa yasan abunda suka aikata,duk inda ake tunanin labarin bai jeba tuni har ya wuce nan,,Haka nan zuwa wannan lokacin su kansu SAJIDAR da Aisha cikin hukuncin Ubangiji tun da jimawa suka yi aure suna zaune duka a cikin garin Kano a mabambanta

Chapter 62 of 63