zata amsa,amma sai yaji tayi shiru bata iya amsawa ba,killer smirk ya sake mata a hankali ya d'agota zuwa jikinsa yana sake caressing jikinta slowly,hannunsa tayi saurin rik'owa ba tare data bud'e idon ba ta furta
"Stop Yah Prince.."
Murmusawa ya sake yi cikin kunnenta ya rad'a mata
"Why will i stop..?"
Bata iya magana ba dan har lokacin numfashinsu bai gama saituwa ba,gefen neck d'inta ya sakar mata sounding kiss yana kuma shinshinar jikinta,nok'ewa ta fara yi a jikinsa shima kuma bai bari ba sai da yayi son ransa sannan ya janyo liquid soap yasa a hannunsa ya soma shirin wanke su duka..
*A GURGUJE...*
Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya a kullum basu da wani aikin daya wuce na bawa junansu kulawar data dace,idan har Yarima baya gidan to sai dai ko appointment ne da shi na duba wasu patient ya taso a b'angaren surgery aka kira shi,wani lokacinma tare da ita zaisa ta sha k'aton hijab d'inta har k'asa da nik'ab su fice,a hankali rayuwa ta ci gaba da juyawa wanda ya kasance yau dad'i gobe kuma kishiyarsa,cikin haka ne ABEELA ta haihu inda suka samu d'a namiji,tashin farko YASEER yace shi kuma baiga sunan daya dace da wannan yaron ba sama da sunan ABU YAZEED,nan yaro yaci suna Muhammad suna kiransa da BAQIR (ma'ana mafi soyuwa,ko makusanci da zuciya) sosai yaro yazo duniya da goshi kan kace me haihuwa tuni ta karad'e family'n,nan kowa ya fara k'ok'arin nuna kalar tasa bajintar,yayin da a gefe guda kuma itama Jeeddah laulayi ya sakota gaba sai dai ba wani mai zafi bane dan bayan ita da Yarima babu wanda ya sani shima dan dai yadda yake jin jikinta da dare da zafi ne yasa shi fahimta,haka ko da suka je asibiti aka tabbatar masa tana d'auke da juna biyu sunyi farin ciki sosai,shawarwarin da aka basu kuwa basu yi saka ci dasu ba nan suka kinkimo suka yo gida cike da tsantsar k'aunar cikin jikintan daya boy'e kamar babu komai a jikinta.
Sabon shafin kulawa Yarima ya bud'e musu daga ita har cikin ta,ko kad'an baya son yaga wani abu da zai tab'a masa su,dan yadda yake kaffa² da su,a haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cike da tsantsar so kamar babu wani abu da zai tab'a su a rayuwar.
B'angaren Aisha da Adda ma zuwa yanzun tuni suke samun lafiya sai dai abunda baza'a rasa ba,kasancewar ita Aisha karaya ne ta samu,while ita kuma Adda socket d'in guiwarta ne ya zare,kuma alhamdulillah zuwa yanzun anyi nasara komai lafiya,sai dai Adda ta sha raki,wanda tuni aka mai dasu gida,masu zuwa dubiya kuwa babu wanda basu gani ba tun suna asibiti har kawo dawowarsu gida,illa Yarima daya murd'e yace Allah ya kasheshi babu inda zashi,a haka rayuwar taci gaba da gangarawa dasu inda sauk'i yake dad'a samuwa a hankali.
*SIX MONTH LATER.*
Zaune take a katafaren parlor'n su duk ta mimmik'e k'afafu,banda ajiyar numfashi babu abunda take yi kamar tayi tsere,bowl ne a hannunta da fork acikin bowl d'in yankakken watermelon ne da yaji madara sai azawa cikin ta take,tayi nisa a sha kome ta tuna tayi saurin ajiye bowl d'in ta dafa chair wing tana k'ok'arin tashi,kasancewar Yarima ya fita wani kiran gaggawa da aka masa yasa take zaune ita d'aya,a daddafe ta mik'e tana takawa a hankali har ta nufi kitchen,shigarta babu jimawa YASEER ya shigo parlor'n da sallama sai dai bai ganta a nan ba kasancewar ba tare suka fita da Yarima ba shi yasa,zama yayi a d'aya daga cikin cushion d'in yana fad'in
"Yau kuma ina kuka shige..??"
Duka ya manta da sunyi magana da Yarima time d'in da zai fita,maganarsa tasa ta lek'owa daga kitchen d'in tana d'an murmushi ta amsa masa sannan ta fito a kitchen tana nufo tsakiyan parlor'n,cikin rashin sani garin sauri bata kula ba ashe gefen plane zaninta ya sauka k'asa ita kuma ta d'ora k'afarta kai,take kuwa yajata tayi gaba zata fad'i,salati ta saki tana runtse idanunta had'e da dafe cikinta da duka hannayenta.
Haka nan tun bayan fitar Yarima yake yawan jin fad'uwar gaba na damunsa,dan haka cikin gaggawa yayi komai ya gama dama signing d'insa kawai ake buk'ata akan aikin da Yarima wata yarinya,ranar ya zo akan shi ne ranar da za'a bud'e fuskar nata da aka watsama Acid,jin yadda gabansa ke yawan fad'uwa akai² yasa shi hanzarin yin signing d'in ba tare daya tsaya an bud'e fuskar a gabansa ba yayi handing over da wani Dr akan ya sanar da shi duk halin da ake ciki,a mota yana tafe yana karanta duk addu'ar data zo masa k'arar wayarsa keta yi tun tuni yak'i kulawa yasa shi gangarawa gefe yana d'auka had'e da sawa a speaker dan baya cikin yanayin da zai iya fahimtar abunda za'a fad'a masa,k'asaitacciyar dariya aka saki daga can gefen da aka kira shin ba tare da anyi magana ba,haushi abun ya so ya bashi dan ganin tsabar rainin hankalin da aka masa,haka ya daure ya fara k'ok'arin magana dan shi sai yanzun nema ya kula da number da aka kira shi d'in batayi appear ba,still ana kan yi masa dariya dan haka ya fusata kawai ya katse kiran,tun kafin ya ajiye wayan wani kiran ya sake shigowa,slender crack ya saki yana reject don baya son ya kasa hankalinsa da yawa shi yasa,haka akaita kiransa yana reject sai da suka yi haka ya kusan sau goma bai k'ara d'aukan wani ba,kamar an hak'ura da kiran nasa a lokacin ya ci gaba da driving d'insa yana mai addu'ar ya isa gida yaga a wane halin take,k'arar shigowar sak'o ne yasa shi d'an kallon wayan kamar bazai kula ba kuma yaji zuciyarsa na umartarsa daya d'auka ya duba,a hankali ya soma bibiyar words d'in,tsaki ya saki mai rai da lafiya yana cilla wayar gefe sannan yaci gaba da shek'a gudu abunsa akan titin kamar was shi d'aya aka shimfid'a kwaltar da haka har ya iso cikin gidan,yana yin parking ya fito bai ko tsaya tattara abunda ya kamata ya d'auka ba yayi hanyar apartment d'insu zuciyarsa na ci gaba da tsinkewar daya fi na farko,daurewa yaci gaba da yi har ya k'araso apartment d'in,dai² yana k'ok'arin d'ora hannunsa saman handle d'in door ihunta ya ratsa kunnensa,ai bai san lokacin daya hankad'a k'ofar ba tayi ciki,ba tare daya jira ta k'arasa bud'ewa ba ya rufa mata baya,sai dai me idanunsa zasu gane masa..?? His KHUSHI ya hango kwance a saman hannun YASEER ya tarota,wani irin kishi ne ya turnuk'o shi lokacin da idanunsa suka sauka kansu,duk bama wannan ba murmushin daya ganin kwance a fuskarta tana kallon YASEER da shi shine ya haddasa masa jin wani irin abu na masa yawo a jikinsa,sai data dai²ta a tsaye sannan YASEER ya cika ta yana binta da wani malalacin kallo had'e da mata sannu,kai ta iya kad'a masa tana masa godiyan taimakonta da yayi,sam basu ankara da shigowarsa ba sai yanzun da k'ofa ta koma mazauninta tayi banging kanta suka kallo sashen gurin,nanfa suma idanunsu ya hango musu shi ya k'ame a gurin tamkar an dasa shi.A hankali YASEER ya nufe shi yana fad'in
"Welcome home broah..!"
Kallonsa kad'ai ya iya yi ta k'asan ido sannan ya juya yana nufan hanyar bedroom d'insa, kallon juna YASEER da Jeeddah suka yi ganin bai amsa ba kafin ta soma d'aga k'afafunta tabi bayansa,a bedroom ta iskoshi sai moving yake daga nan zuwa can,nufansa tayi da zuwanta ta fara k'ok'arin lafewa a jikinsa,ja yayi ya matsa gefe yana jifanta da wani malalacin kallon da har y'an hanjinta sai da suka juya,sai dai duk da hakan bata fasa abunda tayi niyya ba
"Yallab'ai barka da dawowa..!"
Ta fad'a tana sake k'ok'arin rik'e shi,cikin wani tsawan da bai tab'a mata magana ba ya nunata da finger yana karkad'a shi alamun warning nata
"Kad'a ki kuskura ki kusanto ni..!"
Abunda ya fito a bakinsa kenan,turus ta tsaya tana binsa da wani kallon firgicin jin maganarsa
"Yallab'ai.. Me kake son cewa ne..?? Dan Allah idan wasa kake min ka bari k'asan bana jurar irin wannan wasan naka.."
Tayi maganar muryanta na karkarwa,harara ya jefeta da shi kafin yasa hannunsa duka a waist yana mata wani irin kallo
"Zaki fice min a nan ko sai na b'ata miki rai..??"
Ita dai tana tsaye ta kasa magana saboda tsabar mamakinsa,"shin me yake nufi ne..??" Ta tambayi kanta sai dai ta rasa amsa
"Amma Yallab'ai..!"
"Hey! hey!! hey..!!! Stop pretend on me..kina son nunamin cewa ban gan abunda kuke bane..?? Idan baki sani ba wannan ba shi ne karon farko ba,kawai dai ina d'auke kai ne..amma abunda kuka manta da shi shine dole akwai ranar da zan sani..da kuka san kuna son juna meya hana ku mallakar juna before that time..??"
Duka kwakwalwarta ta juya,sai zuwa yanzun ne da kalamansa suka sauka ta fara dawowa daga rud'aninsa,buh amma akan mene yake wannan maganar..?? Shin taimako dama ya tab'a zama cuta..??
"Yallab'ai.. Me kake nufi ne..??"
Sai daya jefeta da mugun kallo sannan ya furta
"Abunda kuke nufi da ni shi nake nufi da ku..kinga ki ficemin an nan kafin na illata ki.."
Ya sake mata magana a tsawace,jikinta duka rawa yake tana kallonsa da idanunta da suke cike taf da hawayen k'uncin maganarsa...............
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 25.*
^^^^^^^^
*#Applecart*
Kallonsa take duka ta koma wata speechless,hawayen dake kwance a idanunta tuni har sun soma sauka bisa chicks d'inta kamar an kwance tap,banda girgiza masa kai mai cike da wani irin yanayin tsantsar tashin hankali babu abunda take,a hankali ya runtse idanunsa ya juya mata baya dan yadda zuciyarsa ke masa wani irin zafi,ya gwammace ace ya ga mutuwarsa da yaga saukar hawayenta,amma to yaya zaiyi idan bai yi hakan ba,juyawansa ya tsurawa window idanu yana nazarin wajen,ya d'auki lokaci yana kallon wajen sannan cikin rashin kuzari ya fara d'aga k'afarsa yana nufar gurin kasancewar curtains d'in sun d'anyi gefe yasa shi janyesu ya maida su ya rufe ko ina,take duhu ya d'an gauraye wajen,cikin wani speed ya waiwayo gareta har lokacin tana a yadda ya barta banda hawaye babu abunda take,rik'ota yayi duka ya bata warm hug yana sakin wasu ajiyar zuciya masu k'arfi dan shi kansa yasan ba k'aramin namijin k'ok'ari yayi ba daya iya shirya wannan dramatizes d'in,saurin d'ago kanta tayi da mugun mammakinsa dan dukanta jin jikinta take a d'aure,hannunta takai k'asan cikinta dai² mararta tana dafewa dan yadda taji ya fara mata ciwo,idanunta a runtse tana furta
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..!"
Saurin d'agota yayi shima cikin kid'imewa yana tambaya
"KHUSHI..! What happen..??"
Girgiza masa kai tayi tana masa nuni da mararta,a hankali yasa hannunsa a gurin yana mata massaging,cikin kunnenta ya fara mata rad'a
"Am really sorry KHUSHI..I know it hurts,buh babu yadda zanyi ne na gano wani sirri face nayi hakan.."
Cak taji ciwon ya d'auke mata kamar anyi ruwa an d'auke,kallonsa take without blinking,sake janyota yayi ya zaunar da ita a bakin bed d'insa sannan ya fara rage kayan jikinsa,sai daya rage daga shi sai boxes da singlet da suka kasance farare tas,sannan ya dawo kusa da ita ya zauna yana sakin numfashi,har lokacin shi take kallo zuciyarta cike taf da mamakin maganarsa,ita dai tun daya furta maganar take ta faman sak'a da warwara akan maganar tasa sai dai ta gaza hasaso ainihin abunda maganarsa ke nufi,yana zama ta sake kallonsa tana shirin yin magana,yayi maza ya d'ora hannunsa akan lips d'inta yana binta da wani kallon dake kashe mata jiki
"I know zaki yi tunanin wani abu akan maganata,maybe i will explain it later,buh duk abunda yasa nayi muku haka ko da nace zanyi muku bayani yanzun babu tabbas ku fahimceni,beside ma bana son saku a had'ari ne shi yasa..Buh am really² sorry KHUSHI na tsorataki da yawa wanda due to ur situation bai kamata ace nayi hakan ba,sai dai babu yadda zanyi.."
Kanta ta kwantar a jikinsa kafad'arsa tana sakin slender breathe masu tafe da wasu hawayen data kasa fahimtar na samun nutsuwa ne ko kuwa na tashin hankalin data shiga ne before.?
"It's OK...ko baka fad'a ba maganarka na yanzun ya wadatar dani,,,buh naji tsorofa da farko sosai.."
Rungumeta yayi tsam ajikinsa muryansa a sanyaye yana fad'in
"Afuwaan *WALIYIYITA* nayi laifi.."
Yatsanta tasa akan lips d'insa itama tana kad'a masa kai
"Ni dai ka daina bani hak'uri..Duka ni dama ko da hankalina ya fara tashi na rashin sanin laifin da nayi maka nefa..for now am OK,let's by gone be by gone..OK..?"
Kai ya jinjina mata yana kamo k'afarta ya d'ora kan laps d'insa ya fara mata messaging,d'an rufe idanunta tayi har lokacin numfashin ta bai koma dai² ba dan iya firgita yau ya tsorata ta,fahimtar hakan da yayi ne yasa shi jinginar da ita a jikin pillow sannan yayi d'an gyaran murya,a hankali ta shiga bud'e lumsassun idanunta ta sauke su akansa while shima nasa idanun na a kanta sannan ya fara magana
"KHUSHI will u remembered wani lokaci can baya da kika tab'a shaida min idan kin fita kina jin kamar ana binki..??"
Shiru tayi kamar mai son nemo amsan abunda ya tambaya akan face nasa,bai jira tayi magana ba yaci gaba da matsa mata k'afar kana yana ci gaba da magana
"A time d'in da kika fad'a min na yarda dake hundred % coz nima ina yawan jin hakan..buh amma abunda ban tantance ba shi ne time d'in da kika fara jin hakan,sai dai ina son ki fad'a min yanzun shin bayan zuwanki gidan nan hakan ya fara faruwa ko before..??"
"Tun kafin zuwana nan nefa..!"
Tayi maganar da wani irin shagwab'a,kai ya jinjina mata sannan ya sake watso mata wani question d'in
"Message fa..??"
Sai data kalleshi ta d'anyi squeeze face
"Message..?? Wane irin message..??"
Mustache d'insa ya shafa yana sakin miskilin murmushi
"Yeah..! I mean text messages..!?? When kika fara samunsu..??"
Kamar ta fahimci abunda yake nufi tayi shiru har saida ya d'ago ya kalleta yana d'age mata one eyebrow
"Don't feel bad akan tambaya na..coz nima ina samunsu lokaci zuwa lokaci.."
Ya fad'a mata haka da niyyan ya kautar da tuaninta akan maganar,ajiyar zuciya ta saki sannan ta furta
"I think it happens tun time d'in da muka yi plan da babban Yaya..!"
"Kina so kice tun ina jail..??"
Ya tambaya yana kallonta,shiru tayi tana sunkuyar da kai k'asa,d'an murmushi yayi kawai yana cewa
"Pleasee mana tell me.."
"Ehh Haka ne.."
Ta fad'a cikin sauri,jinjina kai yayi ba tare daya sake cewa komai ba,kallonsa tayi itama sanda taji yayi shiru kafin ta ce
"Amma me yasa kamin wannan tambayar yau..?? Mene ne ma'anar wannan tambayar a dai² wannan lokacin,mene ne kuma alak'ar ta da abunda ya faru..??"
Sai daya d'ago ya sake kallonta yaga yadda tasa fuskar serious ma'ana dai tana son sani da gaske,d'an murmushi yayi mata kafin ya furta
"Idan lokaci yayi zaki sani..!"
"OK..buh ko da ba yanzun ba,kamin alfarma na sake tambayar wani abun.."
"Yi tambayar ki ina sauraronki.."
Ajiyar zuciya ta saki sannan ta d'an kalli windows daya rufe bayan shigowarsa tana cewa
"Mene ne yasa ka canja mana fuska bayan shigowarka..??"
Bata k'arasa ba ya tari numfashin ta
"It's secrecy..buh zan sanar dake kad'an saboda bana so kiyi tunanin wani abu daban,amma dai ban son fad'a yanzun ba,nayi niyyan bari har zuwa lokacin da zan gama bincikena..."
Kai ta girgiza masa alamun ta yarda da hakan,maganar sak'on da aka turo mata na k'arshe ya d'auko mata wanda har yayi sannadiyyar jefata a tashin hankali a ranar,a lokacin suna tare a parlor,girgiza masa kai tayi alamun ta tuna,ci gaba yayi da cewa
"Tun a that time naji ban aminta da irin wannan sak'onnin ba,sai dai ban san ta inda ya kamata na fara binciko masu sak'on ba,buh matakin farko da zuciyata ta bani umarnin bi shi ne na fara rabaki da wannan phone d'in har ma da line d'in,wannan shi ne mafarin komai,so bayan nan sai kuma abun da yake faruwa dake ya fara k'ok'arin dawowa kaina,duk da nasan wasu abubuwan a dalilin binceken wayanki da nayi sai na fara acting akan babu abunda na sani,wani lokacin ina zaune zanga sak'o,sai dai na karanta na wuce dan nasan duka so ake a jefani cikin zarginki,idan baki manta ba wasu lokutan wayana bai cika ring ba ko..?? Duk nayi haka ne ba don komai ba sai don bana son yasan shigowar sak'onnin yasa kiyi zargin wani abu..wannan shi ne kad'an a cikin abunda zan iya sanar dake yanzun,saura kuma sai zuwa nan gaba.."
Kallonsa kawai take tunda ya fara magana har ya dasa aya,mamaki kuwa harya k'are maganar bata daina ba
"So wannan shi ne abunda ya faru a wancan lokacin,yau kuma ina hanyan dawowa sai kira ya shigomin,after nayi receiving sai ba'a yi magana ba al'halin wayan yana tafiya,da aka sake kira nayi reject sai aka turo min sak'o,duk da ban amince da abunda sak'on ya k'unsa ba a dalilin nasan komai,hakan sai yasa naji zuciyata ta umarce ni da yin wani abu maybe ta hakan yasa na sake gano masu sa hannu acikin al'amuran gidan nan,har na shigo ban daina tunanin abunda ya kamata nayi ba,kwatsam ina tafiya sai naji kamar ana bina a baya na ci gaba da tafiya cike da son tabbatar da zargina duk da babu wani abu da zai nuna na san da hakan har na k'araso,bayan shigowa na saina sake fahimtar lallai ne ana bin nawa a dalilin shade da nake gani a wanda ko a kwanakin baya nakan ga hakan ta window,after na shigo na sai na iske ku a parlor,nayi iya k'ok'arin danne zuciyata ne kawai a time d'in,buh abunda ya faru bawai dan na b'ata muku bane,duka hakan ya faru ne just to pretend na ganin na samu daman damk'e duk mai hannu a cikin matsalolin gidan nan...! Hope yanzun kin gamsu da batuna..?"
Gripping lip tayi tana kallonsa kawai ta gaza amsa masa,gira ya d'age mata ganin irin kallon da take masa,a hankali kuma ta girgiza masa kai,tab'e baki yayi sannan ya mik'e ya nufi hanyan bathroom ba tare daya nemi taimakonta ba..
Bayan shigarsa bathroom ta sauke idanunta daga rakiyar data masa dasu tana sake sakin ajiyar zuciya,sai yanzun ne hankalin ta ya fara kwanciya da tasan abunda ya janyo mata fuskantar wannan matsalar,a hankali kuma ta d'an lumshe idanunta tana shafa k'aton cikinta wanda cikin ko wane irin lokaci za'a iya cewa ta haihu,tunanuka ne iri² a zuciyarta game da maganganunsa sai dai a yanzun itama ta fara wani tunani akan matsalolin gidan,tana a haka da lumsassun idanunta tana tunani bacci ya d'an fara fizgarta,kafin wani lokaci tuni ta b'ingire a nan har bata sanma lokacin daya fito ba,koda ya fito ya tarar tayi bacci sai bai tasheta ba ya rabu da ita dan yasan tana jin jiki,musamman a yanzun da cikinta ya tsufa,y'an shirye²nsa yayi sannan ya saka kayan da zasu bashi damar shan iska ya fita parlor hannunsa d'auke da tab.
Almost 30 minutes da fitarsa a d'akin ta farka a firgice saboda wani irin gigitaccen ciwo daya kawo mata ziyara,bayanta ta dafe amma sai taji kamar ba nan ne yake mata ciwon bama,haka ta aza hannun a saman mararta nan ma dai ta kasa fahimtar anya ma nan d'in ne yake mata ciwon ko kuwa,a hankali ciwo ya fara k'arfi tun tana iya kwanciya har ta mik'e ta zauna,itane rik'e can kama can gaba d'aya nutsuwarta ta soma ficewa a jikinta,wasa² ciwo tun tana yi ita d'aya har abu yaso fin k'arfinta naan ta soma kuka tana karanto duk addu'ar da tazo mata,a jikinsa yaji akwai abunda ke faruwa da ita nan ya taso dan ya dubata,ai kuwa yana shigowa ya isketa durk'ushe kusa da bed while kanta ta jingina shi da bed d'in sai juya kai take cikin tsananin ciwo,a kid'ime shima yayi kanta yana tambayanta lafiya,bata iya samun damar amsa masa ba dan yadda ciwon ke dad'a ingizara,abu d'aya kad'ai ta iya masa nuni da shi shi ne mararta da bayanta da suka mata wani mahaukacin d'aurewa,sannu ya fara mata sannan ya d'agota zuwa jikinsa yana caressing bayanta zuwa mararta,cikin kunnenta kuwa iska ya shiga hura mata amma gani yake ciwon tan na sake gaba,ai nan hankalinsa yayi asalin tashi,bai tsaya b'ata lokaci ba kawai yabi umarnin zuciyarsa bayan ya canja kayan jikinsa ya d'auke ta yayi waje da ita,a mota ya sata sannan ya shiga yana k'ok'arin tafiya,duk iya yadda bayinsa keson musu rakiya su bisu nan ya dakatar dasu dan shi tun can yak'i jinin duk inda zashi sai sun wani yab'o jiki sun bishi,a wani private hospital ya nufa da ita inda take aka karb'eta aka shiga da ita labour room,ko da aka shiga da ita sai da suka dubata sannaan Dr Zainab ta fito tana sanar masa haihuwa ne amma akwai sauran lokaci,kasa zama Yarima yayi tunda aka shiga da ita,banda safa da marwa babu abunda yake a bakin d'akin da take,duk iya yadda yaso su barshi ya shiga sunk'i,can dai daya gaji ya nufi d'akin da take yana fad'an wane irin zancen banza ne za'a ce haihuwa yazo amma ba yanzun ba,ita dai Dr da nurses d'in basu iya tanka masa ba coz zasu iyayin ta aikinsu tunda hospital d'in bana gwamnati bane,sam ya manta akan ya sanar da wani a gida nan ya tsaya yana kallonta,Dr Zeainab na tsayen itama da tare da tawagar nurses d'in dake kula da Jeeddah,saboda Yarima yace bai ga dalilin da zaisa ya bari wani likita namiji ya duba masa ita ba,sai dai sam likitoci matan dake kanta duk sai da yayi dana sanin barinsu kusa da ita dan yadda ya isketa duk ta galabaita sai kiransa take,a fusace ya kalli Dr Zainab
"It is how u performs..?? Uban waye ma ya baki license na aikin likita..??"
Tsilli² tayi da ido tana kallonsa da wani irin tsoronsa dan yadda ya birkice musu cikin k'ank'anin lokaci
"What are u still standing for..?? Kin san aikin ki kuwa ko saina nuna muku yadda ya kamata kuyi..??"
Cikin tsawa yake musu magana,da azama gaba d'aya suka tarwatse daga curewar da suka yi a guri d'aya,wani malalacin kallo yaci gaba da bisu da shi cike da hasala yake cewa
"Matuk'ar wani abu ya samu KHUSHI na..u will pay..!"
Hannunsa ta rik'o dai² lokacin da yake sirfa musu ruwan bala'i duk ya rud'asu sun kasa tantance abunda ya kamata suyi,idanunta duk sun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 44 Chapter of 63