Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk wanda bamu samu mun amsa masa ba,a bunne da yawa shi yasa wani lokacin ake samun irin wannan matsalar,ku sani a ko wane lokaci muna tare daku ko da kuwa ace bama cikin group d'in da ake posting novels d'inmu..In sha Allah wad'anda muke tare zamu yi k'ok'arin ganin mun amsa muku a duk lokacin da dama ta samu.Wannan sak'o me daga duka marubuta ba wai iya *Real smasher* ba,muna godiya sosai da nuna mana soyayya da kuke,#Ina mugun ji da ku.* ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 11.* ^^^^^^^^ *#Distressing of marriage spoken.* Wani mummunan fad'uwa gaban Zahra yayi a lokacin data ci karo da sak'on,wanda kallonsa kad'ai ya haifar mata wani irin fargaba,tun kafin ta kaiga karantawa tuni har jikinta ya fara rawa,stool d'in dake gabanta taja ta zauna sannan ta shiga k'ok'arin bin harufan da sak'on ya k'unsa d'aya bayan d'aya ba tare da tana cikin wadatacciyar nutsuwar da zata sa ta fahimci abunda sak'on ya k'unsa kai tsaye.Babu ko sallama a gaba d'aya sak'on wannan ya sake tabbatar mata sak'on ba daga Yariman yake ba kamar yadda ta zata a farko,ga abunda sak'on ya k'unsa _"Zahra Abdulmalik..! Babbar y'a ga jakadan k'asa mai wakiltar Nigeria,wacce al'ummah da yawa suka fi sani da *ZAHRAMALEEK*, tabbas mun san zaki ji mamakin ganin wannan sak'on a dai² irin wannan lokaci da baki zata ba,kamar yadda muka san zai yi wahala a gareki ki yarda da abunda zamu sanar dake,safari dai muna so ne ki nutsu,sannan kiyiwa kanki adalci,kada ki bari soyayya ta rufe miki ido har ta kai ga kin aikata abunda nan gaba zai zame miki abun tir,Allah wadai da gori a idon duniya..Ke d'in mace ce wacce muka san tana ji da ilimi,wayewa had'e da gogewa irin ta mutanen da suka rayu a k'asashen duniya kuma suka yi gogayya da manyan turawa,sai dai wannan wata y'ar dama ce ta sameki da ya kamata ace kinyi bincike akan wannan hamshak'in saurayin naki da kike rawar k'afa akansa,kafin nace komai zan fara ne da baki shawaran bincikar asalinsa da halayensa,mun san kinsan waye muke nufi a wannan d'an tak'aitaccen zancen namu,duka ba wani muke magana akansa ba face *YARIMA YAZEED* babban d'a ga Sarkin Kano ABU YAZEED...Mun so sanar dake wasu muhimman abubawa dangane da shi,sai dai bama so kiji daga gare mu,amma ga kad'an daga cikin tarihinsa wanda a ciki ya had'a da zamansa a gidan kaso har na tsawon shekaru biyar,idan har kin d'auki wannan maganar wasa lallai ne kin tabbata *lusara* haka nan idan kin yarda kin tabbata *mai wayo*,idan kin aminta da batun/baki aminta ba zaki iya bincikawa da kanki dan ki tabbatar da gaskiyar wannan maganar...Mun barki lafiya.!"_ Maimaita karanta sak'on take ko zata fuskanci abunda ake nufi,a k'alla saida ta karanta ta maimaita yafi sau a k'irga kafin ta fara dawowa cikin nutsuwarta,tana daga zaune saman stool d'in amma jiri take ji yana neman kada ita k'asa,a daddafe ta mik'e a gurin ta isa bakin Italian bed d'inta ta kwanta dan yadda take jin zuciyarta na wani irin skipping kamar zata faso k'irjinta ta fito kan tsabar tashin hankalin da take jinta acikinsa,k'aran shigowar wani sak'on a karo na biyu ne yasa ta d'an mirgina gefe tana kallon wayanta,da kyar ta iya kai hannu ta d'auka dan a lokacin ji take komaima yayi mata nauyi,a hankali tayi clicking sannan ta fara karantawa _"Idan har kin aminta da abundabatun da muka fad'a a yanzun,muna so ki fara investigation daga yanzun,nd kafin kiyi tunanin tunkarar Central Jail ki fara ta kan *REMAND HOME* dake nan Kano state a Goron dutse,Dala L.G.A,coz zaki fi samun abunda kike buk'ata,na tabbata daga lokacin da kika san komai zaki fahimci waye asalin *YARIMA YAZEED..! "_* Shiru ta d'auka har bata san lokacin da wayan ya zame a hannunta ya fad'i k'asa ba,nan da nan saddest tears suka fara chasing akan cheeks d'in ta,ba tare data san dalilin kukan ba,dan kanta kuma koda ta gaji ta bar kukan,ta jima shiru ita d'aya yayin da zuciyarta ta tafi can wani nahiya na daban,tana tsaka da mugun tunanin kirana ya shigo wayantaamma tayi biris da shi ta kasa koda motsawa bare ayi tunanin zata d'auka,haka yayi ta kiranta amma tana ji tak'i koda d'aukan wayan bare ta duba taga waye yake kirantan. A can gefen Yarima kuwa,kamar yadda yayi mata alk'awari zai je,tun bayan da ya gama shirin zuwansa yake ta trying kiranta amma sam tak'i d'auka,ko da ya kira ya maimaita ba'a d'auka ba sai kawai ya hak'ura da neman line d'in zuciyar sa na wani irin tsinkewa dan yadda fargaba ta sashi a gaba har ya rasa abunda zaiyi. Tunani ya d'an tafi tin daga time d'in da yake sanar da ita zuwansa har kawo yanzun da yake tsaye,amma sam ya gaza gano wani abu da zaisa tak'i picking call d'in nasa,"shin mene ne yake faruwa haka da zai ta kiranta ta kasa d'auka...??" Ya d'auki wasu y'an mintuna yana tunani amma ko d'aya bai gano wani dalilin da zai kama ba akan ko yayi mata wani abu ne,a hankali ya koma ya kwanta saman resting chair yana sauke numfashi cikin zuciyarsa yana fata akan baiyi mata wani abu da zaisa tak'i answering call d'insa ba,yana wannan tunanin bacci mai cike da fargaba ya d'auke shi a nan dan dama ba wani cikakken bacci ya samu yayi ba da dare coz bai dawo daga hospital da wuri ba. ^^^^^ A can gefen Aisha ma,ba'a barta a baya ba dan tun daga lokacin da yarima ya gargad'i Sajida akan baya son ganinta ta shatawa gidan line ba'a sake ganinta ba,haka ko data samu labarin abunda ya faru na daga rabuwar auren Sajidar da Yariman duk da taji babu dad'i a ranta na daga faruwar hakan ba,haka tana zargin kanta da aikata mummunan nufin da aka sata duka a garin neman comma buri sai dai ta san ko giyar wake ta sha bata isa ta fito ta bayyana cewar ga ainihin abunda ya faru da har ya janyo hakan ba,kullum a yanzun bata da aikin da ya wuce yini a d'aki idan ta gaji da zaman kad'aici kuma ta d'auka car keys ta fice zuwa park,wani lokacin idan ta rasa abun yi haka zata yita kuka ko ta samawa zuciyarta ta sassaucin damuwoyinta,tare da fatan Ubangiji ya bayyana mata wata hanya da zata sadu da wani nata. Duk irin wannan jin kan da Aisha ta kasance tana da shi a yanzun ta koma wata iri,mutanen da ada take d'aukan su ba komai ba,yanzun idan ta gansu sai dai ta bisu da ido,wanda sosai wannan canjin d'abi'un nata suka fara bawa da yawa daga cikin mutane mamaki,amma kowa ya b'oye abun a ransa yak'i furtawa,ni kuwa dai nace ko me suke tunani da suka k'i fad'an ohoo musu. ^^^^^ Tun data gama kukan ta mik'e da mataccen jikinta da take jin duk duniya ma tayi mata zafi,ta shafe a k'alla mintuna sama da 40 tana tunani da kokwanton al'amarin kafin ta amshi tayin da zuciyarta take mata game da tracing case d'in da aka fad'a matan,sai data gama shiryawa kafin ta nemi guri ta zauna tayi connecting bluetooth d'inta dana wani amintaccen security'nsu mai suna Saleem,cikin kasala take magana da zallan harshen nasara "Hello..! Saleem kana ina...??" Shi ne abunda ta fara fad'a,banji amsan da ya bata ba,sai dai naji tace "Ok..Kazo yanzun ina son ganinka..!" A hankali ta koma ta kwanta da baya tana closing eye's nata,mintuna kad'an akayi nocking door d'in,ba tare data bud'e ido ba kota damu da duba waye ta furta "Shigo..!" K'ofar ya turo bakinsa d'auke da sallama,ya tsaya yana jiran yaji me zata fad'a,still tana daga kwancen ta furta "Saleem..!" Ya amsa mata da girmamawa "Yes ma'am.." "Kasan dalilin da yasa na kiraka..??" "No! Ma'am.." Jinjina kai tayi duk da yadda take jin kanta kamar zai bar gangar jikinta,a hankali taci gaba da magana "Kasan dai yarda ce tasa har yanzun kake nan a matsayin guard namu ko..??" "Yes! Ma'am..!" Sai a lokacin ta yunk'ura ta mik'e zaune tana runtse idonta "Good..! Ina son na saka wani aiki ne,nd ina fatan zaka yi,sannan ya kasance sirri dan bana son kowa ya sani bayan mu biyun nan.." Jinjina kai yayi cike da gamsuwa,a hankali ita ta jinjina kai kafin ta kai hannunta kan laptop dake gefenta ta shiga y'an wasu dube²,kusan mintuna biyar ta d'auka kafin ta d'ago tana fad'in "Na tura maka da abunda nake buk'ata,nd it's urgent,i need it within a few hour's idan da hali..!" "Ok ma'am...as u wish.." Kud'ad'e ta zage jakarta ta ciro wanda ita kanta bata san ko nawa bane,ta mik'a masa tana sake fad'in "Idan da wani abu kuma let me know.!" Bayan nan ta sallameshi bayan ta gama masa k'arin bayani,nan ya fita ya barta zuciyarta cike da wani irin panic da yake taso mata. Bayan fitar guard Saleem daga gurin uwar gijiyar tasa,sai ya shiga k'ok'arin duba abunda ta tura masa,nan yaci karo da sak'onta,ko daya gama dubawa daga nan airport ya nufa don yin bucking flight wanda zai kai shi Kano.Sai dai yayi rashin sa'a dan a ranar bai samu jiri ba,sai dai ya gama komai damar tashi ne babu a ranar,sai ya jira washe gari kasancewar bai riga da yayi bucking da wuri ba da yake yamma yayi masa a lokacin. A washe gari kam tun da sassafe ya gama shirin tafiya,misalin k'arfe 7:00am jirginsu ya tashi sai Kanon dabo,in 3 hours 48 minutes jirginsu yayi arriving,kai tsaye sanda ya fito daga airport d'in yayi nemi cab daga nan zuwa criss cross hotel dake nassarawa don ya kama lodged na kwana biyar kamar yadda yake tunanin binciken nasa ba zai haura wannan kwanakin ba,haka nan baya tunanin zai haura wad'annan kwanakin ba tare daya koma ba,sanda ya huta ya samu abinci ya kaiwa yayan hanjinsa sannan ya fara tunanin kiran madam d'in nasa,tana d'auka ya sanar da ita sun sauka lafiya,daga nan kuma suka d'an sake tattaunawa tana sake bashi logic na yadda ya kamata ya fara binciken,amsawa yayi with reverence sannan suka yi sallama. ^^^^^ Yarima kuwa a nasa gefen tun daga kiran da yayi ta mata tak'i d'auka,bayan ya tashi a bacci ma haka bai hak'ura ba ya sake trying number nata amma still bata d'auka ba,jikinsa ne ya sake mutuwa dan yasan haka nan banza bazai tab'a yi mata irin wannan kiran tak'i responding ba,kuma yasan baza taga miss calls nasa ace har tsawon wad'annan awannin tak'i bin kiran ba,sai dai ko idan akwai wani abu dake kan faruwa,wannan tunanin ya zo masa a lokacin. Yini guda haka yayi ta fama da kiranta ba'a d'auka daga k'arshe da ya sake trying sai jin wayar yayi a kashe,sosai abun ya d'aure masa kai dan bai tab'a tunanin hakan daga gareta ba,washe gari ma abunda ya faru kenan,ganin hakan ba mafita bane yasa ko daya tashi a aiki ya kasa wucewa gida,kai tsaye sai ya nufi hanyar gidan su Zahra'n dan jin abunda ke faruwa,sanda ya iso tun daga get d'in farko na line d'in inda securities suke suka fara shaida masa madam d'in bata nan kamar yadda ta bada umarnin a sanar da duk wani mai nemanta,abun ya bashi mamaki sosai har ya fara tambayar kansa "me ke faruwa haka..??" Reverse yayi kawai ya kama hanyar gida,da zuwansa ya yada zango tun daga parlor,dan daga suit d'insa har lab coat d'inma a hannu ya shigo da shi yana shigowa kuwa ya ci gaba da k'ok'arin zare tie d'in wuyansa yana b'alle botiran long sleeve d'in,shigowar YASEER kenan shima bayan y'an mintuna ya tarar da shi a wannan halin idanunsa a rufe ya dafe forehead d'insa da hannu d'aya,kallo d'aya ya masa ya fuskanci akwai damuwa sai dai bai tsaya kusa da shiba ya wuce ya barshi a nan,sanda ya samu nutsuwa ya dawo ya zauna kusa da shi yana tab'a shi,bai d'ago ba haka bai bud'e idonsa ba ya furta "Leave me alone..Please!" Mamaki sosai YASEER yayi da jin maganarsa,nan ya sake tabbatarwa ba lafiya ba,duk da yaji abunda ya fad'a hakan bai hana shi tambayar saba "Broah..! What happened..??" Wani irin huci ya fesar mai d'umi sannan ya bud'e ido a hankali yana kallon YASEER "Ina cikin matsala broah.." Ajiyar zuciya YASEER yayi kafin yace "Duk damuwarka u have to pray,kasan komai mutum yake in har zai dunga addu'ah zaiga sauk'i ko..??" Kai ya jinjina masa cikin wani irin yanayi da bai sanma yayi ba.Wasa² sai da suka shafe ak'alla 4 day's a haka ba tare da ya samu wani madogara ba daga ganeta. ^^^^^ Ita kuwa Zahra tun bayan data gama magana da guard Saleem lokacin daya sauka a Kano take yawan jin fad'uwar gaba mai tsanani,haka ta ci gaba da daurewa tun abun na damunta sosai har ya zama ta fara yakice shi a ranta. Tsawon kwanaki uku Saleem ya d'auka a Kano duk akan binciken a ranata hud'u ya juyo zuwa Abuja cike da nasarar abunda ya kaishi,lokacin daya shigo garin Abuja bai jira zuwa ya huta ba kai tsaye ta wuce gidan Ambassador Abdulmalik don kai rahoton aikinsa.A dai² lokacin daya iso itama Zahra shi d'in kawai take jira dan tunda ya sauka daya shaida mata yana nan tafe ta kasa zaune bare tsaye,cike da zumud'i ta tare shi da muradin ganin abunda tasa shi yayi mata binciken,can k'asan zuciyar ta kuma tana fatan sakamakon ya kasance sab'anin abunda zuciyar ta ke hakaito mata,lokacin daya tsaya gabanta yana gaisheta ko takan gaisuwar sa bata biba dan ita ba shi ne abunda tafi damuwa da shi ba,wani dogon sharhi Guard Saleem ya fara mata nan ta d'aga masa hannu cikin kasala ta ce "Ba abunda nake buk'ata kenan daga gareka ba,ina aikin dana saka..??" Tana mik'a masa hannu,babu yadda ya iya dolensa ne yayi abunda tace,dan haka babu b'ata lokaci ya shiga clicking wayansa yana duba folder d'in da yayiwa duka documents daya samu game da abunda ya shafi rayuwar Yariman a REMAND HOME,Harma zuwa zamansa a Central Jail,lokacin data karb'a harta juya ga laptop d'inta sai kuma ta kalleshi a hankali ta ce "Kaje saina nemeka..!" Daga haka bata kuma bi ta kansa ba ta juya,nan shima yayi mata godiya sannan ya fice.Ita kad'ai ya rage d'akin bayan fitar guard Saleem,nan take tayi connecting wayan da computer ta shiga dubawa,page by page ta fara bi tana dubawa,har ta kai k'arshe wanda duk cikin dauriya ne take binsu,izuwa lokacin kuwa idanunta har sun gaji da tsiyayar ruwan hawayen da har bata san adadin kukan da tayi ba,tana zuwa paging k'arshe kawai sai ta kife computer tana sake rushewa da wani irin saddest cry,sanda ta gama kukanta tsaf sannan ta kuna network d'in wayan dama shi ta kashe bawai wayan ba,number Yarima ta shiga trying bugu biyu ana uku yayi answering yana sakin siririyar ajiyar zuciya,tashin farko kalmar daya fito a bakin Zahra shi ne "Me yasa zaka munafurce ni..?? Why ain't u told me the truth of ur affairs..? Why do u need to hide these important issues..?" Shi dai yarima jin abunda take fad'a ne yasa kalmomin da yake son fad'a mak'alewa a fatar bakinsa "Da gaske ne ka tab'a rayuwa a *Jail...??"* Maganar yazo masa a bazata,had'e da wani mugun tashin hankali daya ziyarce shi wanda tunda yake a rayuwarsa wannan shi ne karo na biyu da zai iya tunawa daya tab'a jin kwatankwacin hakan a tare da shi,shirun da yayi bai amsa taba yasa ta fashe da kuka tana cewa "I will never marry u azzalumi..! Ka cuce ni ka kuma zalunci zuciyata,da sannu zaka ga sakayyan abunda kamin..!" Runtse idonsa kawai ya iya yi yana jin yadda maganarta ke shigar sa tamkar kaifin takobi tana ratsa duk wani gab'a na jikinsa,ko kafin ya kaiga yin wani magana tuni har ta katse kiran tana ci gaba da fashewa da matsanancin kuka............... *#Tofa...! Wannan shi ake kira da "tashin hankali.....(gobarar gemu)" 😢😢,wai shin Fan's me yake shirin faruwa da Yarima ne kuma ma..?? Ni kaina na gaza fuskantar komai...Ku kawo agaji..😭😭😭* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ _Gaisuwa tare da fatan alkhairi gareku my co-writers._ *Aunty Meelat* *Aunty Mounath* *Leematiiy* *Hulbateey* *#Surayyahms (official catty)* *Mr's Xerks* *Aufana* *Sis Nerja'at* *Mai Daddawa* *Ummerhaney nersallerh* *Nasiba I gawo* *Aeshab* *Sawwama* *Mr's j moon* *Hafnan* *Fenerh* *Mom hanan* *Meerahgee* *Na'ikke* _Ina miko gaisuwa musamman wanda suka koyi lab'e,ba'a ganinsu sai tsilli². 😁😁 Kuma dai ban kama suna ba kada wani yace nace Eheen!._ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 12.* ^^^^^^^^ *#Resignation letter.* Almost 20 minutes ya d'auka ba tare da ya motsa ba,k'wak'walwarsa kuwa were in short strike,duka² ya rasa abunda ya kamata yayi a lokacin,"shin bak'in ciki ne zaiyi ko kuwa kuka ya kamata yayi..??" Zuciyarsa ta tambayeshi,cikin wani irin scary voice a fili ya furta "Nooo! I will never failed..until i defeat them..!" Gumi ne yake keto masa had'e da wani zafi da yake jinsa tun daga cikin k'ashinsa,shi kam tunda yake a rayuwa a kuma yanzun tunaninsa ya tafi akan ya wuce shiga irin wannan tashin hankalin,rabon sa da shiga makamancin wannan zai ita cewa tun yana d'an shekaru goma sha biyar a duniya,yana zaton zuwa yanzun yayi bankwana kenan da duk wani tashin hankali makamancin wannan sai gashi lokaci guda komai yana neman lalacewa.Lokaci kad'an tunaninsa gaba d'aya ya gama kwancewa shi duk bama wannan ne damuwarsa ba yadda ta kirashi da azzalumi,tunanin da yafi damun k'wak'walwarsa kenan,yana cikin wannan yanayin YASEER ya dawo,d'agowa yayi da jajayen idanunsa ya sauke su akan YASEER d'in na wani d'an lokaci kafin ya mik'e cikin wani irin speed yana rik'o YASEER irin rik'on tsaurin nan,kallonsa yake da irin rik'on da yayi masa abun sosai ya so firgita shi,ko kafin ya kaiga tambayarsa me yake faruwa tuni Yariman ya shiga watso masa tambaya "Broah.! Am i looos like a tyrant..?? Am i kinda these people..?? Why did she call me with such a name..Why...??" Gaba d'aya ya gama birkicewa,ko da YASEER ya fahimci baya cikin nutsuwarsa kai kawai ya shiga masa nodding alamun ba haka bane,coz yana son yayi calming nasa zuwa ya dai²tuwar nutsuwa,wani irin ajiyar zuciya ya shiga saukewa sannan ya zame hannunsa a jikin YASEER yana sulalewa nan a k'asa,shi kansa YASEER yasan abunda ya faru a wannan lokacin mai girma ne tunda har ya ganshi cikin irin wannan mode d'in to amma bai san mene ne actual abunda ya haifar da matsalar ba,shin ta yaya zai fahimci damuwar d'an uwan nasa..?? A hankali ya sake sauke idanunsa akansa yana nazarin sa,zuwa can kuma ya sauke knees d'in sa a k'asa kusa da Yariman yana dafa shi,in a chill tone ya fara magana "Who calls u with this name..??" Kamar wanda ya furgita haka ya d'ago ya zubawa YASEER idanu kamar mai neman amsan tambayarsa akan face nasa,bai iya amsawa ba har saida ya sake tambayarsa "She's the one..broah me nayi musu ne..Always they were restrict on me..?? Why all these happened on me alone.? Why..?" Kai yake girgiza masa,cikin zuciyarsa shi kansa zafi yake kamar shi ne a cikin halin da Yariman yake ciki,rabonsa da yaga d'an uwan nasa cikin irin wannan matsalar tun a time d'in da aka masa wannan mummunan k'azafin,cikin wani irin yanayi ya mik'e had'e da wucewa ciki,yana shiga ya watsar da kayan da suke hannunsa yana jifa da duk abunda idanunsa suka sauka akai,can kuma kome ya tuna ya tsaya cak yana duban yadda cikin k'aramin lokaci ya haukata bedroom d'in,wayoyinsa ya tuna nan take ya fice a haukace zuwa motan daya fita da shi,sanda ya dawo ma nan ya sake tadda yarima yayi wani irin buga tagumi kamar orphan,ji yake duka tausayinsa na sake lullub'e shi,wayan Yarima daya hango a yashe ya nufa dan yana son kiranta yaji dalilin wannan cin mutuncin,yana kai hannu kuwa Yariman ya furta "Don't call her..She's already told me she were partitioned our relation..." Zare ido YASEER yayi waje kafin ya furta "Akan wane dalili ne hakan zai faru..??" Girgiza masa kai kawai yake ya kasa cewa komai game da tambayar tasa,kallonsa kawai yayi ya jinjina kai kafin ya fara kiranta da line d'in Yariman,kusan miss call goma ya jefa mata amma bata d'auki ko d'aya ba,sauke wayan yayi a kunnensa cikin k'araji yana fad'in "Damn it..she didn't picked..!" Da sauri kuma kamar wani zararre ya d'ago wayan a hannunsa ya shiga kwashe digit d'in zuwa nasa phone d'in,yana gamawa ya sake hankad'a mata kira,cike da zak'uwa yake ta moving a side's,sai da wayan yaje daf da katsewa aka d'auka da fad'in "Hello..! Who's on d line..??" Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi,duk yadda zuciyar sa ke cike taf da bak'in ciki sai ya samu kansa da tausasawa saboda yasan mene ya faru "It's YASEER,Prince YAZEED's brother..!" Sarai yana jinta data ji ya ambaci sunan ta saki wani tsaki,amma sai ya share yana nodding kai tamkar wani lizard "Ok..! So sorry yanzun bani da lokacin wani Prince,nd this will be the last time da wani zai kira ni yana min maganar wani YAZEED,I don't want anything relation with him..!" Tana fad'an haka ta soma k'ok'arin ajiye wayan,cikin tsawa YASEER ya furta "Stop..! U have to clarifies what happened tsakanin ku..!" "Ohh! D'an wannan abun ne yasa kake min tsawa..?? To barin fad'a maka wani abu,nasan dai ya riga da ya sanar da kai,idan ma bai fada ba wannan ba damuwana bane,kamar yadda na fad'a masa kaima zan maimaita,aure tsakaninmu bazai yiwu ba..!" "Heeyy! Madam wannan kwane² da kike yi na mene ne,ki fito kai tsaye ki fad'i abunda ke ranki mana.." "Kaga malama stop shouting on me..Ka haife nine da kake cika min kunne.?? Na ce bazan aure shinba sai akayi yaya..?? Dama tun farko da amincewata ne nace naji na amince,but a time d'in kawai dan bansan waye shiba,for now kuma dana sani na fad'a bazan iya auren captive men ba,wanda rayuwarsa ta k'are a jailhouse..!" "Keeee! Dakata.." YASEER ya buga mata tsawa,ko kafin ya furta wani abun tuni itama ta bashi amsa "Baza'a dakata ba d'in..Na fad'a maka daga kai har d'an uwan naka baku isa ku dinga min wannan hayaniyar akaiba,saboda haka ku kiyaye..nd wannan ya zama karo na k'arshe da wani cikinku zai sake bibiyata..!" "Dallah rufemin baki..ke har kin kai macen da zata nemi raina hankalin mutane..Sai dai ina so ki sani *KIN TAFKA KUSKURE* da har kika kasance wacce take d'aukar magana,zaki yi nadaman abunda kika aikata wata rana a lokacin da ko kusa da D'an uwana baki isa ki zo ba..Kamar yadda kika fad'a ne muma bama

Chapter 34 of 63