Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lokaci yayi da zan d'auki fansar abunda kika min..kece mutum ta farko dana aminta da ita a duniya ta,amma kene ta farko da kika ha'inceni,kin cutar dani kin jefani a *UK'UBA* a wancan lokacin,sai dai nima ya zama dole a wannan karon na rama,na tabbatarwa da raina saina jefa rayuwarki cikin tsananin da yafi wanda kika jefa ni,wannan alk'awari ne na d'aukarwa kaina tsakanin KE,YAZEED da kuma YASEER dole ne saina jefa misali a cikin rayuwar d'ayanku wanda ko sunan wata kuka ji an ambata mai shigen nawa zai saku shiga mummunan tashin hankalin da ban shige shi ba a tsohon rayuwataaa....!" "Da kyau *TAWAN* sai yau ne na tabbatar ke en rainona ce,tabbas wannan alwashi da kika yi babu abunda zai hana shi tabbatuwa,kece alfaharina kuma abar k'aunata..!" Juyowa tayi tana kallon dai² inda Ladidi take tsaye tana magana,ko da suka had'a ido take suka sakarwa juna murmushi mai d'auke da zallan mummunan nufi... Ga Adda kuwa ko data bar wajen direct d'akinta ta nufa kasancewar wayarta na can ta barota bata fito da ita ba,da zuwa bata tsaya sanya ba,nan ta matsa lambar hajiya ta kirata,bugu biyu aka d'auka da sallama,ko kafin hajiya ta tambaya tuni muryar Adda tayi mata dirar MIKIYA a kunnuwanta,shewa suka yi su duka irin wacce suke yi a duk lokacin da suka ga juna ko suka yi waya,sun jima suna hira kan abunda ya shafesu kafin Adda ta sako zancen da dama tayi wayar ne dominsa,tsara hajiya ta fara yi ta yadda tasan duk wata magana da zata biyo baya hajiyar bazata k'i amincewa ba,kafin daga Biyani kuma ta fayyacewa hajiyar duk wani k'udurinta da gurinta akan maganar yadda zasu k'ulla alak'ar Aisha da Yarima YAZEED,duk wani abu da take ganin zaiyi dai² a tafiyar sai data tabbatar ta tsarawa hajiya hatta kuwa da yadda za'a tunkari maimartaba da zancen dan yadda suka fahimci samarin na Maimartaba ba k'ananun y'an ji da kai bane,shi yasa ko da suke wannan zumud'in ma basu tsara zasu fara tunkarar YAZEED da maganar ba kai tsaye,sun tsara komai yadda ya kamata,haka duk wani shiri nasu ya tafi yadda suke buk'ata dan yadda hajiya ta jajirce akan maganar sai ka rantse da Allah akan d'anta ake wannan shirin ba jika ba,bayan ta sani cewa su y'ay'a alfaharin iyayen su ne,haka zalika y'ay'an zamani daban da nasu,ba kowane y'ay'a ne kakanni zasu yanke musu hukunci su biba,kai wanima baya d'aukan abunda iyayensa ke so da muhimmanci bare kuma aje batun kakanni,suna gama wayan bayan Adda ta ajiye wayar ta saki wata irin dariya mai cike da samun nasara,a fili ta furta "A k'arshe dai nayi nasara,nima wata rana zanyi alfahari da cewa nice kakar matar sarkin gobe...." Furucin da Adda tayi sosai ya bani dariya dan yadda ta d'ora yak'inin ta akai sai kuyi zaton har anyi auren Aishar da Yariman,ko kuma ance mata an d'ora shi YAZEED en akan karagar mulki... ^^^^^ Can a b'angaren hajiya kuwa ko kad'an bata d'auki maganar da wasa ba,tun bayan da suka gama magana da Adda data gama tsara mata abunda ya kamata ta sanar da Maimartaba tayi caraf ta hau tayi d'are²,tun a ranar bata bari ta jira komai ba,tasa aka kira mata Maimartaba gefen ta,duk hanyar da tasan idan tayi magana zata yi saurin isar da sak'on gare shi itama shi tabi,nan take tayi amfani da tata damar wajen fara warware masa duk dalilin kiran nasa da tayi,koda ta gama zayyano masa k'udurinta da maimartaba yaji,nan take ya gyara zama da niygar fuskantarta da maganar bud'ar bakin maimartaba kuwa a lokacin sai yake cewa da hajiya "Gaskiya ne hajiya duk maganar nan da kikayi mun tabbata matuk'ar zamu had'a yaran nan aure tofa zumunci zai sake k'arfi haka nan muna da tabbacin wasu abubuwa da suka faru a baya zasu sake yin sauk'i,sai dai wani hanzari ba gudu ba,hajiya mu duka anan ba wannan muke ji ba,yau da ace akan mune wannan abun ya faru mun tabbata bamu da ja akan duk hukuncin ki,mun tabbata za muyi maraba da shi akowane irin lokaci,sai dai kuma jin sha'anin akan y'ay'an yau wanda ka haifesu ne amma baka haifi halinsu ba yasa muke son yin magannar da zata sa mu fahimci halin da za'a iya shiga,mu idan har tamu ne wannan AL'AMARI zai fi kyau ace su daga b'angarrn yaran suka ga junansu suka kuma nuna sha'awar a had'a su aure,amma fisabilillahi hajiya muna gudun ace mun yanke hukunci kai tsaye ba tare da jin ra'ayin su ba,sam idan muka ce mu namu hukuncin da shi za'ayi amfani muna da tabbacin abunda muke so bazai tafi dai² ba,amma muna bada hak'uri bisa wannan magana tamu,sai dai zamu tuntub'i shi yaron muji daga gare shi duk abunda muka yi da shi sai a sanar dake.." Tunda ya fara maganar take kallonsa tana jinjina kai da tab'e baki,a ranta kuwa fad'i take "Lallai wannan shi ne anyi ba'ayi ba,wai an raka bak'o ya dawo...Tabbas da nasan abunda zanji daga bakinka kenan kaima da ban neme kaba,yanzun na gama d'ora yak'inina akan zaka amince d'ari bisa d'ari da duk shawara ko hukuncin da zan yanke sai kawai kuma naji sab'anin haka,ai kam ya zama dole nayi wani abu ko dan kada mutunci na ya zube a idon Adda da ahalin ta baki d'aya.." Bata jira ta gama tunanin ba ta kyab'e baki had'e da fashewa da matsanancin kuka,cikin kukan ta shiga fad'an duk abunda yazo bakinta "Wayyyoooo..! Ni Allah na,shi kenan yanzun duk fad'in duniyar nan bani da wanda na isa dashi,yanzun ace ka haifi d'a amma baka isa dashi ba,baka isa kasashi abu yayi maka ba,fisabilillahi dan wani yayi min haka ai bai kamata naji haushi ko ciwo ba,tunda naka ya bula maka k'asa a ido kaima d'an Abdu yanzun abunda zaka sakamin da shi kenan..? Shi kenan babu komai tunda ka nunamin ban isa da zuri'ar kaba,kaje kawai zan bawa Adda hak'uri zan kuma nemawa y'ar wani mijin a gari,dad'in abun ai bakai kad'ai ne d'a agurina ba bare ka nunamin iyakata,duk na san ba laifin ka bane kaima,laifin wannan sarautarne duk ya maidaka haka,sam yanzun baka ko sauraro na bare kaji magana ta,na gode d'an Abdu kaje kawai babu damuwa ni yanzun na san matsayina a gurinka.." Tana fad'ar haka sai ta sake b'arkewa da kuka,ga maimartaba kuwa hankalin sane ya tashi matuk'a ganin yadda hajiyar ke kuka wiwi,hak'uri ya shiga fara bata wanda shima sai da k'yar sannan ta hak'ura tayi shiru,nan maimartaba ya shiga lallab'a ta da bata baki akan tayi hak'uri ta bashi wasu y'an kwanaki zai san abun yi akan matsalar sannan kuma zai tuntub'i YAZEED en da maganar,koda jin haka nan take annurin fuskar ta ya soma dawowa ta shiga sa masa albarka daga shi har zuri'ar sa,shi kuwa maimartaba amsawa kawai yake amma ba wai don ya aminta da maganar har cikin ransa ba,kawai dai ya amsata ne saboda babu yadda zaiyi da ita,yasan matuk'ar ya nuna k'in amincewarsa a lokacin haka nan zata sashi agaba tana ta koke² kuma daga ranar haka za'ayi ta fama da ita a cikin gidan bazata daina ba har sai an d'auki tsawon lokaci tana mitar al'amarin. Bayan kwanaki biyu da yin wannan maganar tsakanin maimartaba da hajiya,da dare maimartaba yana gefen Fulani ya nemi ganin YAZEED en,tunda yariman yaji Fulani ta sanar masa maimartaba na son magana dashi yasan ba k'aramin abu bane,haka yayi ta k'isima abunda zai iya faruwa idan yane,duk da yadda yake jin jikinsa na bashi abunuwa da dama,hakan bai hana shi amsa kiran mahaifin nasa ba,sai dai koda zuwansa duk tunaninsa da yak'inin sa sai ya zama badai² ba,koda ya gaida mahaifin nasa tun kafin maimartaba ya fara magana sai daya fara kallon YAZEED en tukun fuska babu wata wadatacciyar walwala sannan ya fara da cewa "YAZEED..! Shin a wane mataki zaka d'auki maganar mu...???" Gabansa ne ya fad'i jin a yanayin da maimartaba da yayi furucin,kansa ya sunkuyar k'asa kafin ya furta "Abiiy ai duk wata magana da zaku yi matuk'ar akaina ne ko wani abu daya danganci rayuwata yana nan a matsayin umarni.." Jinjina kai maimartaba yayi kafin yace "Ka tabbata duk abunda muka saka zaka yi ba tare daka musa ba ko a samu akasi..??" Jinjina kai ya fara yi sannaan ya furta "K'warai da gaske ranka ya dad'e,matuk'ar dai bai sab'a da hukunci ko dokar mahalicci ba,na tabbata zanyi shi kamar yadda kuka umarta.." Jinjina kai maimartaba ya sake yi kafin ya ce "Haka muke fata a ko wane lokaci idan muka yi umarni ya kasance kunyi mubaya'a,wannan shi zai sake tabbatar damu akan adalci kuma al'ummah suyi mana zaton alkhairi tare da yi mana biyayya a duk wani hukunci da zamu zartar musu...Sai dai a wannan karon muna son sanar da kai ne ba akan komai muke so ka karb'i umarnin mu ba sai akan muna son ka nemi auren y'ar uwarka *Aishatu...!"* Wata irin fad'uwa gabansa ya sake yi data fi ta farko,nan ya d'an d'ago ya saci kallon maimartaba kafin cikin diriricewa ya furta "Allah ya baka tsawon rai shin wace Aisha kake nufi na nema..??" "Aishatu jikar kakarta Adda muke nufi..!" Dogon ajiyar zuciya ya saki,kafin cikin k'arfin hali ya amsawa maimartaba "In sha Allah Abiiy duk abunda kace zanyi in dai zai faranta muku,sai dai ina neman wata alfarma a gurin Maimartaba." "Fad'i duk abunda kake son fad'a,sai dai ka sani muna gargad'inka da duk maganar da zaka fad'a ta kasance ba'a kan sab'a umarnin mu bane.." "In sha Allah ma Abiiy ba akan sa bane.." Jinjina masa kai maimartaba yayi nan yariman ya sake sunkuyar da kai k'asa yana taradaddin abunda zai fad'a dan babu tabbacin maimartaba yayi na'am da ita "Dama Abiiy ba akan komai bane nake son yin magana,sai dan ina neman alfarma akan kafin a yanke lokacin da za'a yi auren a d'an bani lokaci mu fara fahimtar juna da ita..!" Bai kai k'arshe ba Maimartaba ya tari numfashin sa da fad'in "Matuk'ar wannan shi ne kad'ai abunda kake buk'ata babu makawa ya zama lallai muma mu amsa maka tunda har ka amince dayi mana biyayya akan namu umarnin, saboda haka muke maka Albishir da cewa uzurinka karb'ab'b'e ne a gurinmu..." Godiya yayiwa maimartaba,sannan ya sallame shi ya fita,tunda ya fito daga gurin maimartaba ya fara jin wani irin zafi na keto masa,tafiya yake amma gaba d'aya zuciyarsa banda zafi babu abunda take saboda tsabar yadda jin sunan Aisha ma kad'ai yasa shi rasa nutsuwarsa,cikin lokaci kad'an tuni duk wani tunani nasa ya goce,kafin wani lokaci tuni har ya gama fita a hayyacinsa,cikin haka ne ya k'arasa gefensu a daddafe,yana shiga kuwa tun kafin ya kai ga isa tsakiyar parlour'n ya fara karo da cuitions en gurin da kyar dai ya samu ya nemi guri ya zauna dan yadda yake jin kansa na masa wani mahaukacin sarawa.................. *Tashin hankali kenan wanda ba'a sa masa rana,sai dai abun tambayar anan shi ne anya kuwa wannan aure zai yiwu...???* *A matsayin yarima na wanda aka amince masa su fara fahimtar juna da Aisha shin zai ganeta ko kuwa,me zai faru a duk lokacin da suka had'u...???* #Follow me on wattpad @jeeddahmu898. #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *Facebook:@RealSmasher.* *______________________* *fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY SISTER'S♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻* ___________________ *Pg 23.* ^^^^^^^^ Shigowar YASEER kenan lokacin shima daga b'angaren Ummi,yana zuwa ya tarar da YAZEED kwance a k'asa ya d'ora hannunsa d'aya a forehead idanunsa a kulle sai wani irin ajiyar zuciya yake da zauri² dan yadda ransa duk yake a jagule,k'arasowa YASEER yayi ba tare daya san me yake faruwa ko yayi noticing halin da YAZEED en yake ciki ba ya dungureshi da k'afa "Dillah malam tashi,ni zaka rainawa hankali ka wani zo ka baje a nan.." Shirun da yaji ya masa har ya gota shi ya d'an waiwayo ya kalleshi,yadda chest ensa ke d'agawa da komawa da sauri ya sashi dawowa,a kusa da shi ya durk'usa yana tab'a shi,yadda yaji jikinsa yayi zafi yasa shi saurin janye hannunsa daga saman goshinsa,cikin rikicewa ya furta "Broahh! What's going wrong..??" Yana tambayarsa yana tattab'a shi,jin yak'i motsi yasa shi zaman dirshen a gabansa sannan ya d'ago shi yana k'ok'arin zaunar dashi,rik'o hannunsa YAZEED yayi yana sake runtse idonsa,cikin rashin kuzari ya d'ago hannunsa yana ma YASEER alamar ya k'yale shi "To wai kai mene yake damunka ne..? Naga yanzun babu jimawa muka rabu da kai zaka je gurin Maimartaba,yanzun kuma na zo na taddaka a haka..?? Na tambaya me faru kak'i yimin bayani..?? Kasan dai ni ba Allan misru bane dazan sani ko...??" Daurewa yayi ya d'an d'ago jikinsa yana jan jikin har ya isa jikin seat ya jingina yana sake runtse ido "Dan Allah broh kamin bayani kasan dai bani da masaniya akan abunda yake damunka ko..? Kamin bayani ko Allah zaisa ina da yadda zanyi na iya taimaka maka.." Cike da son K'warata jikinsa,game da k'arfin hali ya bud'e narkakkun idanunsa da damuwa ta saukar masu da sauyin yanayi ya kalli YASEER kamar zai fashe kuka "Broh..! Wai aure Maimartaba yake son nayi..!" Wani uban zare ido YASEER yayi cikin k'ara ji ya furta "What...?? Aure fa..??" Jinjina masa kai yayi yana d'an lumshe ido,kafin maganar YASEER ta sashi bud'e su "To kai maganar auren ne yasa ka koma haka ko mene ya faru..? Mtttsss..! Kai wollahi wani lokacin ka cika abun haushi,ni gaba d'aya ma nayi tunanin wani abune ya sameka daban shi ne kake haka,amma daga maganar aure sai yasa ka koma haka..? Malam idanma zaka tashi ne gara maka dan kasan Maimartaba ba fasawa zaiba tunda ya fad'a..Ni dai kawai abunda zan iya cewa da kai shi ne kayi hak'uri,sannan kaima kuma ya kamata ka bawa kanka hak'uri ka k'arfafi zuciyarka dan ni ina ganin wannan ba abune da zaka sashi a ranka ba har ya saka damuwa..!" "Haba broh..! Me yasa kake tunanin haka..?? Nifa na san abunda yake faruwa,kuma duk yadda zan fad'a maka yanzun babu lallai ka fahimta,amma ni sam ba wai ina son ja da umarnin maimartaba bane,kawai dai auren ne ban shirya ma yinsa yanzun ba,beside ma ni ya kamata ace na kawo yarinyar da nake so,taya za'a ce an zab'a min mata a matsayina na namiji,tanzun kenan auren dole za'a min ko me..???" "Haba mana malam kai en da ko budurwar baka da,taya zasu tsaya jiran har saika nemo wacce kake so ka kawo..?? Kawai dai yanzun kayi hak'uri ka karb'i wannan k'addarar idan Allah ya nuna mana nan gaba kaga wacce kake so shi kenan saika aureta..Amma yanzun kasan babu damar tsallake wannan maganar,hak'uri ne kawai ya kamace mu..!" Bai iya kallonsa ba ya kwantar da kansa yana jan numfashi "Shi kenan d'an uwa na aminta da shawarar ka,Allah yasa haka shine mafi alkhairi garemu baki d'aya...!" Amsawa YASEER yayi yana sake kallon YAZEED en fuskarsa cike da damuwa da kuma tausayin halin da d'an uwan nasa yake ciki. ^^^^^ Daddad'an labarin amincewar YAZEED akan auren da maimartaba ya sanar da hajiya shi ne ya dad'a assasa farin cikinta,fuskarta da bakinta kuwa sam sun kasa b'oye yanayin farin cikin da take ciki,nan tayi ta sa musu albarka tana yiwa ahalin sa da zuri'ar sa addu'ah,shi dai Maimartaba amsawa kawai yake amma badan yana jin ya amince da wannan had'in auren har cikin zuciyarsa ba,ko da suka gama maganar maimartaba ya fito daga gefen ta ya koma cikin gida gefensa,a nan ya tarar da Fulani zaune ita da Inno sai labari Inno'n take bata tana murmusaa,shigowar maimartaba yasa inno yiwa Fulani sallamarta kuma kai gaisuwa ga maimartaba sannan ta fita,sai lokacin Maimartaba yayi mata bayanin abunda yake faruwa,gareta itama Fulani har a ranta bata so hakan ba,sai dai babu yadda za'ayi ta iya nuwa Maimartaba k'in amincewarta ba dan komai ba sai dan kasancewar ta uwa mace,haka kuma bata son tayi magana dan yin maganarta zaisa a gano rauninta ta wannan gefen,addu'ah kawai tayi da fatan sanyawar alkhairi kana ta ja bakinta daga haka ta tsuke bata sake cewa komai akan lamarin ba. B'angaren hajiya ko bayan da Maimartaba ya bar gefen ta murna ta dasa yi a gurin harda rawa saboda burinta ya cika akan wannan maganar,takanas ta aika a kira mata YAZEED duk don ta sake tabbatar masa da maganar ba wani dogon lokaci za'a d'auka ba,shi kuwa YAZEED lokacin da yaji sak'on na hajiya tun kafin bawan data aiko ya gama fad'ar sak'on ya dakatar da shi sannan ya bashi sak'on yaje yace mata baya jin dad'i,sanda ya koma gurin hajiya ya sanar mata YAZEED en baya jin dad'i nan ta tashi hankalinta ba tare da b'ata lokaci ba ta kama hanyar gefen nasu,tun kafin ta kai ga k'arasowa YASEER ya hangota ta tsakiyar curtains en parlour'n a lokacin ya mik'e kenan zai bar wajen,wata mahaukaciyar dariya ya saki tun daya hangota tana tahowa,saurin kallonsa YAZEED yayi fuska a tsuke yana fad'in "Malam lafiya zaka sani gaba kana dariya..??" Yana dariya ya nuna masa window yana sake tuntsurewa da sabuwar dariya,ba tare daya kalli abunda yake nuna masa ba ya zabga masa harara kana yaci gaba da abunda yake,dai² bakin k'ofar shigowa apartment en nasu muryar hajiya tayi masa tsinke a kunnensa,wata irin zabura yayi cike da diriricewa,ba tare daya san abun yi ba ya felle k'afa yayi bedroom,dariya sosai YASEER ya tsaya yi dai² lokacin saiga hajiya ta kunno kai cikin parlour'n,da YASEER ta fara cin karo a parlour sai b'ab'aka dariya yake,wani kallo ta jefe shi da shi cikin jin haushi tana fad'in "Ja'iri..! Ina d'an albarka nan yake..??" Juyowa yayi ya kalleta cikin waskewa da dariyar da yake ya ce "Hajajju tamu..Allah ya bar mana ke..!" "Kai rabani da wannan zancen naka,ni fad'a min inda yake,naji ance baya jin dad'i ko..??" "Ehh! Hajiya ai yana bedroom a kwance.." Dafe k'irji hajiya tayi cikin yanayin jimami tayi hanyar d'akin tana cewa "Ni Ma'u yanzun har jikin nasa ya kai ya kwanta amma saboda iya shege irin naka ka kasa sanarwa,wannan wane irin hali ne ka kwaso..??" "Hajiya kemafa bakya so ace baki da lafiya,ko bama haka ba idan mutum yace baya jin dad'i yanzun saiki hau fad'an ai raki ne irin namu da ririta ciwo yasa bama iya daurewa.." "Kai dallah barni ni da wannan shegen surutun naka,muje ni ka rakani na gano jikin nasa tukun.." Sanda tayi maganar tuni har ta dumfari hanyar d'akin da YAZEED en yake,a baya YASEER ya biyota yana tafe yana tsalle da fatan Allah sa YAZEED en ba'a zaune yake ba,suna shigowa kuwa ta bayan hajiya ya shiga lek'en inda zai gano YAZEED en,can daga saman bed ya hango shi ya k'udundune cikin blanket,a kusa da shi hajiya ta zauna tana ta surutu da nuna jimaminta akan rashin lafiyar tasa,duk abunda take shi kuwa duk yana jinta sai dai yak'i ya nuna mata yana jin nata,ta jima zaune banda son taga ya tashi babu abunda take,ga YAZEED kuwa tunda yaji hajiya tazo gurinsa yasan da walakin dan irin neman da take masa ma kad'ai ya isa ya bayyana hakan,dan haka akan ya zauna ya saurari maganganunta ya gwammace yayi ta zama a cikin bargon duk kuwa da tsananin zafin da yake addabarsa,gumi ne kawai yake faman keto masa saboda tsananin zafi,sai dai yak'i yarda ya fito badan komai ba sai don baya son wata magana ta had'a su dan yasan muddin ya fito ta ganshi zata shaida lafiyarsa lau,k'arya kawai ya shirya mata.Har hajiya ta k'araci zamanta ta mik'e ta tafi bai fito ba,YASEER kuwa tunda suka shigo d'akin yana ankare da yadda YAZEED yake ta faman mutsu²n zafin daya addabeshi,dariya yake ta son yi amma ganin hajiya sam ya hana shi yi dan yasan matuk'ar yayi dariya yanzun zata iya fahimtar abunda yake faruwa,haka dai ta gama zamanta ta tafi,har YASEER ya raka hajiya ya dawo YAZEED bai iya fitowa ba,sai daya shigo bedroom en ya tarar da shi kwance ya janye bargon yana shek'ewa da dariya "Haba malam ai ya kamata ka fito ka sha iska haka nan ko kada zafi ya maka illah..?" Lek'en hanya ya fara yi kafin ya kalli YASEER yana zuba masa harara "Dallah malam so kake sai ta dawo ta tarar dani a haka..?? Ka mayar da shi yadda ka gani idan ba so kake ta gano ni ba..!" "Kai dallah to ta tafi..matsora ci kawai,ai daka san ka zauna ta tarar da kai kawai a haka saika san abun fad'a.." Gumin da yake zirarowa jikinsa yasa shi kallon kansa yana sakin tsaki mai k'arfi,dariya YASEER ya sake tuntsurewa da ita yana fad'in "Kai mutumin nan ka iya pretending fa,irin wannan k'irk'irar jinya haka ta lokaci guda..!" Hararasa yayi ba tare daya bashi amsaba ya mik'e yabar wajen yana nufar bathroom abunsa. ^^^^^ Tunda hajiya ta sanar da Adda nasarar da suka samu ta amincewar maimartaba da YAZEED akan auren,nan itama kanta Adda'n tayi ta farin ciki,lokacin da suka gama waya da hajiya kuwa nan take ta shiga rafkawa Aisha kira,da saurinta ta sauko daga sama dan jin yadda Adda ke kiranta,kai daji kasan bana lafiya bane,da zuwanta tun kafin ta kaiga yin maganna Adda ta rungumeta tana jijjigata tamkar mai rarrashi "Y'an nan Allah yayi miki albarka,Allah yasa auren nan naku yayi albarka,ubangiji ya azurtaku da samun zuri'a ta gari.." Saurin d'agowa tayi ta kalli fuskar Adda tana tsuke fuska "Dawa zan samu zuri'ar..?? Nifa Adda ba haihuwa zan shiga gidan yi ba..!" Tsawa Ladidi tayi saurin yi mata cikin k'araji ta furta "Ke Aisha kin san kuwa abunda bakinki yake fad'a,ke sha²r ina ce da zaki fad'i haka,duk wanda yayi aure ai gurinsa ya haifa ya Yar,amma saboda rashin hankali irin naku na y'ay'an yau har wani cewa kike baki shirya haihuwa ba saboda rashin tunani.." Saurin runtse ido tayi cikin rashin jin dad'in abunda tayi a gaban Adda ta furta "Ohh! Sorry mom sub'utar baki nefa..!" Kallon rashin fahimta Adda ta musu duka sai dai bata kai ga yin magana ba saboda yadda taga ladidi ta rufe ido tana yiwa Aishar fad'a,tsaki ladidi tayi wanda yaja hankalin Aisha kanta,suna had'a ido ta mata inkiya akan ta kula ko dan gaba ta san a inda ya kamata ta dunga sakin baki tana magana,jinjina kai tayi ba tare data yi magana ba ta kalli Adda cikin kissa ta furta "Ameen Adda ta wata rana kema ki d'auki yara kina jin dad'i da alfaharin kin d'auki y'ay'an

Chapter 18 of 63