ensemble nata ne suke take mata baya d'auke da kayayyaki na gani a fad'a,nan suka shiga jerasu a gurin har suka kammala suka koma gefe,da hannunta ta d'auko wani robe mai masifar kyau da d'aukan hankali saboda irin adon dake jikinta ya wuce a misalta ta sanyawa jeeddah da kanta ke k'asa tana ci gaba da share hawaye,haka ta sa mata kayayyakin ado da dama irin na gidan sarauta sannan Ummi da hajiya suka bada umarnin a tafi da ita cikin hadiman fulanine aka ware wasu sai na nan gefen Ummi'n suma amintattu suka mata rakiya zuwa apartment d'in da zasu zauna.Har suka isa k'ofar apartment d'in suka shiga zuciyar jeeddah bata daina taraddadi da fargabar da take jinta a ciki ba tun bayan d'aurin auren,ita dai tasan labarin aurenta amma har yanzun bata san waye mijin nata ba,haka nan tafiyar nan da suke duk da itan tana bisa doki ne ta soma fahimtar wani abu dan a lokacin ta gama fahimtar ba wani guri aka fitar da ita ba kamar yadda tayi tunani tun farko,haka suka barta bayan sun tabbatar komai lafiya babu wani matsala,aka barta daga ita sai halinta.
^^^^^
A b'angaren Yarima YAZEED kuwa tun bayan da suka d'an samu nutsuwa ta dawo musu nan suka sake shiryawa cikin wani shigan na alfarma suka fice a gidan,basu suka samu damar dawowa ba sai wajen 9:30pm lokacin tuni y'an rakiyar amarya har sun gama watsewa a apartment d'in,suna zuwa dai² k'ofa Yarima ya wani shiga had'e fuska na babu gaira babu dalili,d'an satan kallonsa YASEER yayi yagan ya tamke fuska ai take ya tuntsire masa da dariyar rainin wayo,saurin kallonsa Yarima yayi yana d'age masa one eyebrow alamun "what" dinnan,saurin girgiza kai YASEER yayi yana masa alamun babu komai yana kuma k'unshe dariyar dake neman sake taho masa,sosai ya fusata Yarima da dama k'iris yake jira a lokacin,kayan hannun YASEER ya fauce sannan ya kalleshi dai² yana tsayawa tsakiyar hanya
"Heyy! Man sai ka wuce ai na gode da rakiyan..??"
Kallonsa YASEER yayi yana dai²ta kansa
"What do u mean...??"
Ya tambaye shi dan yaga ya sha mur kamar ba shi ba,ba tare daya kalleshi ba ya furta
"Ohoo! Nace dai ka wuce kawai ka juya mana.."
"O'oo! Man ai ba sai kayi min rowar ganinta ba,muje kawai kasan bazan iya barinka kaje mata kai d'aya ba babu d'an rakiya."
K'wafa Yarima ya saki sannan ya juya abunsa ya wuce ciki yana ce masa
"Mu tashi lafiya..!"
Daga haka ya rufe k'ofar apartment d'in gaba d'aya,dariya sosai YASEER yayi dan dama tsokana ne yasa shi fad'in duk abunda ya fad'a,koda yaga hakan ya faru nan shima ya juya ya bar gurin yana sake bin d'an uwan nasa da addu'o'in fatan alkhairi da samun kariya daga Ubangiji akan dukkan wata matsala da zai same shi.
Lokacin da Yarima ya juya ya soma tafiya bayan ya tabbatar ya kulle ko ina na apartment d'in,zuciyarsa ce ta fara wani harbawa cike da wani irin yanayi ya nufi hanyan bedroom d'insa,a saman resting chair ya fara zauna bayan shigansa d'akin yana y'an tunanin da ba za'a rasaba kafin daga bisani ya mike ya nufi bathroom,ya d'an jima a ciki sannan ya fito jikinsa sanye gda bathrobe white colour,bai tsaya wani shafa mayuka ba kawai ya d'auka pyjamas d'in daya fitar ma kansa ya saka,a hankali cikin rashin kuzari sosai ya nufi gaban mirror,curly hair nasa ya fara gyarawa sannan ya d'an murzawa jikinsa turaren CC (cotton club) had'e da oud wood,yana gamawa ya nufi royal bed d'insa cike da gajiya da son ya hutama ransa ya kwanta abunsa yaba lumshe idanunsa masu haske,a hakan yayi addu'o'in kwanciya bacci,can zuwa wani d'an wucewar lokaci da har bacci ya soma fizgarsa,ya tashi ya zauna kamar wanda aka tasa,a hankali ya fara sauke k'afafunsa a k'asa sannan ya mik'e bayan ya zirama k'afarfunsa simple slipper ya kama hanyar fita a bedroom d'in.
Jeeddah kam tun bayan da y'an rakiyarta suka baje taji fargaba ta cika mata zuciya jinta take wani iri duk ta takura a bedroom d'inta,musamman ma da bata ji alamun kowa ba,ta jima zaune shiru kafin taji alamun shigowar mutum sai a nan ne ta d'an samu damar motsowa daga inda take,har ta iya cire robe da Umma'n YAZEED tasa mata,a hankali kuma ta shiga rage kayan jikinta sannan ta shige bathroom zuciyarta na raya mata kan cewa babu wanda zai shigo d'akin nata,kasancewar a d'an zaman da tayi a gefen Ummi kafin bikin yasa ta saba da zaman d'aki da kad'aici shi yasa duk taji bata wani damu ba koda bata ga angon nata ba,sanda ta fito a wankan kuwa kai tsaye luggage's da aka ce mata komai nata na ciki ta shiga dubawa,wasu night wears ta fitar masu kyau ma kanta,sai dai bata kai ga sawan ba,tana tsaye daga ita sai wani bra set na floral lace white color a gaban bed d'in da d'an k'aramin towel a hannunta tana sake tsane ruwan jikinta coz a shirinta time d'in tana gamawa ta shafa had'in mayukanta na gurin Inno,sai dai ko kafin ta kai ga wannan attempts d'in tajiyo takun tafiya,bata ko kai ga gama tunanin da take ba taji an kama handle d'in k'ofan ana niyyan shigowa..............
*D'in...d'in.......d'in...!*
*Auu..! Babu ruwana bari nayi shiru...🤭🤭Idan har kuma kuna son naci gaba to naga ak'alla 100 comments idan ba haka ba kuma Aradun Allah saina huta zan dawo.*🏃🏻♀🚴🏻♀
*Drop ur comments @ 08165726609.*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 18.*
^^^^^^^^
*#Becoming Perfectly*
Da matsanancin fargaba a tattare da ita ta waiwayo cike da son ganin waye,har lokacin tana a yadda take ba tare da zuciyarta ta bata shawaran ta d'aura ko da mini towel dake hannunta ba,duk da kasancewarsa k'arami amma bazai gaza rufawa jikinta asiri ba,haka nan a lokacin hankalinta ko kad'an bai kai ga riganta dake ajiye ko hijab da zata yi sallah ba bare tayi bear na d'aya daga ciki.
A b'angaren Yarima kuwa bayan fitowarsa a bedroom d'insa haka nan yaji zuciyar sa na raya masa yaje ya duba halin da y'ar mutane ke ciki,coz wannan yana d'aya daga cikin dalilin da yasa har ya fara bacci ya tashi,a dalilin tunawa da amanar da aka dank'a masa,tabbas yayi alk'awarin rik'ewa da amana why kuma tun yanzun ba'a je ko inaba zaiyi k'ok'arin canja ra'ayi nd yayi yunk'urin scattering nata,hakan yasa ko da ya fito kai tsaye babu tunanin komai a ransa ko kuma zai same ta bata yi barci ba har lokacin ya nufi d'akin kansa tsaye,dai² ya kama handle d'in k'ofar yana murzawa yaji k'ofar a bud'e,kansa tsaye ya tura had'e da bud'ewa zai shiga,dai² lokacin da hakan ke faruwa ita kuma jeeddah na tsaye ta kafe k'ofar da ido tana jiran ganin abunda zai wakana.Yarima YAZEED ne ya bayyana a gabanta sanye cikin pyjamas nasa masu matuk'ar kyau da suka sake fitar da sirrin kyaunsa,nan take jikinta ya d'auki wani irin kyarma dan yadda taga fuskarsa babu alamun wasa nd bata san mene actual abunda ya kawo shi gareta ba,idanunsa ya sauke a kanta dai² lokacin da ya gama bayyana nan ya isketa tsaye kamar status,tana sanye cikin bra set na floral lace daya kasance white color sun mata d'as yayin da komai yake zaune a muhallinsa kayan ba k'aramin amsar jikinta suka yiba,daga inda yake tsaye tsaf yake iya watching everything a part of her torso,in seconds ya k'are ma halittan jikinta kallo,after ya maida idanunsa kan fuskarta yana fatan ace mamallakin wannan jikin ta kasance mafi kyau sama da yadda halittar jikinta ta kasance,ai idanunsa na sauka kan fuskarta yaji wani irin yanayi biyu at once ya shige shi,first of it tsananin fad'uwar gaba second dismayed na ganinta a lokacin da zuciyarsa ta riga ta fidda tsammanin sake samunta a rayuwa,ya jima yana kallonta mai tattare da wani irin emotions,irin kallon da take masa ne yasa shi saurin saita nutsuwarsa dan yadda ganinta kad'ai yasa shi yaso rikicewa a gabanta,ita kanta sai data so fahimtar wani abu a tare da shi sai dai bai kai ga bata wannan damar ba yayi saurin saita nutsuwarsa coz yasan matuk'ar hakan ya faru za ta d'auke shi wani clown,nd he knows duk ranar da hakan ya kasance yasan zata maida shi contemptible,idanunsa ya d'anyi arouse daga gareta yayin da zuciyarsa ke tambayarsa
"What did she do in his own domicile..??"
Sake kallon fuskarta yayi zuciyarsa cike da son tabbatar masa itance da gaske ko kuwa idanunsa ne suke yaudararsa kamar yadda a lokacin baya suka kasance suna tsokanarsa..?? A hankali ya d'an kauda kansa gefe cikin wani salo yana jin wani irin shauk'i har k'asan zuciyarsa daya tabbatar itane a kusa da shi,a hankali ya d'an runtse ido yana jan numfashi da kyar,can daga k'asan zuciyar sa kuwa godiya yake yiwa Allah daya sa ya kasance cikin mutane masu sa'a da rabo,tabbas Ubangiji yana k'aunarsa tunda har gashi a dai² lokacin da wasu ke kyamar had'a alak'a da shi muradin zuciyarsa ta bayyanar masa,wani b'oyayyan killer smirk ya saki da babu wanda zai iya fahimtar hakan a tare da shi,cikin dabara yaci gaba da kallonta ta k'asan eyelashes nasa yana ci gaba da addu'ah,jin zuciyarsa na fizgarsa zuwa gareta yasashi kallonta sosai,har lokacin tana a yadda take bata motsa ko nan da can ba,shima d'in yana inda yake tun farkon shigowarsa sai dai yanayin daya shigo dana yanzun bayan ya tabbatar ma kansa itace matar da iyayensa suka zab'a masa da bambanci,kallonta kad'ai a wannan lokacin ba k'aramin sake sa zuciyarsa cikin shauk'i da begen su dawwama a haka yake ba,,,,tuna abunda ya kawo shi da dalilin zuwansa ne yasa shi saurin janye idanunsa a kanta yana lumshe su,cikin wani irin voice mai dad'in sauraro ya d'anyi gyaran murya yana cewa
"Ehemn! U supposed to cover ur body..!"
Sai lokacin da yayi magana ita kanta ta samu daman dawowa cikin nutsuwarta,da sauri ta d'an sauke kai k'asa tana duba jikinta taga abunda yake magana akai,sai lokacin itama ta tuna da halin da take ciki bayan da tayi arba da y'an kayan dake jikinta wanda suka kasance marabarsu da babu kad'an kasancewar su duka na wani irin lace mai bayyana surar jiki,nan take jikinta ya ci gaba da wani irin mahaukacin prom saboda tsananin kunyar ganinta a haka da tayi,ta k'asan ido yaci gaba da monitoring nata da duk wani motsinta,ga mamakinsa gani yayi har lokacin ta kasa tabuk'a komai sai tsayuwan da taci gaba idanunta a kulle ta kasa ko da motsa finger nata bare ta iya sarrafa jikinta,d'agowa yayi a hankali yana zuba mata idanunsa masu saurin sa mutum ya distraught yayin da yake kallonsa,ganin yanayin da take ciki yasa shi d'an lumshe ido yana gripping lower lip nasa,a hankali ya tsotse shi kafin ya fara nufar inda take,unknowingly ta ganshi a gabanta fuskarsa cikin wani yanayin da yasa ta kasa apprehending nasa bare ta gano ma'anar abunda yake shirin yi,daf da bed d'inta ya tsaya yana sauke idanunsa bisa gown d'in data fitar ta ajiye,hannusa yasa ya d'auko ya shiga warwareta,ita kuma idanunta a kansa tana kallonsa cikin firgici,shi kam bai ko kalleta ba ya ci gaba da abunda yake yi,cikin nutsuwa yake komai har ya gama saka mata ya kamo threads dake gefen rigan da niyyan d'aure mata su ta baya,tsantsar mamakinsa ne yasa Jeeddah kasa motsi a gurin,d'an jimm yayi yana jiran yaga ko zata juya amma sai yaga tak'i motsawa,a hankali ya d'ago idanunsa ya kalleta,karaf idanunsu suka yi merging,nan ya samu damar sending sak'onninsa through his eyes,yayin da ita kuma take kallonsa da nata idanun masu cike da tsoron sa,janyota yayi kad'an wanda hakan yayi sanadiyyar da jikinsu ya gogi juna,a tare suka saki ajiyar zuciya,ba tare daya kula da hakan ba duk da yadda dukansu sun tsinci kawunansu cikin wani hali mai wuyar fassara,ya shiga mata bundling threads d'in,duk yadda yaso ya kauce a wannan karon sai daya rikice musamman da k'irjinta ya gogi jikinsa,a hankali ya saketa sannan ya d'an matsa kad'an yana sake dubanta k'asa².
Juyawa tayi da sauri kamar wacce aka tilasta,ai kuwa tana yin hakan idanunta suka sauka akan k'aton wacce ke tsaye kamar ita komai nasu babu bambanci,wani razanannen ihu ta saka tana k'ank'ame jikinta guri guda,har ya juya zai fita a lokacin ihunta yasa shi saurin waiwayowa yana nufar inda take,ta bayanta ya d'ora hannunsa guda yana tab'a ta,da sauri ta juya jikinta na karkarwa,kallonta yake kamar wani dolo har sanda ya fahimci akwai abunda ya tsoratar da ita
"Mene ne kuma..??"
Yayi tambayar ba tare da ya shiryawa yin ba,girgiza kai kawai take ba tare da jikinta ya koma dai² ba,d'akin ya fara dubawa ko zaiga abunda take wa ihu amma baiga komai ba,dawowa yayi kusa da ita yana k'are mata kallo
"Mene ne ya faru..?? Fad'a min.."
Sam ta kasa magana sai ajiyan zuciya da take saki da sauri² kamar tayi tseren gudu,fahimtar baza tayi magana ba yasa shi matsawa sosai ya cike sauran gap dake tsakaninsu yana had'e jikinsa da nata,bayanta yake caressing har ya samu ta d'an fara dawoma nutsuwarta,a hanakali ya fara mata rad'a a kunne yana tambayarta abunda yasa ta tsorata,like she were declared him take kallonsa sai kuma tayi shiru ta fasa,magana yake son sake yi mata amma jinsa a jikinta ya saukar masa da kasala har yaji bazai iya koda bud'e baki bama,haka suka ci gaba da tsaiwa har na wani lokaci,sai daya shafe tsawon mintuna da bai san adadinsu ba sannan ya d'an janye mataccen jikinsa k'asa² ya furta
"Ki shirya ina dawowa..!"
Da haka ya juya ya fita a bedroom d'in,bai wani jima sosai ba ya dawo hannunsa d'auke da tray,yadda ya barta haka ya dawo ya sameta har lokacin bata motsa ba,mamaki lamarinta ya soma bashi a hankali ya d'an yamutse fuska yana ajiye tray'n saman bedside drawer,d'an waiwayawa tayi taga ina ya nufa dan a mugun tsorace take,nan ta hangoshi kusa da shi shima d'in
"Hey...! Ka matsa nan kada su janye ka..!"
Da ihu tayi maganar wanda yasa shi saurin d'agowa yana kallonta,jikinta sai ci gaba da rawa yake,shi kam sam ya kasa fahimtar abunda take nufi,fuska ya sake squeeze kafin ya furta
"What..??"
"Na ce ka matsa a kusa da nan zasu tafi da kai..!"
Tayi furucin kamar wacce take magana da deafest person while her eyes closed
"Whom...??"
"Ga sunan a bayanka..Ka matsa please..!"
D'an juyawa yayi yana duba bayan san kamar yadda tace suna bayansa,sai dai iya dubarsa shi kam baiga komai ba,har yayi niyyan tambaya idanunsa suka sauka kan mirror daya bayyana a ciki sai dai baiyi tsammanin shi take nufi ba
"At where..Kika gan wani a nan..??"
Idanunta a runtse saboda yadda tak'i jinin ta kalli gurin
"Suna nanfa kusa da kai.."
Lokacin hawaye kam tuni har sun fara sako mata,shikam ya kasa fahimtar ta buh the way yanda take magana yasan akwai wani abu da take nufi,kusa da ita ya dawo yana dafa shoulders d'inta
"Calm down..Fad'a min me kike cewa..!"
Jan zuciya tayi da ya nuna tabbas ko mene ne ba k'aramin tsoro ya bata ba,cikin firgita ta d'aga idanunta masu cike da hawaye tana kallonsa
"To ba sune suka zo tafiya da kai ba.."
Mamakinta yake shi kam har lokacin sai kace wata mai shafar jinnu tana ta magana akan abu amma shi bai gani ba,daurewa yayi yaci gaba da tambayar ta
"Su waye ne kike maganarsu..??"
"Wani mutum ne ta cikin can..kuma har da..Umm..wata ma a tsaye tana kallonka..!"
One eyebrow ya d'age
"Da gaske kin gan wasu a nan..??"
Ya tambaya cikin son ya tabbatar da zaton sa,kai ta kad'a masa,shima kan ya jinjina kafin ya watso mata wata tambayar
"Ehmm! Wane irin dress ne a jikinsu duka..??"
Sai data sake jan ajiyan zuciya kafin ta d'aga ido tana scrubbing tears d'in da suka zubo
"Ai irin kayanka ne a jikinsa."
"Sure..??"
Ya tambaya yana sake d'age mata one eyebrow,da kai ta iya amsa masa
"What about the woman standing besides..??"
Kanta ta kalla kafin ta sake kallonsa
"Irin nawa ne ta sanya..!"
Tabbas zatonsa ya zama gaskiya,to amma me hakan yake nufi..?? Shin zata ce masa bata san mirror bane ko kuwa me haka ke nufi,cikin zuciyar sa ya furta
"I will understand whether she knows or not..!"
Hannunta ya rik'o yana fad'in
"Ok..let's go ki nunamin inda kika gansu.."
Saurin fauce hannunta tayi daga rik'on da yayi mata tana ja baya cike da tsoro,waiwayowa yayi shima yana jifanta da kallon "what??"
"To nifa tsoronsu nake ji kada su tafi dani..bana sonsu..nafi son na zauna tare da Inno ta..!"
Sosai mamakin ta ya cika shi har ya saki siririn smirk
"No..! Babu inda zasu kaiki,am here for u.."
D'agowa tayi ta kalleshi,nan ya kad'a mata kansa alamun da gaske yake mata
"Ni dai a'a'a babu inda zani,bayan Inno tace duk sanda na kalli abun zasu zo su tafi dani nd bazan sake ganinsu ba.."
Dariya yake sonyi da lamarinta amma yadda take nunawa bilhak'k'i da gaske take baza ta matsa kusa da gurinba yasa ya gintse sannan ya dawo kusa da ita yana kallonta k'asa²
"No..! Let's go..I will show u something important.."
Kallonsa ta sake yi tana son concealing kanta,binta ya soma ita kuma tana ja baya dan ta fahimci inda yake son kaita,da haka har ta isa jikin d'aya daga cikin wall d'in d'akin bata sani ba,sanda ya k'araso daf da ita ta runtse ido tana had'iye wani yahun tsoro
"Mene ne..??"
Ya fad'a cikin k'asa da murya,bata iya bud'e ido ba ta furta
"Am scared..!"
"Relax baby..Am here,so there's no worries,nd I promise to always being near u.."
Kallonsa take tana nazarin kalamansa,tambayar zuciyarta ta fara
"Me yake nufi..??"
Kafin ta kaiga samun amsa tuni ya kama hannunta yana janta,kamar wani rak'umi da akala haka ta dunga binsa har suka dangana da gaban mirror'n sai dai ta kasa d'aga kai ta kalla kamar yadda yake so,chin d'inta ya d'ago a hankali yana tsaye ta bayanta,while yana kallonta ta cikin mirror'n
"Look herein..!"
Kasa d'aga ido tayi saboda tsabar tsoro,shi kuwa ba komai ke burgeshi ba daya wuce yadda yaga tana komai nata cikin nuna pediatric behavior ga d'an banzan tsoro,yayin da take magana kuwa ganinta yake kamar har da wani pampering take had'awa,sosai hakan yake sa shi shagala da kallonta
"Please..baby open it nd look herein..!"
Yadda yayi magana sosai yayi tasiri a gareta nan take ta soma bud'e idanunta a hanakali,tana kallon cikin mirror'n tsoronta ya bayyana da sauri ta kullesu k'irjinta na tsananta bugawa,saurin juyota yayi yana kallon yadda k'irjinta ke lifting,a rikice ya fara tambayarta
"What happened..?? Kina jin tsoro har yanzun..??"
Kai ta d'aga idanunta na kawo ruwan hawaye
"Sorry baby..it's unintended..Ok??"
Kai ta d'aga masa kawai
"Are u okay..??"
Ya sake tambayarta,nanma kai ta d'aga masa ba tare data san me take yi ba
"Ok..kalle ni nan..!"
Kasa d'aga ido tayi bare ta kalle shi
"Kinsan mene ne wannan d'in da kike tsoro..?? It's ur image fa ba wani abune daban ba kamar yadda kike tunani it's just a mirror.."
D'agowa tayi tana kallonsa
"How could it be my image..??"
"Zaki yarda idan na nuna miki..??"
Kai ta kad'a masa
"Ok spun nd look into the mirror.. Don't feel daring..!"
Sai data kalle shi tsaf ta gano babu wani abu da yake nufi face gaskiya sannan ta waiwaya a hankali tana kallon mirror'n cike da tsoro,matsawa yayi kusa da ita sosai yana zagaya hannayensa akan cikinta,cikin razanin abunda yake shirin yi ta d'aga ido tana kallonsa
"Kina kallo..??" Ta d'aga masa kanta
"Ok..me kika gani..??"
Abunda ta gani ta fad'a masa cikin d'an tsoro² dan har lokacin bata amince da abunda take gani ba,kansa ya d'ora gefen wuyanta da sauri ta sake bud'e ido ta cikin mudubin tana kallonsa,cikin rad'a ya furta
"Duk abuna kika gani ki sanar min..!"
Kallonsa taci gaba da yi ta ciki tana kallon sanda yayi kissing neck d'inta,da sauri ta rufe ido saboda wani bak'on yanayi daya ziyarceta tunma ba irin rik'on da yayi mata ba,haka yayi ta mata abubuwa da dama tana kallonsa har zuwa sanda ya d'aga idanunsa ya kalleta ta cikin mudubin,a kunnenta yake magana
"Me kika gani..??"
Wannan karon kasa magana tayi dan yadda take jin tsoro gami da kunyar fad'a masa abunda yayi,sake rik'eta yayi tsam cikin kunnenta yaci gaba da cewa
"It's just a mirror,,da zaki kalli kanki a ciki,duk abunda kike zai miki showing,ke kad'ai ne babu wani,it's ur shadow..!"
Bata ce komai ba sai moving head asides da take,burinta bai wuce ace ya saketa ba dan yadda take jin ya fara mata wasu irin abubuwa,ci gaba yayi mata da bayani har sanda ya tabbatar ta fahimta kuma tsoronta game da cewar idan ta kalli mudubin akwai wasu da zasu zo su tafi da ita ya ragu,sannan ya rad'a matah.
"Okay..muje muyi sallah ko..??"
Ya fad'a yana d'an sassauta rik'on da yayi mata,ba tare data amsa ba yaja ta suka bar gaban mirror'n..........
*Hummm! Tofa..Fan's kunji ita kuma JEEDDAH ta inda ta b'ullo,Fisabilillahi ace mutum ya rasa abun tsoro sai Mirror,to amma abun tambaya a nan shi ne..Shin mene dalilin Inno da yasa ta fad'a ma JEEDDAH haka ne..??? 🤔🤔 Anya babu wani abu a ranta kuwa...?? 🤔 Ko da yake muje zuwa dai zamu gano Inno da nufinta a gaba..*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 63