Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bedroom d'in sa. Lokacin da Aisha ta tabbatar ta shiga d'aki kayan jikinta ta fara ragewa sannan ta nufi toilet,ruwa ta tara a kwamin wankan sannan ta zuba turaruka masu sanyin dad'i da tasan zasu taimaka wajen rage mata rad'ad'in da zuciyarta keyi a lokacin a dalilin rashin sanin madafa da sanin takamaiman inda ya kamata ta fara dosa dan binciken mahaifanta. Kwanciya tayi cikin ruwan yayin da damuwa ke dad'a saukar mata,ta jima a wannan halin kafin ta iya yin wankan ta fito zuciya da gangar jiki duka babu dad'i.Fitowarta babu jimawa tayi shirin kwanciya sannan ta haye bed tana lumshe idanunta wanda suke cike da bacci da gajiya,haka zalika masu d'auke da tsantsar damuwa. ^^^^^ Washe gari tun da sanyin safiya bayan da Yarima ya gama shirinsa,babu wanda ya sanarwa da tafiyarsa ya fice a gidan,dan tun daya fita sallah bai bari ya dawo ba ya nufi airport,bai tsaya bin takan emirate flight ba yayi bucking flight mai zuwa abuja a safiyar,wajejen 8:00am jirginsu ya d'aga sai birnin tarayya,gidan da aka mallaka musu ya nufa,da zuwansa kuwa ya baje a parlor take wani baccin yayi gaba da shi.Sai daya shafe ak'alla awanni biyu yana baccin gajiya kafin ya farka,fuskarnan a had'e kamar ba ta sabon ango ba,haka yaci gaba da gudanar da al'amuransa ba tare da wani damuwa ba ko tunanin neman wani cikin ahalinsa ciki kuwa harda aminin nasa wato YASEER. Can kuwa a Kano lokacin da gari ya gama wayewa,Sajida ta fito daga bedroom d'inta ciki kwalliya,lokacin data nufo cikin parlor da niyyar zama sai akayi knocking,fasawa tayi sannan ta nufi bakin k'ofa da niyyar ganin ko waye,bud'e k'ofar keda wuya tayi arba da matashiyar sanye cikin bak'ak'en kaya hatta kuwa da fuskarta,tsayyawa tayi kawai tana nazarinta har na wucewar wasu sa'o'i kafin cikin isa ta furta "Daga ina baiwar Allah..??" Itanma cikin wani yanayi mai kama dana nuna halin ko in kula da halin da mai maganar yake ta furta "Sak'o ne na kawo daga gurin Fulani.." Kallonta sajida ta sake yi sosai kafin ta matsa ta bata hanya tana sake binta da kallon mamaki,wucewa matashiyar tayi zuwa ciki ta nufi dinning area ta ajiye kayan dake hannunta,sai data ajiye basket d'in sannan ta kama hanyar fita ba tare da tayi wata maganar ba,har ta kusa da k'ofar fita sajida ta d'an d'aga muryarta tana fad'in "Ki mik'a min gaisuwa gurin Umma'n kafin mu shigo.." 'Dan waiwayowa tayi ta kalleta ta tsakanin mayafin daya rufe mata fuska kafin ta girgiza mata kai kawai sannan tasa kai ta fice daga apartment d'in ba tare data sake furta komai ba,fuskar sajida kuwa da mamakin hali irin da kuma k'arfin hali irin na wannan khadima ta rakata da ido. A gefen su YASEER kuwa sanda Fulani ta bada umarnin kai musu breakfast kamar yadda tayi gasu YAZEED,sanda sak'on ya riske su,ko bayan da suka gama break d'in ya d'auki lokaci yana neman lines d'in Yarima sai dai amsa d'aya ya samu shi ne wayoyin a kashe suke,hak'ura yayi da kiransa ya kammala shirinsa sannan ya fita da niyyan zuwa ya duba ko lafiya YAZEED d'in yake zuwa wannan lokacin,tunda ya riga ya san abunda ya faru a daren daya gabata,sanda ya iso apartment d'in ya iske shi a kulle,da har yayi niyyan juyawa kuma ko me ya tuna ya fasa sannan yayi nocking,Sajida da tunda hadimar ta shigo ta fita take zaune tana zaman jiran ganin fitowar Yarima ta mik'e tana nufar k'ofa da niyyan bud'ewa,da YASEER tayi arba,ko da ganin haka sai ta saki fuska tana bashi hanya ya wuce,cikin girmamawa ta gaishe shi,yana tafiya yana amsawa har ya k'araso cikin tsakiyar parlour'n,tambayanta Yarima ya soma nan ta shiga bashi amsa "Ina tunanin ko yana bacci ne dan ban ga fitowarsa ba har yanzun.." Ido YASEER ya d'an bud'e yana kallonta kafin ya furta "Wane irin bacci ne wannan har to 11:00am ace mutum bai tashi ba.." Yana maganar yana kallon corridor d'in da zai sada shi da bedroom d'in "Bari na duba na gani ko ya tashi.." Ta fad'a tana bin hanyar bedroom d'insa,sai dai koda ta shiga bedroom d'in bata tarar da komai ba face k'amshin perfume d'insa,dan haka ko data tabbatar baya nan sai kawai ta fito jiki a sanyaye babu laka ta sanarwa da YASEER halin da ake ciki,mamakinsa sosai ya bayyana dan yadda yake ganin ina ne zai nufa a irin wannan lokacin,wani tunani ne ya fad'o masa nan take ya jinjina kai sannan ya mata sallama da niyyan fita,zuciyarsa da tunanin ina d'an uwan nasa ya nufa da wannan safiyar da har ya fice ba tare da wacce suka kwana guri guda ta sani ba........ *Kuyi hak'uri da wannan masoya,ni kaina ban tab'a tunanin za'a kawo tsawon wannan lokacin ba tare da kun jini ba,sai dai matsalar da muka samu tasa aka samu wannan jinkirin,amma ku k'ara hak'uri in sha Allah matsalar ta kusa zuwa k'arshe da izinin mai duka.* *Don't forgets to follow me on wattpad@jeeddahmu898* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.😉* 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ *Ban san iya adadin farin cikin daya kamata nayi ba,saboda soyayyarku a gareni ta wuce a misalta,fatana har kullum baya wuce addu'ar Ubangiji ya barmin ku har k'arshen numfashi,#Ahabbakumullahul-laziiy ahbabtaniy lahu.* ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 2.* ^^^^^^^^ Duk inda YASEER yake tunanin samun Yarima YAZEED ya duba kuma ya bincika amma ko mai kama da shi bai samu ba,haka duk wanda yake ganin idan ya tambaya game da labarin Yariman sai daya tambaya amma kowa cewa yake masa bai ganshi ba,hankalinsa bai gama tashi ba sai daya dangana da gefen Fulani,ko daya je d'inma bai iya fitowa fili ya tambayi Yariman ba,dan yadda yake jin nauyin yin haka,sanda yayi iya yinsa da dubawa duka dan ya gano ahi,amma hakan ya faskara,dan ko inuwarsa bai hanga ba bare kuma shi d'in kansa,ficewa yayi niyyan yi dan yadda yake jin hankalinsa na sake tashi a duk lokacin da yaje inda yake tunanin samunsa bai ganshinba,har ya dangana da k'ofar fita muryar Fulani ta tarar da shi inda take jifansa da tambayar "YASEER ina ka baro d'an uwanka ne..Naga ka shigo kai d'aya.." Shiru yayi yana sauke b'oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya waiwayo fuskarsa d'auke da murmushin yak'e "Amm! Ummah Fulani ai ina tunanin ko ya rugani shigowa ne shi yasa ban tuntub'e shi ba da zan shigo.." "A'a'a.! Ai kam bai shigo ba,amma wata k'ila ko wani uzurin ya rik'e shi,ina tunanin ko shi yasama bai nemekan ba kai d'inma.." "Ehh! Haka ne Ummah,amma barin duba shi naga ko lafiya.." Murmushi Fulani tayi irin nasu na manya kafin ta furta "Lafiya ai ita take b'oye mutum.." Murmushin shima yayi na k'arfin hali sannan ya mata sallama ya fice zuciyarsa cike da zullumin inda YAZEED ya shige da wannan safiyar.Yana fitowa apartment d'insu ya koma na da,yana shiga kuwa yaci gaba da k'ok'arin kiran line d'insa cikin sa'a yana gwadawa a wannan karon wayan ya shiga,jikin YASEER har rawa yake dan yadda yake fatan yaji Yariman ya d'auka yana jin an amsa tun kafin Yariman ya fara magana tuni har ya rigashi "Broah..!! Where have u been..?? Kasan kuwa yadda kasa hankalina ya tashi,tun safe sai nemanka nake amma na rasaka..Kana ina ka fad'a min.." Wani mugun smacking ya saki ba tare da yayi magana ba "Please mana broah tell me where are u,i will came and take u up right now.." Still murmushin ya sake saki cikin wani isa ya furta "Am at Abuja,can u....??" Kuma sai ya sake sakin murmushi dan yasan babu yadda za'ayi ace yanzun YASEER ya biyo shi har Abuja,cike da mamakinsa ya shiga maimaita abunda yarima ya fad'a a ransa,a fiki kuwa sai cewa yayi "Kace kana ina..??" "Ina kunnenka suke sanda na fad'a maka..?" "Pardon..Rehearses please.." Yadda yaji muryan YASEER yasan yana cikin wani yanayi da jin abunda ya fad'a d'in,nd he's eager to hear the reality of what he say's,a hankali ya maimaita masa,wani uban gumi ne ya fara yankowa YASEER tun yana tsaye har sai da ya nemi guri ya zauna dan yadda hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi,jinjina kai kawai ya iya yi had'e fa furucin "Good for u.." Daga haka bai k'ara cewa da shi komai ba ya katse wayan yayi cilli da shi gefe yana furzar da wani zazzafar iska daga bakinsa mai cike da tsantsar tashin hankali.Can kuwa a gefen Yarima koda yaji YASEER ya katse kiran tsaki yaja mai sauti,har ya ajiye wayan gefe yana shirin shiga bathroom ya watsa ruwa yaji kalaman YASEER na dawo masa,yadda yayi furucin tabbas yasan baya cikin nutsuwa,kuma duk damuwar da yake ciki a yanzun yasan ba'a dalilin kowa ya same shiba sai akan sa,a fili ya furta "Bai kamata nayi maka haka ba..!" Saurin dawowa yayi ya d'auki wayan yabi line YASEER d'in,wayan ya shiga dan sai ring ma yake,amma sam ank'i d'auka,sai da ya kirashi yafi a k'irga kafin yayi ta maza ya d'auka,cike da masifa YASEER ya rufe shi da fad'a "Wato saboda kasan babu wanda zai tambayeni kana ina na fad'a gaskiya ne yasa kayi min haka ba,ka kama hanya kayi tafiyarka saboda ni kasani a damuwa..?? To wollahi kaji na rantse ko dai ka kamo hanya tun wuri ka dawo ko kuma zanje na samu maimartaba na sanar da shi halin da ake ciki.." Ajiyan zuciya ya saki cikin sanyin murya ya katse YASEER d'in daga maganar da yake yi "Please broah..kada kayi min haka,ya kamata ka fara tuntub'ana kaji dalilin tafiya na bawai ka faramin masifa ba.." "God forbid..Ni na tsaya tambayanka,bayan nafi kowa sanin waye kai sannan kace wai na saurareka,naji me...?? Me zaka fad'a min da ban sanshi ba a cikin halinka..??" "For sure broah matuk'ar ka saurareni akan abunda zan fad'a na tabbata zaka fahimci dalilin da yasa nayi hakan.." "Kaga malam ni babu wani surutunka da zaisa na saurara wannan dad'in bakin naka,magana d'aya ne kuma mun gama yinsa saboda haka kawai ka biyo private jet ka dawo gida fak'at,amma idan ba haka ba,kasan Allah saina bayyana inda kake kowa ma ya sani.." Cikin masifa shima Yariman ya hayayyak'o masa,dan jin yadda yake bashi command "Bazan dawo ba d'in idan kaga dama kayi shela acikin gidan kowa ya sani ka ji ba kada ka fasa.." "Haka kace ba..??" "Ehh! Na fad'a,mutum sai shegen son bada umarni wa kafi ne..? Da ko wane lokaci ka dunga nuna sai an bika,ina nuna maka ka saurareni kaji matsalana kai kuma kana kawomin wani zancen banza,idan kaga dama ka iya tsayawa muyi magana idan kuma baka ganshi ba kaje ka sanar musu bana nan na tafi na bar Matar da suka auramin a dalilin bazan iya aikata mata komai ba..!" Wani irin kunya ne ya rufe YASEER duk da ba shi yayi maganar ba,amma yafi mai maganar jin nauyin zancen,yadda Yarima yaji yayi shiru ne yasa shi fad'in "Tunda baka da abun fad'a ka kashemin waya malam.." "Ank'i a kashe d'in ko da nina kiraka da zaka dunga min masifa kamar ka haifeni..??" Tsaki yarima yaja mai sauti,shi kuwa YASEER murmushi ya saki najin dad'in sunyi 1-1 a lokacin,sannan cikin sigar son ya gano inda maganar yarima YAZEED ta nufa ya shiga tambayarsa,tiryan² ya labarta masa duk abunda ya faru dashi wanda har ya janyo yazo ya iske shi acikin mugun hali a Daren na jiya,wani wawan ajiyar zuciya YASEER ya saki kafin ya iya tambayarsa "Broah..for how long wannan matsalar yake tattare da kai amma ka iya b'oyewa bayan kasan dole ne wata rana a sani....??" Cike da rashin fahimta yarima ya katseshi "Hey Mr man wane matsala kake nufi ne..??" "Wanda dai kayi min bayani yanzun shi nake nufi.." Murmushi yarima ya saki mai ciwo kafin ya furta "Haba mana man it's not a big deal da zamu tsaya b'ata lokaci akansa.." "Taya kake tunanin haka bayan ka sanar dani matsalar sannan kace ba Babba bane,taya kake tunanin haka..??" Cikin fahimta Yarima YAZEED ya fara masa bayanin,amma fir YASEER ya nuna masa shi ba haka ba,a nan ne yarima ya shiga yi masa bayanin daga lokacin daya fara fahimtar matsalan data faru da shi,shiru YASEER yayi dan yadda maganar take neman tayar masa da hankali "Shi kenan broah na fahimci abunda kake magana akai,amma kasan wannan hukuncin daka d'auka ba shi ne mafita ba,kamata yayi ace ka bari mun tattauna maganar kafin ace ka yanke hukunci,nd for now abunda nake tunanin ya kamata muyi shi ne kayi k'ok'arin dawowa gida sai musan abunda ya kamata ayi tun kafin su Abba su gane baka gari,ka fahimce ni..??" Jinjina kai Yarima yayi kamar yana gaban YASEER sannan ya furta "In sha Allah,I will try to came back as soon as possible.." "Ok..! See u later.." Daga haka suka katse wayan,ajiye wayan Yarima keda wuya ya fad'a toilet yayi taking shower,misalin k'arfe 5:30pm ya fito cikin wani suit army color sai bak'in long sleeve,bakin trouser nd black cover shoe,fuskar nan tasa as usual babu wani alamu na dariya akanta,sai dai kuma ba wai yana gimtse bane akwai annuri daya haska shi,yana fitowa ya kwaso keys d'in dake yashe saman center table sannan yayi waje abunsa cike da shirin zuwa wani guri. Can a gida masarauta kuwa tun bayan fitan YASEER a b'angaren Fulani bai sake yarda sun had'a hanya da kowa ba dan yadda yake tsoron fad'an inda Yariman yake,coz bai san yadda iyayen nasu zasu ji ba matuk'ar suka ji wannan labarin daga bakinsa,kan haka nema ya gwammace kulle kansa a cikin apartment d'in ko da sallah ma da yaji an kira nan cikin apartment d'in yayi ta a ranar,bashi ya fito ba sai bayan Maghreb. ^^^^^ Tashinta da sanyin safiyar taji jikinta duk yayi mata nauyi haka nan take jin jikinta kamar na wacce zazzab'i yake son shigarta,after tayi breakfast around 12:00pm,ta shirya cikin wani bak'in atamfa mai adon yellow da fari,car key d'in Adda ta zara sannan ta fice tana barma babarta Ladidi sak'on idan Adda ta fito ta fad'a mata taje shopping,da to Ladidin ta amsa mata sannan ta fice cikin hanzari.Da fitowarta a gidan bata nufi ko ina ba face Royal Palace dan can ne kad'ai take da muradin zuwa kuma a can ne kawai take jin zuciyarta zata yi mata sanyi,kai tsaye ko data fito a mota bayan tayi parking b'angaren hajiya ta nufa,da zuwanta bayan ta gaida ita ta amsa mata da kulawa,sai ta mik'e tana labartawa hajiyan zata je apartment d'in Fulani daga can kuma zata lek'a wajen ABEELA,da to hajiya ta amsa mata da sannan ta fice,ko data fito ji tayi duk bazata iya zuwa wajen suba,babban burinta a lokacin shi ne tayi arba da Yarima,dan haka take ta yanke shawaran nufan apartment d'in da take tunanin nan ne nasa duk kan tana tunanin samun sa a gida yau tunda yana hutun angwanci. A bakin k'ofa ta tsaya ta shiga y'an gyare² kafin ta matsa door bell,kamar a mafarki sajida dake kwance tana jiran dawowar Yarima dan suyi break taji door bell d'in a tsakiyar baccin daya saceta ba tare data shirya masa ba,duka itanma a tunaninta lokacin Yarima ne ya dawo,sai data fara saita nutsuwar ta sannan ta nufi k'ofar da niyyan bud'ewa fuskar ta d'auke da murmushi,da Aisha suka fara yin arba ko data bud'e k'ofar,nan take annurin fuskarta ya b'ace dan ganin da tayiwa Aishar a irin wannan lokacin da bazata iya ko da tantance k'arfe nawa bane,still suka yi a gurin suna musayar kallo wa junan su ba tare da sajida ta matsa daga hanyan ba,ita kuwa Aisha ko da ganin haka nan ta matsa kusa da sajida tana fad'in "Heeyy.! Madam hope kin tashi lafiya..ya amarci..??" Yadda tayi maganar kamar akwai wani abu da take nufi a cikin furucinta,sai dai kawai sajida ta share bata nuna mata ta fahimci wani abu ba,ta juya ta koma cikin parlor tana sakin b'oyayyiyar ajiyar zuciya kuma har lokacin bata tankawa Aisha maganarta ba ta koma saman seater ta kwanta abunta tana rufe ido dan bata son wata magana ta shiga tsakaninsu,kallonta Aisha tayi ta tab'e baki ba tare data sake magana ba ta bud'e jakarta ta ciro chewing gum ta cilla a baki tana tauna d'ai² had'e da fara sakin k'as² da abunta tamkar irin kishiyoyin nan da suke kan tsananin kishin abun sonsu haka zaman yaci gaba da gudana tsakanin aminan junan biyu da suka rikid'e cikin k'ank'anin lokaci suka koma abokan gaban juna kowacce na hararar y'ar uwarta da jin haushinta. ^^^^^ Around 9:45pm ya shigo cikin gidan,apartment d'in Umma'nsa ya fara nufa dan yasan yau idan bai je ta ganshi ba akwai damuwa,sanda ya shiga bai tarar da ita ba sai Inno da wasu cikin hadimanta suna ta y'an aikace²n su da ba'a rasa ba,da Inno suka gaisa kawai dan itan tana zaune ne a gurin ko daya tambayi Umma'nsa ta sanar da shi taje b'angaren hajiya ne kawai daga haka ko bata k'ara cewa komai ba,sak'o kawai ya bari dan baya son zuwa apartment d'in Hajiya daya isketa can ya gaidata tunda yasan bai shiga gurinta ba tun safe,coz bai san meya kai Umma'n nasa can ba,yana fitowa apartment d'insa ya nufa yana tafe yana neman line d'in YASEER "Am arrived.." Abunda kawai ya furta kenan da yasa na fahimci anyi answering kiran nasa,daga haka kuma bai k'ara komai ba ya janye wayan a kunnensa,cikin nutsuwa yake takawa har ya iso apartment d'in,door bell ya matsa sannan yaja space yana jiran ganin an bud'e,sai daya kusan shafe ak'alla mintuna 20 a tsaye ba tare da an bud'e ba,cikin tsananin mamaki ya d'ago kansa yana kallon k'ofar kafin ya sake k'ok'arin dannawa,still kusan wucewar ak'alla mintuna biyar sannan yaji ana k'ok'arin bud'e k'ofar,fuskar sa ya sake tamkewa sannan ya dai²ta tsaiwarsa sanda yaji an bud'e k'ofar,cike da mamaki take kallonsa dan yadda bata yi tsammanin ganinsa ba a lokacin,sai data gama kallonsa kafin ta matsa akan hanya ta koma gefe tana kaucewa daga hanyan,wucewa kawai yayi zuwa ciki ba tare daya ko sake kallon inda take ba abunsa yana sakin siririn tsaki mai sauti haka nan babu alamun zai kulata a tattare da shi........ #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *AWESOME WRITER'S ASSO..🏮* ~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~ *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 3.* ^^^^^^^^ Sanda ya wuce ta a tsaye kasa barin gurin Sajida tayi,zuciyartakianda daka babu abunda yake dan yadda taga fuskarsa har tsoron yi masa magana take,lokacin data d'ago kanta daga sunkuyon da tayi masa tuni har ya kusa da corridor,cikin k'arfin hali ta bud'e baki da kyar tana cewa "Yah Prince.." Ko kafin ta kai inda take son zuwa a maganarta tuni har ya dakata da tafiyar da yake ya juyo yana kallonta da sauraren abunda zata fad'a,shiru ta d'an sake yi musamman ganin irin kallon da yake jifanta da shi,jikinta har wani karkarwa yake saboda tsoron abunda zai biyo baya idan yaji abunda zata fad'a,haka ta daure duk da yadda zuciyarta ke gargad'inta "Barka da dawowa.." Wani kallon rainin hankali ya bita dashi yana sakin tsaki ya juya zai bar wajen,har yayi taku biyu ana uku ya jiyota tana cewa "Yah Prince.! Abinci fa yana jiranka.." "Am full..!" Yace mata ba tare daya tsaya ba ya wuce zuwa bedroom d'insa kai tsaye,wani tarin takaici ne ya binneta nan inda ya barta,dana sanin yi masa magana duk ya lullub'eta dan yadda ya mata sam bata ji dad'i ba,inda Allah ya taimaketa ma babu kowa sai su biyun da tafi haka jin bak'in ciki,da kyar ta iya barin gurin itama ta kama hanyar bedroom d'inta,tana shiga ta fad'a bed,take wani kuka ya taho mata nan ta shiga rera abunta ba tare data samu mai rarrashi ba,ta jima tana kukan dan ajiyan zuciya kafin bacci b'arawo ya saceta. ^^^^^ Lokacin da Aisha taga Yarima bashi da niyyan dawowa dan tun data shigo ta zauna bata ji allamunsa ba,ta wuce awanni uku a zaune a apartment d'in,gashi ta rasa waye zata tambaya inda yake,a ganinta Sajida bata isa ta tambayeta ba,shi yasa ma ta zauna ba tare data yi mata magana ba,itama kuma Sajidar hakan ne ya faru dan ko data tashi barin wajen bata ko kalli inda Aisha'n take ba tayi shigewarta bedroom,bata jima da barin wajenba,wasu hadimai mata uku suka shigo cikin parlour'n,a tunaninsu Aisha ce uwargijiyar tasu da aka turo su wajenta,nan take suka zube suna kwasar gaisuwa,babu wacce ta amsawa a cikinsu duk kuwa da irin bambad'ancin da suke mata,dan haka Babbar data d'an fisu shekaru ta fara mata jawabin Fulani ta turosu a matsayin wad'anda zasu dunga mata hidima,bata amsasu ba saima tsaki kawai data yi taxi gaba da sabgoginta,suna nan zaune ko da ganin bata basu amsa ba bare tayi musu jawabin abunda ya kamata suyi daga cikin aiyyukansu ba sai suka ci gaba da zama,kimanin wucewar awa guda suka sake shafewa a zaune babu mai k'wak'wk'waran motsi cikinsu bare asamu mai yin wata magana sai ga Sajida ta fito,kallo ta fara da binsu ganin mutane zaune a gurin yasa ta kasa b'oye mamakinta har saida ta tambaye su "Daga ina ku kuma..??" Cikin nuna gajiyawa da zaman jiran umarni da suke shugabar tasu ta kalli Sajida tana bata amsa "Daga b'angaren maimartaba muke,Fulani ta aikomu nan ne,saboda aikace² kuma mune hadiman da zasu dinga kula da nan.." Jinjina kai tayi sannan

Chapter 28 of 63