Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya koma kan YASEER,shima d'in amsarsa "bai sani ba",,,akan Yarima maimartaba ya sake tsayar da kallonsa,ya d'auki kusan mintuna biyu sannan ya ce " YAZEED..! Ko ka san abunda ya faru kuwa a wannan daren..??" D'agowa yayi yana kallon yadda duka jama'ar parlor'n suka kafe shi da idanunsu suna jiran suji amsar da zai bayar,dan daga dukkan alamun da auka fahimta shi d'in ne wanda maimartaba yake tunanin ya sani,wani sabon had'e rai yayi yana kallon k'annensa cike da aika musu zallar harara,,bai iya amsawa maimartaba ba yayi shiru yana sake sunkuyar da kai k'asa "YAZEED kai muke sauraro idan ka sani ka bamu amsa..idan ma baka sani ba ka amsa mana..!" Abba Galadima yayi masa maganar "A'a Abba..!" Abunda ya iya furtawa kenan,da mamaki Abba Galadima ya kalle shi yana sake jifansa da tambaya "Kamar yaya azancin A'a,,,A'a ka sani..ko kuwa A'a baka sani ba..?" Sake sunkuyar da kai yayi ya kasa magana,fuskar maimartaba da murmushi ya kalli Abba Galadima sannan ya sake kallon yadda Yariman ke wani sunkuyar da kai irin na marasa gaskiya "Shin baka sani bane..?? Ko kuwa kana son b'ata mana lokaci akan wannan y'ar amsar..?" "A'a Abiiy...na..sani.!" Still murmushi duka suka saki a tare sannan Abba Galadima ya ce "K'warai kuwa muma mun shaida da kai kad'ai kasan komai harma da faruwar komai.!" D'agowa yayi ya kallesu duka,nan kuwa ya tabbatar da abunda Abba'n yake fad'a,ba tare da b'ata lokaci ba Abba ya bashi umarnin sanar da sauran abunda ya faru,tsaf ya fara zayyana musu kaf abunda ya faru from a-z bai rage musu ko harafi ba,,,zullumi gami da tsantsar mamaki duka ya hana iyayensu mata magana,har ya dasa aya. YASEER kuwa tun daya fara magana ya zuba uban tagumi gami da sanya masa idanu har ya gama,wani gawurtaccen ajiyar zuciya ya saki sannan ya furta "Allah kyauta..!" Ba sai an fad'awa Yarima ma'anar Allah ya kyauta d'in da YASEER ya fad'a ba,,,bayan an gama zaman jimamin,suma iyayen nan suka hau Yarima da fad'an abunda ya aikata,dan kuwa babu wanda baiga laifinsa ba kan wasa da rayuwar jariri akan cimma burinsa na son kama masu laifi,after kuma suka sake masa nasiha kan duk abunda ya aikata d'in tare da bashi k'warin guiwa akan aikin daya fara. Su JIBO kuwa cikin wannan lokacin duk wani nau'ikan horo da azaba babu wanda ba'a gana musu ba amma har wayewar garin sun k'i fad'in komai,wannan dalilin yasa A.S.P Hood yanke shawaran kiran Yarima ya sanar da shi halin da ake ciki,,,a dai² lokacin da su kuma gidan suke wannan zama,sai ga kiran Hood d'in ya shigo wayarsa,sai daya d'auki excuse a gurin mahaifan nasu sannan ya amsa wayan,after sun gaisa Hood yake cewa "Sir..dama na kira na shaida maka ne har yanzunfa sunk'i fad'in komai.." Ran Yarima idan yayi million a lokacin tuni ya gama b'aci dan a tunanin sa zuwa yanzun tuni sun magantu,maganar Hood kuma a yanzun daya shaida masa nasu yi magana ba sai yake ganin ko dai su d'in basu bi dasu ta hanyar da zasu fad'i wanda ya sasu aikin bane,cikin fusata ya furta "Dama tunda kun sasu a gaba kuna kallo ta yaya za'ayi su shaida muku abunda ya kamata..??" "Noo! Sir wollahi tunda muka zo da su ake horar dasu akan su fad'a amma sunk'i.." Huci ya furzar mai zafi sannan ya cema hood d'in ya jira zuwansa nan da 40 minutes,bai ko sake sauraren shi ba ya yanke kiran wayan,tunda ya fara wayar duka suka yi shiru kowa so yake yaji abunda yake fad'a amma ina ko YASEER dake kusa da shi ba komai ya fahimta ba a maganar da yayi a wayan,kallonsa ya mayar kan iyayen su sannan ya ce zaije headquarter yanzun ana nemansa,addu'ah suka bishi da su na fatan tsarewar ubangiji sannan ya kalli YASEER yana fad'in "Broah..let us go..!" Bai ko kalle shiba ya furta "Ni kuma..?? Na bika zuwa ina kenan..??" Murmushi ya saki sannan yace "Kafa san abunda nake nufi..we have to go,muna b'ata lokaci a nan.." Ba dan yaso binsa ba saboda yana son nuna masa KUSKUREN ware shi da yayi a cikin case d'in sai don ganin idanun kowa na kansu ya mik'e yayi gaba,a baya ya biyo shi suka kama hanya,daga nan sai headquarter. Tun daga shigarsu suke amsar gaisuwa kasancewar su d'in sanannu ne,daga nan suka yi office d'in A.S.P HOOD kai tsaye,a can suka iske shi idanunsa sun d'an sauya launi,da ganinsa ba sai anyi ma mutum jawabi ba zai san yana cikin b'acin rai,hannu suka yi da shi sannan Yarima ya tambaye shi,"suna ina..??" Tare suka fita da shi inda basu zarce ko ina ba sai d'akin da suke,tun daga shigowarsu suka kallesu,dukansu fuskokinsu sunyi luhu² hakama jikinsu duk ya farfashe amma a hakan tambayar su ake sunk'i magana,inda JIBO yake Yarima ya d'an tsaya yana kallonsa da wani kwantacen murmushi a fuskarsa,uncovered nashi yasa aka yi,nan kuwa ya zube k'asa yana maida numfashi d'aya da d'aya saboda ya wahala,a saman kujeran da aka ajiye masa ya zauna yana hard'e hannayensa da aza chin d'insa a kai yana mai ci gaba da kallon JIBO,sai da yayi mai isarsa sannan ya saki numfashi maganarsa cike da rainin wayo yana cewa "Sannu ko..!" Harda wani d'aga masa hannu yana masa winking,,, shi kansa JIBO sai da yayi mamakin Yarima,amma da taurin kai irin nasa sai ya kalli Yariman cikin izgili yana cewa "Ka sanni ne..??" Pout Yarima ya saki yana girgiza kai kafin ya bawa JIBO amsa "Yeah..! I know u somewhere buh... Ehmm! Yeah! Na tuna kamar mun had'u a hospital..right..??" Sai lokacin wani wawan tsoro ya kama JIBO dan da dukkan alamun daya gano a fuskar Yarima a yanzun ya gane shi,,sai dai abunda bai gama yarda da shi ba har lokacin shine shin Yariman ya san duk tuggun daya k'ulla ne,sannan yaji maganar da yake a wancan ranar ne ko kuwa............??? #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 37.* ^^^^^^^^ *#Bleakness 2* Shu'umin murmushi ya sake masa mai d'auke da tsantsar nuna cewa ka gama kewayenka na san duk abunda kake aikatawa,shima JIBO kallonsa yake mai tattare da tsantsar tsoron makomarsa a hannun Yarima,sun d'auki lokaci shiru suna kallon kallo wanda yasa har YASEER ya d'an soma fusata da abunda Yariman yake,sai dai bai tanka masa ba,a hankali Yariman shima ya numfasa sannan ya fara magantuwa "Hope..u won't forget my face..?" Wani kallo JIBO ya sake binsa da shi yana had'iye yawun tsoro,,ko da ganin haka sai yasa Yarima sake yarda da cewa Criminal d'in nasa ya firgice da lamarin sa dan haka sai ya sake had'e masa girar sama dana k'asa sannan ya d'an kalli sergeant d'in daya kwance shi yace "Ask him..maybe he won't hide the truth anymore.." Wuyarsa sergeant d'in ya dank'o ta baya ya d'aga kulkin dake hannunsa ya d'ora masa a ta dai² mak'oshi yana fad'in "Za kayi magana ko kuwa..??" Matsar da yaji tana neman shek'a shi zuwa lahira nan da nan duk taurin kai irin na JIBO ya hau cewa "Yallab'ai kayi min rai zan fad'a... Wallahi zan fad'a maka..!" Alama Yarima yayi da hannu yana nuna masa ya sake shi,dungurar da shi yayi ya matsa daga kusa da shi,tari sosai JIBO yake na wahala saboda shak'ar daya sha bata wasa bace,yana sunkuye gaban Yarima kansa a k'asa sai tari yake,d'an sunkuyawa Yarima yayi yana sakin murmushi sannan yace "Who gives u these project..??" Sai da JIBO ya d'ago jajayen idanunsa ya sauke kan Yarima sannan ya furta "Hajiya..!" Squeezing face yayi yana tab'e baki sannan ya ce "Wace ce Hajiya..??" Shiru yayi yak'i magana daga Hajiya bai k'ara komai ba "Kafi son ayita azabtar da kai kenan..??" Yayi shiru al'halin yana jinsa,pliers Yarima yasa a kawo masa,nan take muguntar ta motsa,abunku da wanda yayi karatun primary-secondary a makarantar sojoji ya kuma rayu a kurkuku kusan dole yasan salon mugunta da dama,kafin k'iftawar idanu tuni har an zube masa su a kusa da shi,kallonsu yayi d'aya bayan d'aya sannan ya zab'i wani mai faffad'an baki,sake kallon JIBO yayi yana susar mustache d'insa da shi sannan ya furta "Baka sani ba..??" Kai ya girgiza masa yana sake yin k'asa da kan,can k'asan zuciyarsa yana sak'a cewa matuk'ar fa yak'i sanar masa ya tabbatar wannan mutumin abunda zai masa bazai ji dad'i ba,yana wannan tunanin ya tsinkayo shi ya kamo hannunsa dake d'aure,a saman nails d'insa ya d'ora plier d'in yana matsawa,ihu JIBO ya saki yana fad'in "Zan fada Yallab'ai.. Zan fad'a..!" D'an sassauta rik'on yayi sannan ya zuba masa idanu "Hajiya ce ta sani.." "Don't ever says Hajiya alone..full name na wanda yasa ka sacemin yaro nake son sani..Nd ka fad'a min uban waye ne yasa ka yiwa matar nan barazana ka sata dole saita d'auko maka shi.." Shiru yayi yana yarfe hannu da duba yatsarsa daya sha matsa,sake fusata Yarima yayi nan ya sake rik'o hannun ya matse da plier,cikin rashin son wasa ya fincike nail d'in JIBO guda d'aya,sai da gurin yayi wani irin fari kafin jini ya fara tsatstsafowa ya fara tsiyayaa gurin,zunzurutun azabar daya ratsa kwakwalwarsa yasa shi har bai san lokacin daya ce "Yallab'ai.. Hajiya Suwaiba ce ranka dad'e,itace ta sani..matar Matawalle..!" Wani dumm Yarima suka ji a kunnuwansu jin sunan Hajiya Suwaiba,cikin zuk'atansu kuwa kowa da irin tambayar da yake yiwa ransa kan wannan rikitaccen AL'AMARIN,shin mene ne hakan ke nufi..??,kallonsa Yarima ya sake yi sannan ya furta "Karya kake..!" Sake kamo wani yatsar yayi yana shirin cire farcen yayi saurin cewa "Wallahil aziiym Yallab'ai ita tasa ni wannan aikin..idan kuma baka yarda ba a kawo waya,,,na tabbatar ba zaka k'aryata muryanta ba.." YASEER ya juya ya kalla yana son yaji mai zaice shi d'in,,a hankali ya lumshe masa idanu yana bashi k'warin guiwa da cewa ayi hakan kawai,take yasa aka kawo wayar JIBO,number ya kallah ya kuma tabbatar nata ne,sai data d'auki lokaci da shiga amma har kiran farko ya katse ba'a d'auka ba sai a kira na biyu sannan aka d'auka,cikin izza da isa irinta hajiya Suwaiba ta furta "Hello..! JIBO..?? Me yasa najika shiru ne jiyan bayan ka sanar dani kana harabar gidan kana jira a kawo maka yaron..Ina fatan ba wani matsala aka samu ba ko..??" Gaba d'ayansu saank'amewa suka yi a gurin tamkar anyi sculpturing nasu cike da tsantsar mamakin da suka tsinci kansu a ciki,wayar dake hannun JIBO sergeant d'in ya karb'e sannan ya datse kiran,jikinsu duk yayi sanyi da AL'AMARIN,,,sun shafe tsayin lokaci kafin Yarima ya maida dubansa akan sauran mutum biyun yana musu wani irin kallo mai d'auke da tsantsar jimamin sanin wanda ya sasu aikin,a hankali ya sake kallon JIBO sannan yace "Kenan dukkan ku mutum d'aya kuke yiwa aiki.?? Duka ita ne ta sa ku sato mata Yarona..??" Har lokacin azabar da yake ciki bai sake shiba,bayan azababben zafi da yatsar ke masa har yanzun jinin da yake ta d'igarwa bai tsaya ba "A'a Yallab'ai.. Ni wad'annan ban sansu ba..sannan ban san waye ya turo suba.." Da mamaki a fuskokinsu duka suke kallonsa kafin YASEER ya bud'e baki yana cewa "Kana nufin kace aikinka da wanda ya saka daban suma nasu daban..??" "Ehh..! Yallab'ai..gasu nan a tambaye su ni ban tab'a had'uwa da suba sai a jiya da aka kamomu tare da su.." Sergeant dake tsaye a gefen JIBO ya kallesu duka yana jinjina kai sannan ya d'auki wani mugun plier yana nufar na farko,tun kafin ya k'arasa inda yake har ya saki wani azababben ihu dan yasan me hakan yake nufi,cikin k'araji yake cewa "Wollahi Yallab'ai zan fad'a.. Zanyi bayanin wanda yasa mu.." Dakatawa sergeant d'in yayi a gabansa yana kallonsa da cewa "Yi bayani muna saurarenka..ka tabbatar kuma ba k'arya zaka mana ba..Idan har ka kuskura ka fad'a mana k'arya ina mai tabbatar maka zan yanyanke maka gab'ob'in hannu yanzun,,,shi nails ya rasa,kai kuma zaka rasa gab'b'ai..sai ka zab'a fad'a mana gaskiya ko kuma yankar jikinka.." Bakinsa har b'ari yake wajen cewa "Wollahi Yallab'ai iya gaskiyar dana sani zan sanar maka..Idan ka sameni da yin k'arya kuma na yarda kayimin duk abunda ya dace.." Girgiza kai sergeant d'in yayi sannan ya kafeshi da kallo yana jiran yaji ya shiryo masa zancen da bai gamsheshi ba ya idar da nufinsa akansa "Yallab'ai..Kamar yadda ka tambayemu,,,ba kowa ya samu aikin nan ba face HAJIYA ADDA.." A tare YASEER da YAZEED suka maimaita "Adda..!" "Ehh! Yallab'ai itace ta bamu contract na karb'o jaririn daga hannun wanda zai kawo shi.!" Kallonsu suke dukansu dan yadda ambaton sunayen Hajiya Suwaiba da Adda daga bakunansu yasa su shiga tsantsar mamaki,ko da yake a gare shima shi kam Yarima yafi mamakin alak'ar Hajiya Suwaiba da case d'in,amma Adda kam baya wani tantama da jin sunanta,dole ne ya tabbatar dama babu yadda za'ayi barewa tayi gudu d'anta yayi rarrafe,kamar yadda yasan alak'arta da Ladidi dole ne dama ya kasance dasa hannunta a cikin duk abubuwan da suka dunga faruwa a can btoshi duk bama wannan ne damuwar ba,yadda zai iya kallon Hajiya ya sanar da ita cewa harda sa hannun y'ar uwarta a cikin matsalar..?? A gefe guda kuma tunanin yadda zai iya kallon idanun Abba matawalle ya shaida masa harda sa hannun matarsa a cikin matsalar yake,,,mutumin da yayi ruwa yayi tsaki akan lamarinsa yayi kuma sanadin fitowarsa daga halin da aka jefa shi,,Ya sani dukansu sun cancanci hukunci ko badan komai ba sai don ya zama izina agaresu haka nan saboda gaba kada suyi k'ok'arin sake maimaita hakan,amma ta yaya zai ce a hukunta su duka..?? Tsayin lokacin daya shafe yana wad'annan tunanukan jin kwakwalwarsa yake gaba d'aya ta cushe da tunanuka iri² har ya janyo YASEER ya fuskanci halin da yake ciki,duk da shima d'in bawai yana cikin yanayin jin dad'i bane sai dan shi ya danne nasa damuwar,sun shafe ak'alla awanni biyar a headquarter saboda matsalar da aka samu d'in,ba tare daya bada izinin kamo su Adda ba,suka yi sallama da A.S.P Hood akan ya jira cewarsa game da masu laifin da akayi maganarsu,sannan suka juya akalar tafiyar zuwa gida.. A hanya koda suka baro headquarter tafiya suke amma tamkar ta kurame,dan babu wanda yake iya cikakkiyar magana har suka shigo cikin gidan,,ba tare daya iya yiwa YASEER sallama ba ya nufi apartment d'insu da matsanancin damuwa dan yadda yake ganin samu da rashi a lokaci guda,gashi dai ya samu damar gano masu laifin amma kuma damar hukunta su na neman sub'uce masa,tunda ya shigo ta d'ora idanunta akansa ta fahimci akwai damuwa a tattare da shi,,,Abir dake zaune tare da ita tun bayan da Abba Galadima ya sallame su daga zaman da akayi ta mik'e zata fita dan tasan halinsa idanma bata fita ba abunda zaiyi mata sai ta gwammace ace fitar tayi da kanta,tana mik'ewa Jeeddah ta bita da kallo tana fad'in "Abir..zo ki karb'e shi,idan kunje ki kaiwa baba Jakadiya shi.." "Toh" tace mata sannan ta karb'e shi,suna fita a apartment d'in itama tabi bayansa,a kwance ta tarar da shi a saman royal bed d'insa yayi ruf da ciki kamar wanda zai shige cikin mattress da yake kwance akai,a kusa da shi ta samawa kanta gurin ta zauna,kansa dake kife ta zura yatsunta a ciki sannan ta fara masa susa,slowly take yawo dasu a cikin curly hair d'insa har ta gangaro dasu gefen fuskarsa ta fara masa massaging gurin,duk da yana cikin matsanancin damuwa hakan bai hana masa fara samun sassauci ba bisa abunda take masa,sanda tayi k'ok'arin janye hannunta kuwa da sauri ya kamosu ya mayar yana sake gyara kwanciyarsa akan laps d'inta zuwa rigingine,har lokacin idanunsa a lumshe suke yana enjoying salon da take masa massaging da shi,sun shafe sama da one hour a haka wanda tayi tunaninma ko yayi bacci ne saboda yadda yayi shiru,a hankali ta d'an zame k'afarta tana mayar da kansa saman pillow ta mik'e da niyyar fita,hannunta ya rik'o yana sauke mata narkakkun idanunsa akanta "Where do u think to go..??" Narke fuska tayi itama tana kallonsa da fuskar damuwa "Zan kawo maka abinci ne..Nasan babu tabbas tunda kuka fita kaci wani abun wa cikinka.." Lumshe ido ya sake yi ya bud'e,zuwa wannan lokacin duka tuni sun gama birkicewa like drunkard,ita kanta saida ta firgita da kallon k'wayar idanunsa har taji bazata iya matsawa a gurin ba,shima d'in bai sake taba saima janyota daya sake yi ya dawo da ita ta gabansa,yana daga kwancen ya janyota ta kwanta a jikinsa,hannunsa yasa a bayanta ya zagayeta da su,cikin wani yanayin ya shiga sauke ajiyar zuciya,kasa kallon yanayinsa tayi ta kwantar da kanta a jikinsa tayi luf tana sake k'ank'ame shi a jikinta sai dai duk sunyi shiru babu mai magana,sun d'auki tsayin lokaci a haka sannan ta d'ora palms d'inta a jikinsa tana caressing,muryanta a k'asa ta fara masa magana cikin rad'a "Yallab'ai..Allow me to go..ina son kawo maka abinci amma ka hana.." Bai bud'e idanunsa ba haka bai sake taba ya furta "No..KHUSHI.. Bana jin zan iya sama cikina wani abu,al'halin ina cikin damuwa.." "Amma Yallab'ai..! Damuwa fa baya maganin komai saima haddasa ciwo,me zaisa ka zauna cikin damuwa..?? Kayi hak'uri ka bari na kawo maka abincin,,ina tunanin an kama masu laifin so why are u still worrying..??" Kai yake girgiza mata sannan ya bud'e rinannun idanunsa "KHUSHI..! Duk yadda kike tunanin matsalar da nake ciki ya zarta hakan..Saboda haka ki daina min wannan maganar..Nasan kina yin hakka ne dan na kwantar da hankalina,buh na sani babu yadda za'ayi burin dana ci akan hukunta duk mai hannu a cikin matsalar nan ya tab'a cika..!" Kallonsa take da idanunta masu cike da damuwa "Me yasa zaka ce haka..?? Bayan mun tabbatar da sun shiga hannu..nd hukuma zasu ji da lamarin su..??" "Da saura KHUSHI..! Da saura...Wanda suka aikata laifin suna nan a gefe ne,,wanda na tabbatar da zaran Hajiya ta sani bazata tab'a bari na aiwatar da k'udurin dana tanadawa zuciyata ba." Tausayinsa ne ya sake kamata,cikin k'ank'anin lokaci har jikinsa yayi wani iri d'umi,wanda jin hakan ya sake tabbatar mata da damuwar da yake ciki ya zarta duk yadda take tunani,sake k'ank'ame shi tayi tausayin halin da yake ciki yasa ita kanta ta kuma shiga matsanancin damuwa,a hankali tasa hannu ta d'auke tears dake ziraro mata "In sha Allah babu abunda zai faru..zasu yi hak'uri su kuma bari a hukunta koma suwaye..Kayi hak'uri Yallab'ai,ka sawa zuciyarka dakewa,kaifa sadauki ne kuma jarumi bayyanar da damuwa a fuskarka tamkar ka bawa mak'iyanka gudun nawa ne na gano weaknesses naka...Dole ka sawa ranka dakiya akan duk abunda ya sameka koda ace a k'asan zuciyarka kana jin ciwon hakan..Matuk'ar ina gefenka babu yadda za'ayi na juri ganin fad'uwarka a gaban mak'iyanka,bana fatan Ubangiji ya kawomin ranar da zata zama sab'anin nasara a gareka..!" Tunda ta fara magana yake kallonta har ta dasa aya,yanayin fuskarta da kalamanta sosai suka tabbatar masa da gaskiyar dake b'oye a k'asan ranta,tsura mata idanu yayi yana kallonta da wani irin shauk'in murna na fahimtar inda kalamanta suka dosa,sai dai damuwar dake tare da shi ya hana masa ya bayyana mata yanayin da yake ciki na jin dad'i "Yallab'ai..!" Ta kira shi can k'asan mak'oshi,yana can duniyar kallonta har baisan lokacin daya amsa mata yana sake aika mata wani kallon daya matuk'ar kashe mata jiki,sake kwantar da kai tayi a jikinsa tana yawo da yatsunta a jikinsa kamar mai neman wani abu,bai hanata ba taci gaba da abunda take "Yallab'ai.. Me yasa kake tunanin baza'a samu goyon baya daga Hajiya ba..??" Shiru yayi yana tunanin abunda zai fad'a mata,ko kafin ya lalubi amsar bata tuni kira ya shigo masa,kamar bazai motsa ba,hakan yasa Jeeddah d'an zamewa a jikinsa sannan ta d'auko masa wayan,sunan data gani a sama yana lilo yasa ta saurin kai masa,Abba Galadima ke nemansa dan haka tayi saurin bashi,jikinsa a sanyaya ya amsa wayan,muryar Abba Galadima ya biyo yana bashi umarnin yazo yanzun ya same su a parlor'n Hajiya,amsawa yayi cike da sanyin jiki sannan ya kamo hannunta suka fice......... *Kuyi hak'uri da wannan aradu bana jin dad'in jikina sosai yau d'innan...* #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر

Chapter 54 of 63