motsi saboda tsabar bala'in dake cin ranta,ko da jin muryar hajiya a wayan tana sallama dai² lokacin data d'auka tuni ta kai hannu tana wawuro wayan daga hannun Aisha'n,hak'oranta a cije saboda masifa sannan ta d'aure ta amsa sallamar hajiyan,ko gaisawa bata jira sun yiba ta fara magana
"Hajiya..! Wai ni shin ina maganar had'a auren yarima da Aishatu ne.?? Naji Kinyi shiru tun tuni baki kuma min zancenba..Ince dai ko lafiya..??"
"Lafiya hayyan ma kuwa..!"
Hajiya ta amsa mata cikin yanayi na nutsuwa da kwanciyar hankali,sake danne zuciyarta Adda tayi kafin tayi magana
"To amma hajiya ai ni baki cemin ga inda maganar ta kwana ba,kuma nasan munyi maganar tun tuni gashi lokaci sai tafiya yake sake yi.."
"K'waraifa kam munyi maganar sai dai idan kin manta bari na tunatar dake abunda ya faru,kamar yadda na fad'a miki tun wancan lokacin zan mai²ta miki yanzun,tun daga ranar dana san gaskiyar da kuka jima kuna b'oyewa na riga na soke wannan batun,kamar yadda tun lokacin na shaida miki,kuma a halin da ake cikima a yanzun da baki sani ba shi ne abunda ya rage a auren yarima yanzun na tabbata bashi da yawa,saboda haka zaki iya nemawa jikarki mijin daya dace da ita amma ba jikana ba,dan ni na riga na masa addu'ah kuma Allah ya sauya masa da wacce ta fita alkhairi..."
Cikin k'arajin masifa saboda yadda maganar hajiya ta daki kunnenta Adda ta furta
"Ya isa haka HAUWA..! Ya isa..!!"
"Hauwa kuma yau d'in..??"
"K'warai Hauwa ina tunanin hakan shine sunan da mahaifin mu ya rad'a miki..?? Hajiya ko yaya da muke kiranki da shi ai ba dashi kika zo duniya ba..Wannan ganin damarmu ne yasa muke sakayawa a matsayin ki na Babba,sai dai tunda baki rik'e girman ba kuma baki d'aukemu y'an uwan naki kamar yadda kike fad'a ba,dole ne muma mu nuna miki kalar namu rashin jin dad'in..."
"Gaskiya ne Aisha kinyi gaskiya..wannan shi ne sunan da mahaifina ya rad'a min,kuma na gode da wannan cin mutuncin,sai dai ki sani shi Babba har kullum bazai tab'a zama d'aya dana k'asa da shi ba,abunda kikamin idan nace zan mayar miki mun zama d'aya kenan,saboda haka kije duniya ce ta ishi bagaruwa jima..!"
"K'waraifa ko baki fad'a ba haka yake,sai dai ki sani Hauwa wollahi tunda kikamin wannan abun banji dad'i ba,na rantse da sarkin dake busamin numfashi kema baza kiji dad'i ba,aurene kuma da kike ik'irarin zaki masa to ayi mu gani...Ba sai yayi auren zai samu nutsuwar ba,to ya samu na gani..Dani kike zancen,duk ta inda zaki bi nima ina da hanyar da zata b'illo dani har zuwa gare ki...!"
Tana fad'in haka tayi hanging kiran ba tare data jira taji me hajiya zata sake fad'a ba,cikin zallar b'acin rai ta koma kan seat mai cin mutum d'aya ta zauna dab'as ta shiga sauke numfashi kamar wacce tayi wani gagarumin aiki.
Can a gefen hajiya kuwa lokacin da Adda ta gama fad'in duk abunda ranta ya so ga hajiyan ta kuma kashe ba tare data saurari abunda ita hajiyan zata fad'a ba,duk abun bai wani dameta ba,sanda hajiya ta tabbatar ta kashe wayan sai kawi ta janye wayar a kunnenta tare da yin murmushi a fili ta furta
"Kiyi duk abunda za kiyi Allah ya fiki,kuma na tabbata ba zai baki nasara akan ahalina ba..Matuk'ar Muna tsaye akan k'afafunmu muna fad'a masa damuwarmu babu wani wanda zaiyi nasara duk k'arfin kaidinsa garemu.."
Tun daga wannan ranar zumunci tsakanin hajiya da Adda tuni ya sake yin baya sosai,ita hajiya ba don komai ta janye jikinta daga Adda ba face rashin hankalin da Adda'n ta gwada mata shi yasa ta yanke shawaran zura mata ido kawai ba tare data ko sake neman inda take ba.Ga Adda kuwa itama tayi haka ne ba don komai ba sai don yadda take kan dokin zuciya,cikin ranta kuwa banda zallar k'unci da son rama abunda aka mata babu abunda yake ciki,wannan dalilin yasa kwana biyu itama sai ta janyewa hajiyan ba don komai ba sai don son sake shiri kafin ta sake tunkarar hajiyan dama ahalinta baki d'aya kamar yadda tayi alwashi.
Kwanakin biki sai dad'a gabatowa suke,ta kowane b'angare zuwa yanzun hidima tayi nisa sosai babu wani wadataccen lokacin zaman banza,watanni biyu da aka sa ranar kenan,cikin wannan lokacin kuwa tuni gidan sarautar gaba d'aya basa wani samun cikakken lokacin zama,haka ko ina ka duba jama'a ne kama daga kan hadimai har zuwa masu gidan duka hadimar bikin ta sha musu kai,a haka sauran kwanakin da suka yi saura suka ci gaba da gabatowa suna kuma wucewa.
Sai cikin satin da za'a fara bikin sannan angwayen suka samu damar isowa garin a ranar Wednesday,wanda tun daga ranar ne kuma dama za'a fara shagali kasancewar hidima irinta masu hannu da shuni,musamman kuma da abun ya had'e biyu ya zama ya had'a alak'a da masarauta sai ya had'u ya bada color mai matuk'ar kyauda k'ayatarwa.
Da Yamma bayan sallar la'asar,lokacin da y'an uwa keta k'ok'arin halartar taron motar Adda ta shigo gidan,cikin kwalliya kamar wata budurwa haka ta fito jikinta sai k'arar k'arafa yake duk inda ta motsa,a haka ta iso harabar gidan dake d'auke da k'ayataccen yanayi mai burgewa saboda gyaran da akayi da k'awata gurin kasancewar a yammacin zasu gabatar da zaman bud'ar kai kamar yadda mazauna yankin gwombe keyi,yayin da yankin had'eja kuma sukan kira hakan da Zaman ajo,haka dai kusan zamu iya cewa ko wane gari da sunan da suke ambatar nasu a al'adance.
Bin ko ina take da kallo tana yatsina fuska a haka har ta iso wajen,tana tafe ahalinta (Aisha) na biye da ita har suka isa gefen Fulani,a can suka fara yada zango,bayan sun mata Allah sanya alkhairi sannan suka nufi gefen Ummi ma suka mata murna,daga nan kam k'in shiga gefen hajiya suka yi direct suka nufi gurin da za'ayi taron suka zauna suna kallon mutane d'ai²,har zuwa sanda aka fara taron daya had'a kaso mafi yawa na y'an uwa,haka k'awayensu Abeela zuwa Abir duk suma ba'a barsu a bayaba,cikin abunda baifi mintuna talatin da zaman su Adda a gurin ba tuni har harabar gurin ta d'inke da jama'a kama daga kan wad'anda aka gayyata zuwa y'an gayyar sod'i irin su o'o (amma dai ban kama suna ba saboda tsaro),sai misalin k'arfe biyar da kwata (5:15) sannan Angwayen suka bayyana,sanye da shadda y'ar ubansu data amsa sunanta,cikin shiga ta alfarma da babu bambanci tsakaninsu tamkar wasu tagwaye,gurin da aka tanada dominsu saman kilisan da aka baje suka zauna sannan aka tafi don fito da amare dake can gefen hajiya,sanda suka fito su kansu shigar tasu iri d'ayan ce kamar yadda su YASEER suke,fuskokinsu k'unshe cikin manyan mayafan da aka lullub'a musu tun daga ka har kusan guiwowinsu sannan aka zaunar da kowacce kusa da angonta,bayan bud'e taron da addu'o'i sannan aka fara gudanar da abunda ya ajiyesu a gurin dominsa,lokacin da aka fara gudanar da al'adar y'an uwa kowa burinsa ace yayi bajinta,dan haka aka nan kowa ya fara zuwa yana zuba adadin abunda ransa ya yanka masa,masu tsokana a ciki na yi wad'anda suke abokan wasa suma suna yin nasu dan babu wanda aka bari a baya.
Can daga baya Aisha dake kusa da Adda ta jinjina kai bayan kallon yadda abun ke tafiya,sannan ta mik'awa Adda hannu tana cije leb'e,murmushi Adda'n tayi kafin ta zaro rafar y'an #500 ta d'ora mata saman hannunta kana ta furta
"Kibi a hankali sannan ki tabbata kinyi taka tsantsan saboda bana son a samu matsala wannan karon.."
Kai ta girgiza mata kafin ta mik'e cikin takun da ko a tarihi bata tab'a zaton ita kanta zata iya ba ta fito cikin dandazon al'ummar ta fara ratsawa tana wucewa,sai data isa har gurin da suke zaune sannan ta d'an dakata tana kallonsu ta cikin glasses en dake manne a idonta tun zuwansu,a hankali tasa hannunfa d'aya ta zare shi daga fuskarta dai² lokacin da suka had'a ido da sajida tayi mata murmushi, mayar mata itama tayi sannan ta d'an matsa kusa da ita kad'an tana mik'a mata hannun alamun suyi musabiha,hannun sajida cikin na Aisha tana mata murmushi mai siyar fassara,a hankali yanayin fuskar Aisha'n ya fara sauyawa sannan ta kalleta tana matsa hannunta dake cikin nata,murya k'asa² ta fara magana ta yadda sajidar kad'ai zata iya jinta
"Kinyi k'ok'ari fa SAJIDA da har kika iya yaudarar zuciyar ki wajen karb'ar soyayyar wanda ba mallakinki ba..Sai dai ina tayaku farin ciki da MALLAKAR juna da kuka yi..."
A hankali ta saketa kafin ta juya ga YAZEED da sam hankalinsa baya kansu bare yayi noticing abunda ke faruwa a tsakaninsu
"Ina tayaka murna Yarima na samun zuk'ek'iyar amarya kamar sajida...!"
'Dan waiwayowa yayi kad'an jin anyi magana daga gefensa,fuska ya tsuke ganin wacce ke tsaye a kusa da shi,ko kafin ya kai ga yin magana tuni har Aisha ta juya ta bar wajen.Lokacin data koma kusa da Adda ta maida glasses enta sannan tace
"An gama Addata...!"
"Kin tabbata kinbi yadda procedure en take..??"
Kai ta jinjina mata kafin suka ci gaba da zuba ido suga abunda zai faru,kusan mintuna biyar tsakani Adda ta waiwayo kan Aisha cikin b'acin rai
"Anya kuwa Aisha ba asara kike neman sani nayi ba..?? Naga shiru har yanzun.."
Ba tare data kalli Adda'n ba ta jinjina kai
"Haba mana Adda kin san dai babu yadda za'ayi nayi wannan kuskuren,ina ji ina kallo wata ta samu damar auren sa..Kawai ki ci gaba da zuba ido zaki ga abunda zai faru.."
Ci gaba Adda tayi da sanya ido akan Yariman tana kuma sake kallon lokaci,duk bayan mintuna idan taga babu abunda ya faru sai kawai ta waiwayo kan Aisha tana sake jifanta da tambayoyin da tun farko sune dai take sake maimaita mata,can bayan wucewar wasu sa'o'i da abun duniya ya ishi Adda saboda ganin har lokacin babu abunda ya faru,sai kawai ta mik'e tana fad'in
"Tashi muje kawai..babu amfanin zamanmu a nan..!"
Kallon Adda'n tayi cikin yanayin rashin jin dad'i sannan ta mik'e,ita kanta a lokacin lissafa yadda akayi aka samu kuskure take a cikin duk abunda aka sanar dasu zai wakana,har sun fito daga cikin rumfar Adda'n take cewa Aisha'n suje su yiwa Fulani sallama sai su wuce,amsawa tayi kawai amma bawai dan har ranta taji dad'in abunda ya faruba suka nufi hanyan apartment en fulani cike da jimami.
Tunda ta juya ta bar wajen ya kalleta tare da sakin tsaki mai sauti,nan ya d'auke kai zuciyarsa cike da mahaukaciyar k'iyayyarta,a hanakli YASEER dake gefensa ya juyo jin yadda yayi tsaki dsan shima bai san abunda ya faru a lokaciba yana masa magana,bai samu damar bashi amsa ba saboda yadda ya soma jin tsigar jikinsa na tashi,sannu a hankali yake jin yanayin jikinsa na sauyawa ba tare da yayitunain sanar da YASEER yhalin da yake jinsa a ciki ba,ya shafe a k'alla mintuna sama da arba'in a cikin wannan halin,kafin ya waiwaya ga YASEER,lokacin daya kalli inda YASEER en yake ne cike da son tambayarsa,har ya bud'e baki zai yi magana take wani mugun shak'uwa ya fara taso masa,sannu a hankali abun yaci gaba tun bai d'auki abun serious ba har labari ya fara neman canja salo,sosai yaci gaba da shak'uwan babu k'ak'k'autawa har sai daya janyo hankalin YASEER kansa,sanda ya kalleshi yana jifansa da tambaya
"Broah! Lafiya kake kuwa..?? Ka nemi ruwa mana ka sha ko zaka daina.."
Girgiza masa kai yayi cikin sauri ya mik'e zai bar gurin,wata abokiyar wasansa ce da zuwanta gurin kenan ta rik'o shi tana tambayarsa inda zaije cikin tsokana,da hannu ya mata nuni dan yadda lokacin yake kan shan wahalar shak'uwan dake damunsa,yadda ta fahimta daga dukkan alamun da yake mata ta gane ruwa yake nufi dan yadda yake shak'uwa,maidashi tayi ya zauna sannan ta bashi tabbacin bari ta kawo masa ruwan yanzun,jinjina mata kai yayi saboda magana ma a lokacin ya gagareshi,mintuna Uku tsakani da tafiyarta a gurin,sai ga wani bawa ya iso kusa dashi hannunsa d'auke da robar ruwa da cup a kan tray k'arami yana fad'in
"Yallab'ai ga ruwan an kawo maka.."
Ko da jin haka da sauri YAZEED ya d'ago kansa,lokacin da yayi arba da ruwan kuwa bai tsaya jiran sai an tsiyaya masa a cup ba ya sura had'e da b'alle murfin robar ya d'aga ya shiga d'ad'akawa cikinsa,sai daya shanye tas sannan ya sauke robber yana sakin ajiyar zuciya had'e da dafe k'irjinsa saboda yadda yake jin yana masa wani iri, asakamakon galabaitar da yayi ta sanadin shak'uwan,sannu YASEER ya masa yana d'an kallonsa da kulawa,bai iya amsawa ba sai kai daya jinjina masa,haka suka ci gaba da zaman gurin ga YAZEED kam jinsa yake duk a takura,a daddafe ba don yana jin sha'awar ci gaba da kasancewa a wajenba yaci gaba da hak'uri har zuwa lokacin da aka tashi a taron,ba tare da ko (a) yariman ya sake furtawa ba duk da dama shi en ba ma'abocin yawan magana bane sai ko idan ta kama.
Lokacin da aka tashi a taron apartment nasu suka nufa kai tsaye saboda yadda gidan yake a cike,nan enma tunda suka kama hanya babu wata magana data shiga tsakaninsu har zuwa lokacin da YAZEED en ya shige bedroom ya bar YASEER nan a zaune a parlour da niyyan zuwa ya watsawa jikinsa ruwa saboda kasalan da take neman lullub'e masa jiki,ruwa mai d'umi ya tara cikin kwamin wankan kafin ya shiga ya kwanta ciki yana jin yadda ruwan ke ratsawa ta cikin ko wace kafar gashi dake jikinsa,yafi minti talatin a haka sannan yayi abunda ya kawo shi ya fita yana d'aure da towel iya k'ugu,tun bayan fitowarsa daga cikin ruwan haka kawai sai ya fara jin wani irin yanayi na taso masa tun daga cikin ainihin jikinsa kamar wanda ake hurawa wuta a cikin jikin,cikin lokaci kad'an tuni temperature en jikinsa ya sauya haka ma ko ga yanayin fitar numfashin sa,saman bed ya hau ya kwanta yana cure jikinsa guri d'aya,jikin nasa na wata irin girgiza kamar na mutumin dake shirin tada iskoki,ya d'auki lokaci a haka shi kad'ai cikin wannan mawuyacin halin kafin YASEER ya kawo kai ya shigo a dalilin jin da yayi shiru har tsayin lokacin bai fito ba,ko da ganinsa a cikin wannan halin tuni yayi saurin nufarsa,cikin kid'imewa kamar ba namiji ba ya juyo da YAZEED en suna fuskantar juna yana tambayarsa
"Broah..! Are u Ok..!"
Kasa amsa masa yayi saboda yanayin yadda jikinsa yake ga wani irin sanyi mai ratsa k'ashi da lokaci guda shima ya saukar masa,tambaya YASEER en yaci gaba da jero masa ba tare daya samu amsan tambayoyinsa na baya daya fara ba,duvet en da YAZEED en ke kaiwa hauri da k'afa yana k'ok'arin janyowa amma ya kasa a dalilin rashin k'warin jiki YASEER en ya janyo ya rufeshi da shi,cikin tsananin ciwo YAZEED en ya furta
"Ka kiramin Ummanah...!"
"Idan tazo me zata maka ne...??"
YASEER ya tambaya da kulawa,cikin zafin ciwo shima yana runtse ido ya furta
"Kawai kace ina buk'atan ganinta.."
Mik'ewa YASEER en yayi ya fita cikin hanzari,da zuwan sa parlor bai yi wata² ba ya suri wayansa yana kiran number family doctor nasu dan yasan a wannan halin da ake ciki shi kad'ai ne zasu iya buk'ata a irin wannan lokacin su samu abunda suke nema,amma kiran Ummah Fulani sam yasan ba mafita bane a gare su...................
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Pg 31.*
*NOT EDITED. ✖*
^^^^^^^^
Fitarsa babu jimawa ya dawo cikin bedroom en,a yadda ya barshi a haka ya dawo ya iske shi,duk da a rufe yake da irin bargon nan kitty universality (duniyar kuliya) amma hakan yana iya sawa ka gane yadda jikinsa ke girgizawa,a kusa da shi YASEER ya zauna yana jefa masa sannu duk da bawai yana iya amsawa ba,a cikin wannan halin doctor Asir yazo ya iske shi,duk wani gwaji da kulawa daya dace a bashi an masa,amma abun d'aure kan shi ne babu wani k'wak'wk'waran dalili da za'a ce shi ne sanadin ciwon,abunda kawai doctor Asir ya ganowa a cikin bincikensa ba komai ke damunsa ba illa zazzab'i da yayi masa kwaf d'aya,ko daya gama duba shi nan yayi prescribe duk wani magani daya kamata ya sha zuwa safiya aga abunda hali yayi.
Godiya YASEER yayi masa sannan ya rakashi har inda yayi parking, ko da lafiyar Dr Asir shima bai koma ba nan ya wuce da kansa ya nufi hanyar well care,a can duk ya siyo duka magungunan sannan ya kamo hanyar dawowa gida,lokacin daya dawo ko daya shigo d'akin a zaune ya iske YAZEED ya jingina bayansa a jikinsa a jikin pillows hannunsa rik'e da glass cup,kallonsa YASEER ya tsaya yi daga inda yake cike da mamakinsu yadda ya dawo ya iske shi,a hankali yaba ya d'aga cup en hannun san ya kai baki yana squeezing face irin yadda marasa lafiya keyi a lokacin da suke taking drugs,yadda yake matse ido sanda ya kurb'i ruwan YASEER yasa shi daurin nufoshi ya amshe cup en yana kaishi bakinsa,tsamin daya ji ya wuce misali yasa shi daurin kautar da cup en yana tsare shi da ido
"Haba malam me kake da wannan abun kuma kai da kake zazzab'i..??"
Bai bashi amsa ba kawai ya mik'a hannu yana masa alamun ya bashi,hana shi YASEER yayi can kuma ya sake jifansa da tambaya
"Wai me kake yi da ruwan lemon ne..??"
"Ina ruwan ka da abunda nake da shi..?? Kawai ka bani abuna malam.."
"Idan Kafa na baka ai saika fad'a min amfanin da yake maka.."
Wani kallo ya jefe shi da shi sannan ya d'auke kai yana sauke k'afafunsa a k'asa ya zura bathroom slippers ya fice,a baya ya bashi dan ganin inda sashi suna tafe YASEER yana tsokanarsa
"Wai kai toma wane irin ciwo ne wannan kayi sai kace mai iska,yanzun na fita na barka kamar zaka mutu amma na dawo na tarar dakai a zaune..To ko dai iskoki gare Kane ban sani ba..??"
Bai kulashi ba ya shige kitchen abunsa ya sake d'aukan wani cup en had'e da bud'e freezer yana d'auko wasu lemon tsamin masu kyau,yana kallonsa ya wanke sannan ya fara k'ok'arin yankawa,cikin sauri YASEER ya dakatar da shi
"Wai har yanzun bai isheka haka ba,saboda na karb'a yasa zaka yi amfani da wani..??"
"Dan Allah malam kayi shiru haka nan mana,kai wai bakinka baya ciwo ne idan kana magana..??"
Murmushi YASEER yayi yana girgiza kai
"Taya ina tare da kai bakina zaiyi shiru..?? Mutum yayi ta abu kamar wani d'an goge.."
Waiwayawa yayi ya kalleshi yana tsaye jikin cabinet ya had'e hannayensa a k'irji
"Ni kake cewa d'an goge..??"
"Kai enfa..! Yo mene marabarka da su..?? Ta wani side enma zan iya cewa gara su da kai ai.."
Dai² lokacin ya gama abunda yake ya d'auko cup en yana juya shi a hannuna yana kallon ruwan lime en,ba tare da yayi magana ba ya fice zuwa parlor, a nan ya zauna saman 1 seater gudun duk kada ya zauna inda yasan YASEER zai zo ya zauna har ya same shi,a bayansa ya fito yazo ya nemi guri ya zauna yana kallonsa kawai har zuwa sanda ya shanye tas ya ajiye cup en had'e da yin baya ya kwantar da bayansa jikin seat en,tab'e baki YASEER yayi cikin yanayi na fuska² ba tare da walwala ba ya furta
"Sai ka d'auka prescription en ai ka san yadda za kayi da su.."
Ba tare daya kalleshi ba shima YAZEED en ya bashi amsa
"Ko kuma kasan yadda za kayi da su ba,dan ni dai banga amfanin da zasumin ba yanzun.."
K'ureshi yayi da ido kafin ya furta
"Kace mene..??"
"Abunda dai kunnenka yaji shi na fad'a."
Bai ko sake tabka masa ba ya zame ya kwanta yana mik'e k'afafunsa yana fad'in
"Idan Kafa dama kana iya zubarwa ai k'arshen rashin so kenan.."
Shiru suka yi duka daga haka ba tare da wani cikinsu ya sake kallon d'an uwansa yace masa ko da ci kanka ba.
^^^^^
A b'angarensu Adda kuwa zuwa wannan lokacin farin ciki ne fal ransu dan yadda suka samu nasarar k'addamar da aikinta da dama dalilinsa ne suka zo gidan ba dan amsa gayyatar da aka musu ba.
Tuna yadda al'amarin ya faru yasa Aisha sakin murmushi tana fad'in
"Kai Adda gaskiya ko da har naji duniyar tamin k'unci,amma yanzun kam na gama samun nutsuwa,dan na tabbatar ta wannan hanyar ne kawai Yarima zai iya zama mallakina.."
Dariya itama Adda'n tayi kafin ta waiwayo tana cewa
"Ai ba iya ke kad'ai al'amarin ya so nawa tsorone ba har dani kaina,yo kina ganinfa irin kud'in dana narkar akan maganin nan amma ace hartsawon saman da mintuna arba'in babu abunda ya faru ni da aka cemin da zaran kin je kusa da shi ya shak'i k'amshin turaren shi kenan zai buk'aci ruwa kuma sai naga abu ya gagara.."
"Humm! Ai Adda ki bari kawai,wollahi nima dai da naga har mun bar gurin babu abuna ya faru nan duk jikina yayi sanyi na gama fidda rai..Sai kawai ga Aunty Salma ta shigo tana neman ruwa,kin san ko a lokacinfa da Fulani ke tambayarta,duk nayi tsammanin itane zata yi amfanin a shi,Amman sai naji tana nawa Fulani labarin wai Yarima ne yake neman ruwan..Ai wollahi yadda kika san zanyi sujjada dan farin ciki a lokacin."
Murmushin dai Adda ta sake yi kafin ta furta
"Ai nima abunda naji kenan yasa ni tunanin ta yadda zanyi na hana ita Salman kai ruwan,shi yasa na tsare ta da jiran yaushe gamo har sai data nemi ki d'auko ruwa ki kawo aika masa da shi..Kinga a nan ai muma mun sani dama ba..!"
"Sosaima kuwa Adda ta tunda har ya sha na gani da idona ai zance ya k'are..Wama yasan a halin da yake ciki yanzun Ohoo..!"
Dariya suka yi su duka lokacin da Adda ke fad'in
"Yo a wane hali kuwa yake daya wuce fad'awa cikin masifar da duk iya neman maganinsu ba zasu samu ba..?? Tunda dai hankalinsu bazai tab'a kaiwa kan abunda mu muka aikata ba.."
"Aifa kam Adda gara da kika kawo wannan shawaran dan nasan ta wannan hanyar ce kawai Yarima zai iya zama nawa,duk iya aure²n da zaiyo k'arshe dole a hak'ura dani idan na nuna na dawo zan iya zama da shi a duk halin da yake ciki..Kinga daga nan sai kawai musa a karya abunda aka yi ba.."
"Ki bari kawai ke dai..Ai idan sun san wata basu san wata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 63