Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Unknown person da yake kiranta da unknown number ne ya sake kiranta,tana d'agawa ta jiyo muryansa yana fad'in "Inno..! Ki ci gaba da tafiya,da zaran kinzo dai² k'ofa sai kiyi kamar zaki wuce,amma kada ki matsa daga nan..Hood zasu ji da AL'AMARIN.." Wahalallen ajiyar zuciya ta saki sannan ta amsa masa da "toh",taci gaba da tafiya abunta not minding buh deeply a matuk'ar tsoracen take,har ta kusa daf da k'ofar wancan d'ayan motan da ta fara nufa ganin bata yi yunk'urin dawowa ba,matuk'in motar yayi warming motan yana sake matsa gear cikin shirin ko ta kwana,sannan ya taso kanta angrily, ns desertion da matsiyacin gudu,cak Inno ta tsaya a gurin cike da fargabar ganin yadda motan tayo kanta da masifaffen gudu na wuce hankali,shima JIBO kansa ko daya hango abunda yake shirin faruwa a masifen shima ya k'unduma wasu gawurtattun ashar sannan ya taso with craziest speed,yadda dukansu suka take motocin da matsiyacin gudu suna nufarta tamkar a irin raceway d'innan AL'AMARIN yake faruwa ko a film d'in SPEED yasa tashin hankali tsantsa yin appears a fuskarta musamman ganin yadda duka motocin biyu suka dumfarota gadan² "Sir Inno..!" Abunda Hood ya iya furtawa kenan saboda tsabar fargabar data lullub'e shi gashi ko kaiwa inda k'ofar yake bata yi ba bare yace ko za'a iya samun wani ya fitowa ya bata kariya,a masife Yarima yake tambayar sa "Ku d'in me kuke yine da bazaku fito ba..??" "Sir..bata k'araso matsaya bane.." "Kuyi abunda ya kamata..Kada ku tsaya cewa sai ta k'araso coz za'a iya samun matsala.." "Ok..Sir.!" Cikin fad'a² irin na son kama aiki tuk'uru Hood yaci gaba da umarni "Heyy.! Guy's kowa ya zama cikin shiri zamu fita,dole ne ya zama mun bada rayukanmu wajen wannan yak'in,imma muyi nasara ko mu ayi nasara akanmu..Ba musan wane irin weapons ne a tare dasu ba,haka adadinsu,amma bana tunanin zasu haura mutane uku-hudu a cikin ko wane mota,buh babu tabbaci,zasu iya yin k'asa da adadin dana fad'a,saboda haka a kiyaye..Sannan mu tabbatar sun koma cikin k'oshin lafiya..." "Ok..boss..!" Duka suka fad'a daga mabambantan mab'oyarsu,motocin su JIBO kuwa a yadda suka taso gadan² d'innan har sunyi daf da inda Inno take,babu yadda za'ayi ace yadda suke kusa² basu tab'a taba,dan gaba d'aya kanta suka nufa bawai kowa kan abokin gabansa ya nufa ba. Hood daga gefensa shima dai² lokacin bayan ya gama musu jawabin,cikin sauri ya furta "Kowa yaa shirya..??" Suka amsa da "ehh Yallab'ai.." "A afka musu..!" Like expelled of arrows haka suka dunga bayyana a gurin,cike da dabara suka fara had'ewa suna circuting field d'in suna kuma matsowa kusa da son saka motocin a tsakaninsu,Hood daya kasance babba ganin har lokacin motocin suna kan gudu basu k'arasa ba tuni yayi harbi sama da son dakatar dasu duka,dukansu babu wanda bai ji harbin ba,amma saboda tsabar k'awa zuci da son idar da aikin dake gabansu duka yasa suka k'i tsaiwa saima ci gaba da nufarta da suke,,,suma su hood d'in basu fasa matsowa ba bindigunsu duka suna saita motocin dasu JIBO suke,harbi na biyu hood ya sake yi zuwa sama cike da warning d'insu kan sufa dakata amma ina duk sunyi biris,jin hakan ya tabbatarwa da Yarima sun fito kuma suna bakin aiki,,,Inno kuwa koda taga haka jikinta tuni yayi sanyi da lamarin duk da taga security'n daya ce amma lamarin ya shallake tunanin ta,runtse idanunta kawai tayi cike da sadaukarwa tana karanto kalimatush-shahadah zuciyarta cike da sarewa,,,ta baya taji an finciketa zuwa ciki sannan aka maida k'ofar aka rufe,bata san waye ba kamar yadda bata ga fuska ba kasancewar idanunta duka suna kulle,abunda kad'ai zata iya fahimta kuma ta bada labarin ta gani shi ne tahowar motocin amma baya nan babu abunda zata iya fad'a ya faru saboda firgicewar da tayi,a hankali ta waiwaya bayanta tana sakin ajiyar zuciya dan ganin waye wannan mai kasada ta biyun daya iya fita a dai² wannan lokacin,da fuskar Yarima tayi arba tsaye a bayanta tamkar wani jarumin sadauki yana kallonta shima da wani irin yanayi,Jeeddah kuwa koda ganinsu cikin k'oshin lafiya da d'an gudunta ta nufo su duka,tana isowa gabansu sai ta tsaya tana kallonsu duka zuciyarta cike da tunanin waye yafi kamata ta fara jin lafiyarsa..?? Mahaifiyarta,mijinta ko kuwa d'anta..??,kasa tantancewa tayi saboda yadda zuciyarta ta shiga taraddadi sai ta kaallesu duka tana fad'in "Kuna lafiya..?? Babu abunda ya faru ko..??" Tana yi tana sake dubansu duka,d'an murmushi ya saki sannan ya rik'o hannunta yana kallon Inno da cewa "Muje Inno.. Zasu yi handling case d'in..!" Ita kam Inno a b'angaren ta har yanzun bata fita a shock d'in da take ciki ba,da kyar ta iya samun damar d'aga masa kai sannan suka juya abunsu,,,,a dai² lokacin da Yarima ya janye Inno a hanyar,da matsawar su a gurin da isowar motocin duka bai yi minti biyu ba,koda faruwar hakan maimakon ace kamar yadda suka yi nufin taka ta da motocin suna hango abunda ke faruwa suma nan suka fahimci duka sun fad'a tarko,a tare suka juya akalar steering da kaucewa a hanyar juna suka kuma yi kan su Hood gadan²,yanayin yadda suka ga sun juyo kansu yasa suma su hood d'in basu fasa nufar su ba,sai dai ganin yadda suke nufo sun ya tabbatar musu baza su saurara ba idan sun zo zasu bi takansu ne yasa hood cikin bada umarni ya furta "Fire them..!" Yana fad'a ko gama rufe baki bai yiba k'arar harbe²nsu ya fara tashi,,,sun d'auki mintuna suna harbin su amma ko kad'an basu samu damar samun ko da jikin motocin ba kamar wad'anda suka sha magani k'arfe,dan yadda matuk'an ke wasa da motocin da kuma hankulansu a gurin abun kamar wani wasan kwaikwayo,cikin hikima,kwarewa gami da sanin makamar aiki hood yayi attacking mota d'aya daga ciki bakinsa na fad'in "Bismillah..!" Dai² nan ya saki kunamar bindigarsa,k'arar sautin k'arfe da yake gogar titi yasa dukansu fahimtar anyiwa mota d'aya lahani,take duka suka sake bada himma akan mota ta biyun,basu d'auki wani lokaci mai tsayi ba itama suka yi nasarar harbin tayarta ta baya dan basa so suyi loosing na masu laifin,sunfi so su kamasu a hannunsu suna masu rai,tasamma motocin suka yi bayan sun tabbatar duk baza su moru ba a yanzun ko dama ace sunyi yunk'urin gudu to baza su tab'a kaiwa labari ba,duka suka yi circuit na motocin biyu suna sake attack nasu,hood na kan gaba cikin bada umarni ya ce "Ku fito..!" Ba tare da musu ba aka bud'e motocin a lokaci guda sannan mamallakan suka fito,mutum biyu daga motar farko,yayin da JIBO shi kuma ya bayyana shi kad'an sa daga motarsa duka suna masu yin surrender,hannayensa su yaran hood suka murd'e zuwa baya sannan suka mak'alawa kowannensu handcuffs suka tisa k'eyarsu,daga nan bomphai suka nufa dasu ainihin headquarter saboda girman laifinsu ya wuce su kaisu station. A gefen su Yarima kuwa tuni suka isa apartment d'insu cikin k'oshin lafiya ba tare da sanin kowa ba,saboda dare ya d'an fara nisa a lokacin,bedroom d'inta Jeeddah taja Inno kai tsaye,bayan ta zaunar da ita ta fita,ruwa mai d'an karen sanyi ta d'auko sannan ta dawo ta tsiyaya a cup ta bawa Inno,bata k'i karb'a ba dan har lokacin tsoronta bai gushe ba,dan yadda taga tashin hankali k'arara a yau ya wuce ta kwatanta. Shima Yarima kai tsaye bedroom d'insa ya nufa,da shigar sa kuwa ta kan kayan jikinsa ya fara,sai daya ragesu sannan ya zauna a bakin Royal bed d'insan yana sakin gawurtaccen ajiyar zuciya da yiwa Ubangiji godiya,ya kwashe mintuna sama da ashirin a haka sannan ya jiyo maganar hood a kunnensa "Hello..Sir.!" Gyara zaman sa yayi sannan ya amsa "Yane Hood..!?" "Congratulations sir..we arrested them.." Numfashin samun nasara ya sake saki yana lumshe idanunsa cike da shauk'i yayi hamdala ga Ubangiji sannan ya furta "Thank God..! Buh u have to take a good care of them..they're criminals so sai munyi taka tsantsan saboda mu cimma burinmu wajen kamo sauran,nd daga yanzun zuwa safiya bana so ko kad'an u saurara musu..!" "Ok Sir.. In sha Allah za muyi yadda kace.." Daga haka Yarima yayi disconnect na wireless bluetooth d'in dake kunnensa sannan ya kwanta da baya,,,a bedroom d'in Jeeddah itama ko data gama kwantarwa da Inno hankali,sallama tayi mata ta kama hanyar fita a room d'in ba tare data iya mata maganar AHYAN ba duk da yadda take k'aunar son jinsa a jikinta,har ta kai bakin k'ofa Inno ta kirata "Ke..! Meye ne haka kike yi..??" Juyowa tayi fuskarta da alamun tambaya,had'e rai Inno tayi sannan ta furta "Waye kika bawa yaron ne..??" A sab'ule ta dawo ta tsaya tana kallonsa ta gefe tana kuma boy'e yanayin dake tattare da ita na kewarsa "To ni Inno meye ne zan masa kuma..!?" Kallon sakarcinta Inno ta tsaya yi da bakinta a bud'e,kafin ta sake b'ata rai tana cewa "Kin zo kin d'auke shi ko kuwa saina sab'a miki..??" Sai data harare shi tamkar gaske sannan ta nufeshi ta d'auko tana tafe tana sakin k'unk'uni k'asa²,ita dai Inno tana jinta sai dai bata kula taba ta dai rakata da ido har ta fice bayan ta mata sallama,tana fita a d'akin wani shauk'in murna ya kwasheta nan ta tsaya tana sake k'ank'ame shi a jikinta da y'an hawaye a idanunta,ta shafe sama da mintuna uku a gurin sannan ta fara d'aga k'afarta ta nufi bedroom d'insa,tana tafe tana sauraren sak'on da yake bayarwa akan hukunta masu laifin har ta shigo dai² lokacin daya kwanta,da sallama a bakinta ta shigo,yana daga kwancen ya amsa mata ba tare daya waiwayo ba,k'arasa shiga tayi ciki tana binsa da kallon mamaki dan ganinsa kwance daga shi sai boxers a ranta ta furta "Shi kuma yaushe ya aikata hakan..?" Idanunta ta janye akansa cikin kasala dan yadda ganinsa kad'ai yayi k'ok'arin taso mata da tsohon tsumin ta,sannan ta koma saman resting chair ta zauna da AHYAN a hannunta tana kallonsa tamkar yau ne farkon ganinta da shi,nd tana nuna irin kamar bata damu ba ko bata sanma halin da Yarima yake ciki ba. A b'angaren su JIBO kuwa.............🤣😂 *Sai kunyi hak'uri da turancin coz na y'an koyo ne...*🙈 #Follow #Vote #Comment. Then #Share. *®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉 💠💠💠💠💠 *©® 2019..*  *WANI AL'AMARIN..!*💥 *(Book 2)* 💣💣 💥 *иα* *♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡* *Wattpad&Instagram* *@Jeeddahmu898* *______________________* *fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/ *_____________________* *LOYAL TO MY FAMILY.♥* بسم الله الرحمن الر حيم. ^^^^^^^^^^^^^^^^^ ___________________ *BOOK 2. 📓* *Pg 36.* ^^^^^^^^ *#Doubtable* A can headquarter kuwa lokacin da su hood su isa da su JIBO,d'akin horo kai tsaye akayi da su,oga hood yana gefe guda a zaune yana kallon su har aka gama d'aure hannayensu da k'afafunsu a jikin wasu manyan k'arafa dake tsaye,JIBO shi ne a farko dan haka shi Hood ya fara kallo sannan ya furta "Mene sunan ka da kuma alak'ar ka da wannan case..??" Shiru yayi fuskarsa babu alamun ya rusuna akan lamarin duk da shiga hannu da suka yi,sake maimaita masa tambayar yayi amma shiru yak'i amsawa,a fusace A.S.P Hood ya ce "Ku wanke shi.." Kafin ace kobo tuni har jikin JIBO ya jik'e da ruwa shataf,banda tsiyayar da ruwa babu abunda yake "Zaka sanar damu abunda muka tambayeka ko kuwa..??" Ya sake yin banza da su,yanayin kallon da hood keyi masa ya tabbatar ba zai magantu ba,take ya bada umarnin suyi ta dukansa har sai yayi magana,masu jiran kad'an had'e da fushin wani tuni suka dirar masa da jibga dan yadda suke jinsu kamar zasu ci babu,kan mutum biyun Hood ya juya yana k'are musu kallo cikin matuk'ar d'aurewar fuska sannan ya furta "Ku kuma fa..?? Zaku bada had'in kai ko kuwa..??" Suma d'in shirun suka masa,take shima ba tare daya sake bi takansu ba yasa aka jik'a su tsaf sannan aka fara casar su kamar yadda akewa JIBO,gashi dai ana dukansu suna ihu amma da zaran an tambaye su sai suyi shiru tsabar taurin kai irin nasu duk yak'i barin su suyi magana. A can masarauta kuwa,dai² lokacin da Yarima yake kwance sai daya shafe tsayin lokaci da lumsassun idanunsa,deeply yake yiwa Allah godiya bisa nasarar daya bashi ya d'ora shi akan abokan gabarsa ba tare da sun samu damar kub'uta ba,yana cikin wannan tunanukan nasa ya jiyo ta a kusa da shi,idanunsa ya ware yana kallonta ta upsidedown,tana kwance a rigingine da AHYAN a saman jikinta haka nan iya tsayin lokacin data shigo har yanzun daya kalleta hijab kad'ai ta iya cirewa sai takalmi,sake lumshe idanunsa yayi a hankali ya furta "A hakan kike tunanin zaki yi bacci..??" Ta tsinkayo muryansa can k'asa,kasancewar itama idanunta a rufe suke sai ta bud'e su ta d'an kallo shi,bata ce komai ba ta sake rufe idonta tana sake gyara kwanciya abunta,jin shirunta bata amsa ba kuma bai ji motsi ko alamun tashin taba yasa shi mik'ewa ya zauna while his back ya jingina da pillow da tashin sa ya d'an sake kallonta ba tare daya sake magana ba ya mik'e a gurin ya nufi side d'in da take,AHYAN ya d'auka daga jikinta ya manna masa kiss a forehead zuwa chicks d'insa,tunda ya d'auke shi ta bud'e ido tana kallonsa har sanda yayi masa addu'o'i ya kwantar a saman cradles d'insa dake ta side d'insa,not minding ya juya ya nufi hanyan bathroom cikin takun isassun maza,idanunta har lokacin akansa dan ita dai Allah ya sani har lokacin zuciyarta ba'a nutse take ba da barin AHYAN saman cradles d'in,yana shigewa ta sake d'auko shi tasa a jikinta,,,ya d'auki tsayin mintuna ak'alla sha biyar sannan ya fito d'aure da towel a waist d'insa,akansu idanunsa suka fara sauka,yana kallonta ya hango AHYAN a inda ya d'auke shi,girgiza kai kawai yayi sannan ya shiga shirin abunsa ba tare daya sake ce mata komai ba har ya gama murzawa jikinsa sanyayyun turarukansa ya shirya kansa cikin pyjamas masu kalar red wine,fuskarsa har lokacin babu wani wadataccen fara'a kamar yadda yake kullum haka take yanzunma amma fa ga sauran al'ummah,sai da yayi sallar nafila raka'a biyu yayi addu'o'i sannan ya nad'e pray mat d'in,inda ya tashi ya koma ya mik'e bayansa ba tare da yace mata komai ba yayi addu'o'insa ya shafe jikinsa sannan ya juya mata baya saboda ta san cewar tayi masa laifi,sannan yayi deactivating fluorescence sai lampshade daya bari,idanunta ta zuba masa tana kallon yadda ya bata baya,ko da bai fad'a mata ba ta karanci dalilin da yasa shi yi mata hakan,wanda ko da a wad'ancan kwanakinma da bashi da wani isashen lokacin su hakan bai tab'a faruwa ba,kuma ta sani sarai matuk'ar ba tayi wani abu da baya so ba baya tab'a mata hakan,magana take son yi amma ta kasa saboda fargabar abunda zai biyo baya,ta d'auki lokaci tana tunanin abunda tayi wanda ya zama laifi daga dawowarsu zuwa yanzun da suke kwance amma ta kasa ganowa,abu d'aya ne ya fad'o mata kuma take tunanin shi ne ya haddasa faruwar hakan,,,a sab'ule ta mik'e ta nufi cradles d'insa ta shimfid'e shi cike da son bin umarnin da zuciyarta take bata sannan ta cire kayanta ta nufi bathroom,ruwa ta had'awa kanta mai d'umi ta zuba turaruka iri daban² masu sanyin dad'i da tada hankalin mai shak'arsu ta shige ciki tayi luf,ta jima tana wanke jikinta da lailaya shi tamkar bazata gama ba sannan ta wanke jikinta da ruwa ta fito d'aure da towel,while hannunta kuma da mini towel da take tsane jikinta da shi,turaruka kad'ai ta sawa jikinta sannan ta nufi inda yake tana wani shu'umin taku mai sawa tsumin mutum ya motsa lokaci guda,tun daga tashinta har ta shige bathroom ta fito zuwa yanzun da take nufo shi abunda bata sani ba duk yana kallonta,haka nan duk wani motsinta akan idanunsa take yinsa,sai da yaga ta kusa k'arasowa ne yanzun yayi maza ya kulle idonsa yana had'iye yahun kwad'ayi,bata bawa kanta wahala ba wajen saka wasu kaya dan tasan muddin ta shiga hannunsa tofa kayan babu amfanin da zasu yi mata,ta gabansa ta tsaya tana gyara zaman towel d'inta daga bundling zuwa stuck,a hankali ta rab'a ta shige cikin jikinsa duk da gurin data rab'a ta kwanta d'in bawai ya isheta bane,yana jinta da duk abunda take amma izzar mulki ta hana shi motsawa,towel d'in jikinta tayi wurgi da shi coz tana ganin zai iya bata damuwa wajen yak'in data shirya tana sake matsarsa tana goga masa na shanunta a fuska,hannayenta kuwa tuni ta cusasu cikin blazer dake jikinsa tana shafa shi ta ciki tana kuma murza teat d'insa,still bai motsa ba sai dai can k'asan ransa yana jin abunda take masa,k'asa² ta bud'e baki muryanta na kyarma ta fara kiransa "Yah Prince..." Shiru bai amsata ba,dan haka sai ta tsinci kanta da fad'in "Am sorry Yallab'ai..!" B'oyayyen murmushi ya saki cikin ransa yake tambayar kansa "Wato ta san tayi masa laifima kenan..??" A zahiri kuwa izza ta hana masa yin magana duk da yana tsananin buk'atar ta da k'ishirwar kasancewa tare da ita a cikin kwanakin,muryanta da tsoro ta sake bud'e baki lokacin kuwa harda wasu munafukan hawaye data tara a idanunta cikin wani fitinannen muryanta take masa magana a kunne tana sheshshek'ar kuka "Pleasee Yallab'ai.. I know i was mistaken buh am really sorry...Forgive my grievance.." Wannan karon kam kasa ignoring nata yayi saboda salonta ya isar da sak'on da take son isarwa,amma duk da haka bai nuna mata kai tsaye ba sai ma matsawa da yayi a jikinta yana cewa "Ohh..Kin san kinyi laifi dama..??" Sake matsoshi itama tayi wannan karon koda ta tashi fuskarsa tasa between her boobs tana d'an motsawa kad'an cikin salonta,k'ok'arin shanyewa yaci gaba dayi duk da yadda jinin jikinsa yake wani irin combustion "Pleasee Yallab'ai.. It was mistaken.. Am sorry..buh i promise..it won't happens.!" Tab'e baki yayi yana k'ok'arin juyawa dukansa tayi saurin cakumo shi itama dukansa sannan tayi k'asa ta had'e bakinsu gurin d'aya ta fara aika masa mahaukatan kisses,kwakwaran motsi kasa yi yayi saboda yadda sak'on ya zo masa a bazata,sai daya barta tayi iyayinta sannan ya karb'i ragamar,cikin rikicewa ya sake rik'ota sosai suka ci gaba da aikawa juna sak'onni a zafafe kamar zasu ci babu,,,,basu suka hak'ura ba sai da suka murji juna son rai suka kuma tabbatar basa tare da ko wane irin damuwa,sannan bacci mai dad'i yayi awon gaba da su rungume da junansu,suna masu tsananin farin ciki. A gefen Inno kuwa yadda AL'AMARIN ya kasance a wannan daren,tun bayan fitar Jeeddah a d'akin nan ta rakata da kallo na tsantsar tausayawa da al'ajabi,sai data shafe tsayin lokaci a wannan halin na tunane² iri² kafin ta yunk'ura ta mik'e,bathroom ta shiga ta d'aura alwala sannan ta fito ta daidaita akan pray mat ta kabbara sallah,,,tsayin wannan daren sam Inno bata iya runtsawa ba har akayi kiran farko tana saman abun sallan,,haka nan ba ita ta kwanta ba sai bayan data idar da sallar asubah sannan ne ta samu damar mik'ar da bayanta tana ci gaba da y'an addu'o'i cikin haka nauyayyen bacci ya d'auke ta ba tare data shirya masa ba. WASHE GARI... A cikin gida kuwa lokacin da gari ya gama yin haske al'ummah kowa ya fara hada² da k'ok'arin fita uzurin gabansa,,sai kuma labarin harbe² ya fara tashi a tsakanin jama'ar da suka ji afkuwar AL'AMARIN,duk da bawai wannan badak'alar data faru akan idanunsu ta faru ba amma mafi yawa daga cikin al'ummar dake cikin gidan sunji harbe²n da tseren da motocin suka yi,buh a tunanin mafiya yawa daga ciki duk sun d'auki hakan a matsayin hari aka kawo gidan,sam babu wanda tunanin sa ya kai kan ai nihin abunda ya faru. Cikin harabar gidan kuwa inda AL'AMARIN ya faru duk inda mutum ya kalla shells ne barbaje a gurin,wannan kad'ai shiya sake tabbarwa jama'a abunda ya farun bisa ga Zatonsa,haka nan suna ganin cewa ba k'aramin d'auki ba dad'i aka yi da y'an ta'addan ba,,duk inda mutum zai wuce kuwa da zarar ya tarar da crowd maganar kad'ai ke sake hab'aka,haka nan dai kowa da abunda zaka ji yana fad'a amma har wannan lokacin babu wanda yasan actual na abunda ya farun,sai dai jita² kad'ai da aketa yad'awa. A cikin gida kuwa tuni labarin komai ya risko fada,wanda tun kafin fitowar Maimartaba tuni har an tattaro shells d'in da suke gurin an kawo masa,yayi mamaki sosai da jin abunda yawancin mutane ke fad'a amma shi d'in haka nan yake jin bai amince da abunda suke fad'a ba,tun kafin ya kammala shirinsa yasa duka ayi masa magana da yaransu cikin umarninsa na kasancewarsa shugaba yace duk su hallara a b'angaren Hajiya,within 20 minutes duka sun iso shi kad'ai suke kan jira kowa cikin zuciyarsa cike da son sanin dalilin kiran duk da suna ganin kamar taron bazai wuce kan maganar dake yawo a gari ba na kawo harin da akayi gidan sarautar.Isowar maimartaba ya bawa gaba d'aya ahalin damar yin shiru daga hirarrakin da suke yi da juna,kowa ya sake nutsuwa yana jiran jin cewar maimartaba,,sai da akayi addu'o'i sannan ya kalle su d'aya bayan d'aya yana mai jinjina AL'AMARIN a ransa kafin ya fara magana "Kamar yadda muka sani cewa duk wani daya kwana a wannan gida namu,zuwa wannan lokacin ya samu labarin abunda yake faruwa,kamar yadda maganar ta zagaya gari gaba d'aya kan cewar an kawo hari wannan gidan.." D'an dakatawa yayi sannan yaci gaba "Alal hak'ik'a mu bawai mun amince da wannan batun bane,saboda har wannan lokacin jita² ke yawo akan maganar amma babu wanda yazo yace ga ainihin abunda ya faru,ko anyi akan idanunsa ya zayyana mana abunda ya gani,,,,amma mun sani cewa cikin mu baza'a rasa wad'anda suka san yadda AL'AMARIN ya faru ba,,,saboda haka muke fatan wad'anda suka san da faruwar hakan za su mana bayani.." Ko da yazo nan shiru yayi yana bin gaba d'ayansu da kallo coz a b'angarensa tuni yasan komai daya faru zuwa lokacin,buh yayi haka ne ba don komai ba sai don yana son bawa Yarima damar fad'an abunda ya farun,amma sai shiru ya ratsa ilahirin parlor'n,maimartaba kuwa idanunsa duk wannan maganar da yake basa kan kowa sai kan Yarima,koda yaga bashi da niyyar yin magana take sai wani shawaran ya fad'o masa,Abba Galadima ya fara kalla yana tambyarsa "Aliyu..! Shin ko k'asan abunda ya faru a wannan daren daya gabata..??" Kai tsaye kasancewar shima Abban ya fahimci abunda maimartaba yake fad'a yayi murmushi sannan ya furta "A'a Yaya..Ko kad'an ban samu wannan labarin ba.." Jinjina kai maimartaba yayi idanunsa akan Yarima sannan yaci gaba da tambayar su d'aya bayan d'aya har ta kai ga ya kai kan matan,amma amsan d'aya ne duka basu sani ba,haka yayi ta tambayarsu koda yazo kan Jeeddah sai ya tsallake bai tambayeta ba

Chapter 53 of 63