ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
_We were disturbed and saddened by the untimely death of ur Grandma (Cweet Hubbeey),May her soul rest in jannatul-firdaus..👏🏻_
___________________
*Masoya ina mai baku hak'uri bisa rashin ganin posting d'ina akan lokaci da bakwa yi,ni kaina ba'a son raina hakan ke faruwa ba,illa transformer d'inmu daya sake samun matsala ranar sallah,amma in sha Allah matsalar ya kusa zuwa k'arshe,ku k'ara hak'uri ni kaina nasan hakan baya muku dad'i ba,bare kuma ni..#har kullum ina tare da ku.*
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 5.*
^^^^^^^^
Tun bayan da suka rabu da mai maganin haka nan Yarima yake jin bai yarda da shi ba haka ma bayanin da yayi musu,kawai dai ya bi abunda YASEER ya fad'a ne ya karb'a maganin saboda yana son ace ko yaya shima ace ya faranta masa,amma ba wai dan yana da tabbaci akan zaiyi amfani dashi ba ko ingancin maganin ba,a zuciyarsa kuwa tuni ya gamma k'udurcewa akan babu abunda zaisa shi yin amfani dasu dan shi a rayuwarsa sam bashi da burin amfani da wani traditional remedy,bare kuma wannan daya ta'allak'a da wannan case d'in,a nasa ganin tunda duk wani bincike ya tabbatar masa lafiyarsa k'alau babu wani sauran abu daya rage masa,sanda suka dawo gida ma ko kafin su rabu sai da YASEER yayi ta jaddada masa yayi fa amfani da maganin akan lokaci saboda su san a irin hierarchy d'in da suke,"toh" kad'ai ya iya ce masa,sai dai ko da YASEER ya kalle shi tuni ya gano a mode d'in da yayi maganar,yadda ya amsa masa yasa shi saurin dakatar da shi dan yasan halin abunsa tsaf zai iya zubar dasu ba tare da yayi amfanin da aka ce masa ba,da rawar baki YASEER yake cewa
"Wait broah..! So nake na rok'e ka wani abu.."
Kallonsa Yarima yayi yana nazarin sa dan bai san abunda zai fito daga bakinsa ba,yadda yayi shiru yasa YASEER cewa
"U don't consent me..are u going to scatter my eye with soil..??"
Girgiza masa kai yayi alamun a'a ba haka bane
"To yaya ne kake so nace maka..?? Ko kuwa bazaka iya min alfarma ba duk da yadda na tsaga bulle na tambaya..?"
"No broah.! U surpassed thus shear..Ka fad'i duk abunda kake so.."
Jinjina kai YASEER yayi cike da nuna jin dad'i yace
"Dama ba komai bane face ina so ka yimin alk'awarin duk abunda nace zaka yi min.."
Kallonsa kawai Yarima yake kafin daga bisani ya jinjina masa kai fuskarsa d'auke da murmushi
"Ni magana zakamin ba wani nodding ba,nima ai baki na bud'e nayi magana so kawai ka fad'a min,idan ina da wannan alfarmar a gurinka..idan kuma babu to kaga gara na sani tun kafin na fad'a kace mun baza kayi ba,kasan zanji haushi ne,kuma bazan tab'a jin dad'i ba..nd harma zan ta kallonka da abunda kayi min..."
"Fad'a mana ina sauraronka.."
"Ohh God..! Nifa duk ba wannan nake so kace ba,just promise me duk abunda nace zakamin..that's it.!"
"Ok..! Go ahead i will do it for u.."
"Gud..Akan wad'annan remedy's d'in da aka baka ne nake son ka yimin alk'awari za kayi amfani da shi kamar yadda aka ce.."
Shiru yayi a maganar yana jiran yaji me Yarima zai fad'a,ga mamakinsa sai gani yayi kawai yayi murmushi
"In sha Allah kada ka damu zanyi.."
Shima yana dariya ya rungume shi yana fad'in
"Thank yuh broah,I know kai d'an uwa ne na gari,mai fatan ganin farin cikina,Allah ya taimaka yasa muyi nasara.."
"Ameen" ya amsa masa sannan suka yi sallama kowa yayi apartment d'insa,sanda ya shige a bedroom ya zubesu saman bedside drawer ya shiga rage kayan jikinsa,boxers da singlet kad'ai ya rage wanda suke farare tas sannan ya shige bathroom d'in da niyyan watsa ruwa,sanda ya fito a wankan bayan ya gama shirinsa cikin kaya masu sauk'in nauyi,yayi kwanciyar sa saman resting chair dan ya d'an huta.
^^^^^
A can gefen su ladidi kuwa duk wani tuggunsu a wannan lokacin bai wuce ace yau yarima ya rabu da Sajida ba,dan yadda suka k'wallafa ransu akan had'a auren Yarima da Aisha,ba dan komai ba sai don suna ganin hakan kawai shi ne mafita a garesu da zata sada su da cimma nasarar FANSAR shekaru da dama da suke ta k'ullewa.
Ga Aisha kuwa,tunda take a iya tsayin rayuwarta wannan lokacin shi ne karon farko da take jin nadamar ayyukan data jima ana ata tana aikatawa,har cikin ranta ji take tayi asarar wani abu,a baya kam ta jima tana nadama akan abubuwan da ake sata ta aikata,sai dai wannan karon nadamar tata tafi tasiri fiye da ko wane lokaci,har tana jin inama tana da wani guri da zata koma dan taci gaba da rayuwa tunda bata san ainihin waye mahaifanta a Royal palace ba bare ta tunkare su,sai dai a wannan lokacin kam tayi d'amara ta kuma yi k'udurin koma waye zata bi dan ta gano ainihin iyayenta,amma to waye ya kamata ta nemi shawarar sa..?? Sannan waye zata nema domin ya bata goyon baya gurin gudanar da wannan binciken..?? Tabbas tasan wannan ba k'aramin aiki bane a gurinta,shi yasama yanzun bata cika yawan fita ba,dan tana son bawa zuciyar ta da k'wak'walwarta cikakken lokacin da zata tantance mutanen da ya kamata ta nema domin su taimaka mata,a kullum tunaninta da burinta kuwa baya wuce ta samu mafita da kuma wanda zai bata goyon baya wajen bincikar mahaifan ta..
^^^^^
Da dare koda ya gama shirin kwanciya bacci,sanda ya nufi royal bed d'insa da niyyar kwanciya nan ya baje a kai,yana daga kwance ya mik'a hannunsa da niyyan kashe bedside lamp idanunsa suka sauka kan remedies d'in daya watsar nan,rufe idanunsa yayi sanda ya tuna da irin maganar da suka yi da YASEER da irin alk'awarin da yayi masa akan zai yi amfani da maganin,kashe lamp d'in yayi yaja panoptic ya rufe jikinsa had'e da rufe idanunsa da niyyan bacci,amma kuma sai yaji ba zai iya yin hakan ba dan jin yadda zuciyarsa ke tunkarar da shi girman alk'awari,ya jima da idanunsa a bud'e kafin ya janye panoptic d'in ya saukar da k'afafunsa k'asa,a hankali ya mik'e daga zaman da yayi ya nufi inda ya ajiyesu sannan ya d'auka ya fita zuwa hanyar kitchen,sai da yayi y'ar tafiya a cikin parlor d'in kafin ya riski inda ainihin kitchen d'in yake,da zuwansa ya duba cup mai kyau ya d'auka amma duk da haka sai daya tara sa a bakin tap ya dauraye da ruwa sannan ya bud'e freezer ya d'auka yoghurt d'in L&Z kasancewar shi mara zak'i ya b'alle murfin,kusan rabin cup d'in ya tsiyaya sannan ya kawo wani brown d'in garin magani dake k'ulle a k'aramar lesser ya dai²ta misalin 1 tablespoon yasa a cikin yoghurt d'in yana juyawa,sai daya tabbatar ya had'u sannan ya d'auka yasa cup d'in dai² saitin bakinsa,bashi ya ajiye cup d'in ba sai daya tabbatar ya shanye tas,ruwa yasa a wani cup d'in sannan ya d'auka wani lesser d'in dake d'auke da green d'in magani a cikinsa shima yasa a ruwan sanda ya shanye tsaf kafin ya tattara y'an kayansa ya juyo yana niyyan fitowa,inuwar mutum ya gani tsaye ai kuwa yana sake dubawa sai ganin Sajida yayi tsaye cikin kayan bacci,da alama kuma wani abu ya fito da ita,fuska ya sake d'aurewa sannan ya wuce abunsa ta kusa da ita,rab'awa tayi ta gefensa ta wuce itama zuwa cikin kitchen d'in ba tare data sake kallonsa ba ta wuce ta d'auka ruwa ta sha sannan ta fito ta koma d'akin ta,shima d'in sanda ya koma kwanciya kawai yayi abunsa,bada jimawa ba bacci mai dad'i yayi gaba da shi.
Wasa² sai da yarima ya shafe tsawon ak'alla sati biyu yana dakon amfani da wad'annan magungunan,cikin sati na uku da fara amfanin da shi ya samu YASEER dan lokacin ma maganin nasa ya kaiga k'arewa,yana zaune ranar a office yaji kawai bari yaje gurin YASEER d'in suyi magana dan lokacin ya gama duba patients d'in sa da yayi wa surgery,wanda mafi yawancinsu matsalar fuska ne ko wani b'angare na jiki,a zaune ya iske shi a office shima yana ta fama da duba file's na wad'anda ya yiwa aiki,da sallama ya shiga yana masa murmushi,koda ya d'ago ya kalleshi murmushin yayi masa sannan ya ajiye file d'in dake hannunsa dan yasan ba k'aramin abune ya kawo shi ba tunda ya ganshi cikin office d'insa
"Welcome broah..!"
"Thanks.how about work..??"
"So gratitude.."
"Allah ya taimaka.."
Murmushi yayi masa da fad'in "ameen" sun d'anyi shiru na wani lokaci sannan YASEER ya kalli yanayin Yarima yana so yayi magana Yariman ya rigashi
"Broah..! I was confused..!"
"About what..??"
"Concerning these traditional remedies..!"
Sai da YASEER ya sauke numfashi sannan yace
"Tofa..! What's going wrong..??"
"Nothing.. Kawai dai ina son shaida maka sun k'are ne.."
Wani mugun smiling ya saki da bai shirya masa ba
"Da gaske broah kayi amfani da su duka..??"
Kai ya jinjina masa cike da tabbatarwa da abunda yake fad'a
"Gud..! What about d result..?? Hope u sight some alterations.."
Sakin baki Yarima yayi yana kallonsa,kafin yayi magana
"How zan gane wasu alterations.. Nifa kawai magani aka bani nd ba'a ce nayi noticing wasu fluctuations ba,sai yanzun kamin wannan maganar..??"
Girgiza kai YASEER ya shiga yi yana murmushi kafin ya magantu
"Haba broah..! Kai yanzun sai ance ka kula da chanjin da kake samu,u are a doctor duk wanda zaka ma aiki ko ka bashi magani dole ne ka bashi k'a'idoji da zai kula da lafiyarsa,harma da yadda zai kiyaye kansa,to kaima kamar hakan ne dole ne baza'a rasa wasu canji daka samu ba.."
D'an tunani ya tafi kad'an kafin ya jinjina kai
"Nifa kaga broah babu wasu canjin dana gani.."
"Bazai yiwu ba,taya za kayi amfani da magani sannan kace baka ga komai ba,kawai dai kace ka manta.."
Musawa zancen YASEER ya dunga yi,dan yadda ya kafe yasa YASEER hak'ura akan ya yarda da abunda ya fad'a d'in,sannan ya bashi tabbacin zuwa k'arshen sati zasu wuce Kano dan komawa gurin mai maganin nasa.
Cikin k'arshen satin kuwa suka kamo hanyar dawowa Kano,sai dai ko da suka dumfari hanyar gurin da suka tab'a had'uwa da mai maganin sam suka nene shi suka rasa,haka nan ko labarin sa basu samu ba bare su ganshi,da suka tambayi mutanen da suke wajen kuwa sun tabbatar musu sam ma su basu san da shi ba bare labarin inda zasu same shi.
Hanyar gida suka kama,kowannensu yayi shiru yana tunani,a bangaren YASEER kam cikin zuciyarsa cike yake taf da bak'in cikin AL'AMARI'N dan yadda lamarin ya d'aure masa kai kuwa sam ya kasa sakewa yayi magana,sannan ga yadda ahi kansa Yarima yayi shiru baice komai,wannan yasa shi shiga taradaddi da tunanin kan irin maganar da zata iya fitowa a bakin Yariman, ilaihi kuwa dai² lokacin da yake cikin wannan halin suna cikin tafiya Yarima ya kalli fuskar d'an uwan nasa kafin ya ce.............
*Afuwaan fan's wollah yau nayi niyyan yin typing sosai sai dai bana jin dad'i sosai,kuyi hak'uri da wannan.*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 6.*
^^^^^^^^
Yarima ne ya kalli fuskar d'an uwan nasa kafin ya ce
"Broah..! What's going wrong ne..?? U looks some differing."
Ajiyar zuciya YASEER yayi kafin ya d'ago idanunsa da suka rine da zallan b'acin ran abunda ya faru,dan a d'an wannan tak'aitaccen lokacin da yayi shiru ya gama fahimtar cewa mai maganin nan da suka had'u da shi ba kowa bane face *'DAN DAMFARA* babban dalilin da yasa shi yin shiru kenan nd hakan baya rasa samun nasaba da rashin tabbacin irin maganar da zata iya fitowa daga bakin Yarima.Bai iya samun damar yin magana ba sai girgiza masa kai kawai da yayi alamun babu komai,gani yayi Yarima ya masa murmushi sannan ya samu gefen hanya yayi parking yana k'ok'arin zare belt d'in dake jikinsa,sanda ya raba jikinsa da seatbelt d'in ya fuskanci YASEER da har lokacin ya kasa magana yana cewa
"Look broah..! This affair that happened is nothing to me,ina so kaima ka d'auke shi amatsayin abunda bai faru ba,na sani zaka ji babu dad'i buh kada kayi tunanin zan fad'i wata magana da tayi kama da kwatankwacin ta rashin jin dad'i gare ka,coz banga komai ba,na sani dole ne kayi zargin ko ka tilastani nayi amfani da thus remedies a wancan lokacin,amma na sani babu abunda zai faru sai da izininsa,kuma yanzun'ma da izinin Allah ni banji wani canji a jikina ba ko wani abu daban,so kaima forget about it.."
Dogon numfashi ya saki sannan ya kalli Yarima yana shirin yin magana
"Cool mana,ni ba sai kacemin komai ba,kawai ka manta,let us confront feud..!"
Jinjina kai yayi cikin sanyin jiki,a hankali kuma ya furta
"Am always grateful dana kasance tare da d'an uwa kamar ka,na gode sosai broah da baka yi zargina akan wannan lamarin ba.."
Girgiza kai shima Yariman yayi,yana masa murmushi yace
"Kada ka damu wannan ai duk ba abun damuwa bane,ka manta da shi kawai.."
Jinjina kai yayi shima sannan yayi murmushin,cikin nutsuwa yarima ya maida seatbelt d'in sannan yayima motan key suka ci gaba da tafiya,ko da suka d'auki hanyan ma shiru YASEER yayi,ganin yadda duk ya takura kansa da tunane² sai Yarima ya d'an shiga jansa da hira,tun bai saki jikinsa ba har kuma ya d'an warware suka ci gaba da hira sama².
^^^^^
Yau kam tunda ta tashi da wani irin mugun tunani ta farka jin yadda k'wak'walwarta ke neman haukatata yasa sai taji baza ta iya zaman gidan ba,dan haka koda ta kalli lokaci haka nan ta mik'e ta shiga shirin fita,cikin wani Arabian gown bak'i mai adon jaa ta shirya,sanda ta fito kuwa bata tarar da kowa a parlor ba dan haka key kad'ai ta d'auka sannan tayi hanyar fita,babu kowa a harabar gidan ko data fito bata tsaya tunanin wani abuba tayi hanyar inda motar take Parke,bata saurari komai ba ta shiga ta fice a gidan,tafiya kawai take ba tare data sanma ina ya kamata ta nufa ba,ta jima tana yawo daga kan wannan road zuwa wancan,ganin hakan ba shine mafita a gurinta ba yasa tayi tunanin komawa gida,har ta juya kan motan zata nufi gida zuciyarta ta shiga sanar da ita wani muhimmin abu da take k'ok'arin mantawa da shi,cikin rashin kuzari ta juya kan motan zuwa hanyar da zata kaita Royal palace.
Tafiya kawai take amma duka jikinta babu dad'i,cikin kwanakin nan kam haka take ta fama,wanda a dai² wannan lokacin idan za ace jininta ya hau sama da 180 tabbas baza ta musa ba,dan yadda damuwa tayi mata kamun kazar kuku,lokacin data iso gidan gefen Sajida ta nufa ba tare data samu damar shiga ko ina ba,da zuwanta tayi nocking,koda suka yi arba da Sajida ta ganta sake had'e ranta tayi ganin ko wace ce a tsaye a gurin,hakan yasa jikin Aisha sake yin sanyi dan yanzun kam tasan da wuya ta iya gyara alak'ar dake tsakaninsu,tabbas ta san ta cutar da Sajida harma da rayuwar aurenta,to amma wane hanya zata bi ta magance wannan matsalar..?? Wannan tambayar shi ne tambayar daya fara zuwa mata arai,a hankali ta d'ago kanta ta kalli sajidar dake ta kallonta duk ta kasa ta tsare sai dai ta kasa ce mata komai
"Hello friend..!"
Aisha ta fad'a tana d'an k'irk'irar murmushin yak'e,k'in kulata sajida tayi face wucewa ma da tayi ta bar gurin,bata ji babu dad'i ba dan a yanzun bata da burin daya wuce ace sun shirya da Sajidar coz tana ganin ta wannan hanyar binciken ta zaifi tafiya dai² daga lokacin da suka samu masalaha,a baya ta biyota zuwa cikin parlour'n ta zauna kusa da ita,saurin kallonta Sajida tayi ganin abunda yake shirin faruwa,kafin ta kai ga yin magana kuwa tuni har Aishar ta riga ta
"Please..! Sajida dan girman Allah kiyi hak'uri ki yafe min,wallahi duk wani abu da kika ga ya faru ko na fad'a miki a baya wollahi nayi ne bisa dokin zuciya,dan nasan ko wace ce haka ya faru da ita zata iya yin fiye da abunda nayi,amma dan Allah ina son kada kiyi duba da abunda na aikata miki a wancan ranar,kiyi hak'uri da duk maganganun dana fad'a kinji..??"
Ajiyar zuciya tayi cikin sanyi kuma ta furta
"Babu komai,Allah ya yafe mana baki d'aya,sai dai Aisha ni kaina naso na sanar dake tun fari game da aurena da yah Prince,sam ban san da wannan had'in ba lokaci d'aya Abbanah yake sanar dani cewa sun min miji,kuma koda ya fad'a min wanda za'a had'a ni da shi i felt improper compatible,wollahi kawai dan bani da yadda zanyi ne,amma da bazan yarda ba,umarnin iyaye ne shi yasa na hak'ura nayi biyayya,amma kiyi hak'uri dan Allah..kuma kimin aikin gafara.."
Girgiza mata kai Aisha tayi tana murmushi
"Kada wannan ya dame ki,in dai nice baki da damuwa komai ya wuce,kuma tun farko laifina ne da na tsaya nayi tunanin hakan duk da ban zargeki ba,kuma da banga laifin ki ba..Amma in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba."
"In sha Allah kam.."
Exchange na murmushi suka yi hannunsa rik'e cikin na juna,suka ci gaba da hira akan abubuwan da suka faru a baya,suna cikin hiran ne aka yi nocking,cikin sauri sajida ta mik'e ta nufi hanyan door d'in da niyyan bud'ewa,Yarima ne ya bayyana tsaye gaban k'ofar ko da suka yi arba da juna,a hankali Sajidar ta matsa gefe ta bashi hanya,cikin isa ya fara takawa cikin parlor da yar siririyar maganarta ta furta
"Barka da dawowa..!"
Ba tare daya d'aga kai ba bare tasa ran zai kalleta ya amsa ta can k'asa² y'ana ci gaba da tafiya,dai² zai wuce zuwa corridor ya tsinto muryar Aisha tana yi masa barka da dawowa,d'ago idanunsa yayi dan jin muryar yake kamar ya santa wani wajen daban,nan fa idanunsa suka watsu akan Aisha,ransa ne yayi mugun b'aci sanda ya kalli fuskarta kuma ya tabbatar itance da gaske ba wai idanunsa ke yaudarar saba,waiwayawa yayi ya kalli Sajida data zauna a kusa da Aisha tana murmushi, cikin wani irin voice ya furta
"Ki same ni a ciki.."
'Dagowa tayi da zummar kallonsa saboda taji maganar wani iri,haka nan tana son tabbatarwa da ita yake ko kuwa.? Amma sai ta tarar har ya juya ya bar wajen,tab'e baki tayi sannan ta tashi tabi bayansa dan ta tabbatar babu wanda yake face ita,a bedroom d'insa ta iske shi yana zaune saman resting chair,tana shigowa ya d'ago idanunsa ya zubasu akanta
"Yah Prince gani..!"
Ai kafin ma ta k'arasa fad'a tuni ya fara magana
"Waye ne ya bawa wannan halittar damar zuwa min nan..??"
"Yah Prince Aisha cefa.."
"Ehhenn! Sai akayi yaya dan Aisha ce..?? Na nemeta ne..?? Maza yanzun nan tun kafin na sauke fushi na akanki ki gaggauta zuwa ki sallameta,nd u prove her kada na sake ganin k'afafunta a nan matuk'ar tana son kwanciyar hankali,idan ba haka ba da ke da ita zaku fuskanci fushi na.."
"Amma yah Prince naga Aisha jinin mu...!"
"Keep ur mouth shut.. Ni sa'anki ne ina magana kina k'ok'arin bani amsa,duk ranar muka kuma makamancin haka zaki gane kuskuren ki.."
"Yah Prince to amma fa.."
"Heeyy! Get out,i don't want heard ur words.."
Magana take son yi amma sam ya hana ta yi,dan haka bata da zab'in daya wuce ta fita kamar yadda ya buk'ata,sanda ta fito duk jikinta a sanyaye yake dan sam bata san ta ina zata fara yiwa Aisha maganar ta dena zuwa ba,dama ace kafin zuwanta ne a yau ya ganta lokacin kafin su shirya data san yadda zata yi ta fad'a mata,amma yanzun sai da tazo da niyyan su shirya kawai sai itan kuma tace kada ta kuma zuwa..?? Gaskiya ita kam tana jin baza ta iya yin haka ba,gara dai kawai ta nemi wani hanyar da zata sa ta fahimta amma bawai ta fito kai tsaye ta fad'a mata cewa shi ne baya son tana zuwa ba.
Har ta iso cikon parlour'n bata bar tunani ba game da wannan al'amarin,lokacin data d'ago da niyyan gyara fuskarta gudun kada Aisha tayi zagin wani abu sai taga gurin wayam babu kowa,wannan abu ba k'aramin bata mamaki yayi ba,nan fa tunaninta ya tafi akan ko Aisha'n taji maganar da suka yi da Yarima.
^^^^^
Aisha kuwa lokacin da Yarima ya shigo har ta masa magana,sanda ya kalleta da irin mugun kallon tsanar da yake jifanta da shi ba k'aramin tsoro abun ya bata ba,wannan tasa ko daya kira Sajida tayi zargin abunda zai biyo baya ba mai dad'i bane,dan daga yadda ya kira sajidar ma kad'ai duk wani mai hankali zai gano hakan,shi yasa tun kafin d'aya a cikinsu ya fito tayi gaggawar tattarawa ta bar apartment d'in..
Tun daga wannan ranar kuwa sai ta shiga yin baya² da gidan ma gaba d'aya ba tare data bari Sajida ta fahimci ta gano wani abu ba,sai dai wannan mataki da Aisha ta d'auka sosai ya dad'a jefata cikin halin damuwa dan yanzun kam tasan bata kuma da wata hanya da zai nuna mata hanyar da zata sa ta gano wani daga cikin ahalinta.
^^^^^
A b'angaren Yarima kuwa tun daga lokacin da suka had'u da wannan D'an DAMFARAR mai maganin,bai sake neman wani magani ba,ko mai maganin'ma idan yaji baya ko d'aga kai bare ya kallesu,dan yasan duk zancen nasu a cikin iska yake yawo,a cikin haka ne wata rana yana zaune a balcony ya jiyo wasu mutum biyu a bayin dake
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 63